Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
whole thing affects me more, na rasa Aminiyata na rasa masoyina Mahmood, wllhi ji nake rayuwar gaba d’aya ta fice raina..!” Yazeed yace “Munafuka rufe mun baki... Duk kece kika janyo halinda na tsinci kaina ciki, kuma yanzu basai anjima ba zaki fara nadaman aurena da kikayi..!” Yana kaiwa nan ya shiga janyota tana tarjewa tana fad’in mai zai mata.... Ko amsata baiba saida ya d’auko sellotape d’in da yake manne bakin Zuhra dashi idan zai jibgeta danma kar tayi ihu aji... Haka Raheema tana ji tana gani tana zaro idanu waje cikeda mamakin abinda Yazeed ke k’ok’arin yi... “Yazeed no...What are you doing..? Please no..!” Inaa ko saurarenta baiba ya manne bakinta da sellotape d’in ya kuma janyota ya d’aure jikin gado ya shiga jibganta tamkar wanda aka turosa, baiji bai gani dukan Raheemah yake tana runtse idanunta masu zuban hawaye babu hali tayi ihu dan bakinta a rufe yake... Duk wani takaici da bak’in cikin da Yazeed ke ciki akan Raheema ya sauk’esu tass da bugu... Saida yaga kaman numfashinta na neman d’aukewa kana ya sarara mata da bugu .. Yana nunata da bulalar yake fad’in “A nan zaki kwana a d’aure kuma babu mai shigowa balle ya ceceki... ** A b’angaren Muhibbah kuwa sosai taci kuka har Ta gode Allah, tayi tunanin tashi ta gabatar da salloli ko zata sami sauk’in halinda ta tsinci kanta ciki amma sai taci karo da al’adarta tazo mata... Tai saurin mik’ewa tana duba bayan skirt d’inta yanda yayi stain... Ga dare gashi bama tasan ya za’ai ta sami sanitary pads ba, gashi Kuyangin duk basa nan... Ta isa k’ofa tana bubbugawa ko za’ajita amma shiru alamun babu kowa gajeren tsaki tayi Ta komo cikin d’akin tana tinanin abinyi... Closet ta bud’e yanda taga kayyaki ne na alfarma jere cikin closet d’in na kwalliyan mata amma saidai babu alamun sanitary pad a wajen... Ta d’an tab’e baki kad’an ta nufi bathroom d’in dan dole tayo wanka a halinda ta tsinci kanta ciki.... Komai na band’akin abin burgewa ne, ga wani ni’imtaccen k’amshi da yake tashi... Harda Sabon toothbrush da toothpaste aje saman sink Wato dai duk an aje mata kenan, ko wane salo Giwa tazo dashi kuma yanzu oho... Can sama da jacuzzi ta hango k’aton tambarin heart mai furanni ciki an rubuta M&A... Taita nanatawa cikin zuciyarta M&A ko mai hakan yake nufi oho... Batayi using ruwan k’amshin da aka had’a mata ba Sabida yanayin da take ciki, koma bata a wannan yanayin bazata shiga ruwan da bata San wane tsidsabaru bane Giwa ta saka mata ciki... Wa ya sani ma ko ta haka zatai mata nata kisan gillan, ta nufi cubicle dake gefe nan cikin bathroom d’in abinta ta sakar ma kanta shower.... Tana jin ruwa mai d’umin na ratsa cikin kanta da jikinta hawaye na kuma gangaro mata... Ansar kurum take hangowa tasan duk yanda yake yanzu hankalinsa yakai k’ololuwa wajen tashi... A daidai lokacin da take wannan tunani tana hawaye Ansar yana can gadon asibiti yasha drip guda an d’aura masa na biyu yana kuma sha... Mommy da Hameedah zaune gefensa an rasa mai lallashin wani cikinsu.... ** Da mamaki Turaki yake bin wayar nasa da kallo, k’arfe shabiyun dare har ta gauta... Allah yasa yana parlor yana kallo bai shige d’aki ba tukuna... Ya d’aga wayar Rankaidad’e suna gaisawa , daga d’aya b’angaren Mahmood yace “Sanitary pads nake so...!” Turaki ya gyara zama yana nanatawa “Cikin daren nan Rankaidad’e...?!” Mahmood ya jinjina masa kai yace “Eh cikin daren nan...!” Turaki yace “Amma Rankaidad’e baza’a bari zuwa safiya ba...?!” Cikeda k’osawa Mahmood yace “It can’t wait till morning... Yanzu nake so..!” Turaki ya murmusa kad’an yace “Toh an gama Rankaidad’e..!” Mik’ewa yayi ya zari car keys d’insa ya tsaya a manyan store’s da yasan zai samesu a bud’e komin daren, ya saya ya nufi Fada dashi.... A parlor ya tadda Mahmood d’in alamun isowarsa yake jira... Kasancewar dare ne yana damk’a masa bai wani zauna ba ya juya abinsa... Mahmood kaw da kansa ya nufi b’angaren dan Dama sashensa da yayi zaman aure da Aliya nan ya aje Muhibbah ciki, yanada mabud’an ko wani k’ofa a sashen... Abinka da dare k’afa ya d’auke babu wanda ya kula da fitowarsa har ya isa shashen... Da mabud’an hannunsa yayi amfani ya bud’e ko wacce k’ofa har ya isa d’akin da Muhibbah take... Yayi tsaye yana jin yanda ruwa Ke zuba daga bathroom alamun har yanzu dai bata fito daga wankan ba... Can gefe ya hangi abincin da aka kawo mata ko tab’awa batai ba, babu abinda taci ko ruwa bata sha... Yasan bazai wuce tsoro takeji ba, hannu yasa cikin aljihun jallabiyarsa ya ciro ‘yar k’aramar pen ya isa jikin paper bag d’in yayi rubutu... Ita kaw Muhibbah har lokacin tunanin Ansar da Mommy take hawaye na ci gaba da zuba mata tasan dukansu biyu hankalinsu ba’a kwance yake ba da tashinta duk yanda suke... Duk azzalumin da ya d’aukota ya aje a nan ya cuceta ya kuma cuci ahalinta, har abada bazata tab’a yafe masa koma wanene.. Balle ma tasan Bazai wuce aikin Giwa azzaluma ba, tasan wani tanadin mugunta take mata, kafin Ta cimma burinta akanta zata San yanda zatayi ta guje daga wannan kurkukun da izinin Allah... Tana wannan tunani Ansar yana can ya kuma bud’e idanunsa ya dubi Mommy ya dubi Hameedah... Mommy Ta taso da sauri ta dafasa tana fad’in “Ansar a kira Dr ne... Ansar d’ah na talk to me..!” Lumshe idanunsa ya kumayi sai yace “Mommy Muhibbah... Take me to her... I want see her... Please take me to her...!” Tin daga haka bai kuma cewa komai ba sai kuma rufe idanunsa da yayi... Kukan da Mommy Ke k’unshewa ya kuma kece mata... Kuka take tana fad’in “Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Oh ni Murjah yau naga takaina... Na halak’a d’ah nah da kaina...! Ansar duk abinda ya sameka Bazan tab’a yafewa kaina ba... Domin kuwa ni ce sila..!” Ta k’arashe cikin kuka sosai... Hameedar ma kuka take sosai Ta isa Ta dafe hannun Mommy tace “Mommy Kiyi hak’uri in sha Allah Ya Ansar zai sami lafiya, ki daina fad’in maganganu haka... Bawa baya wuce k’addrarsa a rayuwa..! Allah ya k’addari hakan sai ya faru.. Kiyi hak’uri kiyi masa addu’a kinji mommy... Addu’arki shi Yafi buk’ata a yanzu..!” Jinjina kai kurum Mommy take bata ko iya amsa mata, Yarinyar ta kamo hannun Mommy ta k’araso da ita saman sofa dake daga can gefe cikin d’akin tace “Mommy ki kwanta a nan, kinga Kema d’azu Dr yace jininki ya hau, ya kamata ki huta Ya Ansar baziji dad’i ya tashi yaga kema kin kwanta rashin lafiya ba.. Ki huta Kinji mommy..!” Ta k’arashe tana taimakawa Mommyn ta kwantarta... Hameedar bata bar gefen Mommy ba har saida taga Ta lumshe idanunta irinta mai bacci.. Ta mik’e ta komo kusan Ansar Tai masa K’uri hawaye na ambaliya a fuskarta... Lokaci guda take masa fatan samun lafiya had’ida sauk’in al’amarin da suka tsinci kansu ciki gaba d’aya... ** Koda Muhibbah ta fito mamaki ne ya cikata ganin shopping bag aje saman gado, kaman mai jin tsoro haka ta isa jikin ‘yar jakan... Gabanta sai fad’uwa yake dan a iya saninta Kuyangin sun tafi bacci Toh waye ya shigo ya aje wannan jakan... Tsoro ya kuma kamata, Ta shiga ‘yan waige waige bataga kowa ba... Toh kodai kuyangin basu tafi bane..? Ta lek’a cikin jakan a hankali nan taga sanitary pads ne cike cikin ‘yar jakan... Gabanta ya kuma tsinkewa... Ya akai Kuyangin suka San tanada buk’atan wannan... Saikace masu aiki da iskokai... Kodai matsafan Giwa ne suka sanar da ita..? Toh amma Maiyasa Giwa bata fara mata azaba ba har yanzu saima treating d’inta nicely da takeyi... Zuciyarta ta raya mata babban ukuba take tanadar miki shiyasa take binki a sannu..! Ta d’ago jakan tana binsa da kallo nan gefe taga wani rubutu mai d’an karan kyau gashi dai da biro akayi rubutun balle tace bugun company ne masu k’era jakan ne suka rubuta... Sam bai yi kama da ace hannu ne ya rubuta ba, abinda aka rubuta shine yafi tafiya da hankalinta.. _Kina tareda kariya a nan fiyeda yanda kike zaton zaki fi samun kariya.. Rashin cin abincin ka iya janyo miki rashin lafiya_ Ta karance sak’on yafi sau abinda yafi... Tinda ta tab’a jakan hannunta ya kamata k’amshin dake jikin jakan... Ta rasa a ina tasan irin k’amshin kuma wannan k’amshin shine taji duk ya dabaibaye jikinta sanda ta farka a bacci... Tasan irin k’amshi but she couldn’t figure out ina tasan k’amshin... Wani ikon Allah bayan karance sak’on nan da tai sai taji natsuwa ya d’an sauk’o mata kad’an, Ta d’auki bag d’in ta bathroom dan kintsa kanta... Lallausar doguwar riga ta zira ta bar kanta a bud’e dan ya ida bushewa, k’anan kitson aurenta da aka mata ya bi wuyanta ya kwanta luf... Tinda Ta fito a haka daga closet d’in ya kasa janye idanunsa daga dubanta, hab’arsa d’aure saman hannunsa yake kallon duk wani motsinta yacce kasan mai kallon shirin film da yayi matuk’ar tafiya da hankalinsa da tunaninsa baiso yayi missing koda scene guda ne... Yanda take tafiyar kaman wata mai tsoron taka k’asa haka ta k’araso saman darduman ta zauna a hankali tana mai bin kayan abincin da kallo... Ta hard’e k’afafunta ta zauna tana bud’e dishes d’in... Allah ya gani batada appetite bazata iya cin komai ba... Maida murafen tai ta rufe kana Ta rapka uban tagumi tana duban jerin abincikan dake gabanta... Ji yake bazai iya bacci ba har sai ta tabbata ta saka wani abu a cikinta, duk abinda ya sameta Ta dalilin yunwa zai zamto laifinsa tinda shi ya d’aukota ya ajeta... Ya lumshe idanunsa a hankali yana tunanin kodai yaje ya turasasa mata cin abinci ne... Amma yin hakan na nufin ya tona kansa kuma bazata bari ya fahimci ainihin motive d’inta gameda Masarautar ba harma da rayuwarsa da na d’iyarsa da taso tarwatsawa... Idanunsa a lumshe yake tinanin kaman ance ya bud’e ya dubeta nan yaga Ta janyo farantin fruits Ta lumshe idanunta had’ida furta bismillah a hankali... Nan Ta soma cakalan fruits d’in dan rabonta da abinci tun had’inda gudidi ta bata tace ta shanye kuma idan har tana so ta cimma burinta na gudu daga wannan kurkuku she needs to maintain her strength idan ba haka ba bazata iya guduwa ba dan haka cin abinci ya zamto mata dole koda bata so... Haka Ta rintse idanunta taita tura abincin tana b’ata fuska tamkar mai cin magani... Yanda take da fuskarta sosai yaso basa dariya... Can k’asan zuciyarsa yana jin sanyin ta saka wani abu a cikinta at least, yanzu zai iya kwanciya... Da wannan tinanin ya mik’e ya nufi band’aki ya d’auro alwalais yazo ya tada sallah nafilfili wanda d’abi’arsa ce duk dare before going to bed...! A b’angaren Muhibbah kuwa tunda ta d’an saka wani abu a cikinta bacci ya kuma yin gaba da ita... Nan cikin baccin nata take mafarki da Mahaifinta... Tana kuka tana sanar dashi azzaluman Masarautar Sun kuma kamata zata nemi hanyar guduwa Ta ko wani hali ta gudu... Mahaifinta ya girgiza mata kai yace “Nan shine gidanki Saudatu..! Bazaki bar gidan nan ba... Akwai mutane da suke buk’atar kasancewarki a nan ciki harda k’annenki guda biyu...!” Daga haka Mahaifinta ya b’ace bata kuma ganinsa ba... Da salati saman bakinta ta farka zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Wannan wane irin mafarki tayi da Abbanta... Mai yasa yace nan shine gidanta..? Su waye k’annenta guda biyu... A iyaka saninta batada k’anne... Kuma k’anwarta d’aya ce mai suna MUHIBBAH kuma ta rasu tana jaririya a lokacinda wuta ya cinyesu itada Mahaifiyarsu a sansanin ‘yan gudun Hijira da suka fake a Sansanin dake Yalawan Shandam..! Hasalima sunan k’anwar tata Muhibbah ta maida wa kanta...Toh su waye k’annenta da Babanta yace suna nan cikin wannan masarauta..?!! SameenaAleeyou 📚 SameenaAleeyou📚 *MUHIBBAH* *65* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* NOT EDITED! Ta lumshe idanunta a hankali mafarkin bai b’ace mata a kwanyarta ba, Toh kodai Taswiran nan abinda yake nufi kenan... K’ila akwai wasu mutane b’oye cikin ginin azzaluman cikin Masarautar nan sun b’oyesu Babanta yanaso ta taimaka masu amma baya ga haka bata tunanin akwai wani jininta cikin wannan masarauta... Toh mi zatai menene abinyi gashi ta baro zanen a gida, hasalima batasan yanda ta jefar ba...! Ta dafe kanta a hankali zuciyarta na ambaton Allah ya warware mata wannan al’amari cikin sauk’i... ** Safiyat Washe gari a d’aki Jamal ya tadda Giwa sai faman kaiwa da kawowa take tana sak’awa tana warwarewa... Yau kam jikin Jakadiya da d’an sauk’i dan tare suka shigo da Jamal d’in Dama isowarsu Giwa take jira... Suna shigowa Giwa ta dubi Jakadiya tace “Kin tabbata Zahra’u ce ta baki mayafin nan..?!” Jakadiya ta jinjina kai tace “Allah shi taimakeki wllhi Allah nayi imani Gimbiya Zara’u itace Ta bani mayafin nan..!” Jamal da Giwa suka dubi juna, Jamal zai magana Giwa ta k’araso gabansa tace “Kada ka damu d’ah na kaje kaji da Amaryarka, so nake ka tareda kyakkyawar Amaryarka a yau... Kaga kai sabon ango ne bai kamata wani hidimar ko wani damuwa yasha gabanka ba, I can handle Zahra I promise..!” Jamal yai shiru ya tsareta da idanu sai kuma yace “Maami gobe nakeda ganin Dr a asibiti yace k’afar roba da aka min ya zama ready... Ni a nawa tsarin nafi so idan aka zaka min sabuwar k’afata na tareda Amaryarta dan banaso ta ga k’afata a haka..!” Giwa Ta k’ak’aro murmushi tace “Toh banda abinka Jamal ai a haka da yankakken k’afar taka ta ganka tace tana sonka, Umaima sam bazata damu dan taga k’afar angonta guda d’aya ba dama tasan abinda ta aura ai... So wannan ba abin damuwa bane... Tuni nasa an gyara maku sashen da zaku zauna, an zuba komai na buk’ata ciki... Gida ya tsaru masu shi kawai yake jira...Ni nafi so ka bada himma ga batun tariyarku dan Farin cikinka shine gaba da komai a wajena..!” Ta k’arashe tana shafa b’angaren fuskarsa guda cikeda kulawa wanda zaka rantse har cikin ranta Farin cikin d’an nata ne ya dameta... Murmushi Jamal yayi yana kuma jin son mahaifiyarsa cikin zuciyarsa... Yasa hannu ya damk’e hannun mahaifiyar tasa cikin nashi, ya sumbaci hannun nata kad’an yace “I love you Maami nah.. Ina matuk’ar k’aunarki Rankidad’e..!” Tai murmushi tace “Nima ina matuk’ar k’aunarka masoyinah Farin cikinka shine nawa... I can’t wait naga ‘yan jikokina ‘ya’yanka da Umaima suna guje guje cikin fad’in Masarautar nan...!” Annashuwa da annuri ya kuma cika Jamal, wani irin sanyi yakeji can k’asar zuciyarsa... Bai kuma bin takan batun Zahra ba kaman yanda Giwa ta buk’ata hankalinsa yafi karkata kan cewa daren yau za’a shigo masa da Amaryarsa...! Yana ficewa Giwa ta dubi Jakadiya ta nuna can gefe k’asan file tace ta zauna nan wajen... Babu musu Jakadiya tayi yanda Giwa tace D’aya daga cikin Hadimanta Giwa tasa tai mata kiran Zahra... Jim kad’an Hadimar suka shigo tareda Zahra, Zahran na mamakin dalilin kiranda Giwa tai mata da tsakar safiyan sanin cewa ba sonta Kakar nata take ba... Zahra ta risina ta gaida Giwa... Gani tai Giwar ta amsa mata da sakin fuska, Ta nuna mata gefenta tace tazo ta zauna... Babu musu Zahra Ta isa ta zauna har lokacin da bata gama aminta da yanayin Kakar nata ba... Giwa ta sakar mata murmushi tace “Zahra wata magana nake so muyi..!” Zahra ta k’ak’aro murmushi tana mai jinjina kai ba tareda Ta amsawa Giwar ba... Giwa taci gaba da fad’in “Zahra nace ba... Shin ina kika sami mayafin nan da kika baiwa Jakadiya..?” Zahra ta d’anyi jim sai kuma tace “Mayafi kuma Maami..? Wanne mayafi kenan..?!” Giwa ta murmusa tace “Karki damu Zahra mayafin ne bai cancanta Bayin cikin Masarautar nan su saka ba shiyasa na tambayeki... Kinsan akwai d’abi’u da al’adu na cikin Masarautar nan da har yanzu you’re not familiar with them... Sai a hankali zaki gama fahimtar komai... Zahra Maiyasa kika baiwa Jakadiya wannan mayafin..? Ko Kinsan cewa kin kusan saka Jakadiya cikin had’ari.. Ki dubi yanda ‘yan uwanta bayi sukai mata jina jina duk a dalilin sun ganta da babban mayafi irin wanda bata kamaceta ba... A nasu zaton sata tayiwa iyayen Gidanta..!” Giwa ta k’arashe cikeda kulawa Cikeda tsoro Zahra Ke duban b’angaren da Jakadiya Ke risine, harga Allah sosai Jakadiya ta bata tausayi, bata so kowa ya cutu sabida ita koda kuwa bawa ne k’ask’antacce, ta maidoda dubantaga Giwa tace “But akan mayafi sai su mata irin wannan bugun Maami... Rhis isn’t good Maami, this has stop, bai kamata a barsu suna irin haka ba...Aunty Muhibbah ce ta bani wannan mayafin tace na baiwa Jakadiya kuma itama nasan batasan tsarin Masarautar nan bane da bata bata ba... Lo siento, esto es todo mi culpa..” ( I’m sorry this is all my fault..) Ta fad’i cikin harshen Spanish tana duban Jakadiya da har lokacin kanta a k’asa yake tana haki da k’yar dan Giwa ce ta umarceta tayi hakan.. Giwa ta nanata “Muhibbah..?!” Ji tayi ma batasan waye mai irin sunan ba... Zahra ta kuma Jinjina mata kai alamun tabbatarwa... Jakadiya ta d’ago a zabure jin an ambaci Muhibbah yarinyar da tun zuwanta Masarautar taceda Giwa ita sam bata aminta da ita ba...! Duban Jakadiya Giwa tai Jakadiyar na isar mata da wani da idanu... Giwa ta maidoda dubanta ga Zahra ta murmusa tace “Kina iya tafiya abinki jikata...!” Zahra ta jinjina kai had’ida risinawa kana Ta mik’e Ta fice... Tana ficewa Giwa ta k’araso gaban Jakadiya tana sakin tsananin huci “Jakadiya wacece Muhibbah..?!” Jakadiya ta risina tace “Allah shi taimakeki Muhibbah itace wannan yarinyar da nace miki inada shakku akanta tun farkon zuwanta Masarautar nan... Muhibbah itace bak’uwar Gimbiya Umaima data shigo da ita cikin Masarautar nan..!” Giwa tai shiru tana nazari lokaci guda tana mai ci gaba da sakin huci... Sai yanzu hoton yarinyar ke kuma dawowa kwanyarta... Ta waigo tana duban Jakadiya bata daina sakin huci ba tace “Jakadiya ya zama dole duk yanda za’ayi musan wacece wannan yarinyar Muhibbah da dalilinta na shigowa Masarautar nan...!” Tana ida fad’in haka ta d’auki wayar salulanta ta shiga dialing layin Jamal... ** A b’angaren Zahra kuwa tana ficewa b’angaren mahaifinta ta nufa tana tinanin Maiyasa a ‘yan kwanakin kowa ke son sanin abu gameda Aunty Muhibbah.. Itakam koda kowa zai tunanin Aunty Muhibbah ba mutumiyar kirki bace bazata tab’a yi mata wannan tunanin ba... Ta tabbata she’s a good person... Da wannan tunanin ta isa b’angaren mahaifinta... Tinda ya tashi a bacci yake jiranta Ta Tashi, ko sauk’a k’asa yayi breakfast ya kasa, yafi so sai ya tabbata da Ta tashi taci abinci kafin shima ya sauk’a k’asa yaci abinci... Duk abubuwan da takeyi akan idanunsa, tin daga tashinta daga bacci har shigewarta bathroom dan yin wanka... Sanda Ta shiga wanka shima ya tashi ya fad’a bathroom d’insa dan yin wankan... A tare sukai wanka kowa a nasa band’akin lokaci guda... Koda Mahmood ya fito daga wanka idanunsa akan na’uran yana duban ko yarinyar nan ta fito daga bathroom... Bai mamakin ganin bata fito ba tinda yasan yanayin da take ciki na rashin tsarki.... Yana rik’e da k’aramar towel yana goge sumarsa kaman ance ya dubi na’uran ya hangota ya fito d’aure da towel daidai cinyarta, yau d’in batai amfani da bathrobe kaman yanda tayi jiya ba... Mutuwar tsaye yayi yana k’arewa santala santalan cinyoyinta kallo... Zuciyarsa taci gaba da bugawa... Ya kasa janye idanunsa daga barin dubanta ya kuma kasa ci gaba da abinda yake...! Zahra na nan zaune parlor tana kuma duba agogo tana mamakin rashin sauk’owan mahaifin nata yau har wannan lokacin... Kodai makara ne yayi... Tasan Paa d’inta baya shige irin wannan lokacin bai breakfast ba, Toh kodai hakan nada alak’a da abubuwan dake kan faruwa cikin Masarautar ne, k’ila fushi yake shiyasa har yanzu bai fito ba.. Itakam idan dai akan rashin auren Aunty Raheema ne da baiyi ba tafi kowa Farin ciki da faruwan hakan, koda mahaifinta baiso hakan ba... Ta isa dining area tana duban breakfast d’in nasa shirye saman dining table ko tab’awa ba’ai ba... Ta d’an kuma komawa ta zauna tana mai ci gaba da duba time.. Gaba d’aya sai tana jin she’s responsible for everything that’s been happening..! ** Yana gani ta nufi closet ta zab’o wasu kaya marassa nauyi Ta dawo cikin d’akin da zummar shiryawa, sosai bugun zuciyarsa ya k’aru ganin da gaske zame towel d’in takeda niyyan yi... Daidai nan yaji knocking daga k’ofarsa d’if ya kashe na’uran zuciyarsa bata daina bugawa ba.. Jallabiya kawai ya zira yana mai sinkayo muryar Zahra daga k’ofa tana fad’in “Paa are you there...? Paa..!” Tana maganan tana k’wank’wasawa a hankali kaman mai tsoron kada Ta d’agasa a bacci... K’arasowa yayi ya bud’e had’ida sakar mata murmushi mai kyau... “Buenos dias paa..!” (Barkada safiya Paa) “Buenos días princesa..” (Barkada safiya Princess) Ya fad’i kyakkyawan murmushin bai bar saman fuskarsa ba... “Paa yau ka makara.. Lafiya kuwa.. Espero que todo esté bien con usted..!” (Ina fatan lafiya kake) Fitowa yayi ya nufi downstairs yana fad’in “Todo esta bien cariño..!” (Komai lafiya sweetheart) “Vamos a desayunar ... Sé que aún no has comido” (Muje Mu Karya kumallo dan nasan bakiyi ba tukuna) Tana murmushi biye dashi take fad’in “Por supuesto que todavía no he desayunado..( K’warai banci karin kumallo ba)..” Ta d’an murmusa a hankali sai kuma tace “Ta ya zanci abinci bayan ban tabbatar da cewa Paa d’ina ya tashi cikin k’oshin lafiya yaci abinci ba after all that has happened..!” Ta k’arashe tana mai zama a kujeran dake daga gefe lokaci guda tana mai ci gaba a karantar yanayinsa, batayi zaton zata gansa cikin annashuwa ba bayan duk abinda ya faru na aurensa da Aunty Raheema da bai yuwu ba... Ta d’an muskuta tace “Paa you seems to be in a good mood... I thought zakayi fushi dani na b’ata tsakaninku da Aunty Raheema da nayi...? Paa I’m sorry.. I truly am...!” Katseta yayi da fad’in “Is okay Zahra... Everything is fine.. I promise..!” Zahra Ta d’an d’ago ta dubesa tace cikin sanyin murya “You’re not mad at me..?!” Murmushi ya sakar mata yace “Of course I’m not...! Oya eat your food before it gets cold..!” Ta jinjina kai a hankali tace “Alright Your Highness..!” Suka sakar ma juna murmushi a tare tana mai cakalan abincin kaman tana tsoro... Mahmood na hankalce da ita... Ya zari tissue paper ya goge bakinsa kad’an, har lokacin bai daina karantar Zahra ba.. Saida yai gyaran murya kad’an yace “Princess, is something bordering you... You look a little bit disturbed.. Tell me akwai abinda Ke damunki ne..?!” Sauk’e ajiyan zuciya tai a hankali tace “Paa it’s about Aunty Muhibbah.. Do you remember her..?!” Gyara zamansa sosai yai jin ta ambaci Muhibbah yace “What about her.?!” Zahra ta d’an kuma muskutawa tace “Paa why’s everyone so curious about her this days.. First it was you, and now...Grandma ta kirani asking questions about her.. Paa I believe she’s a good person... But Maiyasa zata bani mayafi tace na bawa Jakadiya ta yafa..!” Zuciyarsa Ta kuma tsinkewa, ya aje spoon d’in da yake juyawa cikin mug yana mai kuma tsareta da idanu... Sosai ya gyara zamansa yace “Tell me everything Zahra... Ta bawa Jakadiya mayafi, kuma ma Ke ta bayar tace ki baiwa Jakadiya..?!” Zahra Ta jinjina kai tace “You remember that day..? Ranan da nace maka ita ta had’a gaba d’aya plans d’inta tace min I should trust her..!” Mahmood ya jinjina kai yace “I remember..!” Zahra taci gaba da fad’in “Paa the truth is that ta bani wannan mayafin tace na baiwa Jakadiya ta saka, idan har Jakadiya ta yafa toh Babu halin ta bini Mu fita tare kaman yanda ka umarta kace Jakadiya tamin rakiya...! Toh na bata wanann mayafin Ta yafa muka had’uda Uncle Jamal yace zai assigning wata Hadima Ta min rakiya sabida Jakadiya zatai masa wani aikin...! Toh sai nace masa he shouldn’t bordered zan sami wata cikin Hadimaina tamin rakiya... Paa believe me I didn’t know an hana Hadiman cikin Masarautar nan yafa mayafi mai kyau... It was never my intention na cutar da Jakadiya... A dalilin wannan mayafin nayiwa Jakadiya Duka an ji mata ciwo Paa... All because of me..!” Ta k’arashe cikin rawar murya.... Sosai ya fad’a duniyar tunani, kenan Ta kuma tabbata Muhibbah tanada agenda d’inta cikin Masarautar nan... Why’s she connected to almost everything that’s been happening...? Farko rayuwarsa da Zahra, Raheema da Yazeed.. Taswiran da Baba Wambai ya basa wanda ya tsinci makamancinsa hannunta...Yanzu kuma harda Jakadiya da Jamal..? And if Jakadiya is somehow involved Toh Giwa ma might also be involved tinda yasan matsayin Jakadiya wajen Giwa... Kuma

Chapter 43 of 65