Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
did all that for you, sabida Farin cikinka... I hope abinda zan fad’a maka yanzu zaka yarda dani... Kuma ba Dan na saye zuciyarka ko wani abu mai kamada hakan ba... Zan fad’a maka ne because I care about you... And I love you...!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata cikin yanayi mai ban tausayi.... Ganin yayi K’uri yana dubanta ya sanyata samun daman ci gaba da magana... “Yarima akwai wasu mutane da suke maka k’ulleliya a bayanka, mutanen da suke son ganin downfall d’inka... Ni da idanuna na gansu a asibiti sanda naje duba Baba Wambai, su biyu d’in basa jituwa sam amma da na gansu a tare nasha mamaki..!” Katseta yai cikin kakkausar murya da fad’in “Raheema...! Mai kike son cewa, just spell it out once and for all, su waye kike magana akai...!!” Jinjina kanta tai a hankali kana tace “It’s your brother Yazeed and Majidad’i... I saw the of them together, they were conspiring against you... Naji da kunnuwana suna cewa zasu kaika k’asa by every means...!” Ta k’arashe tana zaro idanu waje had’ida jinina kai alamun tattabatarwa.... Tinda ta soma magana yake dubanta ba tareda ya janye idanunsa ba, ga wani irin gumi dake tsartsafowa daga goshinsa, take idanunsa suka kad’a sukai jazir haka nan fatar jikinsa, kana iya hango yanda yake sakin huci cikin wane irin yanayi... Idanun Raheema suka sauk’a kan hannayensa da tuni ya damk’esu jijiyoyin sunyi rud’u rud’u... Baiso ya yarda da zancen Raheema Dan shi ba mutum ne mai d’aukan magana haka kurum ba tareda k’wakk’waran hujja ba... Amma bayan abinda ya faru yanzu a Zauren taro baijin akwai sauran hujja da yake nema... Bai kuma furta komai ba sai ficewa da yai kaman zai tashi sama... Jamal da Fu’ad dake tafe haraban Masarautar hango Yayan nasu a haka yasa suka dubi juna... Fu’ad yaceda Jamal meke faruwa..? Girgiza kai kurum Jamal yai alamun shima bai sani ba.... Fu’ad yace “Mu k’arasa muji...!” Babu musu Jamal ya jinjina masa kai sukabi bayan Mahmood...! ** Giwa na tsaye gaban Yazeed tana ci gaba da sakin huci take furta “Har abada muddin Yayanka na raye bazakai saurata shi ya rasa ba Yazeed... Yazeed mai kake so ka zama..? Shin maiyasa kake neman ka raba kan ahalinmu...! Yazeed ka d’ago idanu ka dubeni ka sanar dani dik abinda Ubandoma ya fad’i k’arya ne kai ka tsara masa Mahmood bazai aikata haka ba..!!” Giwa bata rufe baki ba Mahmood ya banko k’ofa ya shigo cikin yanayin da basu tab’a ganinsa ciki ba... Jajayen idanunsa masu cikeda b’acin rai ya sauk’e kan Yazeed kan kace mai yayi tsalle ya cakumo wuyan Yazeed ya masa wani irin damk’a da duka k’arfinda Allah ya huwace masa.... Cikin kakkausar murya mai firgitarwa yake furta “I have warned you time without numbers... Do not cross me Yazeed... Now tell me what’s your role in all this..! Talk to me Yazeed..! Talk...!!!” Ya k’arashe yana kuma jijiga Yazeed da iyaka k’arfinsa... Giwa da gaba d’aya duniyar ta juye mata ga wane irin rawa da illahirin jikinta keyi, gaba d’aya ta kasa furta komai sai wane irin karkarwa jikinta keyi... Daidai nan su Jamal da Fu’ad suka shigo... A d’ari Jamal ya isa garesu yana k’ok’arin janye Mahmood yake calming d’insa amma inaa tamkar baiji saida matse Yazeed yake yana wane irin huci... Tuni idanun Yazeed sun furfito waje tamkar an matse mage a buhu.... Giwa cikin rawar murya mai cikeda firgici had’ida tashin hankali take furta “Mahmood kar ka kashe d’an uwanka... Ka sakar masa wuya, ka bashi dama yayi bayani...!” Bai sakesa ba sai jijiyoyin jikinsa dake kuma fitowa rud’u rud’u... Dik iyaka k’ok’arin Jamal da Fu’ad wajen janye Mahmood sun kasa, koda wasa basu tab’a ganin wannan side d’in nasa ba basu tab’a sanin cewa yanada zuciya har haka ba... Har saida Giwa ta fashe da kuka tana janye Mahmood tana fad’in idan zai iya kashe d’anuwansa Yazeed Toh itama kawai ya shak’e mata wuya ya fara da ita.... A hankali yake sassauta rik’onda yayiwa Yazeed har ya cikasa gaba d’aya... Yazeed ya zube gefe yana haki sosai had’ida gumin azaba... SameenaAleeyou📚 [8/9, 11:27 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *42* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* D’agowa Yarima Mahmood yai ya dubi Giwa na d’an wani lokaci kana ya furta “Kiyi hak’uri Maami... I’m sorry...!” Daga haka waigowa ya kumayi yana aika muguwar kallo wa Yazeed da har yanzu bai iya mik’ewa ba... Bai kuma cewa komai ba ya fice daga sashen gaba d’aya.... Jamal yai saurin k’arasawaga mahaifiyarsa ya taimaka mata ta suka shige d’aki yana mai k’ok’arin calming d’inta... Parlorn ya rage saura Fu’ad da Yazeed.. Fu’ad kaw girgiza kai kurum yai yana duban Yazeed “Wannan shine abinda nake jiye maka Yazeed, raininka da wulak’ancinka ya soma yawa...!” Katsetsa Yazeed yai da fad’in “Don’t you dare lecture me you idiot... Kaje ka sami wancan mahaukacin Yayan naka shi yake buk’atan lecture sama dani tinda cikin mu biyun shine criminal, ya kashe Wambai tareda taimakon Hadiminsa sannan ya zago yana so ya kashe Hadimin nasa before he rats him out... Kuma Wllhi abinda yayi mun baici banza ba sai na koya masa hankali... No one messes with Prince Yazeed AbdulJabbar..!” Ya k’arashe yana sakin huci da haki had’ida sosa wuyarsa da tuni fatan tayi jazir... Sai yanzu Fu’ad ya fahimci meke faruwa... Gajeren murmushi yai yace “Kafi kowa sanin cewa zancen da kake babban k’arya ne Yazeed, ko ka mance cewa cikin dukanmu hud’u shine ba criminal ba... The three of us are criminals, we are the criminals Yazeed, You Jamal and I...Kuma cikinmu gaba d’aya shi kad’ai ya cancanci zama Sarki sabida ba’a Sarki criminal...!” Katsesa Yazeed yai da fad’in “Shut up! Just Shut the hell up Fu’ad... Kai mahaukaci ne k’waya ya gama illata maka kwanya... Baka da sauran amfani Fu’ad, dakai da babu a Masarautar nan duk d’aya ne... Kai gwara ace babu kaima at least bazaka dinga jawo mana abun kunya da wannan haukar Naka ba wanda bakada ranan warkewa...!” K’walla masu zafi suka ciko idanun Fu’ad lokaci guda... Ya shiga dunk’ule hannayensa sabida tsananin b’acin rai... Yazeed kuwa abinda yakeso kenan yai provoking d’insa, take ya saki shu’umin murmushin nan nasa da gefen baki... Ya mik’e tsaye da k’yar ya matso dab gaba Fu’ad saitin kunnensa yake rad’a masa... “You’re useless Fu’ad, bakada amfani... Babu wanda yake sonka sabida kai psychopath ne, ko budurwar da kake mutuwar so ka kasa samun amincewarta Fu’ad... You’re nothing but a failure Fu’ad...! Just accept the fact bazaka tab’a birge kowa ba Fu’ad... Not even your Criminal brother Mahmood..!!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi had’ida d’an buga kafad’an Fu’ad d’in... Bai kuma tsayawa sauraren kowa ba yasa kai zai fice yana mai ci gaba da sosa wuyarsa... Fu’ad dake tsananin huci hannu yasa ya damk’o hannun Yazeed ya dawo dashi baya... Su duka biyun sukai tsaye suna duban juna... Fu’ad ne ya soma sakar masa murmushi kana yace “You’re a loser Yazeed...! Sarautar da kake so bazaka tab’a samu ba, kanaji kana gani Yaya zai d’ale Karagar nan... Kuma kasan maiyasa na kiraka da loser...” Ya murmusa kad’an kana yaci gaba da fad’in “Sabida dik abinda ka sa gaba baka samun nasara... How about our bet... Nasan maybe ka mance sabida ta yab’a maka magana ta ajeka a yanda ya kamaceka... Kuma kasan menene zaifi maka ciwo Prince Yazeed... Ni da ita d’in masoya ne, she chose that psychopath over you...you lost to me Yazeed and too bad kana cikin Masarautar nan zakaga aurenmu... To cut it short, Na d’agaka na bugaka da k’asa a wannan wasan kaman yanda Yaya zai kuma bugaka da k’asa a wasanka dashi... So now tell me Yazeed AbdulJabbar... Among the two of us who’s a failure..?!” Ya k’arashe yana mai sakar masa murmushi da gefen baki... Yazeed yaci gaba da tururi yana aikawa Yazeed muguwar kallo... Hannu ya d’aga zai kai masa mari “How dare you Fu’ad!!” Fu’ad ya damk’e hannun nasa shima cikin huci yake furta “Kada ka kuskura ka sake kwatanta wannan kuskuren dani Yazeed... If not...!” Ya murmusa kad’an sai kuma ya saki hannun Yazeed d’in ya fice gaba d’aya daga parlorn.... Yana ficewa Yazeed yasa kai ya fice cikin sassarfa zuciyarsa naci gaba da k’una.... Zuhra na ganinsa haka tai saurin sallaman kuyanginta tana mai k’arasawa garesa cikin tsananin tashin hankali... “Prince lafiya... Mai ya faru dakai..?!” Ta k’arashe tana mai rik’e baki ganin wuyansa yayi shati kaman ya tara jini.. Bai amsata ba hasalima kota kanta baibi ba yayi hayewarsa sama, sai sakin fuci yake, gaba d’aya zuciyarsa a jagule take... Haushin komai da kowa yake, Zuhra ta turo k’ofa ta shigo cikin sand’a kaman mai tsoron kada ta tada jariri mai bacci... Ta saci dubansa kad’an ta d’an had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’oshi tana yunk’urin k’arasawa gareshi da zummar duba ciwonsa... Cikin k’arfin hali Ta d’an fuzar da fuci a hankali kana ta nufi yanda yake tana k’ok’arin massaging wuyarsa da towel... Cikin daka tsawa yace da ita “Get out..! Tashi ki fita nace bana buk’atar kulawarki...!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci.. Jiki a matuk’ar sanyaye Zuhra ta mik’e ta fice hawaye masu d’umi na gangaro mata.... Tsaki ya buga tana ficewa ya maida k’ofan ya rufe yana ci gaba da fuzar da huci mai tsananin tururi... Yana sosa wuyarsa yanda Mahmood ya shak’esa kalaman Fu’ad na dawowa kwanyarsa.. Wato Muhibbah take ko waye ta sanar da Fu’ad kalan wulak’ancinda ta masa, Yana nan yana faman famkam famkam Fu’ad na masa kallan k’ask’antacce wanda mace Ta yarfa... How dare she..! Wllhi sai ya koya mata hankali, this isn’t over, in fact is far from over... He must teach her a lesson, a very good one...! Babu macen data kai ta wulak’anta Prince Yazeed AbdulJabbar....! Ya k’arashe tinanin fuskan mutum biyu da yafi tsana na masa gizo cikin idanunsa, Mahmood da kuma Muhibbah.... A b’angaren Zuhra kuwa tana fita parlor ta tadda Raheema ta shigo, ganinta haka ya tabbatarwa Raheema cewa plan d’inta yayi aiki tasan Mahmood ya confronting Yazeed ko babu komai tasan yanzu Mahmood zai soma yarda da ita.... Tai saurin k’arasawa fuska fal damuwa ta kamo Zuhra tana tambayarta meke faruwa.... Zuhra bata iya cewa komai ba saima kukan da take k’ok’arin dannewa ne ya kufce mata.... Cikin nuna kulawa Raheema ta kamota suka zauna saman kujera tana k’ok’arin comforting d’inta... Lokaci guda san jin meke faruwa da Zuhran... ** A b’angaren Fu’ad gaba d’aya yinin ranan yinta yai yana tinanin abinda su kaiwa wa yarinyar shekarun baya... Yana so ya mance komai ya soma Sabon rayuwa musamman da yanzu Muhibbah ta shigo cikin rayuwarsa saidai baijin zai iya yin hakan sabida Shi kanshi baijin zai iya yafewa kansa balle ita yarinyar da suka zalunta da ahalinta... Fu’ad ya dafe kansa dake tsananin sara masa had’ida rintse idanunsa, lokaci guda yake furta “No no no I don’t want to Yazeed...! Just let me go... I don’t want to do it....!” K’ara ya kuma sakewa shi k’ad’ai yana mai watsi da k’wayoyin dake cikin tafin hannunsa yake furtawa da k’arfi “Just leave me alone... Please leave me alone, bana son yin abinda kuke umartana... Just leave me alone.. Leave me alone..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai tak’urewa can k’arshen gado... Yanda Fu’ad yaga rana haka yaga dare, gaba d’aya tashin hankalin ya dawo masa Sabo tamkar mai tab’in hankali haka ya dinga yin abubuwa.... Gaba d’aya Masarautar ma abubuwa sun kuma tab’arb’arewa, a b’angaren Waziri da Giwa basuyi k’asa a gwiwa ba dan koda wasa bazasu bari Yazeed ya soma d’alewa Karagar nan ba maganar Tal’udu ya tabbata kaman yanda ya sanar dasu cikin yaran Sarkin duk wanda ya soma zama Sarki shine gawan fari don fitilar tsafi ta hasko masa mutuwa a Masarautar... Tuni sun samo mafita yanda Waziri ya tafi asibiti cikin shiga na b’adda kamanni tufafi irinta bayin Masarautar mata ya saka sannan ya d’auki farantin abinci tamkar wanda zaikaiwa fursunan abinci yanda babu mai zarginsa.... Yana shigewa d’akinda Ubandoma Ke kwance ya maida k’ofa ya rufe... Ubandoma yai k’uri ganin ba likita bane ya shigo.... Yai Saurin mik’ewa ganin mutumin da yai shiga irinta mata na kuma nufosa... Kafin yai yunk’urin gudu Waziri ya damk’osa ya yaye mayafin daya rufe fuskarsa dashi... Zuciyar Ubandoma ya tsinke ganin Waziri ne... Waziri ya sakar masa murmushi yana mai furtawa cikin sigan rad’a “Kwantar da hankalinka Ubandoma bakada wajen gudu... Kuma idan har kanaso ka tsira da rayuwarka data iyalanka toh kayi yanda nace..!” Ya k’arashe yana sakarwa Ubandoma murmushi mai muni.... Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana mai furta “Waziri kamin rai dan Allah kada ka kasheni ko ‘ya’yana wllhi Yarima Yazeed ne ya tilasta min fad’in duk abubuwan dana fad’a a Masarauta... Amma ko kad’an babu hannun Mahmood cikin abinda nayi, hasalima na sinkayo tattaunawarku da Giwa ne cewa akwai abinda kuke nema gidan Wambai ni kuma naga abinda nada matuk’ar mahimmanci wajenku sannan idan na rigaka samo abin watak’ila Giwa ta ‘yantani na sami ‘yanci na bar bauta abinda na jima Ina burin mallaka tsawon rayuwata... Kaji dalilina Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe jiki na matuk’ar rawa... Waziri ya saki wata bazawar murmushi yace “Shege Ubandoma... Ni dama nasan za’a aika... Wato ki gaka mai wayo koh... Haba Ubandoma kana bawa yaushe har zakai tunanin kaid’in shirinka zai aiki akan namu... Toh kana jina...” Ubandoma yai saurin jinjina kai alamun eh.... Waziri yaci gaba da fad’in “Zan k’yale wannan ya shige Ubandoma amma da sharad’in zaka k’aryata abinda ka fad’i gaban Masarauta... Zaka sanar da Masarauta cewa Yazeed ne ya tilasta maka fad’in hakan Ka fahimta...!” Ubandoma yai saurin jinjina kai sai kuma ya d’anyi jim tamkar yana tuna wani abin... Waziri yace “Ya naga kayi shiru..?” Ubandoma ya muskuta kad’an yace “Toh Yarima Yazeed fah Rankashidad’e kasan halinsa idan na janye abinda na fad’i gameda Yarima Mahmood hakan ka iya janyo min matsala wajen Yarima Yazeed..!” Ya k’arashe fuska fal damuwa... Waziri yace “Bakada matsala Ubandoma Yazeed bazai maka komai ba ina mai tabbatar maka... Kaidai kawai kayi yanda na umarceka...!” Ubandoma ya jinjina kai cikeda girmamawa yana mai tabbatarwa Wazir cewa zai yanda yace.... ** Yazeed ya gama tunanin Ta yanda zai b’ullowa Mahmood ya d’auki Fansarsa, ya saki murmushin nan nasa a hankali had’ida furta “His daughter... Itace weakness d’in Mahmood kuma da ita zai amfani ya tarwatsa Mahmood... Lokaci guda ya mik’e ya fice daga sashen nasa... Zuhra na hango fitarsa ta window ta lumshe idanunta tanai masa addu’an shiriya cikin zuciyarta... ** Zahra Ta ida shirin baccinta kenan taji ana knocking a k’ofarta... D’an jim tai tana duba time kafin ta saki murmushi dan tasan bazai wuce Paa d’inta ba tinda yau d’in duka basu had’u ba ta dubashi a sashensa da duk yanda take tinani cikin Masarautar zata sameshi bata sameshi ba... Tasan bazai iya bacci bai ganta ba, cikin sauri ta isa k’ofa ta bud’e tana mai furta “I thought yau bazan ganka ba Paa...!” Birki tai ganin Uncle Yazeed tsaye bakin k’ofar cikin wane irin yanayi... “Uncle.. Lafiya...?!” Ta tambaya tana dubansa fuska d’aukeda damuwa... Yazeed ya sakar mata murmushi mai kyau yace “Princess... Aren’t you gonna let your Uncle in....?” Cikin sauri ta matsa gefe ta basa hanya tana mai furta “Sorry Uncle... Please come in...!” Yazeed ya kuma sakar mata murmushi kana yasa kai ya shigo... Yana tafe ne Zahra ta hango wuyansa yayi shati jajazir kaman ciwo.... Ta taresa da fad’in “Uncle wait... What happened to you... Mai ya sameka..?” Ta k’arashe cikeda kulawa.... Yazeed ya d’an shafi wuyansa yace “Oh this...” Yai maganar yana mai zama saman doguwar kujera dake cikin d’akin lokaci guda Zahra ta K’araso ta zauna gefensa duk ta damu da ciwon da ta gani wuyarsa... Yana mai sosa wuyan yake ci gaba da fad’in “Someone tried to kill me Zahra...!” Yai maganar yana mai duban cikin idanun yarinyar... Ta zaro idanu waje “Kasheka Uncle... Waye kenan... Maiyasa ba’a kamashi ba... Whoever did this to you needs to pay Uncle..!” Ya murmusa kad’an yace “You think so..?!” Zahra tace “Haka ne ya kamata Uncle...” Yazeed ya fuzar da fuci kad’an sai kuma yace “Zahra’u mai kike tunani a duniyar da babu adalci..? Mai kike tunani a Masarauta mai cikeda azzalumai wanda suka d’auki kashe rai ba komai ba...?!” Kalamanta sunyi mata nauyi, gaba d’aya kwanyarta sai yana neman juyawa, lokaci guda tunanin mutuwar mahaifiyarta yazo mata, k’walla suka ciko idanunta.... Cikin rawar murya take furta “Uncle bana son rayuwa a irin wannan Masarautar... What if... What if this kingdom is cursed... I lost my Maama here... Bana so na sake rasa wani cikin iyayena Uncle what’s wrong with this palace...?” Janyota yai ya rungumeta yana lallashinta lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Kar ki damu Princess, that won’t happen kinji koh... Amma inaso kisan waye yamin wannan abun Princess...” Ta d’ago tana dubansa had’ida share hawayen idanunta “Uncle who attempted to kill you..?” Yazeed ya tsareta da idanu lokaci guda ya furta “Your Father... My brother did this to me... Akan mulki komai za’a iyayi a Masarautar nan.... Mahaifinki kuma d’anuwana da muka fito ciki d’aya shi yayi min haka Zahra...!” Ya k’arashe babu alamun wasa a tattaredashi... Take Zahra ta mik’e cikeda tsoro tana girgiza kai take furta “No...no Uncle You must’ve got that wrong... My Paa can never do something like that... Please Uncle tell me it isn’t true... Dan Allah kace min ba gaskiya bane.. Not my Paa please...!” Ta k’arashe cikin shesshek’an kuka.. Yazeed ya mik’e tsaye ya kamo hannunta had’ida furta “Unfortunately Zahra... It’s the truth... Your Father is not what you think he is... He’s capable of the worse akan Mulki...!” Ya k’arashe yana mai kuma jaddada kalamansa.... K’ara Zahra ta saki had’ida zubewa wajen daidai lokacinda Mahmood ya banko k’ofa ya shigo... Hankali tashe yai kan Zahra yana ambato sunanta yana jijjigata...Lokaci guda ya mik’e ya cakumo Yazeed yana jijjigasa yake furta “What did you do to my daughter... Ka fad’a min Yazeed mai kaiwa d’iyata....Yazeeed!!” Ya k’arashe yana mai kuma jijjigasa... Yazeed bai daina sakin murmushi ba yake furta “I didn’t do anything to your precious princess Your Highness.. But you did.. Kai ka jefata a condition d’in da take ciki Rankaidad’e..!” Mahmood yana tsananin huci yake furta “Yazeed don’t involve my daughter...I’m warning you...!!” Yazeed ya murmusa yana mai furta “Zaka kasheni ne... Banji mamaki ba Your Highness tinda kayi attempting hakan....!!” Cikin tsananin huci Mahmood ya dunk’ule hannunsa yana k’ok’arin kaiwa Yazeed naushi Zahra ta mik’e ta tare Yazeed tana mai girgiza kai take furta “Why Paa... Why...? I’m disappointed Paa... Totally disappointed..!!” Tana ida fad’in haka ta fice a guje tana mai ci gaba da kuka... Mahmood yabi bayanta yana k’walla mata kira inaa ko juyawa batayi... Zahra bata zarce ko ina ba sai masauk’in Muhibbah.... SameenaAleeyou 📚 [8/11, 10:09 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *43* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Bacci ya soma d’aukanta sanda ta jiyo sautin kuka ana bubbuga mata k’ofa... Ta mik’e zumbur tana k’ok’arin danna side lamp, wayarta ta janyo ta duba time tana mamakin waye wannan mai buga mata k’ofa a daidai irin wannan lokacin gashi kuma kukan kaman k’aruwa yake... Jin muryar Zahra na ambato sunanta ya sanyata saurin mik’ewa ta janyo hijab ta zira kana ta nufo parlor... Tana bud’e k’ofar kuwa Zahra batai wata wata ba ta fad’o cikin jikinta tana kuka sosai... Mamaki had’ida tsoro suka kama Muhibbah.... Toh lafiya... Meke faruwa...? Tai tambayar cikin zuciyarta, tana nan tsaye tamkar statue ta hango Yarima Mahmood na K’arasowa cikin tafiya da yafi kama da sassarfa.... “Zahra please, sweetheart listen to me...!” Bai rufe baki ba Ta d’ago fuskarta dake jik’e sharkaf da hawaye tana girgiza kai alamun a’a take fad’in “Just go away Paa... I don’t want to see you..!” Ta k’arashe maganar tana mai fad’awa bedroom d’in Muhibbah a guje ta maida k’ofan ta kulle.... Yarima Mahmood ya lumshe gajiyayyun idanunsa a hankali had’ida fuzar da huci mai d’umin gaske.... Muhibbah dai kallon ikon Allah kurum take tana mamakin Toh mai ya had’a d’iya da mahaifin har haka.... Ta d’anyi gyaran murya ganin har wannan lokacin ya kasa bud’e idanunsa “Your Highness... Lafiya, meke faruwa...?!” Sai sannan Mahmood ya ware idanunsa ya sauk’esu saman fusarta, ya d’an kwashi dak’ik’ai yana dubanta kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Please take care of my daughter...!” Daga haka bai kuma cewa komai ba saima sa kai da yai ya fice daga sashen gaba d’aya... Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya b’acewa ganinta kana Ta nufi k’ofan d’aki tana k’wank’wasawa... Da fari Zahra k’in bud’ewa tai har saida tace mata itace kuma Paa d’in ya tafi sannan Zahra ta bud’e mata.... Tana bud’ewa ta kuma komawa ta zauna bakin gado tana mai ci gaba da matsan k’walla... Gefe da ita Muhibbah ta zauna ba tareda tace komai ba tana sauraron yanda yarinyar ke kuka a hankali, bayan shud’ewan mintoci k’alilan Muhibbah ta kaikaito tana dubanta, lokaci guda ta d’aura hannunta guda saman na Zahra... Zahra ta d’ago kod’add’un idanunta tana duban Muhibban... Murmushi ta sakar mata mai sanyin gaske “Kina buk’atan wani abu...?” Girgiza mata kai tai alamun a’a... Muhibbah Ta jinjina kai tace “Alright, ki kwanta ki huta haka nan is late already kinji koh...!” Bud’e bakin Zahra sai cewa tai “I’ll never forgive him... Ever, wllhi na tsaneshi, Wannan shine abinda yake b’oye min... Na tabbata da saka hannunsa a mutuwar mahaifiyata... If he can kill his own brother da suka fito ciki guda ko shakka babu zai kashe mahaifiyata dik akan banzan Mulkin duniya da bazaka tabbata kanayi ba...!” Kuka yaci k’arfinta.... Sauk’e ajiyan zuciya Muhibbah tai a hankali tace “A duniyar da adalci yayi k’aranci babu abinda ba za’ayi ba Zahra... A duniyar da son mulki da neman dukiya tako wane irin hanya yayi k’amari babu abinda baza’ayi ba... Ana kashe rayuwa domin a cimma wani buri na duniya... Shi d’an adam mai yawan zalinci ne kuma mai yawan bijire maI yawan bijire ma rahamar Ubangijinsa ne... Amma maiyasa kike danganta mahaifinki da munanan laifuka irin wannan...?!” Dubanta Zahra tai hawaye na gangaro mata “Sabida yau d’in ni ganauce ba jiyau ba... Mahaifina ya tasamma kashe Uncle Yazeed akan rikicin mulki... Idan baki manta ba na tab’a sanar dake inaji a jikina yana b’oye min wani abu gameda mahaifiyata wanda baya so na sani... Ko shakka banayi abu ne da ya shafi mutuwarta.. A ido mahaifina yafi kowa kyawawan d’abi’u cikin gidan nan ashe a zuciya yafi kowa munin halayya.... Ya cuceni ya zalunceni ya rabani da mahaifiyata...!” Ta k’arashe ciki shesshek’an kuka... Rungumeta Muhibbah tai cikeda tausayawa lokaci guda cikin kwantar da hankali take fad’in “Wasu lokutan mukanyi mummunan zato ga mutanen kirki kaman yanda wasu lokutan mukanyi kyakkyawan zato ga mutanen da ba na K’warai ba, amma a koda yaushe ana so mutum ya kasance mai kyautata zato tsakanin al’umma... Shi munana zato bazai kaika ga komai ba face tarin dana sani da kuma zunubi mai girma... Zahra shin kina zaton shi Uncle d’in naki mutumin k’warai ne...?!” Tai tambayar tana mai tsare yarinyar da idanu... Dubanta Zahra tai had’ida jinjina kai alamun eh... Muhibbah ta jinjina kai tace “Da kyau da kikai masa zato mai kyau... Toh inaso kiyi haka ga mahaifinki, ki kyautata masa zato... Kince rikicin mulki suke shiyasa kike ganin mahaifinki shine bad guy a nan koh... Tsawon shekarun da kikai da mahaifinki kin tab’a shakkun kyawawan d’abi’unsa a baya...?!” Zahra tai saurin girgiza kai alamun a’a... Muhibbah taci gaba da fad’in “Ya tab’a aibataki ko mahaifiyarki a gaban idonki kokuma kiji labari...?!” Nanma girgiza kai Zahra tai alamun a’a... “Kin tab’a jin labarin yaci zarafin wasu mutane tun kuna k’asar Spain har kawo dawowarku Nigeria...?!” Naman Ta girgiza kai alamun a’a cikin matuk’ar sanyin jiki... Muhibbah Ta sauk’e ajiyan zuciya tace “SARAUTA...! Sai akan sarauta kike zaton zai aikata abubuwan da ya aikata koh...?!” Tai saurin jinjina kai alamun amincewa... Muhibbah ma Ta jinjina kai a hankali kana tace “Toh kisa a ranki cewa rikici na mulki ne tsakanin mahaifinki da d’an uwansa... Amma kar Ki tab’a kokonton k’irkin mahaifinki kinji koh...!” Tai k’uriwa Muhibbah tana dubanta, lokaci guda Ta jinjina mata kai a hankali sai kuma tace “Toh ta yaya zan cire kokonton abinda yake b’oye min gameda mahaifiyata Tia.... I really want to know what he’s hiding...!” Muhibbah tai mata K’uri na wasu ‘yan dak’ik’ai kana tai gajeren murmushi tace “It’s simple Zahra.... Kinaso mahaifinki ya sanar dake abinda yake b’oye miki ba tareda wani kwana kwana ba...!” Yarinyar tai saurin jinjina kai alamun eh... Muhibbah ta jinjina kai tace “You ask him in public... Ki tambayesa a

Chapter 26 of 65