sanar dasu..!!” Ta k’arashe a d’an rikice tana mai k’ok’arin sauk’owa daga saman gadon...
Hannunta Gimbiya Turai ta kamo ta zaunarta kana tace “Sun riga Sun San komai, asirin Izzatu ya gama tonuwa a cikin Masarautar nan..! Illahirin jama’an K’asar nan a halin yanzu sunsan wacece Izzatu da ta’asan da ta jima tana aikatawa shekara da sharkaru..! Allah shine abin godiya wanda ya k’addari sake had’uwarmu ya kuma cire fargurbi cikinmu..!!”
Muhibbah ta jinjina kai a hankali sai kuma tace “Inaso naje naga Umaima domin kuwa Giwa ta sanar dani cewa Umaima ‘yar uwatace wanda matar da mahaifina ya aura a lokacin da ya tafi nemanki ta haifa masa, Ta sanar dani yanda ta hallak’a mahaifiyar Umaima cikin wuta ta kuma tahoda Umaima cikin Masarautar nan..!!”
D’ago kan da zatayi ta hango Umaima na shigowa cikin d’ingishi hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta..! Muhibbah tana ganinta ta mik’e zumbur wasu hawayen na kuma gangaro mata, lokaci guda Ta soma takowa dukda rashin k’arfin dake jikinta, saida ta k’araso har gaban Umaima kana taja ta tsaya hawaye basu daina ambaliya a fuskokinsu ba.. Lokaci guda suka rungume juna suna masu ci gaba da sakin kuka..! Gimbiya Turai tai masu K’uri tana dubansu cikeda shauk’i, Allah sarki d’an uwa mai dad’i, a yau ahalin d’an uwanta Alfah sun had’e waje guda... Allah ya kuma had’asu gaba d’aya shin mai yafi wannan d’ad’i... Inama Alfah yanada rai yaga d’iyoyinsa Allah ya had’esu, tabbas Allah ya cika abin godiya mai yawan rahama ga bayinsa.. Yau ko babu Alfah Allah ya bar zuri’arsa a doron k’asa bayan duk kalan makircin da Izzatu tayi domin ta k’arar da ahalinsa a bayan k’asa... Tabbas Sara da sassak’a baya hana Gamji toho, Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ko ana shaho toh fah sai yayi, Ko a yanzu Allah ya d’auki rayuwarta ya cika mata burinta, ya had’ata da ‘aya’yenta guda biyu bayan tsawon shekarun nan sannan ya had’ata da ‘ya’yan d’anuwanta wanda zataga d’anuwanta a tattare dasu..!
Umaima da Muhibbah hannayensu rik’e cikin na juna suka zauna saman gado Umaima na fad’in “Nayi zaton bayan Giwa da ahalinta banida sauran dangi a duniyar nan kaman yanda Ta sanar dani, Ashe ba haka bane ita d’in hankaka ce mai maida d’an wani nata Domin ta cutar dashi, ita d’in ta k’ware wajen satan yaran mutane..! Taso tarwatsa ahalinmu sai Allah ya sake had’amu a cikin gidan nan, tin kallon farko da na miki Muhibbah naji ina k’aunarki ashe ked’in ‘yaruwata ce ta jini..! Alhamdulillah Allah ya nuna min ahalina na gaskiya, ba wannan azzalumar matar da d’anta da suka so cutar dani ba..!”
Muhibbah ta murmusa ta kuma kamo hannun Umaima tace “Hakance ta kasance dani sanda na soma tozali dake Umaima, Alhamdulillah.. Mun godewa Allah da baiwa wad’annan azzaluman damar cutar damu ba..!”
Umaima ta kuma murmusawa tana goge hawayen fuskarta take furta “Thank you Big Sis for saving me..!!”
Muhibbah tai mata K’uri jin ta ambaceta da big Sis, Ashe akwai rana irin wannan da zatazo ta ga jininta tayi zaton tun bayan rasa k’anwarta da tai bazata kuma jin wani ko wata ya ambaceta da ‘yaruwa ba sai gashi yau d’in taji haka... Tai saurin janyo Umaima cikin jikinta ta rungume suna matsan k’wallan Farin ciki..!
Likita ma saida ta matse k’walla ta dubi Muhibbah tace “Anya Rankidad’e ked’in patient ce kuwa, naga kaman da k’arfinki... Yanda aka d’ago min hankali na fito babu shiri ban zaci zan ganki haka ba..!”
Murmusawa Muhibbah tai tace “Lafiyata lou Dr, kaina ne kawai Ke min ciwo...!”
Dr ta jinjina kai tace “Naji dad’i da jin hakan, Allah ya k’ara lafiya..!” Ta ciro PCM cikin ‘yar jakan nata ta mik’a nata tace “Idan kinci abinci sai ki sha ki d’an samu bacci ki huta koh..!”
Nan ma jinjina mata kai Muhibbah tai had’ida mata godiya..!
Likita tai masu sallama sukai mata godiya gaba d’aya kana Ta fice..
wata Hadima ce ta shigo ta risina gaban Gimbiya Turai tai mata magana kaman mai bata sak’o... Yayinda Muhibbah da Umaima Ke ci gaba da tattaunawa Umaima na fad’in Ta bata labarin mahaifinsu da abubuwan da suka faru..!
Gimbiya Turai ta katsesu da fad’in “Yarana ku tashi muje koh..!”
Babu musu suka mik’e gaba d’aya Muhibbah na dafe da Umaima tana taimaka mata, a tare suka nufo downstairs, nan Muhibbah Ta fahimci b’angaren Rankaidad’e suke, bata dai ce komai ba har lokacin... Suka fito gaba d’aya yayinda wasu Hadimai guda uku suka risina masu alamun gaisuwa, lokaci guda sukai masu jagoranci zuwa masauk’in Muhibbah wanda Yarima Mahmood ya ajeta kafin su Giwa su kamata, Kaman bazata shiga ba taja Ta tsaya turus tana duban Umaima da Gimbiya Turai..
Gimbiya Turai ta kamo hannunta guda tace “Nasan kinada tambayoyi da Dama k’unshe cikin zuciyarki Saudah, wanda da zaki so a amsa miki su cikin gaggawa, amma inaso ki k’ara hak’uri har abubuwa su kuma daidaita cikin Masarautar zakiji komai daki daki kinji koh..! Yanzu ki shiga cikin d’akinki ki samu kiyi wanka ki sauya wannan tufafi domin wad’annan tufafi basu kamaceki ba ked’in Gimbiya ce kuma Sarauniya..!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta..
K’ok’aro murmushin Muhibbah ma tayi ba tareda Ta fahimci abinda take nufi da tace itad’in Gimbiya ce kuma Sarauniya, ta alak’anta maganar nata da kasancewarta d’iyaga d’anuwanta D’an Sarki jinin Sarauta..!
A haka suka k’arasa cikin sashen, yanda suka tadda Kuyangin fin na da, saidai wannan karon wasu ne ba wad’ancan Kuyangin data tadda sanda ta farka ta tsinci kanta cikin d’akin ba.. Gaba d’aya suka zube masu suna kwasan gaisuwa.. Hadimar guda tace da Gimbiya Muhibbah an shirya mata ruwan wanka da komai da komai.. Sannan ko akwai wani abu da Gimbiya Ke buk’ata..?
Umaima ce ta jinjina kai tace “Kuna iya tafiya, Gimbiya hutu take buk’ata..!!”
Hadimar ta kuma duk’awa tayi godiya kana suka sa kai suka fice..!
Muhibbah Ta d’an dubi Umaima ta rausayar da idanu tana mai furta “Nifah wllhi duk ban saba da wad’annan abubuwan ba, sai inajin gaba d’aya kaman wata duniya ta daban nake, nafi sabawa da yin komai ma kaina..!”
Murmushi Umaima tai tace “Da sannu zaki saba da d’abi’u da al’adun Gidan nan..! Muje na zab’a miki tufafin da zaki saka..!”
Ta janyo hannunta suka nufi closet tare..!
Gimbiya Turai ta raka su da kallo murmushi saman fuskarta, mik’ewa tayi itama ta nufi closet d’in tana tayasu zab’an tufafin... Dashike almuru ya riga ya sako kai, dare ya riga ya soma shigowa hakan ya sanyasu zab’a mata tufafi mai sauk’i sanyawa irinta masu mulki da sarauta..!
**
A can b’angaren su Mahmood kuwa ko takan Giwa da ayarinta bai kuma biba tinda ya tabbata an fice dasu daga cikin Masarautar an tafi dasu asibiti domin nema masu taimako Ta gaggawa, iyaka taimakon da zai iya masu kenan dama a fice dasu daga Masarautar a nema masu agajin halin da suke ciki dukda cewa sune silan jefa mawunansu cikin wannan yanayi da suka tsinci kawunansu ciki...!
A parlor ya tadda Ja’afar da Turaki suna jiran sauk’owarsa bayan komai ya d’an lafa, Turaki ya mik’e yana fad’ida Ja’afar “Kaga ga Rankaidad’e d’in ya fito... Ni zanje na baiwa Ansar masauk’i dan yace min idan yaji k’arfin jikinsa gobe yake komawa Bauchi..!”
Ja’afar yace “Bazai bari ya kwana biyu ba.. Kuma ai akwai masauk’i cikin Masarautar nan, inaga basai ya fice..!”
Muryar Mahmood suka sinkaya yana fad’in “Mutumin nan baida masauk’i cikin Masarautar nan..!!”
Ja’afar ya had’iyi sauran kalamansa, Turaki ya jinjina kai yace “Dama can gidana zamu tafi your Highness..! Allah ya huci zuciyar Sarki mai jiran nad’i, Baban Zahra’u, kuma Angon Gimbiya Saudah Muhibbah..!!” Ya k’arashe yana mai d’ago masa hannu alamun jinjina..
Yasan ‘yan tsiyar Turaki ne suka motsa hakan yasa sam baibi takan Turaki ba saima zama da yayi saman kujera ya d’aura k’afarsa d’aya bisa d’aya yana murza zobban hannunsa a hankali..!
Turaki ya risina yace “Rankaidad’e ni zan wuce, Masarauta is all settle now..!”
Ya d’ago idanu guda yana duban Turaki ya dubi Ja’afar dake gefe... D’an gyaran murya yayi ya ambato sunan Ja’afar..!
J’afar ya amsa cikeda risinawa irin yanda k’aramin k’ani keyiwa babban wa..
Tambayarsa yayi Mahaifiyarsu..
Ja’afar yace “Tana can tareda..!” Yayi shiru ya kasa k’arasa sunan Muhibbah..!
Mahmood ya tsaresa da idanu.. K’ok’arin saita kansa Ja’afar yayi yace “Tana can tareda Gimbiya Muhibbah, Tana sashenta..!”
Ya jinina kai a hankali sai kuma ya mik’e yana mai furta “Ka jirani a nan ina dawowa..!” Ja’afar ya jinjina kai a hankali yana mai amsa masa, duban Turaki Mahmood d’in yayi lokaci guda ya soma takawa, Turaki na biye dashi yasan hakan na nufin rakiya zai masa..!
Suna tafe yana furta “Kasan irin kalaman da zaka Ke furtawa gaban k’anina..!!”
Turaki ya had’iyi dariyarsa yace “Tuba nake Rankaidad’e... Yanzu shi Ansar d’in Dawakai nawa za’a basa kyautarsu..!” Had’iye maganar nasa yayi ganin ya kaikaito a hankali yana dubansa..!
“Turaki..!!”
Turaki ya amsa da “Rankaidad’e.!!”
Mahmood yaci gaba da fad’in “Kar ka sake ambaton sunan mutumin nan a nan, nasan mai ya kawo shi ba komai bane ya kawoshi illa tsananin soyayyar da yake mata..!”
Turaki ya jinjina kai yace “Toh amma Rankaidad’e gani nayi baka gabatar da kanka gareta ba tukuna.. Bamuda tabbacin If she feels the same for you, a tunanina sabida binciken gaskiya da kake cikin Masarauta shiyasa ka aurota gudun kar Waliyyinta ya bada aurenta ga wani wanda hakan ka iya hana kasancewarta cikin Masarauta... Tunda yanzu komai ya fito fili inaga ya kamata ka sauwak’e mata tun kafin ka kaiga sanar da ita matsayinka a wajenta..!”
Burki yayi had’ida k’urama Turaki idanu ganin cewa da gaske yake fad’in duk abubuwan da yake fad’i, lallai ya yarda notin kan Turaki sun kwance...!
Saida yayi gyaran murya hannayensa hard’e Ta baya ya soma furta “Idan na sauwak’a mata sai shi kuma ya aureta ko yaya..?! Kai ka tab’a jin Sarki mace talakansa ya aura..?!” Ya k’arashe yana duban Turakin k’asa k’asa
Turaki ya jinjina kai yace “Toh idan kuwa haka ne, ya zama dole Sarki ya Sauk’e kansa ya sanar da ita how he feels..!”
Ya katse Turaki da fad’in “What if zuciyarta na k’aunar Likitan nan ne..?!!”
Turaki ya jinina kai yace “Then sai ka sawwak’e mata, Ta cancanci Farin ciki, Dan bazai yuwu kaita ajiyeta a d’aki ba tareda sanin madafar rayuwarta ba..!”
Muguwar kallo ya kuma aikawa Turaki ba tareda yace komai ba..! Lokaci guda yake furta “Have I ever told you neman shawarinka is useless sometimes...!!”
Turaki ya jinjina kai yace “Kasha fad’in haka Rankaidad’e, Allah ya huci ran Amale tuba nake..! Na barka lafiya Rankaidad’e...!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai bud’e motarsa, yasan cewa k’arshe za’a nemosa ne...!
Da kallo kurum ya raka Turaki har ya shige yana tsaye a wajen hannayensa hard’e Ta baya... Duk duniyar nan Turaki ne kawai mai yab’a masa magana yanda yaga Dama.! Ya kuma fuzar da wani hucin yana tunanin al’amarin... Ta yaya zai fara tunk’ararta da batun, Ta yaya zai soma sanar da ita cewa shid’in mijinta ita matarsa ce..! Mai zai faru idan tak’i amincewa da hakan..!?
Girmansa fah ya fad’i kenan musamman yanzu da yasan cewa su d’in ‘yanuwan juna ne matsayin k’anwa take masa..! Ya fuzar da fuci mai d’umin gaske yana mai shafe fuskarsa da duka hannayensa biyu..!
Kai tsaye sashensa ya koma yanda ya baro Ja’afar na jiransa..!
Daga bakin k’ofa ya tsaya yana duban yanda Ja’afar Ke shafa wani k’atoton hoton Mahmood da ‘yanuwansa su Duka hud’un sunyi shiga irinta Mulki saman Dawakai akai masu hoton, sunyi bala’in yin kyau kana ganinsu kaga ‘ya’yan Sarauta..!
Ja’afar yasa hannunsa yana share hawayen dake gangaro masa yake kuma shafan hoton, a hankali Mahmood ya k’araso ya tsaya bayansa hannayensa hard’e yake duban hoton shima, lokaci guda yake furta “Kai yafi cancanta ka kasance cikin hoton nan, amma bata baka daman hakan ba, she deprived you your right, komai a nan da kake gani naka ne..! Everything is yours, sarautar da komai Naka ne ba nasu bane..! Duk abinda Ke cikin hoton nan ba komai bane face k’arya..!!”
Ja’afar ya kaikaito yana dubansa, lokaci guda yasa hannunsa yana kuma goge hawayensa, a hankali yake furta “Akwai abu guda d’aya da yake ba k’Arya ba cikin hoton Yaya..! And that’s you..! Koda ace ban mallaki damata cikin Masarautar nan ba, ina Farin cikinka girma cikin gata da k’aunar mahaifinmu Yaya..! At least akwai abu guda da yake gaskiya ne a cikin Masarautar... And that’s you Yaya..! Wannan kawai idan na tuna nakanji Farin ciki..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka..!
A hankali Mahmood ya janyo kafad’arsa ya rungume a gefen damansa, lokaci guda yake d’an bubbuga kafad’arsa yana lallashinsa irin yanda yakeyiwa Fu’ad..! A hankali Mahmood d’in yakai dubansa kan Fu’ad a cikin picture d’in... Ya saki murmushi mai sanyin gaske... Saida ya d’anyi gyaran murya kana yace “Gobe in sha Allah ka shirya zamuje wani waje..!”
Ja’afar ya jinjina masa kai a hankali yace “Toh Yaya..!”
Mahmood ya jinina kai kana sukai sallama da d’anuwan nasa ya haye samansa..!
Yana isa d’aki ya kunna computer d’insa dake hasko masa d’akinta tareda nad’o masa sautin abindake wakana...Zaune ya gansu itada Umaima da kuma mahaifiyarsa sun saka a tsakiya...
Ya zauna saman kujera yana mai bada hankalinsa sosai garesu..
**
Muhibbah ta d’ago tana dubansu su duka biyun, saida tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka zubo mata kana ta soma fad’in
“Kaman yanda kuka sani Sunana Saudatu, na taso ni kad’ai wajen mahaifana, mahaifi na da Mahaifiyata ‘yanuwan juna ne sabida kaman yanda suka bani labari cewa bayan mahaifina ya rasa iyayensa sai mahaifin Mahaifiyata ya d’aukesa suka baro can garin nasu domin su tsiratar da mahaifina daga wad’anda suke nemansa da sharri..!”
Ta d’anyi fasali kana yaci gaba da fad’in “Nasha yiwa iyayen tambayoyi da Dama wanda basu bani amsarsu ba sai yanzu nake ganin amsoshin tambayata garesu, daga ciki harda tambayar da nayi masu ina ne asalin garinmu, ina sauran danginsu..? Mahaifina saidai yace min kar na sake tambaya makamancin wannan..! Duk wani abinda zai tuno masa bayansa baya k’auna, sannan na kasance ina son labarun tarihi irinta gidajen Mulki da sarauta amma sam mahaifina baya k’auna, duk abinda ya shafi sarauta mahaifina baya k’aunar wannan abin...! Mun kasance muna tafiye tafiye daga gari zuwa gari tun bayan da muka rasa mahaifin Mahaifiyata wanda shine d’an uwan mahaifina da ya rainesa ya girma gabansa ya kuma ya aura masa d’iyarsa wacce ta zamto amana a garesa Wato Mahaifiyata kenan, bani mancewa mun zauna a wani gari mai suna Katakore a can k’asashen yamma... A wannan garin ne har aka sanyani makarantar boko da na Islama, mun d’anyi dogon zango a wannan garin kafin daga bisani muka soma shirye shiryen dawowa k’asashen Arewa....!” Ta d’anyi birki kana ta d’ago tana duban Gimbiya Turai tace “Bansan ko Zaki iya sanin Kakan nawa ba dan shi d’in d’anuwana ga mahaifina..!”
Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “Tabbas Baba Sadi ne wanda kaman k’ani yake wa mahaifiyarmu, munada dangantaka dashi na tabbata shine ya d’auke Alfah gudun kar masu wawason gadon Mulki su cutar dashi..! Allahu Akbar bansan Baba Sadi yanada d’iya ba.. koda shike watak’ila nayi aure kafin ya haifeta ko kuma ya haifi mahaifiyar taki amma tana k’arama lokacin shiyasa bazan santa ba..!”
Muhibbah ta jinjina kai kana taci gaba da fad’in “Abbah ya tattaro Mu gaba d’aya ya taho damu neman abu mai mahimmanci a gareshi da kullum yake fad’i wanda Nidai ban San menene wannan abin ba mai yuwa Sabida k’arancin shekaruna a wancan lokacin amma ta yuwu Mahaifiyata ta sani..! Ashe a wannan lokacin Mahaifiyata tana d’aukeda juna biyu..! Kafin mu k’araso garin Jos mun tsaya a wani gari mai suna Tafisu a can kusan yankin Niger state..! Toh a wannan garin taita rainon Jaririn cikinta har dai labari ya iso ga mahaifina cewa abinda yake nema yana a nan garin Jos, dukda juna biyu da take dashi haka muka baro garin Tafisu muka nufo garin Jos.. A lokacin juna biyu da Mahaifiyata kedashi ya d’an soma girma...!!” Tai shiru hawaye naci gaba da gangaro mata..! Muryarta yaci gaba da rawa sanda taci gaba da basu labari tazo daidai yanda ‘Ya’yan Giwa sukaci zarafinta, da yanda Ta farka Ta tsinci kanta gaban wannan matsafin..!
Mahmood dake kallonsu daga d’akinsa hawaye ne shima yaji suna gangarowa daga fuskarsa..! Yaci gaba da matse zobban hannunsa wanda har baisan yaji masa ciwo a d’an yatsa ba sabida yanda zuciyarsa Ke tsananin tafarfasa...!
Muhibbah ta share k’wallan da suka zubo mata kana taci gaba da fad’in “Sun tarwatsa ahalin da suka rage min a wancan lokacin..! Sun cinnawa gidanmu wuta wanda hakan ya samu tserewa da rayuwarmu...! Zan iya ce maku bansan yaya akayi na had’u da Mahaifiyata ba, wane irin tashin hankula ne muka tsinci kawunanmu ciki a wancan lokacin wanda baki bazai iya fad’I ba, zuciya bazata iya kwatanta girman tashin hankalin ba... Iyakacin abinda na sani shine Mahaifiyata tace dole mu gudu mu bar wannan garin, dan a daren da abun ya faru a daji muka kwana, gashi cikinmu babu mai wani k’arfi, ita tana fama da juna biyu ni kuma ga iftila’i da tsautsayin da ya auka min wanda ko tafiya bana iya yi saidai Mahaifiyata da take fama da juna Ta Azani a bayanta..! Shin ku gaya min nayi laifi da nace zan dawo d’aukan Fansa..?!!”
Hawaye ya kasa daina gangarowa daga fuskokinsu... Lokaci guda taci gaba da fad’in “Da taimakon wani mai motan kwaso dabbobi daga arewa akwaisu Kudu shi ya taimaka mana ya fitar damu zuwa garin Yalwan Shandam, koda mukaje garin tana cikin yanayi na tashin tashin hankula, a nan wannan garin dai muka samu mafaka a sansanin ‘yan gudun Hijira wanda har na d’an sami kulawa daga likitoci masu kawo agaji ma ‘yan gudun Hijira Mahaifiyata ma ta sami kula daga wajen likitocin duba da yanayin da take ciki...! Maikatan lafiya dake kula da ‘yan gudun Hijiran sunyi mamaki da jin zafin yanda akaci zarafina gashi dududu ba wani shekaru ne dani ba..! Na shiga tashin hankali Mahaifiyata ma ta shiga tashin hankali maras misaltuwa da abinda ya sameni, na zamto bana shiga cikin yaran dake wannan sansanin domin kuwa tinda mutanen dake cikin sansanin suka soma ‘yar gulmace gulmacen abinda ya sameni kowa sai yana janye ‘ya’yensa daga gareni, babu mai barina na kusanci ‘ya’yansa balle nayi wasa taredasu.. Na koma tamkar wata mujiya abin gudu ga kowa... Rayuwa Ta mun d’aci matuk’a, na fuskanci kyara da tsangwama, kowa ya ganni sai gudu tamkar anga dodanniya... Wannan rayuwar itace na fuskanta a Sansanin da muka tsinci kawunanmu ciki... Inada tabbacin tsananin da muka shiga tareda k’uncin abinda ya sameni shi ya sanya Mahaifiyata haihuwa yazo mata ba tareda lokacin haihuwar ya cika ba..! Mahaifiyata ta haifo d’iyarta mace kyakkyawa, saidai tinda Ta haihu batayi lafiya ba... Na buk’aci a sanyawa Yarinyar suna Muhibbah domin ta samu soyayyar mutane kaman yanda sunan nata yake..! A daidai wannan lokaci ‘yan tadda suka kawoma Sansanin Farmak’i... Suka cinna ma Sansanin wuta, aka soma gudu kan mai uwa dawabi ana tattara yaran dake Sansanin dan tseratar da rayuwarmu.. Banga Mahaifiyata ba banga jarriyarta ba.. Na dinga tsalle ina ihu ina k’ok’arin k’watan hannuna daga hannun ‘yan kwana kwanan da suka kawo mana d’auki Ina fad’in su k’yaleni Mahaifiyata da k’anwata suna cikin Tent d’inmu wanda Ke ci da wuta..! Haka suka hanani zuwa suna sanar dani saidai nayi hak’uri Mahaifiyata da ‘yaruwata sun mutu a wannan wutar sun zama toka go gawawwakinsu ba’a gani ba..!”
Ta kuma goge wasu hawayen kana taci gaba da fad’in “Ya kuke tunanin yarinya mai k’aramin shekaru kaman nawa zataji a wancan lokacin.. Ta yaya bazan girma da k’udirin tarwatsa mutanen da suka tarwatsa min ahalina ba..!” Cikin muryarta dake tsananin rawa taci gaba da furta “Na k’wace hannuna na soma gudu banma San ina nake zuwa ba.. A iyaka sanina shine bazan kuma zama a wannan Sansanin babu Mahaifiyata babu k’anwata ba...!”
“Sansanin dake Yalwan Shandam..!” Ya nanata a hankali...Take ya shiga tuna abubuwan da suka faru baya, abinda suka bisne shida abokinsa Turaki tsawon shekaru..!Shafe fuskarsa da gumi Ke tsartsafo masa ya kumayi yana jin yanda Muhibba taci gaba da bada labarin yanda ta kub’uta daga wannan sansanin har kawo zuwa yanda iyayen Ansar suka taimaka mata, suka zamto sutura da Gata a gareta, Ansar ya zamto tamkar wani fitila wanda ya haskaka mata rayuwa.. Shida mahaifiyarsa sunyi mata komai. Taji tsoron sanar dasu abinda ya faru da ita gudun kar suma su k’yamace ta kaman yanda aka gujeta a Sansanin Yalwan Shandam..! Haka taita basu labari har dawowarta Masarautar da k’udirinta da kuma yanda Ansar ya taimaka mata sukayi komai tare hardai zuwa k’alubalen da suka fuskanta daga wajen Yawale da Gudidi kan batun aurensu da yanda mahaifiyar Ansar tak’i amincewa bayan dataji abinda ya sami Muhibbar wanda bata baiwa Muhibbah ko Ansar daman yi mata bayanin abinda ya faru ba..! Hardai zuwa ranan aurenta data farka Ta tsinci kanta a wannan d’akin...!
Gimbiya Turai ta dafe hannayensu su duka biyun tace “Duk wannan iftila’i da rarrabuwan ahali da muka tsinci kawunanmu ciki tuni Allah ya k’addari faruwan hakan saidai akwai sanadi, sanadi kuma Izzatu ce..! Dole mu godewa Allah mu kuma gode masa da a k’arashe ya had’e ahalinmu waje guda..! ‘Yanuwanmu da suka rigayemu gidan gaskiya Ubangiji ya gafarta masu mu kuma idan namu tazo ya d’auki ranmu muna masu imani, mutuwa dole ce hanyace guda d’aya wanda dole kowa sai yabi..! Banaso ku saka ma ranku cewa wani ne ya jawo kuka rasa masoyanku iyayenku da ‘yanuwanku, a’a wani baya rayawa kuma baya kashewa.. Allah shi kad’ai ne mai rayawa ya kuma kashe, duk wanda ya rasu lokacinsa ne yayi saidai wani ya zamto sanadi kun fahimta..!” Suka jinjina kansu a hankali suna masu share hawayensu..! Sun d’an jima kad’an har sukaci abinci tare gwanin dad’I da sha’awa kana sukaima Muhibbah sallama kowa ya nufi nasa b’angaren, Gimbiya Turai ma da nata Hadiman ta nufi nata b’angaren da aka Ware mata na musamman... Can ta tadda Gimbiya Zeenat na zaman jiran K’arasowarta..!
Gabatar da kanta Gimbiya Zeenat tayi had’ida neman yafiya kan biyewa Giwa da tayi Ta kasa tona mata asiri na kisan matar Mahmood Aliya da tayi dan kawai ‘yaruwarta ta auri Mahmood d’in.. Gimbiya Turai tace ai Babu komai itama ta fad’a tarkon Izzatu ne, tana fata abubuwanda suka faru cikin Masarautar ya zamto wa’azi garesu gaba d’aya Dama wad’anda sukaso kwakwayon wannan muggan d’abi’u..!
**
Zama yayi bisa couch yana duban duk wani motsinta tinanin labarinta bai daina Yawo akansa ba... Lokaci guda ya hangota ya fito daga closet, wannan karon doguwar rigar bacci ce mai laushin gaske Wanda ya kwanta luf jikinta..! Ya lumshe idanunsa a hankali yana tunanin idan yana son sanin cewa Muhibbah da Zarah ‘yan uwan junane Toh ya kamata ya d’auko sample d’in Muhibbar cikin daren nan Washe gari ya bada a running masa DNA test tsakanin samples d’in nasu guda biyu..! Toh amma ta ya zai sami sample d’in Muhibbah cikin daren..?!
Ya kuma lumshe idanunsa yana tunanin abinyi, wata zuciya tace kaje ka samo da kanka..!
Yana ganin sanda ta ida sallan shafa’i da wutiri Ta linke abin sallahn ta mik’e ta haye gado had’ida kashe wuta..!
Mik’ewa shima yayi ya zira jallabiyarsa fara k’al sai k’amshi ke tashi ya nufi nata b’angaren..!
Harga Allah bataji shigowar mutum ba dan bacci yayi gaba da ita... Ya jima sosai yana k’are mata kallo da d’an hasken dake hasko cikin d’akin daga waje... Ya zauna a gefenta a hankali yana mai ci gaba da k’arema halittar jikinta kallo...
Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai jin yarrr gaba d’aya stikar jikinsa na tashi... Wata zuciyar tace kayi abinda ya kawo ka ka fice kafin Ta farka ta ganka...!
Da wannan tunanin ya soma zame hular bacci dake kanta a hankali kaman mai tsoron kada ya tada ita ga wani irin bugu da zuciyarsa keyi..!
Cak ya tsaya da abinda yake sanda ya soma sinkayo muryarta cikin tsananin tsoro tana fad’in kada su cutar da ita alamun mafarki take na abubuwan da suka faru da ita..! Tai wani irin k’ara tana mai k’ank’ame jikinta waje guda, juyin da zatai Ta jita cikin jikin mutum ya mata runfa had’ida matseta tsam cikin jikinsa, tanajin hucin numfashinsa alamun yana karanto mata add’u’o’in tsari yana tofa mata..! Zuciyarta yaci gaba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 54 Chapter of 65