inna’ilaihi raji’un.. Ta fahimci wannan d’aki, bayan shekaru goma sha hud’u da suka shud’e Ta fahimci d’akin.. Shine d’akin da ta farka ta tsinci kanta ciki bayan yaran Giwa sun lalata mata rayuwa.. Allah ya taimaketa Ta kub’uta daga hannun wani azzalumin mutumi mushiriki mummuna wanda sam baida kyaun gani...! Yau Gata nan Ta kuma tsintar kanta cikin d’akin bayan duka wad’annan shekaru..! Ta yuwu wannan shine K’addararta.. Koda ta gudu a baya yanzu gashi ta kuma dawowa bayan shekarun nan..! Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka gangaro mata..! Ta yunk’ura zata tashi taji inaa gaba d’aya a zarge take, irin d’aurin da akema abin yanka idan za’a yanka irin d’aurin akai mata..! Aka had’e hannuwanta da k’afafunta aka d’aure waje guda..!
Bud’e idanun da zatai Ta hangi Giwa, Jamal harma da Jakadiya tsaye daga k’ofar d’akin suna dubanta..!
Giwa ta kece da wani irin dariya yau d’in sanye take da bak’ar lkyabbarta na tsafi ga wani bak’in tulu gabanta harda wani jan fitila maici da jan wuta...
SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH*
*74*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin zuban hawaye take dubansu d’aya bayan d’aya zuciyarta na kuma karaya da tinanin watak’ila itakuma tata K’ADDARAR kenan ta mutu cikin wannan d’akin hannun wad’annan azzaluman... Ta lumshe idanunta hawaye suka kuma gangaro mata.. Cikin zuciyarta take furta “Ya Allah kada ka k’addara mutuwata hannun wad’annan azzaluman bayi naka..! Ya Allah ka kub’utar dani da buwayarka kar ka basu nasaran cutar dani..!” Bata ida ba taji Giwa tasa k’afa ta shureta...
Tayi tsaye gaban Muhibbar had’ida k’ura mata idanu, lokaci guda ta shiga jinjina kai tana furta “Tabbas ke ce..! SAUDATU..!” Ta kuma sakin murmushi kana taci gaba da fad’in “Na tabbata kin gane d’akin nan..! D’akin da ya shekara goma sha hud’u a bud’e yana zaman jiranki, yau gashi kin dawo cikinsa kuma zaki dawwama cikinsa domin kuwa wannan d’aki Naki ne wanda aka ambacesa da sunanki Saudatu aka kuma rubuta saman Farin k’yalle, Ked’in kyauta ce ga Sarauniya, a yau Zata cika k’udirin ta ta kuma cika min Mulki na da gudan jininki..!!” Ta kuma kecewa da dariya..!
Muhibbah da hawaye Ke gangaro mata take Ta soma furta “Allah bai baku nasara shekarun baya ba, Maiyasa kike tunanin zai baku nasara yanzu..? Maiyasa kike tunanin zaki tabbata kina zalunci..! Barin tuna miki idan kin mance.. Ni ce nan wacce na shigo rayuwarku na tarwastaku ba tareda kun ankare ba..! Kuma ni ce nan zan zamto silan tonuwar asirinki dake da muk’arabbanki... Zaki gani da sannu Ubangijina zai kawo min d’auki ya kawo wanda zai fiddani daga sharrinku..!!” Batakai aya ba Giwa ta d’auketa da muguwar mari.. Lokaci guda take furta “Babu wanda zai fitar dake daga wajen nan Saudatu, duk duniyar nan babu wanda yakeda mabud’in wannan gini... Mutum guda yake da mabud’in wannan gini kuma ya mutu.. Mabud’in wannan gini guda d’aya ne tak kuma an bisneta cikin K’undi da jimawa... Saudatu bazaki tab’a ficewa daga wajen nan ba... Nima kaina banida wannan mabud’in wanda ya adana wannan mabud’in har ya bar duniya bai mallaka min ba... An busnesa tareda k’undin cikin turb’aya....Tal’udu shi ya bani karatun tsafi da zanke biyawa ginin ya tsage min na shige.. Sannan ko Jakadiya da a kullum take min rakiya bata iya wannan karatun tsafin ba.. Gata nan ga Jamal ki tambayesu ya akai suka shigo wajen nan... Bud’e idanu kawai suma sukai suka gansu cikin wajen nan kaman yanda Kema bud’e idanu kurum kikayi kika ganki ciki..! Har abada babu wanda zai iya fitar dake Saudatu..!!” Ta kuma kecewa da wani irin dariya..
Muhibbah na murmushi take furta “Wanda ya fitar dani daga farko inada tabbacin shi zai kuma fitar dani..! Dashi nayi imani dashi na dogara, kuma na tabbata shine zai taimakeni..! Da sannu zai tona miki asiri, sannan ya k’asak’antar dake, zaki koma bakida wani daraja ko matsayi ta yanda k’ask’antaccen bawa sai ya fiki daraja cikin Masarautar nan..!” Bata kai aya ba Giwa ta kuma kwashe ta da wata mari.. Tana huci take nunata tana fad’in “Ke k’aramar maras kunya..! Na gama da iyayenki na gama da kaf zuri’arki balle ke..Tin daga Kan Kakanki Sarki Jamaluddeen na k’asar Benin wanda shine ya haifi mahaifinki Yarima Alfah d’an uwa ga Gimbiya Turai matar Sarki AbdulJabbar wacce na maidata Kuyanga a gidan Mijinta, mahaifiya ga ‘ya’yan Sarki guda biyu Yarima Mahmood wanda na maidashi nawa tin yana jariri domin na cika k’udirina akansa, da kuma Ja’afar wanda na maidashi d’an Bawa ya girma cikin k’ask’anci da bauta a gidan mahaifinsa a Masarautar Sa.. Dan haka ki sani gamawa dake abu ne mai matuk’ar sauk’i a gareni k’aramar Alhaki..!!” Ta k’arashe tana mai d’ago fuskar Muhibbah wacce ta shige rud’u sosai.. Bata fahimci mai wannan matar take fad’i ba gaba d’aya ta zama lost and confused..! Cikin wane irin yanayi take duban Giwa da idanunta da suka firfito waje tana jin kanta na juya mata...
Giwa ta kuma kecewa da dariya tace “Nasan duk bakisan wad’annan labarun ba, bakida masaniya amma bazan bari ki tafi ba tareda kin sani ba... Zan baki labarin duk abubuwan da nayi ma zuri’arki tin daga tushe... Idan kika tafi a haka ba tareda kin sani ba kinci banza..! Gwara ki San komai, kisan duk abubuwan dana aikata kafin k’ofar d’akin nan ya rufe dake rufuwa ta har abada..!!” Ta kuma kecewa da muguwar dariya...
Take Giwa Ta shiga labartawa Muhibbah duk abubuwan da suka faru tin daga farko, Dik wani k’ulli da makirci da tayi da lokutan da abubuwan suka faru da komai da komai..!
**
A can asibiti wajen Yazeed kuwa bore da hauka yake ci gaba da yi, an masa alluran baccin ma kaman a banza don yana somawa allurar zata sakesa ya farka yaci gaba da ihu yana fad’in a dawo masa da hannayensa da yaransa... Ya dubi Waziri dake zaune gefensa dan tinda ya farka bai bar gefen Yazeed d’in ba...! Cikin wane irin huci yake ceda Waziri “Kai Old Geezer, Take me to the palace..! I want to see Mahmood, I want to rub it to his face... Ina so naga fuskarsa idan yaji cewa shid’in ba kowa bane d’an Baiwa ce k’ask’antacciya mai k’wacen mijin Uwargijiyarta..! Ka d’aukeni ka kaini Masarauta na sanar da Mahmood haka, ya daina jin kansa shid’in wani ne ko shi d’in yafi wani... Baifi kowa ba shid’in k’asaitacce ne d’an Baiwa... Baiwarma Ta wani Masarautar wacce aka sadakar da ita...! Ka d’aukeni Ka kaini nace... I can’t be the only loser..! Mahmood ma dole ya d’and’ani irin k’uncin dana d’and’ana... Na tabbata yana can yana murnan abubuwan da suka sameni..! Amma idan yaji asalinsa da tushensa zai fahimci cewa shid’in k’ask’antacce ne... Bawa bai dace da sarautar Masarautar mu ba... Gwara nakasasshe ya zamto Sarki akanka D’an Baiwa ya gaji sarauta..! Ashe abin a jini yake shiyasa ya k’are ya auri d’iyar bayi...! Toh yau d’in nan wllhi zaiji asalinsa koda zai had’iyi zuciya ya mutu ne..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da fidda huci..!
Waziri dake faman muzurai zuciyarsa na tsinkewa ya soma fad’in “A’a Yazeed kai hak’uri dai har ka k’ara samun lafiya...!”
Baikai aya ba Yazeed ya katsesa da fad’in “Kai Dattijo kayi abinda na umarceka idan kana son kanka da lafiya.. Har gobe nid’in sama dakai nake domin ni d’an Sarki AbdulJabbar ne... Ko a mafarki kada ka tab’a zaton zan kalleka matsayin mahaifi..! Tashi ka kaini masarauta idan baka so na k’arasa kashe kaina yanzu a asibitin nan..!!”
Waziri ya had’iyi miyau da k’yar yana sab’a babbar riga cikeda daburcewa yake fad’in “Toh..Toh.. Toh ai Wato ai gani nayi ciwonka d’anye ne dukda cewa na rufe cikin bandeji..!”
Yazeed ya katsesa da fad’in “Zakayi abinda na umarceka ne kokuwa...!!”
Waziri ya kuma mik’ewa zunbur yana furta “A’a ba za’ayi haka ba Rankaidad’e..!!” Lokaci guda ya mik’e ya nufi k’ofa yana fad’in bari ya kirawo malaman asibiti su kwance ruwan da aka d’aura masa...! Bai kuma tsayawa sauraren Yazeed ba ya fice...!
Yazeed ya shiga k’walla masa kira, inaa Waziri ko juyowa baiba dan ko kusa bazai biyema Yazeed su tapka wannan rashin hankalin ba... Domin kuwa ba asirin Mahmood zai tona ba asirin mahaifiyarsa zai tona...!
Yazeed yaji zuciyarsa kaman zata buga Dan babu abinda zai iyayiwa kansa... Ya shiga shure shure da k’arfin gaske har dai ya samu ya finciki drip d’in dukda tsananin azaban hannayensa da yakeji... Amma dole ya daure koda jini zai b’alle a jikinsa ne sai yaje ya tunk’ari Mahmood ya tarwatsa zuciyarsa kaman yanda nasa rayuwar Ta tarwatse... Haka ya lallab’a ya sauk’o daga saman gado babu hannaye... Taimakonsa d’aya Waziri ya mance k’ofa a bud’e nan yabi ta k’ofar yana tafe yana ciza labb’a sabida tsananin azaban da hannayensa ke masa, zafin zuciya irin nasa da tsanar Mahmood bazai bari ya zauna a asibiti Mahmood yana can yana jubilating nakasan da yayi ba...
A haka ya fito yana bin garu yana satan idon mutane har ya samu ya fito haraban waje... Nan ya iske Waziri na k’ok’arin shigewa Mota... Cikin sauri Yazeed ya nufi Waziri yana furta “Kai Oldtimer..! Kai Dattijo..!!”
Waziri na k’ok’arin kutsa kai Mota dan baiyi zaton zaiga Yazeed ba, Yazeed ya k’araso yana hakin azaba lokaci guda yake furta “Kana jina wllhi ko ka d’aukeni ka kaini masarauta ko kaima na tona maka asiri kaci amanan amininka ka nemi matarsa har kun haihu... Kasan ni a halin yanzu I’ve got nothing to lose..! My whole life is already ruined... Abokin tafiya nake nema shiyasa zan fuskanci Mahmood na sanar dashi asalinsa..! Idan kana son kanka da lafiya, idan baka so ka tafi k’asa taredani da Mahmood, Toh ka d’aukeni ka kaini Masarautar nan,.. Kuma Kai banda abinka, idan naje Masarauta na tona asalin wanene Mahmood ai Kasuwarka ce Waziri, kaga watak’ila sarauta ta fice daga ahalin AbdulJabbar ta har abada Kaga shikenan ka samu tsuntsu a sama gasasshe... All thanks to your Bastard Son, at least ko ban maka noma ba na baka abinda yafi Gonakin ka da ‘ya’yanka suka jima suna noma maka..! Na baka sarautar k’asar baki d’aya...! Ko ya kace Old geezer.. Kaga watak’ila nayi recognizing d’inka as Uba..!!” Ya k’arashe muguwar murmushin nan nasa saman fuskarsa...
Waziri ya shiga Washe baki yana furta “Allah koh Yarima..! Kuma fah kaima ka kawo wani shawari... Idan na zama Sarki shikenan batu yayi dad’i, duk Sadaukarwa da mahaifiyarka tayi bai tafi a banza ba..! Shige muje..!” Ya k’arashe yana mai bud’e ma Yazeed d’in marfin Mota....
**
Neman duniyar nan cikin Masarautar sunyi babu Giwa babu Muhibbah balle Jamal ko Jakadiya..! Babu su Babu alamunsu... Idan Kaga Mahmood dole ka tausaya masa, gaba d’aya ya fice hayyacinsa harta Ansar saidai yasha mamakin kalan tashin hankalin da Yarima Mahmood ya shiga na rashin ganin Muhibbah... Ko shi da yake ikirarin yana sonta sai yaga nasa ashe wasan yara ne..! Saima ya soma tuhumar kansa anya yana sonta kuwa..? Ji yayi kaman ba soyayya yake mata ba tinda yaga yanda Yarima Mahmood ya gama susucewa cikin Masarauta na rashin ganinta da tinanin halinda zata iya kasancewa ciki..!
Allah ya gani Mahmood d’in sai ya basa tausayi sanin cewa ahalinsa ne suka cutar da matar da yake matuk’ar so irin haka...
Anyi searching anyi anyi babu su babu alamun su, idan aka soma tunanin dakatawa da nema Mahmood d’in yakan ce babu mai hutawa koda gari zai rufe ya kuma wayewa ne sai an zak’ulo yanda suke cikin Masarautar..!
Turaki ya dafe kansa kurum yana duban Mahmood d’in dake Ta k’ok’arin tokarin wani k’ofa da iyaka k’arfinsa wanda shida Turakin ne suka k’araso wajen..!
Bai sarara ba saida yaga ya bud’e k’ofar..! Suka ja sukai turus shida Turaki ganin kujera ajiye daga center Babu kowa akai sai handcuffs da sauran busasshen jini... Cikin sanyin jiki zuciyarsa na bugawa ya isaga Kujerar take ya zube ya duk’a saman gwiwoyinsa ya d’aga handcuffs d’in yana juyawa yana kallo... Turaki ma ya k’araso yana kallon kayan mamaki.. Da gaske dai mutanen nan bak’ak’en azzalumai ne.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Can ya hango hawaye daga idanun Mahmood suna d’agowa...
Baida daina juya handcuffs d’in ba yake furtawa cikin tsananin rawar murya “They tortured her..! Sun azabtar da ita Turaki...! They’re not humans..! Ta yaya d’an adam zai aikata haka..! Kodai akwai laifin da nake aikatawa ne Allah ya jarabceni da irin wad’annan ahali..! Tell me Turaki..! Please tell me..!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Turaki ya dafasa yace “Mahmood kowa da irin jarabawarsa a rayuwar nan, wani a jarabcesa Ta iyalansa wani ta ahalinsa, wani ta wajen sana’arsa.. Wani ma da lafiyarsa za’a jarabcesa.. Duk dan a gwada k’arfin imaninmu..! Kada ka kauce hanya your Highness..! Ubangijinka yana gani kuma baya bacci da sannu zai kawo maka sauk’i iftila’in da ya Aiko maka..! Tashi muje.. Watak’ila sun fitar da ita daga cikin Masarautar nan muyi saurin cimmasu..!!” Yai k’ok’arin mik’ar da Mahmood d’in suka nufo waje dukda shi kansa Turakin baisan Ta inda zasu kuma nufa ba..!
Rik’o hannun Turaki Mahmood yayi yace “Kana tunanin sun kashe Muhibbah..?!” Yayi maganar cikin tsananin rawar murya..
Turaki ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali, dan duk abinda zai fad’iwa abokin nasa a halin yanzu yasan k’arya ne, amma babu yanda ya Iya Mahmood yana buk’atar a kwantar masa da hankali a kuma nuna masa akwai hope..! Nan Turaki yaci gaba da basa k’warin gwiwa yana nuna masa kada ya karaya da izinin Allah Muhibbah tana nan da rai kuma zasuyi rayuwa mai tsawo nan gaba tare..!
A tare suka nufo yanda suka baro su Ansar da sauransu, jikkunansu a matuk’a sanyaye daga Mahmood d’in har Turakin tun bayan da sukaga wajen dasu Giwa da Jamal suka aje Muhibbah...
Izuwa wannan lokaci cikin Masarauta ta gama rikicewa gaba d’aya, kama daga b’angaren masu sarauta har zuwa b’angaren bayi.. Zancen kenan guda d’aya ake.. Masu mamaki nayi masu jimami nayi... Illahirin Masarautar tausayin halinda Mahmood ya tsinci kansa ciki suke..! Su matan Wambai kuwa sai jinjina lamarin suke masu k’ara gishiri da onga nayi.. Harda masu cewa Giwa ce ta cinye ‘ya’yan Yarima Yazeed Wai mayya ce, ita ta cinye matar Mahmood ta cinye mai Martaba harma da Wambai itace Ta cinyesa Ta kuma cinye k’afar Jamal guda Ta cinye hannayen Yazeed..!
Juwariyya d’iyar Wambai da itace takaiwa su Raheema da Gimbiya Zeenatu labari gaba d’aya tsoron al’amarin ya gama cikasu.. Gimbiya Zeenatu jikinta yafi na kowa yin sanyi, zataso Ta sami Mahmood Ta sanar dashi yanda ta rufe asirin Giwa na kashe matarsa da tayi dan kawai k’anwarta Raheema Ta aure Mahmood d’in, akan idanunta Giwa Ta halak’a Matar Mahmood, Ta kuma ce ta halak’ata ne dan Mahmood ya auri k’anwar Zeenat d’in Raheemah... matuk’a Aliya nada rai tasan d’anta Mahmood bazai tab’a kallon wata mace ba balle ya aureta, Anya bazat sami Mahmood Ta sanar dashi gaskiyar batun ba..? Ta k’arashe tunanin nata tana mai mik’ewa tsaye cikin tsananin sanyin jiki..
Juwariyya dake ci gaba da labartawa Raheema yanda abubuwan suka kasance dakatawa tai suna duban Gimbiya Zeenat da Ta mik’e jiki babu k’wari..!
Raheema tace “Aunty Ina kuma zakije.. Kinaji ance cikin Masarauta babu lafiya Dakaru ne ta ko ina.. Salon Ki fice wani tsautsayin ya ritsa dake, Allah ya gani Masarautar nan ya soma bani tsoro asubahin fari gobe zan tattara na koma Masarautar mu saidai duk abinda za’a fad’i a fad’i..!”
Gimbiya Zeenat da har lokacin jikinta a matuk’ar sanyaye yake tace “Raheemah Mahmood nake son gani akwai abinda nake matuk’ar son sanar dashi.. Gwara na sanar dashi bazan iya ci gaba da rik’ewa a cikin zuciyata ba..!!” Ta k’arashe tana mai rufa alkyabbarta ta nufi k’ofa...
Raheemah na kiranta inaa ko tsayawa batai ba..
Juwariyya Ta dubeta tace “Ahtoh dai ki tafi ki bar Masarautar nan kafin ta iso kanki..!”
Raheemah Ta dubeta da mamaki tace “Ban gane ba..?! Wai mai Giwan tayi yanzu ake nemanta haka..?!”
Juwariyya ta tab’e baki tace “Tabb! Yanzu ne duk labarin da nake baki ina hankalinki yake..! Ance miki ta sace matar d’anta zata cinye..!”
Raheemah ta girgiza kai tace “Ban fahimceki ba..! Wai kina nufin Zuhra..! Zuhra kam ai tana asibiti inji..!”
Juwariyya Ta dubeta shek’ek’e tace “Wata Zuhrar..! Ana miki maganan matar Yarima Mahmood..!”
Mamaki ya kuma kama Raheemah..! “Matar Yarima Mahmood fah kikace..? Yaushe Mahmood d’in yayi auren..?!”
Juwariyya Ta yab’e baki tace au ashe fah bakida labari kina nan kina jimamin rashin aurensa da bakiyi ba, gashi kin kasa zuwa asibiti kiga yanda mijinki Yazeed ya koma...!”
Cikin tashin hankali Raheemah ta katseta da fad’in “Ke ni k’i k’yaleni da zancen Yazeed, duk halinda ya tsinci kansa ciki ba matsalata bace tinda shine ya jefa kansa ciki..! Tambayarki nake shin Yariman nawa shine yayi Auren...Mahmood ne yayi aure...? Yaushe kuma a ina..?!!” Ta k’arashe idanunta na firfitowa waje hannuwa dafe da k’irji...!
Juwariyya da tai sakare rana dubanta jinjina mata kai tai tace “K’warai kuwa Rankaidad’e yayi aure, ranan da ya d’aura miki aure da Yazeed ranan yayo aurensa shima...! A yanda naji labari na Yawo cikin Masarauta babu wanda yasan yayi auren sai abokinsa Turaki da Hadiminsa, ke ko Giwa bata sani ba, naji ana cewa ya b’oye mata auren gudun kada Ta lashe masa matar tasa ne kaman yanda ta lashe matarsa ta farko, Aiko gashi data fahimci yayi auren Ta lashe sabuwar amaryar tinda babu wanda yasan k’anda suke yanzu.. Labari fah nata Yawo cikin Masarauta gashi ance Sosai Rankaidad’e ya rikice da neman matar tasa da alama yana matuk’ar k’aunarta..!!”
Gaba d’aya Raheemah bama Ta gane mai Juwariyya Ke fad’I saima hawaye dake k’ok’arin ambaliya a fuskarta..! Babu shiri Ta mik’e ta nufi waje cikin kuka..!
Juwariyya Ta mik’e tabi bayanta tana kiran sunanata...! Inaa Raheema bata tsaya ba burinta kawai ta isaga Mahmood ta tabbatar da gaske aure yayi ta kumaga matar da ya aura...
**
Ana tsaka da wannan kwanacala Yazeed ya iso Masarauta....
Ganin yanda ake satan kallonsa ana k’usk’us cikin Masarautar sosai ya kuma tunzura Yazeed, Wato yanzu ya zama abin nunawa da baki.. Wasu bayi da suka kasa janye idanunsu daga barin duban nasa suka kuma kasa duk’awa gabansa wane irin tsawa ya darara masu yana fad’in Shine Yarima Yazeed wanda ya kuma cancanci gadon mulki ko ba’a sarki maras hannaye za’a soma a kansa..!
Shidai Waziri gaba d’aya yasha jinin jkinsa da ganin yanda Masarautar take a hautsine.. Duk basu kawo komai ba dan duk sunyi zaton dalilin tsautsayin da ya afkawa Yazeed da iyalansa ne Masarautar Ke yamutse...
Duk wanda yaga Yazeed sai ya kuma dubansa kafin ya risina...
Sai sakin huci Yazeed yake yana ayyanawa cikin ransa duk Mahmood ne ya janyo, da ace ya auri Raheemah Sun tafi k’asar Spain duk da hakan bata faru dashi ba, da yanzu hannayensa da ahalinsa duk suna nan, wani irin tsanar Mahmood d’in ya kuma tokare masa k’irji... Inama yanada hannuwa biyu da ya shak’e Mahmood a yau ya mutuwa ya huce takaicin ganinsa a doron k’asa...
A daidai mashiga babban k’ofar da zai sadaka da cikin Masarauta su Yazeed suka had’uda tawagar Mahmood.. Da alama ficewa neman su Giwa zasuyi...
Gaba d’aya illahirin jama’an dake wajen suka maida dubansu ga Yazeed wanda tuni ya isa gaban Mahmood yana mai sakin huci... Waziri yana k’ok’arin sallaman wad’anda ba ahalin gidan ba Yazeed ya bud’e murya yace kowa ya tsaya, ayi a gaban kowa susan wanene Mahmood..!
Shi kuwa Mahmood kalaman Ansar ke ci gaba da buga zuciyarsa cewa ‘yanuwansa su suka lalata rayuwar Muhibbah, ya tuna Fu’ad ya sanar dashi Yazeed ne ya soma..! Zuciyarsa taci gaba da bugawa musamman da yaga Yazeed tsaye gabansa... Sai dunk’ule hannayensa yake yana murzasu wani irin gumi na tasowa tun daga tsakar kansa yana bin goshinsa har zuwa saman karan hancinsa yana gangarowa... Ji yake idan ya rik’e wuyan Yazeed tabbas zai iya kaisa lahira... Muryar Yazeed d’in suka sinkaya yana furta “Kaji dad’i..! Nace kaji dad’I Mahmood..!! Yanzu da kake ganin sarauta takace kai kad’ai dan ba’a Sarki muskini..! Idan ba’a Sarki muskini Toh ka sani ba’a sarki k’ask’antacce...! Yes na fad’a ba’a Sarki k’ask’sntacce, jinin Bauta wanda bai gaji komai ba face Bauta..!!”
Mamaki ya cika fuskokin mutane da jin irin kalaman dake fitowa daga bakin Yazeed...! Lokaci guda Yazeed d’in ya juyo yana duban mutane kana yaci gaba da fad’in “Jama’an Masarautar nan a yau d’in nan inaso na sanar daku ko wanene Yarima Mahmood da wasunku suke masa lak’abi da Sarki mai jiran Gado...! Ina son kowa ya shaida cewa Shid’in ba kowa bane face k’ask’antaccen Bawa..! Mahaifiyarsa Baiwa ce ga matar Sarki Gimbiya Turai..! Mahaifiyarsa Hadima ce da Gimbiyar Turai tayi tukuici da ita ga mahaifina Sarki AbdulJabbar mai rasuwa..! A tarihin Masarautar nan d’an Baiwa bai tab’a mulki ba sai d’an Sarauniya..! Wannan dalilin ya tabbatar cewa Mahmood bazai tab’a gadon Karagar mulkin gidan nan ba..!!” Ya k’arashe yana mai sakin huci yana kuma duban Yarima Mahmood wanda jikinsa Ke sakewa a hankali, hannunsa dake faman dunk’ulesu yana waresu a hankali alamun ya shiga tsananin Shock da abinda yakeji na fitowa daga bakin Yazeed d’in...
Ganin haka yasa Yazeed d’in ci gaba da fad’in “K’warai..! Ina so kowa ya shaida cewa ba mahaifiyata Gimbiya Turai bace ta haifi Mahmood Hadimarta ce k’ask’antacciya da taci amanan Uwargijiyarta ta haifo Mahmood.. Wannan magana da nake sanar daku Gimbiya Turai kuma Giwar Amale da bakinta Ta sanar dani sabida zuwan irin wannan rana..! Mahaifiyata bata haifi d’an Sarki Mahmood ba... Inada k’wak’warran shaidu da zasu tabbatar da hakan..!”
Cikin tashin hankali Talba ya katsesa da fad’in “Kai Yarima, kana cikin hayyacinka kuwa kodai had’arin da kayi ya tab’a maka kaine.. Ka kuwa San abinda kake fad’i..?!”
Yazeed ya karkato yana duban Talba kana yace “K’warai kuwa Talba..! Da hankalina tsaf nasan abinda nake fad’i..! Kuma idan kuna ganin k’Arya nake zan gabatar maku da shaidun da zasu tabbatar cewa Mahaifiyata Giwa ba itace Ta haifi Yarima Mahmood ba, shid’in d’an Baiwarta ce kuma k’ask’antacciya ..!!”
Cikin sakin huci da jin zafin abinda Yarima Yazeed keyiwa d’an uwansa a bainar jama’a Talba ya bud’e murya yace “Su waye shaidun da kake magana akai Yarima Yazeed..! Su waye zasu tabbatar da k’arerayin da kake fad’i..?!”
Kafin Yazeed yakai ga bada amsa suka sinkayo wata murya mai amon gaske tana fad’in “Ni ne nan zan bada shaida..!!”
Gaba d’aya suka juya suna duban wanda yayi magana cikin tsananin Shock.. Harda Yazeed d’in wanda yake yunk’urin nuna Waziri a matsayin shaida..!
Ga tsananin mamakinsu suka zuba wa mutumin da yayi magana, sanye yake cikin shiga irinta Mulki, yayi tsayuwa irin yanda masu Mulki keyi..!
A hankali Mahmood ya furta “JAFAR..!!”Koda ace ya sanya tufafi irin na masu mulki tabbas kamanninsa bai b’ace ba..!
Mamaki da aljabi ya cika illahirin jama’an dake wajen sanda Ja’afar ya soma takowa cikin haraban Masarautar..! Mutane sai darewa suke suna basa hanya, wasu na k’ok’arin guduwa ganin Tamkar Fatalwa ne a gabansu.. Babu kaman Waziri wanda tuni fitsari ya cika mararsa..
Kai tsaye gaban Mahmood Ja’afar ya isa ya tsaya su duka biyun suna duban juna cikin idanu... Wani irin duba Jafar keyiwa Mahmood d’in kalman Yazeed na Yawo a kwanyarsa cewa Giwa ba itace Ta haifi Mahmood ba, mahaifiyarsa Hadimarta ce..! Wato mahaifiyarsu d’aya kenan, ya shiga tuno abubuwan da mahaifiyarsa Ta sanar dashi wanda Giwa tai mata..! Kenan Yarima Mahmood shine Babban d’a ga Mai Martaba wanda Bokan Giwa yace sai an haifosa duniya..! Kenan sace Yarima Mahmood tayi Ta rabasa da mahaifiyarsa kaman yanda Ta sacesa shima..! Lokaci guda yaji hawaye na neman ciko idanunsa.. Gashi ga d’anuwansa wanda suka fito ciki guda...!
Shima Mahmood d’in wane irin duba yake ma Ja’afar d’in, sai yana ganin kaman ya tab’a ganin Ja’afar d’in da irin shigar da ya gansa ciki yau... Cikin wane irin murya mai raunin gaske ya furta “Ja’afar..!!”
Hawayen dake mak’ale cikin idanun Ja’afar suka gangaro..! Lokaci guda ya rungume Mahmood d’in hawaye naci gaba da gangaro masa..!
Mamaki ya kasa sakin d’aukacin jama’an dake wajen... Tirk’ashi..!Wannan shine ana wata ga wata..!
Waziri da ya tabbata Ja’afar yake gani raye a gabansa cikin dabara ya soma k’ok’arin silalewa yana neman hanyar da zai fice daga wajen..!
Gudu gudu ya soma jada baya yana k’ok’arin tattare babbar rigarsa, kaman daga sama yaji ya bangaji mutum har rawaninsa na zubewa k’asa. D’aga kansa da zai yaga ba kowa bane face Ubandoma..!!
SameenaAleeyou *MUHIBBAH*
*75*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ubandoma ya sakarwa Waziri murmushi maiji da lafiya had’ida furta “Rankaidad’e..! Mai girma Wazirin Wazirai..!!”
Waziri
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 51 Chapter of 65