is this possible, Muhibbah tanada zuciya mai kyau na kasa yarda zatayi abu makamancin haka..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Janyota cikin jikinsa yayi yana mai furta “Is okay my love, kanta Ta cuta, kanta tayima... Yanzu ni abinda nake so dake, ki fad’a min where we can find her... Kinga an sace wa Maami wani abunta mai matuk’ar mahimmanci kuma munada tabbacin yarinyar nan ita ta sace... So tell me a ina take..?!”
Ya k’arashe cikin lallama da kwantar da hankali...
D’ago idanunta masu zuban hawaye tai tace “K’anwar friend d’ina ne a yanar Gizo...!”
Da tsananin mamaki Jamal Ke dubanta yace “Baby Wai kina nufin Ta yanar Gizo kawai kuka tab’a had’uwa shine har kika aminta da ita kika kawota cikin Masarautar nan aka bata masauk’i... Baby how can you be so naive..? People nowadays ba abun yarda bane.. I mean you can’t just meet someone on social media and trust them like that... What if Ta cutar dake.. What if tayi miki wani abun..!!” Ya k’arashe cikin d’aga murya....
Umaima na kuka take fad’in “Yaya believe me wllhi bansan duk haka zata kasance ba, ni da zuciya d’aya nayi... Kuma Dr Ansar mutumin kirki ne..!”
Katseta yayi da fad’in “Dr Ansar...!”
Ta jinjina kanta a hankali, murmusawa yayi kad’an dan yasan tracking d’insa down bazai wahala ba, ko ta accounts d’insa na yanar Gizo zai sami informations akansa yanzu rayuwa tayi sauk’i ta yanar gizo tsaf zaka sami duk bayanan da kake nema akan mutum... Bai kuma cewa komai ba dan baiso ta fahimci shirinsa na zak’ulo wannan likitan yanda ya shiga ya fita... But idan har yanada wani motive d’insa na shiga rayuwar Umaima zai iya amfani da fake accounts dan ya cimma burinsa hakan na nufin kafafen sadarwarsa zai iya zama na bogi... Tunda gashi ita yarinyar itama bogi ce, da alama saida suka shirya sosai kafin sukayi amfani da Umaima suka shiga jikinta dan su cimma burinsu na shigowa cikin Masarautar., wanda duk suka aikata abu makamancin haka zai matuk’ar wahala a kamasu cikin sauk’i, komai nasu na social media zai iya zama bogi... Kwalin likitancin nasa ma zai iya zama na k’arya ne, Ta yuwu yayi haka ne kawai to get to Umaima...Toh meye abinyi...?
Yana tsaka da tinanin abinyi ne ya sinkayo sautin kukan Umaima tana fad’in “This is all my fault... Duk laifina ne, I feel responsible... Maami bata cancanci haka ba, ta min komai na gata a rayuwar nan... Maiyasa wata zata cutar da ita ta dalilina... I need to go see Maami, this isn’t fair..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye... Saurin rik’o hannunta Jamal yayi, ya dafa crutches d’insa ya mik’e tsaye, har lokacin Umaima bata daina kuka ba... Ya d’an rungumeta ta B’angaren k’afarsa mai lafiya, cikin kwantar da hankali yake lallashinta “Baby stop blaming yourself, you’re also a victim here... Ta miki wayo ne kawai irin nasu na frauds, but I assure you daga kan wannan Masarautar bazata kuma cutar da wasu ba... Ki kwantar da hankalinki Kinji...!” Ya k’arashe yana mai zame d’aurin kanta lokaci guda yana shafa sabon kitsonta a hankali, murya can k’asan mak’oshi yake furta “Lets talk about ourselves Baby.. Tunda akayi aurenmu bamu samu mun zauna ba abubuwa sai faruwa suke daga wancan sai wannan, idan muka biye na mutanen cikin Masarautar nan bazamu tab’a samun lokacin kanmu ba..!” Ya d’anyi fasali yana mai tsareta da mayen kallo... Lokaci guda yaci gaba da furta “Kitson nan yayi kyau Sosai..!” Yai maganar yana mai wasa da yatsun hannunsa saman sumar nata...
Gabanta taji yayi wane irin fad’uwa, haka kurum taji tana jin wani irin muguwar tsoronsa dukda kwantar mata da hankali da yake k’ok’arin yi... Take taji jikinta ya d’auki rawa... Zame jikinta tayi kad’an ta janyo headtie d’inta ta rufa kanta jikinta sai rawa yake... Cikin ‘yar daburcewa tace “I need to talk to Maami, I want to make sure she’s fine...!”
Jamal ya kauda kansa gefe cikeda takaici, ya d’anyi k’ok’arin dannewa yace “Princess Maami is fine, you don’t need to worry... Ita d’in tanada zuciya mai kyau, duk wanda ya cutar da ita tura masa aniyarsa take... Zo nan ki zauna abinki...!” Ya k’arashe yana mai kuma janyota kusansa...
Zuciyar Umaima bai daina tsinkewa ba take furta “Dukda haka... Nidai kawai ka k’yaleni naje na ganta... Kuma ma batasan nazo nan ba... Maybe ma tana nemata..!” Ta k’arashe duk a daburce...
Jamal ya d’an lumshe idanunsa kad’an yace “Baby ko tasan kinzo nan ko bata sani ba babu abinda zatace, I’m your husband and you’re my wife..! Babu wanda zai tuhumeki dan kinje d’akin mijinki so ki kwantar da hankalinki kinji koh... We ain’t doing anything wrong...!”
A d’an daburce ta jinjina masa kai tace “I know... But dukda haka nidai nafi so ka k’yaleni naje naga Maami please...!” Ta k’arashe idanunta suna rau rau kaman mai shirin kuka...
Ganin ta rikice gaba d’aya yasa Jamal dafe crutches d’insa ya mik’e yana furta “Alright fine... Ni zanje na gane miki Maamin na kuma tabbatar miki she’s fine... Amma sai kinmin alk’awarin zaki jirani a nan dan bamu gama tattaunawa ba, zaki bani full name d’in likitan nan da garin da yake zama da duk wani information da kika sani akansa... So Kimin alk’awarin zaki jirani naje na dawo..!”
Tai saurin jinjina kai tace “I promise zan jiraka...!” Daga ganin yanda tai maganar zaka fahimci alla alla take ya bar kusa da ita....
Jamal yana ficewa Muhibbah Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Saida Ta Ta bata ya fice kana tasa kai Ta shige cikin parlorn...
Umaima na ganinta ta mik’e tsaye cikin tsananin tsoro tana nunata da ‘yar yatsa take fad’in “You..!!”
**
A can asibiti wajen Fu’ad kuwa Mahmood na isowa likitan ya taresa da batun, damuwa kwance saman fuskarsa yake furta “Dr are you sure Fu’ad yayi magana kuma sunana yake Ta ambato..?!”
Dr ya jinjina kai yace “I’m his psychiatrist, kuma dani dashi mukai magana, I can assure you jikin Fu’ad da sauk’i sosai... Yayi magana yace a kirawo masa kai kai kad’ai yake son maganada shiyasa bamu kirawo kowa a family d’in ba kaman yanda ya buk’ata muka kiraka...! Za’a shigo dashi in a bit...!”
Mahmood ya jinjina kai a hankali tausayin d’an uwan nasa na kuma lullub’esa... Daidai nan kuwa aka shigo da Fu’ad sanye cikin Farin tufafi kaman yanda majinyatan Ke sakawa, nurse d’in da ya shigo dashi na rik’edashi... Mahmood na ganinsa ya mik’e da sauri yana duban yanda Fu’ad d’in ya koma, kodashike yanzu jikin nasa da kyaun gani akan kwanakin baya... Babu tsananin rama irin na kwanakin baya, sai duhu kawai da yayi, harta labb’ansa da tafukan hannayensa duk sunyi duhu wanda bazai wuce side effect na strong magunguna da allurai da yake sha ba..!
Da murmushi saman fuskar Mahmood d’in ya k’araso garesa ya rik’o hannayensa... Fu’ad na d’ago idanu ya dubi Mahmood sai ya fashe da kuka... Lokaci guda ya rungume d’an uwan nasa yana kuka sosai....
Jikin Mahmood yai matuk’ar yin sanyi, rungume Fu’ad d’in shima yayi yana furta “Is okay Fu’ad..! I’m here now..! Kayi shiru kaji...!”
Cikin kuka Fu’ad ke furta “Yaya..! Yaya...!! I’m sorry Yaya...! I’m sorry please firgive me...! I’m sorry I’m sorry I’m sorry...!” Gaba d’aya sai kuma kaman ya dad’a rikicewa dan abinda yake iya fad’i kad’ai kenan....
Mahmood yaci gaba da bubbuga bayansa yana furta “Ya isa haka Fu’ad... Kayi shiru haka nan kaji..!”
Fu’ad yaci gaba da kuka yana girgiza kai yake furta “No..No Yaya..! I’m a criminal..! I’m a criminal... I need to turn myself in...! I don’t belong here Yaya.. Tell them I belong to prison, I need to pay for my crimes..! Yaya naji sauk’i I can turn myself in now.. Mu gudu Yaya, kar mu tsaya a nan, muje ka kaini police station, I need to give my statement... Muyi sauri mu gudu daga wajen nan kar su kuma kulleni...!”
Yanda yake maganar yana zaro idanu yasa jikin Mahmood yin sanyi, da alama dai lafiya bata samu ba...
Mahmood ya rik’esa sosai yana furta “Ya isa haka Fu’ad... You’re not well, magunguna suke baka a nan ba cutar dakai suke ba...!”
Fu’ad yaja hawaye yake girgiza kai yana furta “No Yaya... Kar ka yarda dasu, wllhi ni d’an ta’addane... Dukanmu UKU ‘yan ta’adda ne... Ni Yazeed da kuma Jamal... Even our Mother itama ‘yar ta’addace... We’re all bunch of criminals..!”
Izuwa lokacin Mahmood ya kuma tabbatarwa haukan Fu’ad yakai wani mataki tunda har zai ambaci mahaifiyarsa da sunan ‘yart’adda...
**
A nan parlorn Jamal kuwa girgiza kai Umaima taci gaba da yi tana mai furta “Wllhi idan baki fice ba zan miki ihu macuciya azzaluma kawai.. Kin cuceni kin yaudareni, kinyi amfani dani ki cutar da ahalina..! How could you do this to me...! Tsakanina dake babu komai face alkhairi amma kika zab’i ki cutar dani... Why..? Maiyasa.??!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka...
Muhibbah na girgiza kai yake furta “Duk abinda kika fad’i gaskiya ne... I tricked you, I deceived you... I used you... But idan kikaji dalilaina zaki fahimceni Umaima... Please hear me out first... Kinsaurareni dan Allah..!”
Umaima Ta katseta da fad’in “You’ve got some nerve..! You really have no shame..! Bayan duk abinda kikayi har kinada k’warin gwiwan had’a idanu dani kice zakimin bayani... Mutanen nan da kika zalunta they’re my family.. They’re my everything... I owe them my life... How could you use me to destroy them... How could someone be so ungrateful...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana...
Hawaye na zubowa daga idanun Muhibbah take furta “Kafin na rok’eki ki bani dama nayi miki bayani... Inaso ki bani dama na kub’utar dake daga mutanen da kike zaton ahalinki ne... Inaso ki bani dama na kub’utar dake daga mijin da kike zaton you’re safe around him...! Ki bani dama na kub’utar dake daga auren da kike tunanin an ginasa ne kan Soyayya..! Umaima your life is in great danger.. these people are planning to have you killed... Burinsu shine idan Jamal ya kusanceki Su halak’aki, suyi tsafi dake... Domin su d’in bak’ak’en matsafa ne..! Dik yanda za’ayi kiyi gaggawan ficewa daga gidan nan kafin su cimma burinsu akanki... Umaima babu lokaci, kiyi gaggawan b’arin Masarautar nan...!”
Da tsananin mamaki Umaima Ke dubanta sai kuma tace “Oh ta nan kika b’ullo... Shin ke wace irin azzaluma ce mai sak’a alkhairi da sharri... Shin ke...!”
Batakai aya ba Muhibbah Ta katseta da fad’in “Ki kirani da duk sunan da ya kwanta miki... Amma ki sani ba k’arya nake miki ba... Wad’annan mutanen ba mutanen k’warai bane kaman yanda kike zato... Wad’annan mutanen ruined my life, they destroyed my family... They abused me... Your husband is one of them... Umaima your husband is a rapist, a heartless being...! A criminal who deserve to rot in jail..!”
Cikin wane irin kuka Umaima ta toshe kunnuwanta tana mai furta “Just shut up..! You’re lying... You’re a liar... How could you expect me to believe someone like you... After all the lies you told me... After how you tricked and used me..! How could you expect me to believe a fraud like you..!!”
Cikin tsananin huci Muhibbah ta k’araso ta damk’e arms d’in Umaima dake tsananin kuka tana mai jijjigata take furtawa cikin tsananin karaji itama hawayen ne Ke zubo mata “I’m telling you the truth..! You need to believe me..! This is nothing but the truth..! Mijinki shi ya b’oye Masoyinki na asali Ja’afar k’ark’ashin bak’in kurkuku a ciki masarautar nan...! Jafar didn’t leave you, Jafar bai gujeki ba Umaima Jamal shine ya b’oyesa tsawon shekara guda dan ya raba tsakaninku..!”
Izuwa lokacin sosai jikin Umaima ya d’auki rawa... Tana girgiza kai take furta “No Ja’afar yamin sallama da kansa cewa ya tafi ya bar Masarautar nan... Maiyasa zaki k’alawa Jamal alhakin tafiyar Ja’afar..! What have I ever done to you to make you destroy my life like this..! Mai na miki da tsanani Muhibbah...?!”
Huci Muhibbah take tana dubanta, lokaci guda take furta “Kinaso ki gani da idanunki....! Kinaso kisan mijinki wane irin mutum ne... Zan nuna miki ko shid’in Wanene.... Watak’ila ki yarda..!!” Daga haka bata kuma tsayawa sauraren kukan Umaima ba Ta finciko hannunta suka nufi matakalan benen da zai kaisu d’akin Jamal d’in...
**
Jamal da ya sinkayi tattaunawar Giwa da Jakadiya ba tareda saninsu ba, a hargitse ya shigo cikin d’akin hawaye na zubo masa...
Daidai gaban Giwa ya isa ya tsaya yana wane irin huci yake furta “Kar kiyi tunanin min k’arya dan na riga naji komai..!! Is it true kashe Umaima zakiyi...? Dalilinki na aura min ita shine dan ki kasheta...! How could you Maami... How could you do this to me...! I love Umaima..! I love her with all my heart and soul... Like I’ve never loved someone before... She’s my life Maami... How could you think of taking her away from me...! Just how..!!” Ya k’arashe cikin tsananin d’aga murya yana mai jijjiga Giwa dake tsaye gabansa tana hawaye....
Lokaci guda Jamal yaci gaba da fad’in “I’ve done everything for you... I’ve become a Criminal duk saboda Ke da k’ok’arin miki biyayya dan cikon burinki... Nayi fyad’ewa k’anan ‘yan mata sunfi a k’irga duk sabida ke... Wad’annan duk basu isheki ba sai kin d’auke mi mace d’aya tak da nake so...! Maami how could you do this to me.. Answer me Giwa...!!” Ya k’arashe jijiyoyin jikinsa na kuma mimmik’ewa...
Cikin kuka Giwa Ke furta “Komai sabida ku nakeyi Jamal, ka yarda dani I’m doing all this for you... Wllhi sabida kai da ‘yan uwanka nake komai...!”
“Shut up..! Just shut up, I’m tired of listening to all this...! You know, I should never have obeyed you from the very beginning... Duk abubuwan da kike shiryawa no one ever works... Maiyasa hakan bai isheki ishara ba... You’re the reason why our family is going through all this... You tormented Fu’ad, Kin haukatasa, kin raba Yazeed da family d’insa... Kin hana Ya Mahmood samun farin cikinsa... I know you’re behind all that I listed.... And now the only person da ta rage a rayuwata kina nema ki d’auke min ita...! Wllhi kinji na rantse bazan barki ki aikata hakan ba... I’m leaving this place together with my wife.! Bazan tsaya cikin Masarautar nan ba and go down with you... Zan d’auki matata muyi nesa da Masarautar nan and start a fresh...!”
Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice... Giwa na kiransa inaaa ko tsayawa baiba balle ya saurareta...
**
Drawer mai k’yallaye d’aukeda jini Muhibbah Ta soma janyowa idanun Umaima suka sauk’a kan fararen k’yallayen... Jikinta na matuk’ar rawa ta shiga warwaresu tana ganin jini had’ida sunayen mata rubuce jikin k’yallen... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa... Ita kaw Muhibbah data tabbata Umaima taga abinda zai sa ta aminta da duk abubuwan da take fad’I mata tuni ta soma neman muhimmin abinda ya shigo da ita... Aiko tana d’aga bakin katifa taci karo da Taswiran...! Ta saki murmushi a hankali tana mai furta “Alhamdulillah..!” Bayan duk tsawon lokacin nan Taswiran guda uku sun fad’a hannunta....
Ita kaw Umaima tsaye tayi da k’yallayen tana duban abin mamaki, jiri na neman kada ita... Daidai lokacin sukaji an banko k’ofa an shigo... Karaf suka d’ago idanunsu suna kallon wanda ya shigo.....
*MUHIBBAH*
*68*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Koda Babba cikin kuyangi masu kula da b’angaren Muhibbah ta shigo mamaki ne ya cikata ganin Hasiya sanye da Kayan Muhibbah... Ta k’araso cikin tsananin tashin hankali tana furta “Ke Hasiya lafiya na ganki da kayan Gimbiya...! Mai hakan yake nufi..? Ina ita Gimbiyar...?!”
Hasiya tai rau rau da idanu tace “Bata nan ta amshi tufafina ta saka kuma ta gudu...!”
Kuyangar ta dafe kanta tana furta “Shikenan Hasiya kin kashemu.! Ta yaya kika amince da hakan.. Hasiya kin kuwa San tashin hankalin da kika jefamu ciki.. Yanzu mai zamu sanar da Rankaidad’e..?! Wata k’arya kike so muyi dan kare kanmu...?!”
Hasiya tace “Ni taimakonta nayi dan tana buk’atar taimako amma ai ga tufafinta jikina ki barni na zauna nan cikin d’akin nata a matsayin ita Gimbiyar idan Rankaidad’e yazo sai na rufe fuskata... Amma idan ba haka ba bana tunanin munada wani mafita dan na tabbata Gimbiya tayi nisan da bazamu cimmata ba..!”
Sauk’e ajiyan zuciya Kuyangar tayi tace “Idan hakan baiyi aiki ba Hasiya kin sakamu a uku dan alhakin b’acewar Gimbiya zai rataya ne a wuyarmu..!” Ta k’arashe damuwa k’arara saman fuskarta...
**
Jikin Umaima ya d’auki rawa, yanda taga fuskar Jamal ba k’aramin firgitata yayi ba, gaba d’aya ta rasa gane wacce duniya take sai rawa da jikinta keyi... Ko motsa ‘yar yatsar k’afarta ta kasa sai tsananin tsoro da ya lullub’eta, ga wani irin b’ari da illahirin jikinta keyi...
Muhibbah kaw rabin idanunta naga kwalban turare dake bisa dressing mirror rabi na kan Jamal dan bataso tayi losing sight d’insa tasan yana iya masu komai yanda Ta hango fuskarsa a matuk’ar dame..!
Murmushi Jamal ya sakarwa Umaima yana k’ok’arin nufota yake furta “Baby don’t believe a single word da wannan mayaudariyar zata sanar dake... She’s a fraud Baby kin mance ne.. She tricked you..!”
Girgiza kai Umaima take tana kuma k’ok’arin jada baya cikin tsananin tsoro da firgici, muryarta na rawa yake furta “No... No don’t come near me..! No no please...!”
Jamal bai daina yunk’urin nufota yana furta “Baby ni ne fah... Ni ne Yarima Jamal d’inki, your husband...!”
Muhibbah dake hararan kwalban turaren tana takawa a hankali tana matsawa kusan dressing mirror d’in take fad’ida Umaima “Run Umaima, don’t listen to this criminal... Run, ask for help... Don’t just stand there..! Ki gudu Umaima karki sauraresa...!!”
Umaima kaw ta kasa katab’us shock d’in abunda tai discovering a yau d’in ya kasa sakinta... Ko motsi mai kyau ta kasa sai rawa da jikinta yake sabida tsananin tashin hankali....
Daidai nan Muhibbah tayi nasan rabza masa kwalban turaren akai... Ya fad’i k’asa had’ida rik’e kansa yana mai sak’in k’ara... Umaima ma k’aran ta saki Ta mak’ale b’angare guda had’ida kame kanta da duka hannayenta biyu, jikinta bai daina rawa ba.. Kana gani kasan ba’a hayyacinta take ba... Muhibbah tai saurin tura Taswiran cikin rigarta, ta shiga janyo hannun Umaima tana fad’in “We need to get out of here Umaima.. Bamuda lokaci, bani hannunki..!!” Bata kai aya ba taji sauk’an wani irin abu a goshinta wanda ya sanyata zubewa a wajen duniyar na juya mata bata iya fahimtar komai ba saima lumshewa da idanunta sukai jini na kwarara daga goshinta...
Sandar crutches d’insa ya rabza mata akai da iyaka k’arfin da Allah ya hore masa... Cikin rawar jiki Umaima ta mik’e tana ambato sunan Muhibbah inaaa bata iya komai sai k’ok’arin bud’e lumsassun idanunta take cikin tsananin azaba...! Da k’yar tana ganinsu nesa nesa take iya furta “Run Umaima..! Run.! Ask for help..! Ki gudu, ki tsira da rayuwarki...!!”
Cikin kuka Umaima ke fad’in “Bazan iya barinki a haka ba...! Ki tashi mu gudu dan Allah..!!”
Inaa tana maganan ma cak ji tayi kaman numfashin Muhibban ya d’auke.... Umaima ta juyo ta hangi Jamal dake k’ok’arin zuba wani ruwan magani cikin handkerchief, a daburce Ta mik’e tana furta “Help..! Someone help us..!!” Ta nufi k’ofa a guje... Saidai tuni Jamal ya cimmata, Ta shiga bige buge tana k’ok’arin k’wace kanta saidai k’arfin namiji da mace ba d’aya ba balle ma ita da take cikin yanayi na matuk’ar tsoro...Tuni ya matseta sosai cikin hannunsa sai hura hanci yake yana haki, lokaci guda ya danna mata handkerchief d’in a hancinta... Aiko tana Shak’an ruwan maganin idanunta suka lumshe jikinta ya sake gaba d’aya, cak Ta daina duk buge bugen da take...
Jamal na murmushi yake furta “Where do you think you’re going Sweetheart..? You’re mine, Ke tawa ce Umaima... Idan kinga kin fice daga gidan nan ni ne kawai zan fitar dake...!” Ya k’arashe zancen nasa yana mai d’aurata saman gado... Haka yana cangwala sandarsa ya isa jikin wani drawer ya zaro igiya doguwa ya shiga d’aure Umaima jikin gado, tsaf ya gama d’aureta yana mai sakin murmushi... Maidoda dubansaga Muhibbah tai wacce take yashe a wajen lifeless kana ya furta “You’re now under my custody Muhibbah..! Zaki d’and’ani azaba zakiyi danasanin shigowa cikin Masarautar nan balle har kiyi gangancin zab’oni a matsayin abokin gaba...!!”
Take ya isa gareta da igiyoyin nasa ya shiga d’aureta tin daga hannayenta har zuwa k’afafunta, wane irin d’auri yayi mata ya had’e hannayen da k’afafun ya d’aure waje guda... Sai gumi yake yana haki yana ciza labb’ansa sabida tsananin bak’in zuciya...
Gefe ya koma yana sauk’e haki yake dubansu su duka biyu, itadai Umaima a nan zai barta yayita kula da ita har ya samu ya shawo kanta su gudu tunda babu mai tuhuma Ina take, matarsa ce babu wanda zai zargesa akanta...ita kuwa Muhibbah tunanin abinyi yakeyi da ita... Take tunanin tattaunawar Giwa da Jakadiya da ya sinkaya ya fad’o masa cewa zasu baiwa Aljanah Sarauniya Tamuna matarsa Umaima matsayin sadaukarwa, Toh mai zai hana ya canzawa Giwa Umaima da wannan ‘yar lek’en asirin, sai Giwa ta bada ita ga Bokanta a matsayin fansar matarsa Umaima, idan yaso shi sai ya d’auki matarsa su gudu daga Masarautar, bayada buk’atan komai cikin Masarautar, ya zab’i ya tsira da rayuwar matarsa...! Take ya saki wata irin muguwar murmushi yana duban Muhibbah da har lokacin idanunta a lumshe suke saiko Jinin dake kwance goshinta, d’aure da manyan igiyoyi... Yasa hannu ya d’an shafi k’eyarsa yanda Ta kwad’a masa kwalban turare yaga d’an jini kad’an... Murmusawa ya kumayi yana mai furtawa a fili... “Ba’a zubar da jinin ahali Sarki AbdulJabbar a banza yarinya..! Kinyi babban ganganci.. Wannan Jinin da kikayi sanadiyar d’igansa zaki biyasa da rayuwarki..!!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin wata murmushi lokaci guda ya kullo k’ofa ya fito ya nufi b’angaren Giwa...
**
Cikin rashin gane inda kalaman nasa suka dosa Mahmood d’in ya kamo hannunsa suka zauna saman doguwar kujera dake cikin d’akin ganawa da marassa lafiyan.... “Fu’ad ka natsu ka sanar dani... Mai kake son cewa..?!”
Fu’ad na hawaye ya d’ago yana dubansa sai kuma ya sadda kansa k’asa yace “It was that night... Daren Washe garin sallah k’arama..! Yaya ka tuna, shekaru goma sha hud’u da suka shud’e...!”
Mahmood ya kuma gyara zamansa yace “Fu’ad ban fahimci mai kake nufi ba, anyi bikukunan sallah da yawa wanne kake nufi..? Kuma mai ya faru lokacin..?!”
Fu’ad yasa tafukan hannayensa duka biyu ya shafi fuskarsa sai kuma yaci gaba da fad’in “Bikin k’aramar sallah wanda bayanshi da kad’an akayi bikin aurenka...!”
Yai shiru yana duban Fu’ad sai kuma ya soma tuno abinda ya faru “We were all together, ni da kai da kuma Yazeed da Jamal, it was such a nice evening..! Tun bayan wannan shekaran bamu sake wata fita saman Dawakai tare ba the four of us, koda kuwa kilisa ne.. How can I forget that Eid.. Yana d’aya daga cikin best Eid na rayuwana gaba d’aya sabida kiran da Mai Martaba ya min a lokacin ya sanar dani an saka aurena da Aliya bayan duk gwagwarmayar da muka sha da Maami na k’in amincewa da auren da tayi... But at the end wannan daren Mai Martaba ya kirani ya sanar dani ya saka mana ranan aure, Kaga kuwa bazan tab’a mance wannan daren ba..!”Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa sai kuma yaci gaba da fad’in “It was such a memorable Evening..! Munyi wasan Dawakai sosai Ni da kai da Yazeed da kuma Jamal harmada Ja’afar... Mukayi dare a hanyarmu Ta dawowa, bamu dawo Fada da wuri ba..!”
Fu’ad ya jinjina kai yace “That same night... Komai ya fara ne daga wannan daren, halinda na tsinci kaina ciki ya soma ne daga wannan daren Yaya...!”
Mahmood ya tsaida murmushin da yake lokaci guda yana mai duban Fu’ad d’in, sai kuma yaci gaba da fad’in “Something happened that night, kaman mun tsinci mutum a hanyar mu ta komawa gida.... I think it was... A girl... Yeah a girl, we even helped her...! But wait, na tafi na barku tareda Yarinyar..! Mai Martaba ya aiko sak’on yana nemana...! What happened that night Fu’ad..! Mai ya faru sanda na barku da yarinyar..? Tell me Fu’ad..! Tell me everything..!!” Ya k’arashe tashin hankali k’arara kwance saman fuskarsa...
Fu’ad yaja wane irin dogon numfashi yana mai lumshe idanunsa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “After you left, Jafar left as well...! Ya rage saura mu uku da yarinyar.. Ni Yazeed da kuma Jamal...! Yaya we did something terrible to the girl...!!” Kuka ya hana Fu’ad ci gaba da magana...
Izuwa lokacin hankalin Mahmood ya tashi sosai, zuciyarsa bata daina tsinkewa ba,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 45 Chapter of 65