Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
masa... Ubandoma ya nufosa zai kai masa damk’a Ja’afar ya dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu, murmushi saman fuskarsa ya kwanto da fuskar tasa dab kusan na Yazeed d’in “We shall see..! Bawa d’an Baiwa..!!” Ya kuma murmusawa kad’an lokaci guda ya shiga zagaye tampatsetsten parlorn Yazeed d’in na alfarma, yana k’arema kayan alatu da aka k’awata Parlorn dashi kallo... Ya iso gaban family Picture d’in su Yazeed wanda yake manne cikin parlorn gwanin ban sha’awa... Yai K’uri yana k’arema picture d’in kallo, lokaci guda yake furta “How Pity..! You’re all alone now, they all left you..” Ya d’an girgiza kansa kad’an yana mai yin wani salo irinta tausayawa, lokaci guda yaci gaba da furta “Babu izza..! Babu sarauta..! Babu asali..! Babu mata..! Babu ‘ya’ya..!” Daidai lokacin ya kaikaito sosai yana duban Yazeed kana yaci gaba da fad’in “And what is worse, kaga wannan luxury d’in da kake cikin zakai bankwana da ita a yau domin kuwa angulu zata koma gidanta na tsamiya.. Za’a koma yanda aka fito.. Yankin bayi da Bauta...!” Ya k’arashe idanunsa tar kan Yazeed d’in wanda ya kasa gaskgata abinda yakeji daga bakin wulak’antaccen Bawan da ya raina a baya irin Ja’afar wanda ko yanda ya taka bai isa ya taka k’asar wajen ba, cikin wane irin yanayi yace “Ja’afar..! B’angaren Bayi fah kace.. Ni Yazeed ne zan koma rayuwa cikin Bayi..?!” Ubandoma ya katsesa da fad’in “Hattara D’an Baiwa.. Ba’a jayayya da Yarima..!” Yazeed ya had’iyi miyau da k’yar yace “Yarima..!” Yai maganar da k’yar kaman mai koyon magana.. Ja’afar ya kaikaito yana dubansa yace “Eh b’angaren bayi zaka koma Yazeed domin kuwa nan ne ya kamaceka..! Da ace ka zamto d’ah ga Maimartab watak’ila da an ajiyeka a gidan tsoffin k’wark’warorin Sarakuna wanda suke rayuwa da ‘ya’yensu amma martabarka da darajarka batakai nasu ba, sabida kaid’in ba ahalin gidan nan bane... Jinin k’ask’antacciyar Baiwa ce wacce taci amanan Ubangidanta... A b’angaren bayin ma yankin da zaku zauna kaida sauran ‘yanuwanka idan sun fito daga asibiti bazai kai na sauran bayi daraja ba domin kuwa kud’in maciya amanan masarauta ne...!” Ya k’arashe yana mai maidoda dubansaga Ubandoma... Murya a dake yaceda Ubandoma aima Yazeed rakiya zuwa sabon sashensa.. Daga haka bai kuma tsayawa jiran komai ba yasa kai zai shige abinsa Ubandoma yana fad’in “An gama Rankaidad’e..! Yazeedu godiya yake Rankaidad’e...!” Da tsananin mamaki Yazeed ya koma tamkar an dasa a wajen yake duban Ja’afar har ya b’acewa ganinsa, ya nemi hawayen da suke zubo masa ya rasa, Ashe kuka ma rahama ne... Ji yayi inama zai iya ci gaba da kukan da yake da sai yafi masa sauk’i... Yanaji Ubandoma ya kamo hak’ark’arinsa ya mik’ar dashi tsaye yana fad’in “Maza a koma tushe, a koma yanda aka fito...” Wai yau shi Yazeed, shi Prince Zeed ne aka maidosa sashen Bayi na cikin Masarautarsu... Masarauatr da yaci burin Mulka kowa ya zamto yana k’asa dashi sai gashi kowa ya zamto sama dashi, harta bayin da yake ganinsu k’ask’antattun yau sun fisa daraja a cikin Masarautar sa... Giwa itace Ta jawo masa wannan k’ask’anci wanda gwara ya mutu da yaga irin wannan rana...Gwara ya kashe kansa da yaga irin wannan takaici.. ** Jiki a matuk’ar sanyaye ta nufi sashen Gimbiya Turai tana ganin hanya na had’e mata kalaman Ansar suna kuma buga kwanyarta _Ked’in sayoki yayi, satoki yayi, bakida wani daraja a idanunsa kuma bazaki tab’a yin daraja a idanunsa ba, k’arfin mulki ya nuna akanki, don yayi amfani dake kawai wajen cimma burinsa ya dawo dake cikin Masarautar.. Kuma burin nasa ya cika tinda kika taimaka masa ya fidda Giwa da ahalinta daga cikin Masarautar_ SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *79* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A parlor ta tadda Gimbiya Turai taredasu Umaima da Zahra, Hadimai sai sintiri suke tsakanin sashen ana kawo mata kyauttutuka daga matayen masu muk’amin gargajiya kaman yanda yake a al’adance... Yanayin da sukaga Muhibbah ciki sosai ya basu tsoro, Umaima ta mik’e da sauri ta isa ta kamo hannunta tana tambayarta meke faruwa.. Duban Umaima takeda idanunta masu zuban ruwa, lokaci guda Ta rungume Umaima kuka na kuma kufce mata... Zahra da Umaima suka dubi juna yayinda Gimbiya tai alamawa Hadiman da hannu cewa su fice su basu waje... Hannun Muhibbah Umaima ta kamo suka k’araso saman Darduman da suke zaune bisa itada Zahra kana ta zaunar da Muhibbar... Zahra ta matso had’ida mata k’uri murya a hankali take furta “Tia.. Is all well..? Lafiya kike kuka haka..? Kodai Giwa ce ta dawo cikin Masarautar..? Talk to us please..!”Ta k’arashe fuska fal damuwa... Umaima Ta kamo hannun Zahra tana mata alamu da ido kan tai shiru ta daina jerowa Muhibbah tambayoyi irin haka... Gaba d’aya sukai mata K’uri suna duban yanda take k’ok’arin daidaita kanta tana share hawayen dake mak’ale cikin idanunta... D’agowa tai ta dubi Gimbiya Turai, muryarta na tsananin rawa tace “Ummi da gaske Rankaidad’e ne ya aureni..? Da gaske shine mijina..?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Zahra da Umaima suka dubi juna suna masu shan jinin jikinsu... Gimbiya tai masu umarni su fice su basu waje itada Muhibbah.. Jiki a sanyaye Umaima ta janyo hannun Zahra suka nufi k’ofa, Zahra na fad’i k’asa k’asa “Kina tunanin bazata amince da auren Paa d’ina ba.. But I thought they loved each other.. And they’ll make a perfect couple together...!” Ta k’arashe cikeda kulawa.. Umaima ta girgiza kai kad’an tace “Just shut up Zahra, and stop meddling...” Zahra ta sauk’e huci a hankali tana mai kuma juyowa tana duban Muhibbah dake duk’a gaban Gimbiya Turai cikeda mamaki, ita gani take idan Muhibbah tak’i Paa d’inta sam bata kyauta ba.. Su Zahra suna ficewa Gimbiya Turai ta saka hannayenta biyu ta kamo Muhibbah ta d’agota had’ida zaunarta gefenta, saida Ta bari natsuwa ya d’an kuma sauk’a mata kana Ta soma fad’in “Mahmood shine ya aureki Muhibbah..! Amma ki sani akwai sharad’inmu dashi, sharad’in kuwa shine idan baki so zaa warware wannan aure kafin ai masa nad’i...” Muhibbah Ta saka hannunta ta goge ragowar hawayenta jiki a sanyaye take duban Gimbiya Turai wacce itama itad’in take duba... Janyota tai cikin jikinta tana shafa bayanta a hankali alamun lallashi... Suna a haka Hadimar Muhibbah Ta shigo Ta risina, ta mik’a gaisuwarta kana tace “Ki gafarceni Rankidad’e.. Mai Martaba yayo aike.. Kinada sak’on kira daga garesa..” Zuciyarta yai wani irin tsinkewa, Ta d’ago tana duban Gimbiya Turai.. Jinjina mata kai tai tace “Maza tashi kije, kuma kar kisa wani damuwa ma ranki... Bazan bari wani basarake ya miki dole ba, share hawayenki maza ki tafi ki amsa kiran nasa..!” Ta mik’e da k’yar tana mai gyara zaman alkyabbarta.. Lokaci guda tasa kai Hadimar tata na biyeda ita.. ** Tinda Ta shigo sashen nasa gabanta Ke tsnananta fad’uwa, tana k’arasowa Barde ya soma mata kirari da jinina yana mai sanar da ita Rankaidad’e yana farfajiyan samansa yana jiran isowarta.. Batareda ta amsashi ba ta haye sama jikinta a matuk’ar sanyaye ga zuciyarta dake ci gaba da bugu... Yana zaune saman Darduma ta alfarma wanda aka k’awatasa da manyan pillows na alfarma irinta gidajen masu Mulki... Kanta a k’asa take takowa tanajin bugun zuciyarta na k’aruwa lokaci guda tanajin kalaman Ansar suna kuma Yawo a cikin kanta da kunnuwanta suna neman tarwatsa mata kwanyarta... A haka take had’e hanya dan wani irin fuzga takejin zuciyarta na mata... Ji tai kaman wacce ake turata da k’arfin gaske, taji wani irin jiri na k’ok’arin kaita k’asa... K’iris ya rage bata zube k’asa ba sai tsintar kanta da tai cikin hannun Rankaidad’e.. Ta bud’e idanunta tana dubansa, shid’in ita yake duba fuskarsa dab nata kaman tsinin hancinsu zai had’e... Dukda kyaun halitta da k’warjini da fuskarsa nasa kedashi hakan bai hanata tuno abinda yayi mata ba, ya auorta zuwa Masarautar a wulak’ance domin cikar burinsa.. Hawaye suka gangaro mata lokaci guda tana mai kauda fuskarta gefe... Ya jima sosai yana dubanta cikin hannunsa kafin ya mik’arta tsaye yana tambaya a hankali “Are you hurt..?” Ba tareda ta dubesa ba ta girgiza kai alamun a’a... Hannunsa guda taji saman nata ya kamo hannun nata ya nufi saman shimfid’ar da ita... Ta dubi hannun nasa yanda ya rik’o nata hannun cikin nasa... Ta kasa janye idanunta har saida yai masu masauk’i saman Dardumar ta alfarma... Zamansu yai daidai da shigowar wayan Turaki, ya mik’e ya d’an taka kad’an zuwa jikin fence ya bata baya yana amsa wayar wanda bazai shige kan sak’on da ya bawa Turakin bane Sai lokaci ta sami zarfin d’agowa ta dubesa, sanye yake cikin tufafi irinta masu mulki, Riga da wando na kufta mai ruwan k’asa wanda suka sha kwalliya da surfani mai ruwan zinari, kansa babu hula sai kwantattun sumarsa bak’i wuluk Sai shek’i suke... Ta kauda fuskarta a hankali tana k’ok’arin nitsa zuciyarta, lokaci guda tana mai kuma aminta da batun Ansar ko kusa kar ta yarda da wannan wulak’antaccen auren,.. Tayi nisa duniyar tunani bama tasan ya k’araso ya zauna ba sai muryarsa ta sinkayo yana furta “I need all your attention here your Highness..” Ya fad’i daga nan yanda yake a kishingid’e yana murza zobban hannunsa... Ta d’ago ta d’an dubesa hawayen mak’ale cikin idanunta, ji tayi wani irin k’warin gwiwa na zuwa mata dukda wani irin abu da yake fuzgar zuciyarta wanda bazatace ga abin ba...Cikin murya mai rauni had’ida zafin nama take furta “Why your Highness..? Maiyasa..? Sabida kayi amfani dani ka toni asirin Giwa da ‘ya’yanta cikin Masarautar nan shiyasa ka sayoni daga wajen Yawale..? To fulfill your own mission...? Maiyasa ku masu mulki kukeda zalunci..? Maiyasa baku duba buk’atan kowa sai kanku..?! Maiyasa kanku kawai kuka sani..?! Mai yasa baku damu ba who’ll get hurt..? Maiyasa baku damu ba..!” Mahmood dake murza hannunsa kad’an yana jin kalamanta suna tsananin masa zogi cikin zuciyarsa, cikin wane irin daka tsawa ya katseta da fad’in “Enough..! Ya isheki haka..! You don’t know anything, so you better hold it right there..!” Ya k’arashe yana sakin huci... Kukan da take rik’ewa ya kufce mata, Ta shiga girgiza kai tana hawaye.. Lokaci guda take furta “This isn’t fair..! It isn’t fair..!” Ta yunk’ura zata mik’e Ta fice cikin sauri rik’eda bakinta wanda kuka ne kawai ciki...Bata ankara ba saiji tai ya fuzgota Ta fad’o cikin jikinsa... Sosai take kuka tana k’ok’arin cire jikinta daga nasa, bai saketa ba saima dad’a matseta da yayi har saida yai tunanin kar ya karya mata wani k’ashi... Saitin kunnenta yake maganar cikin fuci mai yanayi da rad’a “Ba’a tashi gaban Sarki sai yaba da izini.. You lack manners... Ki koyi yanda zakike magana dani idan har kina son samun amsoshinki... Kin fahimta..?!” Ya k’arashe yana mai sassauta rik’on da yai mata... Wani k’arfin hali ne taji yana zuwa mata, ta shiga b’anb’are hannun nasa daga cikin jikinta take furta “Ban amince da wannan auren fin k’arfin ba kuma bazan tab’a amincewa ba... Your Highness..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin cire jikinta... Tsam ya rik’e yatsun hannun nata, yai amfani da d’aya hannunsa ya janyota ta kuma fad’owa cikin jikinsa, hab’arsa ya aza kad’an saman kafad’arta, cikin sigan rad’a yake ci gaba da furta “Haven’t they informed you yet.. Sarki baya saki, idan kika shigo kin shigo kenan.. Prepárate para convertirte en mi reina (Kiyi shirin zama Sarauniyata) Y prepárate para realizar todos los deberes de una mujer casada.” (Sannan kiyi shirin sauk’e duk wani nauyi da ya rataya bisa matar aure) Bata fahimci kalamansa ba kasancewar cikin harshen spanish yayi, saidai ta tsinta kalmomi da baza’a rasa ba... Tana jin sanda ya sakar mata hannu ba tareda ya kuma bin takanta ba ya koma saman darduman yai zamansa lokaci guda yana mai saka apple cikin bakinsa... Tai tsaye tana mamakin k’arfin hali na wannan Basaraken... Kaman bashi bane ya ida magana ko kallon b’angaren da take bai kumayi ba kaman bashi a wajen... Kanta a k’asa ta juya ta fice daga wajen wasu hawayen na kuma gangaro mata.. Ba ma kanta take wannan yak’in ba wa Ansar take domin kuwa sam bai cancanci haka ba.. Rankaidad’e k’arfin Mulki kurum ya nuna masa ya samu Baffah Yawale mutum ne mai son duniya shiyasa yai sauk’in shawo kansa, sannan babu riba cikin auren da babu soyayya tinda ba sonta yake ya aurota ne kawai dan wani buk’ata ne nasa... Tana tafe taji ta bangi mutum, ta d’ago tana dubanta ba kowa bace face Raheemah... Raheemah tai mata K’uri murmushi saman fuskarta lokaci guda take furta “Muhibbah... Ko ince Rankidad’e.. Long time no see.. Kodashike ku matan sarakuna dama da kulle aka sanku..!” Muhibbah dake tsananin huci tana duban Raheemar bud’e baki tai da niyyan magana Raheema Ta dakatar da ita da fad’in “A’a’a no.. Don’t you dare..! Bakida wani excuse Muhibbah.. Kin tona mana asiri nida Yazeed dan kawai ki mallaki Mahmood ma karan kanki... Good burinki ya cika kin zama matar Yarima Mahmood kuma Sarki mai jiran Gado...!” Ta d’anyi fasali tana mai murmusawa, lokaci guda taci gaba da fad’in “Ashe dai ba ni kad’ai maci amana ba... Ni k’awata naci amana kekuwa amanar soyayya kikaci.. Amanar mutanen da suka zamto fitila ga rayuwarki... How shameful ba’a San jinin babban gida da cin amana ba..!” Ta k’arashe tana yatsina fuska... Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Koda wasa kar ki kwatanta kanki dani, balle abunda Kika aikata.. Ked’in kinci amanan mahaliccinki ne bayan ya baki amanan kanki, kinga kuwa cikin mu biyun kinfi dacewa da akiraki da maci amana..!” Dukda kalaman Muhibbah sun mata zafi hakan bai hanata furta “Admit son Mahmood kike.. Ai dama na fad’a tun farkon zuwanki idonki akansa suke...Kin yaudare mutumin da ya shafe shekaru yana dakon soyayyarki... Kin cika butulu Muhibbah..!” Cikin sauri Muhibbah tasa kai zata shige sabida zuciyarta dake tsananin tafarfasa, Raheemah tai saurin tare gabanta tana furta “Fuskarki ya nuna komai Muhibbah... Idan har bada biyu kika toni asirinmu da Yazeed ba, idan har ba don ki mallaki Mahmood kikayi haka ba, idan har ba don kici amanan masoyinki na gaskiya kikayi haka ba.. Toh kisa Mahmood ya sawwak’e maki kafin ai masa nad’i kafin ayi bukin tarewarku domin kuwa muddin akai masa nad’in sarauta bazai sakeki ba sannan ko da ace ya sakeki zaki k’are rayuwarki ne gidan tsaffin matayen sarakuna bazaki tab’a auren wanda ranki yake so ba. Bazaki tab’a auren masoyinki ba har abada domin kuwa haka k’a’idan sarautar yake..! Idan har kin cika jinin sarauta d’iyar masu mulki, idan har jinin yana Yawo a jijiyoyin jikinki bazaki tab’a zama mayaudariya maci amana ba, idan har kin cika duk abubuwan dana zayyano Yo kiyi proving... ki nuna min ba sabida amfanin kanki kika tozartamu nida Yazeed a idanun duniya ba.. Kiyi abinda ya kamata kafin wa’adi ya cika miki Muhibbah..!” Ta k’arashe tana mai gyara zaman alkyabbanta kana ta nufi b’angaren Yazeed zuciyarta na mata wani irin sanyi, don tasan ko shakka babu kalamanta zasuyi tasiri a zuciyar Muhibbah... Ga tsananin mamakin Raheema a gark’ame taga k’ofan sashen... Ta dubi wasu bayi dake zaune gefe tai alama wa guda d’aya ya k’araso cikeda risinawa “Yarima Yazeed fah..?!” Ta tambaya tana dubansa, Bawan yace “Allah taimakeki ai Yazeedu zakice, yanzu bashida maraba damu k’ila mun fisa..” Raheemah ta katsesa da fad’in “Ba wannan na tambayeka ba.. Shin ina yake..!” “Tuba nake Rankidad’e, Wato Yazeed dai ya koma b’angaren can..!” Yai mata alama da hannu Ta sashen Bayi.. K’irjinta yai wani bugawa, Ta dubi hannun nasa da mamaki tana mai girgiza kai cikeda shakku take furta “Ban fahimceka ba.. B’angaren Bayi fah kake nuna min..!” Hadimin ya kuma jinjina kai yace “Haka ne Allah shi taimakeki... Can ya koma b’angaren Bauta da bayi..” Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa, Wai Yazeed Yazeed dai Prince Yazeed a b’angaren bayi... Afujajan ta janyo alkyabbarta ta nufi b’angaren Bawan na kuma risina mata.. Tana isa sashen ta soma yatsine yatsine tana toshe hanci dan wari yake mata a cewarta... Taga wasu ‘yanmata guda biyu sunyi tsaye suna lek’en wani rub’ebb’en d’aki, da alama lek’en Yazeed d’in suke suna gulmarsa... D’ayan har tana cewa “Ashe da rabon a samu kyakkyawan Bawa irin Yarima Yazeed..!” Ta had’iye sauran maganan nata sanda Raheemah ta k’araso wajen.. Gaba d’aya suka duk’a suna gaidata...! Da tsawa tace dasu duk su b’ace daga wajen kana Ta nufi cikin d’akin tsoro da Al’ajabi na kuma kamata.. Zaune taga Yazeed dirshan tamkar mutum mutumi bai um bai um um... Jiki na rawa Raheemah ke dubansa daga nan yanda take tsaye “Zeed..! Zeed is that you...?” Tai saurin k’arasowa had’ida duk’awa gabansa cikin tsananin rawar jiki, murya na rawa take furta “C’mon talk to me Yazeed, Wai da gaske kaine a nan..? Yazeed why..? kan mai zaka k’ask’antar da kanka ka kawo kanka cikin wannan dottin.. Look dubi everywhere is liking.. My Goodness you might catch infection here..!” ta k’arashe tana d’aga kai sama tana duban gajiyayyen d’akin a yatsine... Lokaci guda Ta soma k’ok’arin mik’ar dashi tsaye tana furta “You don’t belong here Yazeed... Tashi mu tafi..” Tarjewa yayi yak’i tashi... Raheemah Ta juyo tanai masa duban mamaki, lokaci guda Yazeed Ke furta “Let me be.. this is where I belong after all..! My life is completely ruined... I have nothing left Raheemah... I don’t want live anymore.. I’m sick and tired of this miserable life I’m living now... Pls end my life Raheemah, just kill me please..!” Ya k’arashe wasu irin hawaye na zubo masa... Take Raheemah ma taji hawaye na zubo mata, lokaci guda take girgiza kai tana furta “No Zeed, this is not the end of it... Bazan barka a nan ba, You’re still that prince with so much pride and power..! Yazeed please ka tashi mu tafi..!” Dubanta yayi da kod’add’un idanunsa kana yace “I’m worthless now, bazan amfani kowa ba, kowa guduna yake even my friends left me.. Kema nasan you’re just faking it... You love Mahmood, kawai dan babu yanda kika iya ne... And you’re doing all this out of pity... Kuma kin sani duk duniyar nan babu abinda nafi tsana kaman naga wani yana jin tausayina.. The moment na koma abin tausayi shikenan rayuwata ta k’are.. And that’s exactly what I’m now..!!” Ya k’arashe wasu hawaye na gangaro masa.. Raheema ta dubi hannayensa guda biyu tana mai tabbatar da abinda yake fad’i lokaci guda yake furta “But you still have me Yazeed.. I’m your wife ka mance...!” Yai murmushi mai ciwo yace “Kar mu yaudari kanmu Raheemah.. Na tabbata daga yanzu jin kanki kike way too outside my world, we are not in the same league anymore... so please , just go and leave alone...!” Share hawayenta tai tace “You know what I don’t give a crap about Mahmood anymore.. Kuma Wllhi sai na tarwatsa Farin cikin da yake k’ok’arin ginawa, kar ka damu Zeed zan d’aukar mana fansa kan wad’anda suka wulak’anta mu... Kuma sai kayi alfahari dani..! Tashi muje to your favorite place..” Ta k’arashe tana mai kamosa ta d’agosa tsaye.... ** Ubandoma ya dubi Ja’afar sanda driver ya ida parking dalelliyar BMW X6 sai walk’iya take.. Yaci Uban gayu kana ganinsa Kaga d’an masu muk’ami... Ga wasu zuk’a zuk’an dogari har guda biyu biyedashi.. Ubandoma na daga b’angaren damarsa suka nufi ward d’in da aka ajesu Jamal bayan sunsha surgery an ceto rayuwarsu... Gadajensu ne guda uku a jere, na Giwa daga farko sai na Jakadiya.. Na Jamal kuwa na daga d’aya b’angaren labule ne ya raba tsakaninsu... SameenaAleeyou📚 SameenaAleeyou📚 *MUHIBBAH* *80* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ko duban b’angaren da Giwa take Ja’afar beyi ba a cewarsa ziyaran na Jamal ne... Muryar Giwa ce ya soma masu sallama a galabaice sanda suka shiga Sai fad’in muggan abubuwan da tayi take... Idan tayi tayi sai ta k’ara da ihu tana fad’in ta shiga uku... Likitan ya dubi su Ja’afar da Ubandoma yace haka nan ta Kwana tana wanann sunbatu tunda aka fito da ita daga surgery... Gaba d’aya ta damesu ta cika masu kunnuwa... Ja’afar ya girgiza kai a hankali ba tareda ya furta komai ba, Ubandoma ne yace “Ai Izzatu Ta tapka ta’asa a doron k’asa dan haka duk abinda kace tanayi likita bazanji mamaki ba... Allah Ubangiji yasa mufi k’arfin zukatanmu..” Likita ya amsada Ameen... Can yanda Jakadiya Ke kwance Ubandoma ya k’arasa, shi kuwa Ja’afar yana nan jikin gadon Jamal yayi tsaye yana k’arema Jamal d’in kallo yanda ya koma abin tausayi lokaci guda... Likitan ya k’araso gefen Ja’afar ya tsaya yana masa bayanin ciwon Jamal d’in dan sosai k’unan nasa ya shiga deep harma ya d’ara na Giwa da Jakadiya da k’yar akai masa aiki aka samu fitsari Ke fita kad’an kad’an daga mafitsaransa a haka ma saida taimakon katata kafin ciwon nasa ya warke aga abinda hali zai, gaba d’aya ya koma tamkar wani halitta ta daban... Ja’afar ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yace “Yanzu Dr kanaga zai iya kaiwa yaushe kafin ya farka..?” Dr yace “Ai ko d’azu ma ya farka, shi kuma duk farkawan da zai toh da tsinuwa da la’antar mahaifiyarsa yake tashi, kaji irin tashin hankali da wad’annan bayin Allah suke ciki..!” Nanma girgiza kai kad’an Ja’afar yai yana mai kuma duban Jamal da tsoron duniya... Dr na matsawa da kad’an Jamal ya bud’e idanunsa yana duban Ja’afar dake tsaye kansa... Yai ma Jafar K’uri idanunsa suna rinewa zuwa ja... Cikin wane irin yanayin murya mai tsananin rawa ya furta “What brings you here..?! Kazo ne kaga yanda na koma..? Kazo ne ka tabbatar da idanunka..? Well, gani nan ga yanda na koma.. K’ask’antacce muskini saika zuba ruwa a k’asa kasha.. And don’t you dare think of taking my wife away from me, dan bazan tab’a bari hakan ta kasance ba.. Umaima tawa ce, she’s my wife, she and I are married.. You better stay away from my wife..!!” Ya k’arashe kaman zai finciko Ja’afar d’in sabida yanda yake tsananin tururi... Tinda ya soma magana Ja’afar bai furta koda kalma ba har ya ida sunbatunsa cikin zuban hawaye, hannu Ja’afar ya zaro paper da pen cikin aljihunsa ya aje gefen Jamal fuskarsa a matuk’ar murtuk’e ya furta “Write..! Rubuta mata tun muna mu biyu nida kai..!” Jamal ya dubi takardan ya kuma dubi Ja’afar yace “Do you think I’m that stupid, well you’re mistaken your Highness idan kana tunanin zanyi abinda kake umarta na... Never bazan tab’a rubutawa she’s mine..!” Ciki wane irin huci Ja’afar ya kwanto da fuskarsa tamkar zai shak’o wuyan Jamal d’in yake furta “Don’t you test my patience..! Idan kana son kanka da lafiya ka rubuta tun muna mu biyu a nan wajen, don idan ba haka ba ni nan zan tabbatar maka ba kai kad’ai ne keda ilimin mugunta ba.. Bakaji azaba ba duk wannan rad’ad’in da kake ciki har sai ka bari ka shigo hannuna baka aikata abinda na umarceka ba.. Sannan ne zaka San the real meaning of the word pain..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Ga tsananin mamakin Ja’afar murmushi saman fuskar Jamal ya gani irin na ko ajikina, lokaci guda yake furta “Babu abu mafi zafi da d’aci a duniyar nan da na fuskanta kaman rabuwa da rayuwata ta baya... So duk abinda zaka min duk kalan horon da zaka min na shirya amsan sa idan dai akan abu guda d’aya tak da ya rage min a duniyar nan ne.. Umaima ita kad’aice ta rage min kuma kaji na rantse maka ko kotun duniya zaka kaini gaban Alk’alin duniya saidai ka kaini amma bazanyi abinda kake umartana ba... Ka fahimta..?!” Ya k’arashe yana sakin huci... Ja’afar d’inma huci kurum yake yana dubansa lokaci guda yake furta “You want battle..? Then I’ll give you war.. And don’t forget I’m the one with power now..!!” Daga haka mik’ewa yai ya nufi k’ofa cikin sassarfa kaman zai kifa k’asa yana iya sinkayo muryar Giwa tana fad’in “Ku kira min d’ah na Mahmood yazo ya kaini asibitin k’asar waje a sake mun fuska.. K’arya Izzatu tazo Ta shera masa, Mahmood d’ah na ne..!!” Ko takanta Ja’afar baibi ba yayi ficewarsa... Ubandoma ne ma ya biyeta da furta “Hattara k’ask’antacciyar Baiwa, Butulu la’antar Allah da tsinuwarsa su tabbata gareki kin cutar da Sarauniya Giwar Amale Gimbiya d’iyar masu mulki... Allah dai ya kwashe miki mushirika..!” Jakadiya tana kiran Ubandoma tana fad’in ya taimaketa ya canza mata d’aki kar zunuban Giwa da Jamal suci gaba da bibiyarta dan Ta tabbata yanda suke tsinema juna cikin d’akin bala’i na gaba nan tafe garesu.. Ya taimaka mata yasa likitocin su canza mata d’aki... Ubandoma ya dubeta yace “Ni... Tare na ganku, dama duk wanda yace tukunyar wani bazai tafasa ba toh fa nasa ma ko zafi bazai ba... Allah ya kawo sauk’i Talle kar Ki damu na yafe marin da kika min bazan rama ba.. Kiji da wannan kawai..

Chapter 56 of 65