Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lumshe idanunta tai tana ambato Allah da neman taimakonsa, Ta bud’e idanunta a hankali tana jin k’warin gwiwa na zuwa mata... Cen ta hangi wani k’ofa da yake daga center, zuciyarta tafi amintar da tabi wannan k’ofa... A hankali cikin sand’a had’ida d’an sauri ta nufi k’ofan, ta d’an tura a hankali tana lek’awa, shima d’in wani hamshak’in parlor ne maiji da tsari... Tabbas ana baza mulki a wannan gida, Ta fad’i haka cikin zuciyarta.... Cikin sand’a ta kutsa Kai cikin parlorn, saidai shigarta Keda wuya Ta soma sauraron wasu muryoyi.... Tai saurin k’arasawa yanda take sauraron maganan, tabbas muryar Giwa ce dan bazata tab’a mance wannan azzalumin murya a dodon kunnenta ba, tana iya sauraro muryan d’aya daga cikin yaranta suna tattaunawa saidai bazatace ga wanene suke maganan ba cikin yaran nata dan gaba d’aya yaran murya kala guda Ke garesu, na Mahmood ne kad’ai ta d’an banbanta dan dik ya fisu gwab’in murya mai cikeda k’warjini... Hakan ya tabbatar mata da d’aya daga Cikin k’annensa Giwa ke tattaunawa.... Bataji gaba d’aya abinda suke tattaunawa akai ba amma tabbas taji Giwa na basa umarnin aiwatar da wani abu.... Jin kaman ana k’ok’arin tab’a k’ofa ya sanyata saurin sad’ad’owa ta fito k’irjinta na tsananin bugu.... Sauri sauri ta nufo dogon open corridor d’in nan tana tafe tana waigawa baya bata ankara ba saiji tai ta bige mutum ta fad’o cikin jikinsa.... SameenaAleeyou 📚 [6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *013* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Ido cikin ido suke duban juna itada Yazeed, ga tsananin bugu da k’irjinta keyi, tamkar ta tsatta ma wannan fuskar tasa miyau haka takeji... Shiko sosai ya had’e rai yanai mata wane irin duba.. K’aran tafiyar mutane da suka soma jiyowa ya sanya tsoro ya kuma bayyana a fuskar Muhibbah tai k’ok’arin sa kai zata rab’a ta gefen Yazeed saidai tuni ya fizgota sun shige tsakankanin gini hakan yai daidai da d’aukewar wutan lantarki...K’irjinta yaci gaba da bugawa, duhu ya soma shigowa dan haka kana iya ganin mutum amma duru duru, tana iya hango Farin fuskan Yazeed cikin duhun yanai mata alamu da tai shiru.... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa sanda taji tafiyar yana nufosu sosai, tai saurin rintse idanunta a hankali yayinda Yazeed yaci gaba da k’are mata kallo from head to toe dan tsaf yana iya ganinta cikin duhun nan dashike shi Allah yayisa mai idon kallon mata... Giwa ce da Jakadiya suka taho zasu shige wani k’ofar, saida suka d’an tsaya kusan yanda Yazeed da Muhibbah Ke lab’e suna tatauna wasu al’amararsu da suka shafi cikin gidan Muhibbah najin sanda suka ci gaba da tafiya suka shige wata k’ofar ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Suna shigewa Muhibbah tai saurin matsawa baya tana sakin huci a hankali, lokaci guda take k’ok’arin saka kai zata shige dan ko takan Yazeed bata kuma bi ba tamkar wani babu abinda ya faru...Yazeed da ya kafeta da mayun idanunsa yana k’are mata kallo saurin tare gabanta yai da hannunsa guda kana yace “And just where do you think you are going..? Fad’a min zakiyi mai kikazo yi nan... Wacece Ke....? mai ya kawoki wajen nan..?!” Banda bugu babu abinda k’irjinta keyi, tsananin tsanarsa ne kwance cikin idanunta, bata d’ago fuskarta ba har lokacin saima bugu da k’irjinta Ke ci gaba da yi.. Mamaki ya cika Yazeed ganin tai masa banza kaman bataji abinda yake fad’i ba.... Wacece ita...? Yai tambayar a zuciyarsa... Ga duhu da ya gauraye wajen saiko hasken walk’iya dake haskawa lokaci zuwa lokaci... A hankali yake k’ok’arin mik’a hannunsa da niyyan d’ago fuskarta... K’irjinta yaci gaba da bugawa, zuciyarta naci gaba da mata zafi.... K’iris ya rage hannunsa bai sauk’a samar fuskarta ba wayarsa dake aljihun wandonsa ya d’auki ruri... Yai saurin mik’a hannu ya ciro wayar hasken wayar ya haske fuskarsa tarau, tai saurin karkatar da fuskarta sabida tsananin k’yank’yaninsa da ya sauk’o mata dikda Uban gayun dake jikinsa.... A yayinda hankalinsa ya ya karkata kan wayar salulansa Muhibbah ta hangi fad’uwan abu mai kamada sark’a ta mata daga aljihun nasa... Tana ganin sanda ya d’aga wayar yana mai juya baya, hakan ya bata daman silalewa tai saurin d’aukar sarkar tana mai sakar masa muguwar kallo kana ta juya cikin sauri ta fice daga wajen k’irjinta sai bugu yake tamkar ana iza mata guduma.... Sauri sauri ta nufo k’asa zuciyarta bata daina tsinkewa ba, dik wani motsin da zatai sai taji tamkar yanzu ne suka bangaji juna ita da Yazeed, uwa uba hannunta da takeji tamkar ba a jikinta yake ba har yanzu... Ji take tamkar ta guntile hannun ta jefar idan ta tuna sanda ya fizgo hannun nata suka b’oye... Takai dubanta ga hannun nata, sai lokacin ta tina ashe akwai sark’a rik’e a hannun nata... Idan bata b’ata gani ba wannan design d’in jewelry d’in irinsa ta gani a kunnen Rahima yau da safe da suka had’u a k’ofar Bayi...Toh kodai nata ne..? Ya akai yazo hannun Yazeed..? Tambayar dataji na tasowa daga k’asar zuciyarta... Ta saki murmushi a hankali dan ko babu komai ta sami wani abin... Sanda ta sauk’o k’asa ta tadda kuyangi da dama wannan karon sai kai komo suke, dik wanda tazo giftawa cikin Kuyangin sai sun risina Sun gaidata, itama har ta koya daga wajensu Umaima saidai ta jinjina masu kai murmushi saman fuskarta alamun amsawa... Tana tafe cikin kantamemen parlorn mai tsawo da fad’in gaske ta hango Umaima tsaye daga waje ta cikin glass d’in sliding door.... Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali kana ta nufi k’ofar da take hango Umaima, saidai tana isa jikin k’ofar ta hango Fu’ad zaune saman wasu kujeru na shak’atawa yayi zama irinta masu mulki k’afafu d’aya bisa d’aya, da alama magana sukeda Umaimar... Fu’ad ya murmusa kad’an kana yace “Kawai tambayarki nake, a ina kika samota...?” Umaima ta murmusa kad’an itama kana tace “Prince F kenan, ai abin ne ya bani mamaki, naga friends d’ina da dama sukan Zo Masarautar nan, baka tab’a tambayar koda sunayensu ba dikda cewa su sukan damu da zancen Princes d’in Masarautar nan... Kaga kuwa bazakaga laifina ba dan na tambaya kodai kodai....?” Ta k’arashe da sigar zolaya tana kashe masa idanu... Ya murmusa a hankali kana yace “I can’t deny that she’s kind of.... Beautiful...!” Ya k’arashe yana alamu da hannayensa tamkar wani mai describing irin kyaun da ya hango tattareda ita.... Umaima tai murmushi mai d’an sauti wannan karon kana tace “Prince F kenan kaidai kawai ka nad’ani matsayin campaign director d’inka dan Muhibbah k’anwarmu ce tinda k’anwar Ansar ce...” “Muhibbah..!” Ya nanata sunan a hankali kana yace “Beloved..!” Yana maganan yana jinjina kai lokaci guda yaci gaba da fad’in “Ta dace da sunanta.....!” Sabon bugun zuciya ne ya sauk’arwa Muhibbah tai saurin jada baya tana maida numfashi a hankali had’ida lumshe idanunta, wayoyin kanta suna k’ok’arin kwancewa... Anya zata iya k’arasa abinda ta fara... Wata zuciya taceda ita “Ke Saudatu what have you gotten yourself into...?” Take kuma taji wani b’angare na zuciyar nata na fad’i mata “Toh mahaifinki fah... Ta yaya zaki San asalin abinda ya samesa idan baki dawo ba...? Sannan mahaifiyarki da kika rasa fah.... Dik uk’uba da masifa da kika shiga a baya fah...? Shikenan sunci banza suna rayuwarsu cikin jin dad’i da zaluntar wasu al’umman... Saudatu zaki iya... Zaki iya abinda kika riga kika fara... Tabbas zaki iya...!!” Da wannan shawari na zuciyarta taji natsuwa na zuwa mata a hankali... Ta waiga gefe ta hangi wata Kuyanga zata shige... K’arasawa tai gareta ta tareta tana tambayarta ko ina d’akin Zahra yake....? Kuyangar ta nuna mata wani b’angare nan cikin parlorn da shima benen za’a d’ale kana tace “Ta nan ne Rankishi dad’e...” Tai mata nuni da b’angaren benen dake kallon hagu, dashike irin babban matakalan nan ne mai kunne biyu d’aya na kallon b’angaren dama yanda ta sauk’o bada jimawa ba saman d’ayan na kallon b’angaren hagu... Muhibbah ta jinjina kai kana tace “Muje ki nuna min....” Kuyangar ta d’an d’ago tana dubanta kana ta kuma sadda idanunta tana fad’in “Kiyi hak’uri Rankishi dad’e bana d’aya daga cikin amintattun dake haurawa d’akin Gimbiya Zahra’u... Amma idan kika haura d’akin nata a nan yake...” Jinjina mata kai Muhibbah tai kana tace “Kina iya tafiya..” Kuyangar ta jinjina kai alamun amsawa kana Muhibbah ta nufi benen kaman yanda Kuyangar ta sanar da ita... Matsakaicin wajene mai kyaun gaske Shima, Muhibbah ta tsaya daga parlorn tana k’arema wajen kallo, tabbas sai a b’adda mutum b’att ba’aji d’uriyarsa ba a gida irin wannan... D’akuna guda biyu ta hango nan ta nufi d’akin dake daga gefen dama.. Ta d’anyi knocking a hankali sallama saman bakinta... Jin ba’a amsata ba ya sanyata d’an tura k’ofar a hankali... Nan ta hangota kwance saman royal bed da akai ma d’akin ado dashi wanda yake d’an tsurut a tsakiyar d’akin sabida girma da d’akin kedashi... Tai K’uri tana duban yarinyar dake baccinta hankali kwance... Ta tsinci kanta tana mai sakin murmushi, lokaci guda ta shigo d’akin had’ida tura k’ofar a hankali kaman mai tsoron kada ta tasheta... Muhibbah ta k’araso gaban gadon tana k’arewa Zahra kallo k’aunar yarinyar na kuma shigarta, batasan dalili ba amma dik tsanar da taiwa mahaifin yarinyar bata hango tsanar tattareda yarinyar saima k’aunarta da takeji na shigarta a hankali musamman dataji cewa ta rasa mahaifiyarta, kaman yanda itama ta rasa mahaifiyarta sannan a kusan shekaru irinta Zahran Ta rasa nata mahaifiyar itama... Janyo bargo tai ta rufawa Zahra kasancewar anyi ruwa garin ya d’anyi sanyi kana ta d’auki remote control d’in AC ta rage mata... Lokaci guda ta zauna a gefenta tana dubanta... A hankali Zahra ke bud’e idanunta har ta bud’esu tarau tana duban Muhibbah dake sakar mata murmushi... Zahra Ta mik’e sosai ta zauna murmushi saman fuskarta...Kafin ta sami zarafin magana Muhibbah tace da ita “How are you feeling now...?” Yarinyar ta d’anyi mata K’uri murmushin bai bar fuskarta ba kana tace “Much better...” Muhibbah ta d’an jinjina kai alamun rashin sabo kana tace “Akwai yanda ke maki ciwo kuma...?” Kanta ta kuma girgizawa alamun a’a... “Kin sha maganinki na dare...?” Take annurin fuskar yarinyar ya d’an d’auke alamun basu shiri da magani... Muhibbah takai dubanta ga yanda magungunan Ke aje bisa ruwa a gefe, kana ta isa ta d’auko... Zahra tai raurau kana tace “Paa ke sakani nasha dole... Banson drugs...” Gefe da ita Muhibbah ta zauna kana tace “Let me teach you something...” Tai maganan tana mai b’alle maganin kana tace “Oya close your eyes now and open your mouth... Just think of your favorite candy, kiyi tunanin shi kike sha... There....!” Ta k’arashe tana mai saka maganin bakin Zahra... Dik yanda Muhibbah tace Zahra tai hakan takeyi, a haka har Ta ida bata magungunan.... Su duka biyun fuskokinsu ya cika da annuri... Tsaye yai nan jikin k’ofa yana dubansu... It’s been a while since he saw his daughter as happy as she’s right now, akwai wani murmushi da takeyi wanda tun bayan rasuwar mahaifiyarta bai kuma hangowa a fuskarta ba sai yau.... So yake budurwar da suke tareda Zahra ta juyo yaga fuskarta don bayanta kawai yake hangowa amma sai bugu k’irjinsa keyi a hankali lokaci guda yana hango tsananin Farin ciki dake tattareda d’iyar tasa... Yai k’asaitaccen murmushi a hankali, bazaiso wani abu ya gifta tsakanin wannan Farin ciki da Zahra Ke ciki ba... A hankali yasa kai kaman zai juya, saidai tuni Zahra ta hangosa... Ta d’an bud’e murya had’ida kiran sunansa... Dummm!!! Haka k’irjin Muhibbah ya buga... Zahra taci gaba da fad’in “Paa ka shigo ku gaisa da Aunty Muhibbah...!” A hakali yake takowa cikin d’akin, cikin takunsa mai cikeda charisma yayinda zuciyar Muhibbah yaci gaba da bugawa da sauri da sauri cikin sakanni... Sai murza sark’ar dake hannunta take ba tareda ta iya koda motsa wuyarta ba balle tai tinanin juyowa.... Tana jin sanda Zahra Ke furta “Aunty Hibbah meet my Paa...!” Zuciyarta taci gaba da tsinkewa, bugun zuciyarta ya k’aru.. Batasan ta yanda zata soma juyawa tai idanu hud’u da wannan azzalumi ba and act like nothing ever happened.... Tana tsaka da tinanin ne sallaman Umaima ya katsesu.... Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali... SameenaAleeyou📚 [6/5, 7:51 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *014* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Umaima ta shigo tana mai fad’ad’a murmushinta “Yaya barka da shigowa...” Ta fad’i cikeda risinawa... Jinjina mata kai yai daidai sanda wayar salulansa ta d’auki ruri, abokinsa Turaki ne mai kiran... Dan haka kai tsaye ya juya ya fice daga d’akin... Muhibbah ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida bud’e lumsassun idanunta... Umaima ta k’araso tana fad’in “Sorry na barki ke kad’ai a parlor Prince F ya rikeni da hira, ashe kin hauro nan...” Muhibbah ta rausayar da idanu kana tace “Eh mana, kin barni ni kad’ai salon naje na b’ata a wannan k’atoton gidan... Allah yasa ban shige wani wajen ba nai karo da d’akin patient d’ita...” Umaima da Zahra suka d’anyi tak’aitaccen dariya a tare cikeda jin dad’i kasancewa da juna Umaima na fad’in “Kar ki damu babu wanda zai saceki cikin Masarautar nan...” Suka kuma darawa a tare Rahima dake lab’e jikin k’ofa k’atutun bak’in ciki ya tokare mata mak’oshi ganin wannan mayyar k’awar Umaimar mai bak’in shishigin tsiya tareda Zahra... Allah ya gani bata k’aunar yarinyar nan.. Bata iya shiga ba sai juyawa da tai zuciyarta na mata zafi... A b’angaren Yarima Mahmood kaw tinda Turaki ya sanar dashi isowarsa bai kuma dawowa d’akin Zahra ba dan tini ya samu Ubandoma ma na jiransa daga waje, yasan isowar Turakin zai sanar dashi.. Hakan sai yafi wa Muhibbah dan harga Allah batajin tayi shirin fuskantar babba cikin azzulaman ‘ya’yan sarki AbdulJabbar a yau bayan karon da tai da Yazeed da kuma zancen Fu’ad da Umaima da ta sinkaya... Dik surutun da Umaima da Zahra keyi da alama hankalinta bai taredasu... Tafi bada mahimmanci ga duban k’ofa kaman mai jiran shigowar wani... Cikin zuciyarta take sak’awa, tinda ba Yazeed bane ba kuma Fu’ad bane Giwa Ke tattaunawa da, tabbas da Jamal kenan take tattaunawar, a shi take bada umarnin zartar da wani abu... Mai kenan..? Meye take umartan Jamal yai da wannan kakkausar murya irin haka...? Idan bata b’ata ji ba kaman taji Giwa na cewa kaje ka duba ka gani ko har yanzu na raye... Wannan statement shi take ta nanatawa cikin zuciyarta har lokacinda sukai karo da Yazeed.... Waye Giwa take bada umarnin aje a duba ko Yana nan a raye... Could it be mahaifinta ne...? Kardai Abbanta ne tsawon shekarun nan yana cikin Masarautar nan basu kashe shi ba...? Ya zama dole tabi bayan Jamal taga yanda Giwa ta aikesa...?! Bata ida tinanin ba taji Umaima na dungurinta tana fad’in “Hibbah Wai ina kika tafi munata tambayarki...?” K’ok’arin saita kanta Muhibbah tai kana tace “Kinsan na baro wayata cen sashen bak’i kuma munyi da Mummy zata kirani toh ko shakka babu nasan tana kan nemata yanzu haka....” Umaima ta d’an girgiza kai tace “A’a Gaskiya bai kamata ki k’yale Mummy taita kiranki no response ba, zatai tinanin ko wani abin ne ya sameki... Kinsan iyaye da nuna damuwarsu musamman idan sun tura yara makaranta... Ki tashi kije ki d’au wayarki gaskiya...” Murmusawa Muhibbah tai kana tace “Toh shikenan ga patient d’ina na barta hannunki amana...” Suka murmusa gaba d’aya kana Muhibbah ta mik’e ta fice Zahra na labartawa Umaima yanda Muhibbah ta bata magani cikin dad’in rai ba tareda taji d’acin maganin ba... ** Gimbiya Zeenat ce hankice a parlornta na alfarma, bayi guda biyu sai aikin tausan k’afafunta dake bisan manyan pillows na sarauta suke... Shigowar Raheema fuska a tamke yasa Gimbiya Zeenat umartan kuyangin nata da su fice su basu waje... Babu musu kuyangin suka mik’e sukai kaman yanda uwar gijiyar tasu ta umarta... Raheema ta zauna saman kujera sai cika take.... Aunty Zeenat ta d’ago tanai mata wani irin duba kana tace “Ke kuma fah.. Wannan kumbure kumburen na minene... Ince kina cen kina kula da d’iyar mijinki... Meye kuma zaki shigo kina kumbura fuska..?” Raheema ta d’an kuma tura baki gaba tana kuma tab’e fuska kana ta dubi ‘yar uwar tata tace “Aunty wata mayya ce ta shigo Masarautar nan take neman shige min hanci da k’udundune.... Wllhi bakiga yanda take rawar k’afa kan ahalin Masarautar nan ba musamman Zahra... Aunty tsoro nake kar wannan shegiyar yarinyar Zahra tasa mahaifinta ya auka wa soyayyar wannan mayyar tinda dama yarinyar bak’ar munafuka ce dan na lura tamkar bata k’aunar alak’ata data mahaifinta....!” Ta k’arashe tana kuma tura baki gaba... Tsegege Gimbiya Zeenatu ke dubanta kana ta murmusa kad’an cikeda k’asaita sannan taci gaba da fad’in “Dad’ina dake Raheema wauta, Ke yanzu har akwai macen da zata baki tsoro akan Mahmood... Mutumin da matan ma basa gabansa, mutumin da har yanzu mutuwar matarsa bai gama ficewa daga jikinsa ba... Ni wannan wauta naki da yawa take Raheema saikace ba d’iyar Saraki kike ba, sam Bakida jarumta... Har yaushe zaki tsaya wata banza can Ta baki tsoro Yo ni ba don inason cimma burina wajen ganin kin auri Mahmood ba yaushe zan tsaya ina biyayyawa Giwa...Toh wllhi ki bud’e kunnuwarki da kyau ki saurareni... Idanma baki son Mahmood wannan Ke ta shafa iayakacin abinda na sani shine idan za’a kashe rai a Masarautar nan sai kin aure Mahmood dan yanda na zamto ‘yar kallo cikin Masarautar nan auren Mahmood da zakiyi shine zai dawo min da Martaba ta ya kuma d’aga darajata, don na tabbata da zaran Mahmood ya zama Sarki Ke kuma kin zamto matar Sarki Toh fah mulki ta dawo hannunmu sai yanda mukai da Giwa cikin Masarautar nan, da Sarki da Uwarsa dik zasu dawo k’ark’ashin mulkin mu....Tunda ban haifa Sarki ba don haka dole na zamto Sirkar Sarki, dole ta ko wanne hanya nasan yanda zanyi mulkin Masarautar nan Ta dawo gareni... Kuma hanya d’aya kenan tak shine ki auri Mahmood...!” Ta k’arashe tana zaro idanu waje... Raheema tai shiru tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali, k’aunar Mahmood na kuma fizgarta, dik yanda za’ai bazata tab’a bari wata tazo Ta rusa mata Farin cikin data jima tana k’ok’arin ginawa ba koda kuwa wann shegiyar d’iyar tasa bataso.... Da wann tunanin ta mik’e ta nufi d’aki shiryawa dan zuwa ganin Yarima Mahmood... ** Turaki ya kuma gyara zama yana mai kurb’an drink d’in dake rik’e hannunsa kana ya nusa kad’an yace “Toh yanzu what are you suggesting your Highness...?” Yarima Mahmood ya fuzar da fuci a hankali kana yace “I don’t know Turaki... Is getting more complicated... Na rasa ta ina zan b’ullowa al’amarin... Waye zan fara tuhuma..? Ta ina zan fara bincikawa... Sannan waye zan yarda dashi cikin Masarautar nan...?” Shiru ya d’an gifta tsakani kana Turaki ya d’an gyara zamansa had’ida fitowa daga cikin kujera sosai “A gaskiya your Highness ko ni ban goyi bayan ka amince da kowa cikin Masarautar nan ba... I’m sorry to say not even your brothers...It might sound ridiculous but gaskiyar kenan... Kuma kaman yanda Baba Wambai yace, if you really want to get to the bottom of all this, Toh fa sai ka zamto shugaba a Masarautar nan... Idan har kana tunanin mutuwar Matarka nada nasaba da mutuwar mahaifinka bazaka tab’a ganowa ba har sai ka zamto kaikeda mulkin Masarautar nan....” Yarima Mahmood yai shiru yana mai shafe fuskarsa da tafukan hannayensa had’ida fuzar da fuci a hankali... Lokaci guda abubuwa da dama ke ziyartan kwanyarsa... Mafarkin da yai da ‘yan uwansa harma da mahaifiyarsa, Sannan Maiyasa Giwa take so ya auri k’anwar matar mahaifinsa... Maiyasa yake jin can k’asan zuciyarsa bai aminta da wannan had’i da suke k’ok’arin yi ba... Maiyasa yake jin abubuwa da dama basa tafiya daidai cikin Masarautar... Tabbas ya kamata ya saka zancen Baba Wambai a ma’auni, bai kamata ya k’yale Yazeed ya d’ale Karagar Mulkin ba har dai yanaso ya samo amsoshinsa.... Turaki yaci gaba da fad’in “Mai kake gudu cikin sarauta Mahmood... Kana tinanin sirrin da ka b’oyewa d’iyarka shekara da shekaru na iya bayyana ne... Is that what’s holding you back...?” Ya k’arashe cikeda kulawa... Kaikaitowa yai wannan karon yanaima Turaki wani irin duba kana ya soma fad’i cikin karaji “She’s never going to find out.... I won’t allow that to happen... I’ll protect that from happening, no matter the cost..!!” Shiru Turaki yai ba tareda ya kuma cewa komai ba dan yasan wanene abokin nasa idan ransa ya b’aci... Bai kuma kawo zancen ba sai ma shiru da yai yana karantar Mahmood d’in da ko ba’ace ba lissafi da sak’e sak’e yake cikin zuciyarsa... Turaki ya girgiza kai cikeda tausayin abokin nasa.... *** A nan yanda ta mak’ale take jiran fitowar Jamal, Ta kusan minti talatin mak’ale a nan wajen tana ganin masu kaiwa da komowa amma bataga koda k’yallin Yarima Jamal ba... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai kuma lek’awa... Har saida ta cire rai bazataga giftawansa ba ta hango wani mutum sanye cikin bak’in kaya mai tsananin duhuwa ya nufo ta yanda take, baka iya hango fuskarsa don ya rufe da bak’ar hula mai yanayi da hular sanyi... Baka hango komai sai alamun mutum... Sosai k’irjinta ke tsananin bugu zuciyarta na tambayarta wanene wannan... Tana gani mutumin ya nufi wata hanya ga walk’iya da har yanzu akeyi had’ida tsawa mai k’arfin gaske... Take taji zuciyarta tana son ganin yanda wannan mutumi zai jesa... Lokaci guda ta sad’ad’o ta fito daga mab’oyar nata ta nufi mutumin cikin sand’a dikda cewa tafiyar mutumin yafi kama da sassarfa tamkar mai tafiya cikin iska dan har b’acewa ganinta yake..... Dikda tsananin tsoro da ya ziyarci zuciyarta hakan bai hanata bin bayan wannan mutumin da bata iya hango komai nasa face bak’in tufafi.... Suna tafe ta hango mutumin ya tsaya cak tamkar wanda aka tsaida shi... Gabanta ya yanke ya fad’i tamkar an iza guduma, idanunta suka firfito waje... Juyowan da mutumin zai yayi daidai da shigewar Muhibbah cikin tsakankanin gini zuciyarta bata daina tsinkewa ba, lokaci guda ta rintse idanunta sanda taji tamkar takun mutumin ya nufota.... SameenaAleeyou📚 [6/8, 8:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *015* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Sosai take jin tafiyar na nufowa yanda take, banda karanto addu’o’i cikin zuciyarta bata iya komai, ta rintse idanunta a hankali tana jiran mai aukuwa ya auku.... Cak kuma sai taji tafiyar ta tsaya, tai saurin bud’e idanunta dake rintse k’irjinta naci gaba da bugu... A hankali ta d’an fito da kanta tana lek’en hanyar, bataga kowa ba sai wasu mage guda biyu suna cin abinci daga gefe.... Allah ya gani tsikar jikinta yai matuk’ar tashi da ganin wad’anann Magen dikda gasu farare ne k’al gwanin ban sha’awa.... Ta kuma lumshe idanunta a hankali tana karanto addu’a na neman tsari, Allah yasa ita d’in ma’abociyar zikirin safiya da maraice ne wanda dik d’an adam idan yai rik’o dasu Allah yayi alk’awarin karesa daga dikkan wani abin cutarwa saidai kuma idan k’addararka ce toh sai ya cimmaka.... Tabbas wannan mutumi mai bak’in tufafi ya b’acewa ganinta, batasan Ta yanda ya nufa ba dan haka dole ta hak’ura da bin bayansa, gashi bataga Jamal ba mak’asudin b’uyarta a wajen... Babu yanda ta iya haka ta nufi masauk’i tana ci gaba da sak’e sak’e cikin zuciyarta lokaci guda tana juya sark’ar data d’auka daga wajen Yazeed.... Tana isa d’aki ta d’au wayarta, Aiko nan ta iske missed calls d’in Ansar kusan guda biyar... Ta d’an lumshe idanunta had’ida bud’esu, lokaci guda tana fuzar da huci a hankali... Kaman jiran isowarta yake nan wayar taci gaba da ruri.... Ta d’auka a hankali sallama saman bakinta... Cikeda tashin hankali Ansar ke fad’in “Hibbah where have you been, I’ve been trying to reach you since ... Tell me akwai wani abu ne..? Are you okay... How are things there...?!” A jere yaita jero mata tambayar cikin tsananin damuwa... Shafe fuskarta tai a hankali kana tace “Relax please Ansar..Just calm down... Babu abinda ya sameni, idan kajini shiru Ina aiwatar da abinda ya kawoni ne kafin lokaci ya k’ure min.... And please I want to ask you this favor... Dan Allah ka daina yawan kirana on and on, someone might get suspicious of me, especially Umaima ta yarda dani sosai banso na breaking trust d’inta da take dashi akaina... She really is a good person banso taga kaman na yaudareta ne ko wani abu mai kama da haka... Kuma kaima yin hakan ka iya shafar alak’arku...Please Doc ka rage yawan kirana...You don’t need to worry about me, I can take care of myself...!”Ta k’arashe Murya fal damuwa... Fuzar da fuci yai a hankali kana ya soma fad’in “Seriously Hibbah...! Cewa kike na rage yawan kiranki bayan nasan abinda kikeyi abu ne mai matuk’ar had’arin gaske... And you’re even telling me kar na damu dake zaki iya kula da

Chapter 8 of 65