tattare da shi... Allah Ubangiji ya tsareki ya kareki ya kuma dafa miki...!”
Ta amsa da “Ameen Baba, kuma kuyi sauri ku d’auki hanya kafin wani abin ya faru...!”
Ta maidoda dubantaga Izzatu wacce ta kasa janye idanunta daga barin dubanta, ta tako har gabanta a hankali kana Ta kamo hannayenta ta rik’e cikin nata, saida ta sakar mata murmushi mai kyau kana tace “Kin tsira da izinin Allah... Babu wanda zai kuma azabtar dake...Ku tafi cikin aminci da kariyar Ubangiji..!”
Mahaukaciyar ta sakar mata murmushi itama kana tasa hannu ta shafi Fuskar Muhibbah, tai wani magana da bazaka iya fahimta ba sabida rashin wadataccen harshe cikin bakinta....
Ubandoma ya dubi Izzatu yai mata alama da hannu kan cewa su tafi kada a cimmasu.... Ta kuma duban Muhibbah kana ta k’araso ta rungumeta sosai cikin jikinta... Hawaye suka gangaro wa Muhibbah da k’yar suka raba jikinsu itada Izzatu ko damunta daud’an jikin matar baiyi ba...
Bata bar wajensa saida ta tabbata sunyi nesa da Masarautar kana Ta juyo tana k’arewa Masarautar kallo daga nan yanda take tsaye....
Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tasa kai ta soma tafiya ta bayan Fada dan bazata iya komawa Ta hanyar da Ubandoma yabi dasu ba...
Ta k’ofar bayi ta b’ulla hakan yasa kawai tabi wannan k’ofar ta shige cikin Masarautar Allah yasa dama tun shigowarta Kuyanga guda ta amshi jakan kayanta ta kai mata masauk’i...
Kai tsaye sashen Giwa ta nufa b’angaren su Umaima da Zahra...
Nan ta tadda Zahra na sharb’an kuka Umaima na bata baki..Tsaye tayi tana sauraren abinda Zharan Ke fad’i “Wllhi Anty Umaima na tsane matar nan na tsaneta Ta ya Paa zaice zai aureta... Of all mata ya rasa wacce zai d’auko sai wannan matar... Wllhi ban sonta kuma bazan tab’a sonta ba....!”
Umaima ta dafata tace “Zahra Raheema batada matsala kece dai baki sonta, Aminiyar Aunty Zuhra ce fah kuma kiga yanda kowa yake yabon kirkin Aunty Zuhra cikin Masarauta nan... Ki kwantar da hankalinki kiyi addu’an Allah yasa haka shine mana alkhairi gaba d’aya..!”
Galala Zahra Ke dubanta kana ta kuma goge hawayenta tace “Ni nasan yanzu Paa bai sona bai damu da abinda nake so da wanda bana so ba, yanayin haka ne kawai dan ya k’untata min sabida ya daina sona, He’s changed now, and he’s becoming more violent har marina yayi abinda bai tab’ayi ba a baya, he really is hiding something from me...But if not for that maiyasa zaice zai auri matar nan all of the sudden..!”
Umaima ta nusa tace “Zahra neman izinin auren suka tafi ba auren ba, watak’ila ya sauya ra’ayi idan har baki sonsa da ita...!”
Ji tai bakinta ya bud’e tana furta “Rankaidad’e ne ya tafi neman izinin aure..?!”
A tare suka juyo suna dubanta, Zahra ta tafi da gudu ta rungumeta “Tiaaa..! I’m glad you’re finally back, you’ve no idea how badly I need you right now... You’re the only one who understands me after all..!” Tai maganan tana mai tab’e baki har lokacin bata saki Muhibbah ba...
Muhibbah ta k’ak’aro murmushi tace “I’m here now... Tell me meke faruwa... Naji kuna maganan saka Rana....!” Tai maganar cikin yanayi na yak’e...
Zhara baki ture tace “Can you believe my Pa, ya tafi neman auren wannan witch d’in... Wai aurenta zai very soon..!”
Umaima ta katseta da fad’in “Ba da wannan zamu fara ba, da gaisuwa ya kamata mu fara kafin komai ya biyo baya...” Ta dubi Muhibbah tace”Sorry Zahra ta tareki da zance babu ko gaisuwa balle sannu da zuwa..”
Murmushin da yafi kama yak’e ta kumayi kana tace “No is alright, after all ni na tambaya...Ya kuke...? How are things here...?!”
Tai maganar tana mai janyo hannun Zahra suka zauna saman couch...
Zahra tace “Um ba wani abu mai dad’i da ya auku a nan tinda kika tafi... Koda yake akwai abu mai dad’i guda d’aya... An sallami Uncle Jamal daga asibiti... And guess what..!” Ta k’arashe tana duban Umaima cikeda zolaya taci gaba da fad’in “Anty Umaima said yes to him... They’re getting married anytime soon... At least auren da mukeso ba irin na Paa da wancan witch d’in ba..!” Ta k’arashe tana kashewa Umaima idanu, itakaw Umaimar sai k’ok’arin toshe bakin Zhara take su duka biyun suna dariya...
Gaban Muhibbah ya kuma yankewa dan tasan sam Umaima bata dace da Jamal ba, ita d’in mutumiyar kirkice shi kuwa akasin haka, kaman yanda Mahmood bai dace da Raheema ba, shid’in mutumin kirki ne itakaw akasin haka....
Zahra taci gaba da zolayan Umaima, Umaimar na kuma janyota tana toshe bakinta tana fad’in zata had’ata da Uncle d’inta... Sai dariya suke cikeda nishadi yayinda Muhibbah tai nisa duniyar tunani... Ta yaya zata hana yuwar wad’annan auratayya...? Kaman daga sama ta sinkayo Umaima na fad’in “Hibbah sorry bamu tambayi jikin Mommy ba, kuma tinda kika tafi baki had’amu a waya ba, shi Dr kam ma ban samun layinsa...”
Jiki a sanyaye Muhibbah ta murmusa tace “Jikinta da sauk’i sosai shisa na dawo....!”
Sukai mata addu’a gaba d’aya Muhibbar tana amsawa da Ameen cikin tsananin sanyin jiki...
Gajeren hira sukai Muhibbah tace zata masauk’i ta d’an huta gajjiya...
Zahra tace zata shigo anjima kafin la’asar... Da kai kurum ta amsa mata amma ta kasa aminta da abinda taji...Wai Rankaidad’e zai auri wannan Trap d’in wacce Ta gama watsewarta da wancan watsattsen k’anin nasa... Inaa no she can’t allow him to fall into her trap, but ta ya zatayi haka... Ta yaya zata bud’e idon Rankaidad’e ya gane wanan matar ba k’aunarsa take ba..? In fact su biyu d’’in duniyarsu Ta banbanta....! Amsar data kasa nemowa... Alolan sallan la’asar tai kana Ta d’an kishingid’a saman gado idanunta na kallon sama, sai faman sak’e sak’e take cikin zuciyarta... Allah ya gani ta k’agu taga ya dawo Masarautar yace ya fasa auran Raheemah ko hankalinta zai kwanta...
Tana nan a haka bacci yayi gaba da ita....
**
Wane irin k’aik’ayi ne na bala’i ya addabeta lokaci guda, ga b’arin kanta yanda sumar suka k’one sunayi ga kuma hannunta k’onanne da shima ya addabeta da k’aik’ayin.... K’aik’ayi ne mai fidda hayak’i wanda ba kowa Ke iya ganin hayak’in ba face ita da abin Ke jikinta.... Tun tana Susa a cikin kallabi hardai Ta cire kallabin tayi wurgi dashi.... A baya susa ba girmanta bane a matsayinta na mai jida mulki da izza sai gashi yanzu Susa na nema ya zama babban d’abi’arta.... Ko dan sabida yawan k’aik’ayi dake addabanta bata fita fadarta cikin mutane.... Yau d’inma a d’aki suke itada Jakadiya taketa faman soshe soshen, k’arshe ta umarci Jakadiya ta sosa mata kanta ita taji da hannunta....
Abin yayiwa Jakadiya banbarak’wai Giwa da susa babuji babu gani....
Jakadiya tace “Allah shi taimakeki Susa ba girmanki bane.... Anya wannan k’aik’ayi naki ba ture bane... Kodai asibiti za’a tafi....!”
Giwa ta katseta da fad’in “Ni Turai nafi k’arfin wani yayo min ture.... Nasha gaban kowa a tsafi, ni nakeda Tal’udu mai Fitilar tsafi...Ni nake turawa badai a turomun ba, kaman yanda na sace Sarautar Izzatu, da rayuwarta data cancanta na kuma guntule harshenta yanda bazatayi magana ba balle wani ya d’auki muryarta sannan na manna mata ciwon hauka daga k’arshe....Na kuma rabata da yaranta da duk wani dangi nata.... Kinga dai yanda nayi da Yarima Alfah da yaransa guda biyu da matansa guda biyu da ya taso har k’asar nan ya biyo sawun ‘yaruwarsa a lokacinda labari ya cimmasa cewa na maida Gimbiya Izzatu baiwa na maye Gurbinta da kaina...!”
Jakadiya Ta had’iyi miyau da k’yar tana jinjina ta’addanci irin na Giwa... A iyaka zatonta Izzatu Hadimarta ce aminattciya dataci amanarta ta aure Sarki AbdulJabbar bayan Giwa ta mallaka masa ita a matsayin tukuici ashe abin ba haka bane... Ashe Giwa Itace Hadimar Izzatu wacce Ta aminta da ita taci amanarta ta sace sunanta da rayuwarta harma da mijinta... Jiki na matuk’ar rawa Jakadiya ta soma jada baya tana duban Giwa cikeda tsoro...
“Rankidad’e Ki gafarceni amma ta yaya akayi haka....?!”
Giwa ta murmusa tace “Kar kiji tsoro Jakadiya nidake mun zama d’aya... Kinsan sirrikana da yawa... Yau zan sanar dake Sirrin da dagani sai Tal’udu saiko Marigayi Wambai ne muka sani... Sirrin da Wambai ya rufeta cikin K’undi...!”
Jakadiya dake rakub’e gefe har lokacin jikinta bai daina rawa ba take duban Giwa....
_WAIWAYE_
Gimbiya Turai d’iyace ga Sarki Jamaludeen na k’asar Benin, su biyu rak Allah ya baiwa Sarki Jamal... Daga ita sai k’aramin k’aninta mai suna Alfah... Sarki Jamal ya d’auki soyayyar duniya ya d’aura akan yaransa guda biyu Gimbiya Turai da kuma Yarima Alfah... Mahaifiyarsu ta rasu a lokacinda ta haifi Yarima Alfah, daga nan Sarki bai kuma haihuwa ba... Hakan sosai yayi dad’i ga Al’umman masarauta dake harin kujeran Sarki Jamal....Gimbiya Turai tanada wata Hadimarta wacce suke kusan s’anni saidai idan ma Hadimar tata zata d’ara mata bai wuce ta d’arata da Shekara d’aya zuwa biyu ba... Gimbiya Turai Allah yayita mace mai sauk’in kai da son Al’ummarta hakan yasa itada Hadimar tata mai suna Izzatu suka zamto aminai daga amintaka suka koma tamkar ‘yanuwa wanda suka fito ciki guda... Gimbiya Turai bata b’oyema Izzatu komai nata... A lokacinda d’an Sarki Mahmood Wato Sarki AbdulJabbar yaji labarin Gimbiya Turai na k’asar Benin... Al’adar k’asar ce a wancan lokacin Gimbiya bazata fita zance wajen manemin aurenta ba sabida mulki saidai Hadimarta ta fita suyi hira da mijin ita Hadimar sai ta kawo sak’on duk abinda aka fad’i a hiran ta gayawa Gimbiya... Kuma Hadimar idan ta fita itama bazata bud’e fuskarta ba har a gama hiran... A tak’aice miji bazai San fuskar matarsa ba sai randa aka kai masa ita gidansa...!”
Giwa Ta numfasa kana taci gaba da fad’in “Tun daga wannan lokacin da nayi shiga irinta masu mulki na rufa kaina na fita wajen Sarki AbdulJabbar a matsayin wacce ta fito ganawa da mijin da zata aura sai na d’and’ani zak’in mulki naji duniyar nan babu abinda ya kaita dad’i ashe... Ina can ina bauta... Uwa uba da na k’yallara idanu kan kyakkyawan Sarkin maiji da k’uruciya da Mulki naji duniyar nan bazan iya rayuwa ba taredashi ba... A lokacin mahaifin AbdulJabbar ya rasu za’a nad’asa sarauta akace sai yayi aure ai masa nad’i gaba d’aya... Hakan yasa yayi tattaki har Benin dan lokacin Sarki Jamal yayi sanarwa k’asashe daban daban cewa d’iyarsa zata zab’i miji, aka saka wa masu Mulki rana kowa yazo ya nuna bajintarsa... Toh koda yaran sarakuna da masu mulki suka Zo wannan gasa na zab’en gwani da Gimbiya Turai zatai Sarki AbdulJabbar bai sami halarta ba baida lafiya... D’anuwansa Wambai shi ya halarta a matsayin wakilin k’aninsa... Anyi gasar gwani Wambai yaci gasa yace ma Sarkin k’asarsu yaci wannan gasa kuma d’an uwansa... Wambai shi kad’ai yasan fuskar Gimbiya Turai ya dawo gida da labari mai dad’iga d’anuwansa Sarki AbdulJabbar... “
“Koda aka d’aura auren Sarki AbdulJabbar da Gimbiya Turai bata buk’aci a kawota wannan Masarautar da tarin Hadimai ba, a cewarta ni kad’ai na isheta.... Al’ada ce a wancan lokacin Matar Sarki bazata iso masarauta ba sai ta yada zango a wata k’aramar gari kafin Ta iso masarauta.. Hakan Ta faru damu... Nida Uwargijiyata Gimbiya Turai matar AbdulJabbar, Wambai wanda shine tsaye akan komai na auren d’an uwan nasa tin a lokacin na hango hassada da k’yashin d’aukaka da Allah ya baiwa d’an uwan nasa sama dashi, nayi amfani da wannan damar na rinjaye Wambai tinda shi yaje gasa shikadai yasan fuskar Gimbiya Turai Sarki AbdulJabbar bai sani ba... Muka had’e kai dashi cewa ni ce zan zamto matar AbdulJabbar da sharad’in zan taimaka masa mu kawar da AbdulJabbar ya d’ale Karagan mulkin mahaifinsu wanda shi ya kamata ya gada amma aka baiwa AbdulJabbar, naita gurb’ata masa zuciyarsa da tunani marassa kyau har na samu nasaran shawo kansa....A wannan garin na fantsama wata daji neman maganin da zan rufe bakin Gimbiya Turai, a nan na had’u da Tal’udu ya sanar dani banida matsala... Tal’udu ya zamto gatana, ya tura bak’in Aljani ya kashe Sarki Jamal na k’asar Benin Wato mahaifin Gimbiya Turai... Daga nan Gimbiya ta zamto batada kowa sai k’aramin k’aninta Alfah wanda shi a lokacin k’aramin yaro ne baida ko masaniyar Sarkin wata k’asa ce ya auri ‘yaruwarsa sabida k’ank’ancin shekaru nasa, yadai an gasa akai wani Sarki ta k’asashen gabas yaci gasar amma bai San wace k’asa bace....Tuni masu wawoson mulki sukai ma k’aragar mulkin caaa, aka mance da Alfah da ‘yaruwarsa Turai...
Saidai tin kafin na tareda Sarki AbdulJabbar Gimbiya Turai ta riga ta basa ni a matsayin kyauta, Wanda dama al’ada ne kyauta tsakanin sabbin ma’aurata, ka d’aga abu mai daraja ka baiwa partner d’inka... Toh ita sai ta basa baiwarta Izzatu a matsayin tukwici, labari ya isa masa daga wajen Wambai... Randa za’a kawoni masarauta ranan muka gana dashi dan tuni Tal’udu ya rufe bakin Gimbiya Turai duk abinda na bata umarni shi takeyi, haka nan mace da ita daga wancan lokacin itace Izzatu Hadimata ni kuma nice Uwargijiyarta Gimbiya Turai... Sadai ta sami kanta da amsa min da min biyayya dan bazata iya ce min a’a ba... Kallon farko ashe Sarki ya auka wa soyayyar Baiwa Izzatu....Sarki AbdulJabbar yabada umarnin a k’arasa dani Masarauta ita kuma Baiwar a bar masa ita a nan wannan garin zasu k’araso tare... Haushi da takaici ya cikani ta yaya gani nan sabuwar amaryarsa ya zab’i ya taho tareda Kuyanga... Na dad’a k’ullatan Turai wacce itace Izzatu a halin yanzu, na tsaneta da duka zuciyata dukda na sace identity nata da komai amma da alama Sarki yana son k’ulla alak’a da ita... Naji takaicin basa kyautar baiwa da tayi... Ashe bayan tafiyar mu Fada Sarki ya umarci Wambai a d’aura masu aure shida Baiwa Izzatu ya kuma riga tarewa da ita yayinda ni kuma muka taho Fada na ije Tal’udu nan cikin Masarauta tareda taimakon Waziri wanda tuni mun k’ulla alak’a dashi ba tareda sanin Mai Martaba ba musamman da mai Martaban ya sanar dani cewa ya tare da Baiwa Izzatu kuma ya aureta Ta zama matarsa kaman ni..
Nace atafau Baiwa bazata tab’a zamtowa kaman ni ba, dan haka dole ya barta a wancan garin Ta zauna a can idan yana neman zaman lafiya... Ban hanasa ya auro ko wata mace ya kawota cikin Fada ba amma banda baiwata Izzatu, nafi k’arfin nayi kishi da ita... Sarki ya amince da sharad’ina musamman da ya lura da irin halarcin da nai masa na basa kyautar Baiwa wacce ya aukawa soyayyarta har takaisu ga aure...!”
K’aik’ayi ya hana Giwa ci gaba da magana... Zumbur ta mik’e taceda Jakadiya su tafi wajen Tal’udu...
Jakadiya ta zaro idanu waje tace “Allah shi taimakeki yau kuma wajen Tal’udu rana tsage tsage....?!”
Tsawa Giwa ta dirara mata tana ci gaba da susa... Babu shiri Jakadiya Ta mik’e zumbur tana furta “Tuba nake Allah shi taimakeki..!!!”
SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH*
*53*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Dariya Tal’udu yake amma wani irin hayak’i ne Ke fitowa daga cikin bakin nasa... Yai alamawa Giwa data masto kusa sosai.... Babu shiri Giwa ta matsa kusansa tana lek’a cikin k’aton tulun tsafi da yake aza mata akanta duk randa za’ai mata wani aiki... Sannan duk randa tulun yaci wuta tabbas babu nasara a aikin da za’ayi....
Giwa ta shiga girgiza kai tana furta “Tal’udu kayi wani abin amma babu ta yanda za’ayi na yarda a kuma azamin wannan tukunyar azabar.. Kaga dik yanda sassan jikina Ke k’onewa, ga azaban k’ai....!”
Batakai aya ba ya katseta da fad’in “Ke Izzatu ba’a mana gardama a nan..!!!”
A zabure ta d’ago tana dubansa jin ya kirata da sunanta na yanka... Ta had’iyi miyau da k’yar tace “Maiyasa yau ka kirani da sunana na yanka...? Tsawon shekarun da mukai tare baka tab’a yin hakan ba..?!” Ta k’arashe tashin hankali bayyane saman fuskarta...
Wata dariyar mai wani irin sauti maras dad’in sauraro ya kumayi kana ya d’auko wata fitila mai launin ja ya haska cikin tulun dashi yace “Lek’a nan..!”
Babu musu Giwa ta lek’a cikin tulun da tuni jan fitilar ya haske ciki da wane irin jan haske maras kyaun gani...
Ga mamakinta Gimbiya Turai na k’asar Benin ta gani cikin shiga irinta mulki da sarauta babu yanayin hauka a tattereda ita... Gefe da ita zaratan mazaje ne guda biyu duk sunyi shiga irinta masu mulki saidai bata tantance fuskokin mazajen ba sabida hasken fitilar dake kawowa yana d’aukewa kaman walk’iya....
Zuciyar Giwa yaci gaba da bugawa, jikinta ya d’auki karkarwa... Ta d’ago a zabure tana duban Tal’udu dake rik’eda fitilar...
Baki na rawa Giwa Ke furta “Mai nake gani haka badai Izzatu ta sami lafiya ba..? Kuma a ina take...?!!”
Ya kuma darawa a karo na biyu yace “Ai saida naja miki kunne, saida na miki kashedi kan cewar kar Ki bari Ta kufce miki...!”
A fusace Giwa Ta katsesa da fad’in “Wannan kuma laifinka ne tinda aikinka kenan ka cika min duk wasu burika na wannan dalilin yasa na d’auko ka na aje cikin Masarautar nan... Idan dukuwa bazaka cika min burikana ba zamanka cikin Masarautar nan baida amfani... Tsohon kawai..!!”
K’uri yayi mata da kannararren idanunsa kana ya murmusa yace “Bakida hurumin fitar damu daga cikin wannan gini da muka riga muka gina alk’aryarmu cikinta... Kuma tinda kikace haka daga yau na barki da iyawarki har sai ranan da kika shiga taitayinki da kyau... Abubuwa suka kuma kwab’e maki... A lokacin Ke da kanki zaki nemi hanyar alk’aryarmu Ki rasa..!” Ya k’arashe yana mai buga mata sandar tsafin akanta... Giwa ta saki wani irin k’aran azaba had’ida rik’e kanta lokaci guda tana mai rintse idanunta sakamakon ji da tai tamkar wuta aka watsa mata cikin illahirin jikinta sabida tsananin azaba... Bud’e idon da zatai ta ganta a gefen Jakadiya Tal’udu ya cillosu waje...
Jakadiya ta k’arasa da sauri tana taimakawa Sarauniyar tata, ta d’agota sosai tana tambayarta “Rankidad’e ya akai...?! Mai ya faru...?!!”
Cikin tsananin tashin hankali Giwa Ke furta “Jakadiya.. Jakadiya Ina cikin tsaka mai wuya, Tal’udu yana neman ya juya min baya...!”
Jakadiya ta nusa tace “Nifa inaga k’arfin tsafinsa ne ya soma k’arewa Rankidad’e.. Kinsan fah duk abinda yakeda rai dole yana tsufa, ilimin tsafin Tal’udu ne ya soma gushewa sabida tsufa... Rankidad’e Allah ne kad’ai mai dawamammen iko kan komai da kuma kowa, shi kad’ai ne rayayye wanda buwayarsa baya gushewa... Anya Rankidad’e lokaci baiyi ba da zamu tuba, mu nemi yafiyar wad’anda muka zalunta..!!!”
Batakai aya ba Giwa Ta katseta da fad’in “Har abada Giwa bata fad’uwa k’asa...Ke Jakadiya kin tab’a jin ance miki Giwa ta fad’i k’asa idan ba mutuwa tayi ba..!! Toh Babu gudu babu jada baya.. Babu abinda zan fasa... Da sannu zuciyar Tal’udu zata huce... Shige muje...!!”
Jakadiya da tin labarin Izzatu da taji jikinta yai matuk’ar yin sanyi a hankali ta soma takawa tabi bayan Giwa tamkar Kazan da ruwa ya shanye... Harga Allah a firgice take da Al’amarin Giwa.. Giwa ta shige duk tinaninta a baya... Suna tafe ne suka hango Jamal na dogarawa da sandar crutches d’insa, sai ‘yan waige waige alamun baiso ai noticing d’insa....
Giwa ta dakata kad’an had’ida dakatar da Jakadiya ma... Suka mak’ale gefe suna duban Jamal da hanyar da yabi... Giwa taceda Jakadiya su bi bayansa...
Sannu a hankali suka dinga bin bayan Jamal har suka shigo wani sunk’urumin waje da su kansu basusan da wajen ba cikin Masarautar...
Yana shigewa cikin d’akin suka take masa baya... Hankali tashe Jamal ya k’arasa jikin k’arfen da ya d’aure Jafar da sark’ok’i, babu Jafar babu alamunsa sai sark’ok’insa zube wajen... Hankali tashe Jamal ya duk’a yana d’aga sark’ok’in dan tabbatarwa idanunsa... Tabbas babu Jafar babu alamunsa saiko magensa da yake zuwa taredasu guda biyu a wajen suna kalatan sauran abincin da ya rub’e a wajen... Jamal ya shiga girgiza kai yana mai furta “No no this isn’t happening..!”
Juyowar da zai sukai ido hud’u da mahaifiyarsa, ga Jakadiya tsaye bayanta kanta a k’asa....Ya mik’e zumbur yana dubanta...
“Maami mai kikeyi a nan... Ta yaya har kika iya biyoni...?!”
“Ba wannan zaka tambayeni ba Jamal... Bayani zakamin meke faruwa a nan... Wanene ka ije cikin wannan waje...? Don’t tell me Izzatu ka aje tsawon lokacin nan da muke nemanta...?!”
Jamal dake asibiti a ‘yan kwanaki baimada masaniyar b’acewar Mahaukaciya Izzatu ya d’an tab’e fuska yace “Maami I don’t know what you’re talking about...!”
Giwa dake sakin huci Ta matso kusansa sosai ta kama kafad’unsa da k’arfin gaske tana furta “Jamal tell me the truth, idan ba Izzatu ka aje cikin wajen nan ba waye ka aje... Kamin magana talk to me...!!” Ta k’arashe tana mai jijjigasa...
Shaye da mamaki yake dubanta yanda tai masa wane irin damk’a tana jijjigasa da iyaka k’arfinta tashin hankali maras misaltuwa bayyane saman fuskarta...Fincika yai yana furta “Enough Maami, let me go... I don’t know what you’re talking about... For crying out loud I just got out of the hospital ta yaya zansan abinda kike fad’i...!!”
Cikin kid’ima da d’imauta Giwa Ke fad’in “Toh idan ba Izzatu ba waje ka aje cikin wajen nan..? Waye ka aje a wajen nan Jamal.. Ka bud’e bakinka kamin maganaa..!!!” Ta k’arashe cikin wane irin tsawa tana mai kuma jijjigasa...
Da k’arfin gaske ya fincike jikinsa yana mai sakin huci yake furta “It’s Jafar..!!! I kept Ja’afar here... And and I’m afraid he’s escaped...!!!”
Jiki a matuk’ar sanyaye Giwa ta sakesa tana dubansa da tsananin mamaki... Wai Jafar ya aje cikin wajen nan tsawon shekara guda harma da watanni da yayi bai cikin Masarautar ashe Yana nan Jamal d’anta ya b’oyesa...
Cikin rawar muryar Giwa Ke furta “Jafaru fah... Jafaru fah kace Jamal..? Shin ba ka sanar dani ka kashesa ba..? Mai kuma kake sanar dani yanzu..?!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
“I couldn’t kill him... As much as I wanted to kill him, I just couldn’t, bansan dalili ba but na kasa kashesa... Na ajesa a wajen nan tsawon shekara guda ina azabtar dashi Ta hanyar injecting d’insa da kuma drugging nasa da miyagun k’wayoyi...!”
Giwa dake tsaye tana duban d’an nata tamkar wacce ruwa ya shanye Ta nanata abinda ya fad’i kana ta d’aurada “Kan mai zaka ajesa a nan idan ba gamawa dashi zakai ba..?!”
A hasale yace da ita “Na tsanesa, na tsane wannan k’ask’antaccen Bawan... Especially idan na gansa tareda Umaima... Maami duk abinda nai masa it’s because of her... Zan Iya yin komai akanta... That’s how much I love her..!!” Ya k’arashe yana sakin huci...
Cikeda tsoro Giwa take dubansa, lallai ta yarda shid’in d’anta ne, zai komai kan abinda yake so kaman yanda zatai komai kan abinda take so... Jamal bai rage mata komai ba hardai zai iya aje mutum yana azabtar dashi tsawon shekara guda, can k’asan zuciyarta kuma sai taji dad’i da ya d’auko wannan hali nata ko Babu komai zai iya tsayuwa yaga ya sami abinda yake so koda bata raye ne... Saidai a halin yanzu tashin hankali ne take fuskanta tinda da alama Jafar ya gudu....
Bata ankara ba sai sinkayo muryar Jamal tai yana fad’in “Someone helped him escaped Maami, kinga hujin da akaima garun nan....!!”
Daga Giwa har Jakadiya suka k’arasa suna kallon ramin da aka huda... Jamal ya murmusa kad’an yace “Tabbas a d’akin dake gefe da wannan aka b’oye Mahaukaciyar da kike fad’i Maami... Kuma sun taimaka ma junane itada Jafar suka gudu...!”
Giwa da kanta gaba d’aya ya kwance, girgiza kai ta soma tana furta “Izzatu babu hankali jikinta bazata iya taimakama wani har su gudu ba..!”
Jamal yai shiru tamkar mai nazari sai kuma yace “Jafar must be very weak, sabida azaban da yasha a nan... Bazai iya taimakama wani ba shima... Toh Who helped them escape...?!”
Baikai aya ba Giwa Ta basa amsa da fad’in “Wanda ya rufe Izzatu a wancan d’akin shi ya taimaka masu suka gudu..!”
Jamal yace “Waye shi Maami... Ki fad’a min sunansa yanzu na gama dashi..!”
Giwa tace “Wanda yafi kowa sanin lungu da sak’o dake cikin Masarautar nan.. UBANDOMA..!!”
Lokaci guda Ta ambato sunan Jakadiya...
Jakadiya da tinda suka soma magana hankalinta bai jikinta sakamakon ji da tai Jafaru da Izzatu sun kub’uta tasan ko shakka babu k’arshensu yazo kenan... Dan idan asiri ya bayyana tayi imani itakam tsire wuyarta tsaf da ayi a matsayinta na baiwa da taci amanan Iyayen Gidanta...
Jin bata amasata ba ya sanyata kuma doka mata kira... A firgice Jakadiya ta amsa da “Allah shi taimakeki..!!” Ta zube a wajen zuciyarta naci gaba da tsinkewa....
Giwa tace “Maza kije kizo min da Ubandoma yanda duk ya shiga ya fita... Ki sanar da Sarkin Dogarai yau kada ya shigo cikin Fada face yana tareda Ubandoma... Idan ba’a samesa ba azo da ‘ya’yansa... Kinji abinda na fad’i..!!?”
Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar, kanta a k’asa take furta “An
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 34 Chapter of 65