Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
k’wayoyin tai saurin bige hannunsa suka watse k’asa.... Fu’ad ya d’ago yana dubanta lokaci guda yaci gaba da matsawa jikin gini yana furta “Please forgive me...Please please please.. I don’t want to.. Please...!!” Tamkar mai tab’in hankali haka yake sunbatu yana kuma matsawa jikin gini.... Muhibbah tai zaman rak’umi gabansa tace “Fu’ad meke faruwa... Please tell me wane laifi ka aikata kake neman afuwa...?!” Ta k’arashe cikin d’an d’aga Murya.... Dubanta yai da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda yake furta “Please forgive me Muhibbah... Baki cancanceni ba... I’m a monster a killer... A ra....!!” Ya kasa ci gaba da magana sai hawaye dake kuma ambiya a fuskarsa.... Lokaci guda yanayinta ya sauya, idanunta sukai jazir, cikin dakewa take ci gaba da fad’in “If you truly love me, you tell me what exactly you’re hiding Fu’ad... Idan ba haka ba ka mance dani dan bazan tab’a kasancewa da mutum irinka ba... Now go ahead and tell me what really happened...!!” Cikin wane irin yanayi yake furta “I cant Muhibbah... Mahaifiyata da ‘yanuwana zasu disowning d’ina muddin maganan ya isaga Ya Mahmood...!!” Cikin wane irin sanyin jiki had’ida bugawan zuciya tace “I don’t get you Fu’ad... Meye kake b’oyewa Yarima Mahmood..!?” Fu’ad na kuka sosai yake furta “Wani babban laifi da muka aikata nida ‘yan uwana guda biyu... Yazeed Jamal da kuma ni Fu’ad... Wani laifi ne da muka aikataga wata ‘yar talikan yarinya shekaru goma sha hud’u baya... Mun aikata laifin ne a bisa umarnin mahaifiyarmu... A cewarta idan har bamu hakan ba bazamu tab’a tabbata akan Karagar mulkin Masarautar nan ba... Na aikata laifin ne dan sadaukarwa ga ahalina Muhibbah... Amma tun bayan wancan lokacin ban kasance cikin kwanciyar hankali ba har yau...!!” Ya k’arashe hawaye na kuma ambaliya a fuskarsa... Muhibbah da tuni duniyar ya soma juya mata, cikin tsananin sanyin jiki had’ida rawar murya take furta “Mai kuka aikatawa yarinyar da ahalinta..?!” Ta k’arashe siririyar hawaye na gangaro mata.. Fu’ad yace “Zalunci mafi muni... Mun mata fyad’e dukanmu uku... Muka kashe mahaifinta sannan muka cinna wuta cikin gidan ta k’one da ita da mahaifiyarta suna cikin gidan... Wuta ya cinyesu a gaban idanuna... I couldn’t do anything to stop the fire... Yazeed da Jamal sun janyeni sun hanani taimakon yarinyar da mahaifiyarta... Haka muka k’yalesu suka k’one k’urumus cikin gidan... Bazan tab’a yafewa kaina ba Muhibbah...!!” Ya k’arashe cikin tsananin kuka... Muhibbah da hawaye Ke ambaliya a fuskrta cikin tsananin rawar murya tace “Kana nufin ku kuka aikata laifin banda Mahmood...?!” Fu’ad ya jinjina kai yace “Idan Yaya ya sani tabbas zamu rasashi bazai tab’a yarda ya rayu cikin ahali azzalumai ba... Mahaifiyarmu zata rasashi amma a cewarta duk abinda mukai sadaukarwa ce gareshi dan tasan shi bazai tab’a aikatawa ba shiyasa mu Ta umarce mu muyi... Ranan bukin wata sallah ce... Mun fita mu dukanmu hud’u akan dawakanmu dan zaga gari, saiko bawanmu Ja’afar dake rik’eda linzami na sabida a lokacin ni k’arami ne sosai ban wuce sha uku ba shisa Jafar ke rik’e min linzami ko fita kilisa zamuyi... A can wajen gari muka tsinci yarinyar tanata kuka da alama tabi ‘yan kallon dawakai da wasan sallah masu zaga gari shine ta b’ace... A lokacin almuru ya k’arato... Yaya shine ya soma hango yarinyar ya umarci Ja’afar ya k’arasa ya duba dan yaji kaman kukan mutum... Jafar yai kaman yanda Ya Mahmood yace....!” Ya d’anyi fasali hawaye naci gaba da gangaro masa... Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Akai sa’a Jafar yasan yarinyar a bayan masarauta gidansu yake kaman yanda Jafar ya sanar da Yaya... Yazeed yace mu tafi mu barta bai kamata a ganmu da k’ask’antattun mutane irin wad’Annan ba... Yaya yace koda wasa baza’ai haka ba... Yaya da kanshi ya d’auketa ya azata saman dokinsa da yake bisa tana gaba yana baya ya bata apple d’in da yake ci, kallo guda zakai masa ka fahimci tsantsan tausayin yarinyar da ya kamasa...” Muhibbah Ta lumshe idanunta a hankali hawaye suka gangaro mata tana mai tuna tabbas anyi haka, wannan kyakkyawan murmushin nasa shine saman kyakkyawan fuskarsa... Ta sinkayo muryar Fu’ad naci gaba da fad’in “Ga dukkan alamu yarinyar da Jafar sunsan juna sosai dan na kula da irin duban da sukewa juna tana daga saman doki Jafar na janye da linzamin doki na.. Hasalima sanin Jafar da tai yasa Ta amince damu...” “A Haka muka iso har masarauta, dan lokacin da muka iso har yarinyar tayi bacci jikin Yaya sabida tafiya ne saman doki dole akwai gajiya musamman ga yarinya mace irinta... A lokacin da muka iso masarauta d’an aike ya taremu ya sanar damu mahaifinmu Wato Mai Martaba Amale yana kiran Ja’afar kirata gaggawa... Yaya Mahmood yace maza Ja’afar yaje ya amsa kiran Amale shi zai kula da yarinyar zai kaita Gida sannan zai sauk’o ya rik’e linzamin dokina dan kar na fad’i...Ja’afar yai masa kwatancen gidansu yarinyar kana ya tafi Fada amsa kiran Mai Martaba... A daidai lokacinda Ja’afar ya tafi amsa kiran Amale ita yarinyar ta farka daga baccinta... Tabi bayan Ja’far da kallo tsoro sosai saman fuskarta, da alama Ta razana sosai damu tinda dama sabida Ja’afar ta yarda ta bimu gashi shi kuma ya tafi....” “Mun kula tunda Ja’afar ya tafi hankalin yarinyar bai kwanta damu ba... Sosai tsoronmu ya bayyana a tattareda ita musamman dataji Yazeed yanata mitan maiyasa zamu taimaka ma k’ask’antacciya irin wannan yarinyar...! Ya Mahmood shi ya sakar mata murmushi ya tambayeta zata gane gidansu daga nan bayan Masarauta, tai saurin girgiza kai cikeda tsoro tace dashi ita bazata gane ba dan basu jima da dawowa garin ba kuma a lokacin akwai duhun dare..! Mukaita dariyarta muna daga saman doki Yaya ya tsawatar mana yace mu daina mata dariya, ya kwantar mata da hankali da fad’in cewa zamu kaita har gida....!Ana haka muna tafe Yaya ya rik’e linzamin dokina da kuma dokin da ita yarinyar ke bisa d’an aike ya kuma zuwa yayi kiran Yaya inji mai Martaba... Yaya ya bar mana amanan Yarinyar ya janyo Yazeed gefe yaja masa kunne kan cewa mu tabbata mun kai yarinyar har gidansu, shi zai jeshi ya amsa kiran Mai Martaba.... Muhibbah ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen suka zubo mata... Tabbas bata kula da tafiyar Mahmood ba sabida duhun dare kuma muryar yaran Sarkin kusan duka iri guda ne ashe Mahmood ya tafi bata sani ba... Ashe amanarta ya damk’a hannun ‘yanuwansa da ya aminta dasu.... Wasu hawayen masu d’umi suka kuma gangaro mata sanda Fu’ad Ke ci gaba da fad’in “Ga mamakinmu Yazeed ya amsa masa bai masa gardama ba, yace ya jeshi babu matsala shi zai kula damu gaba d’aya... Bayan tafiyan Yaya Jakadiya Ta cimma Yazeed da sak’on Giwa kan cewa a daren ranan zamu yarinya muyi mata fyad’e mu dukanmu uku idan har munaso mu tsira da mutuncin gidanmu... Yazeed ya sanar da ita cewa anyi an gama... Dan koda Jakadiya Ta tambayesa ina za’a sami yarinya cikin daren nan sai ce mata yai akwai yarinyar da suke tafe da ita.... Jakadiya tace hakan yayi su tabbata sunyi yanda aka umarcesu... Ta bada garin magani ma Yazeed kan cewa duk wanda yazo amfani da ita cikinmu sai ya Shafa a al’aurarsa kaman yanda malamin Giwa yace... Muna jin sautin murya ana k’walla kiran suna SAUDATU alamun ahalinta na nemanta, kafin tayi yunk’urin amsawa Yazeed yai saurin rufa mata alkyabbansa akanta ya toshe bakinta ya janyota muka shige wani lungu nan bayan masarauta.... Jamal wanda shima da alama yasan abinda Ke wakana shi ya d’aure idanun yarinyar da k’yalle duk ihu da birgima da take.... Abinda ban tab’a gani ba shi ya faru gaban idanuna... A gabana Yazeed ya lalata rayuwar yarinyar cikin wulak’anci da cin zarafi.... Bayan ya gama Jamal ma yayi... Ina kuka ina sanar dasu ni k’aramin yaro ne haka suka tirsasa min shafa wanann garin maganin a al’aura na abin mamaki kuwa sai ji nayi ina matuk’ar son kasancewa da mace... Nima nabi sahunsu... Muka wulak’anta k’aramar yarinyar da Yaya ya bamu amanan cewa mu kaita ga iyayenta.... Koda muka gama sai k’arasowa Jakadiya Tai ta d’auki yarinyar wacce ko numfashi batayi tace kar mu damu bata mutu ba ita zata kula da ita, a cewarta ita zata Kai yarinyar ga iyayenta Ta sanar dasu an tsinceta an mata fyad’e.... Nidai tindaga wanann lokacin kuka kawai nake bansan meke faruwa ba, umarni kawai suke bani sai ganin dogari guda biyu nayi Yazeed da Jamal suka janyoni muka bi bayan dogaran... Ina tambayarsu Ina Yarinyar... Jakadiya ta Kaita gida..? Sai ce min sukai eh Jakadiya takaita ga iyayenta... Kuma yanzu zamuje ne mu tabbatar da hakan... Hakan yasa nabi bayansu muka k’arasa wani gidan wanda gidansu Yarinyar ne.... Dogaran su suka sanar da mutumin cewa anyiwa d’iyarsa fyad’e tana can asibitin bayan Fada yazo ai masa rakiya yaje ya ganta... Mutumin ya kame k’irjinsa yana salati... Ashe Jakadiya na biye damu amma babu yarinyar a tattareda ita... Tanayi tozali da mutumin mukaji Ta ambato sunansa... Tace Saudatu d’iyarka ce....??! Mutumin ya zaro idanu waje bai iya bata amsa ba... sai gani nayi ta juya cikin sauri ta janyo Dogari guda sunyi magana... Dogarin yana dawowa baiyi wata wata ba ya zaro Takobi da niyyan cire kan mutumin ni kuma nai k’ok’arin kare mutumin Jamal da Yazeed suna k’ok’arin janye ni... Ina fad’i masu bazai yuwu munaji muna gani mu bari a kashe bawan Allahn nan ba bayan cin zarafin da akayiwa d’iyarsa wacce bamusan yanayin da muka barta ciki ba... Yazeed yana janye ni yana yunk’urin hanani saiga wani mutumi ya fito daga cikin gidan Dogari guda ya cakka masa Takobi a ciki... Nayi k’ara na finciko Takobin dake d’amaran d’aya Dogarin nayi k’ok’arin kare Mahaifin yarinyar saidai tuni k’addara ta riga fata ainka da k’aramin yaro Takobin yamin nauyi sosai ban ankare ba sai ji nayi na sare k’irjin mahaifin yarinyar da takobi b’angaren da yake rik’eda tin sanda Labarin fyad’en ya isa masa.... Na saki wane irin k’ara a wajen na kama kaina dake tsananin bugawa, take na zube wajen ban farka ba saida naji d’umin zafin wuta da sautin k’onewar abubuwa, turirin hayak’i shi ya tadani... Naga gidan su yarinyar nata faman ci da wuta... Na yunk’ura zan fad’a cikin gidan Ina mai sanar dasu Yarinyar da mahaifiyar na cikin gidan mu taimaka masu... Yazeed ya janyoni baya ya kikkifa min mari masu zafin gaske yace yarinyar da mahaifiyarta sun mace cikin gidan wuta ya cinyesu, nima idan na shiga saidai nabi sawunsu.... Haka Ina kuka suka janyeni muka nufo Fada Giwa da Jamal suka kafa min warning kan cewa babu abinda ya faru idan kuma nayi gigin sanar da wani fa abinda ya faru zan mance cewa ni ahalin gidan ne musamman Yaya Mahmood wanda ake shirye shiryen bikinsa a lokacin....!! Shin Ta yaya zan iya yafe wa kaina wannan babban laifi wanda muka aikata... Ki fad’a min Muhibbah..!!” Ya k’arashe cikin tsananin kuka... Itama d’in kuka take sosai... Tabbas farkawa kawai tai ta ganta a wani d’aki a kulle ga wani tsohon mutumi kaman maye yanata zagaye kanta da jan k’yalle yana maganganu marassa dad’in sauraro... Ganin haka yasa tai likimau dukda azaban da takeji wanda bata tab’a jin irinsa ba... Hankalinta bai gama tashi ba saida taga wannan tsinannen halittan ya duk’a ya bud’e k’afafunta yana katsan wani abu a al’auarta ga tsananin zafi da zogi mai d’imautarwa da takeji har k’wak’walwan kanta.... Ta kuma rintse idanunta dan hawayen ma sun daina fitowa... Tana jin sanda tsohon mai k’irar abin tsoro ya mik’e ya fice rik’eda k’ok’on da ya gama katse jinin dake fita daga al’aurantar a hannunsa... Ta hango sararin waje daga yanda take kwance cikin d’akin mai tsananin duhuwa... Dukda azaban da takeji hakan bai hanata furta Basmala ba ta karanto ayatul kursiy ta karanto falak’i da nasi... Cikin wane ikon Allah yunk’urin da zatai sai ji tai Ta mik’e zunbur... _Laa ilaha illa Anta subhanaka inni kuntu minazzalumin_ Shine addua’an da harshenta keta nanatawa... Tafiya kawai take ba tareda tana ganin hanya ba take kuma nanata addu’an... Tabbas taji ana kirawo sunan ya da wani irin sauti amma wannan addu’a bai bar saman harshenta ba, duk razanata da ake da abubuwa na ban tsoro bakinta bai daina karanto wannan addu’a ba har saida Ta bud’e idanu Ta ganta a wajen Masarautar... Sai lokacin zafin ciwowwukan dake jikinta suka kuma dawowa ga busasshen jini dake bin k’afarta... Wato ashe Jakadiya ita ce ta kaita ga wannan matsafin mutumin data farka ta ganta gabanshi.... Ashe Mahmood baida laifi hasalima baisan komai ba... Ta zalunci bawan Allah ta had’asa fad’a da d’iyarsa... She needs to stop Zahra tun kafin lokaci ya k’ure... Muryar Fu’ad ne ya dawo da ita daga duniyar tunaninda ta tafi yanda yake fad’in “Baya duk abubuwan da kikaji gamedani nasan bazaki tab’a sona ba Muhibbah... Will you still accept me...?!” Wani irin duba take masa da idanunta masu zuban hawaye, tsanarsa na kuma ratsa zuciyarta lokaci guda take furta “Ka cuceni Fu’ad... Kasa na fara soyayya dakai... You’re a Criminal, I’d never love someone like you... Never, ka mance ka tab’a soyayya da wata mai suna Muhibbah... I hate you.. Na tsaneka Fu’ad, bazan tab’a soyayya da criminal irinka ba... Kuma kasan meye.. Hauka shi ya cancanceka bayan abinda kukayiwa yarinyar can da ahalinta... Ina fata ka tabbata cikin hauka Fu’ad, kada Allah ya kawo rananda zaka warke..!!!” Tana kaiwa nan ta mike ta fice a guje tana kuka sosai, kukanda batasan na tausayin kanta bane ko na tausayin Mahmood ne wanda baida laifi ko k’ank’ani cikin duk abinda ya faru da ita... Cikin wane irin k’ara Fu’ad ya k’walla mata kira yana mai kuma tamke kansa dake ci gaba da sara masa... Lokaci guda ya shiga tattaran pills d’in da baisan adadinsu ba yana turawa cikin bakinsa.....Take ya zube a wajen rik’eda kansa tamkar maras numfashi... Gudu kawai take cikin Masarautar tana addu’an cimma Zahra Ta tareta kafin Ta isa babban Zauren Taro Ta tozarta Mahmood... Saidai tana isowa ta hango Zahra ta fito daga Zauren a guje tana kuka sosai... Tana hango Muhibbah ta fad’a jikinta tana mai kuma fashewa da kuka... Take Muhibbah ta rungumeta hawaye masu tsananin zafi na gangaro mata... Tabbas d alama ta makara Zahra ta riga ta yarfa Mahaifinta cikin d’imbin jama’an Masarauta... D’ago idanun da Muhibbah zatai suka had’a ido da Mahmood wanda fitowarsa kenan daga parlorn ya biyo bayan Zahra... wasu irin kwantattun hawaye Muhibbah ta hango cikin idanunsa wanda ko ba’ace ba jarumta ne da tsananin k’arfin hali suka hanasu zubowa..... SameenaAleeyou 📚 [8/14, 10:58 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *45* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Hawaye ne suka ci gaba da gangaro mata su biyun suna duban cikin idanun juna, Ta kasa janye idanunta daga barin dubansa ta kuma kasa sakin Zahra dake shesshek’ar kuka saima dad’a matse Zahra da tai cikin jikinta hawaye masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata.... Tana ganin sanda Mahmood yasa kai ya fice daga wajen baki d’aya Turaki na biyedashi... A hankali ta lumshe idanunta wasu hawayen na kuma gangaro mata tsananin tausayin Yarima Mahmood da d’iyarsa cikin zuciyarta... Zahra ta d’ago tana dubanta, cikin kuka take fad’in “Dan Allah ki fitar dani daga Masarautar nan wllhi banson zama a nan... Na gaji na gaji da rayuwa cikin gidan nan... Dan Allah ki fitar dani daga gidan nan..!” Kuka yaci k’arfinta.. Muhibbah tai saurin rungumo kanta cikin k’irjinta cikeda tausayawa, cikin tsananin rawar murya take furta “Everything will be ok Zahra.. Ki kwantar da hankalinki kinji komai zai shige ya zama tarihi... Zo muje you need to rest..!!” Bata jira amsar Zahra ba ta janyeta suka nufi Fadar Giwa... Har lokacin jikin Muhibbah a matuk’ar sanyaye yake... Suna tafe suka hange Zuhra da Raheema harmada Umaima hankali tashe sun fantsama cikin Masarauta dan da alama labarin abindake faruwa ya gama karad’e cikin Fada... Muhibbah tana hangosu Ta kuma janyo hannun Zahra had’ida canza masu hanya cikin sauri dan bata fata ta had’uda kowa cikin Masarautar a halinda Masarautar Ke ciki.... Gaba d’aya ranan Masarautar a yamutse take abubuwa ne da dama suka faru gashi uwa uba an nemi Mahaukaciya Izzatu cikin Masarautar an rasa... Neman duniyar nan anyi an rasa yanda Ta shige... Ga Jamal kwance rai hannun Allah kan kace mai dafin jikin Takobin da Majidad’i ya sara masa a k’afa tasa k’afar tayi bak’ik’irin tamkar ba’a jikinsa yake ba, shi kad’ai yasan azaban da yakeji... Cikin gaggawa aka nufi asibitin koyarwa dashi koda wani abinda za’a iya dan da alama cikin sakanni dafin Ke haurawa jikinsa kaman wani Saran bak’in kumurcin maciji, gaba d’aya k’afar ta sauya halitta ta koma tamkar bak’in gawayi Dukda kuwa hasken fata da Jamal kedashi..... Duk wannan hali da ake ciki babu wanda yasan Fu’ad yana kwance cikin d’aki yana aman farin kumfa sakamakon drug overdose da yai... Tashin hankali ne dai wanda ba’a saka masa rana kowa cikin Masarautar hankalinsa a tashe yake.... Dole Mahmood da Turaki ma suka nufi asibitin koyarwa dan sanin halinda Jamal Ke ciki Dukda kuwa tashin hankali da shi kansa Mahmood d’in yake ciki bayan abinda d’iyarsa Zahra tai masa a bainar jama’an Masarauta.... Shi kuwa Yazeed tinda ya samu ya kub’uta daga hannun Majidad’i babu wanda ya kuma sakasa a ido dan tin lokacin yai ficewarsa gaba d’aya daga cikin Masarautar, bai zarce ko ina ba sai club d’in da suka saba had’ewa da watsattsun abokansa... Tinda ya isa wajen kuwa banda kwankwad’an Barasa baya aikin komai, harta abokan nasa saida suka razana da irin giyar da Yazeed Ke zubawa cikinsa... Bai masu magana ba bai ce masu komai ba tinda ya isa wajen shan barasa kawai yake ko zai mance tashin hankalin da ya baro cikin Masarautar su... ** A b’angaren Muhibbah kuwa bata k’yale Zahra ba daidai da dak’ik’a guda, har saida bacci ya d’auki yarinyar, tai zaune a gefenta tana duban fuskarta cikeda tausayawa, taita tuna abubuwa da dama gameda yarinyar da mahaifinta tin farkon zuwanta Masarautar... Hoton Zahra rungume da Mahaifinta dake gefen bedside Muhibbah ta d’auko tana kallo hawaye tab idanunta, tasa hannu a hankali tana Shafa hoton hawayen na zirarowa daga idanunta... Ta lumshe idanunta a hankali sanda taji kuka mai k’arfin gaske na zuwa mata, a hankali Ta maida hoton yanda ta d’auko kana Ta fice daga d’akin cikin sauri... Masauk’inta ta tafi ta shige k’uryar d’aki ta fad’a saman gado tana shesshe’k’ar kuka mai tsuma zuciya... Tana ganin kiran Ansar na shigo mata amma sam bata iya d’agawa ba sai kuka dake kuma kufce mata mai ban tausayi.... Kaman wacce aka sinkaya ta mik’e ta soma shiri... Kayanta ta shirya cikin akwati da zimmar Washe gari idan Allah yakai rai asubahin fari zata d’auki hanyar Bauchi... ** Babu yanda Mahmood baiyi ba Giwa ta koma masarauta amma fir tak’i tace bata barin cikin asibitin har sai likitocin da suka shiga aiki ma Jamal sun fito sun sanar da ita d’anta is stable, daga ita har Jakadiya sai faman kai komo suke, tana tafe Jakadiya na take mata baya sauran Hadiman nata na risine daga gefe... Mahmood da Turaki harmada Waziri suma duk suna gefe suna jiran fitowar likita... Jim kad’an likitan ya fito ya nufosu, sukai masa chaa suna jiran ta bakinsa.... Da hak’uri likitan ya soma masu, Giwa ta shiga girgiza kai tana fad’in “Likita bana son jin irin wad’annan kalaman, ka bud’e baki ka sanar dani halinda d’ah na Ke ciki...!!” Dogari guda ya bud’e murya yace “Hattara Bokan Turai, Giwar Amale bata jiran amsa daga bakin Talakawanta....!!” Likita yai gyaran murya yace “Prince is stable now....But there’s something in his life that would remain irreversible... I’m sorry to say we did everything we could ganin gubar batai tasiri cikin jikinsa ba, a dalilin haka... we had to amputate his leg... Da ace bamuyi gaggawan cire k’afar ba tabbas da gubar ta haura zuwa zuciyarsa wanda hakan ka iya kawo sanadiyar mutuwarsa....!!” Kuka ya kufcewa Giwa yayinda Mahmood ya lumshe idanunsa a hankali, yai saurin k’arasawa ga Giwa yana bata baki... Ya dubi likitan yace suna iya ganin Jamal... Likita ya jinjina kai yace “We’re moving him to the resting room in a bit... Zaku iya shiga can ku gansa Your Highness... Excuse me...!” Ya k’arashe yana mai shigewa... Yarima Mahmood ya janyo hannun Giwa da har lokacin bata koma daidai ba ta k’asa yarda Wai Jamal d’inta ya zama mai k’afa guda, haka suka nufi d’akin da aka kwantar da Jama cikin matuk’ar sanyin jiki.... Giwa tana hango Jamal kwance da yankakken k’afa Ta rintse idanunta tana k’ok’arin danne kukan dake zuwa mata, Ta k’arasa jikin gadon tana shafa k’afar nasa take fad’in “Jamal d’ah na..!!” Tsananin rawa da muryarta keyi ya hanata ci gaba da magana... Mahmood ya tsaya daga d’aya gefen yana duban d’an uwan nasa cikeda tausayawa... A hankali Jamal ya bud’e idanunsa yana dubansu, lokaci guda ya yunk’ura zai tashi yaji tamkar babu k’afarsa guda a jikinsa... Yai saurin kai hannunsa maras cannula dan tabbatarwa ai kuwa babu k’afar an cire... Cikin tsananin tashin hankali yake furta “No no no no... This can’t be happening... Maami what’s going on... Where’s my leg... I want my leg back... Tell them to bring me back my leg...!!” Mahmood ne yai saurin dafasa cikin k’ok’arin bashi baki “Calm down please Jamal, everything will soon be alright kaji, just calm down kaji d’an uwana... Bayan takobi mai guda da Majidad’i ya sara maka is a miracle you survived... Ka gode ma Allah kaji da ya k’addari cewa akwai sauran rayuwa gaba gareka...!” Cikin zuban hawaye Jamal Ke fad’in “Yaya shikenan na zama nakashashhe... Yaya ka dubeni fah ka gani... Ka dubi halinda nake ciki you could you except me to calm down...! I shouldn’t be in this position, maiyasa na karb’i fad’an Yazeed wanda shi bazai min haka ba... He should be the one here not me...!” Mahmood yai saurin dafasa yana mai girgiza kai yake furta “Kar kayi magana haka Jamal kai musulmi ne kuma nasan ka yarda da K’addara mai kyau ko akasinta... Wannan itace k’addararka Jamal, koda ace Yazeed bai zama sanadi ba kasa a ranka hakan zai sameka... Bawa baya wuce k’addararsa kaji koh... Kayi fatan Allah ya baka ikon cinye wannan jarabawa taka...!” Jamal da hawaye Ke gangaro masa k’uri yayima Mahmood yana dubansa lokaci guda yake furta “Yaya... Yaya I’m sorry... Please forgive me...!!” Mahmood ya dubesa da mamaki yace “Jamal mai kai kake neman afuwa... Ni baka mun komai ba...!” Wani irin duban da Giwa ta aikawa Jamal ya sanyashi lumshe idanunsa a hankali daidai lokacinda wayar Mahmood d’in ta soma ruri... Excusing kansa yai ya fice amsa kiran dan da alama daga masarauta ake masa kiran... Mahmood na ficewa Giwa ta dubi Jamal tace “Koda wasa kada kayi gigin sanarda Yayanka wani abu... Koda wasa Jamal...!” Jamal na hawaye yake aika mata wani irin muguwar kallo da rinannun idanunsa, lokaci guda yake furta “Maami zunubaina ne suke bibiyata, shiyasa na tsinci kaina a halinda nake yau, na tabbata hakkin wannan yarinyar da duka ‘yanmatan da na lalatawa rayuwa suke bibiyata.... Wanda Duka ke kika umarceni kan son mulkin banza wanda ba tabbata zai ba....Yau ga halinda na tsinci kaina ciki...!!” Saurin toshe bakinsa Giwa tayi tana fad’in “Rufe bakinka Jamal, duk abinda kayi sadaukarwa ne ma gidanku da ahalinka... Kuma abinda ya sameka ba laifin d’an uwanka Yazeed bane kaima ba laifinka bane laifin wancan tsinannen mahaukacin ne kuma nayi imani sai ya biya abinda ya aikata... Dan haka koda wasa kada na sake jin maganganu irin haka daga gareka...!” Banda aika mata mugun kallo Jamal baya komai, lumshe idanunsa yai wasu hawayen suka kuma gangaro masa Mahmood ne ya turo k’ofa ya shigo, yanayin da suka gansa ciki sosai ya kuma firgitasu.... Giwa ta tsaresa da ido tsoro bayyana saman fuskarta, duk a nata zaton yaji tattaunawarsu da Jamal ne.... Ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Sadauki lafiya na ganka haka...?!” D’an satan kallon Jamal yai yaga idanunsa a lumshe suke kana ya matso kusan Giwa yai mata rad’a a kunne... K’unshe bakinta tai ba tareda ta iya furta koda kalma ba duniyar na neman juye mata... Mahmood ya isa ga Jamal dan baiso hankalinsa ya kuma tashi a condition d’in da yake ciki... D’an dafasa yai kad’an yace “We’d be around idan kana nemanmu, for now Likita yace ka sami hutu kaji...Akwai dogari guda da

Chapter 28 of 65