Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kaw saidai taceda Mommy aita had’a masa da addu’a har Allah ya sassauta masa... Yana zaune cikin d’aki ya bada hankali ma wayarsa lokaci zuwa lokaci yana sakin tsuka yana fuzar da fuci.. Hamida dake mak’ale jikin k’ofa rik’eda jug da cup tana San shigowa amma batasan ya zasu kwashe da mijin nata ba.. Tai k’arfin halin yin sallama ta shigo.. Dukda sanin darajar sallama bai iya amsa mata ba sabida tsananin tururi da zuciyarsa keyi... Tasan bazai mata magana ba koda zata kwana tana tsaye wajen.. Ta duk’a a hankali ta shiga tsiyaya masa juice d’in dake cikin jug d’in a cup d’in a hankali.. Jiki a matuk’ar sanyaye ta mik’a masa tana fad’in “Yaya kasha wannan, na kula yinin yau d’in bakaci komai ba..!” Wani duban da ya watsa mata ya sanyata had’iye sauran kalaman nata.. Ta sadda kanta a k’asa zuciyarta na kuma harbawa.. “Ke ni sa’anki ne..? idan baki fice min a d’aki ba kinji na rantse saina b’abb’allaki Kinga sai akai ma Baffah k’asusuwanki ya had’a ya sayar ya k’ara jari kan wanda ya amsa da sunan kud’in auren Muhibbah.. Munafukar banza tashi ki fita min a nan.!” Hameedah ta tintsire da wane irin kuka mai k’arfi ta mik’e zata fice a guje.. Ya katseta da fad’in “Dawo Ki tattari tsiyarki dan ban San mai aka baki akace ki zuba min ba.. Tattara and get the hell outta my room..!” Ya k’arashe yana mai mik’ewa tsaye had’ida nuna mata k’ofa... Cikin kuka Hameedah ta tattari jug da cup d’inta Ta fice... Tana ficewa yaja dogon tsaki had’ida furta “Munafuka kawai..!” ya mai maida hankalinsa kacaukam kan wayarsa... Tin safe dialing wayar Raheemah yake bata d’agawa.. Cikin sa’a yaji ta d’aga... Da masifa ta taresa da fad’in “Wai kai bakasan uzuri bane a rayuwarka.. Sau nawa zan ce maka mijina baida lafiya ina asibti taredashi kan mai zaka bi duk ka d’aga min hankali..?!” Ansar ya katseta da fad’in “And do you think I give a damn about that Bastard..?! Toh ya mutu ma mana for all I care..” Raheemah ta katsesa da fad’in “Bana son tashanci ka gane.. Na fad’a maka matarka will soon come back to you.. I’ve already poisoned her mind... Na tabbata bayan abubuwan dana sanar da ita bazata bari ayi nad’in sarautar Mahmood da aurensa akanta ba.. So just chill lover boy..!” Ansar dake tsananin huci ya katseta da fad’in “No bazai tab’a yuwa Sarkin nan ya tsare Muhibbah ya hanamu kasancewa ba.. She’s mine.. Ita d’in tawa ce... Da kika San zakije ki tare asibiti wajen d’an iskan mijin nan naki da baki bari na baro Masarautar tareda Muhibbah ba...!!” Mommy dake tsaye k’ofa bayan Hameedah taje mata tana kuka ta taho d’akin Ansar d’in rai b’ace danjin Ba’asan abinda yai mata take kuka sosai nan ya sinkayi wayar da yake da Raheemah... “Ansar..!” Mommy ta furta a hankali tana mai dubansa fuska a matuk’ar d’aure.. Gaban Ansar ya yanke ya fad’i babu shiri ya kaste wayar da yake da Raheemah... Mommy ta ida shigowa cikin d’akin tana tambayarsa cikin tsananin Shock.. “Ansar dama ka sami Muhibbah.. Ka San yanda take, ka sanar damu kwnanka guda kana nemanta baka sameta ba..! Ansar what is going on..? Ka sanar dani..!” Ta k’arashe tashin hankali kwance saman fuskarta... Ansar dake girgiza kai cikin wane irin yanayi yake furta “Mommy ki saurareni..!” Katsesa tayi da fad’in “Saurarenka nake Ansar... Tell me, where’s Muhibbah..? Where’s my daughter..?!” Ta k’arashe idanunta na firfitowa waje... Cikin sanyin jiki Ansar ya silale saman gwiwoyinsa hawaye na gangaro masa, lokaci guda yake furta “Mommy I’m sorry... I lied to you..!” Cikin tsananin sanyin jiki Mommy ta duk’a gabansa itama had’ida furta “Ansar... Mai kake cewa..?!” Cikin zuban hawaye yaci gaba da furta “I lied to you Mommy.. Na miki k’arya.. Nasan yanda Muhibbah take kuma nasan wanda ta aura...!” Cikin tsananin mamaki da sanyin jiki Mommy Ke fad’in “So tell me.. Where is she.. Ina take Ansar.. We need to go get her, tashi muje Ansar tashi muje ka kaini.. I need to see my daughter.. You shouldn’t have kept something like this Ansar..!” Jawo hannunta Ansar yai yana hawaye yake furta “ Mommy I’m afraid we can’t..! Muhibbah Sarki take aure... Abubuwa da dama Sun faru Mommy, na b’oye miki ban sanar dake komai ba.. But believe me I didn’t mean to.. I only want her back in our lives... Mommy I still love her.. So much...!” Ya k’arashe cikin tsananin rauni... Hannunsa Mommy ta kamo tace “Ansar tell me everything..! Ka sanar dani labarin Muhibbah gaba d’aya harda wanda ban bata daman sanar dani ba... Please tell me everything Ansar..!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata.. Cikin zuban hawaye Ansar ke jinjina kai yana furta “Zan sanar dake Mommy.. Everything..!” Lokaci guda Ansar ya soma zayyanowa Mommy labarin Muhibbah tin daga kan abinda su Yazeed sukai mata, har zamanta a sansanin Yalwan Shandam da yanda akai Ta rasa ‘yar uwarta da mahaifiyarta... Har kawo tsintarta da sukai suka taimaka mata... Har zuwa shirinta na komawa Masarauta, da yanda ya taimaka mata ta koma masarauta.. Had’uwarta da ahalin Masarauta harmada Yarima Mahmood, da yanda al’amarin aurenta ya kasance da ta’asan da Giwa tayi a Masarautar da kuma dangantakarda Muhibbah kedashi da ahalin cikin Masarautar... Mommy ta kasa daina zuban hawaye da jin cikakken labarin Muhibbah... Sosai take kuka gumi na tsartsafo mata.. Ansar ya share hawayen da suka kuma gangaro masa yace “Mommy ki daina kuka haka, Muhibbah is safe babu abinda zai kuma samunta da yardar Allah... Gida take cikin ahalinta...!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa dukda hawaye dake zubo masa... Mommy na kuka take furta “Ta yaya bazanyi kuka ba Ansar da jin irin wannan al’amari... Ta yaya bazanyi kuka ba... Ban baiwa Muhibbah dama tamin bayani ba nabi zugan Gudidi da Yawale.. Ta yaya bazanyi kuka ba Ansar...!!” Ta k’arashe tana mai kuma fashewa da sabon kuka... Ansar ya jinjina kai yace “But Farin ciki zamuyi yanzu Mommy, Muhibbah ta samo asali, ita d’in ‘yar asali ce d’iyar masu mulki ce.. Duk wad’anda suke mata girin asali it turned out ita d’in ta fisu asali... Mommy baki ganin abin muyi mata murna ne..!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi.. Murmusawa Mommy ma tai tace “Haka ne... Dole nayi ma d’iyata Farin ciki dukda cewa bazamu kuma irin rayuwar da mukayi tareda ita a baya ba... Ta sami asalin ahalinta, Sannan tayi aure yanzu ta auri d’an uwanta na jini kuma mai mulki.. Ita d’in mai mulki ce da mai Mulki ta dace..!” Take annurin dake bisa fuskar Ansar ya d’auke cak... Ya dubi Mommy yace “No mommy, she’s coming back to us.. She’s not staying there.. She’s mine Mommy..!” Ya k’arashe yana sakin huci.. Da tsananin mamaki Mommy ke dubansa, lokaci guda take furta “Kar na sake jin kalma makamancin wannan daga bakinka... Ina karatun naka yake..? Ina hankalinka yake..? Matar wani kake cewa ita d’in taka ce..? Ansar kana cikin hankalinka..?!” “Mommy ina cikin hankalina.. He took her against her will dan haka dole ya sakar min ita... ita d’in tawa ce..!” Baikai aya ba yaji sauk’ar lafiyayyar mari a fuskarsa.. Ya d’ago dafe da k’uncinsa da tsananin mamaki yana duban Mommy dake ci gaba da sakin huci... SameenaAleeyou 📚 [10/3, 5:48 PM] Sameena Aliyou: *MUHIBBAH* *83* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Mommy kan na fad’i gaskiyar abinda Ke zuciyata..?” Ansar ya furta har lokacin dafe yake da k’uncinsa.. “K’warai kuwa, kuma idan ka sake furtawa zan k’ara maka wani marin.. Shashasha kawai maras hankali...!” “But Mommy ko ban fad’i ba auren nasu ba k’argo zai ba..!” Mommy ta katsesa da fad’in “Anya Ansar kana cikin hayyacinka.. Maiyasa zakace haka..?!” Silalewa yai ya zauna saman kujera yana mai furta “I did something terrible Mommy... Worse than wanda kikaji..!” Cikin bugawan zuciya Mommy Ke tambayarsa “What did you do Ansar..? Ka sanar dani..!” Ya d’ago idanunsa masu zuban ruwa yace”Mommy na fad’awa Muhibbah k’arya da gaskiya akan Mahmood gameda yanda aurensu ya kasance.. I badmouthed him, na Fad’i abubuwa da dama gameda Shi.. And what’s worse nayi teaming up da ex girlfriend d’in Mahmood kuma matar Yazeed dan mu raba auren Muhibbah da Mahmood..” Ya k’arashe cikin zuban hawaye.. Baki sake Mommy Ke dubansa lokaci guda take girgiza kai tana furta “Ansar.. You did all that.. Why Ansar..? Maiyasa zakayiwa Muhibbah haka..?!” Cikin zuban hawaye yake furta “Because I still love her Mommy.. I couldn’t get over her... Shiyasa na zab’i na bi ko wani hanya domin na rabata da Mahmood...!” Girgiza kai Mommy take cikin rashin yarda da abinda takeji daga bakin Ansar “Shiekenan ka zama shed’an mai datse igiyan sunnan ma’aiki...!” “Mommy shaid’an fah kikace min...?!” “Yo Ka zama Shaid’ani mana..A cikin shaid’anun ma Babba mai datse aure... Ta yaya zaka zab’i ka rabata da nata Farin cikin don samuwar Naka Farin cikin..? Haba Ansar..? Haba.. How could you do something terrible like this... Wanann ba tarbiyarka bane... Kai banda shashanci ma irin naka ina ka tab’a jin sarki ya saki mata wani ya aura.. Wanann ai raina Sarki ne da sarauta ma kake.. Wanann magana ya isa fa Sarki ka kuka da kanka, domin kuwa duk abinda yai maka kai da kanka ka saya da kud’inka.. Har zaka biye wata can ku k’ulla makirci irin wanann...Wannan shiririta da yawa take... Kuma idan har kana son Muhibbah kaman yanda kace ai zaka barta ta samu farin cikin da bata samu ba baya tsawon rayuwarta.. Kana wajen kaga komai kaga gwagwarmaya da fad’in tashin da shi Mahmood d’in yayi dan ya ceci rayuwarta amma duk kayi biris ka k’ek’ashe idanu ka sanar da ita k’arya da gaskiya.. Allah na tuba da ace ba shine ya aureta ba ince da yanzu bamuSan duniyar da Yawale ya aikata ba, amma da shike batada hakki sai Allah ya turo masoyinta kuma jininta ya aureta ya maidata gida cikin ‘yanuwanta, haka Allah yake al’amarinsa idan har mutum baida hakki toh sai ya kawo masa mafita ta yanda bai tsamman ba.. A duk labarin da ka fad’i Sarkin nan ya fika k’aunar Muhibbah Ansar... Ya soma k’aunarta ne tin had’uwarsu Ta farko... K’addarar rayuwa ta rabasu., idan ma wa ta soma sani ne ai shi ta soma sani kafin kai...Tashi muje..!” Ta k’arashe tana mik’ewa tsaye... Ansar ya dubeta a sanyaye yace “Ina zamuje Mommy..?” “Masarautar zamuje ka warware abinda ka k’ulla..” Ya shafe fuskarsa a hankali yace “Mommy Idan Sarkin nan yasa aka fille min wuya fah..?!” “Oho maka wanann kuma ai kai ka siya da kanka, wayace ka shiga hurumin da ba Naka ba, waye ka shigar masa gonansa, ai duk hukuncin da yanke maka kai ka siya da kud’inka... Kuma tafiya masarauta babu fashi..!” “Wai yanzu yanzu zamu tafi Mommy..?” Ya kuma tambaya jiki a sanyaye “Maimaita maka kake so nayi.. Ka tashi nace, ai sanda kaso tafiyarka baka tina yamma tayi ba, dan haka yanzu ma Jos zamu tafi babu b’ata lokaci... Zan shiga nayi sallama da Hameedah da Larai kafin nan ka shirya kaima ka fito..!” Jinjina mata kai kurum yai zuciyarsa na tsinkewa, Allah ya gani baisan da wasu idanu zai dubi Muhibbah ba bayan k’arerayin da ya Fad’a mata gameda Mahmood.. Sannan ya tabbata idan sukai idanu hud’u da Mahmood d’in ya kumaji abinda yayi toh fah kashinsa ya bushe...Da k’yar ya mik’e ya soma shiryawa... Har wajen Mota Hameedah taiwa Mommy rakiya.. Ansar yana ganin yarinyar yai kaman zai kauda kai Mommy na tsaresa da idanu... Ga mamakinsu yau d’in har sallama yai mata.. Nanda nan suka d’auki hanyar Masarauta.. ** MASARAUTA Kishingid’e Zahra Ta samesa a parlorn nasa alamun yana jiran k’arasowarta... Sallama saman bakinta ta shigo cikin parlorn cikin tsananin sanyin jiki, gaba d’aya tinda Muhibbah ta sanar da ita aurensu da Paa d’inta na kwanaki k’alilan ne sai ta koma wata sukuku da ita, gani take shikenan zasu rasa Muhibbah ma zata fice daga cikin rayuwarsu gaba d’aya... Ta risina a hankali ta gaishesa bayan ta duk’a nan gabansa... Mahmood yai mata K’uri yana karantar ta, ko bata furta ba yasan akwai abinda yake damun d’iyar tasa... Saida dak’ik’ai kad’an suka d’an shud’a kana ya bud’e murya ya kirawo sunanta.. Ta d’ago a hankali had’ida amsawa.. “Akwai abinda Ke damunki ne..?” Ya tambaya yana dubanta.. Jiki a sanyaye Ta girgiza kai tace “A’a Paa babu komai..!” “Are you sure..?!” Ya kuma tambaya cikeda kulawa... Ta kuma jinjina kai cikin tsananin sanyin jiki da tausayin Mahaifin nata, tasan dole ce tasa zai rabu da Muhibbah amma yana matuk’ar k’aunarta... Muryar Mahmood ya katse mata tianin nata sanda yake ci gaba da furta “Zahra, tarihin rayuwarmu zai iya canzawa gaba d’aya.. Inaso Ki sani a yau d’in zaki samu wasu amsoshi da kika jima kina nema tsawon rayuwarki..!” Ya k’arashe yana mai janyo wata doguwar envelope fara k’al... Gaba d’aya Sai Zahra tama rasa mai yake fad’i, tunda taga ya janyo doguwar takardan nan tasan bazai shige takardan sakin Muhibbah bane... Shiyasa yace labarin rayuwarsu zai kuma canzawa... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un, Muhibbah gaskiya ta fad’i mata da tace aurensu da Paa d’inta bazai k’argo ba.. Gashi nan kuwa hakan ya tabbata... K’ok’arin saita kanta ta d’anyi dan bata so ya fahimci tasan wani abu, muryarsa ne yankatse mata tinaninta “Zahra..!” Ya ambato sunanta cikin dakewa... Lokaci guda ya mik’a mata doguwar takardan yace “Make sure kin damk’a mata a hannunta...!” Bata amsa ba Sai tsananta fad’uwa da gabanta yake, tana son tambayarsa takardan ta Mecece amma yin hakan ba huruminta bane, wace ita ma da zata bud’i baki taima Mahaifinta tambaya makamanciyar wannan.. Ta kuma sinkayo muryarsa cikin dakewa yana furta “Karb’a mana..!” Jiki a matuk’ar sanyaye, hannunta na tsananin rawa Ta amshi envelope d’in da duka hannayenta biyu... Mahmood yai gyaran murya ya furta “Tashi kije, ki bata hannu da hannu sak’o ne mai matuk’ar mahimmanci ciki wanda ban amince wani Ko wata cikin Hadiman gidan nan su bata ba face ke.. Dan haka kar kiyi wasa dashi Kin fahimta..?!” Ta jinjina masa kai a hankali tace “Na fahimta Paa...!” Lokaci guda ta kuma neman izinin tafiya yace tana iya tafiya kana ta mik’e jiki a matuk’ar sanyaye Ta nufi k’ofa.. ** Koda suka isa nan suka sanar sud’in bak’i ne zuwaga Gimbiya Muhibbah sannan wasu Dakaru daga cikin masu tsaron babban gate d’in Fada sun gane Ansar, hakan yasa ba’a wani tsaya tsananta bincike akansu ba.. Aka had’a Mommy da wasu Dogarai guda biyu sukai mata rakiya cikin Fada, a wani parlorn sauk’an bak’i aka sauk’i Mommy kafin aka tura wata Hadima taje ta sanar da sak’on bak’uwa da Gimbiya Muhibbah kedashi... Koda sak’on ya isa ga Muhibbah batai zaton Mommy bace, sanin cewa bata wani San mutanen garin sosai ba ya sanyata tinanin ko daga inane bak’in nata.. Da wannan tinani ta nufi parlorn bak’in.. Ga tsananin mamakinta Mommy ta gani.. Aiko sunan ganin juna Muhibbah ta taho a guje ta rungumeta... Suka rungume juna suna hawaye... Ai tuni Muhibbah tace ta k’araso daga ciki, sashenta suka nufa suka k’ule a d’aki suna kukan yaushe rabo... Nan Muhibbah ke sanar da Mommy watak’ila su koma tare idan har Mahmood ya sawwak’e mata... Aiko nan Mommy ta gyara zama ta ambato sunanta, Muhibbah ta amsa cikin sanyin jiki “Dama maganar ya kawo ni, dan ko ruwa bazan sha ba zan amo dashi... Sannan koda ace kina matsayin Gimbiya kuma Sarauniya ni zan miki fad’a a matsayinki na d’iyata..!” Gaban Muhibbah ya fad’i tana mai duban Mommy da Ta had’e rai sosai, cikin rawar murya tace “Mommy mai nayi.. Kema kina zaton zan maku butulci ne..?!” Kasteta Mommy tai da fad’in “Ashe bakida hankali ban sani ba..?” Ta d’ago idanunta da sukai rau rau tana duban Mommy... Mommy taci gaba da fad’in “Ansar ya sanar dani komai kuma banji dad’i wannan rashin hankali da yayi ba.. Yau idan mun taimakeki sai kin saka mana.. Idan akace haka za’ake taimako don a rama maka abinda akai maka mai sunan abin kenan.. Ashe ba wajen Allah kake neman ladanka ba kenan..! Muhibbah Ansar ya fad’a miki k’arairayi ne kawai dan ki dawo cikin rayuwarsa amma ba gaskiya bane.. Mahmood masoyinki ne Muhibbah domin kaw ina mai tabbatar miki badon Allah ya k’addari aurenku ba da yanzu bamu San waye Yawale ya aura miki ba..!” Muhibbah da gabanta yai wani irin tsinkewa ya fad’i d’agowa tai tana duban Mommy dake ci gaba da karanto mata duk yanda al’Amara suka kasance... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa wasu irin hawaye suna gangaro mata.. Abubuwan sai suna Zuwa kanta daki daki... Mommy ta k’arashe da fad’in “Koda wasa kar inji kin kashe aurenki akan shiriritar banza kinji koh...!” Girgiza kai Muhibbah take tana hawaye take furta “Mommy I’m afraid it’s too late...! Mommy any moment Rankaidad’e zai iya sauwak’a min..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya.. Baki sake Mommy Ke dubanta “Ban fahimceka ba Muhibbah..!” Cikin rawar murya Muhibbah ta sanar da Mommy yanda sukaida Rankaidad’e... Mommy ta shiga tafe hannaye tana salallami... Yanzu duk yanda nake ganinki mai wayon nan Ashe ba haka bane.. Ina tunaninki ya tafi Muhibbah da har zakiyi irin wannan yarjejeniya da mijinki... Kin kuwa San girman zunubin mace Ta bud’i baki Ta nemi saki daga wajen mijinta..? Haba Muhibbah.. Ina karatunki ya tafi..?!” Cikin zuban hawaye take furta “Mommy banso na cutar da kowa, a tunanina Ansar bai cancanci abinda Rankaidad’e yai masa ba.. Dan duk abinda kika sanar dani is a total opposite da wanda ya sanar dani.. I was so confused Mommy, dan Allah kada kiga laifina..!” Ta k’arashe cikin zuban hawaye murya na rawa sosai.. Bata ida rufe baki ba Hadimarta ta nemi izinin shigowa ta risina ta sanar da ita shigowar sak’on Gimbiya Zahrau wacce Ke zaune parlor tana jira.. Muhibbah dake k’ok’arin saita kanta, share hawayen da suka wanke mata fuska tai kana taceda Hadimar tana nan tafe... Hadimar ta risina Tai godiya kana ta fice... Jim kad’an Muhibbah ta fito waiting room d’in yanda Zahra Ke zaune saman wasu kujeru na alfarma tana jiran fitowarta... Fuskar Zahran kad’ai Muhibbah ta gani ta fahimci babu lafia, domin kaw ta hango tsagwaran tashin hankali kwance saman fuskar nata.. Tasan bazai shige fushin da take da ita bane... Murmushin k’arfin hali saman fuskarta Ta k’arasoga Zahran... Saidai bata kaiga furta koda kalma guda ba Zahran ta mik’a mata envelope dake rik’e hannunta tana mai furta “Paa yace na baki wannan..!” Muhibbah ta dubi Zahra da mamaki Ta kuma dubi takardan da take mik’a mata zuciyarta na tsananta bugawa... Bata amsa ba saima duban Zahra data kumayi tana mai furta “Wannan kuma fah Zahra..?!” A hankali Zahra ta girgiza kai tace “I’ve no idea, he just asked me to give it to you..!” Lokaci guda Muhibbah ta shiga girgiza kai tana mai furta “Ni kuma..? Rankaidad’e..?” Zahra ta kamo hannunta guda ta damk’a mata takardan cikin tafin hannunta.. Lokaci guda take furta “Bansan mai takardan Ke k’unshe dashi ba, amma ga dukkan alamu k’unshe yake da abu mai mahimmanci tinda har ya tsallake Hadiman gidan nan ya bani umarnin na kawo... Watak’ila burinki ya cika miki cikin Takardan nan..! Ina miki fatan alkhairi.. Tia..!” Tana ida fad’in haka bata kuma tsayawa sauraren wata kalma daga Muhibbar ba tai saurin sa kai tana matsan k’walla... Muhibbah dake tsaye wajen tamkar wacce ruwa ya shanye duban Zahra kurum take har ta b’acewa ganinta tana rik’eda takardan dake rik’e cikin hannunta.. Cikin tsananin bugun zuciya ta sauk’oda idanunta masu zuban ruwa tana duban takardan tana kuma juyasa Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Takardan Saki Rankaidad’e ya bata,shikenan ya sauwak’a mata kaman yanda yace idan taci jarabawar zai sauwak’a mata... Batasan sanda sanda kuka ya kufce mata ba... Ta nufo cikin d’aki afufujajan tana kuka take fad’ida Mommy “Mommy Rankaidad’e ya sawwak’e min, shikenan ya rabu dani Mommy... Mommy dan Allah kice masa na fasa banso naci jarabawar kuma..!” Cikin tsananin kuka take maganar dunk’ule da takardan a hannunta... Mommy Ta taso da sauri ta rik’eta tana tambayarta ta nastu ta sanar da ita abinda ke faruwa.. Inaa kuka kurum Muhibbah take.. Lokaci guda Ta mik’e ta nufo waje da gudu alkyabbarta na biye da ita tana shek’ar kuka.. Babu shiri Mommy ta mik’e ta biyo bayanta.. Hadimanta suna tambayarta “Rankidad’e meke faruwa..?” Bata tsaya basu amsa ba suma ta shigesu tana mai ci gaba da kukanta ta nufi sashen Gimbiya Turai... Kan cinyarta ta fad’a tana kuka sosai dunk’ule da takardan a hannunta take fad’in “Ummi dan Allah kice masa na fasa, wllhi banson lashe jarabawar kuma..! Dan Allah Ummi kice masa yayi hak’uri ni na fasa yarjejeniyar..!” Gimbiya da bata fahimci yanda Muhibbah ta dosa ba, d’agota tai tana kuma tambayarta abinda Ke faruwa.. Tace “Ki natsu kimin bayani Saudah, Wai meke faruwa..? Ina Sarakin yake..? Mai kuma ya faru yanzu..?!” Cikin kuka Muhibbah Ke fad’in “Ummi cewa yayi ya sauwak’a min...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana... Gimbiya Turai ta shiga karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.. Ta kuma duban Muhibbah dake matsan hawaye tace “Shi ya sauwak’a miki..?!” Cikin kuka ta kuma jinjina kai ba tareda ta iya furta komai ba sabida tsananin rawa da muryarta keyi... Gani kawai sukai Gimbiya ta mik’e ta fice cikin tsananin b’acin rai... Muhibbah ta rarrafa kusa da Mommy ta kwanta saman cinyarta tana ci gaba da shek’ar kukanta har lokacin takardan damk’e yake cikin hannunta... Mommy sai bata baki take tana calming d’inta amma kaman cewa take ta k’ara, tinanin ‘yan kwanaki biyun da sukai matsayin ma’aurata take.. Beautiful moments da suka tsinci kawunansu ciki a ‘yan kwanakin gashi yanzu shikenan ya zama tarihi Rankaidad’e ya kufce mata na har abada, domin kuwa a tsarin Sarki baya komen mace, idan ya sauwak’a mata kafin nad’in sarauta shikenan bayan nad’in sarauta bazai kuma dawo da ita ba.. Sabon kuka ya kuma kufce mata labarin yanda al’amarin aurensu ya kasance da Mommy Ta sanar da ita na kuma Yawo a kwanyarta, Rankaidad’e is her savior, tin daga fari shi ya soma tsintarta a lokacin data b’ace ranan bukin sallah kuma badon Allah ya k’addari su Yazeed sai Sun cutar da ita ba tabbas da Rankaidad’e bai Tafi ya k’yaleta taredasu ba.. Sannan ya kub’utar da ita a hannun Yazeed a lokacinda yaso lalata mata rayuwa a karo na biyu.. Bayan wanann ya kub’utar da ita a hannunsu Giwa da Jamal wanda shima Jamal d’in yaso kuma lalata mata rayuwa a karo na biyu... Gashi da taimakon Allah shi ya kub’utar da ita bai bari Yawale ya aurarta ga duk sharan da yaso ba... Shin tayaya zataso rabuwa da irin wannan miji wanda a kullum burinsa shine ya zamto mata katanga... Shid’in ya zamto tamkar garkuwa ga rayuwarta.. Maiyasa bazatayi kukan abinda tai masa ba.. Tana tsaka da kukan taji hannayen mutum saman arms d’inta.. Cak ta had’iye kukan nata sakamakon jiyo dadd’an k’amshinsa da tai wanda yayima k’ofofin hancinta sallama... Mahmood ya mik’ar da ita tsaye, har lokacin bata daina ajiyan zuciya ba, ta kuma kasa d’ago idanu ta dubesa.. Mommy ta mik’e sad’af sad’af ta fice ta basu waje, kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Hadimar Gimbiya Turai taceda Mommy ta biyo bayanta dan Tuni Gimbiya tace ai mata iso... Parlorn ya rage saura Mahmood da Muhibbah, kanta saman k’irjinsa ta kasa d’agowa sai ajiyan zuciya da take... Kaman mai rad’a yake furta “Maiyasa kike kuka, ba Abinda kike so na baki ba..?!” Kasa cewa komai tai dan har lokacin ajiyan zuciya take... Mahmood yaci gaba da fad’in “Na cika miki alk’awarinki na baki abinda kika jima kina so ..!” Sai Sannan ta d’ago pale eyes d’inta ta dubesa, shid’inma ita yake duba, lokaci guda yace “Oya open it.. Bud’e ki karanta dan nasan baki karanta ba...!” Yanda Yai maganar a tsare ya kuma sanyar mata da gwiwa, Ta mak’e masa kafad’a tace cikin rawar murya.. “Ni banaso naci jarabawar..!” Sosai ta basa dariya amma ya tsime yace “Don’t you want be brave again..?” Ta kuma mak’e masa kafad’a.. Ya murmusa kad’an har lokacin tana cikin k’irjinsa hab’arsa saman kanta da shike ya d’arata a tsawo, lokaci guda yaci gaba da furta “Bakisan cewa Sarki baya sab’a alk’awari ba..? Sunnan Sarakuna ne yin magana d’aya tak.. Dan idanma baki bud’e ba ni zan sanar dake da bakina..!” Hawaye suka kuma gangaro mata, sharad’in saki shine idan bata karanta da idanunta ba ko kuma idan bai fad’a mata da bakinsa taji ba Tabbas bata saku ba shiyasa ma tak’i karantawa.. Muryarsa ya kuma katse mata tunani “Hibbah open that envelope and read now..!” Cikin tsananin dakewar murya yayi maganar.. Tasa bayan hannunta ta share hawayen da suka kuma zubo mata, lokaci guda Ta shiga warware envelope d’in hannayenta na matuk’ar rawa... Zuciyarta naci gaba da tsananta bugawa... Cak Ta tsaya

Chapter 59 of 65