Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sauraron abinda Giwa da Yazeed Ke magana akai ta tabbata bazai shige kan rashin ganin iyalinsa da batai wajen bane... Ba Muhibbah kad’ai ba harta Raheema ta kula da wani abu... Tasan kad’an ne daga cikin aikin Yazeed ya hana Zuhra da yaranta halarta wannan waje, tsaf tasan ko wanene Yazeed ba mutunci bane dashi... Yanzu haka wani abin Zuhra tai ya hanata fitowa.... Tana gani ya kirawo Hauni babban bawansa yai masa magana bayan mahaifiyarsa tai masa magana... Cikin sauri Hauni ya mik’e ya fice yana sab’a babban gyare.... Jim kad’an bayan ficewarsa saiko gashi nan ya shigo tafeda yaran Yazeed guda Sultan da Noor.... Su duka biyu cikin shiga Ta alfarma da sarauta... Suna k’arasowa suka tafi wajen Kakarsu a guje suka zauna cikin jikinta... Giwa ta rungume ‘yan jikokinta tana sumbatar kawunansu.... Daga yanda Muhibbah ke zaune ta gama karantar komai, Wato dai maganar da Giwa sukaida Yazeed bai shige kan rashin ganin matarsa da yaransa wajen bane kenan, har saida Giwa tai magana sannan ya bari aka kawo yaran... Toh matarsa Fah..? Shin mai yasa ya hanata..?? Tambayar da taita wa Muhibbah Yawo a kwanya, lokaci guda tana hankalta da irin duban da Yazeed da Raheema Ke aikawa juna tsakaninsu.... She really needs to figure something out... Idanunta suka sauk’a zuwa kunnen Raheema.... Tabbas earrings d’in wannan sark’a data tsinta ne daga aljihun Yazeed... Wato dai da gaske hasashenta ya tabbata, Yazeed da Raheema sunyi tarayya wajen cin amanar Zuhra... Tabbas b’atan basira ne ya sanya Raheema saka wad’annan ‘yankunnen.... Tana nan zaune tana tinanin taga Raheema tai alamawa Yazeed da idanu kana ta mik’e ta nufi wani k’ofan daidai sanda hankulan mutane ya karkarta zuwaga cin abinci... Jim kad’an taga Yazeed ya mik’e yabi bayanta... Ta waiga gefe da gefe tana tinanin abinyi... Tana jin Umaima na tambayarta mai zataci amma sai ta rik’e mararta kad’an tace “I’ll use the restroom first, Ina dawowa bada jimawa ba....” Umaima ta jinjina kai tana mai furta “wait kinsan hanya ko nai assigning wata cikin kuyangi tai miki rakiya....?” Muhibbah ta girgiza kai murmushi saman fuskarta “No karki damu ai dai yanzu Bazan b’ata cikin gidan nan ba na fara sabawa I guess...” Sukai murmushi su Duka biyu kana Muhibbah tai saurin bin hanyar da taga Yazeed da Raheema sunbi.... Tana tafiyar tana sand’a had’ida waige waige.... Cen ta soma jiyo muryoyinsu a hankali.... Tai saurin k’arasowa yanda take jin sautin muryoyin nasu na fitowa... Gabanta ne yai mummunan fad’uwa ganin irin yanayin data hangi Yazeed da Raheema ciki... Sun fice hayyacinsu gaba d’aya kaman zasu cinye bakunan junansu.... Tai saurin komawa da baya had’ida rintse idanu tana mai sakin ajiyan zuciya a hankali... Banda Innalillahi da tir da Allah wadai zuciyarta bata iya komai... Ta mak’ale nan wajen tana sauk’e ajiyan zuciya a hankali... Dan harga Allah ta razana da abinda idanunta ya gano mata... Cen kuma sai ta soma jiyo muryar Raheema na fad’in “Enough Yazeed... Please ya isa haka ka mance ina muke ne...?” Yazeed da bai cikata ba yaci gaba da fad’in “And so what....! Tsoron wannan lusarin husband to be d’in naki kike ya ganmu ko kuwa k’awarki aminiyarki kike tsoro ta ganmu....?!” Turasa ta d’an kumayi tana fad’in “Duka ba laifi bane idan naji tsoron faruwan hakan... Yazeed please Zuhra doesn’t deserve any of this...Wllhi tausayi take bani... Tana matuk’ar k’aunarka bai kamata kake tsnanta mata horo don ta nuna damuwa akanka ba... Sanin kanka ne idan Ta rubuta wasik’a ta fad’i halinda take ciki a Masarautar nan Ta tura tasu Masarautar komai ka iya faruwa... You might lose your wife Yazeed... Watak’ila harda yaranka...!” Murmushi ya saki yana shafan gefen fuskarta kad’an kana yace “Babu wanda ya isa yaga downfall d’ina because I am Prince Yazeed AbdulJabbar... Sarki mai jiran gado.... Zuhra tawa ce, kuma bazata tab’a aikata abinda kike tunani ba... Idan na riga na shiga rayuwar mace bazata tab’a iya rabuwa dani ba kuma har abada... Kaman yanda kema bazaki iya rabuwa dani ba koda bayan kin aure Yaya na...!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa.... A hankali Muhibbah ta soma jada baya zuciyarta naci gaba da bugawa... Tana tafe da baya da baya bata ankara ba Ta bangaji flower vase ya fad’i k’asa.... Ta kame bakinta had’ida zaro idanu...Tai Saurin mak’alewa jikin gini tana jira mai aukuwa ya auku... Tana ganin sanda suka fito daga mab’oyar tasu suna lek’e lek’e kasancewar basuga kowa ba yasa suka kuma komawa yanda suka fito.... Tai saurin fitowa ta fice daga wajen gaba d’aya bata daina waige waige ba... A daidai hanyar da zai fiddaka haraban wajen suka kusan yin kar da mutum yana tafe waya manne kunnensa.... Ta juyo a firgice had’ida rintse idanu alamun tsoro sai kuma ta shiga basa hak’uri idanun nata a lumshe “Sorry sorry sorry... Dan Allah kai hak’uri wllhi banga isowarka ba...!” “Muhibbah..!” Ya ambato sunanta yana mai dubanta cikeda mamaki... Jin muryarsa ya sanyata had’iye sauran kalaman nata ta kuma kasa bud’e idanu sai kunyan kanta ma da ta soma ji ganin irin firgitan da tai lokaci guda.... Yarima Mahmood ya saki murmushi a hankali yana mai duban yanda ta kasa bud’e idanunta.... “Are you alright...!” Ya tambaya yana mai dubanta cikeda kulawa.... Sai lokacin ta d’an sami zarafin ware idanunta kana ta sadda kanta k’asa tace cikin sanyin murya “Lafiya nake your Highness... Am... I’m sorry Your Highness, ban San kana tafe bane....!” Tsareta da idanu yai kana ya d’an murmusa kad’an sai kuma yace “Yanayinki yafi kama da yanayi na tsoro...kaman wani abin gudu ne ya biyoki a guje...?!” Tai k’arfin halin d’ago idanunta had’ida waresu murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta take furta “No..no Your Highness babu komai...!” Baisan dalili ba amma harga Allah ganinta ya sanaya shi nishad’i musamman d’abi’unta da yanda fuskarta Ke komawa idan taji tsoro... Gashi dai sau biyu suka tab’a had’uwa kuma duka da dare ne amma zai iya cewa k’wayan idanunta daban suke a cikin nashi idanun... Yanayi na tsoro yana matuk’ar k’ara masu kyau.... Jin kaman bazai magana ba yasa Muhibbah fad’in “Tuba nake Rankashi dad’e...!” Ya d’anyi gyaran murya a hankali had’ida maida hannayensa duka baya kana yace “Ina kika nufa....?” Ta d’ago tana k’ok’arin yi masa alama da hannu saidai gaba d’aya ma gani tai kaman ta b’ata hanyar... Gaba da’aya sai ta daburce tama rasa inane hanyar... Ya kuma murmusawa a hankali yana mai jefa wayar salulansa cikin aljihun wandon kayan sarautarsa kana yai gyaran murya cikin dakewar murya “Looks like Princess ta b’ata cikin Fada trying to rescue her prince....!” Ta d’ago da tsananin mamaki tana dubansa tamkar bashi yai maganar ba, da alama babu yanayin wasa a fuskarsa sannan wani b’angaren ma yake duba...sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Muje na fitar dake... But next time Ki kiyaye kisan ina kike zuwa...!” Godiya ta kuma masa kana tabi bayansa sad’af sad’af kaman wata munafuka kanta a k’asa.... Giwa da gaba d’aya ta soma jin kaman wani abu na mintsilinta, gaba d’aya kasa sukuni tai a wajen... Take hannunta na hagu da ko yaushe rufe yake cikin wani bak’ar safa ya soma mata k’aik’ayi.... Takai dubantaga Jakadiya wacce tuni Ta fahimci halin da Uwargijiyar tata ke ciki.... Tai saurin k’arasowa gareta had’ida kwanto da kanta alamun jinjina da gaisuwa a zahiri... Saidai su biyu d’in saiko mahaliccinsu ne suka san abinda suke tattaunawa.... Cin abincin da ba’a ida taredasu ba suka bar wajen.... A b’angaren Gimbiya Zeenatu kaw K’uri tai masu sanda suke k’arasowa, tabbas gabanta ya fad’i sanda Ta hangi Yarima Mahmood tace da wannan budurwa, sai yanzu take ganin ashe ba laifin Raheema bane da ta tada hankali kan yarinyar... Tin yaushe ake jajen isowar Yarima Mahmood sai gashi ya k’araso tareda wannan yarinyar... Ita data tura Raheema taje ta nemo Mahmood yanda ya shiga ya fita su taho tare, gashi tana cen tana sakarci wannan shu’umar ta samosa... Waima ina Raheema ta tsaya...? Amsar data kasa samowa... Cen kuma ta hange mazaunin Yazeed babu kowa, fuci ta saki a hankali tana mai girgiza kai... Sarai ta sani wajen d’an iskan cen Yazeed ta makare... Tabbas sai ta koyawa Raheema hankali yau d’in nan basai gobe ba... Cikin tsananin k’unan rai ta mik’e tai tafiyarta itama Kuyanginta na biyeda ita.... Yayinda Zahra dasu Sultan su Noor yaran Yazeed suka kewaye Yarima Mahmood kowa yanaso ya sauraresa hakan ya baiwa Muhibbah daman silalewa ta isa gefen Umaima ta zauna tana hango tsananin k’aunan yaran gaba d’aya a fuskar Mahmood.... Maiyasa takeji cen k’asar zuciyarta shid’in yanada wani kyakkyawan hali cikin mutane gaba d’aya wanda ba kowa Keda irin wannan halin ba...? Maiyasa takejin tsira da kwanciyar hankali a duk sanda ta kasance tare dashi... Daren jiya bayan tattaunawarsu sosai ta sami natsuwa cikin zuciyarta, sannan yanzu datai zaton su Yazeed zasu kamata bayyanarsa sai ya jefata cikin nastuwa da kwanciyar hankali.... Bugu da k’ari alak’arsa da mutanen Masarautar gaba d’aya ko shakka babu yanada kyau....Toh maiyasa ya kasance azzalumi daga fari...? Kasa samun amsar tai sai wani b’angare na zuciyarta dake raya mata.. Ba’a canza wa tuwo suna... Watak’ila wannan nasa salon kenan na yaudara... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tanajin tsanarsa na kuma taso mata daga cen k’asar zuciyarta lokaci guda.... Saurin kawar da fuskarta tai Daga barin dubansa hakan yai dai dai da hango Raheema da tai tana k’ok’arin k’arasowa wajen sai waige waige take kana ganinta Kaga maras gaskiya.... Muhibbah ta kafe Raheema da idanu yanda take bin Yarima Mahmood da Mayen kallo, ko ba’ace ba so take taje wajensa saidai hakan ba mai yuwa bane kaman yanda yake a tsarin gidan... Idan d’an sarki na neman aurenki koda kina rayuwa cikin gidan kai tsaye bazaku keb’e ba har sai Jakadiya tai iso an shirya had’uwar ta musamman kafin ku gana... Lokaci guda Raheema Ta maidoda dubanta ga Umaima da Muhibbah dake cakalan fruits d’in gabanta tamkar wata mai tausayinsu.... Cikeda k’asaita Ta soma takowa garesu... Umaima ce ta tarbeta da fari’a yayinda Muhibbah ke binta da kallon k’yama bayan abinda Ta gani tsakaninta da Yazeed.... Murmushi saman fuskar Raheema take duban Muhibbah, nan taga hankalin Muhibbar naga Zahra da mahaifinta yanda take serving d’insa abinci ba tareda ta bari wata baiwa tai masa ba.... Bud’e murya Raheema tai kana tace “Sun burgeki koh...?” Da mamaki Muhibbah ta kaikaito tana duban Raheema dake ci gaba da sakin shu’umin murmushi.... Lokaci guda Muhibbar ma ta d’aura murmushi saman fuskarta kana tace “Duk wanda ya dubesu dole su burgesa sannan kuma yai masu fatan su tabbata a haka ba tareda wani ya shiga tsakaninsu ya zamto sanadiyan lalacewar wannan kyakkyawan alak’a dake tsakaninsu...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta tana duban Raheema da tuni kalaman Muhibban sun sanyaya mata jiki... Murmusawa Raheema ta kumayi kana tace “Muhibbah koh...? I hope you know your place... Ya kamata ki rage shigewa Zahra..!” Muhibbah ta kuma murmusawa tana duban Zahra dake cen wajen mahaifinta kana tace “I’m sorry your Highness, but I think that’s for her to decide... You can’t choose her friends... Am I right...?!” Raheema tai murmushi da yafi kama da yak’e kana tace “What Zahra needs is a mother, and not a friend..Kin fahimta..!!” Wannan karon daga sama zuwa k’asa Muhibbah ke duban Raheema, murmushin bai bar saman fuskarta ba take furta “And wa kike tinanin ta cancanta da zama mahaifiya ga Zahra... You..?!” Lokaci guda ta kuma sakin murmushi kana tace “Ki kwantar da hankalinki your Highness, Yarimanki bai gabana, bashi bane a gabana... Karatun da ya kawoni garin nan shine gabana... So Ki kwantar da hankalinki kinji, I’m not an enemy here Princess...Kema idan kinaso mu k’ulla k’awance zamu iya zama k’awaye kinji koh....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin wani murmushi kana ta furta “Na barki lafiya your Highness... Have a good evening...!!” Har ta juya zata wuce sai kuma ta juyo tana kuma duban Raheema kana Ta kuma sakin murmushi tace “Oh... Nice earrings tho...!” Tana ida fad’in haka tasa kai tai shigewarta ko sallama da Umaima ma bata sami zarafin yi ba aka bar Raheema baki sake tana bin bayanta da kallo... Shiko Yarima Mahmood lek’en ta yanda zai hangota yake kan faman yi amma bai hangota d’in ba... Ba dan yaso ba ya kuma maida hankalinsa ga yaransa.... *** Yamutsettsen tsoho mummuna abin tsoro da k’yama da Giwa Ke kirada Tal’udu shine ya kuma mik’ewa tsaye gaban Giwa cikin tsananin k’unan rai ga hayak’i da ya gauraye wajen gaba d’aya lokaci guda yake furta “Turai..!!! Kina Ina d’anki ya had’o kan Malamai suna cikin Masarautar nan suna k’ona min dakaruna dake ko wacce kusurwa ta cikin gidan nan....!! Idan har hakan yaci gaba da faruwa toh fah dole ya wargaza duk wani sauran shirinmu....!” Giwa ta soma girgiza kai tana furta “Bazan tab’a barin Mahmood ya wargaza min shirina ba...Kafin ya wargaza min ni zan gama dashi...!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci.. Tal’udu yai wani irin dariya mai mummunan sauti kana yace “Kina gab da makara Turai domin kaw wannan yaro naki da shirinsa ya dawo... Kuma ya dawo ne domin ya yak’eki ya bankad’o duk wasu sirrikanki...!!!” Giwa ta d’ago tana huci lokaci guda take furta “Bazai yuwu yaron dana rik’esa matsayin d’anda na haifa shekara da shekaru ya zama silan rugujewata ba... Dannewa da nai da rik’onsa da nai tsawon shekarun nan ya isheni uk’uba, ya isheni k’unci... Kai da bakinka ka fad’a min Mahmood bazai k’argo kan gadon Mulki ba... Da zaran ya mutu kuma d’ah na ne Yazeed zai d’ale Karagar....!!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci.... Tal’udu ya kuma fashewa da wata irin dariya kana yace..... SameenaAleeyou📚 [6/15, 7:17 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *019* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tal’udu yaci gaba da fad’in “Ai kin makara tinda kika sake wannan yarinyar ta kufce miki.... Fitilar tsafi ta nuna min gudan jinin na tattareda ita...!!” Wani irin mummunan fad’uwan gaba ne ya dirarwa Giwa lokaci guda... Ta d’ago idanu tana duban Tal’udu dake tsaye gabanta daga shi sai wata ‘yar bante kalan ja, yamutsattsen fatarsa babu kyaun gani...... Giwa Ta shiga girgiza kai tana furta “Wacce kenan... Wace yarinya ce wannan Tal’udu....?!!” Ya kuma fashewa da wata irin dariya kana yace “Yarinya Ta farko da ya kamata na tara da ita, ban tarada ita ba Allah ya bata sa’an tserewa.... Tabbas itace gudan jinin...!!” Gaban Giwa ya kuma bugawa... Batasan sanda Ta mik’e tsaye ba tana fad’in “Kana nufin kace ba’a sami gudan jini tsakanin duka wad’annan ‘yanmatan da suke wajen nan ba...?” Tal’udu ya kuma fashewa da dariya kana yace “Ai na fad’a miki gudan jinin ka iya tsayawa akanta ita d’ayanta... Kuma idan har ya tsaya akanta ita d’aya toh fah ko shakka babu K’addarar Masarautar nan na rataye ne a wuyanta....!!” Giwa na tsananin huci take furta “Amma yarana sun tabbatar min cewa wannan yarinyar Saudatu ta jima da mutuwa sun kasheta..!!” Tal’udu yai wata murmushi mai mummunan sauti kana yace “Tin a lokacin na fad’a miki yaranki k’arya suke maki Allah bai basu sa’an kashe wannan yarinyar ba kaman yanda suka sanar dake Sun kasheta...!!” Giwa Ta soma ganin jiri duniyar na juya mata, ta dafe kanta da ya shiga sara mata lokaci guda.... Meke shirin faruwa da ita, idan Saudatu tana raye toh tana ina... Kai ina ita bata yarda ba, bata yarda Saudatu na raye ba... Bata kuma yarda k’addarar Masarautar Ta na rataye a wuyarta ba... Lokaci guda ta d’ago tana duban Tal’udu cikin wane irin fuci take furta “Hakan ba mai yuwa bane Tal’udu... Babu yanda za’a ce k’addarar Masarautar nan na rataye a wuyar wannan k’ask’antacciyar yarinyar d’iyar k’ask’antattu... Idan duk baka sami gudan jinin cikin wad’annan ‘yanmatan goma sha hud’u da suke a matsayin mallakinka a yanzu dole a sake nemo wata budurwa a jarabba da ita... Ni bazan tab’a yarda da fad’uwa ba Tal’udu....Na riga dana bisne sirrinka da babu wani mahaluk’i da ya isa ya bincikosu.....!” Ta k’arashe tana tsananin huci Juya mata baya Tal’udu yai kana yace “Turai ina gargad’inki dik randa Mahmuda yai nasaran bud’e kurkuku dake k’ark’ashin k’asan Masarautar nan.... Ki tabbata daga wannan rana daga ni har Ke k’arshemu yazo....!!!” Yana ida fad’in haka hayak’in dake cikin d’akin ya kuma turnuk’ewa hannun Giwa dake lullub’e cikin bak’in safan shima ya soma hayak’i... Ta zaro ido tana duban hannun nata cikeda firgici... Cen kuma hayak’in ya soma gushewa, a haka itama hayak’in dake fitowa daga cikin hannun nata ke tafiya har dai hayak’in ya k’are gaba d’aya... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya tai kana Ta sauk’a daga saman jan darduman su ta tsafi mai d’aukeda Tambarin Masarautar tasu.... Tana fitowa ta tadda Jakadiya na jiranta, tai tsaye tana k’arema ‘yanmatan dake kai komo wajen kallo... Ta hangi wannan d’aki da kullum yake a bud’e... D’akin da ya kamata ace Saudatu ce a ciki amma an bar d’akin da gib’i... Wannan yarinya ba k’aramin cutarta tai ba, da ace bata gudu daga wajen Tal’udu ba da yanzu babu wani barazana gaba gareta... Ta yaya Tal’udu zaice k’addarar wannan Masarautar na rataye a wuyan tsinanniyan yarinyar nan wacce itada iyayenta suka tasamma kawowa mulkinta sanadi... Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tai alamawa Jakadiya suka soma Tafiya, ‘Yanmatan gaba d’aya masu sanye da tufafi iri guda su goma sha hud’u suka jera a layi sahu biyu kansu a k’asa har Giwa ta fice daga cikin wajen... Koda Giwa ta iso d’aki hankalinta bai kwanta ba, kaman ko yaushe Yarima Jamal ta tadda zaune a d’aki yana jiran k’arasowarta.... Yanayinta da ya gani ya tabbata akwai abu mai girma dake damun Mahaifiyar tasa.... “Maami lafiya na ganki haka...?” Ya bid’a fuskarsa d’aukeda damuwa... K’ak’aro murmushi Giwa tai dan har abada bata yarda ta nuna gazawarta ba kana tace “Lafia lou nake Ubana... Baka kwanta ba...?” Jamal ya murmusa kad’an kana yace “Maami kinsan bazan tab’a kwanciya ba tareda naga kin kwanta bacci cikin aminci ba....!” Tai murmushi cikeda jin dad’i kana tace “Allah shi maka Albarka Jamal, biyayyan da kake min kaima Allah shi baka yara masu yi maka irinta...!” Bata Kai aya ba tai saurin katse addu’ar tata kaman wacce ta tina wani abu... Jamal ya tsareta da idanu yana jiran yaji k’arshen addu’an nata... Kaman ko yaushe yaji tayi shiru batai masa fatan samun yara ba... Mik’ewa yai ya k’araso gabanta had’ida duk’awa, ya d’ago kai yana dubanta kana yace “Maami mai ya hanaki k’arasawa...Shin baki so nima nai aure na haifi nawa yaran ne....?” Tai masa K’uri tamkar mai tunani, kana ta shafi gefen fuskarsa kad’an, lokaci guda ta sakar masa murmushi kana tace “Tanadin da nai maka na musamman ne Jamal, K’warai Inaso naga ‘ya’yanka kuma wataran zasu gaji sarautar gidan nan... Toh amma Jamal idan Kai aure yanzu waye zaike kula dani yanda kake kula dani... Sanin kanka ne cikin ‘yanuwanka kaf ka fisu kula dani da kuma al’amra na... Kaine Gwarzo na Jamal, idan Kai aure hankalinka zai karkata zuwaga iyalinka.... Wa zai kula dani Jamal...?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Jikin Yarima Jamal yai sanyi... Yana matuk’ar k’aunar mahaifiyarsa fiye da komai a duniya... Ko wace irin biyayya ne yai alk’awarin yi mata wannan biyayyar matuk’ar zai sanyata cikin Farin ciki... A hankali ya mik’e daga durk’ushen da yake ba tareda ya kuma juyowa ya dubeta ba yai ficewarsa zuciyarsa na matuk’ar masa zogi... Ya rasa gane dalilin da yasa sam mahaifiyarsa bata k’aunan ya kawo maganan aure cikin rayuwarsa... Maiyasa take masa haka, ya kasance mai tsananin biyayya a gareta, Bai tab’a sab’a umarninta ba tsawon rayuwarsa... Toh Maiyasa shi bazata barshi ya cika burinsa na ganin ya aje iyali ba...? Idan dan tsoron kar biyayyan da yake mata ya daina ne yayi imani babu macen da zatazo Ta hanasa biyayyawa mahaifiyarsa... Da wannan tinanin ya nufo matakalan benen, idanunsa suka sauk’a zuwa b’angaren Umaima da Zahra... Yai K’uri yana duban k’ofan parlorn nasu... A hankali ya soma takawa har ya isa ya bud’e k’ofar parlorn cikin tsanaki.... Ya soma takowa cikin d’an madaidaicin parlorn yana mai k’arewa k’ofar d’akin Umaima kallo... Lokaci guda idanunsa suka sauk’a kan zanen gidan sarautar dake lank’aye wajen wanda shine ya baiwa Umaima ta lank’aya a wajen.... Ya tako har zuwa gaban zanen ginin gidan sarautar yana shafawa a hankali tamkar mai nazarin wani abu.... Lokaci guda ya maida dubansa zuwaga k’ofar d’akin Umaima, ya jima yana duban k’ofan d’akin kafin ya soma takawa a hankali cikin tsanaki ya isa jikin k’ofar ya tura a hankali, nan kuwa k’ofar ta bud’e.... Cikin sand’a yake takowa zuwa cikin d’akin har ya iso gaban gadon Umaima dake baccinta hankali kwance.... Yai mata K’uri yana dubanta, daidai lokacinda Umaima Ta d’anyi juyi cikin bacci bargon da ta rufa ya d’an janye ya yaye k’afafunta zuwa cinyoyinta suka bayyana... Zuciyar Jamal tai wani irin tsinkewa, yai saurin rintse idanunsa yana mai kauda Kai gefe... K’irjinsa bai daina bugu ya soma k’ok’arin Kai hannunsa da niyyan janyo mata bargon ya rufa mata, hannayensa sai rawa suke... Ba tareda ya kuma duban k’afafun nata ba ya janyo bargon ya gyara mata a hankali... Bayan ya rufa mata durk’usawa yai gaban gadon nata kana yai mata k’uri... Ya saki murmushi a hankali yana duban idanunta dake rufe ruf alamun bacci.... Cikin zuciyarsa yake fad’in “Ke tawa ce Umaima... Na rabaki da Ja’afar domin na mallakeki... Na kuma mallaki soyayyarki... Bazaki sake ganin Ja’afar ba har abada Umaima... Ja’afar bawa ne k’ask’antacce wanda bai cancanci soyayyarki ba... You’re mine Umaima... Kuma duk namijin da yai yunk’urin raba tsakaninmu zan b’atar dashi kaman yanda na b’atar da Ja’afar... Umaima, koda ace mahaifiyata bazata amince min da aurenki ba, toh kema bazan tab’a bari kiyi aure ba... Sabida ked’in tawa ce, na gwammaci nayita ganinki haka koda bazamu sami zarafin kasancewa da juna ba... Ina sonki Umaima.. Ina matuk’ar k’aunarki.. With all my heart..!” Ya k’arashe siririyar Hawaye na gangarowa Daga idanunsa guda... Ganin ta soma muskutawa alamun farkawa ya sanyashi saurin mik’ewa ya nufi k’ofa... Cikin sand’a ya fice kana ya janyo mata k’ofar a hankali ya nufi k’asa ya fice daga sashen gaba d’aya... *** Washe gari ta kama asabar ranan hutun aiki sannan d’alibai ma suna gida babu makaranta... Hakan yasa koda Zahra ta tashi tai wanka ta shirya sai ta nufi cen b’angaren bak’i yanda Muhibbah take.... Muhibbah batai mamakin ganin Zahra zaune a parlor tana jiran fitowarta ba... Suka sakar ma juna murmushi kana Zahra ta soma gaidata, Muhibbah ta amsa da sakin fuska ta k’arada “Yau mai nayi da na cancanci amsar bak’uncin kyakkyawar Gimbiya da sanyin safiyar nan... Gaskiya yau d’in ga dukkan alamu na tashi da sa’a...!” Ta k’arashe tana mai fari da idanu... Zahra Ta murmusa kana tace “Zuwa nai na gayyaceki karin kumallo a cen b’angaren mahaifina...!” Take annurin fuskar Muhibbah ya d’auke cak... Gabanta yai wani irin yankewa ya fad’i... Karin kumallo a b’angaren Yarima Mahmood... Wai kuma tareda ita Muhibbah...?! Ganin yanayinta ya canza ya sanya Zahra sakin murmushi kad’an kana tace “Bakiso ko...?” K’ak’aro murmushin yak’e Muhibbah tai kana tace “Ba haka bane Princess, kawai gani nai kaman bai dace ba... Maybe mahaifinki ma bazai so haka ba, or maybe hakan ya sab’a al’adu da d’abi’un Masarautar nan... Karki mance Zahra nan ba Spain bane yanda dik abinda kike ganinshi normal a can a nan ka iya zama akasin haka...” Ta k’arashe cikeda kulawa... Zahra Ta d’anyi rau rau da idanu kana tace “But ni banga komai ba cikin yin hakan... You’re my only friend here... Har yanzu ko sch banyi k’awaye ba.... Kuma shi yace min nazo muyi breakfast taredashi, na tambayeshi idan zan iya zuwa da friend d’ita.. Ya tambayeni wacece friend d’in tawa nace mishi ke ce.... Bai hana ba, kuma ai abinci kawai zamuci tare duka ni banga wani kuskure a cikin hakan ba... Ko shima sab’a dokan gidan nan ne...?!” D’an fuzar da iska kad’an Muhibbah tai kana ta k’araso ta rik’e hannayen Zahra cikin nata “Princess ba haka bane... But baki tunanin maybe Paa d’inki yanaso ku kasance ku biyu ne, to spend time together... Daughter and Dad bonding... Baki tinanin haka.?” Ta k’arashe tana kashe mata idanu guda.... D’an turo baki kad’an kana tace “Fine tinda kink’i zuwa... But promise me anjima zamu fita mu shak’ata a Lambun Masarautar nan sai muyi namu bonding time d’in...” Murmusawa kad’an Muhibbah tai kana tace “I promise you...!” Ta k’arashe tana mai d’aga tafin hannunta alamun alk’awari.... Zahra na ficewa da kad’an Umaima ta shigo ta d’auketa suka tafi b’angaren Giwa domin karya kumallo daga cen kuma sashen Zuhra

Chapter 11 of 65