Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
k’arashe da alaman tambaya.. A hankali Umaima ta jinjina kai kana tace “Tabbas ga babban misali akaina, kaman yanda kikai magana haka Jafar Ke fad’a min... Alak’armu dashi sam bazai d’ore ba, kuma hakance ta kasance...!” Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Nan kuma Ina mukazo...?” Umaima ta saita kanta “Nan shine sashen Ya Yazeed da matarsa Gimbiya Zuhra, zamu shiga ku gaisa...!” Ta jinjina mata kai sanda suke shiga gate d’in sashen.... Tangamemen sashe ne mai ji da kyau da kuma tsari... A hankali take k’arewa sashen kallo har idanunta suka sauk’a zuwa parking lots, yanda hanshak’an motoci na alfarma Ke jere cikinsu ko wacce mota d’auk take da plate number mai sunan *Prince Zeed* hankalinta yafi karkata kan wata Jeep k’irar Ford, take hotunan abubuwan da Ta gani daren jiya suka shiga dawo mata, tabbas wannan motar ta gani ya shigo cikin Masarautar a daren jiya, nan kuma tunanin Rahima yazo zuciyarta... Kai tsaye bazatace itace ta gani ta shige sashen da Umaima ta ambata da sunan na Aunty Zeenat ba, toh amma mai yakai motarta k’ofar Bayi..? Sannan Maiyasa Ta razana sanda ta gansu...? Could it be Yazeed da Rahima ne jiya suka dawo Masarautar cikin dare..? Idan kuwa har haka d’in ne da gaske zatafi kowa Farin ciki... ! Ta saki murmushi mai cikeda ma’anoni tana ayyana abubuwa da dama cikin zuciyarta, zatai k’ok’ari Ta gano bakin zaran komai cikin gaggawa... Allah sa hasashenta ya tabbata haka d’in domin kaw wannan ba k’aramin gudumawa zai baiwa mission d’inta ba... A haka suka nufi cikin gidan ** A b’angarensu Yazeed kaw K’uri sukai masu har saida yaga yanda suka shige Wato sashensa, saida ya tabbata sashensa yaga sun shige kana ya jefa gyad’a k’wara d’aya a bakinsa had’ida furta “Bingo..!!” Yai maganar yana mai sakin shu’umin murmushin nan nasa... Jamal ya furta “Wacece ita...?” Fu’ad da ya kasa janye idanunsa ya furta “She’s... Beautiful...!” Juyowa Jamal yai yana duban Yazeed dake ci gaba da jefa gyad’arsa a baki yanai masu wane irin tauna mai cikeda kasala da izza ya had’e rai kaman bashi bane ya gama murmushi yana furta Bingo... D’an girgiza kansa yai dan yasan wanene Yazeed ya kuma San mai yake nufi da ya furta Bingo.. Wato tama fad’a sashensa da kanta...Lokaci guda Jamal ya d’anyi gyaran murya kana yace “Probably ‘yar uwar Maami ce tinda gata tareda Umaima...” Fu’ad yace “But how comes bamu tab’a saninta ba...?” Jamal yace “Must you know everyone.. .” “No, naga dai tanada kyau ne... Ya kamata ace mun santa...” Ya k’arashe yan gutsiran apple da yaketa faman juyawa a hannunsa... Jamal ya d’an murmusa da gefen baki kana yace “But fuskarta ya min kaman na tab’a sanin mai irinta wani waje...” Katsesu Yazeed yai da fad’in “Cut it out you two, dik wannan yaba kyaunta da maganan da kuke none of you, babu d’aya daga cikin ku da yakeda courage d’in fad’i a gabanta... Let’s start with you vet Dr Jamal... Kai yaushe ma ka fara son mata..? Koda wasa ban tab’a jin kayi zancen mace ba, saidai ka k’are da duba lafiyar dabbobi...And you Fu’ad...” Yai murmushi mai cikeda k’asaita kana yace “Babu macen gaske wacce ta amsa sunanta mace da zata kula mahaukaci irinka dikda kuwa sanin cewa kai d’in jinin sarauta ne, kai inaga saidai a k’are a cikin kuyangin gidan nan a aura maka guda d’aya... Tarihi ya maimaita kansa kaman yanda Yayanka ya auri ‘Yantacciyar baiwa....So ku dena b’ata lokacinku ku already...!” Murmushi da gefen baki Jamal keyi kana yace “Well, kar kayi gaggawa dear brother... Duk duniyar nan mutum d’aya ne tak yasan Ko ni wane irin mutum ne... But idan haka ka d’auka then be it...After all, banida lokacin mata kaman yanda kace...!” Ya k’arashe murmushin saman fuskarsa.... Fu’ad da kalaman Yazeed sukai matuk’ar masa zafi, jinjina kai yai kana yace “Kana tinanin kai kad’aine Yariman da mata Ke rububi Prince Yazeed, well let me remind idan ka mance...Babu abu guda da kake tak’ama dashi wanda ni Fu’ad banida shi a fuskar halitta... Kwalin karatu da kake tak’ama dashi zan iya komawa makaranta a yanzu don bai k’ure min ba, I’m still young.. I can still make it...!” Ya k’arashe yana sakin fuci a hankali... Gira d’aya a sama Yazeed ke dubansa kana ya murmusa da gefen baki yana mai jefa gyad’arsa a baki lokaci guda yaci gaba da furta “Well, yanda muka banbanta ni bani bane zanbi matan su suke bina su suke kawo kansu gareni... Just like yarinyar da yanzu kuka gama sunbatu akanta, kuna gani dai akan idanunku ta shige b’angarena.. Kuma kaman yanda ta shige haka sauran matan suka kawo kansu... Yarima Yazeed baiga macen da takai shi ya nemeta ba saidai Ta kawo kanta har yanda yake...!” Ya k’arashe yana karkad’a k’afa daga kishingid’e cikeda izza... Fu’ad ya kuma fuzar da fuci a hankali yana k’ok’arin mik’ewa Daga wajen Yazeed ya katsesa da fad’in “But still, zan baka chance idan har kana sonta... I challenge you to win her heart first... Zaka iya...?!” Ya k’arashe yana mai d’aga gira guda sama had’ida tsare Fu’ad da idanu... Fu’ad yai tsaye yana dubansa tamkar bazai ce komai ba yayinda Jamal ma ya zuba masu idanu.... Yazeed yaci gaba da murmusawa yana mai furta “Jeka abinka and keep on doing drugs, that’s what suits you after all....!” Fu’ad bai iya furta komai ba sai zuciyarsa dake ci gaba da bugu, har yaushe Yazeed zai daina d’aukansa useless mutum maras amfani, har yaushe zai daina jifansa da muggan kalamai.... Yai tsaye yana sakin huci yana duban Yazeed... Jamal ya d’anyi gyaran murya kana yace “Fu’ad jeka abinka... Jeka ka soma shirin taron da za’ai anjima... Gani nan biyeda Kai...” Fu’ad ya girgiza kai alamun a’a... Kana ya mik’awa Yazeed hannu alamun masabaha yace “Challenge accepted... Prince Yazeed AbdulJabbar...!” Yazeed ya d’ago da mamaki yana duban Fu’ad, kana ya saki cruel smile d’in nan nasa... Bai mik’a masa hannun ba saima kwalbar gyad’a da ya dank’a masa kana yace “Kayi replacing drugs da wannan...!” Fu’ad da k’walla Ke neman ciko idanunsa cikin sauri ya bar wajen tamkar zai kifa k’asa... Jamal ya dubi Yazeed dake ci gaba da sakin murmushinsa kana ya girgiza kai “Yazeed ina tsoron ranan da zaka Kai Fu’ad bango ya bud’i baki ya fad’iwa Mahmood komai, dik abinda muka aikata... Dan Allah ka k’yale yaron nan haka he’s suffering already....!” Da gefen idanu Yazeed ke dubansa, saida dak’ik’ai suka shud’a kana yace “And what makes you think ina shakkan Mahmood yasan wani abu gameda rayuwata... I got nothing to be ashamed of... Idan da akwai wanda zaiji kunyar bayyanar abinda ya aikata a baya that person should be Mahmood.... Sabida ni dik barikancina ban yarda na bar tabo wa Zuri’ata ba...Cikin yarana guda biyu babu shege....!”Ya fad’i cikeda isa.... Jamal ya dubesa da mamaki kana yace “Ban fahimceka ba... Maiyasa kace haka...?” Yazeed ya kuma murmusawa kana yace “Kune Mahmood ke cika maku ido da salonsa na yaudara, amma bani ba... Babu wanda ya tab’a shafawa Masarautar nan irin abin kunyar da ya shafa mana...!” Jamal ya kuma girgiza kai kana yace “Yazeed Wai mai kake cewa ne...? Mai kake nufi... Please explain it to me...!” Duban Jamal yai yana mai gyara kishingid’arsa kana yace “Ask him about his daughter... Da aure ya haifeta kokuwa ciki yayima d’aya daga cikin ‘yanmatansa... Ask him idan Aliya matarsa ce ta haifa masa yarinyar...!” Ya k’arashe yana girgiza had’ida tsare Jamal da idanu... K’irjin Jamal bai daina bugu ba yake girgiza kai alamun a’a... Lokaci guda yake furta “No...no Yazeed... This is not possible...!” “Of course it is..!” Yazeed ya katsesa da fad’in haka kana yaci gaba da fad’in “So tell me Jamal, among us all wankeda bak’in tabo a tattaredashi....? Wa yafi cancanta yai sarautar k’asar nan...?” Share gumin da ya tsartsafo masa Jamal yai yana mai furta “Maami Ta sani...?” Yazeed ya tab’e baki kad’an kana yace “Duk duniyar nan babu wanda ya sani, daga ni sai Abokinsa Turaki... And now that I told you everything, ina son full support d’inka wajen neman Karagar mulkin nan, idan ba haka ba kuma zan fasa kowa yaji a Masarautar nan...!” Jamal ya shiga girgiza kai yana furta “No, no Yazeed hakan na nufin downfall d’inmu ne gaba d’aya, it will affect us all, including our mother...!” Yazeed ya jefa gyad’a bakinsa yana mai d’aga kafad’a guda alamun ko a jikinsa yayinda Jamal yaci gaba da jinjina lamarin cikin zuciyarsa... Tsananin mamaki kwance saman fuskarsa... Ya kasa aminta da abinda ya gama sauraro daga d’an uwan nasa... *** Shigowan su Muhibbah da kad’an Rahima tai ficewarta dan Allah ya gani tak’i jinin wannan Muhibbar, gashi dai yau suka fara had’uwa amma sam taji bata kwanta mata ba ko kad’an... Dan haka tuni tai sallama da k’awarta tana fad’in zata shigo da dare... Zuhra da san mutane nan ta rik’esu da fira, ta kuwa ji dad’in shigowar su Umaima da Muhibbah dan ko babu komai sun d’ebe mata kewar k’uncin da mijinta ya jefata ciki, dikda k’ok’arin b’oyewa da take saida Muhibbah taso fahimtar wani abu... Ta saki jikinta sosai da Zuhra kaman sunsan juna tuntuni... Dad’ida k’ari Umaima da Zuhra suna shiri sosai, dan koda suka Zo tafiya sai cewa Zuhra tai su tsaya suyi lunch a nan zuwa yamma sai su tafi... Hakan sosai yaima Muhibbah dad’i don ko babu komai zatai k’ok’arin k’ulla Sabo tsakaninta da Zuhra dan sanin meke wakana cikin gidan Yazeed... Harta da yaran Zuhra da suka dawo daga school sun sake sosai da Muhibbah dama Umaima kam ‘yar gidansu ce.... Gaba d’aya yinin ranan a sashen Yazeed sukayita saidai sam basuji d’uriyarsa ba dashike yana cen shirye shiryen ganawarsu da king makers... Koda suka dawo sashen Giwa ma basu taddata ba, Ta fice zagayen ran gadi kaman yanda take yi ko wani yammacin Alhamis tana bin fad’in Masarautar tana duba buk’atan kowa da lafiyarsa... Wannan na d’aya daga cikin dalilin da yasa suke kuma son Giwa had’ida bata girma.... *** D’aki ne mai tsananin duhuwa suka shige, Jakadiya na tafe gaba yayinda Giwa Ke take mata baya.... Mahaukaciyar matar ce kwance cikin d’akin an d’add’aureta da k’atoton sark’a.... Ubandoma ya risina kana ya kwashi gaisuwa wajen Giwa..... Ta jinjina masa kai tana mai kuma duban matar.... Lokaci guda Giwa ta K’araso gabanta cikin taku mai cikeda izza.... Giwa ta duk’a gaban mahaukaciyar nan tana k’are mata kallo, lokaci guda ta damk’o Fuskar mahaukaciyar tana tsananin huci take furta “Mai yasa rayuwarki Keda matuk’ar mahimmanci ga cikar burina..? Tabbas nafi kowa son naga kin mutu Izzatu... Ganinki ba komai yake tuna min ba face tozarci da na fuskanta daga wajen mijina... Guntile harshenki kad’ai yayi kad’an a irin uk’ubar dana tanadar miki da zaran burina ya cika... Da zaran na tabbatar sarautar Masarautar nan ahalina sun gajeta...!” Ta k’arashe tana mai jifa da fuskr nata had’ida sakin huci akai akai.... K’uri mahaukaciyar taiwa Giwa tamkar mai tinani sai kuma ta fashe da dariya mai kamada kuka, lokaci guda ta d’aga kanta sama tamkar mai duban wani abin... Cikin muryarta da bai fita sosai sabida harshenta da aka yanke mata take fad’in “Ranan ta matso kusa... Gaskiya zatai halinta... Bayyanar Hasken ya fitar dani a jiya...Zata zamto sanadiyar warwarewar wasu al’amra...!” Ta k’arashe tana dariya irinta masu tab’in hankali... Ba lallai ka gane ma mai take Fad’i ba don harshenta rabi ne cikin bakinta.. Maganan nata yafi kama da sunbatu a zahiri, saidai ga wanda zai iya fahimta maganace mai harshen damo.... Sam Giwa bata fahimci mai take fad’i ba sai aika mata mugun kallo da take, lokaci guda ta jifa mata ledar bread kaman jira take ta capke ta shiga mamuk’an biredin.... Giwa ta waigo tana duban Jakadiya, lokaci guda tai mata alama da idanu... Jakadiya ta jinjina kai kana suka nufo k’ofa Ubandoma ya kuma gark’ameta suka fice yanda Giwa taci gaba da zagayen rangadinta tamkar babu abinda Ke faruwa... A yayinda Giwa ke zagayen rangadinta yaran nata gaba d’aya suna cen babban gwanin Maimartaba kaman yanda yake yau d’in ne zasu gudanar da zama tin bayan dawowar Mahmood k’asar a karo na farko.... Hakimai, Galadima Waziri Talba da dai sauransu duk sun hallara a babban gwanin mai marigayi mai Martaba.... Mahmood da sauran ‘yanuwansa guda Uku duk sunyi shiga irinta mulki, ga algaita daketa faman tashi a d’aukacin Masarautar... Tinda Yazeed ya shigo cikin babban gwanin ya tsaya daga nesa yana k’arewa Karagar mulkin kallo, hannayensa hard’e yake duban Karagar mulkin wanda rawani had’ida takwabi, alkyabba da kuma sandar sarakuna Ke aje bisansa, dik wanda yayi nasaran zamtowa Sarki shi zai gaji wannan rawani Alkyabban da kuma takwabin... Ya saki murmushi da gefen bakinsa Dan ba kowa yake hangowa saman Karagar ba face shi Yazeed... A hankali yake takowa har ya k’araso cikin katafaren parlorn, ya zauna a mazauninsa nan yanda aka tanadar domin zaman yaran Sarkin... Ya kaikaito kad’an yana duban Mahmood dake zaune gefensa shu’umar murmushi saman fuskarsa... SameenaAleeyou 📚 [6/2, 6:08 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *012* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Cikin sand’a ta fice ta nufi b’angaren babban gwani, sauk’inta guda hadari ne sosai a garin wanda yasa akasarin dogarai suka nemi mafaka, can bayan wani bene ta samu ta mak’ale saidai sam kunnuwanta basa sauraron abinda ake tattaunawa cikin tangamemen d’akin sarautar, abinka da gini mai aminci wanda ya kwashe d’inbin shekaru, tabbas ba hakan taso ba amma babu yanda ta iya, tinani ta soma ta tafi ne ko ta tsaya, saidai bata ida tinaninba ruwa ya kece tamkar da bakin k’warya...Ta rintse idanunta a hankali tana kuma duban yanda ruwa Ke zubowa da k’arfin gaske, ga gida na sarauta ko wani angle magudanan zuban ruwa ne...Ta kwashi kusan mintuna a k’alla goma sha biyar kana ta hango masu sarauta na aza babban riga na ficewa d’aya bayan d’aya... Yanayin fuskokinsu ya tabbatar mata basu samu yanda suke so ba.... Can ta hango Yazeed sai Washe baki yake yana taku cikeda izza ga bafaje guda ya rik’e masa lema sai kod’asa yake... Gabanta ya yanke ya fad’i, kardai Yazeed shine zai zamto Sarki na gaba, bazataso d’aya daga cikin iyalan Sarki AbdulJabbar su kuma d’alewa Karagar mulkin ba, burinta shine su rasa sarautar, su tozarta su kuma fice daga cikin Masarautar cikin k’ask’anci.... Zuciyarta taci gaba da mata zafi, ta kasa katab’us Dan batasan Ta yanda zata b’ullowa al’amarin ba... Yanzu mai zatai next...? Tana tsaka da tinanin ta hango wani Dattijo biyedashi Mahmood ne, sun nufo Ta yanda take b’oye... Ta kuma k’ara mak’alewa jikin gini dan kar su ganta.... Mahmood ya risina yana sauraren Dattijon “Yarima ba Wai ina neman haddasa gaba bane tsakaninka da sauran ‘yanuwanka, amma sanin kanka ne Mahmood babu wanda ya cancanci d’alewa wannan karaga face kai...Burin mahaifinku kenan tin kafin ya rasu, ka zamto magajinsa.... Mahmood Ta yaya zakace kai ka janye neman mulkin Masarautar nan... Ko akwai wani abinda ban sani bane...?!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Gyara tsayuwarsa ya d’anyi kana ya soma fad’in “Baba Wambai Maiyasa kake goyon bayan nayi sarauta bayan D’anka Majidad’i yana d’aya daga cikin masu neman mulkin nan....?” Mutumin da ya ambata da Baba Wambai murmusawa yai kana yace “Muhammadu kenan... Wato a sha’ani na mulki cancanta ake dubawa ba dangantaka ba... Maiyasa zan goyi bayan Majidad’i ko Yazeedu bayan nasan cikinsu dik kafisu cancanta.... Mahamuda, idan baka amshi sarautar k’asar nan ba don ra’ayin kanka zaka amsa ko dan wasiya da mahaifinka ya bari...!” Mahmood yai shiru tamkar mai nazari yana duban wani b’angaren hannayensa hard’e Ta baya, lokaci guda ya d’an kaikaito yana duban Wambai.... “Baba kana wajen mahaifina ya rasu...? Kuma Maiyasa bai zab’eka matsayin wanda zai gajesa ba sai ni... Kai yafi cancanta ka gaji sarautar Masarautar nan sabida Kai Uba ne a garemu, sannan kai Yayan mahaifina ne kafisa a haife, tun a fari kai ya kamata kayi sarauta bashi ba, yanzu da babu shi inaga lokaci yayi da zama amshi ragamar sarautar...!” Baba Wambai ya kamo hannun Mahmood suka zauna saman wata itaciya... Saida yai gyaran murya kana ya soma fad’in “K’warai kuwa ni ne gaba da mahaifinka a haife, amma a b’angaren cancancanta ya fini, shi yayi karatu mai zurfi boko da islama ni kuwa banyi boko ba, kuma sanin kanka ne a halain da muke ciki yanzu karatu na zamani na taka muhimmiyar rawa cikin rayuwarmu gaba d’aya, k’anina ya had’a komai da ya cancanta ya rik’i Karagar Masarautar nan, yanzu kuma da babu shi kaine magajinsa... Sannan Ina wajen sanda Allah yaiwa mahaifinku kuma d’an uwana cikawa.... Mahmood idan baka amshi sarautar nan ba kana kallo sarautar zata fice daga k’ofarmu, kana gani dai Talba da ‘yanuwansa sun k’wallafi ransu kan wannan muk’ami... Kuma abinda baka sani ba shine, Ina mai tabbatar maka mahaifinka kashesa akai dik akan wannan Mulki... So kake burinsu ya cika su amshe mulki daga hannun ahalin AbdulJabbar... Na tabbata bazakaso haka ba....!” Ya k’arashe yana dafe da hannayen Mahmood idanunsa k’unshe da damuwa... Mahmood ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Wambai kana yace “Kashe mahaifina akayi akan neman mulki...? Su waye suka kashe shi...?!” Wambai ya gyara zamansa kana yaci gaba da fad’in “Mahmood akwai sirrika da dama da suke lullub’e cikin bak’in duhu a Masarautar nan... Ka jima baka Masarautar nan, akwai abubuwa da dama da suka faru...” Yarima Mahmood ya katsesa da fad’in “Shin mai ka sani gameda mutuwar mahaifina..? Shin mutuwar mahaifina nada alak’a da mutuwar matata..? Wad’annan amsoshin na dawo nema Masarautar nan amma ba mulki ba...” Baba Wambai Yai murmushin cin nasara kana yace “Alhamdulillahi yanzu ka dawo hanya... Idan har kana son samun amsoshinka sai kanada k’arfin mulki a hannunka, idan ya kasance kaine wanda Allah ya d’aura masa nauyin gudanar da al’amaran cikin Masarautar nan toh fah ina mai tabbatar maka zaka sami amsoshinka cikin sauk’i... Amma muddin kace bincike zakai a gida irinta mulki da sarauta ba tareda kanada wadataccen ilimi gameda al’amran dake aukuwa cikin gidan ba to zaka b’ata ne a hanya ko kuma a b’ataddakai, Mahmood a gida irinta sarauta an b’atar da mutane da dama wanda har yau babu d’uriyarsu....Mahamuda, Kai tinani akan abinda muka tattauna, Ina mai tabbatar maka hardai Ina d’aya daga cikin masu nad’a sarki a wannan masarauta bazan tab’a saka hannu a zab’i wani matsayin sarki ba kai ba..!” Sauk’e ajiyan zuciya Yarima Mahmood yai kana ya mik’e tsaye lokaci guda... Ya d’an kaikaito yana duban Baba Wambai kana ya jinjina kai a hankali yace “Shikenan Baba... Zanyi tunani, na gode K’warai....!” Wambai ya jinjina kai kana yace “Allah shi maka Albarka...!” Yana k’ok’arin mik’ewa abinka da jikin tsufa Mahmood yai saurin tallafa masa ya mik’ar dashi tsaye... Daga yanda Muhibbah ke lab’e ta gama sauraren tattaunawarsu tana kallon yanda Yarima Mahmood Ke rik’eda wannan Dattijo suna tafe, Mai yasa yake nunawa kaman wani shid’in mutumin arziki ne... Maiyasa yake nuna tausayi da jin k’ai cikin Al’umma bayan tasan ba haka yake ba.. Mugu ne azzalumi ne... Wanda sukai tarayya shida ‘yanuwansa wajen ruguza rayuwarta data ahalinta.... Take ta kuma jin tsanar Mahmood dana ‘yan uwansa da uwarsu kanta na kuma mamaye illahirin ruhinta, abubuwan da Ta gama ji bazaisa ta janye k’udirinta ba, tayi imani sune azzaluman cikin Masarautar ba wasu daban ba, they cannot be victims, Ta tabba sune azzaluman... Tasa baya hannu Ta goge hawayen da suka zubo mata kana ta fito cikin sand’a, lokacin a idda ruwa saiko d’an yayyafi kad’an kad’an... Tana isowa d’aki kwab’e jik’akk’en kayan jikinta tai kana Ta fad’a bathroom had’ida sakar ma kanta shower, ta rintse idanunta sanda take hango Mahmood cikin k’wayar idanunta yana taimakawa Dattijon nan yawa wani mutumin arziki... Kuma rintse idanunta tai da k’arfin gaske ganin wani b’angare na zuciyarta na neman amincewa tabbas Mahmood mutumin kirki ne... Sauri sauri ta gama wankan nata ta d’auro alwala dan already magrib ya gabato... Tana fitowa ta shirya tsaf cikin wani cotton material sea green d’inkin doguwar riga da yai matuk’ar amsar jikinta... Ida shirinta da kad’an wayar Mummy ya shigo mata ta d’aga cikeda kewan gida.... Bayan sun gaisa Mummy Ke tambayarta karatu... Jiki a sanyaye Muhibbah ta amsa mata dan gani take kaman bata kyautawa Mummy ba b’oye mata babban al’amari iri wannan da tai... Har suka ida wayar jikinta a matuk’ar sanyaye yake, bugu da k’ari tinda taji tattaunawar Mahmood da Baba Wambai ta kuma jin rauni sosai daga wani b’angare na zuciyarta wanda bata tab’a jin irin hakan ba tun sanda ta sanyawa ranta k’udirin d’aukan fansa daga wajen wad’anda suka zalunceta.... Tai lamo cikin kujera tana mai lumshe manyan idanunta a hankali... Kiraye kirayen sallan magrib da aka soma ya sanyata mik’ewa dan gudanar da nata sallan... Bayan ta ida ta d’auko alk’ur’ani tana karantawa, take ta kuma jin wani irin rauni na ratsa illahirin b’argo da tsokanta, taji wasu irin hawaye suna k’ok’arin ciko idanunta... Tabbas Alk’ur’ani maganin dik wani gyambo ko k’ulli ne dake a cikin zuciya, kuka sosai Muhibbah keyi ba tareda ta iya ci gaba da karatun ba... Wani irin rauni takeji can k’asar zuciyarta, tai lamo saman abin sallar had’ida lumshe idanunta hawaye masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata, Ta tina sanda ya tambayeta da muryarsa mai cikeda k’warjini had’ida dad’in saurare murmushi saman kyakkyawan fuskarsa _”Kina son kiga wasan dawakin ne...?”_ Ta jinjina masa kai a hankali kana yace _Ya sunanki_ _Saudatu_ Ta fad’i tana wage baki cikeda jin dad’i tana kuma gustiran apple d’in da ya bata... Ya murmusa a hankali kana yace _Zo na d’auraki saman dokin_ Ta tina sanda sauran ‘yan uwan nasa keta dariya suna nunata da yatsa... Wannan tunani da Muhibbah keyi ya sanyata saurin bud’e idanunta zuciyarta na mata tsananin zogi, a fili Ta furta “Mayaudari ne, yaudarar mutane yake da kyawawan d’abi’unsa, dashi yai amfani suka cimma burinsu kan k’aramar yarinyar da bataji ba bata gani ba... Take taji wani b’angare na zuciyarta na raya mata, karki janye k’udirinki, kar Ki d’agawa d’aya daga cikinsu k’afa.. Ruin them all, expose them and take them down.... Ta k’arashe tana mai goge ragowar hawayen da suka zubo mata, sallaman Umaima ya sanyata saurin mik’ewa had’ida saita kanta kaman babu abinda Ke wakana... “Ke Wai baki gajjiya da zaman d’aki...Kinga taso mu tafi b’angaren Giwa d’iyanin muci dinner a cen....” Umaima ta fad’i daga nan yanda take tsaye... Saida ta d’an rausayar da idanunta kana tace “Yo naga dai gidan sarauta ai zaman d’aki da kulle ya gada ko ba haka ba... Kinga dama ke nake jira muje na duba jikin Zahra, tana raina tin d’azu...” Umaima ta d’an girgiza kai kurum tana mai janyo hannunta tana fad’in “Iyanin Ki amsa kiran Ya Mahmood..!” Saida k’irjinta ya buga jin tace ta amsa kiran Mahmood, harga Allah ta mance Wai yana kiranta... Banda guntun gulma mai zai mata, yaji da abubuwan da suke gabansa, tabbas da ace yasan wacece ita da kuma k’udirin da ya kawota wannan masarauta ko mai irin sunananta bazaiso ji ba balle ya buk’aci ganinta... Wani tapkeken parlor suka soma shiga, babu kowa cikinsa sai manya manyan standing ac daketa faman aikinsu suna huro ni’imtaccen sanyi... Hotuna ne a jere a parlorn sahu sahu na ahalin Sarki AbdulJabbar mai rasuwa.... Muhibbah tai k’uriwa hoton da yake daga center... Yaran Sarkin ne su duka hud’u cikin hoton, dukansu cikin shiga irinta mulki da sarauta, k’asaitaccen murmushi irinta ‘ya’yan sarauta kwance saman fuskokinsu, idanunta suka waiga gefe kad’an nan ta hango wani hoton, su duka hud’u amma wannan suna yarane masu k’ananun shekaru wanda tsaf ta gane fuskokinsu domin kaw sanin da tai masu kenan....Tai K’uri tana duban hoton zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri da sauri....Ji take tamkar ta rarumi koma minene ta tarwatsa hoton dashi, so take ta finciko hoton daga ma’ajiyinsa ta zane fuskokinsu tai masu lamba mai muni wanda suma har abada bazai shafe daga tarihin rayuwarsu ba kaman yanda sukaima nata rayuwarta lamba...Take ta dunk’ule hannayenta duka biyu tana mai ci gaba da sakin huci a hankali.... Sam bata ko kula da Umaima da ta fice ta wani k’ofar tana amsa kira a waya ba... Waige waige ta soma sanda ta tabbata babu kowa cikin parlorn sai ita kad’ai saiko na’urorin nasara.... Nan ta hangi matakalan haurawa bene daga gefe, ta soma takawa a hankali ta nufi benen dikda tsananin bugu da k’irjinta keyi, ita kanta ta sani abinda takeyi abune mai matuk’ar had’arin gaske.... Abinka da gini irinta sarauta nan ta hangi dogon corridor da yake open, ga k’ofofi birjit iyaka ganinka.... Ta rasa ta wane k’ofar zata soma bi,

Chapter 7 of 65