Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tana duban Zahra “Kina nufin tun tana tsumman goyo...!” Zahra ta jinjina kai “K’warai kuwa haka Uncle Fu’ad ya sanar dani kaman yanda ya sami labari Kinsan Iatda Uncle Fu’ad shekaru biyu ne tsakaninsu ya d’an girmeta kad’an so tare Maami ta rainesu... Amma saidai ita an barta hannun Kakata mahaifiyar Maa d’ita ita ta raineta har saida takai kusan shekaru goma kafin aka dawo da ita cikin Masarautar nan... Maybe shiyasa nake jinta sosai cikin zuciyata, itada Maa are practically sisters.... I love her..!” Ta k’arashe cikin sanyin murya murmushi saman fuskarta Muhibbah ta d’an girgiza kai kad’an tana duban Zahra “Ban fahimceki ba Zahra... Kina nufin kice Umaima ‘yar uwar mahaifiyarki ce..?!” Girgiza mata kai tai alamun a’a sai ta d’orada “Aunty Umaima d’iyar k’anwar Maami ce, wani tafiya Benin da Maami tayi shine ta dawo da Aunty Umaima rik’e a hannu cikin zanin goyo, a cewar Maami wuta ya cinye Iyayen Aunty Umaima...!” Ta d’anyi fasali sai taci gaba da fad’in “Kinsan Maman Mamata Baiwa ce toh shine Giwa ta bata rainon Aunty Umaima tun tana jaririya har zaita takai shekaru goma kafin ta dawo da ita hannun Giwa a lokacin ana shirye shiryen Bikin mahaifiyata da Paa d’ina...!” Shiru Muhibbah tai tamkar mai nazari had’ida k’urama waje guda idanu... Ta juyo tana duban Zahra ta d’anyi gyaran murya kad’an tace “Toh ina Kakarki mahaifiyar maman naki take..?!” Zahra ta bud’e hannayenta alamun bata sani ba, taci gaba da fad’in “You know that’s why banson gidan sarauta... Sirrika sunyi yawa, all I know gameda mahaifiyar Maama shine tun lokacinda Paa ya dage zai auri d’iyarta Maami ta umarceta da tai nesa da Masarautar nan a cewarta baza’a ringa nuna d’anta a gari ana cewa ya auri d’iyar bayi ba...!” Muhibbah ta katseta da fad’in “Toh baki tab’a tambayar Mamanki Ina mahaifiyarta ta tafi ba...?” Zahra ta d’anyi shiru kaman mai nazari sai kuma ta girgiza kai tace “Dik sanda na tambayi Maa sai tace nayi shiru kuma kar na sake tambayarta and I don’t think ko Paa ma ya sani... Ina tsamman babu wanda yasan yanda Maman Maama Ta tafi...!!” Ta k’arashe cikin sanyin murya... Sauk’e nannauyan ajiyan zuciya Muhibbah tai tana mai bin maganganun Zahra’u daki daki nan ta sinkayo muryar Yazeed yana waya zai shige b’angaren Giwa, da alama wayan nasa ya shafi kama Ubandoma da akai... Duban Zahra ta d’anyi kana tace “Ki shiga ki duba Umaima, I’m sure akwai abindake damunta... Maybe ke zata sanar dake k’ila ganin ina wajen tai shiru bata sanar dake komai ba...” Jinjina mata kai Zahra tai tace “Ok zan dubata yanzu..” Ta k’arashe tana mai nufa d’akin Umaima... Muhibbah ta sauk’e wani ajiyan zuciya kana ta lek’o kanta kad’an yanda ta hangi Bayi guda biyu rik’eda kaya hannunsu, suka risina suka gaida Yazeed da har lokacin waya yake kana suka shige... Saida ta jira shigewan Bayin kana ta sad’ad’o ta fito... Taso bin bayan Yazeed dan taji tattaunawarsu da Giwa saidai hakan ba mai yuwuwa bane domin kaw da alama yau sashen Giwan cike take da bayi, kawai sai ta zab’i tabi bayan Yarima Jamal zuwa sashensa taga yanda zaiyi da zanen da ya d’auka daga wajen Umaima.... ** Giwa ta d’ago tana duban Yazeed idanu a kannare sanda yaci gaba da fad’in “Bansan Maiyasa kika dage sai Mahmood bane zai gaji sarautar nan... Amma ki sani Maami what so ever your reason might be bazan canza k’udirina ba... Sarautar nan tawace..!!” Ya k’arashe yana sakin huci... “Ka gama Yazeed...?Nace ka gama...?!!” Har lokacin hura hanci yake yayi zama irinta masu mulki sai karkad’a hannunsa guda yake... Giwa ta mik’e cikeda izza tana takowa zuwa gareshi.... “Yazeed kalleni nan..!” Ya d’ago rinannun idanunsa yana dubanta “Ka sanar dani shin kaine ka tura Ubandoma gidan Wambai...?!” Da tsananin mamaki yake dubanta kana ya gyara zamansa... “Maami what exactly are you implying here..? Mai kike nufi....?!” Ba tareda ko Gizau ba Giwa ta kuma furta “Nace ka sanar dani idan Kai ka tura Ubandoma Gidan Wambai dan ka k’ala sharri wa d’anuwanka a hanasa sarauta, tunda nasan akan sarautar nan you’re capable of anything Yazeed.. Kuma dani dakai sarai munsan Mahmood bazai aikata abu makamancin wannan ba, So gwara ka sanar dani komai tun muna mu biyu...!” Ta k’arashe cikin tsananin k’unan rai tana mai sauk’e fuci... Take idanun Yazeed suka kuma kad’awa sukai jazir, fatarsa Ta sauya zuwa ja... Tururin k’unan rai da fuci kurum yake har wani rawa jikinsa keyi... Lokaci guda ya mik’e tsaye yana duban cikin idanun mahaifiyar tasa ”Unbelievable!.. Are you seriously throwing that on me Maami...! Sabida d’anki mafi soyuwa a gareki yayi laifi and you can’t simply accept the fact that Mahmood isn’t what you think he is shine bari ki d’aura laifin akaina... Maami tell me Ubandoma Hadimin waye...? Da wa ake ganinshi..? Ma waye yake hidima..? Is it me or my brother..?!” Shiru ya d’an ratsa tsakani sai hucin da Yazeed ke sauk’ewa, lokaci guda yaci gaba da fad’in “Bakida amsa Maami....! Bari kiji na fad’a miki Giwa, believe whatever you want to believe I do not give a damn! babu abinda zai sa na fasa k’udirina... Idanma kina tinanin nine bak’on Buzu, then be it.... Abu guda da zan sanar dake shine kiyi taka tsantsan domin kuwa rayuwar Mahmood is in great danger... Kuma bani bane abin tsoron akwai wani wanda yafini san ganin Mahmood bai d’ale Karagar nan ba...I’m sure bakisan da wannan ba, duk abinda ya sami Mahmood karkiyi tinanin nine domin kaw Kurayen sunada yawa..!!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice cikin tafiya da tafi kama da sassarfa... Yarfe gumin da ya keto mata tai sanda ta doka kiran Jakadiya..! Nan kuma ta tuna ashe Jakadiya bata warware daga bugun da Izzatu tai mata ba... Taja gajeren tsuka a hankali sanda hadimarta guda ta shigo tana mai risinawa... Giwa ta fatattaketa tace tajeta tai mata kiran Jakadiya bata damu ko ta warke ko bata warke ba, dik yanda za’ai tazo Ta tana nemanta... Babu shiri Baiwar ta mik’e cikeda girmamawa ta fice... Giwa sai faman safa da marwa take tana huci.... *** Sauri sauri ta fito da niyyan bin bayan Jamal amma saidai mai, tana fitowa suka kusan karo da Fu’ad zai shige sashen Giwa.... Fu’ad ya tsaya cak yana mai dubanta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... Dukda k’atutun bak’in ciki da ya tokare mata mak’oshi hakan bai hanata k’ak’aro murmushin yak’e ta sakar masa ba.... “Your Highness... Barka da rana...!” Ta fad’i murmushin bai bar saman fuskarta ba... Saida ya rage girman idanunsa kad’an sai kuma yace “Bazan amsa irin wannan gaisuwar ba Hibbah... Mu gaisa a cen..!” Ya k’arashe yana mai duban sliding door dake gefe yanda zai fitar dake madaidaicin wajen shak’atawa... Bayi masu kaikomo kaw idan suka Zo shigewa sai Sun risina Sun gaidasu... Muhibbah da gaba d’aya ranta ya gama jagulewa sabida plan d’inta da Fu’ad ya b’ata mata k’ok’arin saita kanta tai tace “But your Highness ka mance sharad’ina, banso kowa yasan alak’ar for now a Masarautar nan... Gudun k’anan maganganu irinta gidan sarauta... Nafiso mu fahimci junanmu sosai and... to be sure of what we feel for each other..!” Fu’ad ya d’an kuma takowa kusanta kad’an had’ida rage muryarsa “And you think zan iya jure wannan sharud’an Naki Hibbah... Is not as if we are doing anything wrong.... So banga abin damuwa ba... And one more thing...!” Ta d’ago tana dubansa jin yayi fasali Fu’ad yaci gaba da fad’in “My feelings for you are real Muhibbah... Bana buk’atan yin wani tunani gameda soyayyarmu... Unless kuma kece baki so na...!” Ya k’arashe yana mai tsareta da idanu... Tamkar takai masa naushi a fuska haka takeji jin yanda yake furta mata kalaman Soyayya wanda tayi imani da yasan ko wacece ita bazai soma hakan ba... Badon karta ruining plans d’inta ba data masa kaca kaca tun daga nan amma saidai hakan ba mai yuwa bane... Tai k’ok’arin d’aura fake smile saman fuskarta “Ba haka nake nufi ba your Highness..” Fu’ad ya katseta da fad’in “Idan har ba haka kike nufi ba, then prove it...!” Bai jira cewarta ba ya shige k’ofar... Ta fuzar da fuci a hankali badon taso ba tabi bayansa zuciyarta gaba d’aya a cunkushe.. Shiko Fu’ad ganin ta biyo bayansa sai zuciyarsa ta aminta tabbas Muhibbah k’aunarsa take... Toh wata mace ne ma zata k’isa, baijin akwaita... Kyakkyawan murmushi saman fuskarsa yake dubanta cikeda jin dad’i, tuni ya sakankance yaci gaba da jero mata kalaman k’auna... Shigowarsa sashen kenan ya hangesu, kanta a k’asa tana faman sakin murmushi ga Fu’ad tsaye gabanta yana kasheta da wane irin kallo wanda ko ba’a fad’i maka ba kasan abinda irin kallon Ke nufi... Da gani suna matuk’ar jin dad’in zancen da suke.... Cikin sakanni zuciyarsa Ke harbawa.... SameenaAleeyou 📚[7/24, 6:11 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *36* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali yake murza hannunsa dake rufe cikin bandage wanda sam baisan yana yin hakan ba, ya kasa janye idanunsa daga barin duban nasu bai kuma daina murza hannun nasa ba wanda da alama ko zogin ciwon baiji... Ji yake tamkar zuciyarsa zata b’allo daga cikin k’irjinsa ta fito waje.. Kan kace mai jini ya soma d’iga a wajen... Sauk’owar Zahra kenan Ta hangi mahaifinta ya k’urama waje guda idanu ga jini na kuma d’iga daga cikin hannunsa... Cikin sauri Zahra ta k’araso tana duban hannun nasa take fad’in “Paa... Paa you’re bleeding again....!!” Muryar Zahra da Muhibbah ta sinkayo ya sanyata saurin waigowa tana duban wajen... Ido suka had’a da Mahmood saidai tuni yasa kai ya juya ya fice gaba d’aya daga sashen yana mai tamke hannunsa mai d’igan jini, lokaci guda yake ceda d’iyarsa it wasn’t serious she shouldn’t worry... Zahra tuni tabi bayansa yayinda Muhibbah kacaukam hankalinta ya koma garesu... Ta dubi Fu’ad daketa faman duba abu cikin waya da alama baisan wainar da ake tuyawa ba... D’an dafa kanta tai kad’an had’ida tamke idanunta... Fu’ad ya d’ago yana dubanta had’ida daina abinda yake “Are you alright..?!” Ya tambaya yana dubanta... K’ak’aro murmushi tai tace “Kar ka damu just a headache...!” Cikin nuna kulawa Fu’ad Ke fad’in “Headache.! Subhanallah, do you want to see a Doctor... Should I call one...!” D’an girgiza masa kai tai tace “No kar ka damu, idan nai bacci zai daina, na gode da kulawa...!” Ya sauk’e fuci a hankali sai kuma yace “Are you sure..?” Ta jinjina masa kai ba tareda tace komai ba... Daidaita tsayuwarsa ya kumayi sai kuma yace “Muje na rakaki..” Ta girgiza masa kai a hankali “Ka mance conditions d’ina... We shouldn’t be seen together..” Ya d’an ware idanunsa kad’an kaman zaice wani abu sai kuma yace “Alright fine... But promise me one thing..!” Ta d’ago tana dubansa.. Fu’ad yaci gaba da fad’in “You’d take good care of yourself for me..!” Ya k’arashe cikin kwantar da murya.. Dariya yaso bata amma sai ta gimtse tace “I’d in sha Allah... I promise..!” Fu’ad ya murmusa kad’an yana mai bata hanya alamun ta shige... Ta tako zata shige, Daidai k’ofa Ta sinkayo muryarsa yana fad’i tamkar mai rad’a “I love you..!” Murmushi kurum ta sakar masa ba tareda tace komai ba ta shige... ** A b’angaren Mahmood kuwa suna tafe shida Zahra Raheema ta hangosu, cikin sauri ta take masu baya tana tambayan Zahra meke faruwa... Shi kuwa Mahmood cikin sassarfa kurum yake tafiyar nasa ba tareda yabi takan Raheema dake tambayar Zahra abindake faruwa ba... Hannunsa a tamke sosai yake tafiyar zuciyarsa naci gaba da bugawa, suna shigowa parlorn ya shiga warware bandage d’in k’arfi k’arfi wanda har saida yaso baiwa Zahra tsoro... Raheema ta k’araso cikin rawar jiki take fad’in “Yarima mai ya sameka... Ina ka sami wannan k’aton yankan...?” Ta dubi Zahra dake tsaye gefe tana duban mahaifin nata cikin kid’ima tace “Zahra get the first aid let’s treat his wound...!” Muryarsa suka sinkayo yana furta “No..!” Raheema Ta dubesa tace “But you’re bleeding..” Katseta yai cikin tsananin d’aga murya “I said no... Ko bakiji bane..!!” Raheema ta koma gefe tana duban ikon Allah yayinda Zahra Ke furta “Paa should I call Aunty Muhibbah tunda itace tai maka treating, na kirata ta sake..” “Whattt..!!” Raheema ta furta cikin zuciyarta, ina take har akai wannan iskancin... Wannan shegiyar mayyar yarinyar ta wanke ciwon mijinta... Eh lallai Aunty Zeenatu tayi gaskiya da tace wannan yarinyar karuwanci kawai take sonyi da Princes d’in Masarautar nan.... Toh wllhi tayi k’arya ta fara da Mahmood d’inta.. Tayi nisa cikin tunani har batama San sanda Mahmood yai hayewarsa sama ba Zahra kuma ta fice tuni ta barta nan tsaye... Ta d’aga Kai tana duban matakalan bene zuciyarta naci gaba da harbawa... Toh maiyasa har yanzu maganin bai soma aiki ba, maiyasa gaba d’aya bata gabansa, tama kula tamkar yanzu yafi yin watsi da ita unlike before, dik tsiya da yakan aika ai kiranta koda ba wani zancen arziki zasuyi ba amma yanzu ko takanta baiyi, jibi har ciwo yaji duk bata sani ba tana can baki sake wata ‘yar banza na neman k’wace mata Mahmood d’inta... Toh wllhi da sakel hakan ba mai yuwa bane... Ta k’arashe tunanin nata tana mai ficewa fuuu tamkar zata tashi sama... ** Yana haurawa sama shirin fita yai kana ya fito waya manne kunnensa yana magana da Turaki... Turaki yace “You can’t drive like that your Highness ka bari nazo na kaika...!” Cikin kakkausar murya yake fad’in “Mai ka d’aukeni, kan wannan k’aramin ciwon kake cewa bazan iya driving ba... Banida lokacin jiranka Turaki, and I don’t trust anyone cikin Masarautar nan...!” Yana ida fad’in haka bai ko jira cewan Turaki ba ya katse kiran had’ida jefa wayar cikin aljihu... Turaki na kiran sunansa inaa ko amsa sa baiba ya isa ma’ajiyan mitocinsa ya shige guda d’aya yayi ficewarsa... Yana ficewa Waziri ya lek’o daga mab’oyarsa yana wani muzurai da idanu, take ya ciro waya cikin babban rigarsa ya k’ara a kunnensa “Ya fito, kabi bayansa... Kuma ka tabbata bai b’ace maka ba....!” Daga haka katse kiran Waziri yai kana ya nufi sashen Giwa... Duba d’aya Giwa tai masa ta kauda kanta gefe... Waziri ya saki murmushi mai taushi yana mai duban yanda Giwa Ke sakin huci... Da kirari ya soma mata, ya wasata sosai yai mata kirari da yabo sosai kana ya k’arada “Muddin Waziri na numfashi bakida damuwa, idan akan Mahmuda ne kisaka ma ranki Mahmood a tafin hannunki yake domin koda Ubandoma ya munafuncemu ya had’e kai da wani cikin Masarautar nan na aje mutum guda wanda zai dinga bibiyan al’amaran Mahmood da kuma duk yanda yake zuwa zai sanar damu...!” Giwa Ta d’an dubesa kad’an har lokacin fuskarta babu walwala.. “Allah yasa gaskiya kake fad’i...!” Ya kuma murmusawa yana mai takowa gabanta kad’an “Burinki k’iris yake da cika, Ina mai tabbatar miki..!!” Sai wannan karon ta murmusa kad’an kana Ta mik’e cikeda k’asaita, fuskarta na duban wani b’angare take furta “Waziri akwai sauran rina a kaba... D’azu Yazeed yazo min da wani zance kuma na duba maganganunsa sosai na aunasu, tabbas akwai kuraye da dama cikin Masarautar nan... Idan har Ubandoma nada k’arfin halinda zai iya cin amanamu toh ko shakka babu zai iya tona mana asiri.. Ubandoma yasan sirrikanmu da dama bazai yuwu mu k’yalesa haka nan ba..!” Waziri ya tako kad’an yace “Mai kike so Ayi....?” Giwa ta waigo tana dubanasa lokaci guda take d’an buga hannunta dake rufe cikin bak’ar safa... “A sakashi yayi shiru na har abada... A b’atar dashi kaman yanda aka b’atar da sauran..!!” Waziri ya kuma takowa kad’an, shiru na d’an dak’ik’ai suka gifta “Ba abu bane mai sauk’i duba da cewa Mahmood yana nan cikin Masarautar nan a halin yanzu, amma bakida damuwa Allah shi taimakeki... Zan kula da wannan..!!” Giwa ta juyo tana dubansa murmushi saman fuskarta, lokaci guda ta tako daidai gabansa su duka biyun suna duban juna cikin idanu murmushi kwance saman guskokinsu.... K’wank’wansa k’ofan da suka sinkayo ne ya sanya Waziri komawa da baya kad’an ya wani risina kaman mutumin arziki yayinda Giwa ta k’arasa saman kujera tai zamanta... Jakadiya ce ta shigo cikin d’ingishi ga fuskarta gaba d’aya a kumbure sai tururin man zafi ne Ke tashi a jikinta... Waziri yaima Giwa sallama yayinda Jakadiya ta k’araso tana mai gaida Waziri... Kallo guda Giwa tai mata ta ayyana cikin zuciyarta lallai Jakadiya ta daku wajen mahaukaciyar nan, amma ya suka iya haka dole zasu sake komawa har Izzatu ta bud’i baki ta sanar dasu yanda zasu sami Saudatu kafin tayi ajalin mulkinta... Jakadiya ta zube da k’yar tana nishi take gaida Giwa... Giwa ta amsa a dake ko sannu da jiki Jakadiya bata sami darajan wannan ba wajen Giwa... Murya a dake Giwa Ke fad’in “Jakadiya wajen Izzatu muka nufa..!” Gaban Jakadiya ya yanke ya fad’i, ta d’ago kumburarren idanunta tana duban Giwa tsoro dabaibaye saman fuskarta “Allah shi baki yawan rai matar nan fah zata iya kisa... Anya bazamu k’yaleta..” Batakai aya ba Giwa ta aika mata wani irin muguwar kallo, lokaci guda take furta “Yaushe kika fara sanar dani abinda ya kamata nayi Jakadiya...?!” “Tuba nake Allah shi taimakeki... Ayimun aikin gafara..!!” Ta k’arashe tana mai sadda kai... Giwa Ta kauda fuskarta gefe tana mai furta “Zamuje muga Izzatu daren yau dan haka Ki shirya...!” ‘Yan hanjin Jakadiya suka kuma kad’awa, cikinta ya bada wani sautin k’ara, Allah ya gani ko sunan Izzatu taji an ambata yanzu sai gabanta ya fad’i... Tamkar ta kurma ihu haka ta daure tana amasawa Giwa murya cikin inda inda.... Kana ganin Jakadiya kasan ba har cikin zuciyarta take maganar ba akan dole takeyi... ** Tafe yake cikin mota hannunsa duka biyu saman steering wheel, har lokacin itada Fu’ad yake hangowa cikin idanunsa, maiyasa tunanin ya kasa barin zuciyarsa, maiyasa suka kasa b’ace masa daga k’wayan idanunsa... Maiyasa ma abin Ke damunsa in a any case...! Ya d’an fuzar da fuci kad’an yana mai dukan steering wheel da hannunsa maras ciwon.... Yana k’ok’arin saka trafficato kenan ya d’ago idanunsa yana duban mirror nan ya hangi wata mota tamkar tana biye dashi... Idan bai b’ata gani ba wannan motar tun fitowarsa daga masarauta take biye dashi... Speed ya rage kad’an kana ya canza hanya... Yana ganin mai motar ma yai slow kad’an yana k’ok’arin juyawa... Mahmood ya murmusa kad’an yana mai ci gaba da driving d’insa... Kai tsaye gidan Turaki ya nufa ya kirawo Turakin yace dashi gashi nan tafe ya fito haraban gidan kawai ya jirasa dan ba shiga zai ba... Turaki ya fito waje yana jiran isowar Mahmood.. Jim kad’an Mahmood ya k’araso, Turaki ya isa da kansa ya bud’e masa gate... Mahmood ya shigo cikin gidan yai parking motarsa a parking lot... Turaki ya nufo garesa yana tambayarsa meke faruwa... Dubansa Mahmood yai yace “Bani car keys d’inka...” Turaki ya dubesa da mamaki saidai baice komai ba ya nufi cikin gidan, Jim kad’an ya fito da key ya damk’a masa... Mahmood ya amsa cikin sauri kana ya nufi ma’ajiyan motar Turaki.. Turaki ya d’an k’araso yana tambayarsa meke faruwa Kaikaitowa Mahmood yai yace “Kaikam zamuyi magana idan na dawo, just make sure mota ta bata fice daga cikin gidan nan ba..!” Jinjina masa kai kurum Turaki yai yana mai furta “Do you want me to come with you..?” Girgiza masa kai kurum Mahmood yai yace “Kar ka damu kaidai kawai kayi yanda nace...” Turaki ya jinjina masa kai yana mai masa fatan sauk’a lafiya... ** Mahmood yana fitowa daga gidan Turaki bai zarce ko ina ba sai asibiti wajen Baba Wambai kaman yanda likitan ya sanar dashi cewa Baba Wambai ya farka amma sunan Mahmood d’in kurum yake ambata tinda ya farfad’o shisa bai kirawo kowa ba sai shi... Mahmood ya k’araso cikin sassarfa yanda Likitan tuni ya tareshi... Tare suka nufi cikin d’akin Mahmood na tambayarsa ya jikin Baba Wambai... Suna shiga d’akin ya hango Wambai kwance idanunsa na kallon sama... Mahmood ya k’arasa cikin sauri yana ambaton sunansa... Lokaci guda yakai hannunsa ya dafa saman na Wambai yana mai furta “I’m here Baba...!” Baba Wambai da idanunsa Ke duban sama a hankali yake kuma ambato sunan Mahmood da k’yar cikin muryarsa da bai fita sosai tamkar ta ‘yan koyo, lokaci guda yake k’ok’arin ciro wani takarda k’asan matashinsa... Mahmood yai masa K’uri yana duban abinda Baba Wambai keyi... Lokaci guda ya d’ago hannunsa dake tsananin rawa rik’eda wata ‘yar takarda ya aza saman hannun Mahmood.... Mahmood ya rik’e takardan yana juyawa a hankali daidai sanda Majidad’i da mahaifiyarsa suka shigo d’akin a kid’ime.... Saidai shigowarsu Keda wuya Wambai ya soma wane irin numfashi tamkar ransa zai fice cikin jikinsa..... Dr ya k’araso da sauri yana mai umartansu da su fice su basu waje domin su duba jikin Wambai.... Majidad’i kuwa sai fuzga yake yana ambaton sunan mahaifinsa... Nurses sai turasa waje suke yana tarjewa... Mahmood ne ya kamo hannunsa yana k’ok’arin fitar dashi yayinda Majidad’in ya d’ago jajayen idanunsa yana duban Mahmood cikin wane irin huci.... SameenaAleeyou 📚 [7/28, 9:43 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *37* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Turaki yai turus yana duban Mahmood da ya koma tamkar babu laka jikinsa... Lokaci guda kuma yai saurin basa hanya yana fad’in “Shigo daga ciki Your Highness...!” Babu musu Mahmood yasa kai ya shigo cikin parlorn ya k’arasa ya zauna saman kujera, har lokacin bai iya ceda Turaki komai ba... Glass of water Turaki ya mik’awa Mahmood d’in yana fad’in “Have some water..” Nan ma babu musu ya amsa ya kurb’a kad’an... Turaki ya k’arasa ya zauna saman kujera mai kallon na Mahmood d’in.... “Talk to me Your Highness... Meke faruwa..? Ya jikin Baba Wambai..?” Sumarsa ya shafa da duka hannayensa biyu had’ida fuzar da fuci a hankali “Dole na bar cikin asibitin Turaki...That idiot almost creates a scene there regardless of his father’s condition....!” “Kana nufin Majidad’i...?” “Who else..!” Ya bashi amsa yana mai kuma kurb’an ruwan... Fuzar da fuci kad’an Turaki yai sai kuma yace “Allah dai ya baiwa Wambai lafiya ya tashi kafad’unsa, jikina na bani ta hanyarsa zaka sami wasu amsoshin da ka jima kana nema...” Bai rufe baki ba Mahmood yakai hannunsa cikin aljihu tamkar wanda ya tina wani abu, nan ya ciro takardan da Wambai ya damk’a masa ya shiga warwareta... Turaki yai masa K’uri yana duban yanda yake ware takardan... Tas ya warware yana duban hoton zanen gida tamkar na sarauta.... Ya jima yana duban hoton yana k’arema zanen kallo... “What’s that..?!” Turaki ya tambaya... Ba tareda ya amsa masa ba ya mik’a masa zanen... Turaki ya amsa yana juya zanen mai wahalan fasaltuwa... Ya d’ago ya dubi Mahmood “Ina ka sami wannan...?” “Wambai ya bani before na bar asibitin...!” Turaki yai shiru yana mai kuma duban zanen.. “Kaman ginin gidan sarauta..” ya fad’i yana mai kuma juyawa... Mahmood ya jinjina masa kai alamun tabbatarwa... “Bansan mai yake nufi da dank’a min wannan zanen ba, amma koma menene nufinsa nasan zanen nada matuk’ar mahimmanci..!” Turaki ya jinjina kai yace “K’warai kuwa,and probably it might link you to all the answers you’ve been looking for...” Mahmood ya dubesa kad’an kaman zaice wani abu sai kuma ya linke zanen ya tura cikin aljihu, ya d’ago ya dubi Turaki “Ya labarin neman Jafar... Have you found something yet...?” Ya girgiza masa kai a hankali “Dik yanda nake tunanin abin zaizo da sauk’i ya wuce haka... But kar ka damu ina nan ina bincike...” Mahmood ya kuma jinjina kai a hankali... Turaki ya d’an kuma muskutawa yace “Wai mai ya faru ka aje motarka a gidan nan ka fita da tawa..?” Dubansa da gefen idanu Mahmood yai yana mai kuma kurb’an ruwan dake hannunsa, saida ya kwashi wasu dak’ik’ai kana yace “I noticed Someone was following me... Dole nai branching a gidanka dan ya rasani... I’m sure ko wanene Ubangidansa yana can yana basa bad news..!” Turaki ya murmusa kad’an yana mai duban Mahmood da har lokacin juya cup d’in dake hannunsa yakeyi ya k’urama waje guda idanu... Ba komai yake hangowa ba face Fu’ad da Muhibbah... Ya d’an lumshe idanunsa a hankali had’ida fuzar da fuci lokaci guda yake kauda fuskarsa zuwa wani b’angaren... Sosai yake so ya yakice tinanin amma ya kasa... Gyaran murya kad’an Turaki yai yace “But your Highness are sure babu wani abu dake damunka kuma... You seemed preoccupied..” Mahmood ya dubesa kad’an ya kuma kauda kai gefe, bayan shud’ewan wasu dak’ik’ai ya mik’e yana furta “With everything that has been going on you still ask me that question..... I’ll go ahead Zamuyi magana anjima... Keep me posted idan akwai abinda ya canza regarding the search for Jafar...” Turaki ya jinjina masa kai a hankali yana mai furta “An gama Ranakashi dad’e...” Har saida yakai k’ofa ya juyo yana furta “Aff kaga na mance ban tambayi Madam da yara ba...” Turaki ya murmusa kad’an yace “Daga baya kenan Your Highness, bayan kayi nisa duniyar tunanin Gimbiya Raheema.. Toh Madam da yara duk suna lafiya, gobe suke cika sati guda a Jalingo, inaga cikin satin nan zanjeni na d’aukosu dan duk gidan ya min girma gwara su dawo hutun ya

Chapter 22 of 65