Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Isha ta nufi layin bayansu gidansu k’awarta Meenatu... A parlor ta tadda Meenatu da k’annenta suna kallon shirin film a zeeworld yayyensu maza na shirin fita sallah suna masu fad’an suma su tashi su shige suyi sallah su bar kallon nan... Muhibbah ta gaisa dasu Yaya Huzaifa kana Ta nufo cikin parlorn... Meenatu na ganinta ta tafi da gudu tanai mata oyoyo had’ida tambayarta sauk’an yaushe... Tai aya tana duban idanun Muhibbar dake d’aukeda alamun kuka... Janyo hannunta tai suka nufi d’aki tana tambayarta lafiya meke faruwa... Muhibbah ta kuma saka hannu ta goge hawayen da suka ziraro mata “Meenah komai ma ya faru...!” Meenah Ta gyara zama tace “Ban gane ba, Kina nufin a sch d’in..A can Jos d’in... Kinga kin ma tuna min jiya a Islamiya Malam Ayuba Ke tambaya kwana biyu baya ganinki nace masa ai kin tafi makaranta Jos zaki k’ara karatu zakiyi Bsc Nursing... Toh.. Wai meke faruwa ne Hibbah..? Ni kinsa duk jikina yayi sanyi..!” Ta k’arashe cikeda kulawa... Ta Sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Meenah ba makaranta na tafi Jos ba...!” Meenatu ta dubeta da tsananin mamaki “Ba makaranta kika tafi ba... Toh ina kika tafi....?!” Cikin muryar kuka take furta “I went there for a mission Meenah... And everything now is a complete messed up...!” Jiki a sanyaye Meenatu ta zauna gefenta “Hibbah you’re scaring me...Wane irin mission kuma Ni Saamina....?!” Cikin zuban hawaye take furta “Zan fad’a miki komai k’awata... Zan fad’a miki harda labarin da baki sani ba game dani... But for now dan Allah so nake ki sanar dani ya kake gane kana son mutum...?!” Meenatu Ta rausayar da idanu kad’an tace “Toh yau kuma Keda kanki kike tambayar haka ta Yaya Dr... Bayan ked’in tuni kin tsaida gwani...?!” Muhibbah ta lumshe idanunta a hankali had’ida fuzar da fuci tace “Haka nayi zato a baya... Bayan abubuwan da suka faru dani a yau, inajin shakkun abubuwan da naji a baya... Please tell me Wai ma mecece ita soyayyar nan..?” Meenatu an tab’o chapter da take so... Ta murmusa kad’an had’ida rausayar da idanu, harda su sauk’e ajiyan zuciya tace “Toh ita dai soyayya wata aba ce da Allah ya kana halitta a zukatan ‘yan adam... Idan kina son mutum zakiji kin damu dashi sosai kuma kin damu da al’amransa gaba d’aya, sannan kina son kasancewa dashi...Idan ya shiga damuwa zakiji kema kin shiga damuwa... Haka idan yana cikin Farin ciki kema zaki tsinci kanki cikin Farin ciki...Kina gudun duk abinda zai b’ata masa sannan kina muradin duk abinda zai faranta masa... Na tak’aice maki soyayya is all about CARE...Kalman Kula da ita soyayya ke farawa kafin komai ya biyo baya.... Kin gamsu...?!” Ta k’arashe tana Ware idanunta gaba d’aya hab’arta saman hannayenta... Muhibbah dake kallonta tamkar wata d’aliba gaban malama ta jinjina kanta a hankali had’ida sauk’e ajiyan zuciya tace “Na gode k’awata... Bara na tashi naje kafin dare yayi..!” Meenatu tace “Kai k’awata da wuri haka... Ki tsaya kici cake gaya can Ummati na baking mana...” Muhibbah na daidaita mayafinta akanta take fad’in “Aiko ga k’amshin duk ya cika min hanci amma dai bazan iya jira ba, ku ajiye min nawa share d’in da safe ku kawo min.. Ina Mama ban gaisheta ba, kodashike barta kawai dare ma yayi na shigo gobe mu gaisa tinda yanzu na dawo...!” Meenatu tace “Toh bara na taka miki...!” Tai maganar tana janyo mayafinta suka jera suka fito a tare... Suna tafe suna hira har saida suka hango ‘yan masallaci na fitowa kana Muhibbah taceda Meenatu ta koma kawai gaya can ‘yan masallaci sun fito ma... Meenatu tace Ok sai goben, sukai sallama kowa ta nufi gidansu... A daidai gate ta had’u dashi ya fito masallaci... Da sauri tayi niyyan shigewa ya tare k’ofan “Ina kika fito a daren nan..?” Ya tambaya yana dubanta.. Fuskarta naga wane b’angaren tace “Ina ruwanka da yanda na fito, ko har yanzu zargin nawa kake baka yarda dani ba...?!” Dafe kansa yai kad’an yace “Wai har yanzu maganan zargin nan bazai fita daga bakinki ba... Hibbah why are you acting like this.. This isn’t you, gaba d’aya kaman an canzaki, yaushe kika soma maida min magana anyhow...!” Wannan karon galala ta dubeta kana ta kuma kauda kai gefe tace “Dan Allah ka matsa min na shige bazan iya jure tsayuwar nan ba...!” Ansar yai shiru yana dubanta, lokaci guda yace “Alright, naji zan matsa ki shige amma sai kin tabbatar min kinyi hak’uri kuma bazaki sake maganan zargin nan ba... Only then zan baki hanya ki shige... Ta d’an cizi leb’en bakinta kad’an tana mai duban wani gefe tace “Naji shikenan ya wuce... Ka matsa min na shige...” Ya d’anyi mata K’uri na dak’ik’ai kana ya matsa mata tasa kai ta shige... Bayanta ya biyo yana mai fad’in idan Mommy bata parlor ta jirasa a nan zai d’auko wayarsa a d’aki ya k’araso... Ko amsasa bata iya yi ba saima shigewa da tai cikin sauri... ** MASARAUTA Shi kad’ai a d’aki yana neman mafitar hanyar da zai b’ullowa Mahmood, bazai yuwu ya k’yalesa yaita cin kashinsa a ransa yanda yake so ba, har shi ne Mahmood zaice zai dank’asa ga Hukuma.. Toh ma su waye hukumar..? Ai Fada itace hukuma mai zaman kanta... He needs to take Mahmood outta his way completely... Toh amma ta yaya zai hakan...?! K’aran da wayar salulansa tai ne ya katse masa tunanin nasa... Zayyad ne mai kiran.. Ya d’aga kaman baison d’agawa.. Daga d’aya b’angaren Zayyad yace “Allah shi taimaki Sarki mai jiran Gado...!!” Gajeren tsaki Yazeed yai yace “Zayyad this place is a complete chaos...But trust me I’d never give up... The word losing is not even in my vocabulary... I was born to become a King..!!” Ya k’arashe cikin tsananin karaji... Daga d’aya b’angaren Zayyad ya murmusa yace “Gaskiya ne Your Highness, nasan bazaka tab’a giving up ba my King... The throne is surely yours... Allah shi ja zamaninka... Ai yanzu ma nake jin rad’e rad’i cikin gari kan abin kunyar da d’iyar Yarima Mahmood tai masa cikin d’inbin jama’an masarauta...!” Yazeed da baisan da wannan zancen ba, mik’ewa tsaye yai sosai yana furta “Ban fahimceka ba Zayyad.. Yimin bayani yanda zan fahimta, mai ya faru..?!” Zayyad yace “She creates a scene there... Apparently tana kokonton mahaifinta na b’oye mata wani abu, something very big da ta danganta da mutuwar Mahaifiyarta... Na tak’aice maka zance your Highness bayan abinda d’iyar Mahmood tayi bana zaton za’ai nad’in sarautarsa a matsayin Sarki..!” Baisan sanda ya bushe da dariya ba wanda ya jima baiyi irinta ba “At last labari mai dad’i... Zayyad kaci kyauta, Madalla da wannan labari naka...!” Bai kuma jiran cewar Zayyad ba ya katse kiran yana mai ci gaba da darawa shi kad’ai cikin d’akin... Ya akai Hauni Hadiminsa bai labarta masa wannan batu ba mai dad’i haka ba, kodashike gaba d’aya yau d’in shi ya hana Hauni kusantar yanda yake sabida tsananin b’acin rai da bak’in ciki da yake ciki... Zuciysrsa tayi wasai yanzun... Zahra itace greatest weakness d’in Mahmood... What if yaje ya k’yank’yasa wa Zahra wani abu gameda ko wacece ita...? Yai murmushi a fili yana mai jinjina kai lokaci guda yake d’an buga kafad’arsa kad’an yana mai ziga kansa da fad’in “You’re genius Prince Yazeed... Great..! Good..! Kaid’in na daban ne...!!” Ya kuma sakin murmushi yana mai furta “Sarautar taka ce Yazeed.!” Ya k’arasa jikin k’aramar fridge ya ciro kwalban barasarsa ya d’aga sama had’ida furta “Cheers to you victory..!” Lokaci guda ya kuma fashewa da wata irin dariya kana ya shiga kwankwad’a... ** Giwa zaune gaban Tal’udu ga wani bak’in tulu akanta mai tsananin nauyin gaske sai haki take gumi na tsartsafowa daga ko wane sak’o na jikinta... Tal’udu yaci gaba da sumbatu cikin wane irin yare maras dad’in ji... Take cikin bak’in tulun dake bisa kan Giwa ya kama da wuta bal bal... Tal’udu ya daka tsalle ya jada baya yana duban cikin tulun... Giwa kuwa k’ara Ta saki sabida azaban zafi da takeji daga tsakar kanta har zuwa k’asanta... Fad’i take “Ka cire min wannan azaban kai Tal’udu... Kar ka barni na halak’a..!!” Sai ihu take tana jin kaman ana dafa naman jikinta har zuwa b’argonta cikin wuta mai k’unan gaske... Take wutar ta kuma ruruwa sosai Giwa na kuma sakin k’ara har saida tulun ta tsage wutan ya soma k’ona sumar Giwa... Birgima ta shigayi a wajen tana ambaton Tal’udu ya taimaketa ya cire mata wutan dake k’onata... Da k’yar wutar ta daina ci amma kam ya k’one rabin sumarta... Ta koma gefe tana haki bak’in hayak’i ya b’ata mata fuska kaman wata dodanniya... Tal’udu ya tako gabanta ya kirawo sunanta cikin wata irin kakkausar murya “TURAI..!!” Giwa ta d’ago da k’yar tana kallonsa... Tal’udu yaci gaba da fad’in “Garin yaya kikayi sake Izzatu ta kufce daga hannunki..?!!” Giwa na haki take furta “Banida masaniya... Kayi duk abinda zakayi ka zak’ulo matar nan... Wannan shine aikinka dama...!!” Sandar hannunsa ya buga k’asa kana ya d’aga Kai sama yana girgiza kai yake fad’in “Na fad’a miki, duk randa mahaukaciyar nan ta bayyana tashin hankali ne gareki, sannan idan har kika sake ta kufce miki gaba d’aya hakan ka iya zamtowa bayyanar sirrikanki gaba d’aya... Kar ki mance na fad’a miki ita kad’aice zata iya sanar dake yanda yarinyar nan Saudatu take...!! Sannan abu na gaba d’anki Jamalu zai karya lak’anin da muka d’aura kansa cewa bazai tab’a yin aure ba... Kin mance kin sadaukar dashi ga Aljana Tamuna wacce duk ‘yanmatan da yake masu fyad’e k’wark’warori ne gareta... Duk macen da zai tara da ita dole ta na kusanceta kuma dole ta zamto k’wark’wara ga Sarauniya Tamuna... Kinga hakan na nufin Matar da zai aura dole ta zamto tamu... Sarauniya kuma bata tarayya da wata mace wani yaci gaba da tarayya da ita hakan na nufi D’anki Jamal zai iya mutuwa kenan idan har hakan ta kasance..!! Tun a fari ke kika janyo muka rasa wannan yarinyar Saudatu... Da ace Sarauniya Tamuna ta sameta da shikenan d’anki bazai shiga halinda yake ciki yanzu ba... Idan har kina son dawamammiyar Mulki irinta Sarauniya Tamuna dole d’anki yaci gaba da kawo mata k’wark’warori ta hanyar fyad’e wa k’anan ‘yan mata... Babu aure a tsarin mu Turai... D’anki Jamalu bazai tab’a aure ba... Wannan itace dokar..!!” Cikin rawar jiki Giwa Ke fad’in “A’a a’a Jamal Bazai tab’a aure ba... Alk’awari na maka... Shid’in bazai aure ba... Bazan rasa d’ah na ba...!!” Tal’udu ya kuma buga sandarsa yace “Turai fitilan tsafi ya hasko tashin hankali gaba gareki... Idan har baki nemo Izzatu cikin kwanaki UKU ba... Zaki iya rasa komai na rayuwarki, Mulkinki da kuma ‘ya’yayenki..!!” Ya k’arashe yana mai buga sandar tasa guguwa ya kaure b’att ya b’ace cikin d’akin.... Giwa ta shiga doka masa kira tana fad’in duka wanann iftila’in da take ciki yana nufin akwai wani gaba gareta...! Gefe ta koma tana shafa gefen kaita yanda wuta ya kwashe sumar... Da farko ta rasa hannunta guda da ya k’one k’urumus yanzu gashi ta rasa wani b’angare na sumarta... Shi haka wuta zaita cinye b’angarori na jikinta har ta k’one gaba d’aya kafin burinta na kafa ‘ya’yanta kan mulki ya tabbata..! Inaa bazata bari hakan ya kasance ba... Dole Waziri yasan yanda za’ai ya zak’ulo Izzatu duk yanda ta shige a fad’in k’asar kuwa... Da wanann tunani ta mik’e ta rufa alkyabbarta ta fito ta tadda Jakadiya.. _Sak’on ta’aziya ga d’aukacin members na Sameena Aleeyou novels sakamon rashin member guda d’aya da ya riskemu... Umm Jafar Muna addu’an Allah ya karb’i shahadarki... Allah ya baki Aljannah mad’aukakiya ya kuma d’ayyaba bayanki... Ameen thumma Ameen..! Dan Allah muna rok’onku da bakunanku masu albarka duk wanda yaga wannan yai mata add’ua.._ *MUHIBBAH* *49* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Jakadiya na ganinta tai saurin zabura kaman taga wani abin tsoro sai kuma ta zube tana kwasan gaisuwa cikeda tsoro, dan harga Allah uwargijiyar tata ta bata tsoro a yanayin data ganta ciki... Giwa ta watsa mata muguwar kallo tace “Dodanniya kika gani ko mai...?!” Jakadiya tai saurin girgiza kai tana mai kuma risinawa “Allah shi baki yawan rai kinfi gaban dodanniya annurinki da k’warjininki ya cika wajen nan gaba d’aya..!” Ta k’arashe tana d’ago babbar yatsarta alamun jinjina... Cikin zuciyarta kuwa cewa take ai kinfi gaban dodanniya a munin halitta yau d’in... Ta kuma risinawa tabi bayan Giwa dake kuma rufe fuskarta cikin bak’ar alkyabbarta... Mahmood dake tsaye sararin farfajiyan sashensa nan ya hangi mutane suna tafiya cikin bak’ak’en kaya... Kafin ya ankare sai wulk’awansu ya gani bai kumaga yanda suka nufa ba... Toh su wanene wad’annan..? Take tinanin abinda ya gani kwanakin baya ya dawo masa... Mutumin da ya tab’a gani cikin Masarautar da bak’ak’en kaya... Toh su kuma wad’annan su wanene... Shin su waye suke shawagi cikin dare a Masarautar..? He needs to find out..! Ya k’arashe tinanin nasa yana mai kuma k’arema fad’in Masarautar kallo daga can sama yanda yake tsaye... Zanen ginin gidan Sarauta da Wambai ya basa ya d’auko ya k’urama taswiran idanu sosai yana son fahimtar wani abu abinka da mai ilimin sanin sirrikan zane iri da kala... A hankali ya saka yatsar hannunsa guda yana bin wani layi dake jikin zanen, yaita bin dik wani hanya da layin ya ratsa har saida ya iso mahad’an layin yanda dogon layin ya tsaya... Da alama layin ba’a nan zai k’are ba, duk yanda akai akwai ci gaban wannan zanen dake rik’e hannunsa... Toh ina zai samu...?! Yai shiru tamkar mai nazari... A hankali ya ninke taswiran ya maidata ma’ajiyarta ya aje.... ** Juyi taketa faman yi saman gado amma babu bacci babu alamunsa, tayi salloli tayi addu’o’i amma duk dai baccin bai Zo mata ba... Idan ta rintse idanunta shi take hangowa sanda ya fito daga babban Zauren taro kwantattun k’walla cikin idanunsa, Ta mik’e ta zauna sosai tana tina tun Farin had’uwarsu sanda ya d’aurata saman dokinsa tun tana k’aramar yarinya, ta tuna had’uwarsu ta farko bayan komawarta da nufin tarwatsa ahalinsu, ta tuna sanda ya saving rayuwarta a cikin museum sanda ya tureta katako ya fad’i kansa...Ta tina kub’utar ta da yai yau d’in a hannun Yazeed.. Ta tuna yanda ya kawota har gida ya tabbata she’s safe...! A hankali ta kuma lumshe idanunta wasu hawayen suka gangaro mata... Shin Maiyasa rayuwa haka..? Maiyasa mutanen kirki suke shan wahala... Yanzu shikenan ta janyo mutumin da yafi kowa cancanta da mulkin Masarautar zai rasa sarauta kuma ya rasa d’iyarsa... Maiyasa ta mishi mummunar zato...? mutumin da tun farkon had’uwarsu bai mata komai ba sai d’inbin alkhairi..? Anya zata iya yafewa kanta abinda ta aikata garesa..? Tabbas zata rayu da guiltiness ne tsawon rayuwarta..! Ta koma jikin gado ta kwanta wasu hawayen masu tsananin d’umi suna kuma gangaro mata... Ta mik’e a hankali ta isa jikin jakan kayanta ta ciro zanen ginin gidan sarautar nan da mahaukaciyar nan ta bata, tai K’uri ma zanen tana kallo... Toh wacece mahaukaciyar nan da har sunanta ta kira alamun ta santa, sannan Maiyasa ta bata wannan Taswiran...? Tabbas tanada unfinished job a wannan masarauta, duk yanda akai mahaukaciyar nan tanada dalilinta na mallaka mata wannan Taswiran... Toh amma meye dalilin nata...? Babban tambayar ma a nan shin wacece wannan mahaukaciyar..? Ta kuma lumshe idanunta a hankali had’ida fuzar da fuci mai d’umin gaske... So many reasons for her to go back to that Kingdom... K’uri taima zanen tana kuma karamtarsa Dukda cewa ba fahimtar wani abu tai gameda zanen ba.... ** MASARAUTA Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Yazeed dake ci gaba da jinjina mata Kai alamun tabbatarwa “Uncle what exactly do you mean...? Uncle ban fahimceka ba..! Mai kake nufi...?!” Yazeed ya kamo kafad’un Zahra ya zaunarta saman kujera ya tsaya sosai gabanta yace “Zahra gaskiyar kenan... Mahaifiyarki ba itace ta haifeki ba... Ni nan da kike gani naji tattaunawarsu da Yaya na Mahmood before they left for Spain....!” _Flash Back_ Yazeed yaci gaba da fad’in “Cikin dare naga shigowar motarsa cikin Masarautar nan, nabi bayansa a hankali dan na kula da yanayinsa kaman akwai abinda yake b’oyewa... Aikuwa to my surprise sai gani nai ya fito da jaririya lullub’e cikin zani ya shige cikin sauri alamun baiso wani ya gansa... Nabi bayansa har zuwa sashensa ba tareda yayi noticing d’ina ba... Aliya dake zaune parlor tana jira dawowarsa, tana jin an tab’a k’ofa ta dubi time k’arfe biyu da rabi na tsakar dare... Share hawayen da suka gangaro mata tai ta mik’e tana jiran shigowarsa... Yana shigowa ta daskare tana duban abin mamakin da Yarima Mahmood ya shigo mata dashi... “Yarima... Mai nake gani hannunka..? Ina ka fito da jariri cikin daren nan....?!” Aliya tace cikin rashin fahimta... K’arasowa yai ya mik’a mata yana furta “Karb’eta ki ganta, ba jariri bane, jaririya ce... And I named her after my grandmother, Maman mai Martaba.. Na sanya mata sunan Fatima Zahra...!” Yai maganar yana mai duban jaririyar kyakkyawan murmushi saman fuskarsa... Kukan da Aliya ke dannewa yaci k’arfinta “Yarima... A ina ka samu jaririya, wacece mahaifiyarta..?!” Ya d’ago yana duban Aliya “She’s my daughter... And you’re her mother... D’iyarki ce Aliya, inaso ki rik’eta matsayin d’iyarki kuma har abada kada ki tab’a ce mata ba kece kika haifeta ba...!” “Yarima dan Allah ka sanar dani ina ka samo yarinyar nan...!!” Cikin d’aga murya yaceda Aliya “I told you she’s my daughter... ‘Yata ce ita d’in ‘yata ce, banida lokacin maki duk wani bayani... We’re leaving to Spain in a couple of days... Bana so kowa yasan da jaririyar nan cikin gidan nan... Not even Jakadiya... Bazasu San da labarinta ba har sai mun kuma dawowa k’asar nan wani lokaci... A lokacin zamuyi introducing d’inta matsayin d’iyarmu da muka haifa can Spain... Kin fahimta..?!” Aliya na hawaye Ta amshi jaririyar tana kallo, wane ikon Allah kallo d’aya taima jaririyar taji shauk’i na k’aunarta, kaman sunada connection haka taji koda shike Mahmood yace d’iyarsa ce k’ila sabida soyayyar da take masa yasa taji take itama son yarinyar ya shigeta... Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tana duban Yarima Mahmood lokaci guda take furta “Nai maka alk’awari zan rik’eta tamkar ni ce na haifeta, bazata tab’a sanin ba nice mahaifiyarta ba... Ta zamto tawa kaman yanda kake nawa, Zahra d’iyarmu ce ni da kai Yarima...!!” Ta k’arashe tana mai rungumar jaririyar hawaye na gangaro mata... Yarima Mahmood ya k’arasa ya rungumesu gaba d’aya yana mai furta “Kud’in ahalina ne... Ahalin da zamu rayu a Spain, cikin rayuwa mai ‘yanci ba tareda an tak’uramu da maganar bin dokoki na gidan sarauta ba.. Zamu rayu kaman yanda sauran mutane suke rayuwa babu tak’uri da nauyin bin dokoki irin na gidan sarauta... I promise to make you both happy... In sha Allah.. You two are my world..!” Ya k’arashe yana mai kuma matsesu cikin k’irjinsa....” Yazeed yana kaiwa aya ya kuma juyowa yana duban Zahra da tuni hawaye sun wanke mata fuska.... Ya k’araso gabanta ya duk’a yace “Zahra d’ago ki kalleni... Na aje wannan abu cikin zuciyata tsawon shekarun nan... But I know ko ba dad’e ko ba jima watarana zaki sani... As they say no secret remains hidden forever.... Mahmood ya b’oye miki haka ne dan watak’ila watarana zaki iya zama magajiyarsa... Amma kuma kinsan ko a shari’a d’an da aka haifa bata hanyar aure ba baida gadon Mahaifinsa... Mahmood yaji tsoron rasa Magaji a Masarautar nan shiyasa ya b’oye miki sabida Ke kad’ai ce k’wall magajiyarsa.... Zahra yau kinsan abinda mahaifinki ya jima yana b’oye miki tsawon rayuwarsa... Yanzu abinda ya rage miki shine kije ki tambayesa wacece mahaifiyarki... Da wacece yaci amanar Aliya har ya haifeki ta k’azamar hanya..!!” Ya k’arashe cikin karaji.... Mik’ewa Zahra tai tana kuka sosai take furta “So wannan shine dalilin.... Wannan shine abinda ya jima yana b’oye min... Paa ka cuceni, kazalunceni... Ka lalata min rayuwa... Na tsaneka na tsaneka...!!” Ta k’arashe cikin fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya... Yazeed yai K’uri yana duban yanda Yarinyar Ke kuka tana furta Ta tsani Mahmood... Muguwar murmushin nan nasa saman fuskarsa yake ayyanawa cikin zuciyarsa “That’s it Mahmood... K’arahenka yazo... Na tabbata zaman Masarautar nan zai gagareka... I’m getting rid of you at last.. Yarima Mahmood..!!” Ya k’arashe yana mai kuma gyara tsayuwarsa zuciyarsa nai masa wani irin sanyi.... ** Tafiya kurum take tana had’a hanya bataji bataji bata gani... Raheema dake tafe zata nufi sashen Yazeed wajen k’awarta Zuhra nan ta hangi Zahra ta nufi sashen mahaifinta tana kuka sosai... Lokaci guda Raheema ta fasa shigewa b’angaren Zuhra tabi bayan Zhara cikin sauri.... Yana tsaye tareda sabon Hadiminsa Barde yana basa umarni kan wasu abubuwa Zahra ta shigo kaman wacce aka jefota... Duban Barde yai ya basa umarnin tafiya kana ya maidoda hankalinsa ga Zahra wacce Ke tsananin huci... “Princess meke faruwa... Ya na ganki haka..?!” “Paa tell me the truth... Who’s my real mother..?!!” Tai maganar cikin tsananin dakewar murya... Zuciyarsa ta yanke lokaci guda, ya kuma duban Zhara da mamaki kana yace “Zahra lafiyarki... Where did you get that idea from... Tell me ina kika samo wannan gurb’attacciyar tunani...?!” Yai maganar cikin tsawa Ta d’ago idanunta masu zuban hawaye tace “Paa please na rok’eka, babu wani nok’e nok’e it’s over, na riga nasan komai, nasan Maa ba ita ta haifeni ba... I’m your daughter with another woman right..? So tell me wacece mahaifiyata...!!” “Get out Zahra... Fita nace kafin ranmu gaba d’aya ya b’aci...!!” Da tsananin mamaki take dubansa “Paa ka zaci bazan tab’a sani bane... Paa I’m not a kid anymore... For once in your life tell me the truth please..!!” Sauk’ar marin da taji a fuskrta ne ya sanyata had’iye sauran maganganun nata... Dafe da k’uncinta take dubansa da jajayen idanunta masu cik’eda k’unci hawaye naci gaba da gangaro mata.... “I hate you... I hate you Paa..!!” Tana kaiwa nan ta fice a guje... Raheema na k’ok’arin tareta Ina ko tsayawa batai ba... Juyowa Raheema tai ta dubi Mahmood dake ci gaba da sakin huci, lokaci guda ta isa ta kawo masa ruwa tace dashi ya zauna yasha ruwa... Bai mata musu ba ya zauna ya amshi ruwan yana kwankwad’a zuciyarsa naci gaba da masa d’aci.... Bai tab’a zaton zaiga negative impact a irin tarbiyan tashin cikin turawa da d’iyarsa tai ba sai gashi yanzu yana gani...Muryar Raheema ya katse masa tinaninsa “Your Highness, Kai hak’uri har yanzu ita d’in yarinya ce... But...!” Shiru tai ta kasa ci gaba da magana sabida tsananin shakkunsa da take ji... Wani duba Mahmood yai mata yace “Continue, ci gaba... Go ahead and ask me... Nasan kema shakku kike gamedani bayan abubuwan da kikaji Zahra ta fad’i mun... Right..!” Saurin girgiza kai Raheema tai tace “Your Highness bazan tab’a saka kokonto ko shakku gameda kai ba, I know you’re a good person, kuma nasan ko meye kake b’oye mata is for her own good... Na sani bazaka tab’a yin abinda zai cuceta ba... Your Highness na yarda dakai d’ari bisa d’ari... Idan da zakabi shawarina, kai gaggawan d’auke d’iyarka daga Masarautar nan... Send her to boarding school, idan hakan bazai yuwu ba kafin ka rasa Martabarka da kimarka cikin Masarautar nan ka d’auke d’iyarka ku koma yanda kuka fito... Babu komai cikin Masarautar nan sai cin amana da tashin hankali, kai tunani Tunda ka dawo babu wani abu mai kyau da ya faru dakai sai akasin haka... Ka d’auki ku koma can Spain ki ci gaba da rayuwarku mai tsafta babu hayaniyar cikin Masarautar nan... But before then make sure ka sama wa d’iyarka uwa... Kar ka mance Zahra tana delicate stage ne yanzu... Gaba mai had’ari take, tanajin kanta itad’in yanzu young lady ce... A wannan shekaru na teenage da take ciki tana buk’atar uwa a tattareda ita your Highness... Ka sama mata uwa wacce zata kula da ita da shawarwari masu kyau ku tafi ku koma Spain... Shawarina kenan your Highness..!” Ta k’arashe cikeda kulawa... Mahmood da yaima b’angare guda k’uri sai faman juya cup d’in dake hannunsa yake yana kuma jinjina maganan Raheema... Raheema tai masa K’uri zuciyarta na mata dad’i, Tunda ta kula asirinsu ba kamasa zai ba gwara tai amfani da wannan damar ta saye zuciyarsa da kalaman kwantar da hankali, ta gwammaci suyi aurensu su tafi can Spain d’in dan dama ita wannan sarautar ba wai ya dameta bane muddin zata sami Mahmood ita shikenan koda sarauta ko babu sarauta ba damuwarta bane.... A hankali ta mik’e ta risina tace “Na Barka lafiya your Highness...!” Lokaci guda tasa kai zata shige sai sinkayo muryar Mahmood d’in tai ya ambato sunanta... Taja ta tsaya kana ta juyo a hankali ta risina had’ida amsa masa... A hankali ya furta “Thank you..!” Raheema ta murmusa zuciyarta na mata wasai ta jinjina masa kai a

Chapter 31 of 65