Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zaizo ya kula dakai, Allah ya baka lafiya kaji k’anina...!” Jamal ya jinjina masa kai yana mai dubansa cikeda so da k’auna, ya rik’o hannunsa kad’an yace “Thank you Yaya..!” Murmushi Mahmood ya sakar masa had’ida shafa sumar kansa kad’an kana yasa kai ya fice Giwa na biye dashi tamkar tayita kurma ihu haka take ji ko zata sami sanyin rad’ad’in da zuciyarta Ke mata... Suna tafe take ceda Mahmood “Ina Fu’ad d’in... Oh ni Turai naga ta kaina wannan wane irin al’amari ne Ke faruwa da ahalina...?!” Mahmood ya rik’ota kad’an yace “Maami ki kwantar da hankalinki, Fu’ad yana ER and he’s out of danger now... Turaki yana can wajensa taking care of everything...!” Giwa na hawaye take duban Mahmood tace “Shi kuma mai ya sameshi...?!” “Drug overdose...!” Ta kuma rintse idanunta tana wasu hawayen na zubo mata tashin hankali daga wannan sai wancan... Mahmood yaima Jakadiya alama da hannu tazo... Ta k’araso cikeda risinawa.. Nan yace Ta kula da Giwa zai k’arasa ya sami Likita... Babu musu Jakadiya Ta k’arasa wajen Uwargijiyar tata wacce ta koma tamkar wata abin misali cikin k’ank’anin lokaci... Tabbas Mulkin duniya ba komai bane, take Allah yake sauya al’amaransa ya maida bawa ba koman komai ba ya nuna masa kasawarsa da kasawar duk wani mulki da dukiya nasa... Bawa yabi Allah shine tsiransa, kada Allah ya jarabceka da d’an wani k’ank’ani mulki na duniya ko k’ank’anin arziki da zai gushe ka zata ka samu duk wani power da kake nema a duniya kuma zaka iya takawa kowa yanzu sai ya karb’e komai ya kuma maidaka ba kowa ba dan shid’in shi kad’aine mai dawammamen mulki da baida farko baida k’arshe... Ya Allah kada ka jarabcemu da bijire ma rahamarka garemu..Ameen! A d’an tsakanin wannan lokaci idan Kaga Giwa dole ta baka tausayi, gaba d’aya Ta fice a hayyacinta Ta koma tamkar ba ita ba, yaranta har guda biyu kwance asibiti, duk San mulki irin na Giwa wanda k’asa ma da k’yar take takawa sabida Izza sai Gata nan tana taka k’asar asibiti cikin sanyin jiki da karb’an umarni daga wajen likitoci... Idan da ace Tanada sauran rabo tabbas zata fahimci darasi cikin abubuwan dake faruwa da ita... Har kawo zuwa dare Fu’ad yana kwance unconscious bai farfad’o ba baisan yanda kansa yake ba, koda ace ya farfad’o su kansu likitocin basusan da mai zai farka ba, hauka ne kokuwa akasinta... Hakan yasa suka sanar da family d’in Fu’ad they should be ready for anything dan komai ka iya faruwa... ** MASARAUTA Sassafe ta ida shirinta tsaf da zummar barin gari, saidai ji tai bazata iya tafiya bata duba halinda Zahran Ke ciki ba, Ta mik’e ta nufi b’angaren Giwa yanda ta tadda Zahran da Umaima na shirin fita zuwa asibiti duba Jamal da kuma Fu’ad... A nan ne suke sanar da ita abinda ya sami yaran Sarkin... Harga Allah bayan abubuwan da sukai mata itada ahalinta zata iya cewa ko gizau bataji tausayinsu ba hasalima ma abinda ya cancancesu suka samu... Umaima ta dafata kad’an tace “Ni kad’ai nasan labarin soyayyarku da Fu’ad, are you sure bazakije ki ganshi ba...?!” Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali kana tace “Zanso hakan Umaima amma saidai nima kiran gaggawa na samu daga gida Mummy na asibiti ba lafiya tin daren jiya... Idan kinje ki gaisar min da Fu’ad... Harmada Jamal d’in...!” Shiru Umaima ta d’anyi tana karantar yanayinta kana ta jinjina kai tace “Tace shikenan, zan fad’i sak’onki, kuma nima ki gaisar min da Mummy da kyau, kice ina mata fatan samun lafiya...!” Ta jinjina kai a hankali tana murmusawa... Zahra ta k’araso sukai K’uri suna duban juna... Lokaci guda ta isa ta rungumeta tace “Tia ki gaishe da Mummynki, kuma idan kinje please ki had’amu a wayar na gaisheta...!” Muhibbah ta jinjina mata kai a hankali kana ta Shafa kan yarinyar kad’an tace “Kiyi kaman yanda Nace miki jiya, apologize to your Paa kinji... Kinga dai abubuwan dake faruwa cikin Masarautar nan, your Paa is going through a lot Zahra... Please don’t add to his problems kinji... Try to be more understanding with him... Baya buk’atan tashin hankali daga gareki a halinda yake ciki yanzu...!” K’uri Zahra tai mata sai kuma ta girgiza kai alamun k’in amincewa tace “That has nothing to do da amsoshin da nake nema daga wajen Paa.. I won’t stop har sai ya sanar dani...!” Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa, tabbas tasan tank’waro Zahra ba abu bane mai sauk’i... Murmuahin da yafi kama da yak’e ta sakar mata kana ta kuma masu sallama... Umaima tace ta bari su fita tare ko ma a kaita gida a motar masarauta.. Fir Muhibbah tak’i hakan hasalima sauri sauri ta fice daga Masarautar... Tana tafe tana neman abin hawa ya hangeta, tinda ya fice daga Masarautar jiya bai dawo ba, hasalima watsewarsa ya gama a club sai yanzu ya nufo gida dan jin yanda al’amra suka kwana... Yana hangota ya saki murmushin nasa yana mai shafa hab’a... Lokacin da yake jira, dama itama shak’e yake da ita... Kaf takaicinsa zai sauk’esu ne akanta Ta yanda gobe ko mai irin sunansa taji zata basa Girma...! Ya k’arashe tinanin nasa yana karya kan Mota... Tana tsaye bakin kwaltar da babu mutane sosai babu ababen hawa saman kwalta saiko jifa jifa abinka da hanyar da ba’a faye bi ba.... Kaman daga sama taga bak’ar G-wagon taja ta tsaya gabanta, haka kurum taji bata aminta da motar ba dan tasan ba motar k’anan mutane bane, idanunta suka sauk’a kan plate number na motar aiko nan Ta hango Prince Zeed rubuce jiki... Innalillahi kawai take karantowa Ta soma janye luggage d’inta cikin sauri tana San barin wajen... Saidai tuni motar taci gaba da nufota, daidai gabanta ya kuma jan birki ya zube glass yana k’arema Fuskarta dake cikeda tsoro wane irin duba... Ya sakar mata murmushin nan nasa kana yai gyaran murya kad’an “Look who’s here...! Tafiya cikin rana bai kamace Tough girl irinki ba Rankidad’e... Shigo mana let me give you a ride..!” Take taji k’arfin hali na zuwa mata, Ta murmusa kad’an dukda tsananin tsanar wannan fuska tasa da takeji... “Karka damu Your Highness.. Ai mu talakawa mun saba da wahala... Yanzu ba da jimawa ba zan sami abin hawa irin namu na talakawa...!” Yazeed ya kuma murmusawa yace “Ba’a rejecting offer d’ina... So dole ki shigo...!” Jada baya ta soma tana fad’in “Ni kuma nace bazan shiga ba Rankaidad’e.... Why can’t you just go ahead....!” Fitowa yai daga cikin motar zuciyarta naci gaba da tsinkewa, taci gaba da janye jakarta cikin sauri saidai tuni ya cimmata.... Dosowarsu hanyar kenan zasu nufi masarauta ya hangi Yazeed na kokawan tura mace cikin mota... Yai saurin duban Turaki dake driving yace “Wait... Mai nake gani haka...!?” Sai sannan Turaki ya kula da abinda ya gani.... Mahmood ya furta “Wacece yarinyar can da Yazeed yai forcing d’inta cikin motarsa... Lets follow them Turaki... Muyi saurin bin bayansu, jikina na bani wani abu maras kyau Yazeed zai....!” Turaki ya karya kan Mota yana fad’in “Got it your Highness...!” Take motarsu tabi bayan motar Yazeed... Suna ganin yanda motar Yazeed ke sharara gudu saman kwalta tamkar mai shirin barin gari... Mahmood K’uri kawai yai wa motar yana ganin yanda Yazeed Ke wasa da k’arfen nasara saman kwalta... Shikadai sai murza ‘yan yatsunsa yake yana ganin tamkar Turaki ba gudu yake ba, traffic light ya raba tsakaninsu... Cikin tsananin huci yake fad’iwa Turaki “Speed it up Turaki we can’t lose them.!!” Turaki jinjina kai kurum yake yana mai ci gaba da falfala gudu had’ida k’ok’arin ganin Yazeed bai kufce masa ba saidai duk iyaka k’ok’arinsa suna karyo kwana suka nemi motar Yazeed suka rasa, mashigar hanyoyi ne har guda hud’u suka rasa wannene d’aya Yazeed yabi.... ** Suna isowa gidan Yazeed ya zakayo Ta yanda take zaune ya bud’e motar ya shiga fincikota da iyaka k’arfinda Allah ya hore masa, sosai jikinta ke rawa tana tarjewa tana fad’in kada yazo kusanta... Take abubuwan da suka faru da ita shekarun baya suka shiga dawo mata... Sosai ta shiga matsanancin tashin hankali tana mai furta “Please don’t... Don’t please..!!” Tarjewa yakushi cizo da dik wani abinda take tunanin zai ceceta hannun wannan azzalumin bawa tayi amma a banza... Haka Yazeed ya dinga janyota har suka shige cikin gidan... ** Suna nan suna tunanin hanyar da zasu bi Mahmood yai shiru tamkar mai nazari sai kuma ya d’ago ya dubi Turaki yace “Ina tinanin nasan yanda Yazeed ya tafi... Around this place idan ban mance ba akwai guest house d’in mahaifinmu... Inada tabbacin can Yazeed yakai yarinyar nan... Lets go before he does something to her...!” Cikin sauri sukabi hanyar da Mahmood yakeda tabbacin nan ne gidan yake... Aiko suna zuwa suka hango motar Yazeed.. Suka dubi juna a tare... Babu shiri suka nufi cikin gidan.... A daidai sanda suka shigo parlorn daidai lokacinda Allah ya baiwa Muhibbah daman roza ma Yazeed flower verse a kansa... Ta taso a guje tana kuka sosai... Da tsananin mamaki Mahmood ke dubanta “Muhibbah..!!” Ya fad’i zuciyarsa na bugawa... Bata iya cewa komai ba sai kuka... Tsananin tsoro bayyane saman fuskarta... Zuciyar Mahmood taci gaba da bugawa da sauri da sauri, shi kad’ai sai sakin huci yake suna sauraro muryar Yazeed alamun yana neman Muhibbah.. Cikin zafin nama Mahmood ya nufi yanda yake sinkayo muryar Yazeed d’in... Turaki na kiransa inaa ko waigawa baiba... Yana hango Yazeed ya tafi ya dunk’ule hannu yakai masa naushi a hanci, take Yazeed ya zube bakinsa da hancinsa na fidda jini... Cikin wane irin karaji Mahmood yasa hannayensa biyu ya kuma d’ago Yazeed sama ya k’ara masa wata naushin, dukan sa’a yakewa Yazeed wanda Ke kwance waje yana haki da k’yar... Mahmood na nunasa da yatsa yake fad’in “Kaci amanan iyalanka, ka wulak’anta Martaban gidanmu... Ka zakunci ‘ya’yanka... You should be ashamed of yourself Yazeed...!!” Ya k’arashe yana kuma kai masa tokari da k’afa... Yazeed bai iya komai sai haki da k’yar jini da yai masa faca faca a fuska ga yanda Muhibbah ta fasa masa da verse ga kuma uban bugun da yaci hannun Mahmood... Fitowa yai yana huci, Turaki ya taresa yace “Ina Yazeed..?!” Wane irin duba yaiwa Turaki ba tareda ya amsasa ba saima tambayarsa yarinyar da yayi... Turaki yai masa nuni da yanda Muhibbah ta tak’ure ta kifa kanta tana cazgan kuka... A hankali ya isa gabanta ya durk’usa, yana mai k’ura mata idanu cikeda tausayawa... Tai saurin d’agowa da zummar jada baya.. Mahmood ya d’an bud’e murya kad’an yace “Karki damu we won’t hurt you, you’re safe now... Did he do something to you..?!” Tai saurin girgiza masa kai alamun a’a hawaye naci gaba da ziraro mata... Mahmood ya jinjina kai had’ida kauda kai gefe yana mai fuzar da huci a hankali.... Gyaran murya ya kumayi yace “Mai ya fito dake daga masarauta kuma Ina zakije da kaya...?!” Tasa hannunta share hawayen fuskarta, cikin rawar murya tace “Gida Zanje...!” Mahmood yace “Kina nufin garinku..?!” Tai saurin jinjina masa kai alamun eh... “Ina ne garin naku..?!” “Bauchi..!” Ta basa amsa a tak’aice... Juyawa yai ya dubi Turaki dake binsu da kallon mamaki, lokaci guda ya mik’e had’ida furta “Saka luggage d’inta a mota, zamu tafi Bauchi yanzu..!” Turaki ya dubesa da mamaki “Bauchi fah kace your Highness..!” “Bazaka iya zuwa bane..?!” Ya tambaya yana duban wani b’angaren.. Turaki yace “A’a ni ban isa nace haka ba Rankaidad’e, Ina Jos ina Bauchi ai ko Borno kace zamu tafi yanzu babu b’ata lokaci balle nan Bauchi..!” Ya k’arashe yana mai janyo jakan kayan Muhibbah... Ta d’ago tana duban Mahmood kaman zatai magana, kafin tai maganar sai cewa yai cikin dakewar murya “Tashi muje...!” Babu musu ta mik’e tabi bayansa jiki a sanyaye... SameenaAleeyou📚 [8/15, 9:48 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *46* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Har suka shige Mota Turaki bai daina mamakin Wai da gaske Mahmood yake barin gari zasuyi tsakar safiyar nan, Wai ma Toh wacece wannan yarinyar, ga dukkan alamu sunsan juna itada Prince, kuma ko a wasa bai tab’a kawo masa labarinta... Turaki ya murmusa a hankali yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa saidai ba Mahmood d’in ba, abinda zai baiwa mutane mamaki shi ba komai bane wajensa... Back seat Ta shige Turaki na driving Mahmood na mazaunin mai zaman banza, yanda ta tak’ure cikin motar zai tabbatar maka har lokacin tsoron abinda ya faru da ita bai fice daga jikinta ba... Ta side mirror yake dubanta zuciyarsa naci gaba da k’una, ya k’udiri niyyan bazai k’yale Yazeed ba da abinda yayi mata, tabbas sai ya koya masa darasi ta yanda nan gaba idan yaga mace ko wata irice zai koyi girmamata, a duniyarsa yak’i jinin yaga ana wulak’anta mace a cewarsa duk namijin da zaici zarafin mace shi d’in ba namiji bane, hasalima bai cancanci a kirasa namiji ba.. Kuma Wai a haka Yazeed yake ikirarin zama Sarki da wannan disgusting halin nasa...! Ya k’arashe tinanin yana mai ci gaba da murza zobban dake hannunsa har lokacin fuskarsa a matak’ar murtuk’e... Lokaci zuwa lokaci Turaki Ke satan duban b’angaren Mahmood d’in amma Ko gizau fuskar nan nasa babu alamun walwala sam.. Sanin halin abokin nasa za’a iya tafiya duk nisan duniyar da za’a tafi baice uffan ba yasa Turaki danna radio d’in motar, ya kamo tashan labarun wasanni dan yafi zaman hakan.... ** Tinda Jamal yaji cewa Umaima na asibitin hankalinsa ya gaza kwanciya, baya fatan ta gansa a halinda yake ciki dama da yakeda cikakkiyar lafiyarsa bata so shi balle yanzu da ya riga ya zama nakasasshe... Ya rintse idanunsa a hankali hawaye na kwaranyo masa... Zahra jiki a mace ta matsa jikin gadon nasa tace “Uncle please ka k’yale Anty Umaima ta shigo ta ganka wllhi ta damu dakai sosai...!” Jamal ya dubi Zahra da idanunsa masu zuban hawaye, lokaci guda yake girgiza mata kai alamun a’a “No Zahra... Umaima can’t see me like this, dan Allah kice mata ta tafi kawai na gode da gaisuwa...!” Ya k’arashe wasu hawayen na kuma zubo masa... Zahra ta fuzar da fuci a hankali kana ta kaikaito tana duban Zuhra wacce itama juyin duniyar tayi kan Jamal ya k’yale Umaima ta shigo ta gaishesa amma yak’i amincewa... A hankali Zuhra ta tako gaban gadon nasa, sukai shiru gaba d’aya suna sauraren yanda Jamal Ke kuka mai tsuma zuciya, lokaci guda yake ci gaba da fad’in “Labarin soyayya na ya k’are tun kafin ya fara... Bayan abinda na zama yanzu na tabbata Umaima bazata tab’a sona ba, shikenan burina bazai tab’a cika ba... Mace d’aya k’wal da nake so bazan tab’a kasancewa tareda ita ba... Bazata tab’a yarda ta auri mai nakasa irina ba Zuhra...Shikenan na rasa farin cikina har abada..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Zuhra tasa ‘yar yatsanta ta goge hawayen da ya mak’ale mata cikin ido, ta girgiza kai a hankali tace “Jamal don’t talk like that... Nakasa ba kasawa bace, kuma dukkanmu nan da kake gani babu wanda ya isa yace hakittarsa ya kammala har sai ranan da Allah ya kiramu zuwa gareshi... Jamal, a kowace rana na rayuwarmu sabon shafin rayuwace take bud’ewa kuma Ko wacce tana zuwa ne tareda k’alubalenta da jarabawar data k’unsa... Kowa da kake gani a nan yanada nasa damuwar babu wanda zaice maka rayuwarsa gaba d’aya jin dad’i ne duk dukiyarsa duk lafiyarsa duk mulkinsa... In one way or the other yanada nasa matsalan da yake dealing... Jamal this is the reality now, you just have to accept it, and stop making things harder on you... Ina fata Allah ya baka lafiya ya kuma baka ikon cinye wannan jarabawa da ya jarabceka dashi..!” Daga Jamal har Zahra shiru sukai suna saurarenta, dagajin yanda take magana zaka fahimci wani damuwa dake kwance cikin zuciyarta take son amowa.... Basu ankare ba sai hango Umaima sukai tana shigowa hawaye na gangarowa saman k’uncinta.... Jamal yana hangota yai saurin kauda fuskarsa hawaye naci gaba da siraro masa lokaci guda yake k’ok’arin janyo bedcover yana kuma rufe gundulumin k’afarsa.... Zuhra na ganin haka ta janyo hannun Zahra suka fice suka basu waje... D’akin ya rage saura su biyu... Fuskarsa naga wani b’angare yake furta “What are you doing here...Maiyasa kika shigo...? Dan Allah ki fice bana san ganinki, just get out please..!” Ya k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka... Bata fice d’inba saima kuma matsowa kusansa da tai...Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka ziraro mata, lokaci guda take furta “You can’t avoid me forever Yaya... Maiyasa zaka gujeni bayan kaid’in masoyina ne... Maiyasa bazaka karb’i k’addarar ka ba bayan ansan musulmi mai imani da yarda da k’addara kyakkyawa koko akasinta... Ya Jamal dan Allah kada canjin dake jikinka a halin yanzu yasa ka gujeni kaji... Promise me bazaka gujeni ba..!” Tai maganar cikin rawar murya su duka biyun hawaye na gangaro masu... Girgiza mata kai take a hankali yana mai furta “You deserve someone better than me Umaima... Tambayar da na miki kwanakin baya bata buk’atan amsa, halinda na tsinci kaina ciki yanzu itace amsar..!” Ta girgiza kanta da sauri tana mai kuma share hawayen fuskarta take fad’in “Don’t talk like that please... Muyi fatan Allah ya baka lafiya ni kuma na maka alk’awarin bazan tab’a guje maka ba...!” Yai mata K’uri tsananin soyayyarta na kuma ratsa duk wata k’ofa na zuciyarsa... Shigowar Dr ne ya sanyasu k’ok’arin saita kansu, Umaima ta fice ta barsu da Dr Jamal sai binta da kallo yake har ta b’acewa ganinsa... Likitan ma saida ya fahimci haka d’in ya kuwa samu abin zolayar Prince Jamal.. ** Tafiyar awanni biyu jal sukai suka shigo garin Bauchi, idanunta naga window abubuwa da dama cikin zuciyarta harma batasan sun kusa shige unguwarsu dake daga farkon shigowa gari ba... Turaki ya d’an waigo kad’an ya dubeta yace “Destination..?” Tai k’ok’arin saita kanta kana tace “Tambari housing estates..!” Sai lokacin Mahmood ya kaikaito yana dubanta, Shiko Turaki idanunsa naga kwalta yake fad’in “Aiko mun shige Tambari dan gashi har mun iso Zaranda...!” Cikin ‘yar daburcewa tace “Laa dan Allah kuyi hak’uri, ban kula bane...!” Turaki ya murmusa yace “A’a Rankidad’e karki damu ba wani abu bane ai sai muyi U turn, Keda kike tafe da rakiyar Mai Martaba da kansa...!” Kallon da Mahmood ya jefa masa ya hanasa k’arasa zancen nasa... Ya d’anyi gyaran murya kad’an ya dubi Mahmood d’in yace “Rankaidad’e sannu da hanya..!” Yanda yai maganar dole ya baka dariya amma Mahmood Ko gizau bai dariyar ba, idan da Sabo ya saba da halin Turaki, abokinsa ne amininsa ne kusan tare suka taso,Kakansa Tukari shine Turakin Jos mai rasuwa.. Asalin sunansa kuwa Yusuf ne Yusuf Turaki, tun daga makaranta Turaki yabi bakin mutane dashike family name d’insu ne hakan yasa gaba d’aya sunan nasa ya koma Turaki.. Itada Turaki ne suketa maganarsu yanda take masa kwatancen street d’in nasu har suka iso, shiko mai sarautar tamkar kurma haka ya koma cikin motar, baya um baya umum... Suna isowa Turaki ya bud’e motar, ya fito ya bud’e booth ya ciro jakan kayanta... Fuska d’aukeda murmushi ta gyara zaman mayafinta, ta risina tanaima Turaki godiya... Turaki ya murmusa yace “A’a Rankidad’e ai ba wani zakiyi godiya ba... Wa Rankaidad’e zakiyi godiya...” Ta d’ago idanu tana duban Mahmood dake zaune gaban mota shid’inma ita yake duba... Haka kurum taji gabanta yayi mugun fad’uwa, Ji take kaman ya fahimceta ita d’in itace silar tashin hankalin dake tsakaninsa da d’iyarsa.. Gaba d’aya sai taji kaman duk Duniyar kallon mai laifi ake mata... Kanta a k’asa tace “Na gode Rankaidad’e... Na gode sosai da taimakonku gareni...!” Ta d’an kuma duban Turaki tace “Bazaku shigo ku sha ruwa ba..!” Turaki yace “Wai ai sai abinda Rankaidad’e yace, idan yace mu shiga musha ruwa bazamuk’i tayin Sarauniya ba...!” Mahmood ya jefo masa wata kallo da tabbas yasan ma’anar kallon... Girgiza mata kai Turaki yai yace “Mun gode da tayi Rankidad’e, amma yanzu zamu d’auki hanyar Jos, Kinsan yanayin da muka baro Masarautar ciki..!” Ta jinjina kanta a hankali tace “Haka ne... Allah Ubangiji ya tsare maku hanya ya kaiku lafiya.. Na gode sosai...!” Turaki ya amsa mata da Ameen sai kuma yace “Rankidad’e na shigar miki da jakan ciki mana..” Yanda yai maganar yaso bata dariya,ta d’an murmusa kad’an tace “A’a karka damu zan iya na gode sosai ..!” Turaki ma ya murmusa yace “Tunda kince haka shikenan Kinsan ba’a jayayya da mutanen Fada..” ya k’arashe yana mai bud’e mota ya shige... Turaki na k’ok’arin jan mota Mahmood ya dakatar dashi, kallo yabi bayanta dashi har saida yaga gidan data shige... Tana shigewa kuwa yace suje... Turaki yaja mota yana shirya kalolin tambayoyin da yai zaiwa abokin nasa kan wannan yarinyar da Ko shakka babu yana jin akwai wani alak’a mai girma tsakaninta da Mahmood d’in dukda kuwa yasan bazai samu amsoshinsa yanda yake so ba sanin ko wanene abokin nasa... Tindaga nesa da ya hango mota k’irar BMW new brand Ta fito daga ciki yaketa alla alla ya iso dan idanunsa ya gane masa kaman itace ta fito daga motar... Aiko tana k’ok’arin tura gate motarsa ya k’araso, duba d’aya yai mata yaji gabansa yayi mugun tsinkewa musamman da ya ganta da kaya ga kuma yanayin da take ciki wanda zaice bai tab’a ganinta ciki ba... Ta kaikaito a hankali tana dubansa, murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar masa... Yana k’ok’arin fitowa tace “Yi zamanka Dr bara na bud’e maka gate d’in...!” Shidai bai tankata ba saima duban mamakin da yake binta dashi... Ansar ya ida shigowa da motarsa ya k’arasa parking lot yai parking yana mai hangota daga can bakin gate d’in yanda take k’ok’arin rufe gate d’in cikeda kasala tamkar babu laka jikinta... Baba Larai ce ta fito daga kitchen tana fad’in “Likita ka dawo baka jira nazo na bud’e maka Gate d’in ba...!” Tai Burki sakamakon hango Muhibbah da tai da kaya nik’i nik’i... “A’ah kace bak’i mukai gidan namu, Hibbatu sauk’an yaushe...?” Ta k’arashe tana amsar jakan kayan... Muhibbah ta murmusa ta gaisheta kana tace “Yanzu shigowata Iya Larai, mun sameku lafiya..?” “Lafiya lou Hibbatu ya karatun..?!” Saida ta saci kallon Ansar da yai kaman bashi a wajen saima k’ok’arin rufe motarsa da yake kana ta maidoda subantaga Iya Larai... “Alhamdulillahi Iya Larai, Mummy bata dawo daga office ba koh...?” Iya Larai ta jinjina mata kai alamun eh “Kinsan Mamar taku kaman agogo take wajen aiki ko Likita nan ya ganta ya barta wajen san aiki...” Muhibbah ta murmusa dan tayi kewarsu gaba d’aya, daidai lokacinda Ansar ya k’araso Iya larai na masa sannu da zuwa ta shige ciki abinta tana fad’in yau d’in mutuminsu Ta dafa... Muhibbah da Ansar suka jero suna takowa, kaman babu mai magana ma d’an uwansa.. Ta d’an bud’e murya kad’an ta gaishesa.. Ya amsa yana mai rataye lab cot d’insa a kafad’a.. Yai mata sannu a hanya itama ta amsa har suka k’araso cikin parlorn... Juyowa Ta d’anyi Ta dubesa kana tace “Ni zan shige ciki na gaji sosai...!” Ansar ya tsareta da idanu har Ta soma tafiya ya kirawo sunanta.. Ta d’anyi still a wajen kana ta juyo gareshi... “Haka zaki shige ki barni without any explanation..?” Yai maganar yana dubanta.. Ta d’an dafa kujeran da take tsaye gefensa tace “Gani nai yanzu ne dawowarka kaima Dr... Ya kamata ka k’arasa ka huta kafin lunch ya kammala..!” Katseta yai da fad’in “Kema Kinsan akanki bazan huta ba sai naji komai, you come first before anything else..!” Ya k’arashe cikin dakewar murya.. Rausayar da idanunta tai kad’an had’ida fuzar da iska tace “Ansar please not now... Can’t you see I just got here., Please ka k’yaleni ba yanzu ba... Ni na shige we talk later..!” “Muhibbah I’m serious... Whose car was that, su waye suka ajiyeki... Maiyasa zaki shiga motar wasu, wannan shine agreement d’inmu, kinje kina shiga motar maza maza suna dawowa dake har gida... How could you Muhibbah, wannan shine rayuwar da Kika zab’arwa kanki cikin Masarautar... Who knows mai kikeyi a can, just answer me Muhibbah..!!” Katsesa tai da fad’in “Ya isheka haka.. Don’t you dare judge me, you have no idea what I’ve been through... So you better hold it right there..!!” Ta k’arashe cikin wane irin karaji hawaye na ambaliya a fuskarta.. Lokaci guda tasa kai zata shige... Ansar yai saurin shan gabanta yana furtawa cikin sanyin jiki “Hibbah please.. Kiyi hak’uri..!” Yai maganar cikin sanyin murya.. D’ago idanunta masu zuban hawaye tai had’ida girgiza kai “Why is it so easy for you to judge others bayan watak’ila bazaka Iya d’aukan rabin iftila’in da suka tsinci kansu ciki ba... Ansar ba ma wannan ba shin haka ka d’aukeni... Ballagaza mai bin maza..!” Kuka yaci k’arfinta, cikin sautin kuka take ci gaba da fad’in “Do you think I went there just catch some fun... Not a day goes by banji zafin rayuwa k’asan rufi guda da nake taredasu

Chapter 29 of 65