Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ya k’arashe yana duban Mahmood d’in.... Shiru ya d’an gifta tsakani ba tareda ya kuma cewa komai ba, tabbas yana so ya nemo Ja’afar yanda ya shiga ya fita.... Ya kuma d’agowa ya dubi Baba Wambai kana yace “Na gode Baba, ni zan wuce...!” Yai maganar yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye... Baba Wambai ma k’ok’arin mik’ewan yake saidai tuni Mahmood ya taimaka masa ya mik’ar dashi tsaye had’ida rik’e hannunsa guda.... Lokaci guda suka nufi k’ofan gidan Baba Wambai a haka, yayinda Dattijo Wambai yaci gaba da fad’in “Sarkin gobe bazaka sha ko ruwa gidan Baban naka ba...?” Murmushi saman fuskarsa yake fad’in “A’a Baba na gode k’warai, Allah ya k’ara maka lafiya.....!” Baba Wambai ya amsada Ameen yana mai ci gaba da sakawa Mahmood Albarka, a daidai sanda suka iso Gate d’in gidan... Baibar k’ofar gidan ba har saida ya tabbata Baba Wambai ya shige ciki lafiya kana ya matsa daga wajen ya ciro wayarsa a aljihu yana neman layin Turaki... ** Giwa dake tsaye tana huci had’ida aikama Ubandoma dake duk’e gabanta jahilin kallo, lokaci guda Ta ambato sunan Ubandoman cikin wane irin kakkausar murya... Ubandoma ya risina yana mai amsawa had’ida kirariwa shugabar tasa... Giwa da kanta Ke sama tana duban wani gefen cikin tsananin k’unan rai taci gaba da fad’in “Zaka amshi horon mari daga hannun Jakadiya..!” Jakadiya da Ubandoma suka dubi juna a tare cikeda firgici.... “Jakadiya..!!!” Giwa Ta kuma ambato sunan Jakadiya cikin kakkausar murya... Babu shiri Jakadiya ta risinawa tana mai furta “Angama rankishi dad’e, Ubandoma godiya yake...!” yayinda Ubandoma ya baje babbar riga yana mai kuma neman gafara wajen Giwa, Jakadiya ta mik’e tana nad’e hannun rigarta su duka biyun duban juna suke itada Ubandoma... Yana k’yafata mata idanu had’ida had’e hannayensa biyu waje guda alamun neman afuwa... Gigirza masa kai kurum Jakadiya takeyi alamun batada zab’i... Ubandoma ya kuma risinawa yana fad’in “Rankishi dad’e a duba lamarin nan dai.. Ai mani aikin gafara bazan sake ba Allah shi taimakeki....!” Duban da Giwa tai masa ya sanyashi had’iye sauran kalaman nasa... Take Ubandoma ya soma karanto sunbatu cikin zuciyarsa yana mamakin Wai Jakadiya ce zata mare sa.... Aiko bai ida tinanin ba yaji sauk’ar wata jahilar mari a k’uncinsa wanda saida ya tafiyar masa da jinsa da ganinsa na wasu dak’ik’ai... . Ya dafe k’uncinsa a birkice yana kuma sadda kai k’asa yana fad’in “Tuba nake Allah shi taimakeki... Tuba nake sarauniyar Masarautarmu... Ki yafeni Giwar Amale...!” Giwa ta kuma takowa gabansa kad’an cikeda mulki da isa kana tace “Ka sanar dani Ubandoma shin kunje wani wajen ne...?!” Ya girgiza kai cikin sauri yana mai furta “Allah shi taimakeki tare muke a masallaci toh sai ya bani damin kud’i na rabawa mabuk’ata da musakai dake zama bakin masallaci... Daga nan na nemeshi na rasa Rankishi dad’e... Ko k’yallinsa ban kuma hangowa ba...!” Ya k’arashe yana mai kuma sadda kai k’asa har yanzu rik’e yake da k’uncinsa yanda Jakadiya Ta shata masa mari... Taci gaba da huci tana aika masa muguwar kallo, lokaci guda take ci gaba da fad’in “Sabida Mahmood d’in Aljani ne shiyasa zakace ya b’ace maka ko... Sau nawa zan sanar dakai koda wasa kada ka kuskura ka bari Mahmood ya b’acewa ganinka... Dik yanda Mahmood zai kasance ya zamana kaima kana wajen... Toh kan mai zaka Zo min da batu irin wannan...?!!” Ta k’arashe cikin tsananin huci lokaci guda ta juya ta bada baya tana mai fad’in “Ubandoma..!!! Zaka karb’i horona mai tsanani idan har abu makamanciyar haka ta kuma faruwa...!!” Ubandoma ya kuma zubda kai k’asa yana mai ban hak’uri da neman gafarar Giwa, jikinsa har wane irin karkarwa yake... Alamu da ido taima Jakadiya kana Jakadiyar ta bud’e murya tace “An sallameka Ubandoma... A kiyaye ayi kuma hattara....!!” Ubandoma ya kuma risinawa yana mai mik’a godiyarsa tareda tabbatarwa Giwa hakan bazai kuma faruwa ba... Yana ficewa Giwa ta dubi Jakadiya dake zube k’asa a wajen kana tace “Jakadiya..!” Jakadiya ta kuma risinawa had’ida d’ago jannu guda alamun jinjina kana tace “Allah shi taimakeki...!” Giwa taci gaba da fad’in “Mai kike tunani kan Yarima Mahmood...?!” Jakadiya Ta kuma risinawa kana tace “Allah shi baki yawan rai Yarima Mahmood yaro ne mai biyayya tun tasowarsa...!” Giwa tai shiru tamkar mai nazari kana tace “Mai kike tunani idan ya tsananta bincike...?!” Wannan karon a firgice Jakadiya ta d’ago tana duban Uwar gijiyar tata kana ta kuma maida kanta k’asa, cikin daburcewar murya take furta “Bazai fahimci komai ba Rankishi dad’e... Amma saidai... Ina tsoron ranan da zai tono sirrikan da muka jima da aza masu k’as.....” Batakai aya ba Giwa ta dakatar da ita da fad’in “Jakadiyaaa.!!” Cikin sauri Jakadiya ta rik’e labb’an bakinta duka biyu tana mai furta “Tuba nake Allah shi taimakeki... Yarima Mahmood bazai tab’a tono komai ba... Amma Rankishi dad’e idan har ya tabbata Sarki na gaba komai ai ka iya faruwa....!” Wannan k’asaitaccen murmushi Giwa tai kana tace “Inada manufata da yasa nake so lallai lallai shine zai d’ale Karagar mulkin a daidai wannan lokaci.... Tal’udu bazai tab’a min K’arya ba Sarautar bazata fice daga cikin Ahalin Mijina ba....!!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin murmushi had’ida kishingid’a cikin gadon mulkinta.... *** Da tsananin mamaki Turaki ke dubansa hannu a kunkumi, lokaci guda yake furta “Unbelievable..! Wai dan Allah your Highness kaine haka...? Shikenan daga Spain ka koma Niger....!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa... Mahmood yace “Ina ka aje motar...?” Turaki yai masa nuni da motar dake pake tsallaken kwalta... Yarima Mahmood yace “Muje da Allah kafin wani yai noticing d’inka ma...” Bai ko jira amsar Turaki ba yasa kai ya nufi motar... Turaki yabi bayansa da kallo yana furta “Mahmood mai abin mamaki...” Lokaci guda ya girgiza kai yana mai sakin murmushi kana yabi bayan abokin nasa.... Daidai nan motar Majidad’i D’an wajen Baba Wambai mai neman sarautar Ta shigo kwanar... Bayan Turaki kawai ya hango ya gane abokin Yarima Mahmood ne... Toh mai ya kawo abokin Yaima Mahmood gidansu...? Kardai Mahmood ne ya turosa wajen Mahaifinsa dan su kuma saye zuciyar Mahaifin nasa su kuma karkatar da ra’ayinsa... Lallai Mahmood baisan ko Shi d’in wanene ba har yanzu... Bazai yuwu ya shiga tsakaninsa da mahaifinsa ba ya hanasa amshe gadon sarautar Kakansu da Uban Mahmood yai fin k’arfi wa mahaifinsu....Toh idan za’a tashi Masarautar wllhi sai ya amshe mulkin gidan daga hannun ‘ya’yan Abduljabbar..... Da wannan tunani ya isa Gida, ko parking mai kyau bai ida ba ya fito yana tafe yana sakin huci kaikaice tafashesshen Koko ne.... Ya iske ma’aikatan gidan tsakar gida suna gaidasa ko ci kanku baice dasu ba ya nufi b’angaren mahaifiyarsa tamkar zai kifa da k’asa, yana tafe yana k’walla mata kira... “Innani..! Innani..!! Innani...!!!” Budurwa mai kimanin shekaru 26 wacce ke kwance bisa kujera mai d’aukan mutum uku itace Ta amsa masa da fad’in “Kai Yaya irin wannan kira saikace Aunty Jamila ce ko kuma Yasir ko Nimra ne ka rasa d’aya cikinsu.. Ni wllhi ka razanen...!” Ta k’are ashe baki a ture.. Majidad’i yace “Ke Juwairyya ni ba sa’anki bane zakiyi ma sarki magana haka ne...?” Juwariyya ta zaro ido waje had’ida k’ame baki “Tabb Yaya ai wllhi dama hak’ura Kai dan...” Batakai aya ba ya bige bakinta yana fad’in “Sai na karyaki na sake jin kince banyi zubin sarakuna ba... Ina Innani take...?!” Juwariyya na k’unk’uni rik’eda bakinta ta nuna masa hanyar bene.... Daidai sanda Majidad’i yakai dubansaga b’angaren benen Dattijuwar mai k’aramin jiki irin masu suffan mafad’atan nan ta fito tana gyara d’aurin kwali take fad’in “Yaya Wai yaya akai ne...Sarkin gobe Kai kuma fah, lafiya daga Ina haka.. Waye ya b’ata maka rai inyi...?!” Juwariyya dai ficewa tai tana ci gaba da k’unk’uni... Lokaci guda kuma ta lab’e jikin k’ofa tana sauraran tattaunawan Yayanta da Mahaifiyarta.. Majidad’i na sakin huci yake fad’in “Innani uban mi ya kawo Mahmood gidan nan...?” Innani ta dafe k’irji tace “Mahmuda fah... A’a badai shi ka gani ba don baizo gidan nan ba...” Majidad’i bai daina tururi ba yake fad’in “Ba yanzu naci karo da abokinsa waje ba...!” Innani dafe da k’irji take girgiza kai kana tace “A’a bakadai duba da kyau ba... Yo Mahmuda yazo gidan nan yamin mai balle har abokinsa...!” “Ai dama ba wajenki zaizo ba wajen tsohon nan mai d’aure masa gindi da zigasa zai zo shi....!” Innani ta girgiza kai tace “Kai Majidad’i ka b’ata gani, yau bak’o guda Babanka yayi tun wayewar gari kuma bak’on Buzu ne... Ka kwantar da hankalinka Majidad’i ko Mahaifinka baya so sai kayi sarauta kaji koh... Haba ni da na tabbata Mahmood da ‘yan uwansa kashe juna zasuyi sabida fitinan son mulki.... Kaga cikin sauk’i zakayi sarauta.. Su Turai a fice a bamu waje, yanda nake ‘yar tsurut d’in nan haka zan fitar da Giwa daga gidan wayaga cinnaka ta kori Giwa...!!” Ta k’arashe tana mai fashewa da dariya... Yayinda d’an nata ya bita da kallo yana mai ci gaba da sakin huci a hankali... Juwariyya na gama nad’e komai ta koma gefe ta zaro wayarta take ta shiga neman layin Raheema...! *** Kasancewar duk daren Juma’an k’arshen wata Ahalin Giwa na hallara gaba d’aya a sashenta da daddare don cin abinci a farfajiyan b’angaren nata yanda ake k’awata wajen da manyan dardumai da kuma pillows na alfarma had’ida k’awata wajen da ado da kwalliya irinta alfarma yasa sai shirin fita taron suke.. Muhibbah ta dubi Umaima da mamaki kana tace “Kuma Wai Hakan a’adan gidan nan ne... Toh maiyasa ni zanje tinda Ahalin cikin gidan nan ne kawai Ke hallara...” Umaima tace “Ke bak’uwarmu ce dan haka har zuwa lokacinda zaki tafi ki bar gidan nan ki dinga lissafin kanki cikin Ahalin gidan nan, ai dai kinji mai Maami tace, bazataji dad’i ba idan bata ganki wajen ba....” Muhibbah tai shiru tamkar mai nazari, hakan na nufin zata had’u dasu kaf d’insu kenan a daren nan.... What if ta kasa jurema hakan har tai wani abinda zata fallasa kanta..? Take taji b’angare na zuciyarta na k’arfafa mata gwiwa da fad’in zaki iya Saudat.... D’agowa tai ta d’an dubi Umaima murmushi saman fuskarta kana tace “Shikenan na amince zanjeni...” Umaima ma Ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yauwa ko kefa yanzu naji batu...” Take Umaima ta fito masu da kaya irinta mulki da sarauta tace shi zasu saka... Muhibbah ta dubeta ta dubi kayan... Kafin tai magana Umaima tai saurin katseta da fad’in “Don’t say anything Hibbah... Tashi kawai ki shirya bara nayi wanka Zahra ma na shiryawa already....” Ta k’arashe tana mai fad’awa bathroom yanda Ta bar Muhibbah tsaye nan cikin closet d’in rungume da lallausar Cotten lace kalar ja anyi masa ado da duwatsu masu d’aukan idanu anyi mata d’inkin doguwar riga irin mai bajewa daga k’asa... Ga wani mayafi mai k’yalk’yali da d’aukan idanu jikin kayan... Murmusawa Ta d’an kumayi kana ta saka rigar kaman yanda Umaima Ta buk’ata.... Ya Subhanallah! Sosai rigar ya zauna jikinta, ita kanta saida ta jita wane iri cikin kayan... Ita kanta saida ta yaba kyaun da kayan yai a jikinta sanda ta dubi kanta jikin marfin wardrobe d’in da yake zallan madubi ne... Tsaf Ta ida shirinta ta nufo parlor sai watsa k’amshi take, ita kanta tasan tayi kyau dukda babu kwalliya a fuskarta.... Tai tsaye a parlorn tana kallon wani hoton zane na ginin gidan sarauta dake lank’aye jikin garu nan cikin parlorn tsakanin D’akin Umaima da Zahra.... A haka Umaima ta gama shirinta itama ta fito.. Tai tsaye tana duban Muhibbah dake bin zanen ginin da kallo cikeda nastuwa tamkar mai nazarin wani abu.... Umaima ta k’araso tana fad’in “Wai dama Kina tsaye a parlor...? I thought kina tareda Zahra...” Ta murmusa kad’an had’ida juyowa tana duban Umaima da Ta fito cikin shiri kana tace “Ina tsamman Zahra bata gama shiri ba dan banga fitowar Kuyangarta ba...” Umaima Ta jinjina kai a hankali tana duban hoton zanen gidan Sarauta da Muhibbah ta tsaresa da idanu kana tace “Wannan hoton Yarima Jamaludden naji dashi sosai... Kyautarsa aka basa sanda yai rakiyawa mahaifinsa zuwa wata masarauta a cen k’asashen nahiyar Yamma...!” Jinjina kai Muhibbah tai tana mai kuma duban hoton da yake k’unshe da wasu sirrika kana tace “Duk wanda ya zana tabbas ya iya zane...” Umaima ta jinjina kai “Sosai kuwa, ai kyautace ta musamman akaiwa d’an Sarki...” Muhibbah Ta kuma jinjina kai kana tace “Amma Maiyasa Yarima Jamal ya lank’aya hoton a nan dik irin mahimmancin da hoton kedashi a gareshi... Ya kamata hoton ya kasance yana kusa dashi ne...” Ta k’ara tana mai tsare Umaima da idanunta da suke farare k’al wanda suka dace da cute round face d’inta... Umaima da tai shiru tamkar wacce tai nisa a wani duniyar na tunani a hankali ta soma takowa ta k’araso gaban hoton... Lokaci guda tasa hannu tana shafawa, hannunta nakan hoton take furta “Kasancewata masoyiyar zane ko wanne iri yasa ya aje hoton a nan, da fari naso ya bani kyauta amma ya sanar dani mahimmancin hoton a gareshi don haka ya aje a nan don na dinga gani....!” Muhibbah ta jinjina kai a hankali tana mai kuma nazartan wannan zanen gida mai dadd’en tarihi da aka yishi da wane irin fasaha mai rud’ar dakai... Dan kashi dai zanen gidan sarauta ne mai kyaun gaske amma baka isa kace ga k’ofar shiga ba dukda cewa ta wata fuskar idan ka dubi zanen zakaga kaman ga k’ofofi rututu amma idan ka matso sosai k’ofofin zasu b’acewa ganinka sai Kaga Tamkar kwalliya ne ba k’ofofi ba.... Tana nan tsaye tana kuma nazarin hoton taji muryar Umaima na fad’iwa Zahra “Yauwa kin fito, dama fitowarki muke jira... Muje Hibbah...” Ta k’arashe tana mai janyo hannun Muhibbah da har lokacin bin wannan hoto takeda kallo... Zarah kaw sai yaba kyaun da Muhibbah tai take Umaima na tayata, ita kaw Muhibbar bama tasan sunayi ba dan har wanna lokaci nazarin zanen nan take.... Suna tafe bisa matakala suna sauk’owa Zahra Ke fad’in “Nifah Aunty Umaima wllhi banson Kuyangar nan da Maami tace lallai lallai ita zatake kula da al’amra na, nifa ban saba haka a Spain ba, nafi ganewa nayi komai da kaina daga ni sai Paa d’ina....!” Ta k’arashe baki a ture daidai sanda suka ida sauk’owa Kuyangar kaw na biye dasu kai a k’asa... A daidai sanda suka ida sauk’owa daga matakalan benen Umaima ta d’agawa Kuyangar hannu alamun ta daina binsu kana ta dubi Zahra tace “Aiko hak’uri zakiyi Gimbiya, dan nan da spain ba d’aya bane... Sannan a wannan stage d’in da kike dama dole a miki assigning Kuyangar da zatake kula dake da kuma al’amaranki musamman da shike babu mahaifiyarki a raye...!” Ta k’arashe cikeda tausayawa... Kalaman Umaima na k’arshe ya sanya Muhibbah juyowa kad’an tana duban Zahra cikeda tausayawa musamman da taga yanayin da fuskar yarinyar ya shiga.... Hannun Zahra ta kamo kad’an kana tace “But you’ve your Grandma, and your Paa, ga kuma Uncles d’inki sanan ga Auntynki Umaima... Kuma duka suna sonki kinji koh...!” Ta k’arashe tana k’ok’arin cheering yarinyar... Murmushi Zahra ta saki a hankali kana tace “Thanks Aunty Muhibbah... Amma saidai kin mance da mutum guda...!” Muhibbah ta d’an zaro ido kad’an kana tace “Wa kenan...?” Umaima tai karaf tace “Raheema matar Paa d’inta....” Take annurin fuskar Zahra ya d’auke lokaci guda take furta “No, bana sonta, kuma bana so Paa ya aureta.... Ni ke nake nufi Aunty Muhibbah, kin manta baki lissafo kanki ba cikin wad’anda nake dasu a yanzu...” Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Aw ai gani nayi ni ba jimawa zanyi a Masarautar ba shiyasa... But Kiyi hak’uri kar Ki d’auka da wani nufi kinji.... You’ve me as well..!” Ta k’arash murmushi fal fuskanta.... Cikeda jin dad’i Zahra ta rungume Muhibba tana fad’in “Gracias Tìa Hibbah....!” Ta murmusa itama kana tace “Wait mai kikace kinsan bana jin Spanish...” Zahra ta rausayar da idanu kana tace “Well, Assignment...!” Muhibba ta girgiza kai kana tace “No way... I hate assignments... Nadai San Gracias godiya ne but Tia... Ban sani ba....” Zahra ta d’an kuma darawa kad’an had’ida yin fari da idanu kana tace “Tia Sabon sunan da zanke kiranki dashi kenan.... Tia means Aunt in Spanish...” Suka d’an dara gaba d’aya a tak’aice harda Umaima daidai lokacinda Raheema ta shigo parlorn Kuyangarta na biyeda ita a baya.... Cak Ta tsaya tana dubansu yanda suka cika da Farin ciki gwanin ban sha’awa... Zuciyarta ta soma mata zogi, hannu ta d’agawa Kuyangar nata alamun dakatarwa kana ta soma takowa garesu cikeda k’asaita..... SameenaAleeyou 📚[6/14, 6:09 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *018* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Raheema na K’arasowa tai k’ok’arin d’aura fake smile saman fuskarta mai cikeda k’asaita, a daidai lokacinda Umaima tai noticing d’inta.... Umaima ta tareta da fad’in “Barkada isowa Gimbiya Raheema kuma matar Yayanmu....!” Tai maganar murmushi fal fuskarta... Dik sanda aka ambaceta da matar Mahmood ji take kanta na kuma fashewa, tana jin wani irin dad’i can k’asar zuciyarta... Ta d’an fad’ad’a murmushinta had’ida furta “Barkanki Gimbiya Umaima kuma k’anwar mijina....!” Suka kuma murmusawa a tare kana Raheema ta kaikaito tana duban Zahra da tai kaman bataji isowar mutum wajen ba... Ta d’an tako zuwa gaban Zahra kad’an kana tace “Daughter ya jikin naki.... I’m glad you’ve recovered....!” Ta k’arashe cikeda kulawa Rausayar da idanu Zahra tai kana tai wasu ‘yan maganganunta cikin harshen spanish sannan ta sakarwa Raheema murmushin yak’e tace “Oh really... Well thanks then.. If you’re really sincere...!”Ta k’arashe tana mai janyo hannun Muhibbah had’ida furta “Tia Hibbah muje, let’s sit together... There’s a lot more I need to know about you....” Ta k’arashe murmushi fal fuskanta yayinda Muhibbah ta saci kallon Raheema dake binsu da wane irin kallo kana Ta maidoda dubantaga Zahra tana mai ci gaba da amsata cikeda Farin ciki... Fuzar da huci kad’an Raheema tai daidai sanda wayar salularta ya soma ringing... Gimbiya Zeenat ce mai kiran nata.... Rai b’ace ta d’aga wayar... Daga d’aya b’angaren Gimbiya Zeenatu tace “Kina ina...? Maza kizo ina nemanki...!” Bata jira amsar Raheemar ba Ta katse kiran..... Rausayar da idanu Raheema ta kumayi tana hangen su Zahra da Muhibbah daga nan yanda take tsaye ta cikin k’ofar glass sai raha suke daga cen yanda suke zaune a farfajiyan haraban.... Ta kafe Muhubbah da wani irin duba na tsana kana Ta juya ta fice Kuyangarta na take mata baya... Tana isa ta tadda Gimbiya Zeenat a d’aki sai faman safa da Marwa take... “Aunty lafiya irin wannan kira haka....!” Muguwar kallo Gimbiya Zeenat ta watsa mata kana tace “Raheema Wai lafiyarki kuwa.... Kan wane dalili zaki k’i d’aga wayar Juwariyya bayan kinsan kalan information d’in da muke samu daga wajenta.... Sanin kanki ne wannan Majidad’in ba yarda da uwarsa mukai ba, na tabbata ko asiri sai tayi dan d’anta ya d’ale Karagar mulkin nan... Mu kuma babban burinmu shine Mahmood ya sami mulkin domin mu sami yanda muke so... Amma kan mai Juwariyya data juyawa ‘yanuwanta baya zakiyi banza da kiranta harda baiwa Kuyangarki wayar kice bakida lokacin d’agawa... K’ilan baki son mijin naki ya sami sarautar ne koh...?” Ta k’arashe tana kuma aika mata wani duban... Fuzar da fuci kad’an Raheema tai kana tace “Allah Aunty na zaci wani abinne... Yo kan wannan ne dama...?” Gimbiya Zeenat ta kuma watsa mata harara kana tace “Ban fahimceki ba, wannan d’in k’aramin abu ne... Muna magana ne kan sarautar mijinki Raheema...!” “Aunty nifa yanzu ba sarautar Mahmood bane gaba na... Wllhi ni yanzu na mallakesa gaba d’aya shine damuwata da sarauta ko babu sarauta... Ni shi d’in kawai nake so na mallaka, babu ruwana da wani sarauta ko rashinta as long as he’d remain mine, ni kad’aina and no body else’s...!” Ta k’arashe tana sakin huci... Shaye da tsananin mamaki Gimbiya Zeenat Ke dubanta kana tace “Eh lallai na yarda...! Toh barikiji na fad’a miki, wllhi wllhi bazan zauna na zuba miki idanu Ki rusa min plans d’ina ba... Dole Mahmood yai sarauta dan idan ya aureki bai a matsayin Sarki banga amfanin auren ba.... Dan haka dole kici gaba da baiwa Juwariyya had’in kai tana kawo mana rahoton dik abinda Ke wakana cikin gidansu...!” Daga haka Gimbiya Zeenat tasa kai zata shige... Raheema ta katseta da fad’in “Aunty duk bazaki fahimci Abinda nike nufi ba, amma idan kika fita kikai tozali da shegiyar yarinyar nan mai bak’in shishigin masifa da nake baki labari zaki yarda ba yak’in neman mulkin Mahmood bane gabanmu yak’in raba wannan tsinanniyar da Masarautar nan ne babba gabanmu....!” Ta k’arashe tana mai k’arasowa gaban ‘yar uwar tata.... Dubanta kurum Gimbiya Zeenat tai kana ta saka Kai Ta shige dan ita bama ta d’auki maganan Raheema da mahimmanci ba, yo har wata tsiyace zatazo ta tsone masu idanu bayan suna d’iyoyin sarki jinin sarauta gaba da baya... Ta tabbata shashanshanci ne kurum irin na Raheema ba wani abu ba.... ** Daga yanda suke zaune su Duka ukun Sun kafeta da idanu Fu’ad yai gyaran murya kad’an kana ya furta “She’s different...! Way too different, bansan a wani sahu zan ajeta ba... But her beautiful eyes sunada matuk’ar gizo ka dubi cikinsu and tell her how exactly you feel about her....!” K’asaitaccen murmushi Yazeed yai yana mai jefa grapes cikin bakinsa kana yace “While you’re here thinking of how to approach her... prince Yazeed already had body contact with her..!” Ya k’arashe yana mai kuma daidaita kishingid’arsa shu’umin murmushin saman fuskarsa, yanayi yana shafar hab’arsa Daga Fu’ad har Jamal dubansa sukai da tsananin mamaki... Jamal yace “Yazeed mai kake nufi... Wai kana nufi har ka mata magana...?” Murmushin bata bar saman fuskarsa ba, idanunsa kan Muhibbah da ko shakka babu a tsarge take a wajen dan tasan ‘ya’yan Sarkin ita suke duba probably ma magananta suke... Yazeed yaci gaba da fad’in “Prince Yazeed never fails...! Kuma babu macen da Ta tab’a rejecting d’insa duk fad’in duniyar nan.... And believe me, she and I have an unfinished business...!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushin nasa.... Girgiza kai Jamal yai kana yace “But you’ve your own wife Yazeed... Kar ka b’ata mata lokaci...” A kaikaice yake dubansa kana yace “Did you hear yourself Jamal... B’ata lokaci fah kace... Ka mance ni namiji ne, I’m entitled to 4 wives Jamal, Shari’a Ta yarje min nayi hud’u kuma idan na zama Sarki dik mace mai kyau dake cikin Masarautar nan Ta zama Kuyangata, sun zama nawa sai abinda naga dama nayi dasu... Kai duk mace mai kyau idan ta shigo Masarautar nan ta zama baiwata dokan da zan zartar kenan....!” Jamal ya murmusa kana yace “Dama k’ara auren kai ka dena b’ata lokacin ‘ya’yan mutane....” Yazeed ya tsaresa da fad’in “Correction! duk su suke kawo kansu babu wacce na tab’a bi....!” D’an girgiza kai Jamal ya kumayi kana yace “But still your Highness ya kamata a duba lamarin....” Fu’ad ya katsesu da fad’in “Leave Muhibbah out of this Prince Yazeed, don’t you dare try that with her...!”Yai maganan yana sakin huci.... Duban da mai kiwon kare keyiwa sabon kuikuyo da kariyarsa Ta haifo masa yai ma Fu’ad kana yace “Looks like those pills you’ve been taken ya maidaka mahaukaci na gaske... And here I thought kafin mu fito wajen nan, I made it clear to you boy, that you should be in your best behavior tonight..!! Don’t tell me kasha kayan haukan kafin ka fito nan...?!” Jamal ne yai saurin katse zancen da fad’in “Wai ina Yaya... He should be here by now...!” Daga Yazeed har Fu’ad babu wanda ya amsashi saima aikama juna muguwar kallo mai had’eda huci da suke faman yi.... Yazeed ya saki cruel smile d’insa kafin ya maida dubansaga Muhibbah wacce itama shi take duba wannan lokacin... Daidai sanda Gimbiya Zeenat da Raheema suka k’araso wajen... Idanunsu k’yam kan Muhibbah Raheema na sanar da ita cewa ta dubi abinda take sanar da ita da kyau.... Su duka biyun duban Muhibbah suke, itama d’in su take duba Kuyangi har kusan guda uku biye dasu.... Suna k’arasowa Rumfar da aka tanadar masu suka k’arasa, kaman yanda yake a al’adarsu ba’a gaishe gaishe har sai Giwa ta iso ta zauna kafin kowa ya mik’e ya kai mata gaisuwarsa saiko sauran jama’a a gaisada juna..... Jim kad’an kuwa mai gayya Ta samu hallara, tawagarta guda biyeda ita, kaga yanda ake karramata ake bata girma abinda tafi k’auna a rayuwarta... Fadawa kuwa sai kod’ata suke suna wasata tamkar wata bakin wuk’a.... Bayan ta zauna a nan mazauninta wanda yake gefen na Gimbiya Zeenat kowa ya soma tasowa yana kawo tasa gaisuwar.... Sukanyi irin wannan royal gathering d’in sau d’aya ko wacce wata, dik juma’a da take zuwa a k’arshen wata hakan sukeyi, so kowa ya saba da had’uwar... Hardai aka soma ciye ciyen abinci Muhibbah Ta kula bataga Zuhra matar Yazeed da yaransa ba, sannan ko k’yallin Yarima Mahmood ma bata gani ba.... Tana tsaka da tinanin taga Giwa tai alamawa Jakadiya... Babu b’ata lokaci Jakadiya ta isa rumfar su Yarima Yazeed tai masa iso da mahaifiyarsa.... Dikda Muhibbah bata iya

Chapter 10 of 65