Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma dubanta da mamaki kana tace “Mai ya kawo Juwariyya cikin batun nan Aunty..?!” Murmusawa Gimbiya Zeenatu Ta kumayi kana tace “Itace solution d’inmu... Itace zamu umarta ta bincika mana komai gameda Muhibbah... Idan muka San ko wacece ita kaita k’asa bazai mana wuya ba, dan ni ban yarda da wannan Muhibbar ba...!” Raheema ta saki murmushi cikeda jin dad’i “Gaskiya Aunty Ke d’in ta dabance, badon Giwa ta rigaki shigowa gidan nan ba da anyi shu’umar Sarauniya.! Toh amma do you think we can trust Juwariyya..?!” Murmusawa Gimbiya Zeenat ta kumayi tana mai zama cikin kujerar lilonta, tana juyi bisa take fad’in “Ai a halin yanzu babu wacce zamu yarda da ita samada Juwariyya tinda har ta juyawa ahalinta baya dan cikar burinmu... Karki mance duk wani information kan Yayanta ita ke kawo mana, so na tabbata bazamu samu matsala da ita ba....!” Murmusawa Raheema tai kana tace “K’warai kuwa Aunty shawarinki yayi..!” Suka kuma duban juna a tare suna masu sakin murmushin cin nasara.... *** Zagaye d’akin take faman ci gaba da yi waya manne kunnenta tana mai ci gaba da fad’in “Ansar please pick up... Pick up please... Ina tsananin buk’atar shawarinka...!!” Har saida wayar ta kusan katsewa Ansar ya d’aga yana mai furta “I can see someone’s already missing me, Sorry wanka na shige ban jima da isa masauk’i ba na tsaya restaurant nayi takeaway... Do you want some... Na kawo miki...?!” Yai maganan teasingly... Katse wasan nasa tai da fad’in “Ansar akwai matsala....!” SameenaAleeyou 📚 [7/1, 10:39 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *026* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Gathering natsiwarsa yai waje guda yana mai furta “Ina saurarenki... Meke faruwa...?” Fuzar da fuci tai a hankali tana mai zama cikin gado “Ansar Mahmood yana so ya dasa cameras in every angle cikin Masarautar... I mean he can’t do that... Zai b’ata min shirina, bayan babu abinda na fara...” Ta k’arashe cikeda damuwa... Lokaci guda ya isa ya zauna bakin gado yana mai furta “What..! Hibbah you need to leave that place right away, muddin aka saka cameras you’d definitely get caught..!” Jinjina masa kai tai kaman yana kallonta kana tace “What do I do now Ansar... Mai zanyi na hana yuwar hakan...?!” Fuci ya fuzar a hankali kana tace “Muhibbah ki bar maganan mission d’in nan naki... Abubuwan da suke faruwa sign suke nuna miki cewa akwai matsala gaba... Before everything gets out of hands let’s leave, tun ban bar cikin garin nan ba... Zanzo ni na d’auki, mu koma gida...!” Katsesa tai da fad’in “Haba Ansar, kai saikace ba namiji ba, sai gashi kaman ka cire tsoro da shakku cikin sai kuma ka sake komawa ruwa..!” Shima ya katseta da fad’in “Dik abinda ya shafeki Muhibbah bazan masa tinani d’aya ba.. I’ll think through and think through and think it through... Karkiga laifina sabida banso ki shiga matsala ne....!” “Are you saying na ajiye makamaina na bika mu koma gida, what about the justice that I deserve..? So kake na tafi na mance komai..!?” Cikin kwantar da murya yake fad’in “Ba nufina ba kenan Muhibbah... Nafi kowa so Ki samu adalcin da kika cancanta duk duniyar nan...!” “Idan gaskiya kake fad’in then ka dena sare min gwiwa with your negative thoughts...!” Ansar ya fuzar da huci, cikin b’acin rai yake furta “Ni ban hanaki aiwatar da komai ba... From the very start, I’ve done nothing but supporting you, amma abinda nakeso ki gane a nan shine dik abinda zakiyi do it the right way...think it through first Muhibbah.. Idan Ke baki damu da kanki ba wasu sun damu dake..!!” Cikin tsananin b’acin rai take furta “You know what...! I should not have called you, you aren’t helping at all... Zanyi abuna yanda na tsara ba tareda neman shawarinka ba.. Goodnight.!!” Ta k’arashe tana mai katse kiran... Shiru yai had’ida k’urama waje guda idanu... A hankali ya fuzar da fuci mai tsananin d’umi had’ida shafe fuskarsa da duka tafukan hannayensa biyu.... A b’angaren Muhibbah kaw zama tai dirshan saman gado tana tinanin mafita... Ita yanzu bama saka cameras a fada ba, mai zai faru idan Mahmood nada shakku da kokonto akanta ne..? Zahra..! Itace Ta fad’o ranta... Lokaci guda ta mik’e ta soma shiri kana ta nufi sashen Giwa.... Saidai a bakin k’ofan parlornsu Zahra taja ta tsaya sakamakon sauraro muryar Zahra cikin kuka tana fad’in “Paa you actually take that woman’s side..? Paa banifa na k’onata ba, bani naji mata ciwo ba... Ita da kanta taji ciwo ma kanta... and Paa...” Cikin tsananin k’unan rai ya katseta da fad’in “Just shut up Zahra... Ban miki wannan goyon ba, rashin kunya ba d’abi’arki bane... First thing in the morning zakije ki baiwa Raheema hak’uri...sannan kiyi alk’awarin bazaki sake abinda kika aikata ba....!” “Really now Paa... You believe that woman over your own daughter...? Paa that woman is a liar.. She is a hypocrite...” “Zahraa..!!” Ya daka mata uban tsawa yana mai k’ok’arin d’auketa da mari... Muhibbah tai saurin shigowa ta shige tsakaninsu had’ida rungume Zahra lokaci guda take furta “I’m sorry your Highness, I didn’t mean to interfere...But please don’t hurt her she’s still a kid...!” Tsaye kurum yai yana mai ci gaba da sakin huci, jijiyonsa sunyi rud’u rud’u sabida tsananin b’acin rai... Gaba d’aya itakam Muhibbah ma tsoro ne ya rufeta ganin yanda Mahmood ya koma lokaci guda, babu yanda Ta iya ne dole tai hakan badon haka ba da koda wasa batai gigin shigowa har ta shige tsakaninsa da Zahra ba... Cikin tsananin huci yake nuna Zahra yatsa kaman zai magana sai kuma ya juya yasa kai ya fice daga d’akin gaba d’aya... Zahra ta kuma shigewa jikin Muhibbah tana mai ci gaba da sakin kuka.... Muhibbah kuwa sosai ta rungumeta tana kuma lallashinta, cikin zuciyarta take ayyana cewa ko shakka babu goyon turai akaima Zahra, wannan zai bata dama ta shawo kan yarinyar cikin sauk’i ta tarwatsa mahaifinta.... Ta saki murmushi a hankali tana mai ayyana yanda Mahmood zaisha kunya ya kuma fad’i k’asa warwas a bainan jama’an sa.... Lokaci guda ta kuma janyo Zahra suka zauna saman gado tana mai furta “Is ok Zahra... Kukan nan ya isa haka, maza share hawayenki kinji koh....!” Zahra ta d’ago tana dubanta da idanunta masu zuban hawaye lokaci guda take furta “My Paa has changed, bai tab’a d’aga min murya ba sai gashi yau har zai maren all because of that witch...!” Ta k’arashe tana mai kuma tintsirewa da wani kukan... Bubbuga bayanta Muhibbah keyi a hankali tana fad’in “Kukan nan ya isa haka Zahra, karkiyi saurin yanke hukunci kan mahaifinki... Abinda ya fad’i maki gaskiya ne, ya kamata kije ki baiwa Raheema hak’uri.... Ba’a San d’iya Ta gari ‘yar babban gida da raina mutane ba kinji koh...!” Da mamaki Zahra ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana dubanta kana tace “Kema kin zab’i kibi bayan wannan mayyar ne... Wllhi nayi imani ba tsakanida Allah take son Paa d’ina ba... I know she’s after something, sam bana son ya aureta...!” Ta k’arashe cikin rawar murya... Dafa hannunta kad’an Muhibbah tai kana tace “I understand where you’re coming from, it’s natural for girls like you to get jealous idan mahaifinsu zai k’ara aure, ko dan taya mahaifiyarsu kishi.....Kiyima Raheema kyakkyawan zato kinji koh... Sannan kiyi kaman yanda Paa d’inki yace... Apologies to her kinji koh...And also to your Paa..!” D’an kallon Muhibbah tai kana tace “Alright fine zanjeni amma sabida ke... Kuma tare nakeso muje...!” Jinjina mata kai Muhibbah tai tana mai kuma dafa kanta take fad’in “Sure... Zan rakaki in sha Allah kinji koh... So ki kwantar da hankalinki....!” Ta jinjina mata kai a hankali tana mai goge ragowar hawayenta... Mahmood dake tsaye daga k’ofa yana saurarensu take yaji wane irin sanyi cen k’asar zuciyarsa, ji yake Zahra na cikin aminci muddin tana tareda Muhibbah... Can k’asar zuciyarsa yakejin kwanciyar hankali da tarrayan Muhibbah da kuma Zahra, bugu da k’ari wannan kyawawan shawari da Muhibbah ke bata su suka cancanci yarinya mai shekaru irin nata... Take tinanin matarsa Aliya ya fad’o masa, tabbas ko wace uwa wannan shekarun take jiyewa d’iyarta, wannan dangerous stage ne a rayuwa da yake buk’atan taka tsantsan, shekarun teenage... Idan har Muhibbah zata kasance da d’iyarsa a haka baida haufin cewa zai sami kwanciyar hankali da yin hakan... Ya saki murmushi mai taushi a hankali kana yasa kai ya fice... Muhibbah dake satan kallon bakin k’ofan da wutsiyar idanunta murmushi Ta saki a hankali don ko babu komai tasan kwalliya ta biya kud’in sabulu, tarkonta ya d’anu.. Ta sami yardar Yarima Mahmood... Yanzu next move d’inta shine maganan dasa camera...! Taita faman sak’e sak’e cikin zuciyarta tana neman hanyar da zata b’ullowa Al’amarin... Mutum guda ne ya fad’o zuciyarta Yazeed...! Ta kuma sakin murmushi a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta... Tabbas Yazeed ne kawai zai kawo cikas a wannan shiri na dasa na’urorin d’aukan hoto masu motsi cikin gidan....! Da wannan shiri ta Kwana cikin zuciyarta da niyyan Washe gari zatai k’ok’ari ta riga Mahmood making move... Sam Zahra bata bari Muhibbah ta koma cen masauk’inta ba, haka taita mata magiya saida suka kwana tare... Ko shakka babu SHAK’UWA CE mai tsafta ke shiga tsakaninsu a hankali.... Washe gari bayan Muhibbah ta nufi sashenta ta shirya dawowa tai ta jira har Zahra ta farka bayan ta sad’ad’a asibahin fari ta ajiye likankken takarda mai d’aukeda rubutu jikin k’ofar motar Yazeed yanda dole a gani... Koda ta ijiye takardan successfully murmushi ta saki a hankali tana mai furta “You’re the only person that can ruin his plan... After all kud’in baku jituwa.. Hakan dalili ne na kuma tarwatsa tsakaninku...Da sannu zaku rasa mulkin Masarautar nan gaba d’ayanku sannan ku fice a Masarautar cikin k’ask’anci da d’ibewa juna albarka....!” Tana ida fad’in haka tai saurin gyara alkyabbarta Ta rufe fuskarta kana ta fice daga wajen gaba d’aya... Koda ta shigo duba Zahra nan Ta makara wajen taya Zahra shiryawa, daidaida kayan da Zahra zata saka Muhibbah ce ta tayata zab’e.... Gaba d’aya yarinyar ta cika da farin ciki gwanin ban sha’awa... A haka Umaima ta shigo ta taddasu tana mamakin yanda Sabo mai k’arfi ya shige tsakanin Zahra da Muhibbah lokaci guda, hakan sosai yaiwa Umaima dad’i ko dan ganin Zahra cikin Farin ciki bayan rasa mahaifiyarta da yarinyar tai... Dik mai k’aunar Zahra dole yaji dad’in kasancewar Muhibbah cikin Masarautar domin kaw ta maidowa yarinyar wani b’angare na Farin ciki data rasa sakamakon rashin mahaifiyarta da tai... Su duka ukun sukai karin kumallo Umaima Zahra da kuma Muhibbah a nan parlorn su Umaimar.... Idan ka gansu yanda suke gudanar da al’amransu del su birgeka... Muhibbah sai saka masu chapter take suna darawa kaman ba gidan sarauta ba, sosai suka baje suna jin dad’in moment d’in.... Giwa da Jakadiya ne suka taho zasu shige nan suka sinkayo hayaniyar su Zahra... Giwa ta dubi Jakadiya da alaman tambaya saman fuskarta... Jakadiya tai gyaran murya tana mai furta “Allah shi baki yawan rai ai wannan yarinya bak’uwa da akai a masarauta mai suna Muhibbah itace ta dawowa Gimbiya Zahra’u da Farin cikin data rasa...!” Ta k’arashe tana mai kuma jinjinaga shugaban tata... Giwa tai shiru tamkar mai nazari kana ta jinjina kai tace “K’warai yarinyar tanada saurin shiga zuciya banga laifin Zahra’u ba... Hakan zai kyau idan har zata zamto mai d’ebewa yarinyar kewa...!” Ta k’arashe k’asaitaccen murmushi saman fuskarta lokaci guda ta nufi parlorn su Umaima Jakadiya na biyeda ita... Muhibbah ce ta soma hango Giwa tai saurin mik’ewa alamun girmamawa kana ta risina tana kwasan gaisuwa had’ida kambaba Giwa... Giwa ta saki murmushin jin dad’i sanda su Umaima da Zahra sukai kaman yanda Muhibbah tai, abin sai ya kuma birge Giwa, tana matuk’ar son girma.. Tana son mutumin da zai bata girma ya kuma aza mata k’asa sam bata lamuntan raini shisa ba ko yaushe tasu ke zuwa d’aya da Raheema ba.... Sosai taji dad’i har k’asan zuciyarta tana mamakin yanda Muhibbah ta k’ware wajen koyi da d’abi’u da al’adun babban gida... Daga Umaima har Zahra mamaki suke yau Giwa ce ta shigo har parlornsu, ita kaw Jakadiya sam zuciyarta bata aminta da wannan k’auna da Giwa ke nunawa Muhibbah ba yarinyar da sam basu wani San tushenta da asalinta ba, ita dai sam zuciyarta bai kwanta da yarinyar ba musamman ganin yanda zuciyar Giwa dana yarinyar suka had’e waje guda tun daga had’uwar fari... Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yarima Yazeed yana dokawa Jakadiya kira dik Kuyangin dake bisa hanya k’arewa suke suna kwasan gaisuwa wajen Yazeed...Jakadiya ta dubi Uwargijiyarta kana tai mata izini ta hanyar jinjina kai.... A hanyar matakala Jakadiya ta iske Yarima Yazeed, tai saurin zubewa tana kwasan gaisuwa... “Jakadiya ina Maibabban d’aki...?!” Yai tambayar a hasale... Jakadiya ta kuma risinawa zatai magana sai muryar Giwa suka sinkaya tana fad’in “Yazeed mai kake nema da safiyar nan....?!” A cen parlorn su Umaima kaw tinda Muhibbah taji Yazeed na neman Jakadiya tasan tarkonta ne ya d’anu dan haka murmushin jin dad’i kurum ta saki tana mai tiniwa Zahra cewa anjima kad’an zasuje sashen Gimbiya Zeenatu domin neman afuwan Raheema... ** Yazeed na matuk’ar huci yake furta “Your beloved Son, the perfect one among us all yana nema ya b’ata al’adun gidan nan tun kafin ya hau mulki...!” Dubansa Giwa tai ba tareda ta furta komai ba kana ta nufi wata k’ofar yanda zai fitar dakai sararin veranda dake a saman benen... Suna shigewa Giwa ta kuma dubansa kana tace “Ina saurarenka Yazeed mai kuma Mahmood yai wannan karon...?” Yazeed ya kuma fuzar da fuci kana yace “Kan mai zaice zai saka CCTV cameras cikin Masarautar nan..? Maami hakan karya dokan masarauta ne, cin amanan tsari da tarihin Masarautar nan ne... Sannan wulak’anta babban gida irin wannan ne... Yanzu inada tabbacin cewa kin yarda Mahmood bashi ya cancanci gadon sarautar nan ba, tin yanzu tin bai d’ale Karagar ba gashi nan yana nema ya kawo sauye sauye cikin Masarautar nan... Yana nema ya rusa ya lalata duk wasu al’adu na cikin gidan nan tin shekara da shekaru... Yana neman ya kawo mana d’ab’un Yahudu da Nasara cikin Gidan... Maami Masarautar nan bazata tab’a amincewa da wannan ba sam..!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci... Giwa da taji wani irin gumi na neman keto mata, duban Yazeed Ta kumayi kana tace “Bakaji da kyau ba Yazeed... Ta ya Mahmood zaizo da batu irin wannan cikin Masarautar nan, tin iyaye da kakkani ba’a tab’a zuwa da batu mai kama da wannan ba... Hakan wulakanta ahalin gidan nan ne..!!” Ta k’arashe cikin tsananin tashin hankali... Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yarima Mahmood yana fad’in “A’a Maami hakan ba wulak’anta ahalin gidan nan bane... Hakan na nufin tsare ahalin gidan nan ne... Kuma babu gudu babu jada baya, kaman yanda ka fad’i Yazeed tabbas za’ai instilling cameras cikin Masarautar nan ta ko wane b’angare domin tabbatar da tsaro cikin Masarautar.... Abubuwa da dama Sun faru cikin Masarautar nan kuma suna kan faruwa, misalin mutuwar mahaifina da akace heart attack ne yai ajalinsa, mutuwar matata wacce gawarta kawai aka sinkaya cikin d’aki... Sannan b’acewar Ja’afar da har yau babu shi babu dalilinsa... Don’t you think duka abubuwan da na lissafa sunada connection...?!” Ya k’arashe d’aukeda alamun tambaya hannayensa hard’e Ta baya yayi tsaye gaban Yazeed su duka biyun suna fuskantar juna... Babu alamu ko gizau na shakku da tsoro a tattareda Mahmood...! Giwa kuwa tuni kanta ya soma juyawa, hankalinta yakai k’ololuwa wajen tashi, batai zaton Mahmood went far har haka ba... Lallai tayi gangancin raina capabilities d’in wannan d’an mijin nata... Mai zatai yanzu kafin Mahmood ya tono sirrikan gidan, shin anya batai ganganci uzzura masa ya dawo Nigeria ba..? Ya zata dawo dashi yazo yana yak’arta... Karfa maganan Tal’udu ya tabbata cewa Mahmood yak’i ya dawo yai da ita, dole tasan abinyi... Dole tasan yanda zatai ta takawa Mahmood birki da wannan shiri nasa da yakeyi... Muryar Yazeed ta sinkayo yana fad’in “And kana tinanin kashe maka matarka akai cikin Masarautar nan...? Ko kana tinanin kashe mahaifinmu akai...?!” Mahmood ya katsesa da fad’in “Everything is possible a gida irin wannan, d’ah zai iya kashe Uba dan ya gaji Kujeran mulkin mahaifinsa...!!” Cikin murya mai yanayi da kuka Giwa ta katsesa da fad’in “Haba Sadauki ya zakake magana haka..? So kake kace cikin ‘yanuwanka wani ne ya kashe mahaifinku dan ya gaji sarauta... Shin akan wannan mulkin ne rabuwar kai da zargi ke neman shiga tsakaninka da ‘yanuwanka, shin zargin ahalinka kake da alhakin mutuwar mahaifinku da matarka... Sadauki ban zaci haka daga gareka ba... Da zuciya d’aya nai muradin ka dawo ka amshi jagorancin Masarautar nan a matsayinka na babban Magajin mahaifinku... Da ace nasan abinda zai dawo dakai kenan rabuwar kawunanku da ahalinmu da banyi burin ka dawo ba... Bana nufinka da komai daga kai har ‘yanuwanka sai alkhairi amma bazan so naga kawunanku ya rabe ba... Mahmood kaine Babba cikinku kai ya kamata ace ka had’a kan ahalin nan sai gashi kana k’ok’arin rabawa tin ina raye balle ace Babu ni... Nayi zaton I can count on you koda bayan raina ashe nayi kuskure..!!” Ta k’arashe cikin kuka kana ta nufi saman d’aya daga cikin kujerun shak’atawa dake baje fsrfajiyan Ta zauna tana hawaye... Dafe kansa kad’an Mahmood kana ya nufi Giwa ya duk’a gabanta, cikin kwantar da murya yake fad’in “Maami baki fahimci ne... Please karki mun mummunan fahimta...” Katsesa tai da fad’in “Banaso na fahimceka Mahmood... Ka bani kunya, a koda yaushe nida mahaifinku mun zaci kaine zakabi yanda yake tafiyar da mulki da kyawawan d’abi’unsa da halayyarsa, kuma kaine zaka had’a kan ahalin gidan nan... Ashe munyi kuskure, na godewa Allah da mahaifinka baiga rana irin wannan ba tabbas da wannan maganan Naka shi zai kashesa fiyeda bugawan zuciya..!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin kuka daidai lokacinda Jamal ya shigo.... Jiki a matuk’ar sanyaye ganin mahaifiyarsu na hawaye dan ba k’aramin abu Ke sakata kuka ba, sannan ga Yayansu Mahmood duk’e gabanta ga kuma Yazeed nan tsaye gefe yana sakin shu’umin murmushin nan nasa, ya sakasu gaba yawa TV... Jamal ya dubi Yazeed yana tambayarsa meke faruwa “Yazeed what’s going on here... Why’s Maami crying..?!” Yai tambayar cikin tsananin tashin hankali... Yazeed bai daina murmushin ba saima gyara tsayuwarsa da ya kuma yi yana fad’in “Why not ask your beloved brother... The one you all think is a saint, I’m sure yanada ansar da zai baka don na tabbata shine dalilin zuban hawayen mahaifiyarmu...” Da mamaki Jamal ke duban Mahmood da tuni ya mik’e tsaye yana aikawa Yazeed wane irin firgitaccen duba... Jamal ya d’an tako kad’an yana duban Mahmood yake fad’in “Yaya mai Yazeed yake fad’i... Shin da gaske sabida kai Maami Ke kuka...?!” Kafin Mahmood yakaiga basa amsa suka sinkayo muryar mahaifiyar tasu tana fad’in “Jamal Yayanku zargin ahalin nan yake... Yana zargin ahalinsa da alhakin mutuwar mahaifinku da matarsa gashi har yana k’ok’arin dasa na’urorin cameras da zasuke hasko masa abinda ke wakana cikin gidan nan dikda ya sani cewa yin hakan wulak’anta Martaban Masarautar nan ne..!” Ta k’arashe tana mai kuma matsan k’walla... Lokaci guda Jamal ke duban Mahmood yana fad’in “No Yaya you can’t do that... Yin hakan tozarta al’adu da tarihin Masarautar nan ne... Yaya idan akan mutumin da kake tinanin ka gani jiya cikin Masarautar nan ne shisa kake yunk’urin aiwatar da wannan abu bana tinanin nima zaka sami goyon bayana... Ko wane masarauta Yaya sunada d’abi’a da kuma tasu al’adun... Abinda kake shirin yi kaman bud’e duk wasu sirrika na Masarautar nan ne da wasu kafi na tun iyaye da kakanni... Yaya I’m sorry but I don’t agree with you either..!” Ya k’arashe yana mai k’arasawa ga mahaifiyarsu ya rik’o hannunta yana fad’in “Maami muje ki huta, this isn’t good for your health..!” Mahmood yabi mahaifiyarsu da kallo har suka fice kana ya maidoda dubansa ga Yazeed wanda ke ci gaba da sakin shu’umin murmushi, lokaci guda Yazeed d’in ke furta “Slowly slowly Yaya...I’ll prove to everyone that I’m better than you, sannan ni ne nan na cancanci Karagar nan, na fara daga cikin gida zan isa har izuwaga wad’anda sukeda alhakin nad’a sarki a Masarautar nan...!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi kana yasa kai ya fice... Fu’ad dake tsaye daga k’ofa mugun kallo suka aikawa juna shida Yazeed har Yazeed d’in ya fice kana Fu’ad ya k’arasoga Yayansa Mahmood... Murmushi suka sakarma juna Fu’ad d’in na k’ok’arin gaidashi, ko ba’ace ba Kasan Mahmood k’arfin hali kurum yake... Kai a risine Fu’ad ke fad’in “Yaya dan Allah kayi hak’uri da Yazeed da halayyan da yake maka... Baka cancanci hakan ba...!” D’an dafasa Mahmood yai murmushin bai bar saman fuskarsa ba yake fad’in “Is Ok Fuad, nasan Yazeed tun yarinta... So babu wani d’abi’a nashi da yake Sabo a idanuna... Kar ka damu kaji koh...!” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’anshi... Jinjina kai Fu’ad yai a hankali kana yace “Yaya dama akwai abinda nake so na fad’a maka...!” Wanann karon cikin tsananin nuna damuwa yai maganar, tsoro da tashin hankali kwance saman fuskar Fu’ad... Mahmood yai masa K’uri kana yace “Ina saurarenka Fu’ad mai kake son sanar dani...!” SameenaAleeyou 📚 [7/4, 7:09 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *027* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kasa magana Fu’ad yai sai duban Mahmood da yake da idanunsa wanda tuni sun sauya launi... A hankali Mahmood ya dafasa “Fu’ad... Brother are you alright...?!” A hankali Fu’ad ya jinjina kansa yana mai k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa... Daidai nan Jamal ya k’araso yana sakin murmushi had’ida aikawa Fu’ad wani irin duba... Yarima Mahmood yace “Fu’ad ina saurarenka menene zaka sanar dani..?!” Fu’ad ya soma k’ok’arin saita kansa sabida irin duban da Jamal Ke aika masa, tuni ya soma ‘yan kame kame... Mahmood ya dafa kafad’arsa kad’an “Fu’ad, ka natsu ka sanar dani abinda kake son sanar dani....” Jamal ne ya katse zancen da fad’in “Yaya our little brother here wanted to tell you that he’s going back to school, zai koma makaranta yai karatunda baiyi ba a baya... Right Fu’ad...?!” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai tsare Fu’ad d’in da idanu... Fu’ad ya d’an shafa kansa kad’an yana duban Jamal, lokaci guda ya jinjina kai a hankali “Eh haka ne... Haka ne Yaya, na yanke shawari ina so na koma makaranta...!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya... Mahmood ya d’an dafasa kad’an cikeda tausayinsa kana ya janyo dokin wuyarsa irin yanda babban wa keyiwa k’ani suka nufi wasu kijeru na shak’atawa dake nan farfajiyan suka zauna... “Fu’ad nayi matuk’ar farin ciki daka yanke shawarin komawa makaranta... Kuma zan baka goyon bayana d’ari bisa d’ari kaji koh... So tell me, wane makaranta ne ka yanke shawarin komawa...?” D’an fuzar da fuci kad’an Fu’ad yai kana yace “I haven’t decided yet Yaya, ban zab’i makaranta ba tukuna...” Yarima Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “Ka zab’i dik yanda kake so kuma a ko wacce k’asa... Saidai a shawarce nafi so kayi karatun naka a nan gida Nigeria, if possible ma a jami’ar garin nan ta yanda bazakai nesa da gida ba...!” D’an dubansa Fu’ad yai cikeda k’auna kana ya jinjina kai yace “In sha Allah Yaya, and this time around I won’t disappoint you...!” Mahmood ya kuma murmusawa yana mai buga kafad’an Fu’ad a hankali kana yace “Yayi kyau Fu’ad... May Allah always be with you...!” A tare Fu’ad da Jamal suka amsa da Ameen kana Jamal ya d’an bud’e murya yace “Yaya a nawa shawarin kamata yai a tura Fu’ad can wani wajen yaje yai karatunsa zaifi bada himma samada idan yana gida...!” Bai kai aya ba Fu’ad ya shiga girgiza kai tamkar mai k’aramin tab’in hankali yake furta “No... No I don’t want to leave.... Banso naje ko ina, no.. No... I wanna study here...!” Yana maganan yana girgiza kai yana rintse idanu had’ida kame kansa.... Saurin rik’osa Mahmood yai yana k’ok’arin calming nasa yake fad’in “Calm down Fu’ad... Babu wanda zai sakaka tafiya makarantar da bakaso kaji koh... Dik yanda ka zab’a nan zakiyi ka kwantar da hankalinka...!” Fu’ad yai masa K’uri k’walla tab idanunsa yake furta “Thank you Yaya... Na gode Yaya Mahmood...!” Ya k’arashe yana mai kai masa runguma had’ida k’ank’amesa sosai kaman mai tsoron kada a rabasu.... Mahmood ya jinjina masa kai a hankali yana mai amsawa kana ya maidoda hankalinsa kacaukam kan Fu’ad dan shi bai yarda Fu’ad iyakacin gaskiyar Abinda yake son sanar dashi ya fad’i mishi, he can feel akwai abinda yake b’oyewa, yanaji cen k’asan zuciyarsa kaman akwai abinda yake tsananin damun yaron kuma yanaso ya fitar saidai baisan yaya zai ya fitar da abin ba.... But tinda yanzu Yana nan zai k’ok’ari ya taimaki d’an uwansa da izinin Allah.... Murmusawa Jamal yai yana mai dafa kafad’ar Fu’ad yake furta “I wish you all the best

Chapter 16 of 65