Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ina Sarkin yake..?” Guda d’ayar Ta basu amsa da fad’in “Yana ward 3 naji ance brother d’insa Yarima Yazeed yazo dubawa..!” Bata rufe baki ba Giwa dake kwance saman gado matashiyan Ta soma fad’in “Mahmood.! Mahmood yana asibtin nan..? Mahmood ni yazo dubawa.. Yazo d’aukana mu tafi..!” Daidai lokacin Fu’ad ya shigo d’akin idanunsa naga Giwa yanda takeda korirtoto tana ambaton sunan Mahmood... K’walla tab idanunsa ya soma takawa cikin d’akin... A haka har ya isa gaban gadon da Giwa Ke kwance bisa... Yai K’uri yana duban yanda fuskar nata ya sauya, halittarta gaba d’aya ta sauya... Fatar fuskar mele gaba d’aya, idanun baka ganin Farin Sai k’wayan bak’in kawai kake iya hangowa suma da k’yar aka bud’esu bayan anyi surgery d’aya yayi sama d’aya yayi k’asa.. Karan hancin babu sai alamun huji guda biyu wanda suma saida akayi surgery Allah ya taimaka aka bud’esu... Fatar bakinta kuwa gaba d’aya ya kwashe babu Sai hak’waran kawai kake hangowa a waje... Kanta ne kawai mai iya motsawa a jikinta... Sanda taji alamun tsayuwar mutum akanta Ta soma furta “Mahmood.. Sadauki nah.. Mahmood kaine...!” Ta k’arashe tana mai karkato a wuyanta wanda shi kad’ai take iya motsawa a gaba d’aya illahirin jikinta... Fu’ad Ta gani tsaye kanta hawaye na gangaro masa... Lokaci guda Giwa Ke furta “Kukan mai kake Fu’ad bayan burinka ya cika ka gayawa Mahmood gaskiya.. Duk kai ka soma jefa Mu a bala’in Da muka tsinci kanmu... D’aukeni ka kaini wajen Mahmood Ina son ganinsa.. Nasan munafukan Masarauta ne suka shiga tsakaninmu.. D’auken ka kaini Fu’ad..!” Ta k’arashe cikin daka tsawa hawaye basu daina zubowa daga cikin idanun Fu’ad ba... Jamal dake can basa b’angaren yana sauraron duk abinda ake fad’i Wai Mahmood cikin asibitin.. Mahmood shine yayi sanadiyan kasancewarsa kwance a nan cikin nakasa, tabbas idan har Mahmood na cikin asibitin duk yanda zai sai Sun had’u shima ya nakasa sa koma yayi ajalinsa gaba d’aya... Ya saki muguwar murmushin nan nasa da gefen bakinsa... ** Yazeed na kallon sama hawaye naci gaba da zubo masa yake fad’in “Na kasance d’ah maras ji a idon mahaifinmu dukda cewa ni ne nake kula da duk wasu al’amran sarauta na gidan... Abbah baya gani, ko da yaushe kaine a gabanshi, Kaida Fu’ad kune favorites d’insa dukda cewa kud’in baku kasance masu son gadon gidan ba... Baka hidiman da ni nake masa..But still ya zab’i ya fifitaka sama dani wanda banida buri da ya wuce na gajesa.. Maybe yanaji can k’asar zuciyarsa kaida Fu’ad ne kawai ‘ya’yansa shiyasa yafi baku duk wani kulawa da soyayyarsa, especially you...!” Ya kaikaito yana duban Mahmood d’in wanda shima shi yake duba... Lokaci guda Yazeed yaci gaba da fad’in “Banida burin da ya wuce na tozartaka a rayuwana, but Look at me now, babu sarautar babu asali babu dangantaka.. And what’s worse na kashe yarana da hannayena guda biyu..Kai kuma gaka nan da sarautar, yau Allah ya baka... Na yarda cewa Rayuwar nan gaba d’ayanta jarabawa ce.. Allah shike bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, fad’in rai da nuna d’agawa da isa ba ya kai mutum ga Komai face k’ask’anci.. Tabbas duk wanda yayi d’agawa ya nuna shi wani ne ya nuna yanada k’arfin Mulkin da zai taka kowa kafin ya bar duniya sai Allah ya nuna masa isharan cewa shid’in ba kowa bane kaman yanda ya k’ak’antar da Fir’auna ya nuna masa shi bai isa ba Allah shi kad’aine isasshe...!” Muryarsa ya soma rawa sosai sanda yake furta “ Your Highness a yau inaso na rok’eka gafara from the bottom of my heart Dan Allah ka yafe mun duk wasu abubuwa da nayi maka a baya... Sannan ka rok’ar min matarka itama Ta yafe mun... Dan Allah ku yafe mun ko naji sauk’in halinda nake ciki..!” Kuka ya hana Yazeed ci gaba da magana... Daidai lokacin Fu’ad dake tura Giwa saman wheelchair kanta a karkace gefe suka nufo d’akin Yazeed d’in.. Duk wanda yayi arba da Giwa sai yaji kaman ya ruga a guje sabida yanda fuskarta ta koma... Ja’afar da tawagan Dogaran Sarki Mahmood dake tsaye daga k’ofa tsaye sukai suna duban ikon Allah dan ko gane Giwa basuyi ba, sundaiga Fu’ad na turo dodanniya saman wheelchair... Saida ta soma korortoto kafin suka d’ago muryar Giwa.. Dogarai suka k’araso suna fad’in bazata shiga ciki ba Sarki na cikin d’akin.. Giwa taci gaba da ambato sunan Mahmood tana fad’in su barta ta shiga taga d’anta... Ja’afar ya tako gabanta yana k’are mata kallo.. Kafin yayi magana Fu’ad yace dashi “Please Ja’afar, nasan bata cancanta but please ka k’yaleta Ta ganshi just this once..!” Ya k’arashe cikin rawar murya... Tausayin Fu’ad d’in ya kama J’afar, duk shirin walak’ancin da yayi niyyan yi ma Giwa sai yaji bazai iya ba ko dan idon Fu’ad.. Duk abinda tayi she’s still his mother.. Sosai Fu’ad ya basa tausayi.. A hankali ya matsa gefe yai umarni ma dogaran su basu hanya su shige... Suna shigewa shika yabi bayansu ya shige cikin d’akin... Aiko Jamal dake biye dasu dafe da sandarsa sannan ya kuma dank’wafewa sabida k’unan wutan da yayi.. Aiko Dogaran nan suna bada hanya shima ya duk’a yana rarrafawa da hannayensa had’ida janyo sandarsa a hankali har ya samu ya shige cikin d’akin hannayensa rik’eda almak’ashi har guda uku wanda ake masa dressing dasu.. Dukda azaban zafin da yakeji amma sabida taurin zuciya bai fasa jan jiki har ya tsinta kansa cikin d’akin.. A yayinda hankulansu gaba d’aya yayi kan Giwa dake ambato sunan Sadauki kaman yanda take kiran Mahmood d’in, a daidai wannan lokaci Jamal yai k’ok’arin mik’ewa saman sandarsa Sai ciza labb’a yake sabida azaban da yakeji... Mahmood da idanunsa ke kan Giwa yana ganin halittar data koma Sam bai kula da Jamal ba wanda ya saita almak’ashin yana sakin huci zai cakkawa Mahmood a k’ahon zuciya... Daga nan yanda yake tsaye can bayansu dafe da sandarsa yake fad’i cikin zuciyarsa.. A yau zaka bak’unci lahira Mahmood.. Wannan karaga bazaka tabbata akai ba kaman yanda Ubana Tal’udu ya fad’i a yau zan gajesa zanyi ajalinka nayi ajalin Mulkinka.. Zan cikawa Mahaifiyata burinta sannan na tabbatar da kalaman mahaifina cewa Mulkinka Bazai k’argo ba....! Yana ida tunanin ya saita bakin almak’ashin masu tsananin tsini dai dai saitin k’ahon zuciyar Mahmood yai majajjawa ya jefasu a tare.... SameenaAleeyou 📚 [10/10, 7:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* _(MAY 2021)_ *88* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Yazeed da shi kad’ai ne yake iya hango Jamal da abinda yake k’ok’arin yi... Dan hankalin Mahmood gaba d’aya naga Giwa yayinda Fu’ad da Ja’afar suka bama Jamal d’in baya hakan yasa bazasu iya ganinsa ba...Wani irin k’arfi ne yazo ma Yazeed yai tsalle daga nan saman gadonsa ya isa ya hankad’a Mahmood gefe ya tare masa makamin da Jamal ya jefa masa ai kuwa take guda biyun suka cakki wuyansa suka huda, guda d’aya ya karjesa a k’irji amma babu Wai na wuyan sun huda masa wuya sun b’arka masa mak’ogoro, take ya zube a k’asa jini ya shiga fita daga bakinsa har hancinsa... Mahmood ya tallafosa ya fad’o saman hannunsa yana ambaton sunansa yayinda Giwa Ta k’walla wani irin k’ara tana ambaton sunan Yazeed itama... Ja’afar da Fu’ad a tare suka juya suna duban wanda yayi wannan aika aika wanda target d’insa Mahmood ne... Aiko Jamal yana ganin sun waigo ya shiga jada baya cikin sauri dafe da sandarsa..Mahmood ya shiga fad’I masu cikin tsananin tashin hankali su kira Dr, a d’ari Ja’afar yabi bayan Jamal da tuni ya fice bayan ya shime dogari guda da sandarsa sannan ya cakka ma guda d’aya scissors a wuya... Can Ja’afar ya hango Jamal yana k’ok’arin guduwa Ta k’ofar baya... Cikin wane irin doka kira yace dashi “Jamaaaal..!!” Aiko Jamal yana hango Ja’afar ya k’ara sauri, take Ja’afar ya nad’e hannun rigarsa yabi bayan Jamal a guje... Jakadiya wacce dama tana biye dasu a rakub’e saidai sanin batada ‘yancin shiga d’akin ya sanyata tsayawa daga waje tana ganin abindake faruwa Ta sami zarafin shigowa cikin d’akin itama... Aiko Giwa tana ganinta tace da ita maza ta fitar da ita taga Jamal d’inta kar su kamasa su kashesa... Jakadiya zatai magana Giwa ta katseta da fad’in ta fitar da ita taga Jamal d’inta kar wani abu ya samesa ba k’oshin lafiya bane dashi... Haka Jakadiya ta shiga turo Giwa suka nufo waje... Yazeed da jini ke zuba daga cikin jikinsa kwance yake saman cinyar Mahmood yana so yai magana amma babu hali... Cikin d’igan hawaye Mahmood Ke dubansa yana fad’in “Just hang in there Yazeed... Zaka samu lafiya in sha Allah, Fu’ad yaje kiran Likita yanzu zasu shigo su dubaka... Just stay with me kaji...!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin k’arfafawa Yazeed d’in gwiwa... Daidai lokacin Fu’ad da Dr suka shigo cikin tsananin sauri tare da wasu nurses biye dasu...Fu’ad ya isa ya dafa kan Yazeed yace “Brother zaka sami lafiya In sha Allah...!” Shidai Yazeed bai iya furta masu komai ba Sai dubansu da ido da yake... Sauri sauri Fu’ad ya fice dan ya cimmasu Jamal da Ja’afar.... Dr da nurses suka amshi Yazeed daga hannun Mahmood suna fad’in “We’d take it from here your Highness...!” A hankali Mahmood ya jinjina masu kai kana ya fito waje yana jiran su gama duba Yazeed d’in su fito masa da bayanai, Allah ya gani ko motsawa daga wajen bazai iya ba har Sai yaji a wani hali Yazeed yake... A can waje kuwa Jamal ya haye can k’ololuwar saman wani bene uncompleted building dake a nan cikin asibitin yana duban Ja’afar dake k’ok’arin cimmasa yana lek’a k’asa Dan babu wajen tsira wajen gudu ya k’are... Saidai yayi tsalle ya fad’o k’asa... Ja’afar ya d’anyi surrender hannayensa duka biyu a sama yake fad’in “Don’t Jamal.. Don’t jump, it’s over... Just turn yourself in...!!” Cikin huci Jamal ke fad’in “I rather die than na tsaya na tafi prison ko na zamto bawanka.. Gwara na kashe kaina da na zamto bawanka Ja’afar..!!!” Ja’afar ya jinjina kai a hankali yace “Please don’t Jamal, don’t kill yourself, just surrender now...!” Daidai lokacin Fu’ad ya k’araso saman benen, ya tsaya gefen Ja’afar shima yana duban Jamal dake yunk’urin fad’awa daga saman ginin... Fu’ad ya shiga girgiza kai yana k’ok’arin K’arasowa kusan Jamal d’in yake furta “Please Jamal, don’t, don’t think of doing that...!” Cikin zuban hawaye Jamal Ke dubansa yana fad’in “No Fu’ad... Babu sauran rayuwa a gareni, bazan tsaya na zamto Bawa a gidan dana girma cikinsa matsayin Yarima ba.. Bazan tsaya na kalli matar da nake matuk’ar son kasancewa da ita ta k’are da wancan Bawan ba..!” Ya k’arashe yana nuna Ja’afar lokaci guda yaci gaba da furta “Just take care of Maami please Fu’ad.. Duk abinda tayi tayisu ne sabida mu.. Nida kai da kuma Yazeed.. Bata da kowa sai kai Yanzu, dan Allah ka kula da ita kaji..!” Ya k’arashe cikin zuban hawaye... Fu’ad d’in ma cikin zuban hawaye yake furta “You can still choose to do what’s good Jamal, please don’t kaji..!” Ya k’arashe yana kuma matsowa a hankali yana so ya rik’o Jamal d’in ya hanasa fad’awa.. Sandarsa ya d’ago ya dafe gini kad’an yana nuna Fu’ad da sandar yake fad’in “Don’t come near me Fu’ad idan ba so kake mu fad’a tare ba.. Just stay right there.. Maami still needs you, take care of her kaji.. Tell her I love her, and I do everything for her...! Goodbye Fu’ad... Goodbye brother! Yana ida fad’i haka ya ci gaba da takawa da baya da baya har ya isa k’arshen ginin... Fu’ad ya nufosa a guje yana k’walla kiran sunansa inaaa tuni Jamal ya fad’a da baya... Suna jin sautin k’aran da ya saki alamun wani abu ya sokesa kafin ya k’arasa k’asa... Giwa da k’arasowarsu kenan Ta hangi wannan tashin hankali Jamal d’inta ne Rodin gini ya sokesa ya huda cikinsa... Ta saki wane irin k’ara mai tsananin gaske tana duban wannan tashin hankali... Fu’ad da Ja’far suka k’arasa cikin sauri yanda suka hango Jamal a k’asa k’arfen da ake ginin dashi ya hudasa... A tare sukai saurin rintse idanunsu had’ida dawowa da baya.. Ja’afar yai saurin rungume Fu’ad wanda tuni ya zama out of control sabida ganin wannan kayan tashin hankali da yayi... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Kowa farkonsa ya sani bai San k’arshensa ba.. Ya Allah ka bamu k’arshe mai kyau kasa muyi mutuwa mai kyau ..Ameen..! Yau ga bak’ar zuciya takai Jamal ga kashe kansa, hukuncin wanda ya kashe kansa kuwa babu shi babu rahamar Ubangiji domin ya mutu kafuri ne... A daidai gaban Giwa ya fad’o.. Babu abinda zata iya yi, ko motsawa ta isa garesa bazata iya ba sabida Jamal d’in ya riga ya nakasata da allurar da yaso nakasa Muhibbah dashi.. Haka Giwa tanaji tana gani taga d’anta mafi soyuwa a gareta wanda suke duk wani dirty works d’in tare kwance a k’asa cikin jini, yanda suka halak’a mutane da dama ba tareda wasu nasu sun Iya yin komai ba yau ga Jamal d’inta itama kwance gabanta kuma babu abinda zata iya akai... Rayuwa kenan ka shuka alkhairi domin ka girba mai kyau... A can cikin asibiti ma likitoci sunyi all they could amma da alama lokacin Yazeed ya riga yayi, Jamal yayi sanadiyan mutuwar Yazeed sannan shima ya kashe kansa... Mahmood ya buk’aci ya shiga yaga gawan Yazeed.. Yai tsaye saman kansa hawaye na gangaro masa.. Lokaci guda ya shiga tuno rayuwarsu na baya, sun kasance basa jituwa tsawon rayuwarsu yau sai gashi Yazeed d’in ya sadaukarda rayuwarsa gareshi, sai gashi ya zamto shine mutum na k’arshe da ya gana da Yazeed d’in kafin ya bar duniya.. Take wani irin kuka mai k’arfi yazowa Mahmood, ya kifa kansa gefen Yazeed d’in yana kuka sosai, lokaci guda yake furta “Allah ya yafe maka Yazeed.. Allah ya yafeka Brother..!” Ya k’arashe yana mai dafa tafin hannunsa saman goshin Yazeed... Hankula sun tashi sosai, kan kace mai labari ya isa masarauta.. Wannan kayan tashin hankali da yawa yake, yau babu Yazeed babu Jamal... Innalillahi wa Innalillahi raji’un.. Ya Allah ka bamu jarabawar da zamu iya ci... Idan Kaga Fu’ad dole ne ma ya baka tausayi saidai ko kusa Ja’afar bai bar side d’insa ba tun bayan da abun ya faru.. Kullum Ja’afar na taredashi yana kwantar masa da hankali... Yau kwanaki bakwai kenan da mutuwar Yazeed da kuma Jamal Fu’ad yai sallama ya shigo Babban Gwani... Ya risina ya gaida Mai Martaba... Mahmood yace dashi “Fu’ad an fito..?” Fu’ad ya jinjina masa kai a hankali yace “Eh Rankaidad’e na shirya, flight d’in k’arfe shabiyu na rana ne..” Sarki Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Da kyau..! Mun riga munyi magana da mutanenmu na can Spain d’in komai an gama shirya maka, da zaran ka isa zasu nemeka..” Fu’ad ya risina ya kuma yima Mai Martaba godiya kana ya k’arada “In sha Allah nayi maka alk’awari zan nastu na k’arasa karatuna... In sha Allah..” Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Masha Allah.. Ubangiji yayi jagora, I trust you Fu’ad..! Nasan zaka iya, and zamanka a can zaisa ka d’an mance wasu abubuwan.. I know there’s nothing we can tell you that will ease the pain you’re going through.. So the best solution shine kayi nesa da Masarautar nan na d’an wani lokaci...Just focuss on your studies kaji koh..!” Fu’ad ya jinjina kai a hankali yana amsawa lokaci guda ya k’arada “Dama inason alfarma Your Highness.. Inaso naje na duba Maami a asibiti kafin na wuce..!” Mahmood ya jinjina masa kai a hankali yace “Kafin driver ya wuce da kai airport sai ka tsaya kai mata sallama ko...” Ya jinjina kai a hankali yana mai furta “Godiya nake Rankaidad’e..!” Ya nemi izinin tafiya.. Har ya mik’e ya soma tafiya Mahnood ya ambato sunansa, ya dawo da baya kad’an... “You take care and study hard..!” Mahmood ya fad’i yana duban Fu’ad d’in... A hankali Fu’ad ya saki murmushi had’ida jinjina kai... Lokaci guda yasa kai ya fice fadawa na masa fatan alkhairi.. Mahmood kaw yabi bayansa da kallo har ya b’ace masa zuciyarsa cikeda k’aunan d’anuwan nasa.. Iyakacin gatan da zai masa kenan ya fitar dashi daga wannan environment for the mean time... Fu’ad yana fita ya tadda Ja’afar na jiransa, suka sakar ma juna murmushi suka nufi Mota a tare, Zahra da Umaima dake tsaye daga can saman bene suna hangensu.. Zahra taci gaba da fad’in “He’s my favorite you know.. I feel sorry for him... Ace ga halinda mahaifiyarka ke ciki ‘yanuwanka babu ko guda d’aya.. Jamal ya kashe Yazeed ya kuma kashe kansa wannan tashin hankali da yawa take gwara yayi nesa da wajen nan hakan sai yafi masa sauk’i fiyeda zamansa a nan.. Koda kuwa muna son kasancewarsa a nan tareda mu..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Umaima Ta jinjina kai a hankali idanunta naga su Fu’ad d’in take furta “Yeah.. Zaifi kyau yayi nesa da wannan Masarautar na d’an wani lokaci..!” Daidai lokacin kaman ance Fu’ad ya d’aga kai sama... Ya hangosu tsaye suna dubansa hawaye saman fuskar Zahra... Ya murmusa kad’an had’ida Girgiza mata kai alamun banda kuka, lokaci guda ya d’aga mata babban yatsa cikin salon da suke ma juna.. Ta saki murmushi mai bayyana hak’wara itama tai masa irin yanda yai mata... Umaima da Ja’afar suka murmusa suma kafin Fu’ad yai masu waving suma sukai masa suna masu sakin murmushi had’ida masa fatan alkhairi har suka nufi yanda aka paka hamshak’iyar SUV d’in driver na jiran isowarsu... Dogarai suka bud’e masu motan Ja’afar da Fu’ad suka shige tare Dan har airport Ja’afar d’in yai masa rakiya... Kafin su k’arasa airport d’in saida suka biya yai sallama da Giwa dake asibti tana ci gaba da jinya... Abubuwa goma da ishirin sun taru sun mata yawa Ta wayi gari yau babu kowa nata a tareda ita.. Babu Yazeed babu ‘ya’yan Yazeed sannan babu Jamal ga Fu’ad ma ya tafi nisan duniya wanda bata San ko su sake had’uwa ko ba su sake had’uwa ba... Giwa Ta koma bata kowa bata da komai daga ita sai ko Jakadiya wacce itama a halin yanzu Ta kanta take ba Ta Giwa ba.. Koda aka sallamesu a asibti Basu San yanda zasuje ba Dan basu san yaya zasu kwashe da ahalin Masarauta ba... Ta yaya ma zasu soma shiga cikin Masarautar..? Da wasu idanu zasu dubi ahalin wannan gidan wad’anda suka masu bak’in zalunci a baya... Jakadiya taja Ta tsaya tana haki Dan harga Allah ta gaji da tura Giwa saman wheelchair.. Lokaci guda take furta “Ke Izzatu nifa ba baiwarki bace ki barni najida ciwon jiki dake damuna wanda kece kika jaza min.. Kowa ta kama gabansa cikinmu Dan Allah ya gani bazan iya d’awainiyar Ki ba ehe..!” Giwa na hawaye take furta “Jakadiya ni ce fah Giwa..!” A wulak’ance Jakadiya Ta dubeta kana Ta shek’e da wata irin muguwar dariya tace “Giwa a ina.. Giwa ko b’arauniya.. Kin dai sace sunan asalin Giwa kin rad’a ma kanki.. Nida Ke babu maraba.. Ke har gwara ni na rik’i matsayin Jakadiyar Sarki Ke kuwa Baiwa ce tukuf wacce a cikin bayin ma ina tsamman ke Bakida cikakken asali.. A nan zan barki kema kiyita kanki.. Ai na gama miki mai wuyan tunda na fito dake nan..!” Giwa na hawaye taci gaba da fad’in “Yanzu idan kika barni a nan naje Ina Jakadiya..? Kema babu yanda zakije Don bakida wajen zuwa, kina tunanin Idan kin koma masarauta zasu karb’eki ne.. Jakadiya bamuda Kowa sai mu biyun... Gwara mu taimaki juna..!” Jikin Jakadiya yayi sanyi Dan gaskiya Giwa Ta fad’i basuda kowa sai su biyun.. Lokci guda Jakadiya tace “Toh Ina kike so muje Izzatu.. Tinda dai masarauta yafi k’arfin shigarmu yanzu...” Giwa tace “Haka zamu sad’ad’a mu shiga ta k’ofar bayi mu samu wani waje mu fake tunda duk duniyar nan babu yanda zamuje da ya shige Fadah..” Jakadiya tai shiru sai kuma ta jinjina kai tace “Haka ne Izzatu bamuda wajen zuwa da ya wuce masarauta a yanda kike d’in nan idan na shiga gari dake gudu za’ai gashi ni kaina ba wai lafiya bane ya isheni Tabbas mafaka muke nema a halin yanzu..” Giwa tace “Naji dad’i da kika fahimci haka, yanzu mu San yanda zamuyi mu shige cikin Masarauta koda da dabara ne..” Jakadiya tace “Hakan bazai yuwu ba sai cikin dare lokacin k’afa ya d’auke tinda ta k’ofar Bayi zamu samu mu shige...” Suka tsaida shawari akan cikin dare zasu saci k’afa su shige Masarauta.. Hakan ce ta kasance... Suka saci k’afa suka bi Ta k’ofan Bayi abinka da wanda suka San kan gidan... A wani tsukin d’aki da ya gama rub’ewa ciki babu komai a nan suka samu suka yada zango.. Babu komai cikin d’akin sai wata mutacciyar tabarma.. Haka Jakadiya ta watsar da Giwa saman tabarman... Kafin safiya Giwa ta gama b’ata wajen da k’azanta.. Wanda hakan yasa Jakadiya tashi tana fad’in gaskiya bazata iya rayuwa Inuwa guda da Giwa ba Allah ya gani bazata iya mata jinya ba.. Saidai Ta rub’e a wajen... Giwa na kiran Jakadiya ko sauraronta Jakadiya batayi.. Saidai Jakadiyar na ficewa taga gungun Bayi suna fad’in saidai ta koma cikin d’akin ta fito da Giwa su shige su bar cikin Masarautar dan basu buk’atan annoba taredasu kokuma su had’asu gaba d’aya itada Giwan su cinna masu wuta su ida k’onewa.. Haka babu yanda Jakadiya ta iya ta shiga ta zuba Giwa saman wheelchair d’inta daga ita har k’azantarta, ga wani irin d’oyi da takeyi.. Jakadiya sai toshe hanci take ta fito da Giwa.. Aiko nan gungun Bayin nan suka shiga toshe hanci masu gudun gananin yanda halittar Giwa ya koma nayi... Take yaransu suka shiga jifanta suna kiranta dodanniya... Kan kace mai Bayi sun cika dam a wajen ana kallon abin Al’ajabi yanda Giwa Ta koma.. Muhibbah da Umaima harma da Zahra suna zaune gefen Gimbiya Turai a Fadarta tana basu labarin masarautarsu da d’an uwanta mahaifinsu Sabuwar Jakadiya tai sallama Ta risina ta kwashi gaisuwa.. Yanayinta kad’ai ya tabbatar masu babu lafiya.. Gimbiya Turai tace “Lafiya Jakadiya..? Meke tafe dake..?!” Gaba d’aya su Muhibbah suka zuba mata idanu suna duban yanda take a birkice gaba d’aya.. Lokaci guda Jakadiya Ke fad’in “Allah shi taimakeki cikin Masarauta ne babu lafia...!” Su Umaima suka dubi juna cikeda mamaki, rabonsu da ace cikin Masarauta babu lafiya tun bayan ficewarsu Giwa a Masarautar.. Gimbiya Turai tace “Ina saurarenki Jakadiya.. Meke faruwa cikin masarauta..?!” Jakadiya tace “Allah shi taimakeki Tsohuwar Jakadiya mai murabus tareda Baiwa Izzatu sune a cikin Masarautar nan, gashi can gungun bayi sai jifansu suke dasu da yaransu..!” A tare Su Umaima suka mik’e da jin wannan batu.. Giwa a cikin Masarauta..? Gimbiya Turai taceda Jakadiya ta tsaya su tafi tare.. Jakadiya ta jinjina kai har Gimbiya ta mik’e ta kintsa, su Muhibbah ma suka rufa Alkyabbarsu kana suka nufo bayan Gimbiya Jakadiya na masu jagoranci har suka iso yanda Giwa da tsohuwar Jakadiya suke a wulak’ance sai jifansu yaran Bayi suke suna fad’in basa son dodanniya su fice masu.. Gimbiya Turai tai tsaye tana duban Giwa yayinda Giwar ma ta zuba masu idanu gaba d’ayansu yanda suka jeru gaba gareta cikin shiga irinta masu Mulki.. Ga Gimbiya Turai ga kuma ‘ya’yan Yarima Alfah Muhibbah, Umaima da kuma Zahra..! Mutanen dataso ganinsu a k’ask’ance a wulak’ance, mutanen dataso d’aid’aita rayuwarsu da k’arfin gaske.. Mutane data sace komai daga garesu ta azurta kanta dashi yau gasu nan sun tsaya gabanta bayan duk k’ok’arin da tayi Dan Ta kawar dasu a doron k’asa Ta kafa mulkinta da nata zuri’ar Allah bai nufa ba... Yau ga Turai itace Allah ya nufi nata zuri’ar da samun duka wad’annan abun... Sabuwar Jakadiya tai tsawa ma yaran ta hanasu abinda suke.. Aiko illahirin bayin suna ganin su Gimbiya Turai da kuma matar mai Martaba Gimbiya Muhibbah take suka risina waje yai tsit saima k’ok’arin kwasan gaisuwa da suke.. Gimbiya Turai ta soma takowa gaba ga Giwa tana kallon yanda Allah ya maida Giwa cikin lokaci k’ank’ani.. Izzatu ta zama k’ask’antacciya abun wulak’antawa abun gudu, abin tsoro... Giwa na hawaye take duban Gimbiya Turai.. Lokaci guda ta lumshe idanunta tana furta “Ya Shugabata..! Kimin aikin Gafara, nasan na zalunceki kuma ban cancanci neman afuwa daga gareki ba... Na zalunci kaina kin sakani a inuwa na fitar dake rana.. Kin cireni daga cikin k’angin Bauta kika bani ‘yanci amma na miki butulci.. Kin bani komai naki sarautar Ki harmada abinda yafi soyuwa a gareki Wato mijinki amma na zab’i naci amanarki na rufe idanu sabida son zuciya na miki butulci mafi muni...!” Cikin rawar murya

Chapter 64 of 65