Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
“Kaidai saidai kawai Allah ya kyauta duniyar Ta gama lalacewa da kwad’ayi da kuma rowa, mai kud’i baya tausayin talaka kansa da ‘ya’yansa kawai ya sani babu taimakekeniya tsakanin Al’umma, shima talakan baya tausayin kansa ga bak’ar hassada da k’eta da zai samu dama sai yayi zalunci... Hassda da k’eta had’ida bak’ar zalunci sun dabaibaye Al’umma ta yaya kuwa zamu zauna lafiya ba dole bala’u da musiba suyi yawa ba.. Kaidai kawai saidai muce Allah yayi mana maganin abun ya shiryar damu zuwaga tafarkin daidai.. Shi kuma Baffah idan Allah zaisa hakan ya zamto hanyar shiriyarsa ai abin mu godewa Mai Martaba ne daga ni har Hameedar domin kuwa duk kalan wa’azin duniyar nan da ka sani anyi wa Baffah akan kwad’iyin dukiya da jaraban son abin duniya.. Yanzu idan aka barsa haka nan gobe ma zai iya aikata abu makamancin hakan.. Ni naji dad’i da aka masa haka.. Allah yasa hanyar shiriyarsa kenan ..”Turaki ya amsa da Ameen kana ya k’arada “Mu k’arasa Masarautar koh..” Ansar ya amsada “An gama Mai Sarauta..” Tare suka nufi Masarauta motarsu gaba a baya.. ** Suna shiga da Yawale motar suka gyara maza zamansa suna masu risinawa had’ida gaidashi.. Mamaki ya cika Yawale.. Yana ‘yan koke kokensa yana fad’in “Bintu shikenan ashe ba da rabon na miki sallama ba.. Ni kuma haka Allah ya k’addaro min.. Oh ashe dai ajalina ne yazo..!” Cak Yawale ya dakata da koke kokensa yana duban mutanen, cikin rawar jiki da rawar murya yace “Yal.. Yallab’ai nace ba.. Dama wllhi inaso ince maku na tuba.. In sha Allahu ni bazan sake aikata abu mai kamada haka ba.. Kuma kud’in auren yarinyar yana nan idan kuna so sai in baku.. Shikenan ku rabu dani salin alin in komaga iyalina.. Yallab’ai Iayalai ne dani nid’in..!” Ya k’arashe yana d’ago masu hannu alamun rok’o.. Babu dai wanda ya amsasa cikin su har suka shigo cikin Masarautar... Tsaban tsoro da tsananin tashin hankali da Yawale ke ciki baima fahimci cewa Masarauta ce suka shigo ba.. Shidai damuwarsa kawai su k’yalesa ya tafi... Suka isa wani b’angare nan cikin Masarautar aka bud’e masa k’ofa bayan driver ya ida parking... Guda d’ayan ya dubi Yawale ya risina yace “Muje Baba..” Yawale yace “Na’am.. Toh toh.. Yallab’ai nace dai a duba lamarin kar a yanka ni wllhi Dattijo ne ni akwai iyalai.. Na baro iyalai gida..!” Guda d’aya yace “Baba mu shiga daga ciki za’a baka sutura ka shirya sannan ka gudanar da sallar mangariba kafin a kaika kaga shugabanmu...” Zuciyar Yawale Ta kuma tsinkewa, shikenan saima an shiryasa kafin akaisa ga shugaban mayankan.. Kaico son duniya irin nashi.. Bai tab’a nadaman kwad’ayi da son abinda duniya da yake irin na yau ba.. Wato ashe haka yarinyar nan Muhibbah taji.. Allah sarki ya cutar da ita.. Watak’ila ma har an yankata ansha jininta.. Yau gashi yanajin irin abinda taji.. Baisan ya akai ya isa cikin k’atoton parlorn na alfarma, dogari guda yai masa rakiya zuwa wani d’aki.. Yawale ya saki baki da hanci yana duban kayan alatu a wannan gida.. Nan fah ya mance da cewa mayanka aka kawosa sai jinjina mak’udan kud’ad’en da aka kashe a wannan tsararren gida yake wanda ya masa lak’abi da aljannar duniya.. A hankali yake furta “Wai dank’ari mak’ari Aradu wagga gini kinci kud’in kayukan bil’adama.. Allah kad’ai yasan Kayuka nawa akayi ginin nan dasu...!” Yai tsit kuma yana tuna Toh wato dai yanzu harda nasa kan za’a k’ara watak’ila sai gidan yafi haka tsaruwa idan aka k’ara da nasa kan... Ya cire hularsa ya shiga shafa kansa kaman mai auna size din kan nasa... Ga tsananin mamakin Yawale kaya irinta masu mulki aka basa, kaya masu matuk’ar tsada harda rawani.. Ya juya kayan yana kuma furta “Ikon Allah kenan.. Su kuma wad’annan tufafi fah.. Toh kodai kar yasa ne.. Amma idan bai saka ba rabjejen mutumin nan idan ya kuma shigowa ya taddashi fah..? Wata zuciyar tace ai gwara ka saka kayan kafin su yanka ka ko banza ka tab’a saka kayan masu mulki irin haka... Yawale am ka shiga tarihi.. Ya k’arashe tinanin nasa yana kwab’e nasa gajiyayyun tufafin... Koda Yawale ya fito zasu tafi fannin oga Sai rarraba idanu yake yana mamakin mutanen da suka kamosa sun sauya shiga sun saka jajayen tufafi masu ratsin koriya irin tufafin dogarai.. Mamaki ya cika Yawale musamman da suka fito yaga dogayen benen da suke ciki masu zubi da gidajen masu mulki.. Ikon Allah toh meke faruwa ne... Ya tambayi kansa cikin zuciyarsa... Yaga sunata shige mutane sahu sahu kama daga masu shiga irinta Bauta zuwaga masu shiga irinta muk’ami, yaga duk sanda zasu shige taron bayi sai an risina an gaidashi.. A’a Yawale naku fah Sai ya soma k’umewa yana wani jin kansa yana jinjina kai alamun amsawa.. Jin kansa yake yawa wani basarake... A haka suka iso babban Parlorn Mahmood wanda tsarinsa da kyaunsa yasha gaban wancan parlorn da aka soma sauk’an Yawale.. Ya saki baki da hanci yana kallon chandeliers ta ko ina sai wal wal suke kaman wani rana.. A fili yake furta kalman yabo ga wanann gida mai matuk’ar kyaun gaske... Sanda zasu shiga asalin Parlorn da Mahmood Ke ciki yaji muryar Dogarai masu tsaron wannan k’ofar suna furta Gyara kimtsi..! Gyara kimtsi da kyau..! Had’ida masa maraba da isowa... Yawale yaci gaba da Washe baki yana jinina kai... Suna shigowa parlorn ya hango wani kyakkyawan Basarake zaune saman kujera yasha kwalliya cikin tufafi irinta masu mulki, kallo guda zaka masa ka fahimci shid’in Basarake ne.. Gefe dashi saman darduma kuwa matsa ne guda biyu.. Bai ida tantance matasan ba saida ya k’araso sosai yaga ashe Ansar ne d’aya matashin d’ayan kuma kaman yaso ya gane fuskarsa.. Yawale ya k’arasa kusan Ansar yana furta “Yakubu..! Yakubu ina ne nan..? A ina muke..?” Muryar Mahmood ya sinkayo yana furta “Barkada k’arasowa Baba..! Fadah tayi Farin ciki da tarban bak’uncinka..!” Yawale ya kaikaito da k’yar yana so ya d’ago yanda yasan muryar.. lokaci guda yake duban Mahmood dukda tsananin gizo da k’wayar idanunsa ke masa.. Tabbas yaso ya gane wannan k’wayan idanu da karan hancin.. Ya shiga tuna a cikin nad’in Buzaye yaga wannan k’wayan idanun.. Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa sanda ya kuma waigawa da sauri yana duban Turaki dake gefe wanda a zuwansu na farko shi babu nad’in Buzayen a tattaredashi.. Barde ya bud’e murya bayan Mahmood ya ida magana yana furta “Godiya yake Sarkin Sarakuna..! Dattijo yana godiya da karramawa Sarki...!” Hannu na rawa Yawale ya shiga nuna Turaki yana furta “Yakubu gasu nan.. Wad’annan sune suka amshi auren Muhibbatu..! Alhamdulillah Allah ya nuna mana su.. Yanzu sai a warware aure kaga sai a fasa cinikin kaina...” Barde dake tsaye daga gefe ya furta “Hattara Dattijo kana gaban Mai Martaba Sarki ne..! Hattara da kalamanka Dattijo Sarki baya saki.. Gimbiya Ta shigo gidan Alkhairi.. D’iyar masu mulki ce kuma matar masu mulki.. Jaaa zamanin Dogon Sarki...Sarki Mahmooda ibn AbdulJabbar..!” Tinda Barde ya soma magana zuciyar Yawale ke ci gaba da tsinkewa... Meke faruwa..? Wannan mutumin Dama Sarki ne.. Gimbiya..? Wacece Gimbiya..? Muhibbar ce Gimbiya..? Yai saurin juyowa ga Ansar yana furta “Yakubu meke faruwa ne a nan.. Shin ina kasan mutanen nan..?” Ansar yace “Baffah wannan Sarki ne.. Kuma shine ka aurar masa da Muhibbah b’adda kamanni yayi dan ya ceci Muhibbah daga gadar zaren dakaso k’ulla mata.. Shid’in d’an uwanta Baffah.. Muhibbah asalinta d’iyar masu mulki ce kuma ma d’an uwanta ka aurar da ita.. Gida Ta koma Baffah.. Shine yace azo dakai domin Masarauta tayi maka karramawa na musamman...” Ansar ya k’arashe murmushi saman fuskarsa.. Innalillahi wa Inna’ilaihi raji’un..! Tinda Yawale yake bai tab’a jin kunyar duniya irin wanda yaji yau ba.. Wato ashe haka al’amarin yake.. Dukda sanyin Ac dake circulating cikin parlorn bai hana zufa tsartsafowa Yawale ba.. Allah mai iko.. Yanzu ashe Dama wa Sarki ya aurar da Muhibbah.. Kai jama’a Kaicon hassada da son zuciya.. Mai za’ayi da hassada da k’yashi.. Ubangiji Allah ka tsarkake mana zukatanmu ka nisantamu da wad’Annan munanan d’abi’u.. Ai tuni hawaye suka soma zarya saman kumatun Yawale.. Ya kasa kaikaitowa ya dubi yanda Mahmood Ke zaune saima juyawa da yayi gaba d’aya ya basu baya hawaye naci gaba da gangaro masa.. Ansar ya rarrafo kad’an ya kamo hannayen Yawale yana fad’in “Baffah, ka juyo kayi ma Sarki gaisuwa sannan kai masa godiya...” Girgiza kai kurum Yawale yake yana ci gaba da hawaye yake furta “Yakubu bazan iya ba.. Allah ya gani bazan iya juyo ba.. Kace ma Rankaidad’e ya yafeni.. Kace ma Gimbiya Muhibbah ta yafeni.. Wllhi sharrin zuciya ne da son abin duniya had’ida muguwar hassada da k’eta... Yakubu kace Rankaidad’e ya yafeni.. Na tuba wllhi..!” Kuka ya hana Yawale ci gaba da magana... Turaki ya k’araso gabansa ya duk’a yace “Baba bakaima Sarki laifi ba.. Hasalima dan yayi maka godiya ya gayuaceka Fadah tareda karramawa..!” Yawale da hawaye da gumi suka wanke masa fuska girgiza kai yake yana duban Ansar da Turaki yake furta “A’a.. Wllhi A’a ni ne nazo neman gafara da yafiya.. Kuyiwa Allah kuce Mai Martaba ya yafeni na tuba wllhi.. Itama Gimbiya ta yafeni...!” Yaci gaba da matsan k’walla.. Da k’yar Turaki da Ansar suka sa Yawale ya kaikato daga nan yanda yake duk’e yana fuskantar Mahmood.. Turaki ya d’anyi gyaran murya kad’an bayan shud’ewar wasu dak’ik’ai kana yace “Alhamdulillah..! Mun gode ma Allah da yasa ka fahimci kuskurenka Baba.. Ina kuma fata wannan ya zamto wa’azi gareka da masu hali irin naka... Ka aurawa Mai Martaba macen da yake matuk’ar k’auna a lokacinda kake da ikon aurartaga waninsa dan haka ka cancanci kyauta daga Masarauta dukda cewa da wani nufi kayi hakan cikin zuciyarka.. Allah yasa wanann ya zamto izna a gareka damu baki d’aya.. Kar dan ka samu dama akan mutum kace zaka cutar da rayuwarsa baka San mai gobe zata haifar ba..!” Cikin rawar murya had’ida rawar jiki Yawale Ke furta “Wannan gaskiya ne.. Wannan gaskiya ne Rankaidad’e.. Allah dai yayi mana tsari da sharrin zuciya..” ya saci duban Mahmood yana mai kuma duk’awa had’ida d’ago babbar yatsa yake furta “Godiya nake Allah shi taimakeka..! Tuba nake Allah shi baka yawan rai.. Ja zamaninka angon Gimbiya Hibbatu d’iyar albarka..!” Shi kansa Mahmood saida Yawale yaso basa dariya.. Ansar da Turaki suka murmusa a hankali kana Ansar ya dubi Mahmood wanda shima gajeriyar murmushi ne saman fuskarsa yace “Your Highness zan tafi dasu masauk’i idan kamin izini..” Mahmood ya jinjina kai yana mai alamawa Turaki da ya k’araso.. Turaki ya matso yana sauraron sak’on da yake basa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... Ko da gani kasan bazai shige kyautukan karramawa yake umarta a baiwasu Yawale... Sukai masa sallama had’ida godiya kana suka fice tareda rakiyar Turaki.. Yawale yana fad’in shidai so yake yaga Murjah yayi mata murnan wannan babban al’amari mai dad’in ji sannan idan da hali ma yaga Gimbiya Hibbatu ya nemi yafiyarta da gafararta ya kuma mata murnan wannan babban abin arziki da ya sameta... Sun sami ganin Mommy harma da Muhibbah kasancewar a daren za’a rufeta a lalle kaman yanda yake a al’adarsu sai kuma Washe gari akaita d’akinta kai tsaye bayan an rufa mata Alkyabba Ta amarci, nan Yawale yayita neman afuwa a wajenta, shima Ansar ya rok’eta Gafaran abinda yayi mata da Mahmood.. Fadah ta kuma cikada albarka.. Su gudidi ba’a sama ba’a k’asa an samu karamci Sune kan gaba wajen saka Amarya a lalle.. Sai pictures ake ana watsawa social media ko wanne picture da Gudidi zata maka status sai tayi caption maiji da lafiya tace gasu waje kaza Iyayen matan Sarki.. Mommy dai saidai ta kalleta ta murmusa tace oh su Gudidi budurwar zuciyar na nan dai ba’a girma ma hidiman social media.. Gudidi tace ah zamaninsu ne dole su shana ina ta tab’a zaton zata zamto k’awar Maman Matar Sarki da kansa.. Hidima yayi hidima ta ko wanne b’angare sai son barka.. Washe gari tun bayan ida sallan asubahi tambura da algaita Ke tashi cikin masarauta, lokutan sallah ne kurum yake sanyasasu tsagaitawa ana idar kuwa sautin algaita zaici gaba da tashi.. Matayen masu Mulki dasu Mommy harma da Gimbiya Zeenat su suka raka Amarya Muhibbah sashen mahaifiyar mijinta Gimbiya Turai.. Sai gud’a mata suke, nan aka rufa mata sabuwar Alkyabba k’ar mata naci gaba da gud’a .. Masu zuba turare nayi masu rawa nayi.. Masu fatan Allah sanya albarka nayi.. Zigazigai kuwa Sai kod’a Amarya da ango suke harma da uwar angon da Marigayi mahaifin Amarya Wato Yarima Alfah.. Duk wannan hidima Raheemah na k’ume a d’aki tana sharb’an kuka dan akan kunnuwanta komai ke faruwa saidai ko fitowa ta k’asa saidai kawai taga pictures a status din Umaima.. Ko asibti wajen Yazeed ta kasa komawa, tana nan k’ume a d’aki tana cazgan kuka.. Su Zahra dasu Umaima dasu Meenatu suma dai da alama ‘yan team d’in Aunty Gudidi ne ‘yan ayi pictures a tura status ne... Sai pictures suke Meenatu na turo ma K’awayensu da basu samu halarta ba.. Kai saidai ace Masha Allah komai ya tafi yanda ya kamata... Su Mommy sukai mata rakiya har sashenta dake nan cikin Masarautar yanda komai kama daga finiture zuwa duk wani abin buk’ata na cikin sahen a tsakanin satin Rankaidad’e yasa akayo order.. Allahu Akbar yau dai ga Muhibbah cikin d’akinta sosai suka rungume juna itada Mommy suna kuka su Gudidi da Aunty Salma Sai basu baki suke.. Mommy ta kuma mata nasiha kan rayuwa da abinda ya shafi zamantakewa na aure domin kuwa sabon babin rayuwa zata soma.. Daga bisani sukai mata sallama kowa ya koma masauk’insa... Tana nan zaune tana tinanin rayuwarta tin daga farkon abinda ya sameta a wannan masarauta har zuwa had’uwarsu da Rankaidad’e da yanda Allah ya k’addari faruwan abubuwa... Sam batasan lokaci yaja ba tana nan zaune taji k’amshin turarensa nayima hancinta sallama.. Ya zauna gefenta kad’an yana mai tsareta da idanu har lokacin fuskarta rufe take cikin alkyabbar.. Zuciyarta taci gaba da tsinkewa jin ya zauna gefenta.. Hannunta guda dake aje saman gadon ya kai nasa hannun ya d’aura saman nata.. Lokaci guda yai amfani da d’aya hannun ya yaye alkyabbar dake rufe fuskarta.. Yai mata K’uri yana duban yanda hawaye ke kuma gangarowa daga cikin idanunta... A hankali yake furta “I thought kuka ya k’are tunda baza’a sake jarabawar ba..Unless kuma kina so a sake..?” Ya k’arashe tamkar bashin yai maganar ba ‘yan yatsun hannunta cikin tafin hannunsa... Ta saki murmushi a hankali tana mai sanne kai had’ida mak’ale kafad’a, ya murmusa kad’an wannan karon yace “Have you eaten..?” Ta jinjina masa kai a hankali alamun eh.. Cikin kashe murya yace “You sure..?” Nan ma jinjina masa kai tai.. Goran fresh milk da ya shigo dashi ya shiga bud’ewa yana furta “But still you’ll drink this..!” Ta d’an marairaice fuska tace “Nifa na k’oshi your Highness..” Bai daina abinda yake ba, cikin tsarewa yake furta “Do I need to remind you your Highness, ko kin mance ba’a gardama a Fadah.. so just open your mouth and drink all this.. I need an empty bottle.” Ya k’arashe yana mai matso da goran saitin bakinta.. Yana furta “If you don’t drink this zamu sake sabon jarabawa yanzun nan.. So just drink it..!” Kaman zata kurma ihu haka ta lagnab’e kanta waje guda.. Yanda ya tsareta da rikitattun idanunsa ya sanyata bud’e bakinta a hankali tana mai shan madaran da k’yar.. Bata wani sha sosai ba tace ta k’oshi saidai Mahmood bai k’yaleta ba saida ya tabbata tasha sosai.. Ya gyara zamansa sosai yana dubanta kana yace Ta shiga bathroom tayo alwalwa tazo suyi sallaha.. Jikinta a matuk’ar sanyaye Ta mik’e Ta nufi closet, cire alkyabbar jikinta tai ta lank’aye kana ta nufi bathroom ta d’auro alwala kaman yanda ya umarceta.. A nan closet d’in ta tsaya duba hijab yanda ta samesu a shirye a anjesu a mazaunansu.. Ta d’auko wani dogo har k’asa mai ruwan k’asa ta zira kana ta komo cikin d’akin yanda Ta hangi bayansa yana shimfid’a masu abin sallah.. Jallabiyarsa fara k’al sai d’aukan idan take.. Tai tsaye a wajen tana dubansa.. A hankali ya kaikaito yana dubanta yanda tai tsaye nan wajen.. Ya sakar mata murmushi kana ya soma takowa gaba gareta.. Hannayenta ya kamo yana duban kyakkyawan fuskarta dake duban k’asa... A hankali ya matso da ita cikin jikinta had’ida manna mata kiss a goshi, Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali tanajin sauk’an labb’ansa had’ida hucin numfashinsa saman goshinta... Murya can k’asa ya furta “Lets pray mu kuma godewa Allah da wannan babban Ni’imah da ya lullub’emu dashi..!” Ta jinjina masa kai a hankali har lokacin k’asa take duba, ya shiga janyo hannunta tana binsa kaman rak’umi da akala har saida suka isa saman abin sallar tasu.. Mahmood yai masu limanci suka sallaci raka’a biyu na nuna godiya kaman yanda yazo a sunnah... Ya kuma kama forehead d’inta ya karanto addu’an neman alkhairi da tsari... Daga nan janyota cikin jikinsa yai yana mata tambayoyin da suka shafi addininta musamman b’angaren fiqhu tana basa amsa daidai gwargwado, dukda wani irin bugu da zuciyarta keyi.. Yanda yake mata tanbayoyin cikin sigan raha har sai ya sanya ta soma sakin jiki dashi.. Idan Ta basa amsa sai yai murmushi yace ashe dai zata lashe wannan jarabawar..! A haka dai salon jarabawar tasu Ta soma sauyawa.. Tun tana fahimtar tambayoyin Sarkin nata har dai ta kasa banbance yaren da yake mata jarabawar da ita... Tabbas wannan jarabawa yafi duk sauran jarabawar da yai mata a baya... Dare ne mai matuk’ar mahummanci a gareta kaman yanda yake a wajen ko wacce d’iya mace.. Saidai in her own case can k’asan zuciyarta tanajin kaman ba haka zai kasance a gareta ba bayan tuna tsautsayi da iftila’in da ya faru da ita da tai... Dukda kuwa cewa Angon nata zallan k’aunarta yake nuna mata... Sosai ta k’ank’ame bedcover tana kuka da duka zuciyarta harda shesshek’a.. Wanda hakan ba k’aramin karyar masa da zuciya yai ba... Tausayinta gauraye da k’aunarta na kuma ratsa duk wani k’ofa na zuciyarsa... A hankali ya matso kusanta ya janyota cikin jikinsa... Kaman zatai magana amma kuka ya hanata.. “Shiii!” Ya furta yana mai kwantar da kanta cikin k’irjinsa, lokaci guda hawayen zafin zuciya ya d’igo daga cikin idanunsa zuwa cikin sumarta...A hankali yake fad’in “Don’t say a word..! I love you.. I love you so much.. I love everything about you... Just stay right here..!” Ya k’arashe yana mai sumbatar cikin sumarta had’ida lumshe idanunsa... Wani hawayen ya kuma d’igo masa.. Allah ya gani baida tabbacin zai tab’a yafe wa su Yazeed... A wanann dare Mahmood ya tabbatar mata shid’in masoyinta na gaskiya ne.. Haka yaita tarairayanta yana nuna mata soyayyarsa mai tsuma zuciya.. Safiyar washe gari idan Ta tina abubuwan da suka faru saidai ta kulle fuskarta taita sakin murmushi a hankali.. Anya ma zata iya sake had’a idanu da Rankaidad’e..? Ta shiga girgiza kai ita kad’ai tana mai kuma sakin wani murmushin a hankali.. Gaba d’aya jiyan ya juye mata tamkar dai ba Rankaidad’e data sani ba, ko ina sarautar tasa suka tafi oho.. Ta kuma murmusawa a hankali tana tuno kalamansa a gareta... Murmushi bai bar saman fuskarta tayi k’uri ma hasken hantsi take furta “Allah ya tsare mun kai Rankaidad’e..!” Ta k’arashe tana mai kuma lumshe idanu tsan tsan k’aunar mijinta na fuzganta....Shige da ficen Hadimai da take saurarowa daga downstairs ya sanyata mik’ewa a hankali Ta nufo k’asan nan kuwa Ta tadda su Meenatu da Umaima shigowarsu kenan suma.. Meenatu ta shiga zolayarta da fad’in Amarya baki laifi ko kin koda kin k’ona Karagar Sarki..” Bata amsata ba Sai hararar da take jifanta dashi... “Tuba nake Rankidad’e kar kisa Dogarai suyi majajjawa dani...” Sai sannan Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Kedai bazaki bar hali ba... !” Meenatu tace “Ina kuwa zan bari Rankidad’e, ni yanzu haka ma zuwa nai na miki sallama anjima zamu tafi..” Muhibbah Ta zaro idanu waje tace “A’a Haba banson rashin M.. Ai dai zaki jira ayi nad’in sarauta...” “Anya kuwa Toh Bandai San mai Mommy zatace ba dan dama kwana biyu Mama ta bani..” Muhibbah Ta katseta da fad’in “Ba sai na kira Maman ba nace a barki kiyi sati..” Meenatu Ta zaro idanu tace “Sati.! Ai sai kisa Sarki ya koreni garinmu babu shiri..” Umaima ce ta k’araso waya mak’ale kunnenta tana fad’in “Eh Ummi ta tashi lafiya.. Muna can side d’in nata ma.. Okay I’d make sure she eat..” Daga sallama sukai Ta zauna daga gefe tana fad’in “Surkarki ta kira tana tambayan ko kinyi breakfast, nace mata kar ta damu muna nan a nan, we’d feed you if we had to tinda hidiman sarauta ya hana Angon zana balle ya kula da amaryar tasa..!” Ta k’arashe cikin sigan zolaya... Suka d’an dara gaba d’aya Muhibbah na fad’in “Zaki sani ne..” daidai lokacin Mommy dasu Aunty Gudidi sukai sallama ga Kuyangi biyedasu nik’i nik’i da kaya.. Gudidi na baiwa Hadiman umarnin yanda zasu aje kayan.. Su Gudidi abin nema ya samu sai bada doka da order ake.. ** A b’angaren Mahmood ma yanda take yau d’in babban rana ce a gareshi kaman yanda daren jiya ya zamto babban dare mai cikeda alkhairai a gareshi, yanajin kaman bazai iya amsar shugabancin nan ba domin kuwa ko shakka babu Sarautar ya shige hakkinsa.. Kamata yayi ace yanzu yana tareda amaryarsa yana tarairayarta amma gashi wannan hidimar sarautar ya hana faruwan hakan, shi gaba d’aya ya soma tantama idan zai amshi mulkin... Isowar Turaki ya katse masa tunanin nasa... Barde ya shigo ya zube yai gaisuwa kana ya sanar da zuwan Turaki... Mahmood ya basa izinin shigowa... Daga yanda Turaki ya gansa ya fahimci abokin nasa ango yake, dan kyakkyawan annashuwa na musamman kake hangowa saman fuskar tasa mai cikeda gizo... Tun kafin Turaki yakaiga mik’o gaisuwarsa Mahmood ya soma fad’in “Ba’a Turaki da yaro..!” Turaki ya duk’a yana masa jinjina yake furta “Rankaidad’e..!” Mahmood ya kuma fad’in “Ba’a Turaki da yaro..!” “Rankidad’e.. Godiya nake..!” Turaki ya kuma fad’i yana masa jinjina murmushi saman fuskarsa... Lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Galadima ya sanar dani komai ya kammala fitowar ka kawai ake jira Rankaidad’e.. Already an bud’e Babban Gwani (Fadan Mai Martaba Sarki) anyi all the necessary arrangements.. Sarakun yankinmu na kusa sun soma isowa.. Hakimai da manyan masu muk’amin cikin masarauta duk sun hallara kaid’in ake Jira Rankaidad’e..” Ya k’arashe yana mai kuma d’ago masa yatsa alamun jinjina... Mahmood yai shiru tamkar mai nazari wanda har saida yasa Turakin d’gowa yana dubansa... A hankali Mahmood Ke furta “Im not sure Turaki.. I think I’m having a second a thought...!” Turaki ya d’an dubesa da mamaki yace “Ban gane ba your Highness..!” Mahmood yaci gaba da fad’in “I just want to be with my wife.. That’s all Turaki... Babu hidimar sarauta babu damuwar komai..” Turaki ya d’an fuzar da huci yace “But your Highness..” Katsesa yai da fad’in “Can’t you see I’m stuck here... Turaki I can’t do this anymore.. I’m stepping down..!” Ya k’arashe yana murza zobban dake hannunsa.. Turaki ya d’an fuzar da iska kad’an yace “I understand where you’re coming from Your Highness... But ya kamata ka fahimci girma ne ya hau kanku both you and your wife, dole ku sadaukar wasu lokutan naku ga al’umma.. Your Highness you can’t back down now.. I mean ya zamuyi da d’imbin manyan mutanen da aka gayyata.. Mai zamu fita mu sanar dasu..?!” Mahmood ya shafe fuskarsa a hankali had’ida fuzar da huci “Just come up with something.. Whatever, ko kuma a nad’a wani ba dole sai ni ba..” Baikai aya ba Turaki ya katsesa da fad’in “But you’re their choice.. Kaine zab’in mutane.. People chose you.. I’m sure you don’t want to disappoint your People... Babu wanda yafi cancanta sama dakai your Highness.. Na tabbata ita kanta Muhibbah bazata so jin haka daga gareka ba balle Ja’afar da mahaifiyarka.. Please do this for them.. for your people.. And for me as well..!” Ya k’arashe cikin tsananin rauni... Mik’ewa Mahmood yai suna duban juna shida Turakin... Lokaci guda yake furta “Ko da yaushe kana tare dani, through good times and worse... Ka wuce aboki a wajena Turaki.. You’re my brother, kai d’in d’an uwa ne a wajena... Today I want to thank you from the bottom of my heart...For everything...” Katsesa Turaki yai da fad’in “That’s what brothers are for... Bani da buk’atan kamin godiya your Highness.. Fata ne shine Allah ya sanya maka albarka a aurenka ya kuma yi maka jagoranci a shugabancinka.. Allah

Chapter 62 of 65