gaba da tafiya ba yanda taso ba... A halin yanzu nad’in sarautar Mahmood da auren Jamal da Umaima ne kawai take tinanin Sune sa’arta na k’arshe, amma kam b’acewar Izzatu da Jafar harmada Ubandoma ba k’aramin d’aga hankalinta hakan yayi ba... Daga ita har Waziri an rasa mai dannan wani... Shima a nasa tinanin lokaci ya kusa da zai juya mata baya dan a nasa tsarin da zaran sun kauda Mahmood Karagar tasa ce ko kusa bazai bari Yazeed ya d’ale Karagar ba... Wannan k’udiri nasa ya jima cikin zuciyarsa tun ba yanzu ba...
**
A b’angaren Yarima Mahmood kaw tinanin abubuwan da Turaki ya fad’i masa sun kasa b’acewa daga kwanyarsa... Kullum cikin tunani yake, kalaman Turaki na k’arshe su suka tsaya masa a zuciya _”Abinda kake k’ok’arin yi cin amanan masarauta ce, cin amanan Ahalinka ne.. Cin amana Al’ummanka ne..! Cin amana Zuciyarka ne..”_
Ya kuma lumshe idanunsa a hankali yana mai aje pencil d’in da yake sketching dashi... Ya mik’e yana zaga farfajiyan benen nasa lokaci guda yana tunanin abinyi... Wata zuciya tace ka sami d’iyarka da batun kar rana tsaka taga zaku koma Spain Ta kuma zarginka da wani abin...! Ya kuma sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana yayi kiran Hadiminsa yace a kirawo masa d’iyarsa Zahra...
Babu jimawa Zahra ta shigo kanta a k’asa ta duk’a ta gaida mahaifin nata... Ya amsa mata da sakin fuska kana ya nuna mata gefensa yace tazo Ta zauna...
Ta d’an d’ago idanu ta dubesa daga nan k’asa yanda take zaune kana tace “Paa kaifa Maimartaba ne yanzu...!”
Ya murmusa kad’an yace “Kema Maimartaba ce, Zo ki zauna...!”
Ta mik’e cikeda jin nauyi ta isa ta zauna a d’arare ba kaman yanda ta saba a baya ba domin kaw tabbas mulki ba k’arya bane akwaita da gizo... Mahmood ya karkato kad’an yana dubanta kana yai gyaran murya ya soma fad’in “Zahra Ina son Ki sani duk abinda nakeyi sabida Ke nakeyi, bazanyi abinda zan cutar dake ba... Kuma bazan yanke shawarinda bazai miki amfani ba..!”
Yanda yake maganan gaba d’aya sai yasa jikinta yin sanyi, Ta d’an d’ago idanunta masu rauni tace “Paa you’re starting to scare me now, just tell me ko menene nasan bazaka cutar dani ba.. Aunty Muhibbah tace a koda yaushe na kasance mai kyautata zato wa mutane and especially to you Paa, coz you’re my Father and you love me unconditionally...But with the way you’re talking Paa, sai ina jin tsoron abinda zai fito daga bakinka.. You become totally irrational tinda muka dawo k’asar nan... Paa what exactly are you afraid of telling me..?!” Ta k’arashe cikin raunin murya..
Sirhitaccen murmushi saman fuskarsa yake dubanta, cikin zuciyarsa yana kuma nanata sunan Muhibbah... Lokaci guda ya jinjina kai yace “Your Tia was right... Ina k’aunarki sosai kuma bazanyi abinda zai cutar dake ba..! Zahra, Decidí que volveremos a España tan pronto como me case con Raheema..” (Zahra na yanke shawarin zamu koma Spain da zaran na auri Raheema)
“We’d have a new life there the three of us..!”
Da tsananin mamaki Zahra ke dubansa... Ta d’an girgiza kai tace “Is that really necessary Paa..?, Wai zamu sake komawa Spain, kuma da matar nan...But Paa...”
Katseta yai da fad’in “It’s for the best Zahra.. I promise..!”
Kaman zatai magana sai kuma tai shiru cikin tsananin sanyin jiki take furta “Alright..!Shikenan ..! Si tú lo dices Paa” (Idan kace haka Paa)
Lokaci guda ta mik’e ta d’an sadda kanta tace “Na Barka lafiya Papa..!”
Ya jinjina mata kai a hankali yana mai binta da kallo har ta b’acema ganinsa...
A hanya Muhibbah Ta hangeta tana tafe tana matsan hawaye, babu shiri tabi bayanta tana tinanin mai ya faru da ita kuma...
Can k’asar wata bishiya Zahra Ta k’arasa Ta zauna tana ci gaba da kuka a hankali... Muhibbah ta k’araso ta d’an dafata kad’an “Are you alright..?!” Ta tambaya tana duban Zahran...
Mik’awa Zahra tai Ta rungumeta sosai tana mai ci gaba da kuka...
Muhibbah dake tsaye tamkar statue tana sauraron kukan da yarinyar keyi har cikin zuciyarta, a hankali Ta soma lallashinta tana tambayarta meke faruwa..?
Zahra tasa hannu ta goge hawayen da suka jik’a mata fuska “My Paa have decided we’re leaving back to Spain bayan ya auri wannan witch d’in...!!” Ta k’arashe tana sakin huci wasu hawayen na kuma gangaro mata...
Kaman sauk’an aradu haka Muhibbah taji batun “Zaku koma Spain... Wait he can’t do that... I mean your life is right here...!”
Zahra Ta jinjina kai tace “I don’t want to leave with that woman.. I don’t want her in our lives... Dik iyaka k’ok’arina naga na sota ko kad’an ne wllhi banjin sonta, kullum k’ara tsanarta nake... And and what’s worse is that.. I don’t want us to be separated.. Idan muka koma Spain shikenan bazan sake ganinki ba Tia..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka...
Janyota Muhibbah tai ta rungumeta kad’an tana lallashinta “Everything will be alright in sha Allah... kinji Ki kwantar da hankalinki....!”
Zahra tai shiru cikin k’irjinta tana ci gaba da ajiyan zuciya Muhibban na shafa kanta a hankali, su duka biyun zukatansu na bugawa...
So wannan shine dalilin da yasa Rankaidad’e ya dage da batun auren matar nan lokaci guda... Turai zasu tafi tare, ashe kenan bazai tsaya a nad’asa Sarauta ba... Hakan na nufin idan ya tafi wani zai maye gurbin Sa ya zamto Sarki... Toh waye zai maye gurbin nasa..? “YAZEED” sunan da zuciyarta ya raya mata kenan... Take Ta shiga girgiza kai tana ayyanawa cikin zuciyarta bazata tab’a bari hakan ya kasance ba... Yazeed bazai zama Sarki ba koda na rana guda ne... She needs to come up with something as soon as possible...! Ta k’arshe tana tunanin Menene abinyi...
**
A can Masarautar su Raheema kuwa Amarya gyara ake da shirin biki babuji babu gani dikda cewa Yazeed ya tak’ura mata da waya akan sai ta dawo masarauta sunyi final goodbye da juna... Yau d’inma wayace mak’ale kunnenta anai mata gyaran jiki tai excusing kanta tana mai ci gaba da amsa kiran nasa “Wai mai kake nema a wajena ne prince... Na zaci munyi sallama ai..!”
Yazeed ya murmusa kad’an yana shafan hab’arsa yace “Rankidad’e Amarya hak’uri zakiyi ki dawo masarauta muyi proper goodbye, I’m not even sure idan zan iya barinki wa Mahmood gaba d’aya..!”
Fuzar da huci tai tana mai rausayar da idanu tace “Kaga Yazeed I’m not in the mood to play such game with you, it’s over between us.. Dan Allah ka k’yaleni najida..!”
Katseta yayi da fad’in “And who’s playing games with you...!! It’s not over, until I say so..! Ki dawo Masarauta muyi sallaman k’arshe idan har kinaso Mahmood ya zama naki..!”
Ta fuzar da fuci kad’an tana mai dafe kanta tace “But mai zance... Ta yaya za’ayi na d’auki k’afafu na tafi Masarautar su mijina tun ba’a d’aura aure an kawoni ba... Kasan yanda abubuwan sarauta suke yanzu yin hakan sai ya zama wani babban scandal..!”
Ya katseta da fad’in “Come up with something.. Ba Yayarki tana Masarautar ba, kuma akasarin zamanki tinda yayarki tai aure ya dawo wannan Masarautar ne..Sai kisan k’aryar da zakiyi kizo idan kuma ba haka ba..?!” Yai wata murmushi ba tareda yace komai ba...
Cikeda k’osawa tace “Fine naji... Zanga mai zan iyayi...!”
Yazeed yace “Bawai zakiga mai zaki iyayi bane... Dole Ki Zo, ko dan samun zaman lafiyarki da kwanciyar hankalinki.. Mu had’u gobe a yanda muka saba had’uwa..!!”Daga haka katse kiran yai ba tareda ya kuma sauraronta ba...
Muhibbah dake mak’ale jikin staircase tsaf taji tattaunawar Yazeed da Raheema, cikin sand’a tai k’ok’arin ficewa daga sashen ta fasa shigewa...
D’aki Ta komo tana tinanin mafita, ta tina Yazeed yaceda Raheema su had’u gobe a yanda suka saba had’uwa basai ta shigo Masarautar ba dan gudun maganganun mutane... Hakan zaisa babu wanda zai gane ma tazo Masarautar koda kuwa Yayartace Gimbiya Zeenat...
Muhibbah ta k’ume a d’aki tana tinanin abinyi, wata dabarace Ta fad’o mata... Kai tsaye D’akin Zahra ta tafi yanda ta tadda Zahran na baiwa wasu bayi guda biyu umarnin su sorting wasu stuff d’inta alamun ta saduda ta soma shirya kayayyakinta dan tafiya k’asar Spain dake gabansu... Tana ganin Muhibbah ta sakar mata murmushi ta isa gareta... Muhibbah ta dubeta ta dubi Kuyangin guda biyu dake shirya kayayyakin Zahra.. Ta d’an waro idanu waje tace “Kin fara parking already..?!”
Zahra ta d’an tab’e baki tace “Kind of... Since I don’t have a choice...!”
Muhibbah Ta sakar mata murmushi wanda yafi kama da yak’e... Zahra tai alama wa Kuyangin suka fice... Lokaci guda Muhibbah Ta janyo hannunta suka zauna saman sofa....
Muhibbah tai gyaran murya kad’an tana mai tsare Zahran da idanu tace “Do you really want to leave...?!”
Zahra ta fuzar da iska kad’an tace “Only because I don’t have a choice..I’m doing this for my Paa... Idan tani ce baniso ya auri matar nan balle har mu bar k’asar nan tareda ita...!”
Muhibbah Ta jinjina kai tace “Ki kwantar da hankalinki Zahra... You’re not leaving, and your Paa is not getting married to that woman... I promise you..!”
Zahra Ta dubeta da mamaki tace “But how...?!”
Muhibbah Ta kuma gyara zama tace “I’ve a plan... matso kusa kiji..!”
Babu musu Zahra ta matso kusanta sosai... Take Ta sanar da Zahran abinda ta shirya a zuciyarta...
Cikin Rashin fahimtar abinda Muhibbar Ke nufi Zahra tace “But idan yak’i zuwa fah ...?!”
Muhibbah ta murmusa tace “Ke kad’aice wani abu zai sameki ya bar dik abinda yake ya fito.. So bazaiki’i zuwa ba...!”
Zahra ta d’anyi jim tace “Toh Wai mai zaije gani... I’m lost..!”
Muhibbah Ta kuma murmusawa tace “Abinda zai hanasa auren matar da baki so ya aura shi zai gani... All you need to do is to trust me and stick to our plan... Kin fahimta...?!”
Zahra ta jinjina kai a hankali tace “I trust you... Na yarda dake Tia...!”
Muhibbah Ta murmusa tace “Tomorrow in the evening..!”
Jinjina mata kai Zahra tai tace ta fahimta...
Da wannan shawari Muhibbah harmada Zahran suka sami bacci mai kyau...
***
Washe gari Zahra ta sami mahaifinta da batun tana so taje ta duba Uncle d’inta Fu’ad a asibiti kafin su bar k’asar...
Mahmood ya amince mata amma da sharad’in Umaima ko Jakadiya d’aya zatai mata rakiya....
Zahra Ta marairaice fuska tace “Paa fah harda gidajen k’awayena zan zaga nai masu sallama, ni banson rakiyar kowa...!”
Da wutsiyar idanu ya dubeta, dak’ik’a guda Ta gifta kana ya girgiza kai yace “Bana son gardama...!!”
Ta sadda kanta k’asa kad’an tace “Alright zan fad’iwa Jakadiya..!!”
Bai tankata ba saima kiran Hadiminsa da yai... Hadimin ya k’araso ya zube yana kwasan gaisuwa...
Mahmood dake tsaye hannayensa hard’e ta baya ya bud’e murya kad’an yace “Barde aimin ison Jakadiya..!!”
Barde ya d’ago hannu alamun jinjina “Allah shi taimakeka..! An gama Rankaidad’e..!!” Ya mik’e da sauri a durk’ushe ya fice isar da sak’on shugabansa...
Zahra ta saki baki kurum tana duban mahaifin nata wanda ga dukkan alamu mulkin ya soma ratsa jikinsa, tayi imani da a baya ne iyaka abinda take so shi za’ai amma yanzu abubuwa yake irinta masu ji da Mulki... Ta had’iyi miyau da k’yar dan idan dai da Jakadiya za’ai tafiyar shirinsu da Muhibbah zai b’aci... Yanzu mai zatai..?
Batakaiga samo amsa ba Jakadiya Ta shigo a duk’e tana gaida Sarki...
Mahmood yai gyaran murya kad’an ya ambato sunan Jakadiya
“Allah shi baka yawan rai...!!” Jakadiya ta fad’i tana mai kuma risinawa alamun amsawa...
“A tafi da ita duk yanda take so, karki rabu da ita daidai da dak’ik’a guda...!!”
Jakadiya ta kuma risinawa bayan ta dubi Zahra dake tsaye gefen Babanta kana tace “An gama Rankaidad’e.. In sha Allahu ko k’uda bazai tab’a ta ba...!!”
Zahra ta narkama Jakadiya harara dan yanda bata k’aunar Kakarta Giwa haka bata k’aunar Jakadiya....
Ya jinjina masu kai had’ida basu izinin fita....
Tana fitowa ta turawa Muhibbah sak’o cewa Paa d’inta ya k’yaleta taje asibiti duba Fu’ad amma harda rakiyar Jakadiya...
Muhibbah ta ida karance sak’on had’ida rintse idanunta dan babu Jakadiya a tsarin nasu, kasancewarta ka iya b’ata komai...
Sak’o Zahra ta kuma turo mata _What do I do..?_
Dafe kanta tai tana tinanin abinyi... Kaman ance ta kalli can gefe da yanda take tsaye Ta hango Jamal kishingid’e cikin rumfar shak’atawa ta alfarma yana juya wani guntun k’yalle a hannunsa, Ta tsare k’yallen da idanunta daga nan yanda take lab’e... Ko shakka babu ta fahimci k’yallen mayafinta ne da ya gutsire sanda ta haye saman ginin benen b’angaren Jamal d’in lokacinda take binciken Zanen ginin gidan sarauta dake wajen Jamal d’in....Wato ya d’auki k’yallen kenan yana neman mai tufafin... Tabbas idan yasan wanene mai Tufafin zai fahimci tana masa binciken k’wak’waf ne... Bazata bari ya kamata ba... Amma mai zatai... Take tinanin Jakadiya ya fad’o mata... Ta tina cikin labarin da Fu’ad ya bata Jakadiya itace ta d’auketa ta kaitama wancan tsinannen bokan wanda yaso k’ara aikata alfasha da ita akan wanda ‘ya’yan Sarkin suka mata.... Take taji wani irin tsanar Jakadiya na kuma taso mata... Tabbas Jakadiya yau zata karb’i nata itama wajen Jamal... Ba tareda d’aukan doka a hannunta ba Jamal zai zartar mata da nata hukuncin, dan yanda taga fuskar nan nasa babu alamun rahama tasan idan ya kama mai tufafin nan bazai masa da dad’i ba....
Sak’o ta turama Zahra cewa tazo sashen bak’i ta sameta kafin su fice amma kada ta sanar da Jakadiya ga yanda zataje...
Zahra tai yanda Muhibbar tace... Ta dubi Jakadiya tace ta jirata nan tana zuwa...
Jakadiya Ta jinjina kai tace an gama Rankaidad’e....
Zahra ta iso jikin k’ofar Muhibbah tai knocking a hankali...
Muhibbah Ta lek’o kana Ta janyo hannunta zuwa cikin parlorn...
Ga mamakin Zahra wani mayafi Muhibbah Ta mik’a mata...
Zahra ta juya mayafin tace “Mai zanyi da wannan...?!”
Muhibbah tace “A tsarinmu Babu Jakadiya ciki... Wannan mayafin shi zai hana Jakadiya daga ficewa cikin Masarautar nan... Ki bata kice ta yafashi ke bazaki fice da ita tagajan magajan ba ana kallonku haka.... Idan ta yafa kubi ta k’ofar Shataletale (Yanda Jamal Ke zaune)..”
Zahra dai bata fahimci komai ba amma Ta sami kanta da yin yanda Muhibbar Ta umarta... Sai juya mayafin take hannunta har ta iso yanda ta bar Jakadiya na jiranta...
Tana k’arasowa Jakadiya tai mata jinjina da gaisuwa....
Zahra Ta sakar mata murmushi kana Ta mik’a mata mayafin dake hannunta tace ta yafa shi...
Jakadiya Ta shiga juya mayafin tana mai furta “Allah shi taimakeki wannan ai naku ne masu mulki, Ina na isa yafa wannan Ina talakarku...!”
Zahra ta murmusa tace “Karki damu Jakadiya, dukkanmu da kike gani d’aya muke a wajen Allah, idan ma kinfini tsoron Allah sai ki fini matsayi wajensa... Dukkanninmu bayin Allah ne.. Ke ‘yaradam ce kaman ni... So ki karb’a kawai ki yafa babu wani abu...!”
Jakadiya tai mata K’uri tana dubanta cikin tsananin sanyin jiki, tinda take a Masarautar ba’a tab’a karramata irinta yau ba... Bata tab’a jin tanada daraja a matsayinta Ta ‘yaradam kaman yau ba... Allah sarki sai ta tuna jik’onda Giwa tasa taita d’irkawa matar Yarima Mahmood Aliya wanda ya lalata mahaifarta kuma sukeda tabbacin bazata tab’a haihuwa ba... Sunada tabbacin Zahra ba d’iyar Aliya bace dan Tal’udu ya tabbatarwa Giwa Aliyar bazata tab’a haihuwa ba duk asibitin duniya da zasuje shisa koda suka dawo da Zahra k’asar a matsayin d’iyarsu sukeda shakku da alamun tambaya akan yarinyar.. Amma dai abinda yarinyar nan tai mata yau tayi imani d’iyar halak ce koda kuwa ta wata hanyar aka sameta... Zahra ce ta katse mata tinanin da fad’in subi ta k’ofar Shataletale... Suna tafe tana jan Jakadiya da hira....
Jakadiya sai Washe baki take tana jin kanta tamkar ‘yantacciya musamman data rufa mayafi irinta masu Mulki...
Daga can yanda take kishingid’e a Rumfar hutawarsu Ta ‘ya’yan sarakuna yana mai ci gaba da juya k’yallen ya hango Jakadiya da Zahra na tahowa...
Ya k’urama Jakadiya idanu da mayafin dake kanta, ya kuma juya k’yallen dake hannunsa... Lokaci guda ya shiga jinjina kai... Wato Jakadiya ce mai masa bincike a d’akinsa... Alk’awari ya d’auka idan ya kama mai masa binciken k’wak’waf d’in nan sai ya hukuntasa hukunci mai tsauri dan shi a nasa tsarin babu yafiya, duk wanda ya shiga gonarsa sai ya hukunta sa, hakan yasa ya hukunta Ja’afar sannan Majidad’i ma bai mance dashi ba h’d definitely get what’s coming for him... Yanzu ma dole ya hukunta Jakadiya... Ya k’arashe yana sakin huci...
Bawa guda dake tsaye gefensa yai masa alama yazo.... Take ya basa umarnin yai masa kiran Jakadiya...
Bawan ya tafi yayi yanda Jamal yace.. A tare Zahra da Jakadiya suka k’araso... Jakadiya ta zube tana kwasan gaisuwa...
Zahra ma Ta gaida Uncle d’in nata da sakin fuska....
Jamal ya tambayeta Ina suka nufa..? Yana tambayar yana k’arema mayafin Jakadiya kallo dan tabbatarda zarginsa har dai idanunsa suka sauk’a kan yanda gutsirin k’yallen ya fice... Ta tabbata Jakadiya ce mai masa binciken sirri watak’ila ma bakinsu d’aya da Ubandoma ita ta had’a baki da Ubandoma suka kub’utar da Ja’afar....
Ya dubi Zahra yace “Princess, gashi kuwa inaso Jakadiya tai min wani aiki... Ko na had’aki da wata Hadimace Ta rakaki...?!”
Zahra cikin jin dad’in Ta sami hanyar rabuwa da Jakadiya a sauk’ak’e tace dashi “Karka damu Uncle na bar maka Jakadiya, zan samu d’aya cikin Hadimaina tai min rakiya...!”
Jakadiya na son cewa umarnin mahaifin Zahra ne babu hali haka tanaji tana gani Zahra tasa kai abinta Ta shige bayan tayiwa Jamal sallama....
Tana shigewa ta kirawo Muhibbah ta sanar da ita Uncle Jamal ya rik’e Jakadiya zatai masa wani aikin....
Muhibbah ta murmusa, a fili ta furta “Perfect..!!” Cikin zuciyarta kuwa fad’i take Jakadiya kema tak’i Ta sameki....
SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*
*56*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ba tareda rakiyar ko wacce Hadima ba Zahra tai ficewarta kaman dai yanda suka tsara da Muhibbah... A farfajiyan asibitin Ta umarci driver ya ijeta, tana fitowa daga motar ta soma dialing layin Muhibbah... Juyowar da zatai ta ganta tsaye gefenta, Zahra ta d’an zaro idanu tace “Yaushe kika iso..?”
Hannunta Muhibbah ta kamo tana mai sanar da ita bata jima da isowa ba dan tin fitarsu itama ta fice ta shiga motar haya hasalima biyedasu Zahran suke a baya...
Zahra tace “Toh what next.. Mai zamuyi yanzu..?!”
Muhibbah tace “Zamu shiga ki duba Uncle Fu’ad d’in kaman yanda kikaceda Paa d’inki..”
Zahra ta jinjina kai a hankali kana suka nufi psychiatric ward... Suka zauna a wajen da visitors Ke zama, d’aya daga cikin mai kulada marassa lafiyan ya k’araso yana tambayarsu wajen wanda sukazo.. Babu b’ata lokaci sukace dashi ga wajen wanda sukazo, Zahra tace ita niece d’insa ce...
Nurse d’in ya jinjina kai yace amma saidai Fu’ad bai cikin majinyatan da ake fitowa dasu sabida hauka tuburan da yake, duk mai son ganinsa saidai ya shiga ya gansa a d’aure da sark’ok’i jikin gadonsa...
Koda suka shiga wajen Fu’ad ba Zahra kawai ba harta Muhibbah saida ta tausayawa Fu’ad... Irin d’aurin mahaukata da mahaifiyarsa taima mahaukaciya Izzatu irinsa akaima Fu’ad cikin sark’ok’i sannan yanda mahaifiyarsa Ta yanke harshen Izzatu babu magana haka nan shima gadai harshe cikin bakinsa amma kaman an d’aureta Bai iya cewa komai saidai yana iya sauraron magana...Bai cewa um bai cewa a’a sai kallon mutane da ido... Zahra na hawaye daga nan yanda take tsaye Ta kasa ci gaba da kallonsa... Cikin kuka Ta k’unshe bakinta Ta fice ta bar d’akin dan bazata juri ganinsa a haka ba...
Fu’ad yana ganin Muhibbah ya bar dik wani bige bige da yake yana binta da kallo, Muhibbah tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata... A hankali take takowa har Ta iso kusan jikin gadon, Fu’ad bai daina dubanta ba....
Saida tai k’ok’arin saita kanta kana ta soma fad’in “Wasu lokuta a rayuwa mukanji cewa inama mukeda ikon tsara k’addararmu yanda muke so... Saidai Allah bai hukunta hakan ba a tsakaninmu, shikeda cikakken ikon tsara mana rayuwa yanda duk tazo mana... Wasu k’addaran sukan faru damu ne domin su zamto iznah a garemu, wasu kuma sukan faru ne domin su zamto jarabawa a garemu... Rayuwar gaba d’ayarta jarabawa ce, da dad’i ko Babu dad’i...Mai hak’uri da d’aukan k’addara shi yakeda riba... Ina fata wannan ciwo da kake ciki ya zamto iznah ga ire iren mutane masu tunani irin naka wanda basa d’aukan k’addara su maida la’amaransu ga mahaliccinsu, saidai su jefa kawunansu cikin shaye shayen miyagun k’wayoyi don a nasu k’aramin tinanin wad’annan miyagun k’wayoyin sune zasu zamto makawar damuwarsu da suka tsinci kansu ciki... Watak’ila kuma hakan ya zamto hukuncinka ne bayan abinda kuka aikata ma wancan yarinyar shekarun baya... Fu’ad I’m quite certain you’re not like your two brothers, kaso yin abinda ya kamata tuntuni amma bakada courage... Sabida ‘yanuwanka da mahaifiyarku da suke maka barazana... Ko dan dalilin wannan zan yafe maka dikda cewa akwai jinin mahaifina a hannunka... Jinin mahaifina yayi staining hannunka Fu’ad... Kai ka kashe Abbah na, amma na yarda bada son ranka bane ka aikata hakan....! Na yafe maka Fu’ad kuma ina rok’on Allah ya sassauta maka... Ya baka lafiya, ya kuma inganta rayuwarka..!!” Ta k’arashe idanunta na kuma kad’awa...
So yake yayi magana amma babu hali sai hawaye dake gangaro masa fuskarsa d’aukeda alamun tambaya...Muhibbah dake zuban hawaye ta jinjina masa kai alamun tabbatarwa, lokaci guda take furta “Yes... Yes Fu’ad... I’m that girl that you and your brothers abused... Ni ce Saudatu...!!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata...
Fu’ad yaci gaba da tsareta da idanu hawaye naci gaba da gangaro masa... Muhibbah taci gaba da fad’in “Na dawo cikin rayuwarku ne domin na tarwatsa ahalinku, saidai tun kafin nakaiga tarwatsaku da alama zunubanku suna hunting d’inku d’aya bayan d’aya...I’ve never loved you Fu’ad... Kawai nayi amfani da damar ne to ruin you, saidai kaida kanka tuni ka tarwatsa kanka Ta hanyar d’irka ma kwanyarka miyagun k’wayoyi...Ina fata Allah ya kawo maka sassauci Fu’ad... Sannan Ina maka bankwana na k’arshe watak’ila bazamu kuma had’uwa ba... Allah Ubangiji ya sassauta maka....!” Ta k’arashe tana mai ficewa daga cikin d’akin....
Fu’ad yabi bayanta da kallo har Ta b’acewa ganinsa wasu irin hawaye na kuma gangaro masa... A hankali ya lumshe idanunsa wasu hawayen suka kuma gangaro masa...
A nan kujerun da visitors ke zama ta tadda Zahra tai zaune damuwa fal zuciyarta... Daga gefenta Muhibbah ta zauna ta d’an dafata kad’an, Zahra Ta d’ago idanunta masu rauni tana dubanta lokaci guda take furta “He’s my favorite you know... it breaks me seeing him like this... Uncle Fu’ad yanada kirki, he might have his own faults a matsayinsa na d’anadam but I can assure you he’s a good person...!”
Jinjina mata kai Muhibbah tai tace “Na yarda, yanada zuciya mai kyau... Kiyi mishi addu’a Zahra Allah ya bashi lafiya...!”
Zahra Ta jinjina kanta hankali had’ida fatan samun sauk’iga Fu’ad... Saida suka d’an b’ata lokaci a asibitin kafin suka saci wata hanya suka fice yanda driver d’in bazai gansu ba... Shiru shiru yana jiran fitowar Zahra hardai ya yanke shawarin sauk’a ya duba ta ina Zahran take...
Tin yana d’aukan abin wasa hardai ta tabbata babu Zahra babu dalilinta.... K’ololuwar tashin hankali ya shiga... Haka ya dinga karad’e ward d’in yana furta Rankidad’e amma babu ita babu alamunta... Koda ya tambayi nurses d’in dake wajen sai ce masa sukai eh wata ‘yar matashiyar budurwa ta shigo ta duba Yarima Fu’ad amma Ta fice tuntuni... Kuma Bafajen dake gadin k’ofan d’akin Fu’ad akai rashin sa’a ya fice Sayen goro har Muhibbah da Zahra suka shigo suka fice...
Cikin tsananin kid’ima driver ya kirawo layin Hadimin Yarima Mahmood....
**
Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar tana duban sunk’urun d’akin da suka shigo itada Yarima Jamal wanda babu komai cikinta sai wata kujerar katako k’wara d’aya tak...Ta risina kad’an tace “Allah shi taimakeka ko wani abin zanyi maka cikin d’akin nan..?!”
Yanda ta hango fuskar Jamal d’in ya sanyata had’iye sauran kalaman nata... Sai kuma taga ya sakar mata murmushi lokaci guda... Yai mata nuni da wata ‘yar akwati mai kaman briefcase yace Ta d’auko ta kawo gabansa... Babu musu Jakadiya ta isa ta d’auko Jakan ta aje gaban Jamal cikeda risinawa...
Jamal ya kuma sakin murmushi yace “Dad’ina dake Jakadiya akwai bin umarnin iyayen gidanki... Shiyasa zanji mamaki matuk’a idan akace kinci amanar iyayen gidanki...!”
Jakadiya ta Washe baki had’ida risinawa tace “Ai Rankaidad’e bana fata wannan rana tazo... Ranan da zan juya ma ahalin gidan nan baya... Duk abinda kuka umarceni sami’ina wa’ad’ana ne a matsayina na baiwa mai biyyaya.. Allah shi taimakeka..!!” Ta k’arashe tana mai kuma d’ago masa hannu alamun jinjina...
Kansa a karkace yake dubanta, lokaci guda ya kuma sakin murmushi kana yai mata nuni da wannan kujerar k’wara d’aya tak dake cikin d’akin yace ta k’arasa ta zauna a samansa...
Jakadiya ta soma shan jinin jikinta, ta d’an d’ago tana dubansa kad’an “Rankaidad’e ina baiwa ina zama kan kujera a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 65