zama tawa gaba d’aya... Zanje na kashe wancan munafukar na dawo na d’aukeki mu bar Masarautar nan..!”
Yana ida fad’in haka ya mik’e ya nufi k’ofa...!
Aiko yana ficewa, cikin rawar jiki Umaima ta d’auko wayar ta soma k’ok’arin bud’eta Allah yasa k’aramar wayace ba’a kulle take ba... Babu lambar kowa a gidan saita Giwa cikinta, da alama Giwa kawai yake kirada layin... Ta soma tunanin bayan lambar Jamal d’in lambar waye Ta had dace a gidan..! Lambar Zahra kawai ta had dace hakan yasa ai Saurin latsa lambobin Zahra....
Zahra da tashinta kenan tana k’ok’arin shiryawa ta fito Fadar Giwa taji meke faruwa cikin Masarautar da yasa tin jiya da dare bataga kowa ba nan taga kira da bak’on lamba na shigo mata kaman bazata d’aga ba dan har Ta kusan matsewa tinda tsirarun mutane ta sani a gaba d’aya k’asar zai wahala ace wani bak’on lamba da ba na ahalin cikin gidansu ba na nemanta, sai kuma ta dai taji ta d’aga kiran... Aiko tana d’agawa ta sinkayo murya kaman ta Aunty Umaima tana fad’in “Zahra ki saurareni...!”
Zahra cikin wane irin yanayi tace “Aunty Umaima is that you..! Meke faruwa...?!”
Cikin sauti Umaima dake k’ok’arin saving chajin wayar dan ta kusan mutuwa gaba d’aya battery d’in... Nan taci gaba da fad’in “Follow your Uncle Jamal, and save Muhibbah..! Zahra don’t ask questions kawai kiyi yanda nace.. Ki bi bayansa kiga yanda ya b’oyeta and run straight to your Paa..! Ki sanar da Paa d’inki..!!” Bata ida maganar ba d’iff wayar ta katse chaji ya k’are...
Cikin rawar jiki Zahra Ke juya wayar hannunta....
Sauri sauri ta fito daga d’akin kota kan Hadimatarta dake sanar da ita abincin karin ta ya kammala bata bi ba..! Zuciyarta sai tsinkewa yake... Tana ficewa taga Masarautar babu wani mutane sosai kaman anyi shara, kodashike safiya ne sosai garin bai ida wayewa ba....
Cikin sand’a Ta fito Ta soma tafiya, zuciyarta sai bugawa yake, can kusan sashen Jamal ta hangosa ya fito cikin shiga ta kayan sanyi bak’ar riga mai hood, yanayin data gansa ciki sosai ya bata tsoro tai saurin bin bayansa kaman yanda taji Umaima tace....
Abinda ya bata mamaki shine hanyar da taga yabi mutane basu faye bin wajen ba, hasalima tamkar abandoned waje ne a cikin Masarautar... Dukda zuciyarta dake matuk’ar tsinkewa bata fasa bin bayan Jamal ba....
Tafiya mai nisa sukayi tanayi tana lab’ewa jikin Gini har dai taga ya tura wani k’ofa ya shige... Ta sad’ad’o a hankali ta nufo k’ofar da taga ya shige...!
Zuciyarta ne tayi wani irin tsinkewa sanda Ta hango Uncle d’inta Jamal tsaye gaban Muhibbah dake daure saman kujera kanta a kife a lamun takai mak’ura wajen jigata..! Akan idanunta Jamal ya d’auke Muhibbah da wata irin jahilar mari yana furta “Wake up..! Tashi munafuka it is morning already..!!”
Muhibbah ta d’ago kanta da k’yar tana k’ok’arin bud’e idanunta sukai luhu luhu dan tsananin azaba, ga wane irin tsami da jikinta Ke mata, kwana a zarge saman wannan kujera da ko motsawa baka iyawa ba k’aramin azaba bane...!
Jamal ya sakar mata murmushi yace “Good morning Beautiful..! How was your night..?! Na tabbata kinji dad’i...!”
Wayar salulansa ne da tai ringing ta katsesa..! Ganin Giwa ce mai kiransa abin ya basa mamaki dan shida ita sunada wayan da su kad’ai suke kiran juna da... Toh ina ya bar wayan... Wata zuciya tace tsakanin asibiti zuwa d’aki..
Yana d’agawa ya soma fad’in “Maami nifa van samu naje jana’izan yaran Yazeed ba, na taho direct zuwa wajen yarinyar nan..! Kuma banaso na had’u da Ya Mahmood can wajen jana’izan..!”
A hautsine Giwa tayi da fad’in “Kai Jamal ba wanne bane dalilin kiranka... Karka bar kusan yarinyar nan... Itace ta dawo..!!”
Baiji mai tace ba network ya katse cikin sauri ya fice neman service...
Hakan ya baiwa Zahra daman shigowa, a tsorace take duban Muhibbah dake zuban hawaye... Cikin rawar jiki ta isa da zummar kwance Muhibbah saidai babu hali domin kuwa da handcuffs Jamal ya d’aureta bada igiya ba babu key babu halin Ta kwanceta..! Ta d’ago a razane tana dubanta lokaci guda Muhibbah ke girgiza mata kai domin kuwa ta hango Jamal na dosowa... Take ta tuna sunyi Spanish classes da Zahra, Zahran ta koya mata wasu kalmomi daga cikin yaren... Sannan har Ta bata wani littafi na koyon yaren wanda ta tsinci wasu kalmomi ciki...
A hankali take furtada Zahra cikin Spanish “Zahra, Pon tu mano dentro de mi camisa..!” (Zahra ki saka hannunki cikin rigana.) “Papel..!” (Takarda) Zahra ta gane kalman Papel takarda yake nufi da spanish..
Muhibbah taci gaba da fad’in “No tengas miedo..!” (Karkiji tsoro)
“Solo haz lo que te digo..!” (Kiyi yanda nace)
Zahra Ta jinjina mata kai a hankali kana tayi yanda Tace dukda tana Iya jin sautin sandar Jamal a bayanta alamun ya kusa cimmata..!
Zahra ta ciro takardun Taswiran Muhibbah ta had’esu waje guda Allah yaso ruwan daka watsa mata bai jik’e cikin takardun ba sai gefe gefe...
Muhibbah Tace “Esconderlo..!” (Ki b’oye)..
Zahra Ta kuma jinjina mata kai a hankali kana tayi saurin turawa cikin rigarta...!
Daidai nan Jamal ya k’araso ya finciko wacce yake gani tsaye gaban Muhibbah ta basa baya...
Ga tsananin mamakinsa Zahra ya gani...!
SameenaAleeyou📚
*MUHIBBAH*
*73*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin wane irin sauti Jamal ya furta “Zahra..! Mai ya kawoki nan...? Ya ma akai kika shigo nan..?!”
Zahra dake nan tsaye tana dubansa itama shaye da mamaki tace “Uncle I followed you here...! Wait what’s going on.. Why is she tied up..? Mai Ta maka Uncle..?!”
Huci kurum Kamal keyi yana duban Zahra wacce itama idanu waje take dubansa... Lokaci guda ya kuma finciko hannun Zahra yana fad’in “You’re too young to understand Zahra.. Just come with your Uncle..!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin janyota....
Fincike hannunta tayi da k’arfin gaske tana fad’in “No Uncle I’m not leaving this place sai ka sanar dani mai ta maka ka d’aureta a nan..! Uncle you’re not a bad person right..!” Ta k’arashe cikin yanayin tsoro idanunta suna firfitowa waje...
Jamal da ya gama k’osawa da yarinyar, k’ok’arin finciko hannunta yake yana fad’in “I said come with me Zahra, you talk too much...!!” Ya k’arashe yana mai damk’o hannunta da k’arfin gaske ya shiga janyota...
Tarjewa take tana furta “Let go Uncle,You’re hurting me.. Let me go..!!” Inaa bai saketa ba saima kuma janyota da yake dad’a yi...
Cikin yanayin gwari gwari dan yaren ba wai ya gama nuna a bakinta bane kalmomi take tunowa Ta samu Ta harhad’o su bada ma’ana, nan ta bud’e murya taceda Zahra “Morder su mano Zahra..!” (Ki ciza hannunsa Zahra).. “Y corre directo a tu Paa” (Ki gudu zuwa wajen Paa d’inki)
Jamal bai daina janye Zahra ba yake waigowa yana duban Muhibba yana fad’in “You witch, what are you telling her..?!”
A daidai wannan lokacin Zahra tayi amfani da damar tayi abinda Muhibbah ta fad’a mata, ta sunkuya ta had’e hak’waranta ta gantsarawa Jamal cizo.... Ya saki k’aran azaba lokaci guda ya saki sandarsa da hannun Zahra ya zube k’asa..
Zahra ta soma gudu tana fad’i da Muhibbah “No te preocupes, la tía mi papá vendrá a rescatarte, te lo prometo...!” (Kar ki damu Tia, Paa d’ina zaizo ya taimakeki... Nayi Alk’awari)...
Ita dai Muhibbah idanunta naga Jamal dake k’ok’arin jan jiki yana rarrafawa ga sandarsa... Cikin tashin hankali take ceda Zahra “Ejecuta Zahra..!” (Ki gudu Zahra) “Y dale esos papeles a tu Paa..!” (Ki baiwa Paa d’inki takardun nan)
Zahra da jikinta bai daina rawa ba lokaci guda take jinjina kai tana furta “Si segura le daré..!” (Eh K’warai zan bashi)...
Cikin hawaye Muhibbah Ke furta “Te amo zahra..!” (Ina k’aunarki Zahra)
Zahra da har ta kai k’ofa juyowa tayi cikin hawaye itama ta furta “Yo tambien te amo tia..!” (Nima ina k’aunarki Tia) Daga haka ficewa tayi a guje dai dai nan Jamal ya samu ya janyo sandarsa ya mik’e... Cikin wane irin bud’e murya yake dokawa Zahra kira...
Saidai tinda Zahra ta fice take gudu hanya na had’e mata sam bata gane ta yanda suka shigo wannan wajen ba balle ta fice... Taja ta tsaya zuciyarta naci gaba da yankewa... Juyawa baya tayi ta kalli gabas ta kalli yamma kudu da arewa... Ko ta ina bata fahimci hanya ba.... Ga wasu irin jerin k’ofofi duka iri guda... Tana a haka ta soma jiyo sauti kaman na sandar Jamal alamun yana nufota...
Zuciyarta ta kuma tsinkewa, nan Ta kuma daburcewa Ta rasa wane hanya zata bi...
**
Tinda suka fito daga Janaza basu wuce Fada direct ba yanda aka bisne ‘ya’yan Yazeed a nan cikin Masarauta mak’abartan da ake busne ahalin gidan... Su sai basu k’arasa masarauta ba suka nufi wajen mutumin da suka bigesa a daren jiya, suna addua’n Allah yasa su samu ya farka...
Turaki ne ya soma yin gaba Mahmood ya tsaya amsa kiran Likitan Yazeed dan tun daren jiya Yazeed d’in ya farka yake hauka, he couldn’t accept changes d’in da ya farka ya tarar tattaredashi...! Turaki kaw yana isa d’akin da aka kwantar da mutumin ya tadda sai sa’insa tsakanin likitan da mutunin ake... Mutumin yana fad’in “Look Dr, we have same profession.. You can’t detain me here, da hankalina nasan abinda nake...I’m leaving this place right this moment.. With or without your permission..!!” Ya k’arashe yana mai fincike drip d’in...
Dr ya girgiza kai yace “Toh idan Kai likita ne bana tsammanin kasan aikinka... Maybe you’re a quack..!”
A zuciye Ansar ya mik’e yana k’ok’arin shak’o wuyan likitan yake fad’in “What did you just call me..!”
Daidai nan Turaki yai saurin k’arasowa yana k’ok’arin raba tsakaninsu... Likitan na huci yake furta “Yauwa yayi kyau da ka k’araso... Please ka d’auke mana wannan lunatic a nan, what he needs is a psychiatrist.. Wannan mutumin tinda ya tashi hauka kawai yake... Jiya an kawosa nan ruwa ruwa babu abinci a cikinsa babu komai yau yasha drip har ya samu k’arfin da zai bud’e baki yace yasan abinda yake shi likita ne... Ance maka zama likitan cin tuwo ne..! Take him away please..!!” Ansar ya kuma harzuk’a yana sakin huci zai kuma cakumo mutumin... Turaki yai saurin rik’esa yana basa hak’uri.. Shidai likitan tattara folder d’insa yai ya fice ya barsu nan cikin d’akin...!
Turaki ya k’araso yana duban mutumin wanda goshinsa Ke mak’ale da bandage, ya mik’a masa hannu alamun musabaha yace “Yusuf Turaki..!”
Da idanu kurum Ansar ke dubansa, kaman bazai mik’a masa hannu ba sai kuma ya mik’a sukai masabaha...
Turaki yaci gaba da fad’in “Jiya mun bige ka a k’ofar masarauta sai mukai rushing d’inka to this hospital, bamu samu komai tareda kai ba, babu ID babu komai shisa bamuyi gaggawan kiran family d’inka ba... How are you feeling now...?!”
K’ok’arin sa kai Ansar yake yana furta “Get out of my way... I need to save her..!!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin ficewa...
Cikin sauri Turaki ya take masa baya dan ya soma yarda da batun Dr da yace wannan mutumin kwanyarsa ba’a saite yake ba, kuma sanda suka bigesa tafiya yake gaba gad’i saman kwalta ta yuwu da gaske ba mai lafiyar kwanya bane...
Haka suka nufo dogon corridor na asibitin Turaki na biye dashi yana furta “Abokina tsaya ka saurareni, d’an tsaya ka saurareni.. Sanar dani inane gidan naku sai na kaika... Ko ka kawo lambar wani naka daga gida a kira...! Kanada mata ne..?!”
A harzuk’e Ansar ya juyo yana furta “This is exactly why I’m here, to take my wife back...! Sun rabamu da k’arfi.. Muhibbah is mine..! Ita d’in tawa ce..! We were about to get married but they took her away from me...!!”
Hawaye suka ci gaba da gangaro masa sanda yake furta “Sun cutar da ita..! Sun lalata mata rayuwa, hakan duk bai ishesu ba...! And now sun kuma zagayowa sunyi auren nunafunci da ita kawai dan su gama da ita, su kasheta... Na tabbata wannan dalili yasa suka zagayo suka bada dukiya suka sayeta dan kawai su kasheta... Nayi imani sun fahimci cewa Muhibbah itace SAUDATU yarinyar da ‘ya’yan Sarki suka lalata ma rayuwa 14yrs back..!!” Muryar Ansar yaci gaba da rawa yana duban Turaki dake tsaye tamkar statue a gabansa yake ci gaba da furta “Wannan Masarautar babu komai cikinta face zalunci..! Yes zalunci..!! They all deserve to die..! Ka fahimceni..!! Ka fahimceni yanzu.!!!” Ya k’arashe yana mai jijjiga Turaki dake tsaye tamkar gunki gabansa, cikin wane irin kuka Ansar ke jijjiga Turaki Wanda da gani kasan fitar da k’uncinsa da damuwarsa yake..!
Ba Turaki da yayi mutuwar tsaye yana duban yanda Mutumin Ke kuka dirshan a k’Asa ba, harta Mahmood da tin isowarsa yake tsaye yana dubansu ji yayi jiri na neman kifar dashi k’asa..! Kalaman Fu’ad dana wannan mutumin suna buga k’wak’walwarsa dake barazanar tarwatsewa..! Da zaka d’aura hannunka kuwa a k’irjinsa zaka iya jin yanda zuciyarsa ke bugawa kaman zata b’alle ta fito daga cikin k’irjin nasa... A haka ya dinga jefa k’afafunsa har ya iso gaban Ansar, ya saka hannayensa biyu ya d’agosa, hawayen da baisan daga ina bane suna gangaro masa... Cikin wane irin rawar murya mai rarrabewa yake furta “What did you say..?! Tell me what you know about Muhibbah..! Tell me what you know about my wife..!!!” Ya k’arashe yana mai kuma dage k’arfinsa yana matse rigar Ansar wanda har ya soma b’arkewa sabida tsananin damk’a da Mahmood yai masa...
Tashin hankali sosai ya bayyana a fuskan Turaki... Ansar ya gane Mahmood, ya gane shine Babban d’an Sarki AbdulJabbar wanda daga farko Muhibbah tai masa mummunan zato... Ashe shine kenan ya zago ya aure Muhibbah..! Shine Bak’on Buzu da yayita b’adda kama a cikin Masarautar, lokaci guda cikin tsananin huci Ansar ke furta “Yes your Highness..! You heard me loud and clear.. Your three Bastard Brothers raped Muhibbah when she was a Kid...! Ta girma da k’udirin dawowa wannan Masarautar to take her revenge.. Ko ince tayi zaton mahaifinta was somehow hidden cikin Masarautar... She thought harda Kai a cikin ‘yanuwanka da sukaci zarafinta suka d’aid’aita mata ahali... Suka tarwatsa rayuwarta, shiyasa taci alwashin kai wannan Masarautar k’asa by all means... She promised to take each and everyone of you down koda hakan zai zamto abinda zatayi na k’arshe a rayuwarta..! Taso tayi amfani da d’iyarka to ruin you sai ta fahimci kaid’in baka daga cikin wad’anda sukaci zarafinta suka d’aid’aita mata rayuwa...! Bayan ta had’aka fad’a da d’iyarka Ta zab’i Ta kuma dawowa Masarautar domin ta gyara abinda ta b’ata sabida kaid’in baka d’aya daga cikinsu... Dukda sanin had’arin dake tattareda ita na dawowa cikin Masarautar but still Ta zab’i Ta dawo tayi abinda ya dace, Ta zab’i ta dawo only for you and your daughter... To fix your relationship with your daughter...! That’s how much she loves your daughter..! Amma yanzu daka satota ka kawota cikin Masarautar ranan da ya kamata ya kasance ranan aurenmu nayi imani mugayen ahalinka bazasu k’yaleta ba har sai sunga bayan rayuwarta..!!!”
Mahmood da jikinsa Ke tsananin rawa bai iya k’arasa sauraren Ansar ba yayi jifa dashi gefe guda ya fice a guje cikin wane irin tashin hankali...
Turaki da shima har lokacin bai koma daidai ba ya kasa aminta da abubuwan da yaji, jin abin yayi tamkar wani a film... A guje yabi bayan abokinsa yana furta “Your Highness..!!! Mahmood..!!!” Inaaa tuni Mahmood ya fice...
Ansar ma ya mik’e da k’yar ya biyo bayan Turaki...!
**
Haka Zahra Ta mak’ale jikin wani gini ta k’unshe bakinta tana jin kuka na zuwa nata sosai, sai taji kaman sautin tafiyarsa ta wani wajen sai ta canza wajen b’uya a hankali tana mai kuma toshe bakinta da duka hannayeta biyu gudun kar kukan da take ya kufce ya fito, Ta rintse idanunta da k’arfin gaske wasu irin hawaye suka zubo nata sanda taji alamun gadan gadan ya nufo ta yanda take... Yana gab da cimmata dan har ya soma k’ok’arin tura k’ofar zanan da take mak’ale bayansa taji sautin murya kaman na Giwa tana fad’in “Jamal bamuda sauran lokaci Ina yarinyar take.. Ina Saudatu..!?”
Jamal yace “Maami tana kulle a d’akinta... Yanzu zan k’arasa nai mata alluran..!!”
Giwa Ta girgiza kai tace “Ka bar batun allura Jamal, dama itace gudan jinin da K’addarar Masarautar nan Ke wuyanta, itace wannan gudan jini tol da k’ofarta Ke bud’e a Fadan Sarauniya Tamuna, idan a yau d’in nan Tal’udu yayi abinda bai yi da ita a baya ba shikenan k’ofar zai rufe kaida ‘yan uwanka dole ku tabbata akan Mulkin gidan nan.. Mulki bazai tab’a kufce mana ba... Muje muyi sauri mu mik’ataga Tal’udu ya cika aiki Kaga matarka Umaima ta tsira..!!”
Jamal na girgiza kai yake furta “But Maami Zahra tana nan a wajen nan, Ta b’ace min ban ganta ba, yanzu haka ita nake nema..!!”
Giwa Ta zaro idanu waje tace “Jamal Zahra kuma..! Zahra fah kace..? Mai ya kawota nan.. Ya akai tazo nan..?!”
Girgiza kai yake yana furta “I don’t know Maami..! She followed me..!”
Giwa tace “K’yale batun Zahra ka shige muje kafin damarmu na k’arshe ya kufce mana..!”
Jamal ya girgiza kai yace “Maami don’t underestimate that girl.. What if taje ta fad’awa Mahmood..?!”
Giwa Ta buga Uban tsaki tace “Idanma ta fad’a masa bazai samemu ba dan muna Fadan Sarauniya tareda ita yarinyar, sannan abu ne mai matuk’ar sauk’i yanzu da muka samu k’ofar makullin Mulkinmu zai rufu ruff sai mu kashe Mahmooda harma da d’iyarsa kaga mun cire bare cikinmu tinda daga shi har d’iyar tasa ba jina bane.. Dama na gaji da pretending..! Shige muje.. Muyi sauri bamuda lokaci..!!” Ta k’arashe tana turasa Jakadiya na biye dasu...
Hankalin Zahra yakai k’ololuwa wajen tashi...! Tana jin Sun wuce ta bud’e bakinta data toshe Ta fitar da kukan da ya kuma taso mata tin daga k’irji..! Kuka take tana mamakin badak’alan zalunci da aka jika anayi cikin Masarautar su... Babu abina yafi tsaya mata kaman jin muryar Giwa da tayi tana fad’in Mahmood da d’iyarsa ba jininta bane..! Ashe ba ita ta haifi Paa d’inta ba shisa tun can basa wani son juna irin yanda jika da Kaka Ke son juna... Wasu hawayen suka kuma gangaro mata tsananin tausayin Paa d’inta na kuma kama Ta....! Tunowa da halinda Muhibbah Ke ciki ya sanyata Saurin mik’ewa Ta nufo waje babu shiri tana kuma neman hanya... Allah kurum take ambato tana rok’onsa ya fitar da ita ta isa ga mahaifinta..!!
**
K’iris ya rage bai had’ada masu tsaron k’ofar Masarautar ba, saida ya shige har tsakiyar farfajiyan Masarautar kana yaja wani irin burki... Zuciyarsa bata daina bugawa ba ya finciki marfin motar ya fito... A guje ya nufi b’angaren da ya ajeta, jama’an masarauta sai zubewa suke suna basa hanya cikeda mamakin yanayin da suka gansa ciki... Turaki da Barde harmada Ansar suka k’araso cikin Masarautar suma hankali tashe...
D’aya daga cikin Kuyangi masu kulada b’angaren Muhibbah itace Ta soma hango Rankaidad’e cikin wane irin yanayi da bata tab’a ganinsa ciki ba...! Ta shige a guje tana fad’in “Hasiya..! Hasiya ki shirya ga Rankaidad’e..!!”
Gaba d’aya Kuyangin sun rikice duk sun zuzzube a k’Asa zukatansu naci gaba da tsinkewa...
Babu kaman Hasiya wacce Ke zaune saman gadon Muhibbah ta janyo alkyabba ta rufe fuskarta da ita, zuciyarta sai tsinkewa yake sanda taji Rankaidad’e ya turo k’ofar d’akin ya sako k’afafunsa ciki...
Kai tsaye ya nufeta zuciyarsa bata daina tsinkewa ba, lokaci guda yakai hannunsa ya janye Alkyabban... Zuciyarsa tai wani irin tsinkewa sanda yaga ba Muhibbah bace..!! Fuskarsa Ta kuma rinewa zuwa ja haka nan idanunsa... Ga wane irin gumi da ya wanke masa fuska gaba d’aya sai d’iga yake...
Ita kaw Kuyangar sai karkarwa jikinta keyi sabida tsananin tsoro tamkar zata had’iyi ranta...
Mik’ewa yayi ya dafe kansa da duka hannayensa biyu dai dai lokacinda sauran kuyangin suka shigo kawunansu a k’asa... Shugabar tasu ce ta soma duk’awa tana furta “Rankaidad’e kai mana aikin Gafara...!”
Cikin wane irin yanayi yake dubanta kana yace “Where’s my wife..?! Ina matata nace..?!!”
Kuyangar jiki na rawa take furta “Allah shi taimakeka.. Munyi iyaka k’ok’arinmu ganin mun dakatar da ita amma tak’i tsayuwa..!”
Bai daina huci ba yake dubanta lokaci guda yake furta “Wannan shine umarnin da aka baku..?! Nace wannan shine umarnin da aka baku..?! Wacece take nan sanda hakan ya faru..?!”
Hannu na rawa d’aya ‘yar matashiyar ta nuna Hasiya da tuni ta silalo ta zube k’asa daga saman gadon..!
Tana jin ya soma takowa zuwa gabanta Ta soma fad’i cikin tsananin rawar murya “Rankaidad’e kai min gafara wllhi babu yanda banyida Gimbiya ba amma ta had’ani da Allah tace rayuwarta na cikin had’ari a Masarautar nan ya zama dole ta gudu shiyasa mukayi musayen kaya ta saka nawa na Bayi gudun kar azzaluman da suke nemanta su kamata..! Rankaidad’e Gimbiya tayi nisa da Masarautar nan dan tun jiya bata nan..!”
Zuciyarsa taci gaba da tsinkewa, kenan da gaske su Giwa suna nemanta zasu halak’ata..! Ina Ta tafi..?!
Bai tsaya nemo amsa ba ya nufo waje yanda ya tadda Ansar da Turaki.. Ansar na ganinsa ya k’arasa yana tambayarsa Ina Muhibbah.. Ko kallon arziki Ansar bai samu daga Mahmood d’in ba.. Saima duban Barde da yayi yace a rufe Kuyangin nan har sai an sami Muhibbah... Hakan yasa suka fahimci Muhibbah bata a cikin gidan...!
Bai kuma bin takan kowa ba ya nufi b’angaren Giwa kaman zai kifa k’asa..! Saidai koda ya nufi b’angaren Giwa bata nan babu Jakadiya babu Zahra ma sai taron ‘yan karb’an gaisuwa irinsu matan Waziri Talba Madaki da dai sauran masu sarauta harda iyalan Wambai...!
Cikin sauri ya fito ya nufi b’angaren Jamal tinda harda shi a case d’in..!
Nan ma bai tadda kowa ba, yayi tunanin ko yana waje can wajen maza su Talba da su Liman da dai sauran masu sarauta dake cike a Fada dan karb’an gaisuwa da jajen abinda ya sami Yarima Yazeed...
Yana k’ok’arin sa kai da niyyan ficewa ya sinkayo muryar mace daga upstairs alamun tana neman taimako...
A hankali ya furta Muhibbah... Babu shiri ya nufi saman yana bud’e k’ofofi yake ambato sunanta...!
Can saman gado ya hango Umaima ta gama jigata maganan ma da k’yar take..! Cikin tsananin sanyi jiki had’ida mamakin ahalinsa ya isaga Umaima ya hau kwanceta..!
Yana kwanceta yake tambayar “Who did this to you.?!”
Cikin kuka take sanar dashi duk abinda ya faru tin daga kan abubuwan da Muhibbah ta sanar da ita gameda Jamal har kamasu da Jamal d’in yayi ya d’aureta.. Bata kuma San ina yakai Umaima ba... Har kawo kiran Zahra da tai a waya duk saida Ta sanar dashi..!
Cikin kuka daidai sanda ya ida kwanceta take fad’in “Yaya please you need to go after Zahra..! You need to save them both.. I’m sure idan Jamal ya ganta itama bazai barta ba..!!”
Umaima bata ida magana ba Mahmood ya mik’e ya soma jada baya zuciyarsa na barazanar fitowa waje... Mutane biyu da sukeda matuk’ar mahimmanci a rayuwarsa suna hanun mahaukacin k’aninsa... Matarsa da kuma d’iyarsa suna hannun Jamal..!
Lokaci guda yake girgiza kai yana kuma jada baya..! Take ya nufo downstairs yana ambaton sunan Jamal da k’arfin gaske..!
Duk wanda yaci karo da Mahmood cikin Masarautar sai yasan babu lafiya.. Hanya kurum ake basa ana risinawa, duk wanda ya giftasa kuwa sai ya bisa da kallo....
Yana fitowa babban haraban Masarautar yayi wani irin k’ara cikin muryarsa mai amon gaske yana ambato sunan Jamal...! Can ya hangi Zahra ta nufosa a guje sai layi take alamun Ta jigata.. Fsukarta shar shar da hawaye take furta “Paaaa!!!”
“Zahra..!” Ya furta zuciyarsa naci gaba da tsinkewa..!
Zahra tana isowa ya tarota ta fad’o hannunsa dan k’iris ya rage bata zube k’Asa ba sabida tsananin tangad’i da take..!
Mahmood ya shiga jijjigata yana kiran sunanta yana tambayarta Ina Jamal da Muhibbah..!
Cikin kuka Zahra Ke. Furta “Paa you need to save her..! Her life is in great danger Paa..! Maami and Uncle Jamal zasu kasheta..! Paa I don’t want to lose her..!”
Cikin tsananin rawar murya yake furta “No Zahra bazamu rasata ba kinji.. Tell me ta ina suke..! Talk to me Zahra... Fad’a min yanda suke..!!” Ya k’arashe yana jijjiga Zahra da har lokacin bata gama dawowa daidai ba..
“Paa bazan iya ganewa ba...! All I know kawai daga ta can ne yanda na fito..! Paa you need to hurry..!”
Bai kuma tsayawa sauraren Zahra ba ya nufi yanda take nuna masa.. Turaki dasu Barde harma da Ansar da k’arasowarsu kenan sukabi bayansa... Turaki yaceda Barde yaje yazo da Dakaru a bazama nema cikin Fada...!
Umaima da itama bata jima da k’arasowa ba suka rungume juna itada Zahra suna kuka sosai..!
**
Bata kuma sanin meke faruwa ba tinda taga Giwa da Jamal a gabanta sai bud’e idanu tayi ta ganta cikin wani d’aki a wane irin waje... Ta ware idanunta da sukai matuk’ar mata nauyi tana k’arema d’akin kallo..! Innalillahi wa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 50 Chapter of 65