ba... Ansar na tafi Masarautar nan ne badon kawai na d’auki fansar abinda suka min ba saidan Nayi tunanin mahaifina might still be alive sannan zan iya samunsa cikin Masarautar watak’ila sun maidasa bawa ko wani abu dan bamuga gawarsa ba.. Only to find out he was killed by those monsters, sannan sun k’ona gawarsa cikin gidan... Ansar mahaifina bai samu an masa wanka da sutura kaman yanda musulunci ya tanadar ba... An k’onasa a wulak’ance cikin k’ask’anci wanda ko tokarsa ba’a samu ba baida kabarin da zance eh yana makwancinsa a kwance... Shin idan kaine hakan ya faru da kai yaya zakaji...!”
Hawaye suka gangaro masa, Muhibbah taci gaba da fad’in “Bayan na fahimci wannan na kuma fahimtar wani sabon abu cewa mutumin da nafi k’ullata da gaba baida Sa hannu ko kad’a cikin abinda ya faru dani, na cutar dashi na had’asa da d’iyarsa.. Na kunyatasa a idanun al’ummarsa... Shin wannan wane irin zalunci nayi Ansar..? Da wane ido zan dube mutumin da ya taimakeni a lokacinda mak’iyina yaso cimma mummunan burinsa akaina... Ya k’ub’utar dani daga sharrinsa cikin ikon Allah ya kawoni gida safe and sound, bai bar k’ofar gidan nan ba har saida yaga shigewata gida cikin aminci...Wannan mutumin ne a baya nai masa mummunan zato, na dangantasa da laifin da ko a mafarki shid’in bazai aikata ba... Ansar na cutar da mutumin kirki wanda baida buri da ya wuce ya taimaki bayin Allah... Shin kana tunanin Allah zai barni haka...!”
D’agowa sosai wannan karon Ansar yayi da idanunsa masu zuban ruwa yace “I don’t get you Hibbah... Wane mak’iyinki ne yaso cimma burinsa akanki....!”
Tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka kuma ziraro mata tace “Fad’a maka baida wani amfani, tuno abin tashin hankali ne da k’unci ma zuciya... Sannan komai ya riga da yazo k’arshe bazan koma wancan Masarautar ba... It’s over..!” Ta k’arashe cikin rawar murya..
Ansar dake sakin huci da ya fahimci tabbas d’aya daga cikin yaran Sarkin ne ya kuma attempting raping d’inta for the second time... Dunk’ule hannunsa yai ya daki garu yana mai fuzar da huci yake furta “Wllhi idan nayi ido biyu dashi sai na kasheshi ko ba jima ko ba dad’e..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci... Sanin tsananin suya da zuciyarsa keyi yasa ya fice daga parlorn gaba d’aya kaman zai kifa da k’asa...
Iya larai ta hangosa, tana kiransa tana fad’in abinci ya kammala inaa ko waigowa baiba balle ya amsata saima huci da yakeyi kaman wani zaki... Iya Larai ta bisa da kallo cikeda mamakin meke faruwa...
Parlor ta lek’o yanda taga Muhibbah jingine jikin garu idanunta a lumshe ga hawaye na gangaro mata.. Ta koma da baya a hankali tana k’ok’arin lalumar wayarta dake k’ulle bakin zani dan ya kamata Ta kira Hajiya ta sanar da ita abinda ke faruwa...
**
Turaki yaja Burki gefen kwalta yana duban Mahmood da har lokacin tamkar gunki yake, banda sakin huci da murza zobban yatsunsa baya komai... “Haba your Highness, Wai dan Allah shikenan bazaka cire wannan abu a ranka ba, Allah ya kiyaye we arrived there on time babu abinda yayi mata, ita da kanta tace babu abinda ya faru.. Kayi hak’uri ka cire abin nan haka a ranka please your Highness..!”
“Shut the hell up Turaki...! What if ya sakeyi.. I need to teach him a lesson a very good one ta yanda bazai sake marmarin that disgust act ba..!!”
Turaki ya fuzar da huci a hankali kana ya tashi Mota suka ci gaba da tafiya....
**
Giwa da dawowarta kenan daga asibiti wajen ‘ya’yanta Jakadiya Jakadiya ta tareta da mummunan labarin har yau babu Izzatu babu dalilinta... Dafe da kai Giwa ta zauna gijif cikin kujerarta na alfarma tana kame b’angaren k’irjinta da takeji kaman caccaka mata manyan k’ayoyi...
Fad’I take “Jakadiya idan kika sake zuwa min da labari maras dad’I hakan ka iya sanadin rayuwarki...!!”
Jakadiya ta kuma risinawa cikeda tsantsan damuwa had’ida tashin hankali dan tasan itama idan har asirin Giwa ya tonu to nata k’arshen ne yazo.. “Tuba nake Rankidad’e... Allah ya huci zuciyar Giwar Amale... Allah ya baiwa ‘ya’yan Sarki lafiya...Jaa zamaninki Giwa guda d’aya tilo cikin Masarautar nan..!” Ta k’arashe tana mai d’ago babban yatsarta alamun jinjina...
Daidai lokacin Yazeed ya shigo da kumburarren FUSKA tamkar wanda aka jefosa...
Ba Jakadiya kawai ba harta Giwa saida ta razana da ganin yanda halittar fuskan Yazeed ya koma sabida kumbura da alamun ciwo....
SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*
*47*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin tsananin huci Yazeed yake furtama Giwa “Ina d’anki wllhi sai na kashesa, sai na masa illan da gobe ko cewa akai ya d’aga hannu ya d’aura jikina bazai ba... Ina yake ki fito mun dashi..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji...
Giwa Ta baiwa Jakadiya izinin fita kana ta maida hankalinta kacaukam kan Yazeed dake ci gaba da huci “Yazeed.. Meye haka nakeji, Wai dama ba had’arin mota kayi ba.. Waye ya maka irin wannan bugun...?!”
Yazeed dake aika mata wulak’antaccen kallo matsowa kusanta ya kumayi yana furta “Wllhi sai na kashesa, sai nayi ajalinsa koda hakan zaisa ki had’iyi zuciya tunda shi kika fifita akaina... Wllhi sai nayi ajalin Mahmood muddin Ina numfashi a doron k’asa...!”
Kaman daga sama ya sinkayo muryar Mahmood d’in yana fad’in “Idan bakayi ba Yazeed baka cika ba... Yau ka tabbatar min da cewa kaid’in maras mutunci ne kuma maras imani, so duk abinda zakayi yanzu bazai bani mamaki ba..!!” Yayi maganar cikin tsananin huci k’irjinsa na kuma bud’ewa kaikace wani bugun zai sake yiwa Yazeed...
Giwa da zuciyarta Ke ci gaba da tsinkewa ta tari Mahmood da fad’in “Sadauki Wai meke faruwa ne... Kan wane dalili zakaiwa d’anuwanka na jini irin wannan bugun kawo wuk’an bayan iftila’i da tashin tashin hankula da muke fuskanta cikin Masarautar nan...?!”
Bai janye idanunsa daga duban k’yama da yake aikawa Yazeed ba yace “Maami ask your Son mai ya aikata... Ask him wane irin k’azamin laifi yau d’in ya tasamma aikatawa...!!”
Giwa ta dubi Yazeed wanda shima hucin yake sakewa yana duban Mahmood, Ta kuma juyowa ta dubi Mahmood d’in da shima Ke ci gaba a sakin huci idanunsa kan Yazeed...
“Mahmood mai kake nufi, wane irin kaifi Yazeed ya tasamma aikatawa..?!”
Cikin karaji Yazeed yace “Maami don’t listen to any of his lies... K’age yakeso yamin dan nima nayi kamanceceniya da hali irin nasa sabida yasan cewa d’iyarsa ta hanyar banza ya sameta..!” Baikai aya ba Mahmood ya toshe bakin nasa da naushi, Yazeed ya zube k’asa yana kame bakinsa...
Da yatsa Mahmood ke nunasa “Baka San komai akan d’iyata ba..! Dan haka kada ka sake ambatan sunanata a wannan k’azamin bakin naka...!”
Cikin d’imauta Giwa Ke fad’in “Wai meke faruwa daku ne... Shin sai d’ayanku ya kasheni ne... Wai menene haka kukeyi...!”
Yarima Mahmood ne ya katseta da fad’in “Maami kinada masaniyar cewa d’anki is a criminal... He almost raped someone’s daughter... Tir da hali irin naka Yazeed, kuma kada kaji da Wai baka sha ba ni nan zan damk’aka wa hukuma a k’watar ma wacce kaso zalinta hakkinta... Maras mutunci kawai...!!”
Giwa da duniyar Ke juye mata gaban Mahmood Ta k’araso ta rik’e hannunsa tana fad’in “So kake ka tozartamu ka b’ata Martaban gidanmu... Shin ka kuwa San abinda kake k’ok’arin yi Sadauki... Ka tab’a ganin an kira hukumar ‘yansanda cikin Fada...!”
Cikin k’unan rai yana mai girgiza kai ya katseta da fad’in “Sabida Fada ba’a gayyato hukuma shine ya baiwa mutanen cikinta dama su ci zarafin sauran Al’umma... Shin Maami ki fad’a min wata dokace ta baiwa ‘ya’yan Masarautar nan daman su ci zarafin sauran bayin Allah... Shin wannan shine mulkin adalci..? Idan har baza’a baiwa kowa dama da ‘yanci irinta mutanen cikin masarauta ba bana tunanin wannan sarauta an gina sa ne kan adalci...!”
Giwa da takaicinsa ya gama k’ulle mata mak’oshi ji take kaman ta fincikosa ta shak’esa ya mutu har lahira ko zata huta, saurin katsesa tai a hasale da fad’in “Wane adalci kake magana...? Adalcin da zai tab’a Martaban gidanku... Adalcin da zai sakaku jin kunyar duniya... Adalcin da zai zamto tozarci a gareku.. Shine kake magana Mahmood..? Ince da bakinka kace attempting yayi bai aikata ba... Toh kan wane dalili zaka Sa Jami’an tsaro su shigo har cikin Fada su kama d’an uwanka... Shin wannan shine irin sarautar da zaka gudanar Mahmood... Ka rusa Martaban Gidan nan ka wulak’anta mutuncin rawani...?! Idan har kuwa kayi hakan Ina mai tabbatar maka saidai ka nemi wata mahaifiyar amma bani ba..!!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...
Shaye da tsananin mamaki Mahmood Ke duban mahaifiyar tasu ganin yanda b’aro b’aro ga gaskiya gabanta amma Ta zab’i ta rufe idanunta... A hankali yake girgiza kai kana ya soma fad’in “Ban tab’a tsammanin zanji haka daga bakinki ba Maami a matsayinki na shugaba ga Al’umma sannan kema mace ce Maami, na zaci ciwon d’iya mace na d’iya mace ne... Maami sanin kanki ne babu abu mafi muni da zai auku ga d’iya mace tamkar wani yaci zarafinta Ta hanyar fyad’e... Tashin hankali ne da zai rayu da ita tsawon rayuwar da zatayi a duniya...Maami fyad’e k’azamin laifi ne mafi muni wanda duk wanda zai aikata irin wannan laifi bai cancanci a kirasa d’an Adam ba don babu mutum mai hankali da yake cikin hayyacinsa da zai aikata k’azamin laifi irin fyad’e... Maami koda ace duka yaranki maza ne ya kamata ki tuna ita wacce yaso zalunta d’iyar watace... Maami kiyi tunani da ace Yazeed ya aikata laifin nan wane irin k’unci da tashin hankali Mahaifiyar yarinyar zata tsinci kanta ciki...Fyad’e k’azamin laifi ne, mummunan aiki ne wanda duk mutum mai hankali zai k’yamace shi..!”
A hasale Yazeed dake rik’eda bakinsa da jini ya b’ata ya mik’e yana fad’in “Really Your Highness... Shin laifin ka k’yamata kokuwa dai kanada wani abu ne a zuciyarka... Why can’t you just admit it already, son yarinyar kake shiyasa duk hankalinka ya tashi kake ganin kaman na rigaka saninta saurana zaka samu..!!” Ya k’arashe shu’umar murmushin nan nasa saman fuskarsa...
Mahmood dake tsananin sakin huci da yatsa ya nunasa yace “Idan ka sake magana cikin d’akin nan zan tako har wajen na kikkifa maka mari... Mutumin banza kawai, Allah ya wadaran hali irin naka...!” Ya k’arashe yana mai ficewa daga sashen gaba d’aya...
Yana ficewa Giwa ta k’arasoga Yazeed tana aika masa muguwar kallo, shid’inma muguwar kallon yake aika mata.. Tsuka yai ya mik’e sosai yana furta “What..? Ai na zaci zaki bari Mahmood ya mik’ani ga hukuma ne tinda duk kin fifitasa akanmu and especially me... Da kuwa kinyi gigin barin hakan ya kasance wllhi da na tono baya na sanar dashi wacece ta koya mana aikata laifin fyad’e tun bamu Kai haka ba...!” Yai muguwar murmushin nan nasa
Giwa tai saurin Kai hannu ta toshe bakinsa tace “So kake ahalinmu ya tarwatse...?!”
Yazeed ya fincika hannunta ya bud’e bakinsa yace “Tarwatsewa na yaushe, ga can halinda kika baro ‘ya’yanki ciki and you’re losing Mahmood too dan na tabbata bayan juya baya da kikaiwa gaskiya a yau zai wuya yaci gaba da miki irin biyayyar da yake miki a baya Gimbiya Turai... Kuma barikiji na fad’a miki muddin kikaci ba da goyon bayan Mahmood yai sarauta wllhi kinji na rantse miki sai na tono baya... Sai na sanar dashi mummunan aikin da kika sa muka aikata..!!” Ya k’arashe yana mai jifarta da muguwar kallo kana yasa kai ya fice...
Saiga Giwa tayi zaune dirshan saman gwiwoyinta hawaye na gangaro mata... Bataci ta zama ba da irin babubuwan dake faruwa da ita, dole ta ziyarci Tal’udu taji a ina ya makara tulin abubuwan nan suke faruwa da ita wanda ko ta ina babu wani sauk’i... Jakadiya ce ta shigo tana mata Fadanci dan ranta yayi sanyi amma tsawan da Ta dakama Jakadiyan ya sanyata komawa da baya babu shiri har tana karo da k’ofa... Giwa ta zube wajen sosai tana kuka da gaske ko zata samu taji sanyi cikin zuciyarta...
**
Duk yanda Yazeed zai wuce kowa idan ya dubesa saidai ya kauda fuska sabida yanda halittar fuskar tasa ta sauya, gashi babu rawani balle ya rufe fuskar tasa da ita, banda harara baya aika wa mutanen cikin Masarautar komai, wasu bayi guda biyu da suka kasa janye idanunsu daga barin dubansa ya daka masu tsawa da fad’in “What are you looking at..! Ku b’ace daga nan kafin ku rasa rayuwarku.. K’ask’antattu kawai.!!!” Ya k’arashe yana mai shigewa sashensa...
A parlor ya tadda Zuhra da Raheema suna fira irinta k’awaye...Aiko suna hangosa haka suka mik’e babu shiri... Bai tanka kowa a cikinsu ba saima kallon banza da ya rakasu dashi kana yayi hayewarsa sama....
Zuhra da Raheema suka dubi juna, Raheema tace “Zama bai ganki ba Zuhra, tashi tashi maza kije kiji abinda ya sami mijinki Ina tunanin had’arin mota ya samu...!”
Zuhra ta jinjina kai kana ta mik’e a sauri Ta haye sama d’akin Yazeed... Tana haurawa Raheema ta mik’e cikin sand’a ta waiga gefe da gefe kana ta lallab’a ta haura saman itama, daidai jikin k’ofar d’akin Yazeed ta lab’e tana sauraren tattaunawarsu...
Cikeda tsoro Zuhra ta k’arasa zata amshi ice block d’in dake nad’e cikin towel hannunsa da niyyan taimaka masa, kallon wulak’anci ya aika mata kana yace “Kika k’araso nan sai na fasa miki k’ank’aran nan akai...!”
Tai tsaye daga yanda take tana mai shanye k’uncinta, jinjina kanta tai a hankali kana tace “Naji bakaso na taimaka maka but please ka sanar dani Ina ka sami raunin nan, a matsayina na Matarka ya kamata na sani Prince, kodai had’arin mota ka samu...?!”
Murmusawa yai da gefen bakinsa kana ya shiga k’are mata kallo daga sama zuwa k’asa a gadarance, duba irinta k’ask’anci “Su matata manya..! Dan Ke matata ce sai akace sai dole kisan komai gamedani...? Kin zata dan kina matata kinada wani k’ima ko daraja a idanuna ne... Kin San mai na d’auki mata...! Abun holewa ne kawai da shak’atawa, nothing more nothing less...! So dan kina a matsayin matata hakan bai baki wani kima ko daraja a idanuna ba..Now get out of my sight..! Fita nace kafin Ranki ya b’aci...!!” Ya k’arashe cikin karaji...
Babu shiri Zuhra da tuni hawaye sun wanke mata fuska ta fice a guje tana toshe kukan da yazo bakinta gadan gadan kana Ta fad’a d’akinta tai ma k’ofar key ta haye gado tana canzan kuka...
Raheema dake mak’ale bayan k’ofa Zuhra na ficewa daga d’akin Yazeed tai wuf ta shige ta maidoda k’ofar ta rufe....
Kallo guda yai mata ya watsar yana mai ci gaba da abinda yake cikin ko in kula...
Gabansa ta k’araso ta tsaya tana huci take fad’in “You’re not a man Yazeed... How could you say those horrible things to your wife.... You disgust me..!!”
Da idanu guda yake dubanta daga sama zuwa k’asa kana yace “Did you say I disgust you..? What if I take my anger out on you..!!” Ya k’arashe yana mai zabura kaman zaiyo kanta..
Raheema tajada baya cikeda tsoro lokaci guda Yazeed ya koma ya zauna yaci gaba da abinda yake, murmushi saman fuskarsa yake furta “And the loyal best friend come to the rescue..! Ke har kinada bakin da zakiyi magana dan an wulak’anta Zuhra...Tell me duk fad’in duniyar nan akwai wanda ya wulak’anta Zuhra sama da wulak’ancin da Ke kika mata ne...?!”
Raheema ta katsesa da fad’in “Yes nasan naci amananta in the most painful way but bana goyon bayan ka wulak’anta ta ka aibata Ta, ka k’yaleta taji da cin amanarta da kake da matan banza a waje... Wait speaking of matan banza, don’t tell me garin biye biyen matan Naka ne akaji maka wannan raunin...?!”
Ya kafeta da idanu murmushi saman fuskarsa, lokaci guda ya mik’e yana takowa gabanta sosai har saida suka isa jikin gini, fuskarsu dab kusan na juna yake fad’in “Why... Why do you care..? Tell me are you jealous...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa...
Raheema dake sakin huci a hankali k’ak’aro murmushi tai tace “Me.. Jealous of you..? Allah ya sawak’e min Kaima kasan zuciyata na Mahmood ne shi kad’ai...!”
Wannan karon murmushi mai bayyana hak’wara Yazeed yai kana ya saita idanunsa cikin na Raheema ya kuma gyara tsayuwarsa yana mai furta “What if na sanar dake cewa Yarima Mahmood shine yaji min wannan raunin kuma ba akan kowa ba sai akan mace kaman yanda kikai zato...!”
Ta d’ago firgitattun idanunta tana dubansa a razane “Yazeed mai kake son cewa ban fahimceka ba...?!”
Yazeed ya kuma murmusawa yace “Zama ki fahimceni... Your beloved Prince is in love with another girl... Ke barin fad’a miki Mahmood bai k’aunarki coz I can see it in his eyes wannan yarinyar yake so kuma akanta ne yamin jina jina dan yana tsoron na rigashi saninta... Now that you know get out of my room kafin nima na sauk’e takaicina akanki na miki jina jina a wajen nan..!!”
Huci kurum Raheema take tana mai furta “K’arya kake Mahmood bazai tab’a min haka ba, ni yake so... Hasalima shi ba mai kula mata bane baida wannan lokaci.....!” Batakai aya ba taji Yazeed ya damk’o wuyarta da k’arfinda Allah ya hore masa, cikin huci yake furta “Ni kike kira mak’aryaci... Sai na karya wuya ki a wajen nan naga gatanki...!!”
Raheema sai firfito da idanu waje take tana k’ok’arin janye hannun Yazeed daga wuyarta, tana rok’onsa Allah Annabi ya sakar mata wuya kada ya kasheta cikin muryarta da bai fita sosai... Saida tai Laushi yayi jifa da ita gefe.. Ta fad’i k’asa tana tari da k’yar a hankali dan kar a jiyota, tanayi tana sosa wuyarta...
Tsuka ya buga kana ya k’araso yanda take ya shiga janyota kaman kayan wanki yayi jifa da ita daga cikin d’akin kana ya maida k’ofa ya rufe... A d’ari Raheema ta mik’e ta nufi downstairs cikin sauri dan kar Zuhra ta fito ta ganta.. Tana tafe tana sosa wuyarta da har lokacin zogi yake mata....
**
BAUCHI
Suna zaune itada Mummy a parlor, tv na aiki lokaci guda Mummy na sorting wasu takardu dake gabanta yai sallama ya shigo da alama daga asibiti yake....
Mummy tace “Likita an dawo..?” Tai maganar tana aje wasu takardun gefe had’ida zare Farin gilashi na k’arin k’arfin gani daga idanunta....
Ansar ya jinjina kai yace “Eh Mummy mun sameku lafiya...?”
Ta amsa masa kana ya gaisar da mahaifiyar tasa yana mai satan duban b’angaren da Muhibbah take ko zatai masa magana amma shiru batace komai ba, Mummy na hankalce dasu dan tinda rana da Iya Larai ta kirata ta sanar da ita dawowar Muhibbah da kuma abinda ta gani babu yanda batai ba Muhibbar ta sanar da ita abinda ke faruwa amma sai ce mata tai babu komai lecture free week suke shisa tazo gida..
Muhibbah ta mik’e tana furta “Mummy zan duba Iya Larai a kitchen...”
Dakatar da ita Mommy tai da fad’in “Dawo nan Muhibbah, Zo ki zauna...!”
Babu musu da ta dawo mazauninta ta zauna fuskarta babu walwala, har lokacin Ansar bai daina satan kallanta ba...
SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*
*48*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Dubansu duka biyu Mommy tai kana tai gyaran murya kad’an tace “Ina saurarenku.. Can anyone explain what’s going on here..? And don’t even think of lying to me Dan Larai ta kirani ta sanar dani komai..!”
Muhibbah tai saurin d’ago idanunta masu rauni tana duban Mommy da sam babu walwala tattareda ita...
Jin sunyi shiru su duka biyun yasa Mommy kuma fad’in “What’s wrong with the both of you... Kai Ansar kaine Babba Wai meke faruwa ne..? Meke faruwa tsakaninku..?!”
Ansar ya fuzar da fuci kad’an yace “Mommy is nothing serious, Kinsan Iya Larai da exaggerating abu...!”
Galala take dubansa kana tace “I see, ni zaka rainawa hankali... Tunda nake daku ban tab’a ganin ka dawo aiki Muhibbah batai maka sannu da zuwa ba duk fad’a da fushin da zakuyi da juna, nasan ba abu ne mai sauk’i zaisa shigowarka ya sanyata ficewa daga parlorn nan ba... Amma idan kunce haka, tsakaninku ne, kuyi sulhu da kanku banso tun yanzu na dinga shiga fad’arku..” Ta dubi Muhibbah da har lokacin jikinta a sanyaye yake tace “Tashi kije abinki kinji d’iyata..”
Muhibbah ta jinjina kai a hankali tace “Toh Mommy, kana Ta mik’e Ta wuce jiki a sanyaye Ansar na satan kallanta...
Tana shigewa Mommy ta maidoda hankalinta sosaiga Ansar tai gyaran murya ta kirawo sunansa...
Ya amsa cikin risinawa, Mommy taci gaba da fad’in
“Ni ba ma wannan ba d’azu Baffanka Yawale yaje har office ya sameni da batun saka maku rana, nace masa sai nayi shawari da duka yarana biyu naji yaushe suke so a saka bikinsu...!” Tai maganar tana mai maida glasses d’inta had’ida janyo wasu takardun...
Cikin wane irin bugawan zuciya Muhibbah dake k’ok’arin shigewa corridor taja ta tsaya d’agowa tana duban Mommy daga can yanda take zaune cikin parlor, ta kuma dubi Ansar da annuri tuni ya cika fuskarsa, lokaci guda yake furta “Mommy Baffah Yawale da kansa yake fad’in a saka mana da Muhibbah, kenan yanzu ya amince na aureta..?!”
Sauk’e ajiyan zuciya tai kad’an tace “Ya amince amma Yana nan akan bakansa na aura maka d’iyarsa Hameeda, idan ka amince da sharad’insa sai a aura maka su biyun rana guda...!”
Cikin k’unan rai Ansar ke furta “Wai Mommy Baffah Yawale wane irin mutum ne shi, Wai ana aure dole ne... Nace bana son wannan yarinyar, bana sonta ko ana so dole ne... Mommy ni fah Muhibbah kawai nake so, kuma ita kad’ai ta isheni... In fact banida ra’ayin Auren mata biyu sabida nasan duk macen dana had’ata da Hibbah bazan tab’a mata adalci ba... Haka kawai bazan kai kaina wuta ba Mommy... Nidai ki fad’a masa bana son d’iyarsa...!”
“Kai rufe min baki, bansan rashin kunya... Da kake gaya min sak’o kake bani naje na fad’a masa... Kana gani tun daga tasowarka kawo girmanka irin gwagwarmayar da nayi da mutanen nan akanka... Babu yanda basuyi ba sai Sun karb’eka daga hannuna tun bayan rasuwar mahaifinka amma na jajirce na hanasu nace babu mai rabani da d’ah na dan na tabbata cikinsu babu wanda zai baka future mai kyau... Ansar babu irin wulak’anci da ban gani ba daga wajen dangin mahaifinka ganin sun karb’eka daga hannuna amma na shanye komai, naita gwagwarmayar rainonka ganin ka sami ingantacciyar rayuwa... Babu irin sunayen da basu dangantaka dashi ba sunce ka zama D’an mace, sunce na maisheka had’e, sunce K’abila ta sace d’an Ard’o...Har cewa sukai zan maidaka Arne cikin ‘yan uwana Arna, wanene wanene amma duk na shanye nace naji na gani ni ce nan zan raineka da dad’i da babu dad’i... Toh amma yau dashike ka girma ka zama mutum gashi suna son had’a iri da had’e... Toh amma shi mutum ka tura masa aniyarsa... Hamida da mahaifiyarta basuda matsala, yarinyar tanada hankali da hali irin na mahaifiyarta... Dan ka aureta ni inaga ba wani matsala bane kuma inada tabbacin baza’a sami matsala daga Muhibbah ba...”
Ansar dake k’ok’arin danne b’acin ransa yace “Mommy a gaban idonki mutumin nan yace bazai barni na auri Muhibbah ba sabida batada asali... Shine yanzu zaice ya amince na aureta dan kawai na auri d’iyarsa... Toh gaskiya Mommy ni bazan iya auren d’iyarsa ba... Maganan gaskiya kenan, kawai ni za’a tak’urani ne... I’m sorry Mommy but gaskiya I can’t...!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye zuciyarsa naci gaba da tafarfasa...
Kallo mahaifiyar tasa Ta bisa dashi har ya b’acewa ganinta, ta girgiza kanta a hankali tana mai ci gaba da abinda take...
Muhibbah kuwa d’aki ta shige ta fad’a saman gado tana kukan da ita kanta bata San dalili ba... Kodashike dalili da yawa zai iya zama sanadin kukan nata... Bayan gwagwarmayar da suka sha da dangin mahaifin Ansar na ganin sun koreta ma daga gidan gaba d’aya wanda badon Allah yasa Mommy mace ce jajirtacciya wacce ke tsaye kan k’afafunta da sun jima da yin sanadin barinta gidan musamman da suka fahimci soyayya da shak’uwar dake tsakaninta da Ansar... Bayan duka wannan yanzu at last wanda yafi kowa k’ullatanta da kyaranta ya amince Ansar ya aureta amma kuma wai da sharad’in zai auri d’iyarsa, rana guda za’a d’aura masu aure...Bayan wannan kuma gacan halinda ta baro Zahra ciki a masarauta wanda duk abinda yaje yazo tsakanin Yarima Mahmood da d’iyarsa itace sila... Har abada bazata tab’a samun kwanciyar hankali ba sanin cewa ta b’ata tsakanin d’iya da mahaifi... Ita duk bama wannan ba yau da taji da kunnuwarta ana maganan saka masu rana da Ansar ji tai kwata kwata bata muradin auren, tana ki can k’asan zuciyarta bazata iya rayuwa dashi matsayin miji ba...Shin yaya zatayi... Menene abinyi..?! Ta lumshe idanunta wasu hawayen suka kuma gangaro mata, hijabi Ta janyo ta zira ta fice ta k’ofan baya ana kiraye kirayen sallan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 30 Chapter of 65