Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaji yana so ya lek’a Zahra musamman da ya tuna tsawar da yai mata da kuma rashin jituwa da ya shiga tsakaninsu for the first time dik akan Raheema da yau yaga true color d’inta... Gaba d’aya sai yaji kaman bai kyautawa d’iyar tasa ba dan shekaran jiya har kusan marinta yai dik sabida Raheema... Tsaye yai a bakin k’ofar d’akin Zahran yana hangosu d’aukeda littafi Muhibbah na fad’in “Wait Kinsan gwamnati Ta hana aikin banza dan haka idan na koya miki karatu nima zaki koya min yaren Spanish.. Do we have a deal..?!” Zahra ta jinjina mata kai cikeda raha harda d’aga mata babbar yatsa tana mai furta “Na yarda na amince bakida matsala... Kisa a ranki kin iya spanish an gama...!” Suka tafe hannaye a tare Muhibbah na fad’in “Wayaga Muhibbah na magana cikin harshen spanish... Aiko zanyi tsiyawasu Mummy idan na koma gida dan na daina masu magana da ko wane yare sai Spananci... Wait bari muga, mai zance idan inaso nace “Mummy I’m home..?” Kaman daga sama kafin Zahra ta bata amsa suka sinkayo muryarsa yana furta “Mami estoy en casa..!” Yana fad’in haka yasa kai zai juya saidai tuni sun hangosa, da alama maganar fito masa kurum yai baiyi niyya ba... Zahra ta mik’e da sauri ta rik’o hannunsa tana fad’in “Paa Tia mi Amiga tana koya min biology... Shigo ka gani, she’s very good in biology, so so amazing...!” Burki taiwa kalaman nata jin ta kamo danshin abu cikin hannunsa... Hankali tashe take duban hannun nasa tana mai furta “Paa you’re bleeding... Pa mai ya sameka... What happened to your hand..?!” Gaba d’aya ta rikice wanda hakan yasa Muhibbah ma saurin mik’ewa tsaye tana duban hannun nasa dake d’igan jini... Shafa kan Zahra yai da d’aya hannun yana furta “Is nothing serious princess... Just go and continue with your studies, I’ll be fine.. Okay....!” Girgiza kai take cikeda tashin hankali tana furta “No... No Paa, your wound needs to be treated... Please kashigo let’s clean it...!” Taci gaba da janyo Mahaifin nata cikin d’akin fuskarta fal damuwa take furta “Aunt Hibba please clean my father’s wound... Nasan fanninki ne dan Allah ki treating masa...You stay right here Paa let me go bring the first aid...!” Bata jira cewarsa ba ta barsa nan tsaye gaban Muhibbah suna fuskantar juna ta fice cikin sauri... Yanda sukai tsaye gaban juna ya haifar masu da shiga wane irin yanayi su duka biyun... A yayinda Mahmood ya tsareta da idanunsa ita kaw hannunsa mai ciwo kurum take duba yanda jini Ke zuba.. Batasan dalili ba amma ji tai Ta k’agu Zahra ta kawo first aid d’in ta rufe ciwon Mahmood ya daina zuban jini... Gani take tamkar jinin nasa k’arewa zai.... Jinin sai yanai ma idanunta gizo tamkar yana zuba ne gudu gudu d’aya na bin d’aya cikin sauri... Ji tai zuciyarta na furta “What’s taking you so long Zahra.. You need to hurry...!!” Bata ida tinaninba Ta hango Zahra ta shigo cikin sauri rungume da firstaid d’in... Cikin sauri ta isa ta amshe kit d’in saidai kuma koda ta amsa ji tai ta k’asa juyowa ta fuskancesa... Aima kamata yai Ta barsa jininsa ya k’are ya mutu.. Miye amfanin taimakawa mak’iyi....? Bata ida tinanin ba taji Zahra na janyo hannunta tana fad’in “Please Tia treat my Paa’s wound...!!” Tamkar Rak’umi da akala haka Muhibbah ke bin Zahra har ta duk’arta k’asa gaban Yarima Mahmood dake zaune saman gadon Zahra ya tsare Muhibbar da idanu tamkar mai karantar wani abu, ko k’yafta idanunsa baiyi sai duban fuskarta kurum yake wanda hakan ba k’aramin daburtar da Muhibbah yai ba... Batansan dalili ba amma duban da yake mata na matuk’ar tasiri cikin k’wakwalwarta harma da illahirin jikinta... Ta had’iyi zuciya da k’yar sanda Zahra tai alamawa mahaifinta ya mik’o hannunsa mai ciwon... Kaman bazai mik’a hannun ba har saida Muhibbah ta d’ago dara daran idanunta da rauni ya bayyana cikinsu lokaci guda tana mai dubansa... K’waya idanunsu suka had’e waje guda... Saurin sadda nata idanun tai yayinda Mahmood yai k’ok’arin mik’a hannunsa tamkar wanda ya tina wani abu.... Tabi hannun nasa da kallo Wai itace zata rufe masa ciwon lallai Zahra ta jefata a tsaka mai wuya... Ta yaya zata soma treating wound d’in babban mak’iyinta dan take dik abubuwan da suka faru da ita suka shiga dawo mata... Tsananin tsanarsa na buga zuciyarta da kwanyarta... Jin hannun Zahra tai a kafad’arta rana mai furta “Are you alright...?!” Muhibbah tai saurin daidaita kanta kana ta sakarwa Zahra murmushi tace “Yes let’s clean your father’s wound... Ungo karb’i wannan ki warware min a nitse...!” Ta k’arashe tana mai dank’a mata roll d’in bandage.... Babu musu Zahra ta amsa cikin sauri tana furta “Sure...!” Take ta somayi kaman yanda Muhibbah ta umarceta... Shi kaw Mahmood sai suka zame masa tamkar TV.. Sosai sukai masa kyau yanda suke gudanar da al’amaransu ya shagala sosai da kallonsu har saida yaji zogin shigan magani dake nad’e da cotton wool cikin ciwon... Ya d’an saki k’ara kad’an yana mai dunk’ule hannun nasa da zogi ya ratsa wanda tuni ashe ya had’e da hannunta.... Tamkar wacce aka zabura haka ta d’ago manyan idanunta tana dubansa k’irjinta naci gaba da bugu... Shid’inma ita yake duba fuska a matuk’ar d’aure da alama bai ma kulada abinda yai ba, duban da yake mata irin tamkar da gayya take zuba maganin cikin ciwon nasa... Itama d’in fuska a matuk’ar d’aure take dubansa tanajin yatsunta cikin hannunsa da yak’i saki..... SameenaAleeyou📚 [7/10, 9:16 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *031* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Koda Ubandoma yai rakiyawa Majidad’i zuwa bakin k’ofar Fada fincika Majidad’i yai ya shige motarsa yana ci gaba da fitar da huci.. Saidai ga tsananin mamakinsa yana shigewa cikin motar yai tozali da mutum zaune gefen mai zaman banza sai faman sakin murmushi yake... Shaye da tsananin mamaki Majidad’i yace “You..! Ya akai ka shige min mota...?!” Yazeed dake ci gaba da sakin murmushi yana shafa hab’arsa a hankali gyara zamansa yai yace “Ba wannan zaka tambayeni ba.. Kamata yai ka tambayeni mai ya shigo dani cikin motarka ba yanda akai na shigo ba.... But before that ci gaba da driving.. Let’s get out of here and talk somewhere else...Nida Kai munada abubuwa da dama da zamu tattauna akai...!!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa... Majidad’i da har lokacin mamaki bai sakesa ba dak’ik’ai ya kwashe yana duban Yazeed had’ida karantarsa kana ya finciki motar suka fice daga wajen gaba d’aya... *** Zahra Ke warware bandage d’in tana fad’in ashe dai zata iya aikin asibiti itama, sai faman zuba surutunta take da alama bama ta lura da abindake wakana tsakanin Babanta da Muhibbah ba... Tana gama warwarewa ta d’ago fuska tana mik’awa Muhibbah bandage d’in data warware “Here... Gashi nan na gama...!” Birki taiwa kalaman nata tana binsu da kallo, ta dubi wannan ta kuma duba wannan mamaki kwance saman fuskarta... Lokaci guda zuciyarta na ayyana mata wani abu, take taji murmushi na zuwa saman fuskarta... “Hello..!” Zahra ta furta tana dubansu su duka biyun... A d’an daburce Muhibbah tai saurin danna ragowar maganin dake rik’e hannunta cikin ciwon wanda ya sanya Mahmood saurin sakin hannunta yana mai yarfe hannun nasa cikin dakewa kaman bashine ya shagala da kallon nata ba... Muhibbah Ta wayance da fad’in “Oh sorry sorry Your Highness... Does it hurt..?!” Tai tambayar tana dubansa... Baice komai ba sai kauda fuskarsa da yai kad’an Zahra na fad’in ya mik’o hannun nasa a rufe masa ciwon... Saida ya dubi d’iyar tasa tamkar mai san yin magana sai kuma ya maidoda dubansaga Muhibbah dake k’ok’arin daidaita bandage d’in... Kana ganinta kasan ba daidai take ba, gaba d’aya ma hannunta rawa yake... Zahra ta tsare mahaifin nata da ido har lokacin sihirtaccen murmushi saman fuskarta, a hankali Ta furta “Paa.. Your hand...!” Ta k’arashe tanai masa nuni da cewa ya mik’o hannun... D’an sauk’e fuci yai a hankali kana ya mik’o hannun nasa a hankali tamkar mai tsoron mik’owa... Hannunta bai daina rawa ba sanda take k’ok’arin d’aura bandage d’in saman hannun Yarima Mahmood, ga k’irjinta dake ci gaba da bugu tamkar zai tsage... Addu’a kurum take Allah ya bata jarumta... Idanunsa k’yam akanta take rufe ciwon tana nannad’e hannun da bandage d’in cikin tsanaki dikda rawa da hannunta keyi... Saida ta gama lullub’e hannun da bandage tsaf kana ta d’ago idanunta masu alamun rauni tana dubansa, suka kuwa had’a ido... Tai saurin kaida fuskarta gefe tana fuzar da fuci a hankali... Zahra ta soma k’ok’arin tattara kit d’in saidai tuni Muhibbah ta amshe tana fad’in ta bari zatai, dan harga Allah ji tai tana Allah Allah ta tashi ta bar wajen... Batako jira amsar Zahra ba tuni ta soma tattare box d’in cikin tsananin sauri kana ta mik’e tana mai excusing kanta... A tare suka bitada kallo daga Mahmood d’in har Zahra kana Zahra Ta maido da dubantaga mahaifinta “She’s nice, isn’t she...?!” Ta fad’i tana duban mahaifinta... Jinjina mata kai yai a hankali har lokacin bazai iya cewa ga abinda yakeji cikin zuciyarsa ba... K’aran da wayar salularsa yai cikin aljihu ya dawo dashi daga duniyar tunaninda yai nisa... Yasa hannunsa maras ciwon ya ciro wayar cikin aljihu... Turaki ne mai kiran nasa... Cikin azama ya mik’e yana mai k’ok’arin k’ara wayar a kunnesa... Zahra tabi mahaifinta da kallo har ya fice, ita dai kam ta hango wani abu tsakanin Paa d’inta da Tia Hibbah, da ace hasashenta zai tabbata da sai tafi kowa Farin ciki... Amma tunawa da tai Paa ya canza akwai abinda yake b’oye mata sai taji jikinta gaba d’aya yai sanyi... Idan har zarginta akansa ya tabbata Toh kuwa Tia Hibbah bata cancanci miji irin mahaifinta ba, domin itad’in mutumiyar arziki ce ba kaman mahaifinta da takeda tarun shakku da kokonto akansa ba... Ta lumshe idanunta a hankali tana mai silalewa saman gado... ** A b’angaren Muhibbah tana ficewa bata zarce ko ina ba sai masauk’inta.... Tai zaune saman gado tana maida numfashi had’ida ajiyan zuciya d’aya na bin d’aya.... She shouldn’t have treated his wound... She should have let him bleed to death, it’s what he deserve after all.... Maiyasa bata k’yale shi jinin yaita kwaranya ba...?! Tai gajeren tsuka a hankali tana tina yau d’in taimako biyu taiwa Mahmood wanda duk bai cancanta ba... Na farko tsallake tuggun Raheema, sannan ga gyara masa hannunsa da tai... Tunanin abin sai yasa taji tamkar yanzu ne take rufe ciwon Mahmood, komai ya shiga zuwa mata daki daki tai saurin rintse idanunta da k’arfin gaske tana mai shafe fuskarta da duka tafukan hannayenta... Ware idanunta da zatai tai tozali da d’igon jinin Mahmood cikin tafin hannun nata... Tai K’uri tana duban drop na jinin da tuni ya bushe cikin tafin hannunta, k’irjinta bai daina bugu ba tai saurin fad’awa bathroom ta bud’ewa tafukan hannayenta ruwa tana mai gurje tafukan hannayen nata da k’arfin gaske tamkar zata cire fatarta... Saida ta d’ibi lokaci tana wanke hannun dikda jinin ya fice kana ta d’ibi ruwa cikin tafukan hannun nata ta wanke fuskarta har kusan sau uku, lokaci guda tai K’uri tana duban fuskarta cikin mirror... Ta janyo k’aramar towel Ta goge fuskar tata dashi kana ta nufo d’aki ta d’au wayarta lokaci guda tai dialing layin Ansar... Cikin sauri kuma ta katse kiran saidai tuni ya shiga, ta komo kan gado ta zauna tana tinanin toh ma mai zata soma ceda Ansar...? Ta kuma lumshe idanunta a hankali tana juya wayar cikin hannunta, kaman daga sama sai ganin kiran nasa tai.. Ta d’ago fuskar wayar tana duban sunan Ansar dake kira, kaman dai bazata d’aga ba sai kuma ta d’aga cikin kasaliyar murya.... Daga d’aya b’angaren Ansar ke amsa sallamarta yana mai tambayarta ko tana lafia, kaman dai Babu wani abinda ya faru haka nan yake amsa wayar... Cikeda borin kunya Muhibbah tace “Maiyasa ka kira..? The last time I checked fushi kake dani kuma kace bazaka sake kirana ba...!” Murmusawa yai kad’an kana yace “And last time I checked kece kika soma kirana... So tell me, what’s wrong this time...? Nasan haka kawai bazaki kirani ba, you must have a reason...Fad’a min What went wrong this time...?” Rausayar da idanu tai a hankali kana tace “Yanzu haka ka d’aukeni bazan kiraka ba saida dalili...? Ni ba kiranka nai ba... Idan kuma na kiraka bansan nayi ba..!” Ta k’arashe cikin fad’a... Ya kuma murmusawa a hankali kana yace “Alright fine... Naji baki kirani ba ni na kiraki sannan kuma ni na tambayeki Ki sanar dani abindake faruwa...Is there anything I can do to help..?!” Fuzar da huci tai a hankali kana tace “They wanted to do a background check on me...Ansar they were planning to have me investigated...!” A tak’aice Ta labarta masa tattaunawar Mahmood da Raheema dataji...Ta k’arashe tana mai dafe goshinta da hannu guda... Kaman wanda yake ganinta yace da ita “Just calm down and take a deep breath..! As long as ina taredake bazan bari susan ko ke wacece ba... Karki damu kinji, just leave that to me, I would take care of that...abinda kawai nakeso dake shine kici gaba da kula, karki basu wata k’ofa da zasu fahimci ko ke wacece kinji koh...” Ta jinjina masa kai a hankali “In sha Allah... Bazan basu ba... Thank you Dr, thank you for always having my back..!” Suna gama waya da Ansar tura file d’in gabansa yai yana d’an dukan kansa da pen, baida lokacin tsayuwa yin fad’a ko fushi da Muhibbah... Yafi kowa Allah Allah ta gama wannan mission d’in nata ta dawo ai maganar aurensu once and for all... Dole yai hak’uri da dik wani fushi da fad’a ya aje komai a gefe ya taimaka mata ta ida wannan so called mission d’in nata dan idan ba haka ba the more yana biyeta sunayin fad’a the more yawan lokacinda zatai zaune cikin Masarautar yana k’aruwa... Ya kuma fuzar da fuci a hankali yana mai bada izini ma patient na gaba da ya shigo... *** A b’angaren Muhibbah kaw zuciyarta ne yai wasai dan tasan Ansar zai toshe dik wani k’ofardasu Raheema zasubi a makaranta su gano asalinta, yanzu abinda ya rage mata shine tai monitoring duk wani move nasu Raheema idanma son samu ne ta shige jikinsu ta samu yardarsu dukda tasan hakan abu ne mai matuk’ar wuya tinda tin farkon had’uwarsu babu jituwa sam tsakaninsu musamman dashike Raheema gani take tamkar Ta shigo Masarautar ne dan Ta k’wace mata masoyinta Yarima Mahmood.. Dan haka shiga jikin Raheema zai matuk’ar mata wahala... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai kuma sak’e sak’e cikin zuciyarta had’ida neman mafita... ** A cen parlorn Mahmood kuwa tsaye yai yana duban Turaki hannayensa hard’e ta baya... Saida ya kuma takowa kad’an kana yaja ya tsaya “Turaki bana shakkan su fahimci cewa ni ne bak’on Buzu... Abu guda da zaisa bazan bayyana masu kaina a matsayin bak’on Buzu ba shine nima akwai abinda nake bincike cikin gidan sannan Ina akwai abinda nake son fahimta gameda ciwon Baba Wambai... Idan har da gaske akwai wani abinda Baba Wambai ya sani gameda abubuwan da suka jima suna faruwa a gidan nan Kaga babu makawa za’a nemi a b’addashi Ta ko wacce hanya ko kuma a hansa yin magana.. Everything is possible a gidan nan, zasu iyayin komai to silent him dan asirinsu ya rufu...So kaga dole na k’ara taka tsantsan hardai inaso na sami amsoshin da na jima Ina nema...!” Jinjina kai Turai yai a hankali yace “Wannan gaskiya ne Your Highness... Toh yanzu mai kake shiryawa...?” D’an dubansa da wutsiyar idanu Mahmood yai kana ya kauda fuskarsa kad’an “Lokaci zai sanar damu...!” Ya fad’i yana mai zama cikin kujera... Turaki yai ma abokin nasa k’uri kana yace “Toh shi Majidad’i fah... Ya zakai dashi... I’m sure he won’t stop tunda ya soma kutso Kai cikin Fada d’aukeda makami... Sannan na tabbata a shirye yake sosai...!” Ba tareda ya dubesa ba yake furta “Zan k’yalesa yaci gaba da bincikensa... In the process na bincikensa zai iya samomin wani abu da zai min amfani a binciken da nake, wannan na d’aya daga cikin dalilin da yasa nace a k’yalesa... Is possible someone has been monitoring my every move all this time... Ta yuwu akwai wanda yasan cewa nine bak’on Buzu saidai bazai iya fitowa ya fad’i ba dan shima mafita yake nema ma kansa...Ta yuwu ya fahimci ina gab da tono gaskiya shine bari ya rufe bakin Baba Wambai ta wannan hanya.... But koma menene I’d make sure to be one step ahead of them...!” Ya k’arashe yana mai duban Turakin.... Turaki ya murmusa kad’an cikeda jin dad’i yana mai jinjina kai lokaci guda yake ci gaba da yabawa zurfin tunanin abokin nasa... Tabbas ya yarda Mahmood zai zak’ulo duk wanda sukeda hannu cikin manak’isar wannan gida.... Yarima Mahmood ya d’auki glass cup dake aje gefensa na dama saman k’aramar table dake tsakankanin kujeru ya kurb’a, har lokacin k’uri yaima waje guda yana mai murza bandage d’in dake d’aure hannunsa... Soma murza bandage d’in Keda wuya tinaninta ya fad’o zuciyarsa... Take ya soma tina duk abubuwan da suka faru daki daki, sanda take goge masa ciwon da kuma sanda take rufe tafin hannun nasa da bandeji... For the first time da ya saki murmushi tun bayan abubuwan nan dake kan faruwa... Turaki yai masa K’uri ganin ya k’urama waje guda idanu yana sakin sihirtaccen murmushi mai taushi wanda saika kula ka fahimci hakan... Sallaman Ubandoma ya dawo dashi daga duniyar tinanin da yai nisa ciki... Ubandoma ya zube yana kwasan gaisuwa, nan yake sanarda Yarima Mahmood Giwa tayi Aiken Jakadiya cewa tana san ganin Yarima... Jinjina masa kai yai alamun amsawa... Turaki ne ya soma ya soma mik’ewa sukai sallama kana suka jera a tare suka fito... Suka tsaya nan cikin haraban sashen Mahmood d’in... Yarima Mahmoood yaci gaba da fad’in “Wani aiki nakeso kamin Turaki...!” Turaki ya jinjina kai “Duk abinda mai Martaba yace...!” Jinjina kai Mahmood d’inma yai had’ida yin gyaran murya kad’an “Ja’afar...!” Turaki ya dubesa da mamaki yana jiran yaji mai Mahmood d’in zai d’aura... “Turaki I want you to hire a private detective wanda zai mana bincike akan where about d’in Jafar, dik yanda Ja’afar ya shiga ya fita inaso a samoshi... Can you do that..?!” Turaki ya jinjina kai “Of course your Highness, leave it to me... I can handle that Rankaidad’e..!” Jinjina kai Mahmood ya kuma yi kana sukai masabaha had’ida sallama Turaki na fad’in sai yaji daga garesa... Kallo guda zakai mata ka fahimci tana cikin tsananin tashin hankali.. Aiko Mahmood na shigowa Giwa ta k’araso garesa tana mai janyo hannunsa mai ciwo take fad’in “Sadauki lafia kake... Shin ta yaya wannan mahaukacin yaron zai shigo har cikin gidan nan yai mana wannan wulak’ancin... Toh wannan masarauta bazata lamunta ba, ya zama dole a hukuntasa...!” Ta k’arashe cikin tsananin huci cikeda tashin hankali... Kafad’unta Mahmood ya kamo ya zauanrta saman cushion a hankali lokaci guda yake furta “Take it easy Maami, ki kwantar da hankalinki banaso kina saka irin wad’Annan abubuwan a zuciyarki...!” Giwa ta d’an marairaice fuska tace “Shikenan sai in zuba idanu su sakaka gaba... Kaima kasan bazan iya hakanba Sadauki...!” Ta k’arashe cikeda kulawa... Nusawa kad’an yai yace “Maami a gida irin namu dole mu saba da irin wad’ann abubuwan so ba wani abu bane In sha Allah...!” Ta mik’e daga zaunen da take tana mai karantarsa, a hankali take zagaya d’akin har ta k’araso gabansa ta tsaya “Sadauki... Maiyasa kak’i amsar Sarauta...?” “Maami inada manufata da shirina...!” Ya fad’i kansa tsaye... Giwa ta had’iyi miyau da k’yar zatai magana kenan Jamal ya shigo da sallama... Dubansu yake da alamun tambaya saman fuskarsa dan tuni ya karanci halinda mahaifiyarsu Ke ciki...Shid’in ya santa sosai wanda idan tana cikin tashin hankali zai iya fad’i haka idan tana cikin Farin ciki da annashuwa zai iya fad’i... Shid’in yasan ko wane motsi na Mahaifiyarsu... Jamal na shigowa Mahmood yai sallamada Giwa ya fice... Sukabi bayansa da kallo har ya b’ace masu daga ita har Jamal... Yarima Mahmood na ficewa Jamal ya k’araso da sauri yana tambayarta meke faruwa Giwa ta k’arasa ta zauna saman kujeranta na alfarma “Gwarzo..!” Ta ambato sunan Jamal cikin kakkausan Murya... Ya k’araso ya duk’a gabanta yana dubanta cikeda kulawa “Inaso kaja hankalin d’an Uwanka Mahmood ya amince ya amshi sarautar nan idan ba haka ba munaji muna gani sarautar nan zata kubce daga gidan nan duk abubuwan da muka jima munayi zai tashi a banza, zamu fice daga gidan nan cikin k’ask’anci da tozarci... Nasan bazakaso haka ba d’ah na...!” Ta k’arashe tana aika masa wani irin duba... A hankali ya shiga jinjina kansa “Maami Karki damu zanyi duk yanda zanyi Yaya ya amince ya amshi sarautar nan... Bayan abinda ya faru yau cikin Fada ya zama dole Yaya ya amshi sarautar nan ko dan ya kare Martaban Ahalinmu a kuma gidanmu...!” Giwa ta jinjina kai su duka biyun suna masu duban juna... *** Tafiya mai nisa Majidad’i yai tamkar masu barin gari, saida sukeje wajen gari yanda babu mutane sosai yaja yai parking... Ya kaikaito yana duban Yazeed dake zaune gefensa... “Ina saurarenka, mai kake nema wajena kana jinin AbdulJabbar...?!” Murmusawa kad’an Yazeed yai “Abinda kake nema shi nake nema... The THRONE...!!” Majidad’i ya dubesa da mamaki, lokaci guda ya saki murmushin rainin hankali “Toh mai kakeso nai maka..? Ai d’anuwanka Mahmood ya kamata kaje ka samu da wannan batu amma bani ba...!” Murmusawa Yazeed ya kumayi yana mai gyara zamansa cikin kujeran “Kana tunanin nida kai zamu samu sarautar ne muddin Mahmood na tsakani...?” D’an rage girman idanunsa Majidad’i yai yana mai girgiza kai “Ban fahimceka ba... Go straight to the point...!” Yazeed ya shafa hab’arsa kad’an “Abu guda nake nufi muyi tarayya akai dan cikar burinmu...Let’s take my brother down....!!” Yai maganar yana tsare Majidad’i da idanu shu’umin murmushin bai bar saman fuskarsa ba... SameenaAleeyou📚 [7/12, 4:21 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *032* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Bazawarin murmushi Majidad’i yai a karo na biyu, ya kuma gyara zamarsa sosai yana duban Yazeed da ya kafesa da idanu babu alamun wasa a tattaredashi... “Ni zaka rainawa hankali...? So kake kai amfani dani wajen cimma burinka...? Kai d’in kana tinanin ni zan barka kai amfani dani ne... Har abada bazan tab’a amincewa da wani cikin zuri’ar AbdulJabbar ba..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Shu’umin murmushi Yazeed ya kumayi a karo na babu adadi “A cikin wannan battle d’in you need me more than I need you, zan maka amfani fiyeda yanda zaka min... Kasan ance da d’an gari akanci gari.. Bazaka tab’a samun Karagar nan ba ba tareda taimakon d’aya daga cikin ahalin AbdulJabbar ba... Idan baka amince min ba haka Kanajina kana gani sarauta bazata tab’a komawa gidanku ba, Idan Yayana Mahmood ya gama zamaninsa ni ne nan zan amshi mulkin ba kaiba haka idan na gama Magaji na d’ah na ko d’aya daga cikin k’annena shi zai amshi mulkin... Kaman Yanda Baba Wambai ya tsufa bai gaji gidansu ba tarihin abinda ya faru dashi zai kuma maimaita kanshi akanka kaga har abada jininku bazasu kuma samun wannan sarauta ba... Amma idan ka amince min muka had’a k’arfi da k’arfe muka yak’i Mahmood yak’in neman sarautar zai tsaya ne tsakanin mu biyu... Ni da kuma Kai...!” Ya d’anyi fasali yana duban Majidad’i da tuni ya apka tarkonsa, ya kuma sakin murmushin nasa kana ya mik’a hannu ya d’auki takobin Majidad’i da hannu guda ya d’agata sama yana juyata a hankali yake k’are mata kallo lokaci guda yake ci gaba da sakin murmushi yana furta “Takobi zai maye gurbin Mahmood a tsakaninmu... Domin kuwa shi ne zai fitar da Jarumi cikin mu biyun...Takobi shi zai raba gardama a tsakaninmu sannan ya tantance Jarumi cikinmu...Shi zai tantance waye ya dace da rik’on Sarautar wannan Masarauta...!!!” Ya k’arashe yana mai d’ora bakin takwabin a saitin wuyar Majidad’i murmushin bai bar saman fuskarsa ba... Murmushi Majidad’in ma yai kana yace “Kana tinanin zaka iya karawa dani...?!” Hab’ar Majidad’i kad’an Yazeed ya kama daidai sanda yake Yawo da makamin a saitin wuyar Majidad’in, lokaci guda yake furta “Babu alamun ragwanci ga mutuminda ya nuna abokin karawansa da makami har yai nasaran saita makamin a mak’oshinsa... I can cut your throat right this instant amma bazanyi hakan ba dan nafi so mu kara a filin daga yanda babu Dakarun da zasu kawo mana d’auki... Takwabi ce kad’ai zatai magana a tsakaninmu...!” Ya k’arashe yana mai cire takobin daga wuyan Majidad’i... Wani murmushi renin hankali Majidad’i yai yana mai jinjina kai “Finally jinin AbdulJabbar mai tinani irin nawa... Jarumi shi ya cancanci sarautar wannan masarauta namu, kaman yanda kace Takobi zata raba gardama tsakaninmu a filin daga... Zamu dawo da tsohon Al’adun kakaninmu wanda Jarumi kad’ai Ke yin Sarauta.... Naji dad’in wannan shawari naka

Chapter 19 of 65