shiga karyo masa ya rasa mai zai furta domin kaw Giwa tai masa kashedi mai tsananin kan irin sirrukan da zai bayyanawa d’anta Mahmood wanda a bayan tafiyarsa abubuwa da dama sun faru cikin Masarautar....
Gyaran murya da Yarima Mahmood yai ne ya dawo da Ubandoma daga duniyar tinaninda ya tafi, ya shiga furta “Tuba nike Allah shi baka yawan rai.... Ai wannan mahaukaciya da kake gani, yau shekaru goma sha biyar kenan tana fama da jinyar tab’in kwanya.....”
“Shekaru goma sha biyar.....?” Yarima Mahmood ya maimaita da sigar tambaya...
Kan Ubandoma a k’asa yake jinjinawa alamun tabbatarwa kana yaci gaba da fad’in “K’warai kuwa Allah shi taimakeka....”
Shiru na d’an lokaci ya gifta kana Yarima Mahmood ya kuma d’an takawa kad’an har lokacin hannayensa hard’e Ta baya kana ya d’an dakata a daidai jikin gini yana mai k’arewa kampacecen masarautar nasu kallo iya ganinsa sabida tsananin girma da fad’i da Masarautar kedashi.....
Yanada tarin tambayoyi da suke buk’atar amsa....
Kaikaitowa yai yana duban Ubandoma wanda Ke zube k’asa kana yace “Wacece wannan matar...? ‘Yantacciya ce kokuwa baiwace...?”
SameenaAleeyou 📚
[5/22, 9:35 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑*
*005*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar kana ya kuma risina yana mai furta “Allah shi taimaki Babban Yariman wannan masarauta, ita wannan mata ina tsammanin ba cikin Masarautar nan take ba... Randa dik ta b’alle ne sai ta shigo cikin Masarautar nan....” Ya k’arashe cikin sark’ewar harshe...
Da wasu irin idanu Mahmood Ke dubansa, ba don ya aminta da kalaman dake fita daga bakin Ubandoma ba....
Lokaci guda ya juyo sosai yana duban Ubandoma, saida ya d’ibi wasu dak’ik’ai a haka kana yace “Ya akai har ta tsallake manyan k’ofofi dake a cikin Masarautar nan ta shigo...?”
Ubandoma ya kuma had’iyan wani miyau d’in da k’yar kana yai k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa....
“Allah shi baka yawan rai.... Kasan idan akace mutum nada tab’in hankali komai zai iyayi... Ba yau ce rana ta farko da mahaukaciyar nan ta k’wace ta shigo Fadar nan ba... Dik randa ta k’wace daga turun ta takan fantasmo cikin Masarautar nan aita kokawan fitar da ita.....!” Ya k’arashe yana mai kuma d’aga hannu alamun jinjina yana mai furta “Allah shi baka yawan rai.....!”
Shiru ya kuma biyowa kana Yarima Mahmood ya kumayin gyaran murya, wannan karon sunan Ubandoma ya kirawo cikin wane irin siga mai firgitarwa kana yaci gaba da fad’in “Idan na samu cikin zancenka akwai abinda ba gaskiya ba, zanyi maka horo mai tsanani....!”
Daga haka yasa kai ya nufo k’asa cikin sassarfa da zafin nama...
***
Sashen bak’i Umaima ta sauk’esu, kafin ta iso tuni an cika gabansu da kayan motsa baki, sai bayan shud’ewar wani lokaci Umaima ta k’araso fuskarta d’aukeda murmushin nan nata mai kyau, gefe da ita Zahra ce suna tafe tare dukansu cikin shiga irinta mulki da sarauta....
Tin daga nesa gaban Muhibbah ke fad’uwa, su Umaima da Zahara suna ci gaba da k’arasowa cikin parlorn k’irjinta na tsananta bugu..... Lokaci guda taji k’afafunta sun rinjayeta Ta mik’e tsaye tana dubansu yanda suke k’arowa garesu....
Ansar d’in ma mik’ewa tsaye yai murmushi kwance saman fuskarsa...
Maraba da juna Umaima da Ansar suka somayi kana Umaima ta gabatar masa da Zahra d’iyar d’an uwanta....
Ansar ya d’an risinar da kansa fuska fal murmushi yana mai furta “Barkanki ranki shi dad’e, da fatan mun sameku lafiya...”
Murmushi kad’an Zahra tai a tak’aice tana mai jinjina masa kai ba tareda ta amsa ba.... Idanunta suka sauk’a kan Muhibbah dake binta da kallo irinta k’urilla...
D’an rausayar da idanu Zahra tai had’ida furtawa a hankali “¿Por qué ella me está mirando?” (Mai yasa take min kallon k’urilla) Gashi dik ita a tak’ure take da wad’ann kayan sarautar... Ita harga Allah ta gaji da k’asar da mutanenda ke cikinta, tana gani Ansar na introducing Muhibbah wa Umaima, had’ida dank’a mata amanar ‘yaruwarsa...
Umaima tace “Bakada matsala Dr, in sha Allah ‘yaruwarka tana hannu mai kyau... Nai maka alk’awari....”
Ansar ya jinjina kai a hankali kana ya mik’e daga zaune yana mai furta “Toh ni zan koma kar nai dare.....”
Umaima tace “Da wuri haka kaman ana korarka....”
Murmushi yai a fili a cikin zuciyarsa kaw tsantsan fargaban kewar Muhibbah ne da zaiyi Ke azalzalansa.... Suka dubi juna idanunsu suka had’e waje guda.....
Umaima ta dubi Muhibbah wacce itama Ansar d’in take duba cikeda kulawa kana tace “Hibbah bari mu barku kuyi sallama da yayan naki....Ki saki jikinki tamkar a gida kike.... Ki d’aukeni tamkar k’awa ko nace ‘yar uwa a gareki...”
Muhibbah ta jinjina mata kai fuska fal murmushi take furta “Godiya nake Rankishi dad’e....!”
Umaima ta kuma murmusawa kana tace “You don’t need to be too formal, kar Ki biye na wannan Yayan naki... Just call me Umaima....”
Jinjina kai Muhibbah ta kuma yi kana tace “Na gode Umaima...!”
Umaima ta kuma sakin murmushi kana ta janyo hannun Zahra suka d’an basu waje danyin sallama....
***
Ita kad’ai cikin katafaren d’akin nata, sai faman safa da marwa take, Takai mari takai bango.... Tana jiran bak’in labarin da yau d’in zai risketa dan dik randa mahaukaciyar nan ta bayyana toh ko shakka babu sai tayi gamo da labari mafi muni... Sai wani babban al’amari ya faru cikin Masarautar.... Tana a cikin wannan yanayi Jakadiya Ta turo k’ofa ta shigo cikeda risinawa ta zube k’asa.....
Gimbiya Turai, ko muce Giwa, ko muce Maibabban d’aki dan dika wad’annan sunayenta ne a cikin Masarautar.... Ta juyo tana watsawa Jakadiya wani irin duba, lokaci guda take takowa yanda Jakadiya ke zubewa tana kuma kwasan gaisuwa....
“Jakadiya Wani bak’in labari kikazo min dashi.....?” Giwa ta tambaya cikin kakkausar murya
Jakadiya ta kuma risinawa tana mai furta “Allah shi huci zuciyar Giwar Sarki.... Na bincika gabas da yamma kudu da arewa babu bak’in labari da ya bayyana a cikin Masarautar nan.... Da alama wannan karon bata fito da wani mummunan labari ba... Allah shi baki yawan rai amma saidai....” Tai burkiwa kalamanta sabida k’irjinta dake tsananin bugu....
Cikeda son jin mai Jakadiya keson fad’i Gimbiya Turai tace “Amma mai... Mai kuma ya faru Jakadiya...?”
Jakadiya ta had’iyi miyau kana tace “Allah shi baki yawan Rai, Ubandoma ya sanar dani Yarima Mahmood ya soma tambayar ko wacece wannan mahaukaciyar... Kuma daga yanda Ubandoma ya sanar dani Yarima bazai gajiya ba har sai ya gano ko wacece ita...”
Dakatar da ita Giwa tai da fad’in “Jakadiya akwai k’ofofin da D’ah na bai isa bud’esu ba a cikin Masarautar nan... Wannan kad’ai yayi kad’an ace Mahaukaciyar nan ta bayyana a Fada... Karki mance dik randa ta bayyana wani babban al’amari ne Ke faruwa wanda za’a iya dangantashi da rasa rai.... Tabbas akwai wani abinda ya faru a cikin Masarautar nan wanda bamuda masaniya...!!” Ta k’arashe tana duban Jakadiya wacce itama ita take duba cikeda damuwa mai gauraye da tsoro....
Tabbas zama bata gansu ba...
***
Yana fitowa bai zarce ko Ina ba sai bargan dawakin mahaifinsa.... A hankali yake takawa abubuwa da dama suna zuwa masa daki daki.... Wacece wannan matar...? Maiyasa yakeji kaman ya santa....? Dik yanda ya shige bayi sai sun risina Sun kwashi gaisuwa, Shiko Yarima Mahmood saidai ya jinjina masu kai alamun amsawa... Daga cen ya hango k’aramin k’aninsu Fu’ad yana k’arasowa....
Yarima Mahmood ya d’an fad’ad’a murmushinsa sanda Fu’ad ya k’araso gareshi, jerawa sukai su duka biyun suna ci gaba da takawa cikin bargan dawakin irin yanda masu mulki keyi....
“Barka da yammaci Yaya...” Fu’ad yace yana mai d’an sadda kai...
“Baka Yarima Fu’ad...!” Yarima Mahmood ya amsa cikeda kulawa....
Hira suka somayi irinta ‘yan uwa wanda suka jima basu tareda juna....
Daidai jikin wata farar doki Mahmood ya tsaya yana mai k’are mata kallo tamkar mai tunanin wani abu, hannu yasa yana shafa fuskar dokin a hankali... Fu’ad ya d’anyi gyaran murya had’ida furta “Dik ranan sallah ita yake hawa yaje masallacin idi bisa....Ana mata ado da kwalliya irinta amaren dawakai.... Yana tsananin k’aunar dokin nan....” Ya k’arashe murmushi saman fuskarsa yana mai shafa gadon bayan dokin...
Mahmood ya tari zancen da fad’in “Jafar ne kad’ai yake mata kwalliya irin wanda Maimartaba Ke so... Bai hawanta idan ba Jafar bane ya shiryata...!”
Shiru na d’an lokaci tamkar wanda ya tina wani abu kana yace “JA’AFAR....! Ina Ja’afar Fu’ad...? Tinda na dawo Masarautar nan ban sakashi a idanuna ba....?”
Fu’ad bai iya basa amsa ba saima sadda idanunsa k’asa da yai cikin wane irin sanyin jiki.... Kaman daga sama ya soma jiyo muryar Yazeed yana fad’in “Ta yaya kake tambayar mutumin da shi kansa bai jima da dawowa Masarautar nan ba... Idan zaka tambayi wani abu gameda Masarautar nan toh kada ka tambayi wannan k’anin naka...!” Ya k’arashe yana mai aikawa Fu’ad da kansa Ke k’asa muguwar kallo irinta k’ask’anci....
Yarima Mahmood ya kaikaito sosai yana duban Yazeed kana ya kuma duban Fu’ad....
Cruel smile d’in nan nasa saman fuskarsa yake d’aga gira alamun jaddadawa....
Dafa kafad’an Fu’ad Mahmood ya d’anyi kana yace “Fu’ad tell me, meke faruwa... Mai Yazeed yake nufi da yace baka jima da dawowa Masarautar nan ba... Ina ka tafi... Ko akwai course d’in da baka gama bane a Cyprus...?”
Fu’ad bai iya amsashi ba sai kuma sadda fuskansa k’asa da yayi...
Yazeed dake ci gaba da shu’umin murmushin nan nasa yai karaf ya soma fad’in “Tell him Fu’ad... Tell your big brother how you wasted time and resources a k’asar Cyprus ba tareda ka dawo da koda kwalin tsire ba... Koda shike ka dawo da ciwon shaye shaye na kayan maye... Hodar iblis Ta kusan illata maka kwanya gaba d’aya....!”
Baikai aya ba Mahmood ya katsesa da fad’in “Enough Yazeed..!! Wasu irin kalamai kake jifan d’an uwanka dasu haka...”
Murmushi da gefen baki Yazeed Ke ci gaba da yi kana yace “Gashi nan... Ask him... Ka tambayeshi idan k’arya na mishi.... Shekarunsa 28 amma baisan ina rayuwarsa Ta dosa ba... Ka tambayeshi kalan abin kunya da ya janyowa wannan masarauta... Ka tambayeshi gashi nan... Akanshi k’iris ya rage mulki Masarautar nan bata kufce daga gidan nan ba... Fu’ad you’re nothing but a great disappointment...”
Fu’ad da tuni idanunsa sun kad’a sunyi jazir yana fidda wane irin huci na tsananin k’unan zuciya... Lokaci guda ya d’ago rinannun idanunsa masu zuban ruwa yana duban Yazeed yake furta “Yes..! Yes Yazeed... Ban dawo da ko wanne takarda ba sai na shan kayan maye kaman yanda ka fad’i.... Amma kar ka mance kaine sila... Kaine sanadi... Kaine Kai jagoranci wajen ruguza rayuwar innocent boy.....”
Ganin Fu’ad ya soma sakin layi ya sanya Yazeed yowa kansa yana mai furta “Shut up... Shut the hell up...!! Don’t you dare put the blame on me...!!”
Ganin bayi sun soma dubansu suna yaface had’ida nunasu wa junansu da baki ya sanya Mahmood daka masu tsawa da fad’in “Enough!! Ya isheku haka... Kusan a yanda kuke kun kuma San mai kuke fad’iwa junanku....?”
Gaba d’aya sukai shiru suna maida huci tamkar wasu zakuna....
Yarima Mahmood ya dubi Fu’ad yace “Lets go Fu’ad.....!!!” Yai maganar cikin tsananin dakewa.....Babu musu Fu’ad ya take masa baya suna masu b’allawa juna harara shida Yazeed....
Suna shigewa Yazeed ya dakawa kuyangin dake zube a wajen muguwar tsawa da fad’in “Ku kuma mai kukeyi a nan... Ku b’ace min da gani kafin duk rasa rayukanku....!”
Tuni suka mik’e suna k’ok’arin barin wajen cikin sauri har kaman zasu kifa...
Hauni amintaccen bawan Yazeed yai kansu da k’atotuwar dorina yana zabga masu had’ida kwashe masu albarka....
Yazeed sai faman cika yake yana huruwa shi kad’ansa... Lokaci guda ya kuma sakin wata murmushi da shi kad’ai yasan ma’anarta.... Ya wani d’an gyara zaman rigar sarautarsa dake sanye jikinsa cikeda Izza wanda yin hakan d’abi’arasa ce
**
Cikin sassarfa suke tafe, Mahmood na gaba yayinda Fu’ad Ke biye dashi, kaida ka gansu kasan babu lafiya, a haka suka nufi sashen mahaifiyar tasu...
A daidai lokacinda Umaima, Zahra da kuma Muhibbah suka doson mashigar parlorn, cak suka tsaya suna duban Mahmood da Fu’ad dake tafe tamkar zasu kifa k’asa....
Tin Daga k’ololuwar kanta taji wani abu har izuwa tafin k’afarta.... Dikda fuskar Fu’ad ya canza sabida girma da yai ba kaman lokacinda Ta sanshi yana k’aramin yaro mai k’anan shekaru ba, kaman yanda nata fuskar ma ya canza hakan bai hana ta gane kamanninsa domin kaw kamaninsa da Mahmood ya kuma bayyana wanda shi Mahmood d’in babu abinda ya canza a kamanninsa da shike sanin matashi tai masa, saiko alamun girma da ya sauk’o masa.....
Take idanunta suka kad’a sukai jazir tana duban Mahmood tana tina shine mutumin da ya d’auketa da hannunsa ya azata saman doki kyakkyawan fuskarsa d’aukeda murmushi a lokacin, fuskar da take gani a idanunta tamkar bak’ar k’umurcin macijiya mai mummunar guba....Lokaci guda Ta rintse idanunta da k’arfin gaske tana jin zuciyarta na wani irin fizga tamkar zai fice daga cikin k’irjinta....
SameenaAleeyou📚
[5/23, 6:41 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBAH✨👑*
*006*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Suna k’arasowa kaga yanda Kuyangi ke k’amewa suna zubewa k’asa alamun girmamawa..... Zahra ta dubi Umaima fuska fal damuwa take fad’in “Aunty Umaima meke faruwa... Mai ya sami Paa da Uncle Best....?” Girgiza mata kai Umaima tai alamun itama bata sani ba... Lokaci guda Zahra tasa kai da zummar bin bayan iyayen nata ba tareda ta jira amsar Umaima ba... Saidai tuni Muhibbah ta rik’o hannunta alamun dakatarwa....
Zahra ta dubi hannunta da tsananin mamaki ganin wacece ta rik’eta... Ta kuma d’agowa sosai tana duban Muhibbah dake rik’eda hannunta guda alamun dakatar da ita..... Daidai da Umaima duban mamaki take bin Muhibbah dashi had’ida jinjina k’arfin hali irinta Muhibbah wacce zuwanta Masarautar kenan amma har tanada k’arfin halin dakatar da jinin sarauta daga gudanar da wani abu...
Har saida su Yarima Mahmood da Fu’ad suka shige babban gwanin Giwa (Parlorn Giwa) kana Muhibbah ta d’an saki hannun Zahra had’ida sadda idanunta kad’an murmushin k’arfin hali saman fuskarta take furta “A.... Ki gafarceni ranki shi dad’e.... A ganina bai kamata Ki tunk’ari mahaifinki a halinda yake ciki ba... Kaman ransa ya b’ace yake... Allah shi taimakeki.... Ki gafarceni...!” Ta k’arashe tana mai sadda idanunta k’asa..:
Gyara tsayuwa sosai Zahra tai tana dubanta kana tace “Wait... And who do think you’re... Wacece Ke da har kike fad’in ra’ayinki akan abinda ya dace nayi da kuma wanda bai dace nayi ba...
Quién crees que eres..” (Kina tunanin Ke wacece) Ta k’arashe tana mai tsare Muhibbah da idanunta.....
Umaima ce ta d’anyi gyaran murya kana ta kamo hannun Zahra tace “Zahra I think Muhibbah is right... Bakinsan mai ya b’ata ran Paa d’inki ba, kuma kinga bashi kad’ai bane... Besides nan gidan sarauta ne Zahra bazakiyi komai kai tsaye a bainar jama’a ba kaman yanda kikeyi a Spain... Abu k’ank’ani a nan sai ya zama scandal... Kuma nasan bazakiso Ki baiwa mahaifinki kunya ba... Muhibbah taimakonki tai Zahra... Godiya ya kamata Ki mata a ganina....” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta tana mai dubansu duka biyu daga Zahran har Muhibbar....
Shiru Zahra tai ba tareda ta furta komai ba sai d’an sadda idanunta k’asa da tai tana mai jinjina maganar... Lokaci guda ta d’ago ta d’an dubi Muhibbah kaman zatai magana sai kuma ta dubi Umaima tace “Aunty Umaima ni na shige ciki...” Tana kaiwa nan tasa kai tai shigewarta zuciyarta a b’ace....
Suka bitada kallo har ta b’acewa ganinsu kana Umaima ta maidoda dubantaga Muhibbah... Lokaci guda suka sakarwa juna murmushi kana Umaima tace “Ina fata kiyi hak’uri da d’abi’un Zahra... She’s going through a lot, bata jima da rasa mahaifiyarta ba, sannan bata son dawowa k’asar nan... Akan dole take zaune a k’asar nan shisa take wasu abubuwan da take, shisa take jin haushin kowa da kuma komai a k’asar., You know a teenagers are, a gab’ar take....Amma Zahra yarinyar kirkice ina mai tabbatar miki... Zaki k’aunaceta sannu a hankali....” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta...
Murmusawa kad’an Muhibba ma tai kana tace “Karki damu, na fahimceta... Kallo d’aya nai mata na fahimci ita d’in yarinya ce mai saurin shiga rai... Kuma inaji a jikina we would get along someday...!”
Umaima ta kuma murmusawa kana tace “Muje koh...!”
Muhibbah ta jinjina kai murmushi saman fuskarta kana suka nufi dogon ginin....
***
Daga yanayin tafiyar da suke zaka fahimci ba lafiya ba, hakan yasa suna shigowa Babban gwanin Giwa Kaga yanda kuyangi Ke darewa suna basu waje... Kaf suka fice waje suna masu kwasan gaisuwa, tuni Mahmood da Fu’ad sun nufi upstairs yanda suka tadda Giwa da Jakadiya suna tattaunawa....
Tuni Jakadiya ta risina tana kwasan gaisuwa, Giwa ta jinjina mata kai alamun ta fice ta basu waje.... Take Jakadiya ta nufi k’ofa kai a k’asa tana mai kuma kirariwa yaran Sarkin....
Yanayinsu kad’ai ya tabbatarwa Giwa wani abu na faruwa, kan Fu’ad a k’asa har lokacin bai daina sakin huci a hankali ba....
Giwa tai gyaran murya tana mai furta “Lafiya Sadauki meke faruwa... Ya na ganku haka..? Wani abin ne ya faru...?!”
Da idanunsa masu firgitarwa ya tsare Fu’ad, hannayensa hard’e Ta baya, lokaci guda yake furta “Maami what’s wrong with your son...? Wasu irin labari nakeji cewa zaman da yayi a Cyprus babu abinda ya tsinana... Shin da gaske ne baida wani sana’a sai shan kayan maye..?!!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya....
Daidai lokacin Yarima Jamal ya shigo yana mai dubansu d’aya bayan d’aya yanda sukai tsaye carko carko....
Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Maami Wai meke faruwa ne a Masarautar nan.... Meke faruwa cikin gidan nan....? I need answers...!!” Ya k’arashe wannan karon yana duban mahaifiyar tasu....
Jamal dake tsaye yana rarraba idanu cikin wane irin yanayi k’arasowa yai a hankali had’ida d’an dafa hannun Mahmood.. Lokaci guda yake furta “Calm down Yaya... Babu wani abin tashin hankali dake wakana a Masarautar nan, I promise you....” Yana maganar yana duban mahaifiyar tasu data tsare Mahmood da idanu....
Duban mahaifiyar tasu Mahmood ya kumayi kaman zai magana, saidai tuni ta mik’e tsaye ta iso garesa, lokaci guda ta sakar masa murmushi hannayensa rik’e cikin nata take furta “Haka ne D’ah na, ka yarda da batun d’an uwanka babu wani abindake wakana wanda ya canza a Masarautar nan.... Kada ka soma d’iban jita jitan babban gida kaji d’ah na... Kaine Magajin mahaifinku, a zaman gida irin wannan na sarauta da d’inbin al’umma dole kak’i gani kak’i ji....”
Girgiza kai Mahmood yai kana yace “Maami ba wannan ba... Mai Fu’ad yake nufi da yace Yazeed Keda alhakin kasancewarsa haka...? Menene suka faru da bana nan...??!”
Wannan karon harta Fu’ad saida ya d’ago yana duban Mahmood tsoro da firgici k’arara saman fuskarsa, Wani irin bugu Giwa taji a k’irjinta tamkar an aza mata guduma....Ta ware idanunta sosai tana aikawa Fu’ad wani irin duba na tuhuma....
Jamal ne ya katse shirun da yin gyaran murya kana yace “Yaya kasan halin Yazeed, kasan among us all babu wanda yake shiri dashi face ni da nake tolerating d’insa da halayyarsa... Yaya kasan Fu’ad nada zuciya matuk’a.... So ya fad’i haka ne kawai to get back at Yazeed, sabida yasan idan yace haka bazaka k’yale Yazeed ba, Bawai da wani nufi ya fad’i hakan ba... And one more thing Yaya... Yes, Fu’ad ya had’uda iftila’ai da jarabawa na shan kayan maye, but that was tin yana Cyprus, yeah koda ya dawo he was depressed sabida gani yake ya k’arar da rayuwarsa a iska ba tareda yayi abinda ya kaisa Cyprus din ba, wannan ya kuma Sa Fu’ad ya koma ruwa tsundum shaye shayen miyagun k’wayoyi to get rid of his problems... Anyi ta k’ok’arin ya rabu da abin gaba d’aya don har Rehab a Abuja an kaishi... Allah ya taimaka a cen Rehabilitation center d’in ya rabu da abin completely...ya dawo bai shan komai, ina mai tabbatar maka Fu’ad bai shan komai a halin yanzu Yaya....!” Ya k’arashe cikin tsananin sanyin murya...
A hankali Giwa ta sauk’e wani irin ajiyan zuciya cikeda jin dad’i, dama ta sani idan ba Jamal ba babu mai iya gyarota, shi d’in d’an albarka ne mai tsananin sanyin zuciya a tsakanin yaranta....
K’uri Mahmood yai masa, dan gaba d’aya cikin ‘yan uwan nasa ya sani Jamal is different, tun tasowarsu mutum ne da ko mai zai fad’a maka iyakacin gaskiyarsa kenan dan haka take yaji sanyi can k’asar zuciyarsa... Tausayin Fu’ad ya kamasa....
A hankali ya soma takowa ya k’araso gaban Fu’ad d’in, ya d’an saka hannu saman kafad’arsa ya dafasa.... Fu’ad ya d’ago idanunsa masu zuban hawaye yana duban Mahmood...
K’uri Mahmood yai masa cikeda tausayawa kana yace “Is okay Fu’ad... Mu ‘yan Adam ne masu kuskure... We ain’t perfect, dukkanmu muna kuskure... Mafi alkhairi a cikinmu Sune wad’anda idan suka fahimci laifinsu sai su komaga Allah su tuba.... Ko wane irin abin kunya ka jawowa Masarautar nan ya riga ya wuce Fu’ad... Its all in the past now, ba’a amfani da abinda ya riga ya shud’e..!”
Kaman daga sama suka sinkayo muryar Yazeed yana fad’in “Correction brother!!”
Gaba d’aya suka juyo suna duban Yazeed dake takowa cikin d’akin cikeda isa da k’asaita, lokaci guda Yazeed yaci gaba da fad’in “Unfortunately a rayuwa irinta babban gida kaman Fada, dik abinda kayi a baya zai cimmaka a gaba... Baya tab’a shud’ewa haka nan kawai ya b’ace a tarihi bai bar wani sign ba....Am I right...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa....
Giwa dai K’uri tai masa tana jin kalaman d’an nata tamkar da ita yakeyi.... Yayinda Fu’ad ya mik’e cikin hawaye yana duban Mahmood, lokaci guda yake furta “Im sorry Yaya..!!” Daga haka bai kuma cewa komai ba sai sa kai da yai ya fice Daga parlorn cikin sauri....
Mahmood ya dubi Yazeed da wasu irin idanu saidai a b’angaren Yazeed d’in ko a jikinsa saima shu’umin murmushin nasa dake bisa fuskarsa, lokaci guda yama k’arasa saman d’aya daga cikin hanshak’an kujerun da sukaima parlorn k’awanya ya hakince kan guda d’aya had’ida bud’e hannayensa ya bazasu cikin kujerar kana ya d’auki k’afarsa guda ya aza bisa d’ayan... Ya daiyi zama irinta masu jin mulki da kuma isa... Ya tasasu gaba yana binsu da kallo murmushin bai bar saman fuskarsa ba, saima juya zoben azirfa dake yatsarsa guda da yakeyi a hankali....
Tamkar tv haka Jamal da Giwa Ke dubansa, shid’inma suke yake duba yana mai ci gaba da kad’a k’afarsa da ya azata saman guda..
Girgiza kai kurum Mahmood yai kana yasa kai yai ficewarsa shima, yayinda Jamal ya janyo hannun Mahaifiyarsu ya nufi bedroom da ita yana fad’in “Muje ki huta Maami....!” Babu musu tabi umarnin d’an nata, zuciyarta na wane irin yankewa, dan tinda taji labarin bayyanar mahaukaciyar nan a fada tasan wannan sharan fage ne, dole akwai wani babban al’amari da ya faru cikin Masarautar, fatanta Jakadiya Ta dawo mata da batu mai dad’i...
***
Muhibbah na zaune tana rarraba idanu tana duban kyau da tsarin d’akinda aka sauk’eta cikinsa Umaima ta turo k’ofa ta shigo... Cikin sauri Muhibbah ta mik’e tsaye su duka biyu suna sakin murmushiwa junansu...
Umaima taci gaba da fad’in “Kiyi hak’uri na barki Ke kad’ai... Gashi ban samu ganin Maami ba, ta riga ta haura sama, Ina tunanin wani abin ne ya faru, zai wuya Ta sauk’o k’asa a yau d’un saidai ko zuwa gobe idan Allah ya kaimu....”
Girgiza kai Muhibbah tai a hankali kana tace “Babu komai Ranki shi dad’e, har dai Ina cikin gidan zamu gaisa ai, kinsan masu mulki basa son tak’ura inaga zaifi kyau ki k’yaleta har zuwa wani lokacin....!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi kwance saman black beauty face d’inta da yake tas dashi babu alamun koda k’warzani...
Umaima ta murmusa kana tace “Muhibbah Ina mamakin ya akai kika San abubuwa da dama gameda masu mulki da kuma babban gida... Saikace a gidan sarauta kika girma... Kodai a babban gida kika girma ne...?”
Murmusawa kad’an Muhibbar ma tai kana tace “Ni kuwa Ta ina zan girma cikin gidan sarauta Ranki shi dad’e, bayan gidanmu mu uku tak muke rayuwa cikinta, daga ni sai Mummy saiko Yayana Ansar...”
Umaima Ta jinjina kai kana tace “Da alama ke d’in ‘yar baiwa ce.... Inaji a jikina zan k’aru dake sosai ko ince Masarautar nan zata k’aru dake sosai....” Ta k’arashe cikin sigar wasa...
A tare sukai murmushi mai d’an sauti kana Umaima tace “Bara naje na turo miki aike, nima zan shigo anjima kad’an.... Feel at home dan Allah kinji...”
Jinjina mata kai kurum Muhibbah tai had’ida kuma mik’a godiyarta a gareta...
Umaima na ficewa Muhibbah ta mik’e ta yaye tapkeken labulen tagar tana lek’en yanda k’wan wuta suka kuma k’arawa Masarautar kyau da tsari da shike almuru ya doso... Nan Ta hangi Fu’ad na fitowa Daga b’angaren Mahaifiyarsa kaman zai kifa da k’asa, yanayin data gansa ciki har yafi na ganinsa d’azu da tai... Tai saurin janyo alkyabbar Umaima wanda d’azu Ta barta a nan d’akin... Cikin sauri ta rufa alkyabbar akanta ta janyo hular ya sauk’o kusan idanunta kana ta d’an waiga gefe
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 65