idan hakan Ta kasance zai iya yuwa tasan wani abu gameda ciwon Fu’ad tinda zuwansu asibiti shida Turaki nurse guda ya tabbatar masu cewa matar data shigo da Zahra Ta jima sosai cikin d’akin Fu’ad tana dubasa...Who are you Muhibbah...?! Mai kika shigo yi cikin Masarautar nan..?! Maiyasa kike neman ki tarwatsa ahalinmu..Duk abubuwan da suka faru, everything is pointing directly to you ne... What exactly do want from our family..?!
Har Zahra Ta fice bai fahimci Ta fice ba, sosai yai nisa a duniyar tunani... Idan Muhibbah tanada alak’a da duk abubuwan dake faruwa cikin Masarautar Toh ya zama dole yayi taka tsan tsan dan da alama bata shigo Masarautar ba saida Ta shirya... Babu wanda zai iya tunk’aran masarauta mai girma irin nasu yanda tayi ba tareda shiri ba... Shi mamaki ma abin ya soma basa... Sauri sauri ya haura sama ya kunna na’uran computer d’in yana duban abinda take a daidai lokacin...
Kuangin ne suka shigo nata da abin kari... Ta d’auki fork bayan sun fice tana k’ok’arin bud’e lock d’in k’ofa dashi...
Yayi K’uri yana dubanta yanda take dage k’arfinta gaba d’aya wajen ganin Ta bud’e k’ofar...
Cikin zuciyarta take furta “I really need to escape kafin Giwa ko d’aya daga cikin azzaluman yaranta su cimmani... Nasan mutanen da Abbah yace na taimaka masu suna b’oye cikin Masarautar nan... I need to escape kafin su cimmani..!” Ta k’arashe tana mai kuma dage k’arfinta, saidai abinka da k’ofa mai aminci ko gizau bai ba... Saima karyewa da cokalin yayi... Cikeda takaici tayi jifa da cokalin ta koma cikin d’akin ta zauna dirshan tana kuka mai tsuma zuciya...
**
Huci kurum Jamal yake fitarwa yana mai furta “I knew it.. Since from the beginning ban yarda da yarinyar nan ba Maami... But tinda ita d’in k’awar Umama ce komai yazo cikin sauk’i... Kamota bazai mana wahala ba... Umaima zata sanar damu yanda take rayuwa and believe Maami zan kawo miki ita har nan kiyi yanda kike so da ita... Kiyi gunduwa gunduwa da ita idan kina so... I promise I’d bring her here..!” Ya k’arashe yana mai kuma fitar da huci...
Giwa Ta jinjina kai tace “Na tabbata yarinyar nan koma su waye suka turota ta riga ta gama mana b’arna cikin Masarautar nan... Kuma da alama bata Zo ba saida Ta shirya... Amma zatayi nadama da danasanin sanin wannan masarauta da tayi balle har tayi gangancin shigowa cikinta... Mun gama da wanda suka fita balle ita k’aramar alhaki...
SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*
*66*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Zuwa safiya an samu Ansar ya d’an zama stable saidai har lokacin hawaye basu daina zubowa daga k’uncinsa ba... Cikin zuban hawaye ya kuma duban Mommy yace “Alfarma d’aya zaki min Mommy....! Ki sanar dani su waye suka nemi auren Muhibbah..? Ma waye aka aurar da ita..?!”
Cikin kwantar da kai hawaye na gangaro mata tace “Ansar I’ve no idea they are..! Kuma bana tsammanin shi kansa Yawale yasan daga wata duniya suke...!”
Ansar ya kuma dubanta da tsananin mamaki yana girgiza kansa, ya kasa yarda k’iyayyan da Yawale yakewa Muhibbah har yakai wannan matakin, abinda ko wa mak’iyinka bazakayi ba..! Kan mai zai aurartaga mutanen da babu wanda yasan daga inda suke...
Ya sauk’e wane irin nannauyan ajiyan zuciya yace “Mommy this cant be possible... Dole a nemo Muhibbah kuma dole a warware wannan auren muguntar da akai mata... Yau d’in nan basai gobe ba zan shigar da Yawale k’ara... Wllhi sai na d’auresa kodai ya fito min da Muhibbah..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci...
Mommy kanta dubansa kurum take dan bata tab’a ganin d’an nata cikin yanayi makamancin wannan ba..!
Muryar Hameedah dake gefe tana hawaye suka sinkayo tana fad’in “Baffah ya aurar da Muhibbah ne ga wasu Buzaye... Wanda shi kansa baisan daga Duniyar da suke ba..! Nasan Baffah bai kyauta ba amma dan Allah kayi hak’uri Yaya Ansar kar ka shigar dashi k’ara zai zame min abin gori ne daga cikin gidanmu har izuwa mutanen unguwa... Hamma Ansar nasan baka sona ka aureni... Dole akayi maka, dan Allah naci darajan ‘yan uwantaka... Kada ka tozartani a idon duniya....!!” Ta k’arashe hawaye na kuma gangaro mata....
Tausayin yarinyar dasu kansu gaba d’aya duk sai ya kuma rufe Mommy, tasan yarinyar batada laifi mahaifinta ya jawo mata halinda Ta tsinci kanta ciki... Mommy batakaiga magana ba suka sinkayo muryar Ansar yana furta “Bak’in Buzaye..!” Sai yayi Burki ya kuma furta BAK’ON BUZU..!!” Idan bai mance ba Muhibbah ta basa labarin yanda akaita binciken wanene Bak’on Buzu a masarauta...! Duk yanda akayi Wani ne daga Masarautar yazo ya aureta cikin yanayin shiga na b’adda kamanni...! Zasu halak’ata a wannan Masarautar muddin suka fahimci wacece ita... No no bazai bari hakan Ta kasance ba...! He needs to save her..!
Su Mommy gani kawai sukai ya hau fincike igiyar drip yana shirin dirowa daga saman gado...
Mommy ta isa ta rik’esa gam tana fad’in “Ansar lafiya kake...! Ina zaka a haka..?!”
Bai daina fincika ba yake fad’in “Mommy I need to go..! Muhibbah needs me Mommy... Mommy I need to save her... Her life is in great danger...! Mommy rayuwar Muhibbah na cikin had’ari mai munin gaske..!” Ya k’arashe yana mai zira takalmansa...
Mommy da Hameedar duk sun rikice, a rikice Mommy dake rik’eda Ansar ta dubi Hameedah tace maza ta fice ta kirawo likita...
Taci gaba da fad’in “No Ansar bazan Barka ka fice a haka ba...! Ka natsu ayi komai a sannu, bakada lafiya, Maiyasa zaka fincike drip...!”
B’anb’anre hannunsa daga rik’onda Mommy tai masa yana mai furta “Mommy Wai kin mance ne.. This is my profession..! I’m also a medical Dr... Mommy I know what I’m doing... Please let me go...!”
Mommy na hawaye take girgiza masa kai tana furta “No Ansar I can’t let you go... I just can’t...!” Kuka ya hanata ci gaba da magana...
Girgiza kai shima yake yana hawaye yake furta “Mommy I’m sorry... But I’m going... Ki min fatan nasara kawai... Na tafi ko na mutu ko nayi rai... But I must go..!” Yana ida fad’in haka yasa kai cikin sauri... Mommy na kuka sosai tana k’walla masa kira... Cak ya tsaya ya juyo yana duban mahaifiyarsa... Lokaci guda ya dawo da baya ya rungumeta sosai yace “I love you Mommy.. Please forgive me...!” Daga haka Ansar bai kuma tsayawa wata wata ba yasa kai ya fice cikin sauri...
Mommy na kuka tana kiran sunansa inaa ko juyowa baiba ya fice a d’ari...!
**
MASARAUTA
Koda Zuhra ta fito zata tafi sai taji ta lek’a Raheema taga ya ta kwana dan bataji alamun d’uriyarta ba, wata zuciya tace ina ruwanki sabuwar amaryace k’ila baccin huce gajiyan biki take... Hakan yasa bata kuma bi takan Raheemah ba ta janyo ‘ya’yanta suka nufo downstairs... Saidai tana k’ok’arin sauk’a taji kaman k’aran fashewan abu daga d’akin Yazeed... Ta d’aga idanu tana duban d’akin... Sai kuma ta dubi Hadimarta tace “Hindu fita da yaran ina nan tafe..!”
Babu musu Hadimar tayi yanda tace...
Sauri sauri Zuhra ta koma upstairs ta d’an ja ta tsaya jikin k’ofan d’akin Yazeed zuciyarta na bugawa... Wata zuciya tace idan kikaga abinda zai dameki fah..? Take b’angare na zuciyarta Ta bata amsa da fad’in “Mijin K’warai akema kishi... Toh idan kikaga abinda bai dace ba fah..?! Tai shiru tana tinanin abinyi... Tasan halin Yazeed tsaf zai iya kulle Raheema yayi tafiyarsa ba tareda taci koda abinci bane... Maiyuwa ya kulleta ne ma yayi tafiyarsa tinda ba da jimawa ba taji ficewar motarsa...
Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali zuciyarta na kuka nanata mata “Ina ruwanki, Ke naki a wanne idanma wani abin yayi mata... Ai sunfi kusa a halin yanzu...!” Dikda irin wannan batu da zuciyarta Ke mata hakan bai hanata d’an bubbuga k’ofan ba.. Kaman sautin mutum takeji amma muryar bai fita... Hakan yasata saurin murd’a handle amma da alama an kulle k’ofar... Sauri sauri ta isa ma’ajiyan spare keys na gidan Ta d’auko key d’in d’akin ta bud’e... Can jikin gado ta hango Raheema d’aure ta gama jigata ta galabaita.... Raheema na hango Zuhra ta kuma fashewa da kuka hawaye na ci gaba da gangaro mata...
Shaye da tsananin mamaki Zuhra Ke dubanta irin d’aurinda yayiwa Raheema wanda ko ita bai mata irin wannan... Ta isa da sauri ta b’alle sellotape d’in da ya manne bakin Raheemah dashi... Tai wani irin jan numfashi had’ida shak’an iska... Sauri sauri Zuhra ke kwance hawaye basu daina zubowa daga idanun Raheema ba...
Bayan ta gama kwanceta ne ta mik’e da zummar tafiya dan da alama ko idanu Raheemar ta kasa d’agowa su had’a...
Ji tayi Raheema ta rik’o hannunta guda tana kuka sosai, cikin muryar kuka take furta “Zuhra na gode... Na gode..! Dukda ban cancanci taimako a gareki ba amma kika zab’i ki taimakeni... Hak’ik’a ke d’in kinada zuciya mai kyau... Nasan nan cancanci yafiya daga gareki ba kuma banaso nati taking advantage d’in kyakkyawan zuciyarki na nemi tafiyarki dan nasan babu wacce zan mata abinda na miki ta yafe min... Amma hakan bazai hana na rok’i gafararki ba k’awata... Zuhra dan Allah Ki yafe min..! Kiji taisayina karki tafi ki barni da hakkinki... Ki yafe min dan Allah..!!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya ga rawan d’ari na zazzab’i da jikinta keyi...
A hankali Zuhra Ta juyo tana duban Raheemah hawaye kwance saman fuskarta itama... Lokaci guda take furta “Shi taimako ana yinsa ne a lokacinda ka Keda halin taimakawa... Kar kayi la’akari da ma wa zaka taimaka... Ka tuna cewa waye yayi umarni da ayi taimako... Idan zakayi taimako kayi Dan Allah domin ladanka na wajensa..So kar kiji mamaki dan na taimaka miki...!” Ta d’anyi fasali kana taci gaba da fad’in “Raheemah kin min zalunci mafi muni... Na aminta dake kinci amanata! Kinyi amfani da kusancin dake tsakaninmu kin yaudareni... Amma tun kafin aje ko ina ga sakayya kin fara gani, Allah yasa hakan ya zamto wa’azi gareki da masu halayya irin naki... Ina kuma miki fatan Allah ya kawo miki sauk’i cikin rayuwar da kike fuskanta... Ni na yafe miki Raheemah, bazan tafi da k’ulli cikin zuciyata ba... Na yafeki duniya da lahira.. Ina kuma fatan Allah ya yafe miki..!” Ta k’arashe cikin rawar murya irinta mai kuka...
Rungumeta Raheemah tayi tana kuka sosai, su duka biyun suna kuka sosai mai tab’a zuciya... Cikin kuka Raheemah Ke fad’in “Na gode..! Na gode k’awata..! Na gode miki..! Allah Ubangiji ya canza miki rayuwarki da abinda yafi zama alkhairi a gareki...! Thank you my friend..!”
Murmushi Zuhra Ta sakar mata kana tace “Allah sada mu da alkhairi Raheemah... Goodbye..!”
Raheemah tai tsaye tana duban Zuhrar kaman wanda bazasu sake gamuwa ba, kodashike ta tafi kenan bazata kuma dawowa Masarautar ba a cewar Zuhra, idan Yazeed bai aika mata takardan sakinta ba Alk’ali ne zai rabasu...!
Zuhra na fitowa ta tadda Motar da aka turo daga masarautarsu domin ya kwashesu ya iso... Hakan yasa tuni dogari ya fito ya fara loda kayansu a k’aruwar motar ta alfarma... Haka Hadimanta na cikin Masarautar sukaita kukan tafiyarta domin kaw zasuyi kewarta, Hadimarta d’aya tak da tazo da ita daga Masarautarsu mai suna Hindu kawai ta d’auka.. Amma duk Hadiman Masarautarsu Yazeed bata d’auki ko guda ba...
Motarsu na shirin tashi Yazeed ya iso yana faman cika, cikin huci ya nufo Zuhra zai damk’ota Dogarin ya tare gabansa yana fad’in “Hattara Yarima..! Umarnin mai Martaba ne yace a dawo da Gimbiya Zuhriyya Gida..!”
Yazeed bai daina huci ba yake fad’in “Toh sai mai idan Mai Martaba ne yace a maidata gida..! Shi yake aurenta ko ni nake aurenta..?!”
Ya maidoda dubansaga Zuhra wacce ta cika tai fam yace “Kisa aniya ki fito min da yarana daga motar nan dan babu yanda zaki kaimin yara..!”
Zuhra ta murmusa tace “Na gaba ya riga yayi gaba Yazeed.. Na baya kuwa sai labari..! Ai na fad’a maka k’afata k’afan yarana.. Ka gaya min ma waye zan damk’a amanan tarbiyan yarana cikin Masarautar nan...? Dan haka I’m leaving with my kids..!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin shigewa mota...
Yazeed yayi saurin rik’ota yana sakin huci yake furta “No.. Wllhi bazan barki ki tafi min da yara ba..! They’re my children, ‘ya’yana ne they belong here and no where else.. Nan shine mahaifansu..!”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “K’warai babu yanda zaki tafi dasu Rankidad’e..! Idan zaki tafi Ke kina iya tafiya amma yara zasu tsaya a gidan mahaifinsu...!”
A fusace Yazeed ya juyo yana watsama Waziri mugun kallo lokaci guda yake furta “And who gave you the right to interfere..?!” Yayi maganan cikeda takaicin Waziri dan ya gane nufin Waziri tinda yasan yanzu yaran jikokinsa ne shiyasa bazaiso a fita dasu daga cikin Masarautar ba...
Abu kaman wasa labari ya soma karad’e Fada Gimbiya Zeenat zata tafi da yaranta Yarima Yazeed ya doge ya hana... Babu shiri Giwa ta lek’o ta Samanta tana kallon wannan drama..
Zuhra bata kuma bi takan Yazeed ko Waziri ba Ta bud’e mota ta shige abinta taceda Driver su tafi..!
Ai Yazeed bai bari Driver d’in ya soma tafiya ba ya finciki k’ofar driver d’in ya saka duka hannayensa biyu ya cakumo driver d’in yayi jifa dashi waje ya shige cikin motar... Kaman mai tab’in hankali yake furta “So kike ki tafi fine..! Zamu tafi gaba d’aya..! Zamu mutu gaba d’aya kinga shikenan jin huta...
Sanin rashin hankalin Yazeed yasa Zuhra soma girgiza kai tana duban yaranta dake daga bayan jeep d’in Hadimar Ta rungumesu sai kuka suke... Cikin rawar murya Zuhra Ke furta “Yazeed no please...! Yazeed akwai yaranmu cikin motar nan..! Don’t please Yazeed..!!”
Inaaa ko Sauraronta bai ba ya finciki motar kaman mahaukaci suka fice daga cikin Masarautar... A d’ari Giwa ta sauk’o k’asa tana fad’ida Waziri maza yabi bayan Yazeed dan tasan haukansa komai ka iya faruwa...
Zuhra na kuka tana fad’in yayi hak’uri ko dan yaransu ya tsaya, Ta amince bazata tafi ba.. Amma inaa Yazeed balbala gudu kurum yake saman kwalata yana mai ci gaba da sakin huci wanda da ganin kasan ta ko wane b’angare na rayuwarsa bai masa dad’i... Cikin huci yake furta “No Zuhra I cannot be a loser..! I can’t be a loser.. I’m Prince Yazeed AbdulJabbar... Idan bazan zama Champion ba bazan zama loser ba... We’ll die together... No one is leaving me.. Not you nor our children..!!”
Kuka take tana furta “Yazeed please..!”
Cikin daka tsawa ya juyo yace da ita “Shut up..! Shut the hell up..!!!” Daidai sanda k’aruwa motar trailer ta dososu daga d’aya length d’in wanda sam Yazeed baima kula da zuwanta ba... Ji kake gau motocin sun had’a, motar da suke ciki ta fettu gefe ta had’uda jikin bishiya...
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un...!
**
Duk wannan buduri da ake cikin Masarautar Mahmood baida labari yana nan gaban na’uransa yana ci gaba da hasko masa ita, hannayensa rik’eda Taswiran yana kuma gathering duk abubuwan da ya sani gameda ita cikin kwanyarsa, zuciyarsa naci gaba da bugawa yake furtawa a fili “I need to confront her to end all this..!”
Yana tsaka da wannan tinanin ita kaw Muhibbah dake daga can nata b’angaren itama sak’e sak’en yanda zatai ta fice daga kurkukun da aka ajeta take, tinda b’alla k’ofa bazai working ba she needs to come up with something as soon as possible..! Take tinanin ciwo yazo mata, idan tayi ciwon K’arya tasan dole Kuyangin su bud’e k’ofa, idan kuma suka bud’e zasuyi tinanin taimaka mata harm su tafi kiran iyayen gidansu ita kuma sai tayi amfani da daman ta gudu kafin su cimmata...!
Da wannan tinanin ta soma tamke cikinta ta isa jikin k’ofa da k’yar tana bubbugawa tana fad’in taimako..! Taimaki..! A taimaketa..!!
Kasancewar babu Kuyangin wajen yasa babu wanda ya jita... Bata fasa kame cikinta tana sakin k’ara had’ida ambaton a taimaka mata ba...
Daga nan yanda yake kallonta hankali tashe ya mik’e yana kuma duban yanda take murk’usoso alamun batada lafiya... Bai wata wata ba ya fice ya nufi b’angaren nata hannayensa rik’eda Zanen guda biyu....
Cikin sauri ya bud’e k’ofar ya hangota nan kwance Ta rik’e cikinta sosai....
Cak ya tsaya yana sauk’e haki a hankali yayinda itama ta tsaya cak da rik’e cikin nata tana dubansa idanu waje... Su duka biyun duban juna suke, jiri ne taji yana neman d’ibanta da gaske bada wasa ba... Tana gab da silalewa k’asa Mahmood ya k’araso a d’ari yayi jifa da takardun dake hannun nasa ya isa gareta ya tallafota ta fad’o cikin jikinsa...
Tsananin mamaki ya hanata katab’us saima juya mata da duniyar yake, da gaske Rankaidad’e take gani kuma yasa hannaye ya rik’eta...MEKE FARUWA..?!
Ido cikin idanu suke duban juna har lokacin na tallafe da ita, k’irajensu basu daina bugawa ba... Babu wanda ya iya furta koda kalma sai duban juna da suke... K’aran da wayar salulansa yayi ne ya dawo da hankalinsa... Ya saketa a hankali yana mai zura hannu a aljihun jallabiyarsa, daga can asibiti wajen Fu’ad ake kiran....
Lokaci guda Mahmood ya bata baya yana amsa kiran bataji mai akace ba tadaiga ya nufi k’ofa da sauri yana furta “Are you serous Dr..?! Fu’ad can talk again...! I’ll be there in a bit...!!” Sauri sauri ya fice ya barta nan durk’ushe zuciyarta naci gaba da tsinkewa... What’s the meaning of all this..? Mai ya kawo Rankaidad’e cikin image d’in... What is his role...? Mai hakan yake nufi...? Badai shima sunyi tarayya dasu Giwa bane wajen yunk’urin cutar da ita..? Tinanin da ya tsaya mata a rai kenan, a wani b’angare wayan da Mahmood ya fita yana yi shima ya tsaya mata a rai... Wai Fu’ad ya soma magana..! Wannan shine Ana wata ga wata.. sam bazata tsaya su cimmata ba, yanzu da Ta samu Rankaidad’e ya mance k’ofa a bud’e zatayi maza ta fice ne kafin su cimmata... Sauri sauri take k k’ok’arin ficewa daga d’akin kaman ance ta kalli gefe nan taga Taswirorin nan guda biyu wanda ko shakka babu Rankaidad’e ne ya shigo dasu... Ta duk’a da sauri ta d’auka tana dubawa... K’irjinta ya bada sautin Dammm! Ko shakka babu wannan guda d’ayan nata ne wanda mahaukaciyar nan Ta mallaka mata... Wannan kuma batasan dashi ba sai yau... Ya akai na hannunta ya isa wajen Rankaidad’e..?! Kardai shine yaje har gidan Mommy ya satota... Kuma ko shakka babu wannan Taswira guda d’ayan shine wanda take nema kwanakin baya da ace zata had’a dana cikin wayarta wanda ta gani d’akin Jamal tabbas da zanen ya bayyana mata ya fito fili... Abinda Ta jima tana nema zai bayyana...! Toh amma yanzu wayarta baya tareda ita... Shin yaya zatayi..? Bazatayi wasa da wannan daman na k’arshe ba... Allah yasan dalilin da yasa zanen ya kuma dawowa hannunta... zatayi duk yanda zatayi Ta shiga d’akin Jamal ta nemo wancan na cikin d’akin nasa ta had’e zanen waje guda, watak’ila mutanen da Abbanta yake so ta taimaka cikin Masarautar suna k’ark’ashin wannan zanen ne...!
Da wannan tunanin ta janyo mayafi guda ta nad’e fuskarta dashi yanda baza’a ganeta ba, cikin sauri ta fice daga d’akin....
SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*
*67*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Muhibbah na k’ok’arin ficewa daga sashen kenan taci karo da d’aya daga cikin Kuyangin dake tsaronta... Tai birki taja ta tsaya... Kuyangar ta zaro idanu waje tana furta “Rankidad’e ba’a baki izinin fita ba, Kiyi hak’uri ki koma kada ki jefamu cikin masifa... Ki cecemu ki koma cikin d’akin...!”
Muhibbah na girgiza kai take furta “Hasiya taimako na zakiyi, Ki tuna idan kin taimaki wani Allah zai taimakeki.. Rayuwata data wasu mutane yana cikin had’ari mai munin gaske a Masarautar nan... Ki taimakeni Hasiya bamuda sauran lokaci, na baro ahalina cikin tashin hankali, mutanen nan satoni sukai suka rabani da mijina wanda aka d’aura min aure dashi suka kawo nan suka aje domin cimma burinsu... Hasiya kema mace ce kuma wataran zakiyi aure zaki fahimci abinda nake nufi... Dan Allah Ki taimakeni kada ki tona min asiri..!!”
Jikin Kuyangar ya d’anyi sanyi, ta risina tace “Toh yanzu Rankidad’e ya kike so nayi, mai kike so na miki...?!”
Muhibbah ta murmusa tace “Kayan jikinki nake so ki bani ke ki amshi na jikina Ki saka, idan na fita da wad’annan tufafin zasu iya gane ko ni wacece tunda su suka ajeni a wajen nan...!”
Kuyangar ta d’anyi Jim kaman mai tunani sai kuma tace “Amma ni zaki sakani cikin masifa Rankidad’e...!”
Muhibbah ta girgiza kai tace “In sha Allah Babu abinda zai sameki, Allah yaga nufinki, da niyyan taimako kikayi babu abinda zai sameki... Allah zai kiyayeki...!”
Kuyangar ta jinjina kai tace “Tinda Kikace Allah kin gama magana Rankidad’e... Kuma nima bazanso su cutar dake ba idan har da niyyan cutarwa suka rufeki cikin gidan nan... Zanso nayi taimako koda so d’aya ne a rayuwata a lokacinda nakeda halin yin taimakon... Rankidad’e mu shiga daga ciki na baki tufafi na..!”
Muhibbah Ta murmusa cikeda Farin ciki tai saurin janyo hannun Kuyangar suka shige daga ciki tanai mata godiya....
Haka suka canza Tufafi ta saka kalan tufafin Bayin cikin Masarautar yanda babu mai cewa ba Kuyangar cikin Masarautar bane... Ta kuma rufe fuskarta yanda baz’ai saurin ganeta ba....
Kuyangar Hasiya ta shige cikin d’akin ta zauna a matsayin Muhibbah...
Tana fitowa ta soma bin bango tana tinanin ta ina zata b’ullowa al’amarin, idan ta nufi d’akin Jamal kai tsaye ko shakka babu zata iya taddasa nan cikin sashen nasa zai iya kamata kuma idan ya kamata komai ya b’aci..! Meye abinyi wanne zatayi...?!
B’angare na zuciyarta yace ki fara duba sashen Giwa, da alama hankalin Masarautar ba’a kwance yake ba dan taci karo da wasu bayi a hanyar ta na fitowa sai gudu suke kaman dai cikin Masarautar babu lafiya...! Zuciyarta ya raya mata Ta fara duba sashen Giwa ta tabbata Jamal yana can kafin ta tunk’ari d’akinsa... Haka cikin sand’a da dabara wanda zakayi zaton kuyanga ce ta nufi b’angaren Giwa harda d’aukan paranti daga parlor yanda Kuyangi Ke kaiwa suna komowa Ta nufi upstairs dashi, tsaf zakayi tunanin Kuyanga ce take gudanar da ayyukanta....
A daidai mashigar parlorn Giwa na sama ta soma jiyo muryar Giwa da Jakadiya, Jakadiya na fad’in “Allah shi taimakeki ai Rankaidad’e Yarima Jamal ya kasa hak’ura har dare yayi akai masa amaryarsa, da alama burinki zai cika kafin dare...!”
Giwa tace “Ban fahimceki ba Jakadiya..! Kinaso kice Umaima tana b’angaren Yarima Jamal yanzu haka..?!”
Jakadiya Ta jinjina kai tace “K’warai Rankidad’e..! Gimbiya Umaima tana can b’angaren Yarima Jamal, ni ya umarta yace nai masa kiranta duk yanda za’ai akwai magana mai Muhimmanci da yake so su tattauna.... Kuma nasan bazai wuce kan wannan yarinyar ‘yar lek’en asiri Muhibbah ba... Toh kinga kuwa Rankidad’e idan suka keb’e su biyu ai zai wahala ya barta Ta fito ba tareda wani Al’amari ya gifta tsakaninsu ba... Ke shaida ce yanda yake matuk’ar k’aunar yarinyar da son kasancewa da ita...!”
Take Giwa taji wane irin Farin ciki na zuwa mata finally zata cikawa Boka Tal’udu burinsa... Ta Kece da wani irin dadiyar k’eta tamkar ba basarakiya ba tana furta “Da kyau..! Yayi kyau Jakadiya..! Kin kwana biyu bakizo min da labari mai dad’i irin wannan ba... Daga rana mai kaman ta yau Umaima Ta zama tarihi... Na ajiyeta ne Ta zamto sadaukarwa ta k’arshe daga tsatson Sarki Jamaluddeen.... A yau idan har d’ah na Jamaludden ya kusanceta shikenan ta zama tarihi a wannan duniya tamu..! Nasan wanann babban kyauta zai kuma d’aga darajata a wajen Sarauniya Tamuna..!!” Ta kuma kecewa da dariya kaman wata mai tab’in hankali...
Zuciyar Muhibbah yayi wani irin tsinkewa, k’iris ya rage batayi fatali da farantin dake hannunta ba jin irin k’ullin da Giwa Ke shiryawa Umaima... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai take iya nanatawa cikin zuciyarta... Lallai Giwa tayi nisa a kafurci da son mulkin Duniya... Batasan a sahun da zata aje wanann azzalumar matar ba... Tsayuwa a nan bai ganta ba, she needs to save Umaima duk yanda za’ayi...!
Cikin sauri tasa kai ta juya zuciyarta bai daina bugawa ba...
Da dabara ta isa sashen Jamal, dukda tsananin had’arin dake tunk’aranta ji take bazata iya barin Umaima Ta halak’a ba, ko babu komai Umaima ta mata hallaci... Yanzu ceton rayuwar Umaima shine top priority d’inta... Bazata bari Giwa ta kuma salwantar da wata rai sabida son zuciya irin nata ba...
Zuciyarta sai bugawa yake tana mai hango tsananin had’arin dake gaba gareta, a hankali ta mak’ale jikin window d’in parlorn tana sauraren tattaunawar Jamal da Umaima...
Jamal ya kuma duban Umaima hannayenta rik’e cikin nasa yace “Sweetheart, she deceived you... She tricked you, she used you... That girl is nothing but a fraud..! Nasa anmin bincike ita d’in ba student bace... Kawai Masarautar nan tazo da wani agenda d’inta wanda bai wuce taga bayan ahalinmu ba...!”
Cikin rashin yarda Umaima Ke girgiza kai tana furta “But... How
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 44 Chapter of 65