hankali kana tasa kai Ta fice...
Tana ficewa ya d’auki wayarsa saman center table ya shiga dialing layin Turaki....
**
Raheema na fitowa ta hangi Yazeed tsaye hannayensa hard’e yana dubanta muguwar murmushin nan saman fuskarsa, murmushin itama ta sakar masa kana tabi wani hanya, saida ya waiga gefe da gefe kana yasa kai shima yabi bayanta....
Yazeed ya dubeta yace “So tell me plan d’in yayi working...?!”
Murmusawa tai tace “Kaid’in na daban ne... Na tabbata bayan abinda ya faru Mahmood zai aureni ya d’auke d’iyarsa mu bar k’asar nan...!”
Ta kuma takowa zuwa gaban Yazeed lokaci guda tasa hannu ta dafe fuskrsa, cikin kissa take furta “Yanzu ka hak’ura kenan ka bar wa Yayanka ni..?!”
Murmushin nan nasa saman fuskarsa yake furta “Akan SARAUTAR nan babu abinda bazanyi ba, babu abinda bazan sadaukar ba... That throne is mine.... So na zab’i na rabu dake muddin zan gaji sarautar mahaifina...!!”
Ya k’arashe yana mai d’an bubbuga fuskarta yanda akewa yara...
Yazeed yaci gaba da fad’in “Mahmood is all yours ke kad’anki sai yanda kikaso kiyi dashi...!”
Suka murmusa a tare kana Yazeed yace “Yaushe zaa bani na k’ashe tinda na sallamawa Mahmood..?”
Ta murmusa tace “Karka damu Prince akwai farewell da zamuyi... Just make sure you didn’t ruin our plans...!”
Yazeed ya murmusa yace “An wuce wannan ai tinda har aka sako Zahra ciki... She’s his greatest weakness... Ina mai tabbatar miki nan bada jimawa ba zakiji ya tafi masarautar ku neman aurenki..!”
Raheema ta kuma murmusawa cikeda jin dad’i tace “At last burina zai cika... Na Barka lafiya Your royal Highness...!”
Yazeed ya jinjina mata kai alamun amsawa murmushin nan nasa saman fuskarsa...
**
Cikin rashin fahimta Turaki ya mik’e tsaye yana furta “You can’t be serious your Highness... Please think your decision through, Your Highness you can’t leave... Musamman yanzu da family d’inka suka fi buk’atarka... Ka duba kaga halinda Jamal da Fu’ad ke ciki, haka zaka tafi ka barsu... And and ina labarin neman justice da kakewa mahaifinka da matarka... Ina maganan search for Ja’afar da kake...? Shin duk ka mance wanann zaka aje komai ka tafi.... Your Highness ina alk’awarin da kayiwa Wambai... Are you going to leave all this behind.... Sannan bayan duka wannan ka zab’i ka auri macen da baka so ka tafi kai rayuwa cikin k’unci... C’mon your Highness, think about all this... This is not the right time for you to leave...!”
Katsesa Mahmood yai da fad’in “Yes Turaki na zab’i na bar komai behind for my daughter.. Can’t you see I’m loosing my daughter here... It’s over I’ve made up my mind zan auri Raheema na d’auki d’iyata mu koma Spain... She’s better off this way Turaki banso mukai peak d’in da zan rasata gaba d’aya... Zahra ita kad’ai nake gani na tuna Aliya.... Nothing can stop me now Turaki... Ka shirya within the week zamu tafi Masarautar su Raheema neman aurenta..!”
Turaki dake dubansa cikeda mamaki girgiza kai kurum yake hannayensa dafe da kunkumi, ya kasa yarda da abinda yakeji daga abokin nasa....
**
D’aki ne mai tsananin duhuwa wanda baka iya ganin komai koda kuwa tafin hannunka ne sabida tsananin duhuwansa, Ubandoma ya sa hannu ya daki k’ofar take haske ya bayyana...
Cikin sauri tasa tafukan hannayenta biyu tana kare fuskarta.... Ubandoma ya isa ya aje mata kwanon abincin dake hannunsa...
Matsawa da baya take tsoro bayyane saman fuskarta
Lokaci guda Ubandoma yace “Ki kwantar da hankalinki Kin kub’uta daga hannun azzalumai bazan miki komai ba....!”
*MUHIBBAH*
*50*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ubandoma ya koma gefe ya zauna yai mata k’uri yana duban yanda take jefa abincin cikin bakinta hannu baka hannu k’warya alamun ta galabaita da yunwa.. Shikadai saiko mahaliccinsa yasan abinda yake k’ullawa cikin zuciyarsa.... Ya sani duk duniyar nan yanzu Giwa batada burin da ya wuce ta sami Izzatu... Bazai bari hakan ya kasance ba dan shima nada nasa shirin akanta... Watak’ila Izzatu ta zamto mabud’in samun ‘yancinsa.... Ya saki murmushi a hankali kana ya matso kusanta yace “Ki kwantar da hankalinki bazan sake d’aureki da sark’ok’i kaman yanda nakeyi a baya ba... Kin fahimceni...?!”
Bata amsasa ba saima ci gaba da tura abincin da take cikin bakinta... Mik’ewa Ubandoma yai ya fice daga cikin d’akin ya kuma kulleta nan cikin d’akin kana yai tafiyarsa....
Ubandoma na ficewa mahaukaciya Izzatu ta mik’e tana shafa ginin da Ubandoma ya ijeta ciki a hankali hawaye na gangaro mata... Cokalin da Ubandoma ya kawo mata abinci dashi ta soma karjan ginin tana saka hannunta tana gogewa... Cikin ikon Allah ginin sai ya soma b’anb’arewa yana zubewa duk yanda ta karje da cokalin... Ta zauna sosai tana ci gaba da karje ginin da iyaka k’arfinta bataji bata gani sai aikin abu guda take karje garu.. Ginin sai zuba yake a hankali tana kuma samun hanya...
**
A can asibiti kuwa yau ake saka rana sallaman Jamal shi kuwa Fu’ad har yanzu babu yanda yake, ya farfad’o amma da alama muggan k’wayoyi sun kuma juya masa kwanyarsa dole akai transferring nasa to psychiatric ward... Shi kad’ai yake buga kansa jikin garu yana jin ciwo ma kansa tinda ya farka, aikin abu guda yake babu magana babu komai sai dukan kansa jikin garu ala dole aka dadd’aure Fu’ad da manyan sark’ok’i a fannin mahaukata dake nan cikin teaching hospital d’in, Giwa bata iya komawa ta gansa ba dan bazata juri ganin d’anta a d’aure da sark’ok’i ba cikin hauka tuburan...
Shi kuwa Jamal alla alla yake ya dawo gida sabida duk dare akwai yanda yake zuwa cikin Masarautar, idan baije ba komai ka iya faruwa... Saidai yana tinanin ta yanda zai soma shiga Masarautar a matsayin gurgu makasashe saman wheelchair... Hawaye masu tsananin d’umi suka ciko idanunsa, Umaima dake gefe murmushi Ta sakar masa tace “Yaya Dr yace yanzu zai sallameka mu koma gida... I’ll park your belongings..!” Ta k’arashe tana mai isa yanda kayayyakin nasa suke...
Cikin rawar murya yake furta “I can’t Umaima, bazan iya komawa Masarauta a haka ba... Dan Allah ki ce masu su dawo min da k’afata....!” Ya k’arashe hawaye na gangaro masa...
Gaban wheelchair d’in nasa ta k’araso ta d’an duk’a kad’an tace “Ya Jamal I thought we’ve already talked about that.... Yaya please ka karb’i k’addararka babu wanda Yafi k’arfin hakan... Tsautsayi tana kan kowa... Shin kanaso ka zamto cikin mutane wanda basa yarda da k’addara ne...? Yaya kada ka zamto mai butulci wa mahalaccinka... Kaji please..!” Ta k’arashe kaman zatai kuka...
Dubanta yake da idanunsa masu rauni kana yace “Nasan kina fad’a min haka ne kawai dan naji dad’i amma babu wanda zai kuma accepting d’ina the way I’m, even you Umaima bazakiso ki auri nakasashe irina ba...!”
Hawaye na gangaro mata take dubansa lokaci guda take furta “Ya Jamal ina sonka... Ina sonka a duk yanayin daka tsinci kanka ciki, ka daina doubting soyayyar da nake maka... Wasu lokutan ba appearance na mutum ake dubawa ba, kyawawan d’abi’u da halayya ake dubi da... Mutum mai kyawawan d’abi’u irin naka ba’a sakaci da soyayyarsa... I love you Ya Jamal..!”
Jamal yai mata K’uri yana dubanta zuciyarsa na masa wane irin sanyi“Zaki aureni a yanda nake.. Kin amince da zaran mun koma masarauta a saka bikinmu...?!”
Murmushi saman fuskarta take jinjina masa kai “Yes Yaya... Na amince zan aureka... Na amince a saka mana ranan aure..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta hawaye na gangaro mata...
Murmushin Shima ya sakar mata yace “Thank you so much my love... I love you...!” Daidai nan Dr ya shigo da takardun discharging Jamal sai zolayan Umaima yake yana fad’in daga yau ta daina yinin asibiti.. A ‘yan kwanaki biyun da Jamal yai kullum can wajensa take yini wanda hakan sosai yake d’ebe masa kewa...
**
A b’angaren Giwa abubuwa sun kuma rikice mata, babu labari mai dad’i daga Ubandoma ko Waziri gameda neman Izzatu gashi gobe wa’adin da Tal’udu ya bata yake cika... Gaba d’aya ta rasa yana zata saka kanta sabida tashin hankali, har wani rama da bak’i Giwa tayi.. Ko Fadarta bata iya fitowa kullum cikin neman mafita take... Babu abinda yake gabanta yanzu tamkar taga Ta sami Izzatu yanda ta shiga ta fita, idan kaga Giwa zakai zaton ciwo take... Kowa a Masarautar sabgan gabansa da abinda ya damesa yake... Yazeed na k’ok’arin yanda zai ya kawar da Mahmood daga Masarautar shima Mahmood d’in na k’ok’arin yaga ya shawo kan d’iyarsa daga iftila’in da suka tsinci kansu ciki... Tuni ya sanar da Giwa k’udirinsa na auren Raheema saidai bai sanar da ita shirinsa na barin k’asar tareda Raheema da d’iyarsa Zahra ba, Giwa tayi na’am musamman dataji za’a had’a Bikin aurensa da Bikin nad’asa sarauta ne hakan sosai yayi masu dad’i itada Waziri, a k’arshe zasu rabu da Mahmood su huta su kuma d’aura alhakin mutuwarsa kan matarsa Raheema da kuma yayarta Gimbiya Zeenatu, shikenan sun kashe tsuntsu biyu da dutse guda... Shi kuwa Yazeed bai nuna damuwarsa da batun nad’in sarautar da za’aiwa Mahmood ranan bikin aurensa ba tinda yasan shirin Mahmood d’in barin k’asar zai da zaran ya auri Raheema bazai jira su nad’asa sarauta ba, a k’arshe idan babu Mahmood dole a nad’asa shi Yazeed a matsayin Sarki....
Ita kuwa Raheema tuni ta koma Masarautar su tinda aka soma batun aurensu da Mahmood.. Gimbiya Zeenatu bata sama bata k’asa burinta na mallakan masarauta ya kusa tabbata...
**
Jamal ne a d’akinsa shi kad’ai sai kai komo yake dafe da sandarsa ta crotchets yana zullumin abinda ka iya zuwa yazo bayan kwanaki biyu da ya shafe bai je yanda yake zuwa cikin Masarautar ba... Waht if ya mutu...? Wata zuciya tace idan ya mutu ai hutunka tinda dama kace da Giwa ka riga ka kashesa tun wancan lokacin sannan Umaima zata zamto taka kai kad’ai har abada... Mutuwar nasa zai fi maka... Toh amma idan bai mutu ba fah... Idan ya sami wani hanya yayi escaping fah..? Kai ai Babu hanyar da zai samu ya gudu bayan alluran gusar da hankali da kake jibga masa had’ida k’wayoyin da kake narka masa a ruwan shansa.... Bazai tab’a iya escaping ba... Lokaci guda kaman wanda aka sinkaya ya isa jikin drawer ya janyo ya ciro doguwar syringe d’in ya zuk’i ruwan magani ya d’agata sama yana kallo kana ya saki murmushi a hankali yana kad’a syringe d’in daidai lokacinda Umaima tai knocking hannunta d’aukeda tray na fruits...
A d’ari Jamal yai saurin maida syringe d’in cikin drawer ya juyo yana tambayar ko wanene...
Umaima tace itace daga nan yanda take tsaye bakin k’ofa... Sauri sauri ya maida duk abubuwan da ya d’auko kana ya isa k’ofar dafe da crutches d’insa ya bud’e mata murmushi saman fuskarsa..
Murmushin ta sakar masa itama wanda yafi kama yak’e kana tace “Naga baka parlor nace barin hauro maka dashi tinda ka hana duk Kuyangin gidan nan shigowa sashenka kuma time d’in shan maganinka yayi...!”
K’uri yai mata yana jin dad’in yanda take nuna damuwarta akansa... Lokaci guda ya kauce ya bata hanya yace “Please come in...!”
Umaima ta jinjina kai ta rab’a ta shige a hankali kana ta isa ta aje masa tray d’in saman rug... Jin k’aran rufe k’ofa ya sanyata saurin juyowa alamun tsoro fal fuskarta...
Murmushi ya sakar mata yana mai dogarowa yanda take yace “Ya naga yanayinki ya canza... Ko tsorona kike...?”
Ta kuma sakar masa murmushi wanda yafi kama da yak’e tace “A’a Yaya... Ka sha maganinka kafin lokaci ya k’ure..!”
Ya jinjina mata kai alamun toh zaisha...
Suna a haka Giwa ta shigo sashen nasa... Kallo taiwa Umaima ta watsar, Umaima ta sinne kai ta gaisheta dan tun bayan da suka soma soyayya da Jamal nauyin Giwa ya k’aru cikin idanunta... Tai excusing kanta ta fice Jamal na biyeda ita da ido....
Umaima na ficewa Giwa tace “Kai mai yarinyar nan take d’akinka...?!”
Ya kuwa watsa mata harara dan yanzu kallon arziki bai shiga tsakaninsa da mahaifiyar tasa... “Is non of your business...!” Ya fad’i yana mai juya mata baya....
Giwa ta k’araso sosai cikin d’akin had’ida furta “Tun wuri ka janye wannan shiririta da kake... Babu kai babu auren Umaima...!”
Kaikaitowa yai yana dubanta kana ya murmusa kad’an yace “Da gaske Maami..?!” Ya murmusa kad’an yace “Kin makara, na riga na gama miki biyayya muddin kikai gangancin yunk’urin dakatar da aurena da Umaima... Yau d’in nan basai gobe ba zan sanar dasu Galadima batun aurena da Umaima, in fact tareda na Yaya Mahmood nake so a had’a..!”
Giwa da fuzar da huci kad’an tace “Gwarzona kalleni nan kaji... Ni fah bance kada kayi aure ba amma da ka d’an sarara ka sake dubawa ko zaka sami wata, ni tabbata ba wata soyayya bace tsakaninku da Umaima SHAKUWA CE kawai....!”
Wane irin duba ya watsa mata kana ya saki murmushi da gefen bakinsa yace “A yanayin da nake ciki har cewa kike na tsaya na sake dubawa bayan nasan babu mai k’aunata tsakanida Allah a yanda nake... Maami koma akwai ni bani son kowa sai Umaima kuma dole a saka aurenmu lokaci guda dana Yaya Mahmood tinda nida ita mun sasanta da juna kuma duka abin d’aya ne Maami, nida Umaima duka ‘ya’yanki ne... Idan har zaki amince Yaya Mahmood ya auri k’anwar kishiyarki na tabbata zaki amince na auri d’iyar d’an uwanki... Saidai kuma idan akwai abinda kike b’oyewa wanda ni kaina ban sani ba Maami.....?!” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu...
Ganin ta kasa magana ya sanyashi sakin murmushi yace “Nasan baki fata dark secrets d’inki su soma bayyana...! Dan wllhi if you try something funny zan baki mamaki irin wanda baki tab’a zato daga gareni ba...!” Ya k’arashe yana sakin huci...
Idanu waje Giwa ke dubansa zuciyarta na wane irin bugawa, Yazeed threatens her yanzu ga Jamal ma nayi, wannan wace irin rayuwa ce ace ‘ya’yanka na cikinka na maka barazana bayan duk sadaukarwa da take sabida su ne da samun ingantacciyar rayuwarsu... Ta had’iyi miyau da k’yar kana ta murmusa tace “Yanda kake so Gwarzona...!” Tana kaiwa nan ta juya ta fice cikin sassarfa..
Jamal yabita da idanu har ta b’acewa ganinsa kana ya d’auko syringe d’insa da zummar ficewa.... Yana rik’eda syringe ga kuma crutches hakan yasa yai losing balance Allurar ta karkace ta sokesa a cinya.... K’ara ya saki ya zube a wajen yana rik’eda cinyarsa yanda allurar ta cakkesa... Kan kace mai idanunsa sun soma lumshewa ya zube wajen....
**
Cikin sa’a taci gaba da kankare ginin har ta soma jin wane irin yanayi gaba d’aya illahirin jikinta... Bata fasa abinda take ba taci gaba da karjan ginin ko Allah zai bata dama ta gudu.... Ginin yai dogon rami da kana iya hango d’aya b’angaren dukda ba wani sosai ba... Idanunta ta lik’a jikin ramin ga mamakinta d’aki ta hango iyaka ganinka... Dukda akwai duhuwa saidai kaman tana iya jiyo sautin numfashin mutum yana fita da k’yar... Zuciyarta ya kuma yankewa Ta k’ara manna k’wayar idanunta jikin ramin.... Kaman daga sama taji an tab’a k’ofarta, tai saurin komawa ta zauna a mazauninta had’ida toshe ramin da take karjewa... Ubandoma ne ya kuma shigowa ya aje mata abinci maiji da lafiya harda ruwan sha kana ya kuma ficewa....
Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali ta koma jikin ramin tana ci gaba da karje ginin sannu a hankali....
**
BAUCHI
Fitowa yai cikin shirinsa na tafiya office, ya lek’a kitchen ko zai ganta dan wasu lokutan nan yake taddata tareda Iya Larai sabida akasarin lokutan tare suke ayyukan... Bai taddata ba sai Iya Larai dake sauraron shirye shiryen safiya a radio... Gaisawa sukai kana ya tambayeta Mommy, Iya larai tace ai tuntuni ta fice Office...
Ansar ya jinjin Kai ba tareda ya kuma cewa komai ba, Iya Larai ta fahimcesa sarai Muhibbah yake son tambaya, Ta d’an bud’e murya tace “A kawo maka shayin naka ne...?!”
Ya girgiza kai idanunsa naga wayar salulansa yake fad’in “A’a Iya Larai na gode azumi nake..!”
Iya Larai tace “Aff ashe yau alhamis ai na mance azumin alhamis da litinin basa shigeka... Ka gaisa da mutumiyar taka ce... Tana ciki yau duka bata fito ba..?!”
Janye idanunsa yai daga saman screen d’in wayar tasa yace “Amma lafiya bata fito ba..?”
“Eh Toh kasan tinda ta dawo daga makarantar nan gaba d’aya mun rasa gane kanta amma dai naji jiya da dare tanaceda Hajiya yau d’in Zata koma makaranta sabida jarabawa dake gabato masu...”
Bai ida sauraren Iya Larai ba yasa kai ya shige cikin sauri,.. Iya Larai tabisa da kallo had’ida girgiza kai a hankali...
K’ofar d’akin nata ya tsaya yana knocking...
A zatonta Iya Larai ne ta d’an bud’e murya tace “Iya shigo abinki had’a kaya nake..”
Aya taima kalaman nata ganin wanda ya turo k’ofar...
Ta d’an kauda fuska kad’an had’ida fuzar da iska...
Murya can k’asa ta gaishesa... Ya amsa yana mai bin jakan kayan nata da kallo
“Why are you parking... Ina zakije..?” Yai mata tambayoyin a tare...
Idanunta naga wane b’angaren take furta “Zan koma Masarauta ne..!”
Dafe da handle d’in k’ofa yake dubanta “What.!! Masarauta kuma... What for..? I thought we’ve already talked about that, bazaki koma wannan Masarautar ba...!”
Katsesa tai da fad’in “I’ve changed my mind... Zan koma..!”
Murmushin da yafi kama da yak’e Ansar yai kana yace “But abinda van gane ba shine mai zaki koma yi cen..?!”
“Zan koma ne to fix what I ruined... Bazan iya zama a nan ba alhali ina saneda cewa na b’ata tsakanin d’iya da mahaifi... I need to go back na gyara abinda na b’ata...!”
Fuzar da huci yai a karo na biyu yana mai girgiza kai yake furta “Kinyi haka ne a bisa rashin sani Muhibbah, You don’t need to go back... Ya kamata mu bada hankalinmu kan batun aurenmu dake k’aratowa... Akwai maganar da nake so muyi dake dama..!”
Ta katsesa da fad’in “Kan Hameedah...? Kar ka damu bakada matsala dani, taimakona kukayi and duk wani condition d’in da zaku gindaya min zan d’auka... Nasani Baffah Yawale ya amince da aurenmu ne da sharad’in shima zaka auri d’iyarsa Hameedah right..?!”
Ansar ya shafe fuskarsa da tafukan hannunsa had’ida gyara tsayuwarsa yace “Ba haka bane Muhibbah..!”
“Then yaya ne..? Make me understand..! Shikenan dan an taimakeka sai ace rayuwarka ma sai yanda akeso za’a tsara..? I’m not saying kada ka auri ‘yar uwarka..!”
Katseta yai da fad’in “Hibbah please listen to me first... Wannan ba yin na bane kuma ba yin Mommy bane... Hibbah idan dan tani ne bazan auri d’iyarsu ba amma saidai Mommy bata buk’atan wani tashin hankali a halin yanzu shisa tace na amince da auren Hamidar..”
Murmushin da take ya katsesa, tasa bayan hannunta ta goge hawayen da suka gangaro mata “Karka damu bakada matsala daga b’angare na... All I’m asking now shine ka barni naje na gyara abinda na b’ata kafin ai maganar aurenmu... Besides babu wani zab’i ga wanda yai losing hope..!”
Yanda tai maganar tamkar sak’o take basa a dunk’ule...
Yai mata K’uri na ‘yan dak’ik’ai kana ya girgiza kai yace “Ban fahimceki ba... Wanda tai losing hope kaman yaya...?!”
Ta k’ak’aro murmushi had’ida girgiza kai tace “Rayuwar da kake mafarkin samu wanda bazaka tab’a samu ba... Toh duk rayuwar daka tsinci kanka ciki sai kai fatan Allah yasa hakan ya zame maka alkhairi..!”
Girgiza kai Ansar yai yace “Rayuwa dani ne k’addara..? Kokuwa dai rayuwa da kishiya ne k’addarar...? Kodai kinada wani wanda kike mafarkin rayuwa dashi ne matsayin ma’aurata K’addara take yunk’urin hana yuwar hakan... Muhibbah wannene ciki...? Talk to me answer me... Do you love someone else..?!”
Tambayar da yai mata ya haifar mata da wane irin fad’uwan gaba Ta d’ago dara daran idanunta tana dubansa zuciyarta naci gaba da bugawa...
Murmusawa tai kad’an “Ya kake magana haka... Ni kuma soyayya da wani...? Sanin kanka ne bayan iftila’in da ya auka dani na d’auki lokaci mai tsawo kafin na amince akwai wata aba Wai ita soyayya tsakanin mace da namiji.... Bansan soyayyan kowa ba sai naka Ya Ansar... Maiyasa kake tinanin inada ‘yanci da soyayya da wani bayan kai...?!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...
Cikin sanyin jiki Ansar ya duk’a gabanta yace “Muhibbah you’ve all the right kiyi soyayya da wanda kike s koda ba ni bane.... Muhibbah ina sonki, ina k’aunarki... And I’m not asking you to love me back... Kuma ki daina d’aukan kanki a matsayin wacce aka taimaka dole tayi duk abinda muke so... No kin wuce haka a wajenmu, kin cancanci Farin ciki kema... Idan kikace baki sona I can understand you...!” Ya k’arashe cikin rawar murya...
K’uri tai masa hawaye na kuma gangaro mata... Ansar yai k’ok’arin saita kansa yace “Idan kin gama parking d’in muje na maidake, I’ll cancel my appointments for today...!”
Tai saurin mik’ewa tana mai girgiza kai take furta “No, kar ka damu zan tafi bakin hanya yanzun nan nasan bazan rasa motan Jos ba... Bai kamata ka dakatar da aikinka sabida ni ba...!”
Girgiza kai yai yana mai shafa wayar salulansa yake furta “I insist, you first before anything else, and is not safe nowadays ka shiga mota daga kan hanya, idan har shiga motan hayan ya kama dole toh yafi dacewa kaje tasha ka shiga motar da zai tashi daga gari zuwa gari direct..” (Matafiya a dinga hattara duba da yanzu yanda hanyoyinmu suka koma... Allah yaci gaba da karemu ya kawo mana lafiya da zaman lafiya a k’asarmu..Ameen!)
Jiki a matuk’ar sanyaye take ida shirin nata sanda ya janyo jakan kayan nata waya manne kunnensa yake furta “Doc eh wllhi, tafiya ce ta gaggawa ta taso min.. Ok toh shikenan babu matsala... Zamuyi magana later... Yauwa thank you..” Ya k’arashe maganar yana mai ficewa...
Tausayinsa ya lullub’eta gaba d’aya... Ansar ya cancanci Farin ciki... Shida mahaifiyarsa mutanen kirki ne... Koda ace bata sonsa tabbas zata iya sadaukar da soyayyarta ta amince ta aureshi domin shid’in yayi mata dukkan wani hallaci... So tari zaka so abu babu alkhairi cikinsa, sannan so tari zaka k’i abu shine maka alkhairi... Zataci gaba da addu’a Allah ya sanya aurenta da Ansar ya zamto Alkhairi ya kuma zamto silan mance duk wani k’unci na rayuwa data tsinci kanta ciki a baya...
A haka suka d’auki hanyar Jos duka su biyu d’in babu walwala a tattaredasu... Sanda suka isa yai parking a yanda ya saba parking... Ya juyo ya d’an dubeta kana ya sakar mata murmushi “Idan har dawowarki don ki gyara abinda kika b’ata shine kwanciyar hankalinki na amince miki da hakan... Allah ya baki nasaran cimma burinki cikin sauk’i....!”
Ta murmusa kad’an tace “Na gode Yaya Ansar... Na gode da fahimta da kake min a koda yaushe, sannan ina mai sanar dakai da zaran ka koma Bauchi kuyi shawari da Mommy ku yanke ranan aurenmu, duk lokacinda ya kwanta maka... Ni kuma nayi na’am da hakan... I’m ready to be all yours..!” Ta k’arashe murmushin k’arfin hali saman fuskarta...
Jin abin yai kaman wasa, ya kuma gyara zama yana dubanta “Are you serious Hibbah..?!”
Murmushi saman fuskarta Ta jinjina masa kai alamun tabbatarwa... Murmushin shima yayi kana yace “Bazan iya ce miki komai a yanzu ba, dan bansan ta yanda zan soma had’o kalaman Farin cikin da na tsinci kaina ciki ba... The only abu da zan fad’a miki yanzu shine na miki alk’awarin bazakiyi danasanin aurena ba in sha Allah...!”
Ta murmusa tana mai sadda kai k’asa tace “Ya kamata ka d’auki hanya kada rana yai maka...!”
Ya jinjina kai had’ida d’aga mata hannu alamun salute yace an gama your Highness yanzun nan ma kuwa...!”
Muhibbah ta murmusa tai masa fatan sauk’a lafiya kana sukai sallama ta d’auki hanyar masarauta gabanta na tsananta fad’uwa...
Hanshak’an motoci na Alfarma data gani ne barbaje cikin Masarautar ya sanyata ci gaba da tafiya cikin sanyin jiki tana kuma bin motocin da ido... Ga dogarai da Fadawa Ta ko ina suna gyara kimtsi...
“Tooh yau kuma meke faruwa cikin Masarautar...?!” Ta furta a hankali...
Can ta hangosa cikin shiga ta manyan kaya, farar shadda k’al ‘yar ciki da babban gare ga kuma farar rawani mai kunne biyu akansa, sosai k’warjininsa ya kuma fitowa... Wani taku yake irinta asalin jinin sarauta wanda babu sirki ko gauraye da jinin bauta...Tai tsaye tana dubansa zuciyarta naci gaba da bugawa... Sai fadanci ake masa masu sarauta na take masa baya...
Tana gani aka bud’e masa rantstiyar SUV fara k’al ya shige ciki Turaki ya shige ta d’aya b’angaren shima yayi shiga irinta masu mulki... Hadiminsa ya shige gaban motar bayan ya gama bud’ewa Ubangidan nasa... Sauran masu sarauta su Waziri da su Galadima suka shige sauran motocin yayinda motar security Ta soma ficewa daga cikin Masarautar ana baza hidiman iko...
Tabisu da kallo har suka fice kana ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali ta nufo cikin Fada... Tana tafe ne ta hangi Ubandoma sai waige waige yake a yayinda hankulan jam’an masarauta ya karkataga fatan sauk’a lafiya ga Yarima Mahmood
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 65