ya shiga al’amaranka abokina..!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa harda ‘yar guntuwar hawaye cikin idanunsa...
Su duka biyun murmushi suke suna duban juna suna sauraro yanda Sautin algaita da tambura ke kuma gauraye d’aukacin Masarautar ...
A haka Ja’afar ya shigo ya taddasu ya sanar dasu komai ya kammalla su ake jira...
A haka suka nufo babban Gwani Ja’afar da Turaki sun saka shi a tsakiya ... Dogarai suna biye dasu suna ci gaba da kod’a Mahmood d’in wanda gaba d’aya ji yake jikinsa na wane irin tsuma Wai yau shid’in zai taka k’afafunsa cikin Fadan mahaifinsa Babban Gwani, ya shiga tuno rana na k’arshe da yaga mahaifinsa saman Karagar wani zuwa Nigeria da yayi a lokacin yana can k’asar Spain.. Ya tuna mahaifinsa yace dashi duk daren dad’ewa akwai ranan da zaizo ya gaji wannan Karagar... A lokacin ya dai saurari mahaifin nasa ne amma yafi bada k’arfin Yazeed shine wanda zai gaji mahaifin nasu tinda ya fisa jib’antuwa da al’amaran sarauta... Ja’afar dake gefensa shima wani irin fuzga yakeji zuciyarsa na masa ya shiga tuno abubuwa da dama ciki harda rayuwa k’ark’ashin Inuwar Bayi da yayi cikin Masarautar.. Yau sai gashi nan zai taka cikin Babban Gwanin Mai Martaba kuma shid’in yana daga cikin ahalin gidan... A hankali ya lumshe idanunsa hawaye suka gangaro masa...
Sanda suka isa cikin Babba Gwani gaba d’aya King makers suka mimmik’e tsaye suna bud’e manyan garensu suna furta “Lafiya D’an Toron Giwa... Gaba salamun baya salamun... Ka shigo cikin aminci.. Karagar taka ce..!”
Saida ya isa daidai saman darduman nad’in sarautar mai tambarin masarautarsu yaja ya tsaya yana duban Ja’afar.. Hannun Ja’afar ya kamo suna fuskantar juna, lokaci guda Mahmood Ke furta “Shin zaka iya...? Zaka iya zama saman Karagar nan ka tsare Martabar gidanmu...?”
Cikin tsananin sanyin jiki Ja’afar Ke girgiza kai yana furta “No Yaya.. Bazan iya ba, amma inada yak’inin kai zaka kwatanta da taimakon Allah... We’re all here for you Yaya kai ka cancanci ka d’ale Karagar.. Hawaye suka taru can cikin idanunsa ba tareda sun gangaro ba.. Mahmood ya dafa kafad’ar Ja’afar yace “You spent all your life serving this Palace.. An mai dakai Bawa a cikin Masarautarka.. Bata baka dama ka rayu matsayin d’ah a cikin gidan nan ba, Sabida haka ka cancanci rik’e ragamar jagorancin gidan nan... A yau inaso kai ka gaji mahaifinmu....!” Ya k’arashe hannayensa guda biyu dafe da kafad’un Ja’afar d’in.
Girgiza kai Ja’afar yake yana furta “A’a Yaya kai ka fini cancanta da ka gaji mahaifinmu I’m sure da ace yana raye da abinda zaiso kenan... Sarautar taka ce Your Highness... Mu muka zab’eka ba kai ka zab’I kanka ba... Munbi cancancanta kuma duk munyi mubaya’a cewa kaine kafi kowa cancanta...!”
Kaman daga sama suka sinkayo wata murya...
SameenaAleeyou 📚
[10/9, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*87*
*©️Sameena Ameeyou...✍🏽*
A tare Mahmood da Ja’afar suka juyo suna duban Fu’ad dake takowa gaba garesu, hawaye Tab idanun Fu’ad d’in yake ci gaba da takowa cikin Babban Gwanin, cikin wata irin murya mai gauraye da rauni da k’warjini yake furta “Kai kafi kowa cancanta Yaya... Ja’afar yayi gaskiya, kaine ka cancanci ka gaji Abbah..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya a daidai lokacinda ya k’araso gabansu...
Yai tsaye gaban Mahmood suna duban juna, lokaci guda Mahmood Ke furta “Fu’ad kai nake gani a gabana...?”
Fuad ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Ni ne Yaya.. I’m out of the mental facility..!” Yana kaiwa aya Mahmood ya rungumesa sosai yana furta “Naji dad’i Fu’ad.. Naji dad’i da Allah ya baka lafiya... Alhamdulillahi..!”
Fu’ad ya d’an murmusa kad’an yana duban Mahmood d’in wanda shine favorite d’insa gaba d’aya cikin ‘yan uwan nasa... Take kuma ya sadda kansa k’asa bayan yakai dubansaga Ja’afar yana tuno abubuwan da Jamal ya sanar dashi bayan ya kai masu ziyara a cikin asibitin kafin ya nufo Masarauta... Ja’afar ya d’an dafa Sa kad’an yana sakin murmushi.. “It shall all be well... Brother.. Im glad you’re finally home.. Allah ya k’ara maka lafiya...!”
A tare Mahmood da Fu’ad suka amsada Ameen Mahmood d’in na duban k’annen nasa... Lokaci guda ya rungumosu gaba d’aya ya k’ank’amesu cikin jikinsa.. Su duka ukun suka rungume juna gaba d’aya hawaye na gangaro masu... Tausayinsu ya cika zukatan mutanen dake wajen..
Kaga yanda masu rawani Ke matsan k’walla.. Allahu Akbar dole ka koka ma wannan ahali wanda suka sha fama da gwagwarmayar rayuwa... Bayan lafawan komai Algaita yaci gaba da tashi.. Aka soma gudanar da cika ciken nad’in sarauta kaman yanda yake a al’adance... Mahmood yai zama irin zaman da ake idan za’a ci abinci nan saman darduman, Dogarai sukaci gaba da kod’asa sanda ake fesa masa turaren mulki.. Galadima da Talba suka d’auko Alkyabba fara k’al wanda akai mata kwalliya da zare mai kalar zinari suka rufa masa basmala saman harshensu... Shima Mahmood d’in bai daina tsarkake mahaliccinsa ba Sarkin da babu ya shi... Yanaji wani irin babban al’amari ne Ke aukuwa dashi... Gaba d’aya Sai yanajin zuciyarsa tana wane irin fuzga daga cikin k’irjinsa.. Sanda akazo za’a d’aura masa hular Kambin sarautar Galadima ya umarci Ja’afar da ya d’aurawa d’anuwansa Mahmood Kambin Mulkin a saman kansa... Jafar ya k’araso hawaye da murmushi gauraye saman fuskarsa ya amshi hular hannun Galadima.. Har ya soma k’ok’arin d’aurawa saman kan Mahmood sai kuka ya dakata, gaba d’aya suka tsaya suna dubansa, Sunan Fu’ad ya ambata wanda yasa Fu’ad d’in d’agowa cikin fad’uwar gaba, Ja’afar na sakin murmushi yace dashi a hankali “Come here Brother.!”
Saida ya d’an d’ago yana duban mutanen dake wajen kaman mai tsoron motsawa, Mahmood ya sakar masa murmushi yana dubansa, a hankali Fu’ad ya mik’e ya k’arasa gaban Ja’afar d’in.. Lokaci guda Ja’afar ya kamo hannunsa ya aza saman Kambin yace “Lets do this together Brother..!”
Cikin tsananin sanyin jiki Fu’ad ke dubansa, lokaci guda ya shiga girgiza kai yana furta “No Ja’afar, I can’t do this.. Banida matsayin da zan d’aura Kambi saman kan Sarki..!”
Ja’afar ya dafa hannunsa yace “But you’re our brother Fu’ad, it doesn’t matter idan ba Matar Sarki bace Ta haifeka.. Kuyangar Sarki ce ta haifeka, kai d’in d’an mahaifinmu ne .. Ko ka mance Mahaifiyarmu ta bama mahaifinmu Mai Martaba kyautar Baiwarta mahaifiyarka, kai d’in d’ansa ne Fu’ad.. Kai d’in d’an K’wark’wararsa ce.. Ka amince da haka mu d’aurawa Yaya Kambin mulki akansa...!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa..
Fu’ad dake zuban hawaye lokaci guda ya shiga jinjina kai kana yakai hannunsa saman kambin....A tare suka mik’e suka rik’e hular hawaye na gangarowa daga idanunsu.. Shi kansa Mahmood d’in hawaye ne ya mak’ale cikin idanunsa ya kasa gangarowa sai wane irin tsuma da illahirin jikinsa keyi... Bayan sun d’aura masa Kambin Baba Talba da Galadima sune suka soma d’aura masa farar rawanin akansa wanda take fara k’al sai d’auke idanu take... Take aka nad’a masa rawani mai kunne biyu akansa, Wali ya k’araso da d’amaran Mulki sanda Mahmood zai mik’e Dogarai suka baza babban garensu suna furta gyara kimtsi da kyau.. Saida har ya mik’e tsaye kana Wali da Maga yak’i suka k’araso suna d’aura masa d’amarar... Bayan sun ida d’aura masa d’amaran Mulkin Shattima ya k’araso da Takobin hannunsa... Ya mik’awa Magayak’i.. Magayak’i ya amsa ya sakama Mahmood Takobin cikin damararsa... Had’ida mik’a masa Sandar Mulki ya rik’e yana duban d’imbin Al’umman masarautarsa...Allahu Akbar kallo guda zaka masa kace ga Sarki nan wanda zai amsa sunansa Sarki... Babban Gwani Ta kacame da kalaman yabo.. A hankali Mahmood ya soma takawa sanda ya nufi Karagar zai d’ale.. As he was walking towards the Throne Abubuwan da suka faru cikin gidan sai zuwa masa suke, kama daga canza identity d’in da Giwa tayi har zuwa duk wasu abubuwa da suka faru.. Ya jima sosai yana duban KARAGAR hawaye tab idanunsa.. Take ya nemi tsari daga mahallicinsa daga sharrin dake tattareda wannan Karagar ya kuma rok’i mahaliccinsa da ya tabbatar masa da dukkan Alkhairi dake tattareda Karagar sannan yayi masa jagoranci bisa jarabawar da ya jarabcesa dashi na shigabancin Al’umma... Sanda ya d’ale saman Karagar da basmala daidai nan hawaye guda d’aya ta d’igo daga cikin idanunsa.. Allahu Akbar nan kaji Babban Gwani ya kacame da ambaton Allah... Bakunansu sai furta alkhairi suke.. Algaita yaci gaba da tashi.. Take aka buga masa Tambura guda sha biyu na Masarautar.. Yana jin jikinsa na wani irin Karma alamun da gaske sai dai yau shi Mahmood ya d’ale Karagar.. Bayan tsawon shekara guda da watanni da akai babu Sarki a Masarautar sai iftila’i da k’alubale da sukaita faruwa sai gashi yau Allah ya tabbatar da ikonsa ya d’aura Sarki a wannan Masarautar saidai muce Ubangiji yayi masa jagoranci...
Ko wanne Tambari guda Goma sha biyun nan da za’a buga sai an ambaci ma’anarta.. Haka saida aka buga masa shabiyu russ ana fad’in ma’anarsu... Daga bisani Masu sarauta suka soma k’arasowa suna zubewa suna kwasan gaisuwa... Galadima ya fara yin nasa Barde yana amsa masa da fad’in “An gaisheka Galadima..! Mai Martaba ya amsa..! Matawalle ma yayi nasa Barde ya kuma amsa masa da “An gaisheka Matawalle..! Mai Martaba ya amsa..!” Haka duk masu sarauta kowa saida ya kawo nasa caffan ga Sarki Mahmooda d’an AbdulJabbar...
Turaki na hawaye ya k’araso ya mik’a gaisuwarsa da taya murna ga abokinsa yana mai furta “Long live the King..!”
Ja’afar ma ya k’araso yai masa haka Fu’ad ma... Ko wannensu hawayen Farin ciki kwance cikin k’wayan idanunsu...
Shagulgulan bukin nad’in sarauta sukaci gaba wakana... Zigazigai naci gaba da yin kirariwa Sarki “Allah shi jaaa zamaninka..! Lafiya Baya goya marayu... Lafiya cika sarari..! Lafiya mai sulken yak’i..! Lafiya mai Tambura goma sha biyu... A laaaaafiya azurfa babu gauraye...!” Ire iren kirarin da ake tayiwa Mahmood kenan ana fad’in Allah ya bashi gidansu...
Yinin ranan Masarautar taci gaba da karb’an kyauttuka daga masarautu daban daban.. Yammacin ranan masu mulki suka hau Dawakai sukayita kawo caffa (gaisuwa) saman dawakai ma Sarki dan nuna Farin cikinsu...
Ja’afar ya dubi Fu’ad da har lokacin Bai wani saki jikinsa ba, kana ya dafasa kad’an yace “Kana so mu hau Doki muyi wasan doki..?”
Fu’ad ya dubesa hawaye kwance cikin idanunsa yake furta “You know, to be honest I still can’t believe my own Mother can do all those horrible things.. How can someone be so inhuman...!”
Ja’afar ya dafasa kad’an yace “Fu’ad wasu lokutan mukanso abubuwa su kasance yanda muka tsarasu amma saidai ba muda ikon yin hakan sai abinda Allah yayi... Mutum baya wuce k’addararsa, na sani da ciwo amma kayi hak’uri sai kaci jarabawarka..!”
Cikin rawar murya irinta mai kuka Fu’ad Ke furta “Inajin nid’in kaman ba d’aya bane daga cikin ahalin gidan nan.. Ina jin kaman ban cancanci zama ahalin gidan nan ba..!”
Saurin kamo hannunsa Ja’afar yayi yace “Of course you’re one of us.. You are a part of this family.. You’re our brother Fu’ad we share the same Father.. So don’t say those things kaji.. Kai ahalin gidan nan ne..!”
Kuka ya kufcewa Fu’ad, lokaci guda Ja’afar ya rungumosa shima hawayen na gangaro masa... Saida Fu’ad ya nastu kafin Ja’afar yace suje suyi wasan Doki Su gwada linzami...
Suka d’ale saman Dawakan suna duban juna murmushi saman fuskokinsu... Ja’afar ya dubansa yace “Ready...?”
D’an tsaresa da idanu Fu’ad yai yace “Ta yaya D’alibi zai gwada k’warewa da Malaminsa... Idan ban mance ba kai kake koya min Doki a baya...”
Murmusawa Ja’afar yai yace “Watak’ila D’alibin har Sai yafi malamin.. Lets do this..!” Ya k’arashe yana jan linzamin had’ida zaburan dokin... Take Fu’ad ma ya zabure nasa dokin yabi bayan Ja’afar a guje zukatansu cikeda annashuwa...
**
A b’angaren Muhibbah kuwa yau d’in su Mommy dasu Meenatu zasu tafi hakan yasa hankalinta ya karkarta zuwaga yin sallama dasu dukda cewa kuwa can k’asan zuciyarta tsananin kewar mijinta take.. Yinin ranan zubur basu had’u ba, batasan har haka take son mijinta ba.. Ta fara shakkun idan zata iya jure rashin ganinsa irin haka tinda yauma kenan akayi nad’in balle ace ya soma hidiman al’umma gadan gadan.. Ta lumshe idanunta a hankali tana tuna yanda a lokaci k’ank’ani Allah ya sauya mata k’addarar rayuwarta.. Wai yau itace Matar Sarkin wannan Masarautar.. Ta tuna sanda tazo Masarautar a k’ask’ance yau sai gashi Allah ya k’addari ta zamto matar Sarkin Masarautar gaba d’aya tabbas babu abinda ya gagari Allah... tana nan tana tinanin Ta sinkayo sallamansa... Zumbur ta mik’e tana duban k’ofa... Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake dubanta.. Itama d’in murmushin ta sakar masa tana jin zuciyarta na wane irin fuzga... Ganinsa da tai cikin shiga irinta Sarki sak sai taga k’warjininsa ya kuma bayyana... Ta sadda idanunta a hankali tana k’ok’arin duk’awa gabansa dan kwasan gaisuwa... Cikin sauri ya tallafota had’ida mik’ar da ita tsaye.. Suna fuskantar juna hawaye na zirarowa daga cikin idanunta, da gaske yau babu Giwa kuma Mahmood ya d’ale KARAGA... Cikin hawaye take furta “Kaine Sarki.. Ka cancanci zama Sarki mijina.. Ina maka fatan alkhairi tareda addu’an Ibangiji yayi maka jagoranci..!” Ta k’arashe murmushi da hawaye gauraye saman fuskarta...
Tallafe da fuskarta yake furta “My love... My beautiful Queen.. I don’t need all this things... For me you’re all I want... And Wannan Kambin naki ne.. Idan akwai wanda ya cancanta ba kowa bane face ke..! Kece kika cancanci Karagar da Kambin domin kece kika yak’i Giwa da zaluncinta.. Kece kika shigo cikin Masarautar nan wanda yake gauraye da duhu kika haskaka shi da gaskiya.. Duhu ya yaye.. Haske ya bayyana... Ta sanadiyanki Allah ya kawo k’arshen Giwa da bak’in Mulkin zaluncin data gina cikin Masarautar nan..!” Ya d’anyi fasali hawaye na gangaro masa har lokacin yana tallafe da fuskarta.. A hankali yaci gaba da furta “Just like your name MUHIBBAH tabbas ked’in abar soyuwace ga duk wanda kika crossing path d’insa.. Ked’in kin zamto tamkar wata tsauni cikin Masarautar nan da rayuwarmu gaba d’aya.. Kin taka rawar gani cikin rayuwarmu gaba d’aya... Kinyi sadaukarwa da Dama dan ki tabbatar haske ya bayyana cikin Masarautar nan.. Thank you for coming into our lives..! Thank you for being mine..!” Ya k’arashe a hankali... Kukan da take k’ok’arin dannewa ya kufce mata.. Lokaci guda ta rungumesa tana kuka sosai... Saida tayi mai isanta Mahmood na lallashinta kafin ya kamo hannunta yace tazo suje.. Ta d’an dubesa sai kuma tace “Ina zamuje your Highness..?!”
Bai tankata ba har saida suka k’araso farfajiyan benen... Ya kaikaito da ita suna fuskantar juna lokaci guda kamo hannunta ya shiga janyota yana furta “Come I wanna show you something my Queen.. Turn around and close your eyes..!”
Ta d’an Ware idanunta tana tunanin mai zai nuna mata, lokaci guda tayi yanda yace d’in... Wani k’aton frame dake rufe da Farin k’yalle Mahmood ya bud’e kana yace ta juyo ta gani... A hankali take juyowa har ta sauk’e idanunta kan k’atoton frame d’in wanda zane ne na gidan Sarauta... Ta kame bankinta da hannayenta biyu tana duban yanda zanen ya tsaru... Ya tako a hankali ya tsaya daga bayanta had’ida d’aura hannayensa saman cikinta su duka biyun suna duban zanen yace da ita “Do you like it..?”
Kyakkyawan murmushi saman fuskarta tace “Of course I love it... It is so Beautiful..!”
Ya d’an kwanto da fuskarsa ya manna mata peck a gefen kumatunta kana yace “I’m glad you love it.. Kin gane ina ne..?”
Murmushin bai bar saman fuskarta ba tace “Is this also part of the exams your Highness..?”
D’an tab’e baki yai kad’an yana jinjina kai yace “Maybe..! Idan kin canka daidai na mallaka miki zanen kyauta idan kuma baki canka ba....!” Yai shiru bai k’arasa ba...
Ta d’an kaikaito tana dubansa... Sai kuma ta saki murmushi a hankali Ta furta “Masarauatr su Abbah ne.. Masarautar k’asar Benin...!”
Ya d’an yi K’uri yana duban waje guda har ta soma tunanin kodai bata canka daidai ba, Ta sinkayo muryarsa saitin kunnenta yana rad’a mata “Congratulations..!” Ta d’ago tana duban fuskarsa a hankali ta furta “Na gode..”
Girgiza mata kai yai yace “Ba irin wannan godiyan nake so ba”
Ta d’anyi rau rau da idanu tace “Wanne kake so Your Highness..?!”
Kunkuminta ya kuma kamowa suna fuskantar juna lokaci guda ya turo mata labb’ansa alamun ta sumbacesa..
Ta rintse idanunta sabida kunya.. Mahmood yace “Your Highness yaufa babu yanda zakije sai kin bani tukuwici na..” ya k’arashe yana mai kuma tura mata labb’an nasa.. Tace “Fine amma sai ka rufe idanunka..!”
“Well that won’t be a problem Rankidad’e..” Ya lumshe idanunsa yana jiran ta sunbacesa... Tai masa k’uri tana duban kyakkyawan fuskarsa, wani irin shauk’in k’aunarsa na fuzganta... Ido guda ya d’an bud’e kad’an jin Ta d’auki tsawon lokaci batai ba nan yaga fuskarta dab da nasa Sai faman rintse idanu take Zuciyarta na bugawa...Aiko a tare suka bud’e ido sanda fuskokinsu suka kusa had’ewa... Ta Ware idanunta tana k’ok’arin juyawa yai saurin rik’ota zatai magana yai ma bakinta marfi da nasa... Cak ya sureta ya nufi bedroom d’insa da ita yana nuna mata tsantsan k’aunarsa gareta...
**
Wai akace bayan wuya Sai dad’i sannan tsanani na tareda sauk’i... Al’amara sun soma daidaita cikin Masarauta tuni anyi nad’e nad’en sarauta, a b’angaren su Mommy Tunda suka koma gida kusan kullum sai tayi waya da d’iyarta Gimbiya Muhibbah... Ansar ma tuni ya d’auki matarsa Hameedah sun tare a gidansu.. Hankalin Mommy ya kwanta faranta Allah ya azurta yaran nata da zuri’a masu albarka...
A b’angaren Raheemah kuwa nadama yazo mata itama, musamman duba da yanda Yazeed ke mata wa’azi gameda duniya da rayuwar duniya.. Rayuwar da sukai kad’ai ya ishesu wa’azi a cewar Yazeed ya kuma rok’onta Ta taimaka Ta kirawo masa Mahmood ya gansa ya rok’esa gafara koda abinda zaiyi kenan na k’arshe a rayuwarsa domin kuwa Yazeed d’in ya zama weak sosai da ace zai iya tashi daga saman gadon jinyarsa da koda rarrafe ne zaije ya rok’i Mahmood da Muhibbah gafara... Raheemah na hawaye Ta dubesa tace “Banida tabbacin Sarki zai amsa gayyatarka amma Zanyi k’ok’ari na gwada koda Ta k’afar matarsa ce... Yazeed yai mata godiya kana ta fice hawaye....
Koda Ta iso masarauta Jakadiya ce tai mata iso wajen Gimbiya Muhibbah... Sosai Muhibbah taji tsoron yanayin da taga Raheemah ciki, duk ta kod’e ta jeme kaman ba Raheemar data sani ba...
Jiki a matuk’ar sanyaye Muhibbah Ke dubanta yanda ta duk’a gabanta tana cazgan kuka, lokaci guda take ci gaba da rok’on Muhibbar gafara... Muhibbah ta mik’ar da ita tsaye suna fuskantar juna, a hankali take furta “Raheemah ki daina rok’onta gafara irin haka ni baki min komai ba... Dukkanmu ‘yan adam ne kuma masu kuskure... Idan muka rok’i Allah gafara matuk’ar tuban gaskiya mukayi tabbas zai yafe mana koda kaifukan namu yakai yawan kumfan teku domin kuwa shi Allah mai yawan afuwa ne... Allah ya yafemu gaba d’aya kinji koh...!”
Cikin kuka Raheemah Ta rungumeta tana fad’in “Kinada zuciya mai kyau Muhibbah... Na gode na gode k’warai..!”
Muhibbah ta rik’o hannayen Raheemah cikin nata tace “Babu komai Raheemah...!”
Raheemah ta d’an jinjina kai tana duban Muhibbar sai kuma tace “Wani alfarma kuma nake so Kimin...”
Dubanta tai da mamaki kana tace “Wane alfarma kenan..?”
Raheemah taci gaba da fad’in “Akan Yazeed..!”
Take fuskar Muhibbah ya sauya ta zame hannayenta daga cikin na Raheemah...
Raheemah ta kuma share hawayenta tace “Nasan bai kamata na ambaci sunansa a gabanki ba amma babu yanda na iya ne Muhibbah.. Domin yana cikin tsananin jinya... Abinda yake buk’ata kawai shine yafiyarki... Muhibbah ki yafewa Yazeed dan Allah sannan ki rok’i Mai Martaba yaje yaga Yazeed domin banida tabbacin Yazeed zai iya fita daga asibiti... Please Muhibbah can you do this..?!” Ta k’arashe tana mai kuma kamo hannayen Muhibban cikin zuban hawaye...
Muhibbah da tuni itama hawaye sun fara gangaro mata, a hankali takai hannunta Ta goge hawayen... Tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Fansa baida wani amfani Raheemah.. Tun lokacinda na watsar da k’uduri burin Fansar abinda suka aikata min na samu salama cikin zuciyata Raheemah... Na zab’i na bar komaiga mahaliccinmu yayi hukunci tsakaninmu... Raheemah I’m sorry I don’t know if I can still forgive him... I’m not really sure...! Amma na miki alk’awari zan rok’i Mai Martaba yaje yaga Yazeed kaman yanda kika buk’ata...!” Ta k’arashe hawaye naci gaba da ambaliya a fuskarta...
Cikin tsananin sanyin jiki Raheemah Ke jinjina kai tana furta “Na fahimceki, kuma na gode sosai... Thank you so much Your Highness..!” Muhibbah ta rungumota su duka biyun suna hawaye...
Koda Ta sami Mahmood da batun da fari k’in amincewa Yayi dan a cewarsa bayan abinda suka aikata mata baijin zai iya kuma had’a idanu Yazeed balle har ya yafe masa...
Muhibbah tai rau rau da idanu tace “Please my King.. Kaje kaga d’anuwanka...!”
A tsawa ce ya katseta da fad’in “He’s not my brother, we’re not even related... Not by blood not by anything.. So don’t you call him my brother again..!” Ya k’arashe yana sakin huci...
Had’iye abinda ya tsaya mata a mak’oshi tai kana tace “You grew up together as brothers isn’t that enough...?!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...
Cikin tsananin huci yake ci gaba da dubanta, lokaci guda ya kamo arms d’inta ya shiga jijjigata, bai daina hucin ba yake furta “Are you serious Hibbah..? Do you really want me to go see that Criminal.. What for..? Tell me Muhibba kan mai Zanje na gansa..?!!”
Yanda yake jijjigatan yana sakin huci kuka kurum take tana rintse idanunta, cikin zuban hawaye tai k’ok’arin bud’e muryarta tace “Because everyone deserve a second chance.. Yazeed ya tuba ya gane laifinsa.. Sannan idan zaka yafewa Fu’ad Maiyasa shi bazaka iya zuwa ka gansa ba koda bazaka yafe masa ba...!”
Katseta yai cikin zafin nama da fad’in “You don’t know what you’re talking about, Fu’ad is also a victim here just like you, dan haka kar ki sake ambata mun sanan that imbecile a wajen nan..!”
Cikin zuban hawaye take dubansa yanda yake sakin tsananin huci zuciyarsa naci gaba da tafarfasa, cikin murya irinta mai kuka take furta “Do you think this is easy for me..? Have you ever thought of how I must be feeling..?Kana tunanin ko sunayensu naji bana tuna ga abinda suka min ne..? Amma bazai yuwu muci gaba da rayuwa da grudges cikin zukatanmu ba.. I choose to let go and move on koda ace hakan zai matuk’ar wahala a gareni...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka... A hankali ya rungumota cikin jikinsa sai kuma ya soma lallashinta yanajin zuciyarsa na masa wani irin nauyi... Lokaci guda yake furta “It’s ok..! Don’t you ever think that way.. We are in this together kinji koh..!” Yaci gaba da shafa bayanta yana lallashinta Yanda ake ma babies idan suna kuka...Tai lamo cikin k’irjinsa tana kuka mai tsuma zuciya, haka ya k’ank’ameta yana jin zagin kukan nata har cikin k’ahon zuciyarsa ... Baida tabbacin idan zai Iya sake had’a idanu da d’aya cikin ukun Yazeed Giwa da Jamal.. Amma idan hakan zai kwantar da hankalin Muhibbah baida zab’i da ya wuce yaje asibti ya duba Yazeed...
Washe gari Sarki Mahmood ya shirya tsaf ya nufi asibiti duba Yazeed tareda rakiyar k’annensa guda biyu Ja’afar da Fu’ad...
Kwance Mahmood ya hango Yazeed saman gado cikin tsananin jinya wanda duk rashin imanin mutum dole ya tausaya masa... Daga nesa ya tsaya suna duban juna...
Yazeed yai masa K’uri ganinsa da yayi cikin shiga irinta Mulki kambin rawanin masarautarsu bisa kansa, ga kuma Alkyabba da Sandar Mulkin Masarautar su... Abinda yaci burin mallaka kota halin k’ak’a sannan yayi duk yanda zaiyi yaga Mahmood bai samu ba yau Sai ga Mahmood d’in tsaye gabansa da Duka wad’annan abubuwan da yaci buri... Tabbas Mulki na Allah ne shi yake baima wanda yaso ya kuma hana wanda yaso a lokacinda yaga Dama... Cikin rawar murya Yazeed ke furta Yaya..!” Muryarsa ya sark’e ....
Mahmood ya soma takowa cikin d’akin rik’eda sandarsa idanunsa akan Yazeed d’in yana mai tuno abubuwa da dama da suka faru.. Har saida ya iso gaban gadon Da Yazeed d’in ke kwance bisa....
*
Wasu nurses ne suka shigo d’akinsu Giwa dan masu dressing.. Guda d’ayar sai toshe hanci take tana duban Giwa a yatsine take fad’in “Nifa wllhi bana son shigowa d’akin nan balle na tab’a mutanen nan, harga Allah wane irin d’oyi suke ga fuskar wannan matar tsoro yake ban kullum na ganta sai nayi mafarkin mummunan fuskarta.. Gaskiya bazan iya ba.. Ni zuwa ma zanyi naga Sarki.. Naji ance siren d’in nan da d’azu mukaji daga wajen asibiti Sarki ne yazo..!” D’ayar tace “No wonder ba’a shigo asibti da siren d’in ba aka kashe daga waje ai mun zaci ambulance ne.. Toh
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 63 Chapter of 65