iya d’ago kanta batayi, Gata nan dai d’aure saman kujera iyaka jin jiki tayisa kam...
Ko Iya d’aga kanta Jakadiya batayi, Giwa kanta saida ta firgita da ganin yanda halittan Jakadiya ya sauya lokaci guda, bata tab’a tsammanin muguntan Jamal yakai wannan mataki ba... Jiki na rawa Giwa ta isaga Jakadiya tana k’ok’arin dungurinta take fad’in “Anya tanada rai..?!”
Jamal ya jinjina kai yace “Tanada rai Maami kawai alluran hutu tasha, nanda wasu sa’o’i zata farka...!”
Giwa tai mata K’uri tana duban yanda fuskar Jakadiya ya kumbura ga wata akwati d’aukeda tools a gefe... Dank’ari mak’ari, wannan wane irin azaba Jamal ya baiwa matar nan...
Giwa Ta dubesa tace “Jamal mai Jakadiya tai maka..?!”
“Amanata taci... Kuma kema taci amanarki don na tabbata ita ta taimakawa Ja’afar ya gudu...!” Ya k’arashe cikin huci...
Giwa Ta lumshe idanunta a hankali dan tasan tsanar Jafar ne ya shafi Jakadiya, Jamal zai iya yin komai akan yarinyar nan Umaima...
“Toh amma ya akai ka Sani....?!” Giwa ta tambaya tana mai tsaresa da idanu...
Mayafin Jakadiya dake aje gefe ya nuna mata yace “Kin gani wannan ne shaida...!” Take ya labartawa Giwa duk yanda abin yake...
Giwa Ta d’aga mayafin tana juyawa... Ko shakka babu bai kamada mayafin bayi ba, duk yanda akai wannan ba na Jakadiya bane... Akwai wata k’ulleliya, amma bazatace komai ba har sai Jakadiya ta farka.... Da k’yar ta shawo kan Jamal ya sassautawa Jakadiya da irin uk’ubar da yake mata, Kwanceta yayi ya ajeta a nan d’akin had’ida treating duk wasu wounds dake jikinta... Giwa kanta saida ta tausayawa Jakadiya Dan ko motsi bata iya yi... Haka suka fice suka barta rufe nan cikin d’akin kafin alluran su saketa ta farfad’o....
**
Sharkaf da zufa tamkar babu AC cikin d’akin haka ya farka daga baccin nasa, mafarki yayi wata Murya da baisan daga ina bane tana fad’i masa Maiyasa zai zamto mai munana zato da mummunan zargi ga mutanen kirki... Da yawa daga cikin zato zunubi ne, kuma sashenta ba gaskiya bane..!
Ya shafe fuskarsa da tafukan hannayensa mafarkin na dawo masa daki daki... Wasu mutanen kirki ne ya munana masu zato..? Tambayar da zuciyarsa tai masa... Toh kodai Yazeed ne..? Ko Raheema ce..! Toh amma ya kamasu red handed ba zato yake masu ba.... Take yaji zuciyarsa Ta ambato masa MUHIBBAH...
Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai kuma shafe fuskarsa, Toh idan sashen zaton nasa ya zamto gaskiya fah...?
Wata b’angare na zuciyarsa ta basa amsa da fad’in Kai da kanka ka kasa aminta cewa zatai abinda kake zaton ta aikata...!
Ya fuzar da fuci mai tsananin d’umi tunanin na kuma damunsa, duk yanda yaso ya yakishe tinaninta cikin zuciyarsa ya kasa... Dik yanda yaso ya amince cewa ita d’in mutuniyar kirkice ji yake bazai iya hakan ba musamman da Zahra ta sanar dashi duk wasu shawarwari da Muhibbah taita bata tin daga fari, har cewa da tai ta tambayesa a cikin mutanen da yake jin nauyinsu... Kenan Muhibbah itace Ta tunzuro Zahra tai masa abinda tai... Gaba d’aya sai yana jin bazai iya aminta da ita ba bayan all that he learned about her... Da k’yar ya iya mik’ewa ya nufi bayi Don d’auro alwala....
**
Giwa sai faman safa da Marwa take a k’uryar d’aki Jamal na gefe yana juya mayafin, kenan Zahra itace Ta baiwa Jakadiya...!
Jamal ya dubi Giwa yace “Maami amma Zahra bazata iya lek’en asiri cikin d’akina ba... Maiyasa ma zatayi haka...? What could be her reason..?!”
Giwa tai shiru tana nazari sai kuma tace “K’warai Zahra bazatayi duk abinda ka zayyano mai wannan mayafin tayi ba, duk yanda akai akwaita a k’asa... Kodai akwai wata ‘yar lek’en asiri cikin Masarautar nan ko kuma bata cikin Masarautar amma tana amfani da Zahra...!”
Jamal yai shiru kaman mai nazari sai kuma yace “Maami karki damu, I’ll talk to my niece a nitse nasan zata sanar dani komai... Kinsan na k’ware a iya shan cikin mutane Dan naji labari...!”
Giwa ta murmusa tace “Hakan yayi Gwarzo na... K’warai na yarda dakai.... Idan muka sami wacece wannan ‘yar lek’en asirin...”
Jamal ya katseta da fad’in “Horon da nayima Jakadiya sai ya zamto horo mafi rahama a gareta... Sai ta zab’i mutuwa da rayuwa...! Sai ta tsuguna kan gwiwoyinta tana rok’on na kasheta don hakan sai Yafi mata sauk’i kan irin azaban dana tanadar mata..!!”
Ya k’arashe yana tsananin huci jijiyoyin jikinsa na kuma fitowa...
Giwa tai masa K’uri tana sakin wane irin murmushi na jin dad’i...
**
BAUCHI
Iatakam tasha mamakin ganin Mommy Ta sauk’o daga dokin fushinda ta d’ale, har idan ta shiga gaisheta bata korinta, ganin yanzun ma bata koreta ba ya sanyata zama daga can gefe wajen k’afafun Mommyn... Dak’ik’ai suka d’an shud’a kana Muhibbah ta soma fad’in “Mommy zuwa nai na miki bayanin komai dalla dalla ba tareda na b’oye miki wane abu ba...!”
Mommy ta katseta da fad’in “A’a Hibbah ni bana son naji komai balle ma bak’in labari, kedai kije kuci gaba da shirin biki Keda k’awayenki kinga babu wani sauran time kwanaki ne kawai suka rage, duk abinda kuke buk’ata ku sameni, idan bazaki iya samuna ba Meenatu Ta sameni... Bana son na kuma jin kin tono zancen nan... Allah ya baku zaman lafiya a gidajen aurenku...!”
Jiki a sanyaye Muhibbah Ta amsa da “Ameen Mommy..!” Allah ya gani tana son Mommy ta bata chance ta sanar da ita labarinta daga farko har had’uwarsu har kawo yau, tayi imani Mommy zata fahimceta amma tak’i bata wannan daman ko menene dalilinta... Wata zuciya tace k’ila bataso taji yanda akaci zarafinki ne... That’s how much she loves you.... Bata ida tunanin ba Aunty Gudidi tai sallama tana rangad’a gud’a tafe da wasu ‘yan Office d’in su Mommy guda biyu wanda duka k’awayensu ne...
Muhibbah ta gaishesu Aunty Gudidi harda rungumarta tana nunawa K’awayen nasu ga d’aya amaryar dashike Mommy Ta sanar da ita yanda sukai da Yawale akan Muhibbar... Itadai Muhibbah sai mamaki take yanda Mommy da k’awayenta suka canza lokaci guda... A b’angaren Ansar ma yaji dad’in hakan don tuni sukaci gaba da shirye shiryen biki, har can gidan Baffah Yawalen ma yaje da yaga sun saduda sun amince ya auri zab’insa hakan yasa yai alk’awarin bazai watsa masu k’asa a idanu ba suma zaibi umarninsu a matsayinsa na iyayensa koda hakan bazai faranta masa ba...
**
A can masarauta ma shirye shirye ta kankama, Mahmood ya sanar da Giwa harda auren Jamal da Umaima duk za’a had’a a d’aura, Giwa bata damu ba tinda tasan sunada shirinsu na musamman akan Umaimar, hasalima tuni tasa aka killace Umaima Kuyangi na kula da ita na musamman, wannan dalili yasa sam itada Jamal basu sami damar yin magana da Zahra ba Dan tsananin Farin ciki da Jamal Ke ciki ma yasa ya mance da batun tambayar Zahra, Giwa kaw Ta bada Himma ne sosai wajen ganin Jakadiya ta warke dan tunk’aran Tal’udu dole saida Jakadiya batasan wannan zuwan wane sassan jikinta ne zaici wuta ba musamman sanin yanda sukai baram baram da Tal’udun a had’uwarsu ta k’arshe....
**
Yau d’in Ta kama Alhamis kwanaki biyu tak suka rage a d’aura aurarrakin... Turaki na gefensa yana ci gaba da karantarsa, koda ganinsa kasan babban al’amari ke damunsa...
D’an gyaran murya Turaki yai yace “Your Highness, da an k’ara duba lamarin nan daga gobe ne fah ake saka ran d’aurin auren nan.....!”
Ba tareda ya dubesa ba ya jinjina masa kai a hankali “Na riga na gama magana Turaki, my decision is final... Dani dakai zamu tafi mu karb’o auren yarinyar Dan ina buk’atarta a cikin Masarautar nan... Sannan zan wakilta Galadima da Sardauna harma da Hakimai kaman guda uku su tafi Masarautar su Raheema su karb’o aurenta itama...Waziri dasu Matawalle da Liman zasu tsaya a nan su d’aura auren Jamal.... Haka na tsara tafiyar....!” Ya k’arashe yana murza zobban hannunsa a hankali...
Turaki ya had’iyi miyau da k’yar yana mai jinjina kai Dan yasan wannan hukunci da abokin nasa ya yanke dole nadama ya biyo baya....
Fatansa bai wuce Allah ya shiga lamarin ba ya tabbatar da ikonsa akan komai....
**
RANAR ASABAR 29 GA WATAN AFIRILU...
Kaman yanda Sarki Mahmood ya tsara hakan ce ta kasance, shiga irinta Buzaye sukai daga shi har abokinsa Turaki harmada amintaccen Hadiminsa Barde, baka hango komai cikin nad’in fuskokinsu face karan hancinsu da k’wayan idanunsu...
Suna zaune cikin Mota suna hango dandatson mutane a k’ofar gidan Yawale sai kai komo suke, Mahmood yai k’uri wa mutanen da suke kaiwa da kawowa, Turaki ya d’an kaikaito ya dubi Mahmood dake zaune bayan Mota yace “Rankaidad’e mun iso..!”
Jinjina masa kai Mahmood yai ba tareda yace komai ba, saima sak’on da yake k’ok’arin turawa cikin waya... Yana ida tura sak’on yasa k’afafunsa ya fito daga cikin motar Barde dake zaune gaban Mota ya fito da sauri ya bud’ewa Ubangidan nasa...
Mahmood ya dubesa yace “Barde a nan dani dakai d’aya muke har sai mun koma masarauta...!”
Barde kai a k’asa yace “Allah shi taimakeka bawa bazai tab’a zama kaman kai ba... Tuba nake ka gafarceni Rankaidad’e bazan iya abinda kake fad’i ba...!”
Mahmood yai gyaran murya kad’an yace “Umarni nake baka Barde, ba shawarinka nake nema ba..!”
Barde ya jinjina kai a hankali yace “Tuba nake Allah shi taimakeka, yanda duk kace haka za’ayi...!!”
Mahmood ya jinjina kai yace dasu su k’arasa cikin Zauren taron...
Turaki da k’irjinsa ke ci gaba da bugu yasa kai suka soma tafiya...
A can gidan Mommy kuwa Gudidi da Mommy sun baiwa Ango Ansar da Amarya Muhibbah maganin bacci, K’awayen Muhibbah na nan cike d’akinta amma basuga idanun Amarya ba sun kulleta can d’akin Mommy tana shek’an bacci Tamkar macecciya.... Shima Ansar a nan d’akin dake gefe da na Mommy suka kullesa abokansa dake jiransa a sashensa Mommy ta isa ta taddasu sai trying layin Ansar suke bai shiga... Suna ganin Mommy suka soma gaidata suna sanar da ita abindake faruwa..
Damuwa k’arara saman fuskar Mommy take fad’in “A’a Wai dama bai sanar daku ba..? Ai jiya ya bar gidan nan zai kama d’aki a hotel sabida cunk’oson taron mata na biki... Kunsan akwai Amarya d’aya gidan nan bai kamata ango yana tsakani ba... Kai Musbahu ai na zaci tare kukaje kai ka masa rakiya ya kama otel d’in...?!”
Musbahu ya girgiza kai yace “Mommy wllhi ni bamuyi wannan zancen dashi ba... Kuma ga wayoyinsa duka basu shiga, mun fara damuwa da halinda ka iya kasancewa ciki...!”
Mommy ta d’an murmusa tace “Kayya Babu wani abu zumud’i ne kawai irinta sabon ango, kasan tagwayen mata garesa... Kaima satin baya akayi Naka bukin ai ya kamata ka fahimci haka...! Kudai yanzu kuyi maza ku tafi ku sami d’aurin auren k’ila yama tafi tuntuni ya mance wayoyin nasa a d’aki....!”
Abokan suka jinjina kai sukace Eh kuma hakan ka iya kasancewa, sauri sauri suka fice dan kar su rasa d’ahtoh aure...
K’awayen Muhibbah ma dake zaman jiranta a d’aki Gudidi ce ta shiga ta samesu tace Amarya tana can ana kintsata bazasu sami ganinta yanzu ba.. Hakan yasa K’awayen sukaci gaba da sabgoginsu, masu ciye ciye nayi masu tad’i nayi... Gudidi ta rakasu da harara da gefen idanu tana mai ayyanawa cikin zuciyarta “K’awarku kam kun rabu da ita kenan har abada dan mu kanmu bamusan duniyar da za’a kaita ba..!!” Ta fice tana sakin murmushin jin dad’i....
**
A can Masarautar su Raheema kuwa wata Kuyanga ce ta shigo a fujajan ta zube gaban Raheema tana fad’in “Ki gafarceni ya Shugabata wani labari na kawo...!”
Raheema ta watsa mata harara, d’aya daga cikin Hadiman dake shiryata ta dubi Baiwar tace “Ke kuwa wani labari ne zai sa ki fad’o kan Gimbiya haka, bayan Kinsan yau d’in rananta ne ranan Farin ciki ne a gareta...!”
Baiwar naci gaba da haki take fad’in “Ki gafarceni ya Shugabata wani labari nakeji na Yawo cikin Fada..!”
Raheema da ta kai matuk’a wajen tunzura da wannan baiwa, fincika tai Ta mik’e tsaye tana fad’in “Ke k’ask’antacciyar Baiwa wane labari ne zaisa ki fice hayyacinki haka.. Labari guda d’aya ke yawo cikin Fada, labarin Farin ciki... Labarin auren Gimbiya Raheema da Sarki Mahmood... Shi kad’aine labarin dake yawo cikin Fada..!!”
Baiwar na haki take girgiza kai....
Raheema da k’irjinta ke bugu batasan sanda ta damk’o wuyar Baiwar tana fad’in Ta sanar da ita labarin dake tafe da ita... Batakaiga rufe baki ba suka sinkayo sautin algaita na tashi ana ambato sunan Gimbiya Raheemah da angonta matsayin ma’arauta.....
*MUHIBBAH*
*61*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Raheemah bata daina jijjiga Baiwar nan tana mulke mata fuska da k’unshin dake hannunta ga algaita na kuma tashi duk ya karad’e cikin Masarautar.... Daidai nan Gimbiya Zeenat Ta shigo a fusace hankali tashe tana fad’in “Raheemah mai nake ji, Wai Yazeed aka aura miki ba Mahmood ba... Ta yaya wannan abu ya kasance...?!!”
Raheemah na kuka tamkar mai tab’in hankali duk ta shafe jikinta da k’unshin da ake zana mata tace “Aunty wllhi k’arya ne... Wanda suka Zo d’aura auren su sukayi munafunci, Aunty Mahmood na sona nayi imani yana sona bazai tab’a barina ma k’aninsa ba... Aunty dan Allah tun kafin su tafi ki taresu su warware wannan auren wasan da sukayi su maida aurena kan mijina Mahmood... Aunty I can’t lose Mahmood... Wayyo na shiga uku.... Dan Allah Ki fita ki taresu wllhi dariya za’a mana cikin Masarautar nan... Sanin kanki kishiyoyin Ummah bazasu barmu musha iska da habaici ba..!!”
Gimbiya Zeenat naci gaba da huci take furta “Ai duk laifinki ne... Ga irinta nan..! Ga irin ranar da nake jiye miki, kin maida kanki tamkar wata kariya... Na tabbata Mahmood yasan Keda d’anuwansa kunada alak’a a b’oye shiyasa ya juya akalar auren ya koma kan d’anuwansa... Ai abin kiyi Farin ciki ne yanzu sai kuyi mai dalili.!!!”
Raheemah ta katseta da fad’in “Aunty dan Allah kije ki tari Hakiman nan kar su fice a Masarautar nan... Mishkila aka samu Mahmood ne mijin ba Yazeed ba..!!” Ta k’arashe tana mai nufan k’ofa kai babu ko rufi tsaban ta shiga tashin hankali maras misaltuwa... Gimbiya Zeenat tabi bayanta a fujajan tana k’ok’arin dakatar da ita inaa Raheema bataji bata gani tuni Ta tsallake bene ta nufi dandatson jama’an dake haraban Masarautar....
Abinka da babban gida sai aka samu abinyi, bayi na k’usk’us ‘yan gida kaw masu jimami nayi masu dariya na yi...
Haka Raheema ta fice tana fad’iwa masu algaita su dakata... Ta kutsa sosai har gaban su Galadima tana fad’in wannan auren bai d’auru ba... Sarki Mahmood ne mijinta ba Yarima Yazeed ba..!
Galadima ya girgiza kai yace “Rankidad’e kaman yanda Sarki Mahmood ya umarta hakan mukayi... Yarima Yazeed shine mijinki ba Sarki Mahmood ba...!”
Raheema ta shiga fatali da kayan kid’e kid’e dake wajen tana fad’in k’arya ne wannan auren bai d’auru ba...!
Ala dole wasu bayi ‘yanmata guda hud’u suka kamata aka shige da ita cikin gida sai hauka take wanda hakan sosai ya zubda Martaban masarautarsu... ‘Yanuba kuwa suka sami abin goriwa Zeenat dan sun tabbata wannan abin kunya da Raheema tayi tsaf sai ya koma Masarautar da Gimbiya Zeenat ke aure... Haka Gimbiya Zeenat ta aje shagalin buki a gefe ta shiga rara kuka tana kaico, shikenan Sarautar da take hari ta hanyar auren Mahmood da k’anwarta zatayi ya tashi a aiki... Har abada bazata tab’a samun hakan ba, wannan abin kunya ma da Raheemah tayi bai k’aresu da komai ba face fad’a zubda mata jima da tayi... Yanzu ko nan cikin masarautarsu mahaifarta batada wani kima balle aje can masarautarsu mijinta... Sosai Gimbiya Zeenat Ke kuka tana nadaman abubuwan da tayi a baya... Kaicon son zuciya, yau ga yanda son zuciya ya kaita... Dama komai zakayi ka saka tsoron Allah a ciki idan kuwa ba haka ba sai Kaga ba daidai ba...!
**
Bakin Turaki ya gaza rufuwa, Mahmood ya shammacesa... Wato dama kansa ya nemawa auren Muhibbah... Gashi kuma ya karb’awa kansa auren nata ba tareda wakilcin kowa ba... Kai sai a gaisheda Mahmood inji Turaki..
Fataken Buzaye sun amshi auren Muhibbah yanda suka buk’aci a basu amaryarsu su tafi can k’asarsu da ita...
Yawale yace kar suji komai su taho da motar da sukayo haya su biyosa suje har yanda zasu d’auke amaryarsu... Ba tareda b’ata lokaci ba kuwa sukabi bayan Yawale dake bisa babur d’insa, nan take suka nufo gidansu Muhibbah...
Aka bar mutane da jimamin abunda ya faru da jinjina lamarin, wasu daga cikin Baffanin Ansar da suke Uba d’aya da mahaifinsa suka titsiye Yawale suna fad’in rashin kyautawar da yayi ace baka San mutane ba baka San daga yanda suke ba ka d’auki mutum sukutum ka basu...!
Yawale yace Babu ruwansu tunda ba ‘yarsu bace kuma Ansar shine kad’ai dolensa basu ba...! Haka dai Yawale yai masu d’add’aya ya barsu nan suna jimamin wannan abinda ya faru wanda saikace wani wasan kwaikwayo... Abinda suke ganina wasannin kwaikwayo da littafai sai gashi zahiri a gabansu....
Shidai Mahmood sai karantar Yawale kurum yake da idanu.... Suna isa unguwar Yawale yace suyi Parking daga can nesa za’a fito da ita... Turaki yai parking daga nesa kaman yanda Yawale ya buk’ata...
Nan take Baffah Yawale ya ciro wayarsa a aljihu ya kirawo Gudidi yace da ita masu d’aukan Amarya sun iso Ta fito da Amarya...
Gudidi tace an gama gasu nan fitowa.... Cikin sand’a don ko Mommy bataso ta ganta ta kirawo k’awarsu Salame tace ta taimaka mata su fito da Muhibbah tinda dama bacci take....
Salame dai tsoro saman fuskarta tabi bayan Gudidi suka shiga d’akin yanda Muhibbah Ke yashe tana bacci, tausayin Muhibbah ya kama Salame... Idanunta sukai rau rau tana dubanta.... Gudidi kaw ko a jikinta saima d’auko mayafi da tai Ta rufawa Muhibbar tana k’ok’arin mik’ar da ita tsaye....
Ta dubi Salame dake tsaye tana duban Muhibbah cikeda tausayawa kana taja tsuka a hankali tace “Toh Sarkin tausayi da imani, dramar ya k’are taimaka min zakiyi mu fitar da ita daga cikin gidan nan....!”
Salame Tai k’ok’arin maida k’wallan da suka ciko idanunta tace “Gudidi babu wanda yasan duniyar da za’a kai yarinyar nan... Babu wanda yasan su waye suka auri yarinyar nan..? Wasu irin mutane ne... Na gari ne ko na banza... ‘Yan shan jini ne koma matsafa ne... Gudidi baki tausayin yarinyar nan..? Baki tsoron hakki..!!”
Gudidi ta katseta da fad’in “Kinfi Murja sonta ne..? Dashike ba d’anki aka so lik’awa ba dole Ki wani marairaice kice ke tausayi kike... Itama yarinyar inace iyayenta b’arayin daji ne yo koma su waye ta aura ai ‘yan ta’adda ne ‘yan uwanta... Kinga idan har kina k’aunar Murja a matsayin k’awa zaki taimaka min mu fitar da wannan annobar yarinyar daga cikin rayuwarta....!!” Ta k’arashe cikin huci..
Jiki a sanyaye Salame ta k’arasa ta tallafi b’angare guda na Muhibbah Gudidi na rik’eda b’angare guda suka fito da ita suna janyota kanta rufe da mayafi....A haka suka fakaice idanun mutane da hankalinsu ya tafi ga masu busa dan tuni an soma dawowa daga wajen d’aurin aure ga labaru daban daban na tashi na irin d’aurin auren da akai.... Sai sannan ne Mommy take jin Wai ma wasu fataken Buzaye Yawale ya bada auren Muhibbah... Hankali tashe Mommy Ke kuma tambayar mutanen dake wajen yanda al’amarin auren ya kasance...
Tuni su Gudidi Sun fita Ta can bayan layin suna jan Muhibbah da k’yar da k’yar har dai suka hango Yawale tsaye jikin wata mota.... Yawale ya d’ago masu hannu yace su k’araso...
Tuni suka k’arasa yanda motar take... Take Barde ya fito ya bud’e masu d’aya b’angaren da babu kowa suka ajeta ciki gefeda Mahmood... Itadai Salame tsoron mutanen ne ma ya rufeta, jikinta har rawa yake tana alla alla su bar wajen... Suna ajeta Barde ya maida k’ofar mota ya rufe yai sallama da Yawale....
Suka koma gefe suna kallo aka tafi da Muhibbah Yawale na Washe baki yana fad’in “An yarda k’wallan mangoro an huta da k’uda...!” Harda d’aga hannu yana waving motar...
Guididi ma Ta tintsire da dariya tana tayasa da fad’in “A k’are can a duniyar matsafa dan wannan daga gani ‘yan shan jini ne suka sayi yarinyar nan...!”
Yawale yai shiru kaman mai nazari sai ya jinjina kai yana mai tabbatarda maganan Gudidi da tace ‘yan shan jini ne suka sayi Muhibbah dan ya tuna mak’udan zinarin da suka bada matsayin sadakinta, sai yanzu yake ciza yatsa dama ya saida masu ita da tsada da yanzu yayi dukiya, amma dukda haka ya samu ai, sannan ga Hameedarsa zata auri Ansar d’an Hajiya Murjah...
Mommy a fujajan ta nufi d’aki yanda aka kulle Muhibbah saidai babu Muhibbah babu dalilinta... Take taji wasu irin hawaye na zuwa mata, Ta shiga bud’e k’ofofi tana ambato sunan Muhibbah mutane na kallon ikon Allah...
Shigowarsu Salame da Gudidi yasa Mommy ta nufesu tana tambayarsu ko sunga Muhibbah... Salame na k’ok’arin danne kukanta take girgiza kai, lokaci guda take furta “Murjah Muhibbah ta tafi... Ta tafi kuma bazaki sake ganinta ba..!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata...
Tamkar mutum mutumi haka Mommy ke dubansu hawaye basu daina ambaliya a fuskarta ba... Cikin wane irin zabura tasa kai Ta nufi waje tana fad’in “Ina suke... Na fasa na fasa aura masu Muhibbah... Ku dawo min da d’iyata wllhi na fasa..!!”
Gudidi tai ta maza ta kamo Mommy ta dawo da ita cikin gida... Gidan biki dai ya kacame da maganganu da hargitsi... Wannan kenan..!
**
Tunda suka d’au hanya ya kasa janye idanunsa daga kanta, tsananin tausayinta yakeji na taso masa daga can k’asar zuciyarsa.... Idan da ace bai aureta ba tabbas wad’annan mugayen mutane da Sun bayar da ita ma ko wane irin mutum, tabbas zasu iya salwantar da rayuwarta sabida son zuciya... A hankali harshensa ya furta “You’re safe now..!” Dai dai lokacin da aka d’ale speed bump abinka da mai bacci sai ta fad’o cikin jikinsa tai matashi da k’irjinsa... Dukda bacci take yana Iya jin bugun zuciyarta cikin nasa k’irjin, tamkar zukatan nasu lokaci guda suke bugawa... Yanayin da ya jima bai tsinci kansa ciki ba ya ziyarcesa.... A hankali yake k’ok’arin kai hannu jikinta yana son gyara mata kwanciyar zuciyarsa naci gaba da harbawa... Wai fah ita d’in matarsa ce yanzu, ji yake kaman idan ya tab’ata zata farka.... Ya maida hannunsa ya ajesu ba tareda ya gyara mata kwanciyar ba, tana nan kwance cikin k’irjinsa.... Burki da Turaki ya d’an ja ne ya sanyata zamowa daga kan k’irjinsa zuwa cinyarsa.... Yai mata K’uri yana dubanta, wane irin duba yake mata wanda ko iya janye idanunsa baiyi, a hankali ya kai hannunsa yana k’ok’arin yaye rufin dake fuskarta.... Sannu a hankali yake janye mayafin hardai fuskarta ya bayyana... Zuciyarsa ta kuma bugawa lokaci guda, fuskar nata fayu babu ko kwalliya tamkar ba Amarya ba, hasalima a kod’e fuskar tata take irin na wanda yaci kuka harda sauran busassun hawaye a fuskar nata... Dogayen bak’ak’en gashin idanunta da sukayi marfi wa manyan idanun nata duk sun shige cikin juna alamu kuka taci sosai, idanunsa suka sauk’o kan labb’anta masu d’an duhu kad’an wanda kaman an zane k’arshensu da liner... A hankali ya lumshe idanunsa yana mai k’ok’arin janye fuskarsa daga barin dubanta, nan idanunsa suka sauk’a kan hannunta da yasha zanen flowers na lalle dunk’ule da wata ‘yar takarda... Yai K’uri yana duban hannun nata... Duk wannan bacci da take takardan na nan mak’ale cikin hannunta bai fad’i ba... Daga gani ba rik’on wasa taiwa takardan ba...
Mahmood yakai hannunsa yana k’ok’arin bud’e hannun nata dake dunk’ule da takardar...
A hankali ya warware hannun nata har ya ciro takardan... Gabansa ya buga kikaci guda sanda ya warware takardan... Zanen ginin gidan sarautar nan ya gani... Take mafarkin da yayi da ita tana guduwa da zanen ya shiga dawo masa... Ikon Allah..! Wato dai mafarkinsa ta tabbata gaskiya... Yarinyar nan tanada wani agenda d’inta cikin gidan...! Toh ya akai irin zanen da Wambai ya basa ya fad’o hannunta... Mai takeyi da zanen..? Kuma a ina Ta samu..?! Tambayoyin da suka tsaya masa a rai har suka isa masarauta...
Lokacinda suka hankulan d’aukacin jama’an Masarautar naga hidindimun bikukuna da ake sannan wata labari da d’umi d’umi ta iso Masarautar cewa auren Raheemah dai ba da Mahmood aka d’aura ba da K’aninsa Yazeed aka d’aura...
Wannan hargitsi yasa har Mahmood ya ciccib’i amaryarsa ya shige da ita sashen da ya tanada na musamman Don ajeta ciki...
Yana fitowa ya tadda Barde da Turaki har sun sauya shiga suma, take ya kuma jaddada masu cewa babu wanda zaisan batun aurensa da Muhibbah..!
Barde ya jinjina kai cikeda risinawa yana mai tabbatar masa amincinsa garesa...!
Mahmood ya jinjina kai yace “Ina Kuyangin dana ce ka ware mun su...?!”
Barde ya kuma risinawa yace “Allah shi baka yawan rai suna nan waje suna jiran umarninka...!”
Nan ma jinjina kai yayi yace “Kasan sashen da na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 65