bakin gado abubuwan na kuma zuwa masa... Wannan wane irin mafarki ne mai cikeda rud’ani da kuma tashin hankali.... Mai wannan mafarki yake nufi...? Take yaji wani b’angare na zuciyarsa na raya masa _Akasarin munanan mafarkai Daga shed’an ne ka nemi tsari da kariya daga shedan.._ Ya sauk’e nannauyan ajiyan zuciya yana mai kuma shafe fuskarsa, tabbas ‘yan uwansa bazasu iya kashe ran wani ba koda bawa ne balle nashi.... Ya fuzar da fuci a hankali yana neman tsari daga shaid’an da kuma munanan abubuwan da ya gani a cikin baccinsa... Ya jima zaune wajen har saida ya soma jiyo kiran sallar asubahi... Ya mik’e ya d’auki cazbaha da k’aramar littafin azkar d’insa na hisnul Muslim kana kana ya nufi masallacinsu dake nan cikin Masarautar....
Nan cikin masallacin ya tadda Jamal zaune yana wurdi da alama sallar nafila ya ida yana jiran k’arsowar imam a tada sallar asuba... Yarima Mahmood ya saki murmushi a hankali natsuwa na sauk’o masa, tabbas wannan mafarki nashi daga shed’an ne... Of all people bazai yuwu ma ace Jamal ne zai caka masa wuk’a ba... Nan ya k’arasa had’ida zama gefen Jamal d’in... Suka sakar ma juna murmushi kana Jamal ya mik’a masa hannu alamun masabaha... Zamansa da kad’an kaw Imaam ya shigo suka tada sallah....
Bayan an ida sallah ne suka jera suna fitowa a tare suka nufi b’angaren mahaifiyarsu... Suna tafe Yarima Mahmood ya d’anyi gyaran murya kad’an kana ya dubi Jamal yace “Nikam har yanzu Yazeed na nan da halinsa na k’in zuwa sallah...? Naga tinda na dawo bana ganinsa a jam’i and Fu’ad ya akai yau bai fito sallah ba...?”
Murmusawa kad’an Jamal yai wanda murmushin d’abi’arsa ce kana yace “Babu abinda ya canza da Yazeed Yaya... Fu’ad kuma baijin dad’i ne shisa baka gansa ba...”
Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali suna tafe cikin kamfacecen masarautar nasu da duk yanda suka gifta sai bayi sun risina Sun gaidasu.... A haka suka iso sashen mahaifiyar tasu...
Jakadiya ce Tai masu iso kana suka shiga suka taddata zaune saman abin sallarta da alama itama sallar Ta ida tana gabatar da wurdi...
A jere sukai zama irinta rak’umi saman Darduma dake a saitin mahaifiyar tasu wanda dama dominsu darduman yake aje wajen, dik sanda suka shigo gaisheta a nan suke zama...
Ta ida addu’o’inta suka shafa a tareda yaran nata, murmushi fal fuskarta take dubansu....Tsananin k’aunarsu na ratsa dik wani kafa na jikinta, Mahmood ne ya soma gaidata sannan Jamal... Ta amsa masu cikeda so da k’auna had’ida shi masu albarka... Daga nan ne take sanar dasu jiya Galadima ya sanar da ita cewa Yau d’in da yammaci zasuyi zama kan maganar wanda zai gaji mahaifinsu Sarki AbdulJabbar mai rasuwa...
Sosai suka natsu suna sauraren Mahaifiyar tasu sanda taci gaba da fad’in “Sadauki..!”
Yarima Mahmood ya d’ago yana dubanta, Giwa taci gaba da fad’in “Na riga na zab’eke matsayin wanda ni nakeso ya gaji mahaifinku, toh amma Galadima ya tabbatar min cewa cikin masu neman sarautar nan harda Majidad’i d’an d’an uwan mahaifinku Wambai da kuma biyu daga cikin yaran Marigayi Talba mai rasuwa, sannan da shi kanshi Chiroman gari yana neman Karagar Masarautar garin nan... Dan haka ni a nawa b’angaren na tsaida kai, kuma na tabbata king makers bazasu bani kunya ba, domin kaw daga Galadima har Waziri a b’angaren mu suke, kuma sunyi Na’am cikin masu neman sarautar Masarautar nan babu wanda ya dace ya maye gurbin mahaifinku sai kai Sadauki....” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta, yayinda Jamal yaci gaba da jinjina kai yana furta “Tabbas Maami, Yaya shi kad’ai ya dace ya gaji Abbah... Cikin duka wad’anda kika lissafo, sannan dama ance kyaun d’a ya gaji mahaifinsa... Kuma idan har sarauta ya fice daga gidan nan haka munaji muna gani za’a sallamemu mu bar Fada mu koma cen wani k’auye a nad’amu hakiman k’awye... Yaya you’re the rightful heir to the throne... Kai ka cancanta ka d’ale wannan karaga...!” Ya k’arashe yana duban d’an uwan nasa kyakkyawan murmushi saman fuskarsa....
K’uri Mahmood yai masu yana dubansu kana ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali yana mai shafe fsuksrsa da tafukan hannunsa, ta yaya zai sanar dasu ba abinda ya dawo dashi Masarautar nan ba kenan.. Ta yaya zai sanar dasu ba neman mulki bane gabansa, ta yaya zai sanar dasu abinda ya dawo dashi yasha bambam da abinda suke tinanin shi ya dawo dashi.... Muryar Giwa ya sinkayo tana ci gaba da fad’in “Kai nake sauraro d’ah na nasan bazaka bani kunya ba...!”
K’ak’aro gajeren murmushi yai irinta masu mulki kana ya soma fad’in “Allah shi taimaki Giwar Sarki AbdulJabbar, Allah shi taimaki Mai babban d’aki... Allah shi taimaki Gimbiya Turai d’iyaga Sarki Jamaludden na k’asar Benin, La princesa de benin (the Princess of Benin), La reina de jos (the Queen of Jos)... Mi hermosa madre (Kyakkyawan mahaifiyata) Allah yaja zamaninki...!!”
Tinda ya soma mata kirari take dubansa da murmushi saman fuskarta, hannu tasa ta shafi fuskarsa kad’an k’walla tab idanunta... Tana matuk’ar k’aunar Mahmood, akwai wani abinda ya banbanta dashi cikin ‘yan uwansa...
Yarima Mahmood ya d’an kamo hannunta ya sumbata su duka biyu d’in suna sakarwa juna murmushi kana ya soma fad’in “Maami, bawai na banbanta da ra’ayinki bane... Bawai bana son amsar tayinki bane... Ke duk kin wuce haka a wajena... Umarni kawai zaki bani nabi.... But Maami, sarauta ba layina bane... Almost 14 years bana Masarautar nan saidai nazo lokaci zuwa lokaci, da yawan wasu abubuwan ban saba dasu ba, ban San ya ake gudanar dasu ba... Maami idan nace zan amshi sarautar Masarautar nan hakan na nufin tamkar sabon karatu zan fara, dole na koyi abubuwa da dama.... Inaga zaifi kyau Idan aka nad’a wanda yafini cancanta da dacewa da rik’on Masarautar...”
Cikin saurin Yarima Jamal Ke girgiza kai yana fad’in “No, no Yaya... Babu wanda ya dace ya kuma cancanta face kai, Yaya kana so mun fice daga Masarautar nan ne cikin k’ask’anci da tozarci...? Yaya kana sona fidda matan mahaifinmu a d’akunansu akaisu wani k’auye ne..? Yaya so kake mu fice daga cikin gidan da aka haifemu aka renemu cikinsa...? Yaya so kake mu bar asalinmu da abinda muka gada... Nasan duk bazaka so abubuwanda lissafo su faru ba....!” Ya k’arashe cikeda kulawa...
Giwa kam k’uri taiwa Mahmuda tana kallon sarautar Allah...
Yarima Mahmood ya kamo hannayen Yarima Jamal su duka biyu d’in suna duban juna sanda Mahmood Ke fad’in “Dik ba wannan nake nufi ba Jamal, kuma bana fatan d’aya daga cikin abubuwanda ka lissafo su faru, sannan Allah ya albarkaci mahaifinmu da yara maza d’ai d’ai d’ai har guda hud’u and we are all entitled to the throne.... Ga Yazeed gaka nan, even Fu’ad zai iya zama sarki ba wani abu bane.. Ba lallai sai Babba ba k’aramin cikinmu ka iya zama kan Karagar mulkin nan hardai yanada damar data mallaka masa hakan... So Maami why not a tsaida d’aya daga cikin ‘yan uwana....” Wata kakkausar murya ce da ko shakka babu sun San mai ita ta katsesu da fad’in “Babu wanda ya isa, babu mahaluk’in da ya isa ya fitar da mulkin Masarautar nan daga hannun ahalinmu... Babu wanda ya isa ya fitar dani daga gidan mahaifina, Mu kad’ai ne jinin sarauta, mu kad’aine muka gaji sarautar... And yes Yaya, you’re absolutely right... Naji dad’i daka d’auki shawarina... For the first time we’re on the same page, kai kanka ka amince babu wanda ya cancanta ya zama sarki face ni Yazeed..!!!D’add’aya yake maganar yana takowa cikin katafaren d’akin hannayensa guda biyu hard’e ta baya, cikin taku mai cikeda k’asaita yake tafiyar nasa tamkar wani Amale... saida ya iso dadai tsakiyar d’akin kana ya karkato yana fuskantar Mahmood, lokaci guda yake furta “And now that we are on the same page, inaso ka jaddadawa wad’annan masu sarautun Gargajiyan kar wani daga cikinsu yayi gigin shiga gonata, ina rantsuwa da mahallicina idan d’ayansu yayi kuskuren jayayya dani da sarauta ta, ba rawaninsa kawai da muk’aminsa zai rasa ba, zai iya rasa abinda yafi wad’ann mahimmanci a wajensa... Ina nufin zai iya rasa ransa..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci...
Girgiza kai kad’an Mahmood yai kana yace “And kana tunanin kaine wanda ya dace da kujerar..?”
Saida ya kuma takowa kad’an murmushin bai bar saman fuskarsa ba kana yace “I’m far better than right... I am perfect... Yeah Perfect..!” Ya k’arashe cikeda pride
K’uri Mahmood yai masa yana dubansa , lokaci guda ya mik’e tsaye suna fuskantar juna shida Yazeed, idanu cikin idanu suke duban juna kana Mahmood ya soma fad’i cikin dakewar murya “Wanda duk yace shine toh ba shi bane, sannan ba’a shugaba mai zafin zuciya wanda baida jarumtar kwantar da zuciyarsa idan rai ya b’aci, ba’a shugaba maras d’a’a da ganin girman na gaba, ba’a shugaba maras tsaida dokokin Ubangijinsa... Shi shugaba ya kamata ya kasance mai taushin zuciya sannan Jarumi, taushin zuciya domin ya tausasawa al’ummansa yaji k’ansu sannan ya kwantata adalci a tsakaninsu, Jarumi domin ya zamto sulke wajen kare al’ummansa da tsaresu daga abokan gaba... Mai bin dokokin Ubangijinsa domin ya zamto abin koyi ga Al’ummarsa... Mai girmama na gaba domin wad’anda suke k’asa dashi su girmama shi.... Ta yaya nake tunanin zaka iya zamtowa shugaba bayan baka aikata d’aya daga cikin abinda na lissafo... Nayi kuskure da nai zaton zaka iya maye gurbin mahaifinmu.... Yanzu na tabbata baka cancanta ba Yarima Yazeed....!!” Ya k’arashe yana mai kuma matso da fuskarsa dab na Yazeed cikin muryarsa mai cikeda amo....
Shu’umin murmushin ne nasa saman fuskarsa, lokaci guda ya lank’wasa Kai kad’an yana mai k’arewa Mahmood d’in kallo kana yace “Toh waye ya cancanta..? Kai...?!” Yai murmushi mai sauti irinta masu mulki kana yaci ya a da fad’in “Idan duk kanada qualities d’in daka k’irgosu abu guda d’aya tak da ka aikata ya rushesu... Yarima Mahmood... Mak’aryaci yafi dacewa da shugabanci irinta siyasa amma ba shugabanci irinta Babban Gida ba..!!!”
Cikin zafin nama Mahmood dake tsananin huci yake furta “Don’t Yazeed... Don’t you dare cross the line...!!!”
Yazeed da ko a jikinsa Murmusawa ya kumayi kana yace “Oh really now... Your Royal highness..! Baka so a fad’i naka aibun, bayan Kai ka iya fad’in na wasu cikeda k’warin gwiwa... Ai ba’a sarki matsoraci mai tsoron Ta kife... K’aryar Jarumta kake...Yarima Mahmood..!!!”
“Yazeeeedddd!!!!” Ya daka masa uban tsawa had’ida d’aga hannunsa da niya watsa masa mari... Saidai tuni Jamal ya shige tsakaninsu yana tausan Mahmood “Yaya please don’t... Kar ka mareshi... Kayi hak’uri dan Allah....Allah ya huci zuciyarka..!”
Idanuwansa da suka kad’a sukai jazir yake duban Yazeed dasu, abinda da wanda bai iya b’acin rai ba sai abin ya zama abin ban tsoro... Kana iya hango yanda k’irjin Mahmood Ke hawa yana sauk’a alamun tsananin bugun zuciya da b’acin rai....
Lokaci guda yake nuna Yazeed da d’an yatsa kana yaci gaba da fad’in “I’ll warn you for the last time Yazeed.... Do...not..try..me!!! Do..not..cross..the line..!!!” Daga haka sa kai yai ya fice cikin sassarfa da tsananin b’acin rai...
Yazeed ya rakasa da muguwar kallo kana ya kuma sakin shu’umin murmushinsa, gyara zaman rigarsa yai had’ida kuma hard’e hannayensa ta baya d’abi’ar masu mulki, ya maido da dubansanga mahaifiyarsu data cika tai fam, ta tsaresa da idanu cikin tsananin b’acin rai....
Dukda ya hango tsananin b’acin rai a idon mahaifiyarsu hakan bai hanasa sakin murmushi da gefen bakinsa ba, kana ya isa kusan k’afafunta ya zauna yana mai gaidata, ya k’arashe yana fad’in “A saka min albarka Maami na...!”
Daga Giwa da Yazeed ya d’auko hannunta guda ya d’aura saman kansa alamun saka albarka har Jamal dake tsaye tamkar statue kallon mamaki suke bin Yazeed dashi... Shifa ko a jikinsa da alama, baima san yayi laifi ba... Yazeed bazai tab’a canzawa ba, Ta zaci aure zai canza Yazeed gashi yayi yara har biyu amma halinsa na nan babu abinda ya ragu saima wandake k’aruwa... Har kullum addu’an shiriya takewa Yazeed amma kaman dad’a tab’arb’arewa yake... Tana ji ya gama fad’in iyaka abinda zai fad’i tamkar wani mai bata sak’o kana ya mik’e yai ficewarsa cikeda k’asaita wanda Ke matuk’ar masa kyau...
Jamal ya bisa da kallo har ya b’acewa ganinsa kana ya maidoda dubansaga mahaifiyarsu da ko shakka babu k’walla yake hangowa cikin idanunta, dukda k’ok’arin dannesu da takeyi, shid’in yafi kowa sanin mahaifiyarsu yasani idan abu na matuk’ar damunta... Bai wata wata ba ya isa yanda magungunata Ke aje ya d’auko da kansa yana b’alla mata dan bazai iya jiran wata kuyanga tazo bata magani ba... Sai faman sannu yake mata yana tausanta... Jinjina masa kai kurum take abubuwa da dama k’unshe cikin zuciyarta... Idanma aka ce an bar karagan mulkin nan tsakanin yaranta kad’ai tasan wani yak’i ne mai zaman kansa... Sai yanzu maganan Tal’udu ke kuma dawo mata da yace yaga k’ura mai duhuwan gaske da dandatson mayak’a... Amma koda za’a tashi wannan masarauta bazata tab’a bari dai sarautar ya kufce masu ba... “Wambai” sunan da zuciyarta ta ambata...
Take ta sanar da Jakadiya Tai mata kiran Ubandoma...
***
Tsaf ta shirya cikin jan leshi d’inkin doguwar riga da yai matuk’ar amsarta, ta d’aura alkyabba fara k’al wanda Umaima ta Aiko mata da safen nan... Tsaye tai gaban full length mirror tana duban Wai ita SAUDATU ke sanye da kaya ta mulki da sarauta yau d’in... Ta tina sanda ta fice daga Masarautar cikin k’ask’anci da tozarci yau sai gashi ta dawo cikin karamci da girmamawa... Tabbas Saudatu ta mutu Muhibbah ce a raye yanzu...Ta saki murmushi mai ciwo a hankali kumatunta suka lotsa... A fili take furta “You better be ready, cos my revenge is action...!!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji tana mai duban fuskarta cikin madubi.....
(Anya bakiyi kuskure ba Muhibbah...? Muje zuwa..)
SameenaAleeyou📚
[5/29, 9:41 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑*
*009*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Zama yai gefen bedside yana jiran fitowarta dan yaji alamunta a closet, ya sani bazai wuce shirin school take ba...
Idanunsa suka sauk’a kan picture dake aje gefen bedside d’inta, ya jima yana duban picture d’in... Lokaci guda ya saki murmushi a hankali dan bazai tab’a mance ranan da sukai hoton ba a cen k’asar Spain, lokacin family d’insa na cikeda Farin ciki, inama abubuwa zaku koma kaman yanda suke before.... Yasa hannu ya d’auki hoton yana shafawa a hankali... Zahra da fitowarta kenan daga closet sanye cikin shiga irinta ‘yanmakaranta tsaye tayi tana duban mahaifin nata yanda yai k’urima picture d’insu, lokaci guda tausayinsu gaba d’aya na kuma kamata.... Ta d’an tako kad’an kana ta zauna gefensa...
“Good morning Paa...” Ta fad’i sanda take zama...
Gyara zamansa ya d’anyi yana mai aje picture d’in kana yace “Good morning my love... Da fatan kin tashi lafia..?”
Jinjina masa kai tai kana tace “Lafia Paa... How about you Paa..? You seemed worried... Is something bordering you..?”
K’ak’aro murmushi yai had’ida shafa kanta kad’an “Babu komai Princess, do you want me to take you to school by myself...?”
D’an dubansa tai da mamaki kana ta murmusa “C’mon Paa, kai da kanka kake ce min nan ba Spain bane, things are different here...Well, I’m starting to get used to it... Nasan bazamu tab’a komawa kaman yanda muke a baya ba... It hurts tho..!” Ta k’arashe tana mai zura safar k’afanta....
Dubanta yake da wasu irin idanu, shi kad’ai yasan mai yakeji cikin zuciyarsa, yanada good relationship da d’iyarsa, bazaiso wani ko wani abu ya b’ata wannan alak’a mai kyau da yakedashi shida d’iyarsa ba, Amsar socks d’in da take k’ok’arin sakawa yai lokaci guda ya sauk’o daga saman gado yana zira mata safar a k’afarta... Zahra tai masa K’uri tana dubansa had’ida tunanin anya ba wani abin Ke damun Paa d’inta ba... K’ok’arin amsar safan take tana furta “Paa you don’t need to do this... Zan iya sakawa da kaina, I’m not a little girl anymore Paa...” Tana maganan murmushi kwance saman fuskarta... Bai saurareta ba har saida ya ida saka mata, kana ya d’ago yana dubanta shima murmushin ne saman fuskarsa, lokaci guda yake furta “Well, to me you’d always be the same that little baby I used to carry on my arms... Bazaki tab’a girma a idanuna ba.. And you know why is that my Princess..?”
Ta girgiza kai tana mai dubansa itama murmushin ne saman fuskarta, lokaci guda yaci gaba da furta “It’s because you’re my daughter, my little baby...And I love you, so much..!” Ya k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarsa...
K’arasowa tai ta rungumesa tana k’ok’arin maida k’wallan da suka ciko idanunta.... Lokaci guda Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Never doubt that my Princess...!”
A hankali itama take furta “I love you too Paa...So much...!”
Suka kuma duban juna su duka biyu kana Yarima Mahmood yace “Zahra, I want you to know that whatever happens, I mean ko menene always remember that your Paa loves you... Never doubt that kinji koh...!”
Ta jinjina masa kai a hankali tana duban yanayinsa, dikda da yarinta a tattareda ita zata iya karanto damuwa cikin idanunsa, koda shike tin bayan rasuwar mahaifiyarta haka nan yake wasu lokutan....
“Do you want us to have breakfast together by the pool side..?” Yai maganar yana rik’eda hannayenta..
Jinjina masa kai tai kana tace “Sure Paa..” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye had’ida zura k’aramar hijab d’inta na makaranta...
Hannunta ya kamo suka fito tare...
Kallo d’aya zakaiwa yarinyar ka fahimci tana cikin Farin ciki...
Take ya sanar da Ubandoma ya fad’awa Jakadiya a shirya masu karin kumallo a gefen swimming pool shida d’iyarsa a nan cikin b’angaren mahaifiyar tasa....
Fu’ad da fitowarsa kenan bayan ya gaida Giwa ya hangi Zahra da YarimaMahmood suna cin abinci cikeda Farin ciki, hasken ranan hantsi ya haske fuskokinsu... Murmushi ya saki a hankali kana ya nufo yanda suke....
Kuyangin dake tsartsaye gefe suka rusuna suna gaidashi... Fu’ad ya k’araso k’asaitaccen murmushi saman fuskarsa, Zahra ce ta soma hangosa ta fad’ad’a murmushinta tana fad’in “ Buenos dias Uncle Best, join us for breakfast...”
Dafa kanta Fu’ad yai yana mai furta “Princesa de la mañana..” (Morning Princess) Yai maganan murmushi saman fuskarsa..
Daga ita har Mahmood murmushi sukai Mahmood na furta “Da alama k’aramin k’anina ya kusa komawa spain....”
Suka kuma murmusawa gaba d’ayansu kana Fu’ad ya zauna saman kujera guda yana mai gaida Yayansa Mahmood... Nan da nan d’aya daga cikin Kuyangin dake tsaye gefe guda ta k’araso tana serving Fu’ad....
***
Jerawa sukai itada Umaima suna tafe Umaima na bata gajerun tarihin cikin Masarautar, Muhibbah kaw sai kuma tambayarta take dik yanda suka shige, sosai ta ware idanu tana k’arewa Masarautar kallo tamkar bata tab’a kasancewa cikinta ba... Sashen Gimbiya Zeenat sukazo wucewa Umaima tace “Wannan shine sashen Gimbiya Zeenat amaryar Marigayi Maimartaba, bata jimada shigowa gidan nan ba Allah yaiwa Maimartaba rasuwa, da fari akasarin jama’an dake gidan sun zargeta da alhakin mutuwar Maimartaba tinda zuwanta bada jimawa ba ya rasu, toh amma dashike Giwa mutuniyar arziki ce itace tayi tsayin daka wajen ganin an daina jifan Gimbiya Zeenat da alhakin mutuwar Maimartaba, Giwa ita ta wanke Gimbiya Zeenat daga dik wani zargin da ake mata....Giwa wata irin mace ce mai son mulki lokaci guda kuma mai tsananin sauk’in kai ga Al’umman ta wannan yasa ta saye zukatan d’inbin jama’a dake Masarautar nan, ta d’auki Gimbiya Zeenat tamkar k’aramar k’anwa, bazaki tab’a cewa su d’in kishiyoyi bane, yanzu haka maganar da nake miki ana shirin had’a auren k’anwarta Rahima tareda Ya Mahmood, yanda zaki fahimci Giwa ‘yar uwa ta d’auki Gimbiya Zeenat..”
Tak’aitaccen murmushi saman fuskar Muhibbah tana mai kuma k’arewa sashen kallo idan bata mance ba wannan sashen ne jiya taga wata mace ta shige cikin dare, Ta d’an kaikaito tana duban Umaima kana tace “Ita matar da za’a aurawa Yarima Mahmood d’in a nan cikin Masarautar nan take...?”
Umaima ta jinjina kai fuska d’aukeda murmushi kana tace “Takan zo Masarautar nan wajen ‘yar uwarta ta jima sosai wasu lokutan, zan iya cewa akasarin rayuwarta ma ya dawo Masarautar nan ne...”
Jinjina kai Muhibbah tai a hankali tana mai linke bayanan cikin k’wak’walwanta....
Umaima tace “Muje mu fara zuwa mu gaisa da Giwa kafin na dawo dake sashen Aunty Zeenat...”
Jinjina mata kai tai a hankali kana suka nufi sashen Giwa....
Zahra Ta mik’e tana mai goge bakinta da tissue paper take fad’in “Paa, I’ll be going now nasan su Noor da Sultan na jirana... Uncle best idan na dawo zaka fitar dani kilisa as you promised...” Ta k’arashe tana duban Fu’ad baki a ture...
Abincinsa yake ci yana jinjina mata kai lokaci guda yake furta “But first we need to ask for your Paa’s permission... Idan ya amince sai mu fita amma saidai a d’auraki saman rak’umi...”
Gaba d’aya suka murmusa cikeda jin kana Zahra tai masu sallama ta wuce mahaifinta na saka mata albarka...
Gudu gudu Zahra ta fito dan tuni lokacin tafiya makarantar ta ya gauta... Saurin da take yazo da tsautsayi takalminta ya karkaci tai loosing balance tim kakeji ta fad’i k’asa cikin wasu duwatsu da aka k’awata wajen dasu... K’ara ta saki tana kame goshinta da k’afarta dake mata zafi.... Faruwan hakan yai daidai da shigowarsu Umaima da Muhibbah... A tare suka ambaci sunanta had’ida nufowa gareta... Yayinda kuyanga guda Ta nufi sanar dasu Yarima Mahmood cikin sauri...
Umaima na kiran sunanta tainai mata sannu saidai tuni Muhibbah ta d’agota ta azata saman cinyarta, tai saurin zame hijabin makarantar Zahra had’ida toshe goshinta yanda jini ke zuba ta umarci Umaima ta danne wajenda jinin ke zuba...Daidai kokacindasu Mahmood da Fu’ad suka k’araso cikin sassarfa Mahmood na ambato sunan Zahran....
Fad’i yake “Zahra, sweetheart..What happened to you Darling...!”
Muryarsa data sinkayo daf da ita ya haifar mata da fad’uwan gaba mai tsanani, abubuwan da suka faru suka shiga dawo mata.... Take taji zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, kasa d’agowa tai ta dubesa sabida tsananin zogi da zuciyarta Ke mata saima k’ok’arin d’aure k’afar Zahra take da d’ankwalinta da tuni ta zamesa tana baiwa yarinyar agaji na gaggawa...
Jin muryar mahaifinta ya sanyata saurin d’agowa tana ambato sunansa cikin kuka “Paa..It hurts... My leg hurts Paa..!”
Tuni Muhibbah ta janye jikinta daga wajen yayinda Umaima ke sanar dashi fad’uwa tai, tuni ya d’auketa cak ya nufi ciki da ita yana sanar da Fu’ad ya kirawo family Dr d’insu yanzun nan...
Jikinta sai rawa yake zuciyarta naci gaba da bugawa ta koma sashen da akai mata masauk’i, ganin Mahmood da Fu’ad da tai kusa da ita ya jefata cikin tsananin tashin hankali, anya zata iya k’arasa abinda ta fara...? Tai saurin rintse idanunta had’ida zama bisa sofa, shigowarta da kad’an kuwa ta sinkayo ringing d’in wayarta cikin sauri ta isa domin d’aga kiran dan tasan mai kiran nata bazai wuce Ansar ba....
***
Prescribing magani likitan yai bayan ya gama dubata, Yarima Mahmood yace “Dr kana ganin basai anyi hoton k’afarba...?”
Likitan ya d’an girgiza kai kad’an kana yace “Babu abinda ya sameta, da zaran tayi amfani da wannan magungunan dana rubuta shikenan, babu wani fracture, and it’s a good thing ta samu taimako na gaggawa... Wanda dik ya d’aure mata k’afar yayi k’ok’ari wajen bata agaji irin wanda ake so...”
Sai yanzu abin ke zuwa kansa, ya d’an dubi Umaima dake zaune gefen Zahra tanai mata sannu kana ya maidoda dubansa ga likitan yana mai furta “I’ll walk you out Doc..”
Dr ya jinjina kai yana mai furta “Godiya nake your highness..” Ya k’arashe yana mai sallamawa Zahra had’ida fatan samun sauk’i...
A iyaka tinanin Mahmood Umaima batada wani ilimin abinda ya shafi asibiti, toh ya akai har ta baiwa Zahra irin taimakon da ake so cikin gaggawa.... Da wannan tunanin ya shigo d’akin bayan yayi rakiyawa Dr... A daidai bakin k’ofa ya tsaya yana jin tattaunawar Zahra da Umaima...
Zahra taci gaba da fad’in “I feel bad Aunty Umaima, I treated her badly... Gashi ita ta taimaka min... Kinada gaskiya she’s a nice person... Please tell me Aunty Umaima, am I really a bad person...?” Ta k’arashe kaman zatai kuka...
Hannunta guda Umaima ta kamo murmushi saman fuskarta kana tace “You’re not a bad person Zahra, and I’m sure Muhibbah ma bata d’aukeki haka ba... Ita da kanta ta fad’a watarana zakuyi shiri, and naji dad’i da tun ba’aje ko ina ba kin fahimci hakan... D’an Adam ko wane iri ne babu kyau wulak’antasa kinji sweetheart...”
Jinjina mata kai tai kana tace “Yeah I know Aunty Umaima, my Paa taught me to always be nice toward others... Please kice wa Muhibbah na gode...!”
“Muhibbah...!” Suka sinkayo muryar Mahaifin Zahra...
A tare suka juyo suna duban k’ofa kana Umaima ta d’an risina, murmushi saman fuskarta take fad’in “Eh Yaya, Muhibbah itace wacce Ta baiwa Zahra agaji na gaggawa, ita d’in karatun zama
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 65