Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ni kinga tafiyata..!” Yasa kai ya shige yana fad’ida Ja’afar “Yarima gani nan tafe..!” ** Koda sukaje club d’insu Yazeed k’in fitowa yai, Raheemah ta duk’a gabansa tana fad’in “Zeed ya kamata ka fahimci this is who you are now, if you accept yourself the way you’re that’s when people will accept you.. So just come out and stop hiding from your friends kaji koh..” Da idanu kurum Yazeed ke dubanta kana ya furta “Bazan basu satisfaction d’in ganin downfall d’ina ba.. You know what Raheemah you’re just wasting your time... Bazan shiga wajen nan ba, I was once the king here, bazan tab’a shiga ciki a matsayin k’ask’antacce ba..!” Raheemah Ta murmusa tace “But you’ve my company ba kai kad’ai zaka shige ba... Mu shiga kasha iska kad’an..!” Ta k’arashe tana k’ok’arin mik’arsa tsaye, ya d’anyi k’ara kad’an sabida ciwonsa da sukai masa tsami gashi yau d’in ba’ayi dressing ba... Raheemah na rik’e dashi ta b’angare guda ya fuzge yana fad’in he can walk by himself... Saidai to their surprise suna isa spot d’insu Yazeed aka hanasu shiga... Raheemah tace “Baku gane wanene bane.. Prince Zeed ne fah..” Guard d’in yace “We’re sorry miss.. He’s not allowed in... Kawai ku koma..” Yazeed dake tsananin tururi matsowa sosai yayi yana furta “Cut the crap you imbecile..! How dare you..!” Guard d’in ya kuma furta “We’re just following orders here... Bazaka shiga ba and that’s final..!” Hawaye sukaci gaba da gangarowa Yazeed, ya dubi Raheemah dake tsaye tamkar ruwa ya shanyeta, lokaci guda Ta dubi Guard d’in tace “How much did pay you..? I’ll double the amount... Just let him in...!” “Ma’am.. I think it will be better idan kuka tafi..” Yazeed har wani irin rawa jikinsa yake, yau shine ake wulak’antawa irin haka, baisan ya akai ya isa jikin motar ba, kawai gani yayi Raheemah na bud’e masa marfin Mota... Bai shige ba sai wani irin kuka da ya fashe dashi yana jin zuciyarsa na masa d’aci yana tuna abubuwan sharholiya da sukayi cikin wajen shida abokansa da yanda yayita d’aukan nauyinsu suna abinda sukaso a doron k’asa yau gashi sun juya masa baya sabida halinda ya tsinci kansa ciki... Yana kuka yake furta ya zama k’ask’antacce... Raheemah ta fuzar da huci kad’an tace “Waye yace kai k’ask’antacce ne... Kaifa mijin Gimbiya ce har yanzu, ko ka mance ba Zuhra bace kawai Gimbiya.. I’m also a Princess.. Har yanzu kai d’in mai sarauta ne... I can give you back your title..” Ta k’arashe cikeda kulawa... Cikin huci yake furta “If you can give me back my title, can you bring me back my reputation..? Can you bring me back Zuhra..?! Can you bring me back my two children wanda na kashesu Da hannayena guda biyu...?! Tell me Raheemah can you bring back all that I mentioned..!” Kuka yaci k’arfinsa sanda yaci gaba da fad’in “Of course you can’t Raheemah.. Bazaki iya ba.. look at me now.. D’ago ki kalleni na koma babu hannaye babu mulki babu sarauta babu family babu asali da nasaba..! Toh mai ya min saura a wannan rayuwar Raheemah.. Tell me mai ya min saura..?!” Kaman daga sama suka sinkayo muryan abokansa su Zayyad suna furta “Tabbas babu saura Yazeed... It’s all over, there’s no more Yazeed AbdulJabbar.. You’re completely ruined.. Shara ya fika daraja Yazeed dan na tabbata akwai masu bibiyan bola suna tsintar bola.. But you Babu wanda zai rab’eka sai wannan kwandon sharar ‘yaruwarka..!” Ya k’arashe yana nunida Raheemah a wulak’ance... Wani kukan k’ura Yazeed yai yayo kan Zayyad yana kai masa bugu da gundulumin hannayensa Ta ko ina yana wane irin cazgan kuka... Da k’yar Raheemah ta iya janyesa jini duk ya b’ata Farin bandage d’in da aka rufe hannun ciki.. Lokaci guda Yazeed Ke sakin k’ara yana fad’in hannunsa zafi.. Hankali tashe Raheemah ta nufi mota dashi tai rushing d’insa zuwa asibiti... ** A b’angaren Muhibbah kuwa tinanin abubuwan da Raheemah Ta sanar da ita su suka taru suka tsaya mata a zuciya, Ta k’ule a d’aki tana sak’awa tana warwarewa... Bazata bari Rankaidad’e yai mata wannan Mulkin malllakan ba, kafin ai masa nad’i kafin Ta tare dashi kaman yanda Raheemah tace ya kamata ta amshi takardanta daga gareshi.. Tinda idan Ta bari aka nad’asa sarauta shikenan babu hali Ta koma ga Ansar wanda sam bai cancanci hakan ba.. Life is all about sacrifice, she needs to do this for Ansar...! Ta k’arashe tinanin nata tana mai zama saman gado, toh amma idan tana so ya sawwak’a mata cikin sauk’i dole sai ta sauk’ar da kanta gabansa ta nemi abin cikin lallama babu tashin hankali... Tai shiru tana tunanin toh kodai ta kirawo Zahra ne..? Sai kuma ta girgiza kai. A hankali ta furta “No I don’t want to involve his daughter..” Ta fad’i tana mai kuma mik’ewa tsaye, lokaci guda ta kuma furta “Toh kodai Ummi zan samu da batun.?” “But she’s his mother, koda zatabi bayana cikin zuciyarta zataji zafin abun... I need to this alone by myself..” Ta k’arashe tana mai murza hannayenta had’ida tinanin Ta k’anda zata tunk’ari Rankaidad’e... Daga yanda yake dubanta ya kuma karkata k’afa d’aya bisa d’aya fuskar nan nasa a tamke kaman tana ganinshi, sai faman murza hannunsa guda yake... Cikin ransa yake furta “We shall see..” Lokaci guda ya d’auki wayarsa dake saman table ya shiga dialing layin Hadiminsa Barde Muhibbah na nan tana tunanin yanda zata tunk’ari Rankaidad’e taji ana k’wank’wasa k’ofarta, Hadimarta ce ta shigo ta risina tace “Allah shi taimakeki sabuwar Jakadiya ce take sallama..” Muhibbah ta jinjina mata kai tace “Bismillah shigo da ita..” Hadimar ta kuma risinawa had’ida amsawa, Jim kad’an suka shigo tareda wata Dattijuwar mace mai kamala, Ta risina tana gaida Muhibbah... “Kece sabuwar Jakadiya..?” Jakadiya Ta risina tace “K’warai nice Rankidad’e... Kuma sak’o ne tafe dani daga Mai Martaba, yace Lallai a sanar dake yanada buk’atar ganinki.. Allah shi taimakeki..” Ta k’arashe tana mai kuma risinawa gaban Muhibbar... Ta mik’e zumbur cikeda mamaki saikace yasan neman hanyar tunk’ararsa take, jinjina mata kai tai tace ”Shikenan Jakadiya Ki jirani a parlor ina nan fitowa..!” Jakadiya Ta risina tana mai amsawa kana Ta nemi izinin fita parlor.. Doguwar riga ce ta atampa jikinta anyi mata d’inkin fitted gown, sosai ya amshi suffar jikinta, Ta d’auko alkyyabrta ruwan madara ta zira alla alla take ta isa suyita da wajewa itada Rankaidad’e... A haka ta fito suka nufi sashen nasa itada Jakadiya... Tana tafe zuciyarta na tsananta bugawa domin kaw duk sanda zasu keb’e hakan takeji... Babu kowa a parlorn nasa hakan yasa suka nufi upstairs Jakadiya na gaba tana biyeda ita, A wani madaidaicin parlor ta hangesa yana zaune bisa kujera tv gaba gareshi ya baima kallan nasa mahimmanci sosai.. Ta d’an tab’e baki a ranta tace wayaga Sarki da kallon tv... Jakadiya ce ta soma neman izinin shiga, ta shiga ta zube tana kwasan gaisuwa kana Ta sanar dashi tafe suke da Gimbiya Muhibbah... Mahmood ya jinjina kai a hankali yace a shigo da ita.. Jakadiya ta amsa had’ida godiya da jinjina a garesa.. Nan ta k’araso ta sanar da Muhibbah sak’on Rankaidad’e.. Zuciyarta bata daina bugawa ba sanda ta kutso kai cikin d’an madaidaicin parlorn wanda yasha kwalliya da kayan sarauta irin na gargajiya da akai modernizing d’insu, gwanin ban sha’awa ko ina... Kasa d’ago kanta tai ta dubesa dukda tasan cewa nasa idanun akanta suke, tai tsaye sororo a wajen tamkar wata dogariya... “Meke tafe dake..?” Kalaman da taji sun fito daga bakinsa kenan saikace bashi ne ya aika a kirawota ba... Ta d’an d’ago idanu ta dubesa yayi zama irinta masu mulki k’warjininsa ya cika wajen gaba d’aya... A hankali Ta samu kanta da silalewa saman k’afarta, ta zauna nan gaba gareshi irin zaman rak’umi... Murya can k’asa take furta kalaman gaisuwa, ya amsa a tak’aice ba tareda ya kuma cewa komai ba... Kusan dak’ik’a biyar babu wanda ya kuma magana, da dai taga da gaske bazai kuma magana ba sai ta d’an gyara zamanta tace “Jakadiya tace kana kirana..” Shiru ya d’an gifta kaman bazai amsata ba “Baki amsa min tambayata ba.. Meke tafe dake..?” A ranta tace yau naga ikon Allah ni Muhibbah wannan wace irin tambaya ce, wata zuciya tace watak’ila damarki kenan na rabuwa da aurensa... Ta d’an kuma yin gyaran murya kad’an tace “Nima ban sani ba..!” “Baki sani ba..?” Ta jinjina masa kai a hankali dan bata San ta yanda zata fara ba da gaske... Mik’ewa tsaye yayi ba tareda ya kuma ceda ita komai ba ya nufi wata k’ofar tabi bayansa da kallo tana tab’e baki kad’an... Jim kad’an Ta gansa ya fito da shiga irinta Buzaye... Tabisa da kallon mamaki har ya dawo mazauninsa ya zauna... Saida ya daidaita zamansa saman kujerar kana yace “Kinga haka..! Toh a haka na auroki.. Kuma kaman yanda kika fad’i na auroki ne da dalili.. Toh hakan ne yake, dalili kuwa shine ki zamto min bakin zaren warware matsalolin da suka shige min duhu a cikin gidan nan.. Gaskiya ne..! ked’in kece Bakin zaren kuma kin warware... Akwai k’arin bayanin da kike nema..?!” Ya k’arashe yana mai warware nad’in fuskarsa... Zuciyarta bata daina bugawa ba Ta had’iyi abinda ya tsaya mata a mak’oshi da k’yar.. Lokaci guda ta furta “Tinda na warware maka k’ullin dake cikin Masarautar inaga lokaci yayi da zaka sawwak’e min Rankaidad’e... Tinda wannan shine dalili na auren..!” K’uri yai mata yana murza zobbansa a hankali kana yace “Baki da hurumin da zaki buk’aci wannan daga wajena, har sai lokacin da ni nayi ra’ayin kaina..!” Ta d’ago a razane tana dubansa... Lokaci guda ta mik’e zumbur tana girgiza kai take furta “Kar kayi min haka Rankaidad’e.. I’ve been through a lot.. Dan Allah kar ka zamto sanadiyan da k’addarar rayuwata zata kuma sauyawa..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya hawaye na gangaro mata.. Mahmood yaci gaba da takowa gaba gareta tana k’ok’arin matsawa baya, har saida taji alamun Ta isa jikin gini kana ta tsaya ta daina motsa k’afafunta... Fuskarsu dab kusan na juna yake furta “Kinaso na sawwak’e miki..?” Ta jinina kanta a hankali hawaye na kuma gangaro mata, lokaci guda ya saka hannunsa ya dafe ginin yai mata rumfa gaba d’aya, zuciyarta sai tsinkewa take ko k’wakk’warar motsi ta kasa... Mahmood yaci gaba da furtawa a hankali “Zan sawwak’a miki amma nima inada sharad’una..!” Ta d’an d’ago fuskarta ta dubesa sai kuma ta maida k’Asa a hankali tana mai furta “Menene sharud’an naka...?” Stepping back yai kad’an had’ida juawaya ya bata baya hannayensa rik’e ya bayan, saida wasu dak’ik’a suka kuma shud’awa kana Ta sinkayo muryarsa yana fad’in “Kinada jarabawa na tsawon kwanaki uku, idan kinci zan sawwak’a miki kafin ayi mun nad’in sarauta...! Idan kuma kika fad’i shima zan sawwak’a miki amma sai bayan an nad’ani sarauta yanda ko na sawwak’a miki bazaki tab’a ficewa Ki auri wanda kike so ba.. Zaki k’arasa rayuwarki ne a gidan tsaffin matayen sarakuna da k’uruciyarki.. Kin amince da sharad’ina..?!” Ya k’arashe yana mai juyowa ga dubanta... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa da jin wanann batu nasa,tasan jarabawar zai zamto mai matuk’ar wahala amma batada wani zab’i... A hankali ta shiga jinjina kai tace cikin rawar murya “Na amince...!” Mahmood ya murmusa kad’an for the first time tun bayan shigowarta kana yace “Buena..!” (Da kyau) Ya d’an kumayin gyaran murya kad’an yace “Sharad’i na biyu Ummi must not know about this.. Kin amince..?!” Nan ma a hankali ta jinjina masa kai alamun amincewa... Shiru ya d’an ratsa tsakani yana mai ci gaba da karantar ta... Lokaci guda yake furta “Ki sami Jakadiya zata sanar dake tsarin jarabawar..!” Daga haka bai kuma bi takanta ba ya nufi wata k’ofar ya barta nan tsaye tana mai bin bayansa da kallo zuciyarta naci gaba da tsinkewa da fargaban amsar sharud’an Rankaidad’e da tayi... Cikin tsananin sanyin jiki Ta nufo downstairs yanda Jakadiya Ke jiran fitowarta... Jakadiya tana ganin isowarta ta k’araso murmushi saman fuskarta take furta “Rankidad’e an fito..?!” Muhibbah ta jinjina mata kai a hankali tace “Eh Jakadiya.. Yace min na sameki zaki min bayanin komai..” Murmusawa Jakadiya ta kumayi kana Ta nuna mata wata hanya tace “Rankidad’e mubi wannan hanyar..” Babu musu Muhibbah tasa kai Jakadiya na biye da ita... Wata k’ofa ce hanyar ta fitar dasu, can Ta hangi kuyangi ‘yanmata da manyan mata sai aiki suke da alama kitchen ne na musamman, wasu na yankan ganye wasu na girka abinci wasu na aikace aikace irin na kitchen... Muhibbah tabisu da kallo d’aya bayan d’aya sai aikace aikacensu suke... Jakadiya ta tafe hannayenta biyu alamun kira a garesu, nan da nan kowa ta bar abinda take ta nufo yanda suke tsaye, gaba d’aya suka risina suka kwasa gaisuwa... Jakadiya ta d’anyi gyaran murya tace “Kowa ta bar aikin da take ta fice..!” Idanu waje Muhibbah Ta kaikaito tana duban Jakadiya shaye da tsananin mamaki jin tace subar tulin aikin da suke su fice... SameenaAleeyou 📚[10/2, 12:37 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *81* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Mamaki bai saketa ba take duban manya manyan tukwanen dake bisa madafi, uwa uba tulun tsabar shinkafar data gani an ida wankewa za’a zuba... Bata ida mamaki tana ci gaba da waige waige ba Ta sinkayo muryar Jakadiya tana fad’in “Allah shi taimakeki ni zan koma zuwa lokacin da Mai Martaba ya d’ibar miki sai in dawo...” Tasa kai zata juya cikin risinawa... Baki sake Muhibbah Ke dubanta sam bata fahimci mai take nufi ba... Kafin takai k’ofa tai saurin kamo hannun Jakadiya tana fad’in “Dan Allah karki tafi ki barni a nan ni kad’ai... Bansan mai zanyi ba..” Jakadiya ta d’an dubeta sai kuma tace “Rankidad’e a al’ada irinta gidan nan ranan da Matar Sarki zata soma ziyartan Turakan Mai Martaba akan sakar mata ragamar girkin Fadah gaba d’aya na wannan ranan wanda harta Sarki wannan abincin zaici.. Domin a gwada jarumtar Giwar Amale a fagen Girki.... Za’a zuba saman farantai a shigar ko wani k’ofa kowa yaci ya fad’i ra’ayinsa akan girkin... Idan wanda suka yabi girkin sunfi Rinjayi Masarauta tayi dace, idan kuma wanda basu yaba ba sunfi rinjayi Masarauta Ta samu nak’asu a wannan fannin.... Tsarin kenan Allah shi taimakeki..” Ta k’arashe tana mai kuma risinawa... Zuciyar Muhibbah yaci gaba da tsinkewa, babu abinda zuciyarta Ke nanatawa kaman cewa da Jakadiya tai randa Matar Sarki zata fara ziyartan turakansa ranan ake wannan al’ada ta girkin.. Ta lumshe idanunta a hankali zuciyarta naci gaba da tsinkewa, b’angare na zuciyarta na bata k’arfin gwiwa da fad’in zaki iya Muhibbah.. Zaki iya.. In exchange of your freedom zaki iya.. Ta k’arashe tunanin nata tana mai sauk’e huci a hankali.. Bud’e idanun da zatai taga babu Jakadiya.. Shafe fuskrta tai tana mai kuma k’are ma tampatstetsen madafin kallo... Take taji wani irin k’warin gwiwa na zuwa mata, Ta zame alkyabbarta ta aje a gefe kana ta nufi manya manyan tukwanen tana ganin abinda masu abincin Ke dafawa ciki... Saida ta kuma sauk’e wani ajiyan zuciyar tana mai ambaton Allah ya taimaka mata... Da alama tuwon farar shinkafa ne miyar taushe suke girkawa... Sa’arta guda shine sun rage k’arfin aikin k’arashi ne saiko abinda take fargaban bazata iya ba bazai wuce juya muciya cikin tuwon ba... Ta saka bayan hannunta ta share gumin da tuni Sun karyo mata... Tanayi tana fuzar da fuci.. Ga kayan k’amshi da na d’and’ano ko wanne jere saman faranti... Cikin k’warin gwiwa Ta soma k’ok’arin gudanar da aikin nata mai matuk’ar yawan gaske dukda cewa batada tabbacin idan zata iya wannan aiki wanda sam hankalinta bai kama ba.. ** A daidai k’ofar shiga sashen Gimbiya Turai suka kusan cin karo, zuciyarsa cunkushe take da b’acin rai sakamakon taurin kan da Jamal yai masa yau a asibiti.. Sam baiga zuwanta ba itama bataga nasa ba sai karo da juna da sukai.. Tai saurin komawa da baya tana rik’e goshinta had’ida ‘yar k’ara lokaci guda take Masifan “Wai ku Kuyangin gidan nan yaushe ne zaku koyi tafiya kuna kallan gabanku..!” Birki taima kamalan nata ganin namiji ne tsaye gabanta kuma cikin shiga irinta masu mulki... Ta d’ago tana dubansa har lokacin hannunta dafe da goshinta... “Tuba nake Your Highness..!” Ya fad’i yana mai d’an sadda kai k’asa... Murmushin da yafi kama da yak’e tai tace “Your Highness..!” Ja’afar ya katseta da fad’in “Nafi gane Ki kirani da Ja’afar d’ina Rankidad’e..” Nanma murmushin tai kad’an tana mai daidaita tsayuwarta take fad’in “Dole na kiraka your Highness, domin kuwa Kaid’in Mai Martaba ne a halin yanzu..! Idan Rankaidad’e ya min izini zan shige..!” Ta k’arashe kanta a k’asa.. A hankali ya d’an ja jikinsa gefe ya bata hanya, kaman wacce take bisa k’aya yana matsawa tasa kai zata shige... Saida tai taku kad’an Ja’afar ya ambato sunanta.. Bata juyo ba saidai cak Ta tsaya zuciyarta naci gaba da bugawa... Ya d’an tako kad’an ya tsaya daga gefenta, shiru kaman bazaice komai ba sai kuma yace “Maiyasa tinda na dawo kike guduna...?” Shiru itama kaman bazata amsa ba sai zuciyarta dake ci gaba da tsinkewa.. Siririyar hawaye ya gangaro mata, cikin rawar murya take furta “Sabida haka ne ya kamata gudun kada mu fad’a ga fushin Ubangiji... Ja’afar nasan kanada masaniyar cewa akwai auren wani akaina..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya irinta mai kuka... Jiki a matuk’ar sanyaye yake dubanta kana ya jinjina kai a hankali yace “Haka ne..! You’re right.. I’m sorry, you can go ahead..!” Ya k’arashe yana mai sadda idanunsa k’asa.. Umaima dake k’ok’arin matse kukan da yazo mata gadan gadan, cikin sauri tasa kai ta shige tana mai toshe bakinta... K’ok’arin saita kansa Ja’afar yai yana mai furtawa a hankali bayan Ta shige... “Everything will soon be over... Soon enough.. I promise you..!” Ya k’arshe yana mai kutsa kai sashen mahaifiyarsa... ** Iyaka jigata ta gama jigata, aiki ne na tarumi aikin gayya aikin da mutane da yawa keyi sai gashi cikin ikon Allah taci k’arfin aikin, tunaninta d’aya yanda zata tuk’a wannan Uban tuwo wanda ko gardawan maza iyaka... Ta fuzar da fuci a hankali tana mai furta “You need to do this Muhibbah..! For Ansar and Mommy, you need to be very strong..!” Ta k’arashe tana mai sauk’e huci had’ida gyara tsayuwarta gaban tukunyar, sosai ta bada wani irin balance kaikace wacce take shirin wasan dambe ce... Ta kamo muciyar wanda tuni ya d’auki zafi k’au Ta shiga juyasa da k’yar tana tamke idanu tana ciza labb’a... Ga wani uban gumin dake tsartsafowa daga ko wane mahudan gashi na cikin jikinta... Sai tayi kaman zata saki muciyar sai ta tuno sharud’an Rankaidad’e... A haka tanayi tana hutu hardai Ta samu tayi abinda zata iya dan ba’a ce tayi komai daidai ba aiki ne na gayya mutum guda Ke jagoranta.. Gefe ta koma tayi lak’was tana sauk’e huci tana duban yanda ta kammala aikin cikin ikon Allah, abinda ya rage kawai shine ta jira dahuwar abincin sai a zuzzuba kaman yanda Jakadiya tace... Ta shiga juya tafin hannunta tana ganin yanda cikin hannun yayi jajazir har kaman yanaso ya d’ura ruwa... Ta rintse idanunta a hankali domin kuwa gaba d’aya gab’ob’inta Ji take tamkar ana sassara mata su... Tana a haka Jakadiya ta k’araso tanai mata sannu... Muhibbah ta d’ago a galabaice tana duban Jakadiya... Saida Jakadiya ta isa jikin tukwanen ta lek’a ko wanne ta tabbata Muhibbah ta aikatu kana ta dawo gareta ta kuma risinawa tace “Sannu da k’ok’ari Rankidad’e.. Jibi yanda kika gudanar da komai cikin k’ank’anin lokacin nan kaman wacce aka saka miki hannu..?” Murmusawa Muhibbah ta kumayi kad’an tana mai yarfe gumin dake kuma gangarowa daga cikin kanta zuwa goshinta.. Daga can gefe Jakadiya taja ta tsaya suna jiran dahuwar abincin.. Bayan shud’ewan wani lokaci Jakadiya ta dubi Muhibbah dake kishingid’e gefe tana maida hucin gajiya, ta d’anyi gyaran murya tace “Ki gafarceni Rankidad’e ko zaki duba girkin naki..?” Muhibbah ta mik’e zumbur da k’yar ta isa jikin tukwanen tana k’ok’arin bud’esu, wanda girman murafen ma kawai abin kallo ne... Duk ta soye hannayenta jikin murafen tukunyar... Ta d’auko k’atoton ludayin tana juya miyar ta tabbata yayi... D’an duban Jakadiya tai tace “Jakadiya inaga abincin ya kamalla.. Ya kamata a zuzzuba na samu naje nayi wanka na gaji sosai..” Jakadiya ta jinjina kai tace “An gama Rankidad’e... Tafe hannayenta Jakadiya ta kumayi take Kuyangin suka soma shigowa sahu sahu suna mamakin abinci ya kammala... Suka risina suna gaida Muhibbah, Allah ya gani ko iya jinjina masu kanma batayi sabida tsaban gajiya... Wani hamshak’in paranti na alfarma mai ruwan zinari Jakadiya ta mik’o gaba gareta ta risina tace “Rankidad’e wannan parantin a ciki zaki zuba kason Mai Martaba, Kason Sarki ake soma zubawa kafin kason sauran ahalin Fadah ya biyo baya..” Muhibbah ta amsa tana mamakin fidda ficce da al’adu irinta gidajen Sarauta... Ta isa ta malmala tuwon ta d’ora kan parantin, Jakadiya ta kuma mik’o mata wani d’an madaidaicin bowl wanda da gani basai ance maka mahad’in parantin bane tace ta zuba miyan ciki.. Tayi gaba d’aya yanda Jakadiya ta umarceta kana ta kawo wani marfi wanda da gani kasan shima marfin wannan farantin ne... Aka rufa aka d’aura saman babban tray kana aka kawo wani k’yalle mai ruwan zinari shima aka rufa parantin dashi.. Bayan an gama duka wad’annan ta dubi Muhibbah tace “Toh Rankidad’e kin gama naki, saura ya rage kije kiyi wanka Ki kimtsa Ki tafi B’angaren Mai Martaba, za’a shigo da abincin da zaran kin isa sashen nasa..” Cikeda k’osawa Muhibbah tace “Yanzu Jakadiya abincin ma baza’a kai masa ba sai ina wajen..?” Jakadiya ta murmusa kad’an tace “Ki gafarceni Rankidad’e ai inaga ko ba al’adan gidan sarauta bane hakan ne ya kamata... Miji yaci abinci gaban matarsa domin ya samu daman yabonta... Hakan na k’ara dank’on k’auna tsakanin ma’aurata..” Ta k’arashe cikin hikima irinta wanda yakeda experience.. Ita dai Muhibbah tab’e baki kurum tayi kad’an dan dai Jakadiya bata San akan mai ake duka wad’annan abubuwan ba da bata tsaya b’ata bakinta tana wannan bayanin ba.. Auren da aka yosa babu soyayya wani dank’on k’auna za’a nema cikinsa.. Dan dai kai babu yanda ta iya ne tinda sharud’an da Rankaidad’e ya gindaya mata take bi.. K’in komawa sashen nasa ka iya janyowa yace ta fad’i jarawar... Ta dubi Jakadiya ta jinjina mata kai kad’an zatayi kaman yanda tace... Daga haka Jakadiya ce Tai mata Rakiya zuwa yanda suka baro Hadimarta na jiranta kana Muhibbah da hadimar suka nufi sashenta yayinda Jakadiya ta koma sashen madafi... Da k’yar ta isa d’aki sai sauk’e fucin gajiya take, tana isa ta kwab’e kayanta ta fad’a bathroom ta gasa jikinta da ruwa mai d’umin gaske had’ida kayan k’amshi na wanka... Ta jima sosai cikin bathroom d’in kana ta fito d’aure da towel tana goge sumarta data wanke da wani towel d’in... Cikin zuciyarta take tinanin inama Ta sami dryer da ta busar da wannan gashin nata... Aiko tana tsaye tana ci gaba da tsane sumar nata taji knocking.. Ta janyo hijabi ta zira kana ta bada izinin shigowa.. Hadimarta ce ta shigo rik’eda ‘yar jaka ta risina ta ajiye mata tana mai furta “Aike ne aka bata ta shigo dashi..” Muhibbah tasa hannu ta d’ago jakan tana juyawa, ga mamakinta k’aramar hand dryer ta gani mai kyau ciki..Toh waye yayo mata wannan aiken..? Ta dubi Kuyangar tace daga inane..? Kuyangar tace “Allah shi baki yawan rai d’aya daga cikin Hadiman cikin gida ne ta shigo dashi tace Wai a baki..” Jinjina kai tai tana kuma mamaki, watak’ila Umaima ne ko Zahra d’ayansu ta bata, toh amma ai basu san tana buk’ata ba..? Wata zuciya tace k’ila sunyi tunanin bakidashi kuma zaki iya buk’ata shisa suka baki.. Da wannan tunanin ta amsa kana ta sallami Hadimar.. Nan da nan ta jona ta shiga busar da sumarta... Tsaf ta shirya cikin wani dubai material mai kyaun gaske wanda akai masa kwalliya da sequence mai ruwan zinari sai d’aukan idanu yake.. Batayi niyyan shafa komai a fuskarta ba amma sai tayi tinanin hakan ka iya janyowa ta fad’i jarabawrta, Sannan tafi so ta nunawa Rankaidad’e cewa ita d’in ba raguwa bace zata iya lashe jarabawarsa, ya kamata taje da k’arfin gwiwarta, sam bazata basa wani k’ofa da zaice ta fad’i jarabawarta ba... Ta zauna gaban dressing mirror ta shafa iyaka abinda idanunta ka iya gani wanda tasan baza’a kalleta ace fuskarta tayi fayau ba sannan baza’a kalleta ace tayi kwalliya mai yawa ba.. Abinka da wacce ta jima batayi ba dan zata iya cewa tin tana Collage of nursing rabonta da ta zauna tace zatayi kwalliya na musamman, Yo ita da burin fansarta ke kanta wani make-up ma zata zauna tanayi batada wannan lokacin... Kallo d’aya zakai mata Kaso sake kallonta, babu shakka tayi kyau.. Ta tupke sumarta a k’eyarta

Chapter 57 of 65