Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ya numfasa kad’an yace “Zan nemi wani alfarma a wajenki..!” Zuhra tai saurin d’agowa tana saurarensa cikeda jin nauyin Kalmar alfarma da ya bid’a daga gareta yana Sarki, Allah yasa ba cewa zai ta yafewa Yazeed ba..! Tana tsaka da tunanin ta sinkayo muryar Mahmood d’in naci gaba da fad’in “Banaso Raheemah ko Yazeed susan cewa nasan wannan batu ko kad’an... Zaki Iya min wannan..?!” Zuhra Ta jinjina kai tace “Bakada matsala Rankaidad’e... In sha Allah bazan tab’a sanar dasu cewa kasan komai ba...!” Mahmood ya jinjina kai a hankali yace “Kina iya tafiya..!” Ta risina tai masa sallama kana Ta fice jiki babu laka.... A hankali ya mik’e yana zaga parlorn nasa cikin taku d’aid’ai irinta masu Mulki.... ** Sauri sauri ta ida had’a kayanta kaf dan Allah ya gani bazata kuma kwana ko guda cikin Masarautar ba tinda Ta gama abinda ya kawota... Ta tabbata yanzu Mahmood bazai yarda da auren Raheema ba sannan Zuhra bazata ci gaba da zama da Yazeed a wannan masarauta ba... Auren Yazeed zai lalace Zuhra zata koma Masarautarsu tareda yaranta Yazeed zai zama baida kowa dan bayan abinda Mahmood ya gani bazai tab’a barinsa yayi sarauta ba... Kuma tayi imani idan maganan ya isa Masarautar su Zuhra babu Masarautar da zasu kuma yarda su baiwa Yazeed mata, shikenan martabansa ya zube... Zai rasa ahalinsa ya kuma rasa Sarautar, sannan Jamal ko yanayin da yake ciki ya ishesa Ta tabbata idan yayima Jakadiya horon da hankali bazai d’auka ba Umaima zatak’i amincewa da aurensa... Giwa kuwa halinda yaranta da MasarautarTa Ke ciki kad’ai ya isheta kuma tasan ko ba jima ko ba dad’e Ja’afar da Mahaukaciya Izzatu harmada Ubandoma zasu dawo sannan ne Giwa zata girbi duk abinda ta shuka...! Ta saki murmushi a hankali kana Ta janyo jakan kayanta, sauri sauri ta fice daga cikin Masarautar... Tsaye tayi daga can nesa tana k’arewa Masarautar kallo, a hankali ta furta “Alhamdulillah..! A yau ni Saudatu na kammala abinda ya dawo dani wannan Masarauta mai bak’in tarihi a gareni... Zan koma ga mutaneda suka amsheni suka maidani mutum bayan an wulak’antani anci mutuncina an tozartani...! Ni Saudatu Sabon shafin rayuwa zai kuma bud’e min tareda masoyina na gaskiya Dr Ansar..!!” Ta saki murmushi a hankali kana tasa kai rik’eda jakan kayanta... Sanda ta isa tashan mota ta samu babu motar da zata kuma tashi saidai Washe gari... Wata mata mai saida abinci bakin tasha ne Ta taimaka mata da wajen kwana zuwa Washe gari, Akai sa’a matar mai mutunci taceda ita budurwa kamanta haka bai tsari ta fito tashan motoci cikin dare ba sabida yanda duniyar Ta lalace, mugaye sunyi yawa wani dama kad’an zai samu sai ya cutarki... Muhibbah tai mata godiya sosai tace ta riga ta fito daga cikin makaranta ne kuma idan Ta koma baza’a bud’e mata shiyasa amma in sha Allah nan gaba zata kiyaye... Taita mata godiya kan taimakon da tai mata... Washe gari kuwa motar sassafe tabi zuwa garin Bauchi... ** Dandatson mutanen da ta ganine a unguwar tasu yasa gabanta mugun fad’uwa... Ko ba’ace ba taron d’aurin aure ne.. Toh auren wa ake d’aurawa..?! Tambayar da taiwa kanta zuciyarta naci gaba da tsinkewa... SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *58* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Bata iya bi Ta gaban masallacin unguwar tasu ba wanda yake babu nisa da gidansu hakan yasa mutane har k’ofar gidan nasu, ga kuma ababen hawan mutane a pappake Kota ina... Cikin sauri ta canza hanya tabi ta k’ofar baya k’irjinta naci gaba da bugawa musamman data hango Ansar tsakiyan abokansu sunata d’aukan hotuna, yasha farar shadda k’al kaman wani Ango... Jiki babu laka ta nufi cikin gidan ta nan k’ofar bayan yanda ta tadda Iya Larai na shanya... Ganin babu mutane cikin gidan nasu ya d’an sauk’ar mata da natsuwa k’ila auren d’aya daga cikin abokansa ake a unguwar... Suka gaisa da Iya Larai tai mata sannu da zuwa sai zolayanta take da fad’in “Amarya ta dawo Amarya Ta dawo...!” Wad’annan kalaman Iya Larai d’in ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba “Amarya kuma..?!” Ta nanata a hankali... Kardai hasashenta ya zamto gaskiya..?! Bata iya kuma tsayawa sauraren Iya Larai ba sai sa kai da Tai cikin gidan tana ganin hanya na had’e mata... Babban abinda ya kuma sanyar mata da jiki shine hango akwatuna da kayyaki barbaje tsakiyar parlorn da tai, Mommy da wasu k’awayenta guda biyu Anty Gudidi da Aunty Salamatu sai shirya kayayyakin suke wanda komai set biyu ne... Aunty Salamatu fad’i take “Oh Ansar mai tagwayen mata... Kaga yaro d’an baiwa... Mommy dai sai murmushi take tana Allah san barka yayinda Anty Gudidi ke faman tab’e tab’en baki tana fad’in “Ni wllhi bansan dalilin da yasa kika aje tsintacciyar mage gidanki ba Murjah... Kuma Wai har k’i k’are kice zaki had’ata aure da d’anki... Tabd’im haka kawai babu wanda yasan asalinta, yarinya ta zauna ta tsara maku k’arya kun yarda.. Waima a wace duniyar kika tsintota ne..?!” Mommy Ta katseta da fad’in “A’a Gudidi, Muhibbah ba tsintacciyar mage bace, d’iya ce kaman kowa... Sau nawa zance miki a hanyarmu Ta dawowa daga Lafia muka tsinceta can wajajen dajin garin Jos, wllhi abin tausayi b’arayin daji sun kashe Iyayenta makiyaya suka k’ona rigarsu da dabbobinsu itama suka biyota zasu kasheta Allah yasa muka tsinceta, lokacin Ansar na ajin k’arshe a Secondary sch hasalima d’aukosa mukaje can makarantarsa dake Nasarawa Lafia toh a hanya muka tsinceta, Ansar da Sabo driver na suka dage kan cewa mu taimaka mata... Muka d’aukota muka kawota gida mukai mata duk abinda ya dace har makaranta ta koma... Kuma ban tab’a danasanin rik’e Muhibbah ba musamman da yanzu zata zamto matar d’ah nah..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta... Aunty Salamatu tace “Oh Allah sarki gaskiya Hajiya Murjah kinada zuciya mai kyau, Keda kika amshi musulunci daga baya har kin fimu da muka taso cikin musulcincin zuciyar imani... Allah k’ara ire irenku masu taimako babu dalili...!” Aunty Gudidi Ta katseta da fad’in “Ba maganan imani ake a nan ba, maganar makomar d’anta muke... Wayasani koma B’arayin dajin sune iyayen yarinyar nan, haka kurum d’anki ya auri dangin ‘yanfashi azo ana haifa maki jikoki ‘yantadda babu gaira babu dalili... Shifa aure d’an asali ne... Asali ake jiye miki Murjah da abinda ka iya zuwa yazo in the future...!” Daidai lokacin Muhibbah tai sallama jiki a sanyaye, Mommy Ta fad’ad’a murmushinta “A’a Hibbatu... Lale lale barkada sauk’a...!” Ta k’arashe cikeda fari’a... Muhibbah na murmushi ta k’araso ta duk’a gabansu kanta a k’asa Ta gaidasu.... Mommy da Aunty Salamatu ne kawai suka amsa mata da sakin fuska ita kaw Gudidi a dak’ile Ta amsa mata tana aika mata muguwar kallo... Mommy tace “An gama jarabawar lafiya inji..?” Muhibbah ta jinjina kai a hankali “Eh Mommy..!” “Toh Masha Allah... Ubangiji ya baku sa’a... Kinga kin dawo a daidai ga kayyakin Ki nan da na ‘yar uwarki Hameedah...!” Muhibbah dai bata iya cewa komai ba sai sadda kanta da Ta kumayi tana k’ak’aro murmushi da k’yar... Aunty Salamatu tace “Oh Murjah bakya bari ko d’an surkunta ya soma shiga tsakaninku ba... Duk kinsa tana jin kunya... Tashi Ki shige abinki..!” Mommy Fad’i take “A’a babu wani surkunta tsakanina da d’iyata...!” Gudidi Ta katse zancen da fad’in “Ke tashi kije kin wani zauna kin tsare mutane yaran yanzu babu kunya...!” Muhibbah bata kuma cewa komai ba ta mik’e ta nufi ciki Mommy na fad’in maza tai wanka ta fito taci abinci.... Shigewan Muhibbah da kad’an Ansar ya shigo gidan ya taddasu Mommy nan a parlorn suna ci gaba da sorting kayayyakin... Aunty Salamatu Ke zolayarsa da fad’in angon wani sati ita kaw Aunty Gudidi sai yatsina baki kurum take dan Allah ya gani bata fata ayi wannan aure, ita da zata samu sarari ma zata kuma ziga Yawale koda wasa kada ya biyewa Murjanatu na aurawa d’an d’an uwansa tsinatcciyar mage... Aunty Salame ke sanar dashi Muhibbah ta dawo tana ciki... Ai tuni ya mik’e yana sosa kai tana ci gaba da zolayarsa mai tagwayen mata... Silalewa yai ya nufi corridor, yana k’ok’arin knocking kenan Ta bud’e k’ofar alamun zata fito... Sukai tsaye suna duban juna, sosai shigar manyan kayan ya amshesa dashike ba gwanin saka manyan kayan bane.... Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi kana Ta matsa Ta basa hanya ya shigo... Daga can gefe ta zauna Shiko na tsaye jikin k’ofa, Muhibbah ta gaishesa babu wani walwala tattareda ita... Harga Allah kalaman Aunty Gudidi ya tsaya mata a rai, sai tana jin tabbas Ansar bai cancanceta ba... Gyara tsayuwarsa yai yana mai tsareta da idanu “Mun d’aura auren k’awarku Azeema yau wata sati kuma a d’aura naki...!” D’an Murmusawa tai tace “Aw Wai dama auren Azeema ake..?!” Ansar ya jinjina kai yace “Eh Musbahu ya zama Ango...” Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Allah sarki, Allah yasa albarka... Ai Azeema da Musbahu sun dace da juna..!” (Azeema da Musbahu dukansu ‘yan Estate d’in ne kuma Musbahu aminin Ansar ne Azeema kuma islamiyansu guda dasu Muhibbah.. Taron aurensu Muhibbah ta tadda..) Ganin yanayinta yasa Ansar d’an nusawa yace “Kema Rana itiyau an d’aureki...!” Ta d’an dubesa da mamaki tace “Next week fah kake magana..?!” Ansar ya jinjina kai yace “Bakiga su Mommy a parlorn suna had’a lefe ba..” Ta jinjina kai a hankali tace “Na gani... Amma sai inaga next week kaman yayi kusa...!” Ansar ya d’an tako kad’an ya jinginu jikin dressing mirror yana mai karantar ta “Mai yasa zakice yayi kusa bayan cikan burinmu kenan mu kasance tare...” Gyara zamanta tai tana mai duban wani b’angaren, lokaci guda Ta fuzar da fuci a hankali tace “Ba haka nake nufi ba, ai inaga aure yana buk’atan shiri balle ma Amarya wacce aka santa da wasu ‘yan kintse kintse...!” Yana murmushi ya furta “Relax Amarya Ta to be, Baffah Yawale ne ya matsa a d’aura auren gaba d’aya next week tarewa Mommy tace ba yanzu ba sai ta gama shirin bukinta, kinga auren kawai za’a d’aura ba wai tarewa zakiyi yanzu ba... Nima gidan nawa akwai fittings da ba’a gama ba, Ki kwantar da hankalinki kina nan tareda Mommy har nan da wata guda... Ku gama duk wani shirye shiryenku da zakuyi Keda Mommy, wata guda ai ya isheku..!” Ta murmusa kad’an har lokacin babu walwala tattareda ita... Gyaran murya yai kad’an yace “Hibbah kalleni nan..!” Ta d’ago idanunta masu rauni tana dubansa “Maiyasa nake ganinki haka..? Ko baki Farin ciki ne..?!” Hawayen da ya gangaro mata tasa hannu Ta share, lokaci guda take furta “Ba haka bane Yaya Dr, gani nake kaman baka cancanceni ba... Kar ka mance Mommy batada masaniyan gaskiyar abinda ya sameni, idan nayi shiru na aureka a haka Anya na kyautawa Mommy..? Kai d’aya ne d’anta.. Mommy Ta cancanci sanin komai kafin aurenmu..!” K’arasowa yai ya d’an duk’a gabanta yana kallon yanda hawaye ke gangaro mata... Lokaci guda yake girgiza kai “Hibbah no... Ba lallai sai Mommy tasan abinda ya sameki ba, ni ne zan zama mijinki kuma naji na gani nayi accepting d’inki yanda kike... I don’t care if you’re a rape victim... Ba son ranki bane hakan ya faru dake, Maiyasa zan k’yamaceki bayan nasan k’addara na kan kowa... Su wad’anda suka aikata laifin sune ya kamata suji kunya... Hibbah I...!” Cikin kuka Ta katsesa da fad’in “Kana fad’a min haka ne dan naji sanyi a zuciyata... Amma bazan tab’a zama kaman ko wacce mace ba... Sun cuceni Sun zalunceni Sun d’auke min abinda yafi komai mahimmanci da daraja a gareni... Ansar ko baka fad’a min ba nasan dole can k’asan zuciyarka kana jin zafin abin... Maza har Uku sun lalata rayuwar macen da zaka aura lokaci guda..!!” Daidai nan Anty Gudidi Ta shigo tana tafe hannaye had’ida salallami “Na shiga uku ni Gudidi mai nake ji... Maza har uku, d’aya biyu uku... Sauransu zaka aura Ansar... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un.... Yau na shiga uku ni Gudidi ka kaita ina... Wllhi Allah ya tsari gatari da saran shuka..!!” Ansar ya tareta da fad’in “Aunty ki dakata, ki saurareni..!” Bata dakata d’in ba sai ci gaba da tafe hannaye take tana salallami tana doka kira wa Mommy “Murjah..! Murjah!! Na shiga uku ni Gudidi Toh kizo kiji abinda nakeji a nan..!!” Daidai sanda Mommy da Aunty Salame suka k’araso a firgice suna tambayan Gudidi meke faruwa... Nuni tai masu da Muhibbah dake zaune saman stool kanta kife tana hawaye Ansar tsaye gefe idanunsa sunyi jazir yana aikama Gudidi muguwar kallo.. Mommy tace “Gudidi meke faruwa kike salati haka kaman anyi rashi..!” “Yo ba gwara mutuwa ba da abinda naji... Gata nan Munafuka ta bud’e baki ta fad’i maki... Ta wane sinne kai zatai rufa rufa Ta aure miki d’ah..!” Ansar ne ya katseta da fad’in “Ya isa haka Aunty... Bai kamata Ki saka Muhibbah gaba kina aibatata ba... Babu abinda ta miki na aibu..!” “Kai rufe min baki shashasha.. Wannan ai aurenta da kake k’ok’arin yi shine babban aibu... Ace namiji ba d’aya ba ba biyu ba har uku sun gama watsewarsu da ita kai kuma da yake hidahumi ne shashasha zaka yarda ka aureta a haka har kana wani cewa ba son ranta bane..!” Cikin tsananin k’unan rai Ansar ke fad’in “Eh Aunty I don’t care idan duka mazan duniyar nan ne suka lalata mata rayuwa sabida ba laifinta bane, itama bata tab’a fatan hakan ya faru da ita ba... Akan mai za’a dinga nuna k’yama da tsangwama ga wad’anda tsautsayi da k’addarar fyad’e ya auka masu.. Shin son ransu ne..? Shin suma bazasuyi fatan su kasance kaman ko wacce mace bane..? Aunty rape victims sunada ‘yanci da zasu rayu kaman ko wata mace a fad’in duniyar nan.. Tunanin k’yama da tsangwama da zasu fuskanta tsakanin Al’umma shi yake jefa da yawa cikinsu cikin hali na ha’ula’i wasu a garin haka har kashe kansu suke sabida tsoron tsangwama daga sauran mutane... Maiyasa baza’a jasu jiki ba a nuna masu cewa rayuwa bata k’are masu ba... Zasu iya samun Farin ciki kaman ko wata mace.. Instead ki tsaya a nan kina aibata Ta a matsayinki na matar cikakken Alk’ali da taimakawa kikayi aka capke wad’anda suka aikata laifin, dan rashin hukuntasu shi zaisa gobe su kuma..!” Mommy Ta katsesa da fad’in “Ansar Wai maganan da nakeji gaskiya ne..?! Kenan Muhibbah tai mana k’arya da tace b’arayin daji Sun halak’a ahalinta...?!” Ansar ya d’an fuzar da huci yana shafa kansa yace “Mommy Ki tsaya kiji I’ll explain everything..!” Girgiza kai Mommy tai tace “Shikenan kuma ai... Kasan ni bana son mak’aryaci ko yaya ne... Balle yanda naji kana maganan fyad’e kenan Allah kad’ai yasan B’arayin daji nawa ne sukai mu’amala da ita..!” Anty Gudidi tace “Alhamdulillah abinda nake nufi kenan... Ta yaya zaki bari d’anki k’waya d’aya tol a duniyar nan ya auri wannan abar.... Wayasan mai wad’ancan kmazaman b’arayin dajin suka gama yi da ita kawai d’anki yazo ya kwashi ragowarsu... Wllhi Allah ya sawwak’e wannan ai sai ki zama abin nunawa tsakanin k’awaye...!” Mommy na tsananin huci take duban Muhibbah dake duk’e a wajen tana sharb’an kuka mai tsuma zuciya.... “Ke.. D’ago ki kalleni dan daga yanzu bazan kuma kiranki da sunan Muhibbah ba... Allah kad’ai yasan menene asalin sunanki da abubuwan da kike b’oyewa... Na rik’eki da zuciya d’aya ashe Ke ba haka kika d’aukemu ba.. Kin b’oye mana wannan babban al’amari... Toh kiji da Wai d’ah na bazai auri mace irinki ba...!!” Muhibbah ta d’ago a firgice tana duban Momy da idanunta masu zuban ruwa... Ko saurarenta Mommy bata tsayayi ba tasa kai Ta fice daga d’akin a tsananin fusace yayinda k’awayenta suka take mata baya... Ansar yai saurin bin bayanta yana ambato sunanta inaa ko tsayawa batai ba.... Muhibbah kaw tana ganin sun fice Ta maida k’ofan d’akin Ta silale a wajen tana cazgan kuka mai tsuma zuciya... Ansar ya dawo yana bubbuga k’ofar inaa bata bud’e ba sai ma shesshek’an kuka da take... ** A can Masarauta kuwa daren jiya kusan gaba d’aya mafarkai ya dingayi sarara marassa kan gado... Mafarkinsa na k’arshe ne ya tsaya masa a rai yanda suke tsaye shida ita cikin Babban Zauren ajiya na masarauta... Su duka biyu Suna rik’e da wannan Taswiran ya rik’e b’angare guda itama ta rik’e b’angare guda, kowa a cikinsu yana so ya amshe Taswiran daga hannun d’an uwansa ga Wambai daga gefe yana sakin murmushi yana kallon kokawan k’wace wannan Taswiran da Mahmood keyi hannun Muhibbah... Dik k’ok’arin Mahmood ganin ya amshe wannan Taswiran daga hannunta bai iya amshewa ba dukda cewa ya dage k’arfinsa gaba d’aya... Yana juyawa yana kallon Wambai yana cewa ya taimakesa kada ta gudu da Taswiran, Wambai sai murmushi yake masa lokaci guda yana cewa ya bita duk nisan duniyar da zatai itace zata zamto fitilar haska masa duhun dake gaba garesa... Haka ya dinga binta a guje har ta shige wani k’ofar... K’ofar tana gab da rufewa ya isa ya saka hannayensa duka biyu yana k’ok’arin janyota yana son k’wace wannan Taswiran amma bata sakar masa ba... K’iris ya rage k’ofar bai rufe ba ya farka daga baccin...! Shafe Fuskarsa yai da duka hannayensa biyu daidai lokacin da sallaman Zahra ya daki dodon kunnuwarsa... Zahra ta bisa da kallon mamaki dan bakinta na uku kenan tana sallama mahaifin nata baiji ba.... Ta k’arasa ta zauna daga can kusan k’afafunsa, Ta risina tana gaidashi... Saida ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ya amsa mata... Zahra Ta d’an muskuta tace “Paa are you alright..? You seem deep in thoughts...!!” K’uri yai mata sai kuma ya nusa kad’an ya kirawo sunanta da siga mai firgitarwa... Zahra ta d’ago a d’an tsorace tana dubansa “Paa..!” Mahmood yaci gaba da fad’in “Tell me what really happened, kuma kada kimin k’arya...!!” Zahra Ta shiga murza hannunta cikeda tsoron abinda ka iya zuwa yazo, dan yanda taga mahaifin nata sosai tasha jinin jikinta “Paa... Paa Wllhi bansan mai ya faru ba nima kawai cewa tayi idan kaje zakaga abinda zai hanaka auren Anty Raheema shisa na yarda da plan d’in nata... Amma wllhi wllhi Paa I’ve no idea what her plan was... Kawai tace I should trust her the plan would definitely work... Amma bansan menene ba... Mun shigo motar haya muka dawo masarauta tace na kashe wayata she can handle the renaming parts of the plan... Paa I’m sorry kawai banso ka auri matar nan ne..!” Tinda Ta soma magana yai mata K’uri, ya gyara zama kad’an yace “Wacece ita..?!” Zahra na muzurai tace “Aunty Muhibbah..! But Paa please kar ka mata fad’a laifina ne..!” “Muhibbah!” Ya nanata cikin zuciyarsa, yarinyar da yai mafarki da ita jiya... Toh Wai wacece ita.. Mai take nema cikin Masarautar..? Ya kamata yasan komai gameda ita... Ya jinjina kai kad’an yace “Karki damu bazan mata komai ba... Kije Ki kirawo min ita...” Zahra tace “Ai bamu ganta ba, Ta bar note wa Aunty Umaima cewa Ta gama jarabawa Ta koma gida...!” Ya jinjina kai a hankali yace “Ki kirawo min Umaima..!” Ta amsa had’ida risinawa kana ta fice kiran Umaima.... Koda Umaima ta iso parlorn Mahmood tambayarta komai gameda Muhibbah yayi... Umaima ya sanar dashi duk abinda ta sani gameda ita.... Ya jinjina kai a hankali kana ya baiwa Umaima izinin tafiya... Umaima na ficewa ya kirawo Turaki yace yanaso yaje Jami’ar garin ya bincika masa komai gameda abinda take karantawa dan ko shakka babu ya soma tantaman idan da gaske makaranta ne ya kawota Masarautar.... ** Gimbiya Zeenat Ta kuma kaiwa Raheema rank’washi a matuk’ar fusace tace “Na rasa ke wata irin shashasha ce Raheema, wane jarabar ne zai dawo dake Masarautar nan bayan Muna gab da mallakar Mahmood... Wannan gantalellen Yazeed d’in ban San kalar asirin da ya miki ba...!” Raheema na hawaye take fad’in “Aunty wllhi Yazeed tilasta min yayi nazo... Bansan Zuhra zata kamamu ba... Nidai fata na Aunty Allah Sa kada ta sanar da Mahmood dan wllhi idan ya sani bazai yarda ya aureni ba..!” Gimbiya Zeenatu Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa uwarsu ta sani ma koran wulak’anci zatai mana a Masarautar nan mu k’asa mallakan abinda muka jima Muna hari...! Yanzu ke bazaki bari kowa yasan kinzo Masarautar nan ba... Salin alin kiyi ficewarki Ki koma kuci gaba da shirin biki ni zanji da ita Zuhrar..!” Raheema ta murmusa tace “Yauwa Aunty na shisa nake k’ara sonki... Dan Allah kar ki bari Zuhra ta fasa maganan nan cikin Masarauta..!” Gimbiya Zeenat ya murmusa tace “Yo mud’in na wasa ne..! Ke yanda na k’wallafa rai billahillazim sai kin auri Mahmood sarauta ta tashi daga hannun Giwa ta dawo hannunmu... Maza tashi kije kafin munafukan kuyangin Masarautar nan su soma tururwa...!” SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH* *59* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Hankali kwance Raheema ta koma masarautarsu akaci gaba da shirin biki, a nan Masarautar su Mahmood ma ba’a fasa komai ba anci gaba da shirin biki tareda nad’in sarautar Sarki Mahmood, sam bai nunawa Yazeed yasan wani abu gameda alak’arsa da Raheema ba haka nan Zuhra ma bata nuna komai ba kaman yanda Mahmood d’in ya buk’ata daga gareta... Koda Gimbiya Zeenat ta kirawota har d’aki ta tareta da zancen murmushi mai ciwo Zuhra tai tace “Aunty Zeenat kenan ai abinda ya riga ya faru ya faru, bazamu iya canza komai ba saidai muyi fatan hakan ya zamto na k’arshe domin kuwa Sarki Mahmood mutumin arziki ne bazanso matarsa ta kasance macuciya azzaluma irin Raheema ba...!” Gimbiya Zeenat Ta tareta da fad’in “Naji dad’i da kika fahimci hakan Zuhra, kuma babu wani riba a b’ata sunna ma’aiki da ake k’ok’arin k’ullawa kuma kema Ina fata Keda Yazeed ku daidaita kanku dan ba wani abu bane sharrin shaid’an ne... Koda wasa kada ma Ki bari wannan labari ya fita daga cikin Masarautar nan balle har ya tsallaka Masarautarku..!” Murmushi mai ciwo Zuhra tai tace “Aunty kenan.. Inaga ci gaba da zama gidan Yazeed ko rashin ci gaba da zama dashi wannan wani abu ne da ya dace ni na zab’a ba Ke ba... Inaga bakida hurumin da zaki dubi tsaban idanuna kice min naci gaba da hak’urin zama tareda Yazeed Dan haka kar mu sake wannan zancen... Maganan Raheema kuma tuntuni ni na rufe babinta a rayuwana, na barta da wanda ya halicceni ya kuma halicceta shi zai min sakayyan abinda suka jima suna min itada Yazeed... Hasalima bani Ta sab’a ba mahaliccinta Ta sab’a shi zata nemi yafiyarsa.. Idan babu wani abinda zakice ni zan tafi Aunty...!” Gimbiya Zeenat tabita da kallo jiki a mace ta k’ak’aro murmushi wanda yafi kamada yak’e “Toh..Toh shikenan... Ai Babu matsala kina iya tafiya Zuhra...Allah ya shiga lamuranki..!” Zuhra ta amsada “Ameen Aunty..!” Kana ta mik’e tai ficewarta Hadimarta na tsaye daga k’ofan shiga parlorn tana jiranta... Tana fitowa ta take mata baya suka nufi sashen Zuhran... Saidai suna shiga sashen nata suka tadda Yazeed zaune parlorn tareda yaransa sai wasa yake masu suna tsalle jikinsa abinda bai saba ba... Da gani kasan wani abin kawai yake shiryawa... Zuhra ta sallami Hadimarta kana tasa kai zata haura sama... Yaran suka tafi da gudu suna rik’o hannunta tazo Daddy yai masu doki gaba d’aya.. Wasa suke Sultan ne sarki Daddy ne dokinsa.. Zuhra ta dafa kan yaran tace suje suyi wasansu bacci takeji... Dik yanda yaran suka so tazo suyi wasan tareda ita tak’i amincewa idanun Yazeed k’yam kanta, sam bai tab’a zaton Zuhra nada zuciya har haka ba, shi sam baiyi zaton zata iya fushi irin wannan ba Ta daina shiga sabgarsa gaba d’aya... Kallon arziki ma bai isheta ba... Yana matuk’ar k’aunar Zuhra da bazai iya jure shariyarta garesa ba amma harga Allah shi bai ma San ya ake baiwa mace hak’uri ba balle ya bata... Ya fuzar da fuci kad’an yana mai shafa sumarsa... Tana hayewa ya faki idanun yaran nasa dake ci gaba da wasansu da pillows yabi bayan Zuhra... Aiko tana ganinsa cikin d’akin Ta shiga nuna masa k’ofa “Get out..!” Yazeed ya dubeta da mamaki Wai shine Zuhra ke nuna masa k’ofa tana koransa... Ya shanye b’acin ransa had’ida fuzar da fuci... “I said get out of my room..!!” Ta fad’i a karo na biyu tana mai kuma nuna masa k’ofa... Ko gizau bai ba saima tsareta da idanuwa da yake ci gaba da yi... “The last time I checked this is my kingdom, so duk yanda naga daman shiga zan shiga... Idan kin mance na tuna miki..!” Ya k’arashe cikeda gadara... Murmushi mai ciwo tayi wanda da gani kasan na takaici ne... Lokaci guda Ta d’auki wayarta da counter da take mak’alawa a ‘yar yatsarta tace “Basai ka tuna min ba... Amma tunda kace haka ni zan fice na baka waje Dan na tsani ganin wannan fuskar taka... You disgust me your Highness..!!” Ta k’arashe cikin karaji had’ida sa kai zata fice... Yazeed yai saurin fuzgota ta fad’o jikinsa, su duka biyu suna sakin huci mai zafi yake fad’in “Da alama kin mance da wa kike magana... Zuhra ni ne nan Yazeed wanda mace bata

Chapter 38 of 65