fatar jikinsa ta soma komawa ja...With a straight face yake furta “Fu’ad you tell me what you three did...! What did you do to that girl...! What Fu’ad..?!!” Ya k’arashe yana jijjiga Fu’ad kad’an idanunsa duk sun firfito waje zuciyarsa naci gaba da bugawa..
Fu’ad na hawaye yana girgiza kai yake furta “We abused her Yaya..! The three of us raped her..! Yazeed started it, then Jamal..! Then me...! Ka yarda dani Yaya, Wllhi banso aikatawa ba...But they forced me...! Yazeed da Jamal sun tilasta min sunce umarnin Maami ne dole na aikata hakan....!”
Mahmood da yakejin maganar tamkar sauk’ar takobi cikin zuciyarsa... Dakatar da Fu’ad yayi da fad’in “I don’t get you Fu’ad... What are you trying to say...?! Kana so kace min my brothers... My three brothers Kun lalata rayuwar wannan yarinyar kuma Maami ita tai maku umarni ku lalata rayuwar yarinyar...! Fu’ad talk to me..! Kamin magana da yaren da zan fahimta..!!” Ya k’arashe fuskarsa na kuma rikid’ewa gaba d’aya....
Cikin kuka Fu’ad Ke jinjina kai yana mai furta “Yaya gaskiya nake fad’a maka..! Duk abinda na fad’i mun aikata kuma bisa umarnin Maami muka aikata..!!”
Izuwa wannan lokaci Mahmood ya kasa fahimtar wacce duniya yake..! Ya kasa yarda ‘yanuwansa da suka fito ciki guda zasu aikata mummunan laifi irin wannan, waima bai tsaya a nan ba harda mahaifiyarsu..! Kai inaa Fu’ad baida lafiya bai kamata ya yarda dashi ba in the first place... No ahalinsa bazasu tab’a zama azzalumai irin haka ba.. They might have their own differences amma bazasu tab’a zama azzalumai abin k’yamata irin haka ba...!
Muryar Fu’ad ya sinkayo yana ci gaba da sanar dashi yanda duk abun ya kasance tin daga farko...! Wane irin gumi na tsartsafowa Mahmood d’in, jikinsa ya d’auki rawa... Lokaci guda ya d’ago yana duba Fu’ad d’in, cikin wane irin kakkausar murya yace “Fu’ad you’re talking about our mother here..! My mother Fu’ad...!! Maami can never do something like that..! You are sick in the head Fu’ad..! And this place is where you belong..!!” Ya k’arashe cikin tsananin huci... Lokaci guda ya mik’e yana kiran nurses d’in suzo su shige da Fu’ad su maidasa d’akinsa na majinyata babu alamun lafiya a tattaredashi ko abubuwan da yake sanar dashi....
Take nurses d’in suka k’araso suna k’ok’arin janye Fu’ad yana tarjewa, yana juyowa yana duban Mahmood d’in yake kuma fad’in “Yaya I’m not sick anymore..! I’m telling the truth..! Why can’t you believe me..! Wllhi gaskiya nake fad’i maka..!! Yaya please ka saurareni..! Take me to jail please, I need to pay for my crimes..! Yaya dan Allah ka saurareni..!!”
Inaa tuni an shige da Fu’ad, Mahmood kaw tsaye kurum yayi yana duban yanda aka janye Fu’ad, zuciyarsa na tsananin bugawa kaman zai tarwatse ya fito waje..! Take yaji tsakiyar kansa ma na sarawa kaman kan nasa zai rabe k’wak’walwarsa ta tarwaste...!Ya kasa yarda ‘yanuwansa harda mahaifiyarsa zasu aikata irin wannan mugun abin, mummunan laifi abin k’yamata ga duk wani d’an adam mai hankali...!Ta yaya za’ace ahalinsa sun aikata irin wannan laifi...! Shin wannan wane irin al’amari ne...! Barde ya k’araso cikeda risinawa yana fad’in “Rankaidad’e a k’araso da motar nan ne..? Allah shi baka yawan rai nace a k’araso da motar nan ne...?!” Barde yaji Mahmood d’in bai basa amsa ba bai kuma dakata ba saima ci gaba da tafiya da yake...!
Barde ya d’ago kai yana duban Ubangidan nasa, sosai ya razana da ganin yanayin Mahmood d’in wanda Tafiya kurum yake ba tareda yasan yanda yake jefa k’afafunsa ba...
Cikin sauri Barde ya ciro waya ya shiga kiran layin Turaki....
Turaki na d’agawa Barde ya sanar dashi halinda ake ciki, babu b’ata lokaci Turaki yace yana nan tafe...!
Mahmood kaw hotunan abinda suka faru can shekarun baya ne Ke dawowa idanunsa, dukda bazaice ga kamannin yarinyar ba yana hangota a idon zuci.. Maiyasa ya tafi ya k’yale ’yan uwansa da yarinyar..? Maiyasa bai tsaya ya kaita gida da kansa ba..? Maiyasa ya aminta da cewa ‘yanuwansa bazasu cutar da ita ba..?! Fyad’e fyad’e., mummunan laifin da yafi k’ymata a rayuwarsa, yau sai ga ahalinsa Sun aikata hakan kuma Wai bisa jagorancin mahaifiyarsu..! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!! Yanaji shid’in kaman ba d’aya bane daga cikin ahalin, ta yaya ahalinsa zasu zamto irin wad’annan mutanen.. Koda shike mutum ba shi yake zab’an ahalinsa ba amma kam tabbas da ace zab’a ake da bazai zab’i ya fito cikin irin wannan ahalin ba...! Yana tsaka da tinanin idanunsa suka sauk’a b’angaren emergency.. Ashe har ya k’araso emergency tin daga psychiatric ward da k’afafunsa ba tareda ya sani ba.. Barde na nan biye dashi duk yanda ya saka k’afafunsa.... Yana kallon yanda ake guje gujen d’auko gado mai tayu na d’aukan majinyata ana turawa zuwaga k’atuwar ambulance dake pake tana bada sautin taimakon gaggawa...!
Ganin mutanen yake kaman daga can nesa nesa suke, haka nan sautin mutane da sautin motar yana jinsu kaman daga can wani nisan duniya suke...! Shid’in yana jinsa ne kaman wata duniya ta daban yake... Gaba d’aya baisan mai yakeji ba..!
Can ya hango ana wucewa da mutanen ana koran jama’an dake cike wajen.... A gefe guda ya hango Waziri da wasu dogarai kusan guda hud’u, dogaran suka k’araso garesa cikeda risinawa suna kwasan gaisuwa wajen Mahmood d’in da har lokacin ya kasa katab’us Waziri ne ya k’araso yana kuka shar shar da hawaye yake furta “Rankaidad’e Yarima Yazeed ne..! Yarima Yazeed da ahalinsa sun gamu da mummunan had’arin mota gaba d’ayansu suna cikin mawuyacin hali....!”
Mahmood baikaiga magana ba Dr guda ya k’araso garesu cikeda risinawa ya dubi ahalin Babban Gida yace “Munada buk’atan jini ga Yarima wanda za’ayi gaggawan masa aiki dan tsaida jinin dake zuba jikinsa kafin a iya rasashi...!”
Waziri yayi saurin cewa “Su kuma ahalin nasa wane hali suke ciki Likita..?!”
Dr yace “Bazamu iya cewa komai a halin yanzu ba har sai lokacin da sakamakon gwaje gwaje ya fito, amma a halin yanzu duk suna ciki ana basu agaji na gaggawa.. Abinda kawai zamu iya sanar daku shine ku shirya ma faruwan koma menene...!”
Waziri yaci gaba da salati yana kwarfe gumin dake kuma keto masa....
Nan cikin emergency d’in suka shige suna jiran bayani daga likitocin... Bayan an auna jininsu koda wanda zai dace dana Yazeed, Jinin Waziri shine ya dace da Jinin Yazeed, Jinin yayansa Mahmood bai matching nasa ba... Take aka shige da Waziri aka zuk’i jininsa, Mahmood bai kawo komai a ransa ba hasalima tashin hankalin da yake ciki ya wuce gaban ya tsaya tunanin ya akayi jininsa bai matching na d’an uwansa da suka fito ciki guda ba sai na Waziri... A haka Turaki ya k’araso ya taddasu cikin tsananin damuwa shima
Tinda Turaki yaga yanayin Mahmood dukda kuwa k’arfin hali irin nasa yasan ba k’aramin al’amari bane Ke damunsa, kodashike yanayin da Yazeed da ahalinsa kad’ai Ke ciki sun isa su jefa Mahmood d’in cikin irin wannan yanayi... K’urama waje guda idanu kurum yayi kalaman Fu’ad na kuma Yawo a kansa, mahaifiyarsa tayi umarni ma ‘yan uwansa suci zarafin k’aramar yarinya su lalata mata rayuwa kawai sabida son duniya da Mulki... Mulkin Duniya da babu wanda zai tabbata akansa..! Wannan tashin hankali da mai yayi kama.. Koda yake Spain yana d’aya daga cikin founders na wani foundation wanda suka gina dan k’wato hakki da kuma taimakawa mata da k’anan yara maza da mata da akaci zarafinsu Ta hanyar fyad’e... Yau sai gashi nan laifin da ya jima yana yak’a a k’asar Spain cikin gidansu, cikin ahalinsa.. K’annensa ‘yan uwansa da suka fito ciki guda sun aikata irin wannan laifin da ya k’yamata tsawon rayuwarsa bisa son zuciya da umarnin mahaifiyarsu..! Ya lumshe idanunsa a hankali zuciyarsa na kuma masa zafi...Yana tsaka da tinanin ya sinkayo muryar Turaki yana fad’in suje suyi sallah su dawo, dan lokacin kiraye Kirayen sallan la’asar ake...
Babu musu ya mik’e yabi bayan Turaki dake masa jagora...! Koda sukayi sallah nan cikin masallacin dake emergency d’in sun dawo sun tadda har lokacin ba’a fito daga aikin da akewa Yazeed ba... Yaransa guda biyu ma duk aiki ake masu na gaggawa domin ceton rayuwarsu....
Can kusan magrib dan har an soma kiraye kirayen sallah wasu likitoci guda biyu suka fito suna zane hand gloves d’insu nurse mask...!
Waziri har yana tuntub’e ya nufesu yana tambayan jikin Yazeed ko na yaransa...
Dr ya k’araso har gaban Mahmood wanda shima ya mik’e tsaye yana jiran abinda likitocin zasu ce....
Likitan ya d’an risina yace “We did everything we could your Highness... But we couldn’t save any of his children...! They’re both gone...!”
Rintse idanunsa yayi a hankali d’aukacin mutanen dake wajen suna masu furta Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..!
Mahmood ya fitar da huci a hankali kana yace “And Yazeed... How’s he Dr...?!”
Dr ya d’an dubesa sai kuma yace “Kana iya biyoni domin kaga halinda yake ciki Rankaidad’e...!”
Babu musu Mahmood yabi bayan likitan, kwance ya hango Yazeed saman gado na’ura ko ta ina a jikinsa....
Mahmood yayi tsaye yana duban yanda halittan d’an uwansa Yazeed ya koma cikin sa’o’I k’ank’ani, ya tuna rabuwarsu a daren jiya lafiya lou yake da cikan halittarsa ba kaman yanzu da halittarsa ta sauya ba kuma bazata tab’a dawowa kaman da ba... Hak’ik’a ba’a gama halittan bawa ba har sai randa ya komaga mahaliccinsa, kar ka zamto mai d’agawa da nuna kai wani ne dan kaid’in ba kowa bane, cikin k’ank’anin lokaci labarin rayuwarka zai iya canzawa...!
Muryar Dr ya sinkayo yana furta “Yanda ya rik’e steering wheel haka hannayensa suka dagargaje tareda steering wheel d’in, we had to amputate both his hands...!”
Mahmood yai K’uri yana duban gundulumin hannayen Yazeed dage d’aure da bandage duka biyu tun daga elbows d’insa.. A hankali ya sauk’e ajiyan zuciya yana mai kuma jinjina lamarin...
**
Can d’akin da ya ganawa Jakadiya azaba suka aje Muhibbah.. Saman kujeran da ya d’aure Jakadiya saman Kujeran ya d’aureta itama, saidai ita d’aurin da ya bada igiya bane kaman yanda yayiwa Jakadiya da handcuffs ya d’aureta yanda ko motsi mai kyau bata iyawa...!
Giwa ta Washe idanu tana duban yarinyar zuciyarta naci gaba da tafarfasa..! Duk itace silan komai, Ta tabbata itace Ta janyo duk halinda suka tsinci kansu cikin Masarautar.... Ta dubi Jakadiya dake tsaye rik’eda ruwa cikin bucket tace “Jakadiya..!”
Jakadiya ta risina tana mai furta “Allah shi taimakeki..!”
Giwa taci gaba da fad’in “shek’a mata ruwan nan ta bud’e idanunta..!!”
Babu musu Jakadiya tayi yanda Giwa tace, ta watsawa Muhibbah ruwan mai matuk’ar sanyi tun daga tsakar kanta har zuwa k’afafunta tana mai furta “Tashi Munafuka..!”
Aiko nan tayi wani irin jan dogon numfashi ta bud’e idanunta da suka mata matuk’ar nauyi da k’yar tana jinta gaba d’aya a tamke...!
A hankali Ta ida ware idanun nata yanda taga Giwa, Jamal da kuma Jakadiya tsartsaye gabanta dukansu Uku sun zuba mata idanu....
SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*
*69*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Cikin tsananin huci Giwa Ke furta “Da kyau..! Da kyau d’ahnah..! Kai d’in ka cika jinina, ka cika min alk’awari ka kawo min wannan ‘yar lek’en asirin har tafin hannuna...!!”
Jamal dake dafe da sandarsa idanunsa naga Muhibbar shima yake furta “Maami I told you so.. Na fad’a miki zan kawo miki ita har yanda kike, ban tab’a disappointing d’inki ba Maami...!”
Giwa ta jinjina kai tace “Ina matuk’ar alfahari dakai...!” Ta kuma duban Muhibbah wacce Ke sakin huci tana dubansu da idanunta wanda tuni sun rikid’e sun koma jazir ga ruwan da Jakadiya ta watsa mata sai faman d’iga yake a fuskarta...
Take Giwa ta soma takowa gabanta cikin tsananin huci, saida ta k’araso har gaban kujerar da Muhibbah ke d’aure bisa kana ta bud’e murya tace “Ke k’aramar alhaki, ki sanar damu waye ya turoki Masarautar nan..! Ma waye kike lek’en asiri cikin Masarautar..?! Wacece Ke..?! Su waye shuwagabanninki..?! Daga wace masarautar kike..?!”Ta k’arashe tana mai kamo hab’ar Muhibbah ta d’ago fuskarta da k’arfin gaske...
Muhibbah bata daina huci ba tana aika ma Giwa kallon k’yama take furta “Maiyasa kike tunanin zan sanar da azzaluma irinki ko wacece ni..?!”
Take Giwa ta d’auketada wani irin jahilin mari wanda saida ya tsaga mata leb’en bakinta jini ya fito... Muhibbah ta rintse idanunta sabida azaba, Giwa zata kuma kai mata wani marin Jamal ya dakarta da ita da fad’in “Haba Maami just mari won’t make her talk, har yanzu ita d’in ji take wata babbar k’waro ce tinda har ta Iya shigowa cikin Masarautar nan ta tashi duk wani bomb data dasa ba tareda wani ya fahimceta ba, har Ta iya Sa k’afa Ta tsallake ta gudu, hakan bai isheta ba ta zabi ta kuma dawowa...! Zaifi kyau idan kika mik’a min ragamar hukuntata, Ina mai tabbatar miki nan bada jimawa ba zata bud’e baki tai magana harda abinda ba’a tambayeta..!”
Giwa na sakin huci take furta “Na baka wuk’a da nama Jamal, kayi mata duk wani nau’i na azaba da kakeda tabbacin zaisa ta bud’e baki ta fad’i ko wacece ita da kuma abinda ya kawota cikin Masarautar nan...!!”
Jamal ya murmusa kana yace “Godiya nake Rankidad’e Giwa, hukuntata zai bani pleasure sabida ta shiga gonata..!” Ya kuma kai dubansaga Jakadiya yace “Jakadiya..!”
Jakadiya ta yada kai tana mai amsawa da “Rankaidad’e..!”
Jamal yaci gaba da fad’in “Ki mik’o min jakan kayan aiki na..!”
Babu musu Jakadiya ta jinjina kai tana mai furta “An gama Rankaidad’e..!”
Jakadiya ta tafi mik’o kit d’in Jamal tana mai furta “Yarinya yau ranar ki ce, bayan bani mayafi da kikayi kika k’ala min sharri banci miki ba ban sha miki ba gashi nan zaki girbi irin ukuban da kika sakani ciki..!!”
Ta k’arashe tana mai aje kit d’in gaban Jamal wanda har lokacin bai janye idanunsa daga kan Muhibbah ba..!
Tsoro da firgici suka cika Muhibbah ganin irin takarcen mugunta da zalunci dake cikin jakan da Jamal yai umarni ta mik’o masa... Tana gani ya soma ciro allurai da wasu k’arrafa saikace wanda zaiyi aikin kanikanci...!
A idonta ya soma had’a wasu ruwan allurai yana zira su cikin doguwar syringe irin wanda ake amfani wa dabbobi dashi.. Ta tina ire iren syringe d’in da suka gani a d’akin da ya rufe Jafar, badai itama tura mata wad’annan ruwan bala’in zai ba.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Abinda zuciyarta Ke iya nanatawa kenan dukda k’irjinta dake tsananin bugu, gashi ko motsi mai kyau bata iya yi dan d’aurin handcuffs Jamal yayi mata, harta k’afafunta suma ya d’aure cikin k’araffa yanda ko kusa bazata iya tunanin guduwa ba... Allah kawai take ambato ya ceceta daga hannun wad’annan azzaluman bayi nasa dan tasan shi kad’ai ne zai ceceta..!
Jamal ya nufota da alluran muguwar murmushi saman fuskarsa..! Girgiza kai Muhibbah take tana hawaye bakinta bai daina ambaton Allah ba..! Giwa kuwa fad’i take “Danna mata alluran Jamal, nace kada ka ragar mata ka danna mata ya shiga tin daga kwanyarta har izuwa k’afafunta..!”
Jamal yai wata murmushi na mugunta yana tsaye gaban Muhibbar yake fad’in “Kinga wannan alluran, Ina miki ita shikenan gab’ob’inki Sun tashi a aiki...! Ban tab’a yiwa kowa irin wannan alluran ba a kanki zanyi lunching d’inta..! Allura ce wacce idan na miki ita shikenan kin koma saidai kallo da idanu, babu wani joint na jikinki da zai kuma motsawa, komai saidai ai miki.. Idan har kika sake allurar nan ta huda jikinki shikenan you’ll be paralyzed for the rest of your life...! So I’ll still ask you nicely... Who are you..?! Wacece Ke...?! Wane ganganci ne ya shigo dake cikin Masarautar nan..?!”
Dukda tsananin tsoron abinda ka iya zuwa yazo gameda ita hakan bai hanata murmusawa ba tana mai furta “I’d definitely tell you who I’m Dark Prince..! Mai kake ci na baka na zuba..!? But before then, kafin na sanar dakai ko ni wacece sai na tabbata rayukan da suke cikin had’ari a Masarautar nan sun kub’uta... Ka fahimta..!”
Jamal bai daina huci ba yake dubanta da tsananin mamaki, rashin tsoronta sosai ya basa mamaki tana a matsayin mace, kodashike abinda tayi ko mazan ma ba kowa ne zai iya kasadan da tayi ba, ta tsallaka ta shigo Masarautar ta kuma shiga jikin ahalin Masarautar ba tareda sun fahimci motive d’inta ba...
Hannu ya d’aga zai kwad’a mata mari sai kuma ya dakata yana murmushi, lokaci guda yace “Kafin ki zuk’i ruwan allurar nan ya kamata a soma cire wasu parts na jikinki dan idan kinyi paralyze abin bazai maki wani ciwo ba, gwara kinaji kina gani da lafiyarki a soma rabaki da wasu sassa na jikinki, zan kuma fara da bakin ki, I’ll cut off your tongue sai muga da bakin da zakiyi tsaurin ido...!” Ya k’arashe yana ciro wasu k’araffa cikin akwatin nasa...
Giwa ta katsesa da fad’in “Ai idan ka yanke harshenta bazamuji mai ya kawota ba, ka dai soma da wasu sassa na jikinta kaman yatsun hannayenta zuwa k’afafunta, na tabbata idan taji zogi da azaba zata yi magana..!”
Jamal ya jinjina kai yace “Zan iya farawa da murafen kunnuwanta Ta yanda zataji abinda zamu sanar da ita da kyau...!” Ya k’arashe yana ciro wasu k’araffan...
Zuciyar Muhibbah bata daina tsinkewa ba ganin da gaske wannan mugun yanka sassan jikinta yakeda niyya... Allah kawai take ambato had’ida kauda fuskarta gefe, ta tamke idanunta sosai zuciyarta naci gaba da tsananin bugu tana jira taji ya kama marfin kunnenta guda kaman yanda yace....
Kaman daga sama wayar salulansa ta soma ringing.. Aje k’araffan yayi ya soma k’ok’arin lalumo wayarsa cikin aljihun wandonsa, number ce mai kiran nasa, yana d’agawa aka sanar dashi halinda Yazeed da kuma ahalinsa Ke ciki a asibiti...!
Zuciyar Jamal ya tsinke, ya d’ago yana duban Giwa... Ganin irin duban da yake mata ya sanyata maida hankalinta kacaukam garesa tana tambayarsa meke faruwa...
Hankali tashe Jamal Ke sanar da ita abinda aka sanar dashi a wayar... Take jikin Giwa ya d’auki rawa, cikin yanayi na tashin hankali take furta “Yazeed..! Yazeed.. Yazeed d’ah nah, zanje na gansa yanzun nan... Ina son ganinsa...!” Bata kuma tsayawa bi takan kowa ba Ta nufi k’ofa hankali tashe...
Tuni Jakadiya ta take mata baya, Shiko Jamal duban Muhibbah yayi yace “Allah ya ceceki for now, amma ki sani ina nan dawowa, sai kin d’and’ani azabata..! No one messes with me...!!”
Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice yana cangwala sandarsa...
Muhibbah da hawaye Ke zubo mata sauk’e ajiyan zuciya tayi wasu hawayen na muma kwaranyo mata, ta soma jijjiga kujeran ko Allah zaisa cuffs d’in su b’alle.. Inaa ko gizau batayi, wasu hawaye masu d’umi suka kuma zubo mata... Toh kenan basu ne suka ajeta wancan d’akin ba... Kenan babu saka hannunsu a dawowarta Masarautar..! Toh waye ya dawo da ita idan har ba Giwa bace ba kuma d’aya daga cikin azzaluman yaranta bane..?! Tambayar da zuciyarta tai mata... Toh amma taga Yarima Mahmood a wannan d’akin da aka ajeta..! Toh mai ya kaisa d’akin..? Kodai shine ya satota..? Toh amma mai zaisa ya sato ta ya dawo da ita cikin Masarautar ranan aurenta idan dai har baiyi tarayya dasu Giwa wajen yunk’urin cutar da ita ba... Shin waye zai iya warware mata k’ullin dake cikin kwanyarta..?! Ta kuma lumshe idanunta a hankali wasu hawayen suka gangaro mata, tasan duk yanda akayi Mommy da Ansar suna can suna nemanta, ta sani hankulansu ba’a kwance yake ba kaman yanda nata ma bai kwance... Allah taci gaba da ambato domin ya kawo mata d’aukin halinda Ta tsinci kanta ciki....
**
D’aki Jamal ya dawo domin shiryawa dan shima dole ya nufi asibiti yaga halinda Yazeed Ke ciki...!
Sauri sauri ya kwab’e k’anan kayan dake jikinsa ya zira jampa, Umaima da tun shigowarsa idanunta biyu kikimau ta kumayi tamkar har lokacin bata farfad’o ba.... Tana jin sanda ya ida shirinsa ya k’araso gareta ya manna mata peck a goshi yana mai furta “I’ll be right back my love...! Zan dawo na d’aukeki muyi nesa da wannan Masarautar... Na tanadar mana rayuwa mai kyau sweetheart... You just need to trust me Umaima, zan baki rayuwar data dace dake..! I Wait for me kinji love..!” Ya k’arashe yana mai gyara mata kwanciyarta dukda cewa d’aure take da jikin gado...!
Jamal na ficewa wasu irin hawaye masu tsananin d’umi suka gangaro mata, Ta bud’e idanunta da sukai matuk’ar mata nauyi tana k’arema d’akin kallo... Wani irin d’auri yayi mata hannu da k’afafu yanda zai matuk’ar wahala tai escape...! Take ta kuma fashewa da wani irin kuka wanda bata San na menene ba, na kasancewar wannan azzalumin mutumin a matsayin mijinta ne ko kuwa na tausayin halinda ta tsinci kanta ciki ne..! Maiyasa bata saurari Muhibbah ba tin daga farko k’ila da yanzu daga ita har Muhibbar Sun kub’uta, gashi bata San duniyar da yakai Muhibbah ba, koma tana raye ko ya kasheta sai Allah..! Ta kuma rintse idanunta wasu hawayen masu matuk’ar zafi suka gangaro mata... Tana tsaka da kukan ta hangi wani abu Can k’asa saman rug, kaman waya kaman kwali.. Saidai bazama Ta iya mik’ewa ba balle ta isa ga abun... Ta shiga k’ok’arin janye jikinta tana yunk’urin d’aga kanta, nan Ta hangi tabbas waya ce.. K’ila k’aramar wayar Jamal d’in ce ta fad’i garin sauri da yake don shiryawa...! Ta shiga k’ok’arin jijjiga hannayenta da k’afafunta ko Allah zai bata sa’an kwance d’aurin... Inaa ko motsawa batayi, gadai waya tana hangowa nan k’asa kusan k’afarta amma bazata iya janyowa ba sabida d’aurin da aka mata.. Ta kuma rintse idanunta hawaye naci gaba da gangaro mata...
**
Tashin hankali maras misaltuwa Giwa ta tsinci kanta ciki sanda taga halinda Yazeed yake ciki, da gaske dai Yazeed d’in dataci masa burin zama Sarki shine kwance saman gado babu hannaye...
Yazeed ya rasa hannayensa ya kuma rasa ‘ya’yensa duk a sabida bak’in zuciya irin nasa... Wannan rayuwa da mai yayi kama, abin bazai kuma masa ciwo ba har sai randa ya bud’e idanu ya gansa a halinda yake ciki kuma shine yayi silan faruwan komai, shine yayi silan rasa hannayensa da mutuwar yaransa gaba d’aya... Lallai tashin hankali na gaba gareshi...
Jamal ma sosai hankalinsa ya tashi da ganin halinda Yazeed ya tsinci kansa ciki, dukda ya rasa k’afarsa gani yake nasa mai sauk’i ne tinda gashi har za’ai masa wata k’afar, shi kuwa Yazeed babu hali ayi masa hannaye haka zai k’arashe rayuwarsa babu hannaye bazai iya yiwa kansa komai ba saidai ayi masa dukda kuwa pride da jin kai da isa irin nasa...
Cikin tashin hankali Giwa ta isaga Mahmood da tin shigowarsu asibitin kallon kirki bai shiga takaninsu ba saima kai komo da yake da likitoci suna updating nasa halinda Matar Yazeed da Handimarta Ke ciki... Ga dukkan alamu Hadimar nata itama Allah ya amshi rayuwarta amma matar Yazeed ta rayu, anyi gwaje gwaje akanta kuma babu wani internal injury data samu saidai wad’anda idanu ka iya gani, babu wani fracture data samu saiko buguwar k’ashi, a halin da ake ciki Zuhra tana d’akin hutu tana ci gaba da samun kulawa dan har kawo zuwa lokacin bata farfad’o ba bayan gwaje gwaje da akai mata...
Likita da Mahmood suka gama tattaunawa, Mahmood ya saka hannu a takardan amsan gawawwakin ya kuma yin sallama da likita...!
Tinda Giwa taga Mahmood bai ko bi takanta ba tasha jinin jikinta tasan duk yanda akayi wani babban al’amarin ya faru...
Dakatar da Jakadiya tai kana tabi bayan Mahmood d’in kafin ya b’acewa ganinta, can daidai wani lobby yanda babu mutane Giwa ta cimmasa, sunansa ta kira amma bai tsaya ba saima ci gaba da tafiya da yake... Ta d’an kuma d’aga k’afa tana mai furta “Sadauki ka saurareni..!”
Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba zuciyarsa naci gaba da tsananin zogi, Allah ya gani dukda ta kasance mahaifiyarsa ko fuskrta bai k’aunar gani... Giwa ta k’araso tana furta “Haba Sadauki..! Ya ina maka magana kana kuma tafiya.. Sadauki ba kai kad’ai bane halinda Yazeed da ahalinsa suka tsinci kansu ciki ya d’aga ma hankali, dukkanmu nan hankalinmu a tashe yake.. Kai d’aukacin masarauta hankali a tashe yake...! Ni fah mahaifiyarsa ce har kana tunanin zaka fini shiga damuwa Mahmood..?! Mahmood anya babu wani abinda ke damunka d’ah na.. Ka sanar dani.. Haba Mai Martaba Sarki mai jiran gado..!” Ta k’arashe cikin kwantar da murya...
Juyowar da zai, yanda Giwa taga k’wayar idanunsa da yanayin fuskarsa ba k’aramin firgitata yayi ba, yau d’in sai ya koma mata tamkar AbdulJabbar ranan da asirinta ya tonu a idanunsa, domin kuwa wani kamanni ne na musamman ya kuma fitowa tsakaninsa da Mahaifin nasa...
Cikin kakkausar murya Mahmood ke furta “Sarki..! Sarki..! Mai za’ayi da Sarautar da aka gina kan zalunci...? Mai za’ayi da sarautar da akaci zarafin wad’anda basuda hakki dan a tabbatar da samuwar wannan sarautar..! Ki fad’a min Maami
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 46 Chapter of 65