my brother... Idan ka zab’i yin karatu a nan then fine... Allah Ubangiji ya dafa maka k’anina...!” A tare Mahmood da Fu’ad suka amsa kana Jamal yai masu sallama ya nufi Parlorn Giwa....
Hannun Fu’ad Mahmood ya dafa a hankali kana ya ambato sunansa... Fu’ad ya d’ago yana dubansa.
Mahmood yaci gaba da fad’in “You know you can trust me right..?”
Fu’ad ya jinjina kansa a hankali alamun tabbatarwa kana Mahmood ya d’orada “And you can always count on me...!”
Nan ma jinjina kai Fu’ad yai... Mahmood ya gyara zamansa kad’an kana yace “Idan akwai abindake damunka kar kaji shakkun sanar dani kaji k’anina... Your big brother is here to listen..!” Ya k’arashe yana mai duban Fu’ad d’in cikeda tausayawa...
K’ak’aro murmushi Fu’ad yai kaman zai magana sai kuma ya rungume Mahmood d’in yana fad’in “I’m glad you are here now Yaya... Please don’t leave us kaji.. Kar ka sake komawa Spain ka barmu a nan, ina matuk’ar son kasancewarka a nan...!”
D’an bubbuga bayan Fu’ad yake yana mai furta “Bazan sake tafiya ba Fu’ad, zan zauna tareda ‘yanuwana a nan gaba d’aya kaji koh...!”
Fu’ad ya murmusa cikeda jin dad’i su duka biyun suna duban juna cikeda k’auna...
**
Jamal na ficewa bai zarce ko ina ba sai d’akin Giwa yanda suka k’ume su biyu d’in cikin d’aki..
Zuba masa idanu Giwa tai sanda yaci gaba da fad’in “Your little boy almost screwed up Maami... He almost ratted us out, if only ban isa akan lokaci ba... Nayi imani da Fu’ad ya bud’e bakinsa ya sanar da Yaya Mahmood komai, dik abinda muka aikata ranan hawan k’aramar sallah shekaru gomasha biyar da suka shud’e....!” Ya k’arashe yana sakin huci...
Giwa ta mik’e tana murza hannunta dake rufe cikin safa... “Jamal k’aninku baida hankali da wayo har yanzu, idan Mahmood yasan batun nan bazai tab’a yafe mana ba dikda cewa sabida ku gaba d’aya dukanku hud’u muka aiwatar da wannan abin, da bamu aikata hakan ba ina mai tabbatar maka d’ah na da yanzu an jima da koran mu cikin Masarautar nan, kana tinanin ba dan ina tsaye akan k’afata ba da yanzu ba’a d’aid’aitani a kassarani a Masarautar nan bane yanda akega duka ‘ya’ayan Sarki AbdulJabbar ni ce nan na haifesu gaba d’aya ku duka hud’un... Dik abinda muka aiwatar shekarun baya sabida nasaranku ne... Malami na ya tabbatar min duka ‘ya’yana sai kunyi sarauta tin daga kan Yayanku Mahmood har zuwa kan d’an autanku Fu’ad...”
Jamal ya d’ago yana dubanta cikin wane irin yanayi, lokaci guda ya furta “But Maami Yaya bai aikata laifin ba, shin ya za’ai shi d’in yai sarautar...?!”
Murmushi ta sakar masa tana mai shafa fuskarsa take fad’in “Kud’in kun wadatar ko Yayanku bai aikata ba zai sarauta tinda ku d’in kun aikata....!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta lokaci guda taci gaba da furta “Na sadaukar da abubuwa da dama sabidaku ‘ya’yana ciki harda wani b’angare na jikina...!” Ta k’arashe tana mai duban hannunta guda dake rufe cikin bak’ar safar nan....
Zaunar da ita Jamal yai yana mai furta “Karki damu Maami na fahimceki, babu uwar da bazatai komai dan ceton yaranta da cikar burinsu ba, wanann gidan shine asalinmu kuma shine tushen mu, dik abinda kikai kinyi ne domin amfanin ‘ya’yanki domin Ki rufawa ‘ya’yanki asiri domin Mu dawwama cikin wannan masarauta har k’arshen rayuwarmu kuma ban tab’a dana sanin yin duk wasu abubuwa da kike umartata ba... Ya Mahmood nasan bazai tab’a fahimtar hakan ba, he’d judge you... Shi d’in baisan cewa zama cikin gida na sarauta dole sai kanada shiri ba...!”
Murmushi Giwa ta saki a hankali tana mai duban Jamal, lokaci guda take furta “Kafi kowa fahimtata duk cikin ‘yanuwanka... Shisa nake matuk’ar k’aunarka nake ji dakai Gwarzo na.... Koda wasa kada ka bari Fu’ad ya sanar da Yayanku abinda muka aikatawa yarinyar nan SAUDATU da ahalinta....Munyi hakan ne domin KARE KARAGAR Masarautar nan, da bamu aikata hakan ba da yanzu mun jima da zama tarihi a Masarautar nan....!”
Jamal ya jinjina kai “K’warai kuwa Maami bazan tab’a bari Fu’ad ya sanar da Yaya ba, hasalima lokaci yayi da zamu d’aga Fu’ad daga cikin Masarautar nan, mu turashi makaranta cen wata k’asa mai nisa yanda zai nesa da gida..!” Ya k’arashe yana duban mahaifiyar tasa...
Mik’ewa tsaye tai tana dunk’ule hannunta dake rufe cikin bak’ar safar nan kana Ta shiga girgiza kai tana furta “A’a Jamal, banaso wani daga cikin ‘ya’ya na ya sake nesanta na, Fu’ad har yanzu yaro ne baida hankali k’wayoyin nan sun gama illata masa kwanya, ina tsoron mu turasa wata k’asa yaje ya aiwatar da suicide sanin kanka ne yasha attempting yin hakan a nan gida tin bayan abinda ya faru da wannan yarinya Saudatu da ahalinta...!”
Jamal ya fuzar da fuci a hankali kana yace “K’warai kuwa Maami my brother couldn’t get over it, Fu’ad gawwaki biyu ya tsallake kuma unfortunately Shi ya cakkawa Mutumin takwabi har ya mutu, Saidai baiyi hakan Da nufi ba k’ok’arin kub’utar da mutumin yake daga dakarun da na tura... Maami a wancan lokacin Fu’ad yaro ne d’an shekaru goma sha uku kacal a duniya, it was really a traumatic experience for him... Ban tab’a zaton zai iya rayuwa da Abinda ya rayu ba... Fu’ad ya wahala cikin wannan rayuwar Maami...!”
Jinjina masa kai tai a hankali abubuwan data aikata a Masarautar na kuma zuwa mata daki daki tin daga cin amanan da mijinta yai mata...Ta basa kyautar baiwarta a matsayin tukuici yaci amananta da Baiwar ya ‘yanta Baiwar Sannan ya auri Baiwar a bayan idonta a wani tafiya mai dogon zango da sukai shida Kyakkyawar Kuyanganta data mallaka masa....AbdulJabbar ya tozarta ta ya kuma ci mutuncinta ya wulak’antata sannan Bai cancanci yafiyarta ba even if in his death...!
Gimbiya Turai tafi k’arfin tayi kishi da baiwa, baiwarma ta Masarautar ta...!
Sannan kuma Wai ace Baiwar har ta riga haifawa mijinsu Magaji.... Inaa hakan sam bazai yuwu ba... Bazata tab’a bari jinin bauta ya k’wace mulki daga gareta ba koda kuwa cewa an ‘yanta mahaifiyarsa... Tabon bauta bazai tab’a shafewa a jininsu ba har abada...!! Ta k’arashe tinanin nata tana mai ci gaba da sakin huci...
**
A daren wannan rana Giwa ta ziyarci Tal’udu... Tana zaune kan jan daddumarsu Ta tsafi take ci gaba da fad’in “Idan SAUDATU na raye ya zama dole ka zak’ulota Tal’udu yanda ta shiga ta fita.. Babu kasawa babu fad’i a lamarina, saidai nasara da ci gaba...!” Ta k’arashe tana sakin huci...
Wani irin murmushi mai sauti Tal’udu yai yana mai buga turb’ayan dake gabansa... Wani irin jan k’ura ya tashi ya gauraye wajen gaba d’aya... Saida k’uran ya kwashe mintoci kana ya lafa..
Tal’udu ya dubi Giwa da firgitattun idanunsa “Babu wani haske gameda tak’aimemmen yanda yarinyar take a halin yanzu... Dama tun fari saida na miki kashedi muddin yarinyar nan ta kubce matsala ne Babba zai faru, kikai sake kika bari Ta kufce sannan yaranki suka miki k’arya cewa sun kasheta.... Idan har tana raye hakan nada tabbacin Mahmood zai zamto magajin Mahaifinsa... Sannan hakan zai kuma zamto dalili na rugujewarki..!!”
Gumi ya shiga tsartsafowa Giwa lokaci guda take furta “Yanzu miye abinyi gameda Mahmood..?!”
Murmusawa Tal’udu ya kumayi kana yace “WAMBAI.!!”
Giwa tai saurin d’agowa tana dubansa cikeda firgici...
Tal’udu yaci gaba da fad’in “Mabud’in fursunan sirri na wajen d’anuwan mijinki kuma idan har ya dank’awa Mahmood shikenan bazai tab’a dawowa hannunki ba JAFAR ka iya dawowa...!”
Yanzu kam kan Giwa ne ya soma kwancewa... Tai wuf Ta mik’e tsaye tana fad’in “Bayaga Jafar shin akwai wanda ya isa ya bud’e k’ofar da ni kad’ai Ke iya bud’ewa...?!”
“Kinyi kuskuren aminta da Wambai Turai... Keda Wambai tabbas kunyi tarayya wajen aikata wani laifi saidai kaman yanda na sanar dake zai iya zamewa yaci amanarki.... Kafin yaci amanarki kiyi maza ki aiwatar da wani abu kan Wambai, domin fitilar tsafi ta hasko min cewa akwai cin amana tsakaninku...!”
Huci kurum Giwa Ke sauk’ewa a hankali... Ta yaya Wambai zaici amanarta, ya zama dole ta b’atar dashi kafin a isa wajen... Bayan sun fice daga wajen Tal’udu ta komo d’aki nan ta umarci Jakadiya da tai mata kiran Waziri a waya....
Waziri na d’agawa Giwa ta amshe wayar cikin sauri tana mai sanar dashi cewa yai saurin cimma Wambai kafin Mahmood ya rigasu...
Waziri ya sanar da ita kada ta sami damuwa Mahmood bazai cimma Wambai ba, idanma ya cimmasa saidai ya cimma jana’izarsa....
Giwa ta saki murmushi cikeda jin dad’i Dan tasan Waziri bazai tab’a bata kunya ba har abada...
***
Kaman ko yaushe yauma nad’in buzaye yai ya nufi gidan Baba Wambai... Bak’on Buzu abinda ya sanarda Innani kenan Dan kar ta zargi wani abu... Wannan karon a parlorn Baba Wambai suka keb’e...
Baba Wambai ya tsaresa da idanu kana yace “Ina saurarenka d’ah meke tafe dakai wannan karon...?!”
Mahmood ya d’anyi gyaran murya kad’an yana mai kuma gyara zamansa “Wato Baba abubuwa sun kuma rincab’ewa, dik yanda nake tinanin zasuzo da sauk’i amma abu yaci tura... Baba na rasa yardan mahaifiyata data ‘yanuwana, sun soma saka shakku da kokonto a gamedani...!”
Murmusawa irinta manya Baba Wambai yai kana ya soma fad’i cikin muryarsa da girma ya kama sosai “Sadauki.... Ni na sani za’azo wanann matakin.. Sai ankai yanda kowa zai juya maka baya a cikin Masarautar muddin zaka taho da batu na gaskiya...!”
Mahmood ya fuzar da fuci kad’an kana yace “Amma Baba banaso a sami wani conflict tsakanina da ahalina, banaso mu sami rashin jituwa... Baba ni ne Babba, yanzu da babu mahaifinmu kamata yai ace na had’a kan ahalin ba na wargazawa ba... Sannan mahaifiyarmu...”
Katsesa Baba Wambai yai da fad’in “Mahmood yak’i kake ciki tsundum, yak’i mafi had’ari... Yak’inda baka San yaya kamannin abokin gabanka yake ba balle kai yunk’urin kare kanka idan ya kawo maka sara....!”
Yarima Mahmood yai shiru yana sauraren Baba Wambai... Lokaci guda Baba Wambai ya mik’e yana mai furta “Ina zuwa....”
Jinjina kai kurum Mahmood yai ba tareda ya iya amsawa ba...
Baba Wambai ya shige wata ‘yar d’aki... Jim kad’an ya fito hannunsa rik’eda wata ‘yar k’aramar jaka ta fata mai kaman posa...
Zama yai yana mai mik’awa Mahmood ‘yar jakan “Ungo nan amshi wannan...!”
Mahmood yasa duka hannayensa guda biyu ya amsa a hankali yana mai juya ‘yar jakan....
Muryar Baba Wambai ya sinkayo yana mai furta “Mahmuda, inaji a jikina banida sauran lokaci mai tsawo a wannan rayuwar... Akwai abubuwa da dama da lokaci baida ikon ara mana kansa... Zanso ace ina numfashi a doron k’asa har zuwa wannan lokacin... Saidai bamukeda linzamin rayukanmu a hannayenmu ba...”
Cikin d’an sanyin jiki Mahmood ya katsesa da fad’in “Baba ka daina fad’in haka, tsufa bashine mutuwa ba... Zan iya zamtowa gawan fari na rigaka tafiyaga magaliccinmu wanann duka iko ne na Allah...!”
Baba Wambai yai murmushi irinta manya yana mai jinjina kai “K’warai kuwa Sadauki, maganarka gaskiya ne...Amma tsufa d’aya ne daga cikin alamominta kuma bazan maimaita yawan shekarunda nayi a baya ba sannan ni nasan abinda nake ji Mahmuda D’ah na... Wannan yak’i da keke tunk’ara ina mai rok’on Allah ya dafa maka cikinta... Sannan wannan k’undi dana baka akwai ranan da zaka buk’aci bud’esa... Inaso Kai masa ajiya mai kyau, irin yanda zaka ijiye abu mai matuk’ar mahimmanci a gareka....!”
Mahmood ya jinjina kai a hankali yana mai furta “In sha Allah zan ajiye wannan k’undi da kyau da aminci kaman yanda ka umarta Baba...!”
Baba Wambai ya jinjina kai yana mai sakin murmushi lokaci guda yake kuma sakawa Mahmood Albarka had’ida fatan samun nasara... Bayan sunyi sallama Mahmood ya tafi Baba Wambai ya isa ya d’aga k’asar katifarsa da k’yar ya ciro wani zanen ginin gidan sarauta mai yanayi da zanen dake lank’aye parlorn su Umaima...
K’uri yaima zanen hawaye na gangaro masa... Lokaci guda yake furta “Wannan shine iyaka abinda zan iya yiwa Mahmuda bayan amanan iyayensa dana ci akan dalilin son mulki da son zuciya irin tawa...!”Ya k’ara she yana mai shafa zanen da hannunsa Hawaye naci gaba da gangaro masa...
Yana nan tsaye ya sinkayo muryar Waziri daga waje.... Gabansa ya yanke ya fad’i......
SameenaAleeyou📚
[7/6, 1:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*028*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Daga yanda Wambai ke tsaye yana iya sinkayo muryar maid’akinsa da Waziri suna gaisawa cikeda girmamawa, ya kuma sinkayo muryar Waziri yana tambayarta ko Wambai na Gida dikda cewa safiya ne sosai...
Innani Ta jinjina kai tace “Aikuwa Yana nan yana tareda bak’o....!”
Gaban Waziri ya yanke ya fad’i, lokaci guda yake furta “Bak’o kuma da safen nan...?!”
Innani tace “Eh bak’on Buzu bai jima da shigowa ba, bara na lek’a sai na maka iso...” Ta k’arashe tana nufan sashen parlorn Wambai...
Shidai Waziri sai faman safa da marwa yake a wajen yana sab’a babban riga yana murza hannayensa waje guda.. Waye kuma bak’on Buzu...? Bai ida tinanin ba ya sinkayo muryar Innani cikin wane irin k’aran gaske tana furta ta shiga uku ta lalace, tana kururuwa tana salati tana kiran sunan mijinta....
Babu shiri Waziri ya nufi parlorn da saurin gaske kaman zai kifa da k’asa, hakan ya kuma janyo hankulan sauran mutanen dake gidan ciki harda Juwariyya autar Baba Wambai...
Waziri yai tsaye yana duban ikon Allah, Wambai kwance k’asa tamkar baya numfashi.... Innani sai kuka take tana kuma jijjiga mijinta Juwariyya ma na tayata... Cikin k’ok’arin kwantar da hankali Waziri ke basu baki yana k’ok’arin duba Wambai... Hindu mai aikace aikace na cikin gidan ita ta janye Innani da k’yar tana mai kuma tausanta had’ida bata baki, Waziri ya d’an tattab’a wasu jijiyoyin jikin Wambai lokaci guda ya fuzar da fuci a hankali yana mai sanar dasu su kwantar da hankulansu Wambai na numfashi... Lokaci guda ya umarci Hindu ta kawo masa ruwa ya zubawa Wambai... Innani kaw har lokacin bata daina kururuwa tana salati ba, Juwariyya kuma jin mahaifin nasu bai mutu ba ya sanyata neman layin Yayanta Majidad’i ta sanar dashi halinda ake ciki, ba zallan Majidad’i ba ma harta sauran yayyenta mata dake gidajen aurensu saida ta kirawosu ta sanar dasu, yayyenta maza dake karatu Jami’a saida ta kirawosu suma...
Majidad’i na K’arasowa ya kirawo likita a fujajan, mintoci kad’an likitan ya iso.. Nan ya buk’aci dik su fice a parlorn su barsa ya duba jikin Wambai...
Waziri yai amfani da wannan da wannan daman ya keb’e ya kirawo Giwa ya sanar da ita halinda ake ciki... Yana tsaka da wayar ne ya sinkayo muryar Innani tana tambayar likita maike damun mijinta... Cikin sauri Waziri ya katse kiran yana mai sanar da ita dik halinda ake ciki zai sanar da ita...
Gaba d’aya suka nufo likitan suna sauraren abinda yake fad’i....
“Wato a gaskiya Majidad’i bazan b’oye maku ba, Wambai ya sami bugawan zuciya had’ida shanyewar b’arin jiki lokaci guda, wanda hakan yasa zaiyi matuk’ar wahala ya sake yin magana saiko wani ikon Allah duba da yanayi na tsufa da yake ciki..Paralyze d’in ya shafi idanunsa guda da kuma kunnensa guda had’ida b’angaren harshensa wanda hakan yasa a halin yanzu baiji da kunne d’aya sannan bazai iya magana ba sabida b’angaren harshensa da ya shanye sannan idanunsa guda bazai sake gani dashi ba....!”
Ai likitan bai ida rufe baki ba Innani ta dafe k’irji tana kuka take fad’in “Lafiya lou fah na barsa da bak’onsa... Toh mai bak’on Buzu ya sanar dashi ni...?!”
Gaba d’aya suka dubi juna “Bak’on Buzu...?!” Majidad’i ya nanata...
Innani ta jinjina kai “K’warai kuwa bak’on Buzu, ai ya kwana biyu yana ziyartan mahaifinku...”
Waziri ya cab’i zancen da fad’in “Shin waye bak’on Buzun kuma a ina yake kuma daga ina yake...?!”
Innani tai jigum tamkar mai tinani kana tace “Wambai ne kawai zai iya baku wannan amsa don ni kaina ban tab’a ganin Fuskar bak’on Buzu ba kuma ban san daga wace duniya yake zuwa ba...!?”
Gaban Waziri ya kuma yankewa ya fad’i sanda Majidad’i Ke fad’in “Ta yaya Baba zai iya amsa mana bayan ya zamto bebe kuma makaho... Innani ina san sanin wanene bak’on Buzu don jikina na bani yanada nasaba da ciwon mahaifina....!”
Waziri yai saurin jinjina kai yana mai furta “K’warai kuwa Majidad’i kayi gaskiya, dik yanda bak’on Buzu ya shiga ya fita ya zama dole ka zak’ulosa ya amsa hukuncinsa...Bazanso ganin Yayan aminina Sarki mai rasuwa kwance haka ba..!”
Majidad’i na sakin huci yake fad’in “I’ll make it my mission to catch whoever is responsible for my father’s illness and make him pay...! Bak’on Buzu...!! Ka shirya domin sai na zak’uloka ko a ina kake..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin fuci...
Ya dubi Likita yace “Yaushe za’a tafi dashi asibiti....?!”
Likita yace “Ko yanzu ma dan zamansa a gida komai ka iya faruwa...!” Babu b’ata lokaci suka d’unguma suka tafi asibiti...
Tareda Waziri akai komai domin ko giftawa baiba... Babban tashin hankalinsa shine da akace Wambai bazai sake magana ba, shin ya za’ai yasan cewa ya bud’e sirrinsuwa Mahmood ko bai bud’e ba... Shin ya basa k’undi ko bai basa ba.... Ya zama dole ya bincika gidan Wambai ya samo wannan k’undin tin abubuwa basu ida rincab’e masu ba....
**
Giwa ta kuma fuzar da fuci tana duban Waziri lokaci guda ta marairaice fuska tana fad’in “Waziri dole kayi ko menene ganin cewa k’undin nan ya dawo hannunmu... Bazamu bari Wambai ya dank’awa Mahmood ba...!!”
Matsowa Waziri yai cikeda tausayinta, ji yake tamkar ya rungumeta ya lallasheta Ta daina kukan nan... Lokaci guda yake furta “Karki damu Gimbiya, alk’awari nai miki muddin Waziri na numfashi bazakiyi kuka ba, sai yanda k’arfina ya k’are wajen ganin Duka burikanki sun cika... Wannan k’undi nayi maki alk’awari har abada bazai isaga Mahmood ba....!!”
Ta saki murmushi a hankali tana mai kuma duban Waziri wanda shid’in ma ita yake duba yana sakin murmushi...
Giwa ta nusa tace “Toh shi wannan bak’on Buzun fah, mai kake tinani gamedashi... Anya babu wani rufeffen al’amari gameda Shi,... Kasan fah gidan nan kowa ba abin yarda bane... Anya wani bai rigamu isaga Wambai ba koda ba Mahmood bane...?!”
Murmusawa Waziri ya kumayi kana yace “Bakida damuwa da wannan, na riga na ziga Majidad’i cewa dik yanda Bak’on Buzun nan yake ya zak’ulosa domin kuwa shikeda alhakin ciwon mahaifinsa... Kinsan halin yaron da kafiyan bala’i na tabbata sai ya nemo koma wanene wannan bak’on Buzun... Muna nan dake zakiga yanda za’a zak’ulo Bak’on Buzu a yanke masa hukunci mafi tsauri... Yanzu abinda Ke gabanmu shine binciko wannan k’undi dake cikin gidan Wambai, zan tura yarana cikin dare suje su bincika gidan tinda yanzu hankulan mutanen gidan gaba d’aya ya karkarta zuwa asibiti... Zasu bincika gidan sannan su kawo min wannan k’undi... Babu wanda zai fahimci cewa mai akai saidai suyi tinanin cewa b’arayi ne suka shiga gidan cikin dare...!”
Giwa ta girgiza kai kad’an kana tace “Waziri zama bai ganmu ba, ai bazamu bari Majidad’i ya rigamu capko Bak’on Buzu ba, ya kamata kafin Majidad’i ya gane ko wanene bak’on Buzu mu ya kamata mu soma cimmasa koma shid’in wanene Dan idan ya rigamu ko shakka babu bana haufin hakan ka iya tona asirinmu...!”
Waziri ya jinjina kai yace “K’warai kinyi gaskiya amma bakida damuwa Ki barmin wannan zan kamo Bak’on Buzu yanda ya shiga ya fita.....!”
Ubandoma dake lab’e jikin k’ofa ya gama jin komai, a hankali yasa kai ya fice yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa ya zama dole ya samo wannan k’undin kafin ya isa hannun Waziri, Dan idan ya samo k’undin nan zai sami Abinda ya jima yana buri Wato ‘Yanci... Yana matuk’ar san ya tashi daga bauta ya koma ‘yantacce, wannan itace kad’ai Damarsa don ya tabbata idan ya samo wannan k’undin dik abinda yace Giwa tai masa in exchange zatai masa domin ta mallaki wannan k’undi koda kuwa menene...!Ya kuma sakin murmushi a hankali kana yasa kai ya fice cikin sauri.....
***
Koda labarin ciwon Wambai ya isa Fada sosai hankalin Yarima Mahmood ya tashi musamman da yaji irin abinda ya sami Wambai wanda idan ya had’uda tsufa da k’yar ake tashi saiko wani ikon Allah... Haka yaita tuna tattaunawarsu Ta k’arshe wanda tamkar bankwana Wambai d’in ke masa... Yana matuk’ar k’aunar Wambai baya k’aunar abinda zai cutarda Wambai... Tamkar mahaifi haka ya d’auki Baba Wambai dikda cewa shid’in d’anuwan mahaifinsa ne dama....
Shida Fu’ad suka garzayo zuwa asibitin babu b’ata lokaci Ubandoma na biye bayansu.... Suna doso kai d’akinda aka kwantar da Wambai Mahmood ya sinkayo muryar Majidad’i na fad’in ko Wanene bak’on Buzu sai ya zak’ulosa don shikeda alhakin ciwon mahaifinsa... Yasan shid’in ne shine bak’on Buzu amma baisan ya akai ciwon Wambai Keda alak’a da bak’on Buzu ba tinda yasan lafiya lou sukai sallama... Tabbas bazai bada wani clue ma Majidad’i da har zai fahamci cewa shine bak’on Buzu... On the other hand shima yanaso yasan komai in details, yanda akai bak’on Buzu Keda alhakin ciwon Wambai... Toh ko hakan nada alak’a da wannan k’undin da ya dank’a masa ne..?? Tabbas ya kamata Shima ya bincika don ko babu komai Baba Wambai ya masa abinda babu wanda ya masa shi tin dawowarsa cikin Masarautar...
Da sallama suka shigo cikin d’akin... Majidad’i da Innani suna ganinsu suka had’e FUSKA gaba d’aya tamkar sunga ajalinsu... Mahmood bai k’asa a gwiwa ba ya soma gaida Innani dake faman cika, Ta amsa da k’yar kana Fu’ad ma ya gaidata sukai mata yaya mai jiki... Nan ma da k’yar ta amsa...
K’warjinin Mahmood ya cika wajen gaba d’aya wanda hakan ya hana Majidad’i da mahaifiyarsa wulak’anta su Mahmood.... Amma kam tabbas Majidad’i ji yake tamkar ya fitarda Mahmood daga cikin d’akin, da ace yanada ikon yin hakan da yayi....
Bayan sun ida gaisawa ne Mahmood ke tambayarsu yanda al’amarin ya kasance....Innani ta karanto masa komai yayinda Majidad’i ya k’arada “Bak’on Buzu baici banza ba Innani wllhi sai na zak’ulosa na d’auki fansar mahaifina akansa...!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci lokaci guda ya janye jiki ya fice daga d’akin gaba d’aya....
Mahmood yaima Wambai dake kwance saman gadon marassa lafiya K’uri tausayinsa na d’awainiya dashi.... A hankali ya isa jikin gadon ya dafa hannun Baba Wambai maras cannula... Lokaci guda yake karanto masa addu’o’in samun lafiya, cikin zuciyarsa na ayyanawa cewa in sha Allahu sai yanda k’arfinsa ya k’are wajen ganin Baba Wambai ya sami lafiya.. Akwai abubuwa da dama da yake neman amsoshinsu daga wajen Baba Wambai bayan dank’a masa wannan k’undi da yayi... A hankali ya furta “Allah ya baka lafiya Baba ya tashi kafad’unka....!”
Gaba d’aya mutanen dake cikin d’akin suka amsada Ameen...
***
Fitowarsu daga cikin asibitin Mahmood yaga kiran Turaki na shigo masa, excusing kansa yai ya nufi ‘yar wata hanya nan cikin asibitin domin amsa kiran Turaki yayinda Fu’ad da Ubandoma suka nufi mota....
Yana tafe yana k’ok’arin amsa kiran ya hango Juwariyya d’iyar Baba Wambai... Tabbas tsaf ya ganeta don ga kamanninsu nan tanadashi dikda cewa rabon da yaga yarinyar zai iya cewa tun wani zuwansa Nigeria lokacin yana Spain... Abinda ya tafida hankalinsa ya mantar dashi wayar da zai amsa shine sinkayo muryar Juwariyya da yai cikin waya tana fad’in “Ni fah Raheema babu wani binciken k’wak’waf da zan maki gameda Muhibbah sabida ni yanzu abindake gabana yafi k’arfina... Ni dama ba ‘yar bincike bace kawai dai Ina baku information ne gameda Yaya na Dan nima banaso yai sarauta sabida na tsani matarsa nafi so Ya Mahmood yai shisa nake baku duk wani information akan abindake faruwa cikin gidanmu... Amma ni harga Allah ba ‘yar bincike bace bazan iya wani bincike kan wata Muhibbah ba... Naji da jinyar mahaifina ne ko naji da wani bincike...Mtsww..!” Taja dogon tsaki tana mai katse kiran take ci gaba da fad’in “Ko sun zata sabida abin duniya nake masu aiki oho... Allah ya sawak’e su sakani wani aikin da banyi niyya ba ina a matsayin jinjin sarauta... Yanda suke jin kansu d’oyiyin Sarki nima jikar Sarki ce nafi k’arfin......!” Burki taiwa kalamanta sakamakon hango Yarima Mahmood da tai fuskar nan nasa tamau ya tsareta da idanunsa masu firgita dik wani mai laifi....
Jikin Juwariyya ya d’auki rawa, tasan Yarima Mahmood ya gama sauraren wayarta yaji komai, ai ko irin duban da yake mata tasan ya riga da yaji wayar da take da Raheema... Juwariyya ta had’iyi miyau da k’yar tana murza wayar salulanta da duka hannayenta biyu... Lokaci guda kuka Ke k’ok’arin zuwa mata, tuni ta soma kuka tana k’ok’arin duk’awa gaban Mahmood dake tsaye hannayensa hard’e Ta baya tana fad’in “Yaya Dan Allah kayi hak’uri... Wllhi Anty Raheema so take kawai Kai sarauta shisa Ta sakani nake kawo mata rahoton dik abinda ke faruwa cikin gidanmu gameda neman mulkin da Ya Majidad’i yake... Yaya wllhi mu kai muke so kai sarauta shisa.. Amma babu wani abu mai muni da mukai sai yanzu da Anty Raheema Ke cewa nai mata bincike kan Muhibbah Wai Dan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 65