Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta k’araso a hankali kyakkyawan murmushi saman fuskarta, tana duban mahaifin nata yanda ke zanen cikeda k’warewa had’ida shauk’in abinda yakeyi..... Daga cen gefe ta zauna ta d’ora hab’arta saman hannunta guda tana mai duban mahaifin nata murmushi bai bar saman fuskarta ba.... Aje alk’alman dake hannunsa yai kana ya kaikaito yana dubanta shima d’in murmushin ne saman fuskarsa... “Such a beautiful evening.. Everything is so beautiful...!” Zahra ta fad’i fuskarta d’aukeda murmushi, lokaci guda ta isa ta mik’a masa pills d’in... Babu musu ya amsa ya sha yana mai mata godiya... Ta koma ta zauna daga gefe tana mai ci gaba da duban Art work d’insa... Sihirtaccen murmushi saman fuskar Yarima Mahmood yace “Do you like it...?” Ta fad’ad’a murmushinta “Of course I love it Paa...it’s so beautiful..!” Ya murmusa shima yana mai kallon zanen.. Ga wanda yai masa Farin sani zai iya fahimtar wani yanayi ne mai wahalan fasaltuwa Yarima Mahmood Ke ciki... Yayi nisa duniyar tunanin sanda ya sinkayo muryar Zahra na fad’in “Tunda muka dawo k’asar nan banga kayi painting ba Paa bayan kuma sanda muke Spain kana matuk’ar son Painting... Naji dad’i dana soma ganin Paa d’ina na Spain na dawowa gradually... I’ve missed the old you Paa...!” Ta k’arashe cikin tsananin raunin murya irinta mai kuka... Janyota yai ya rungumeta kad’an had’ida share mata hawayenta, tausayinsu su duka biyu na ratsa zuciyarsa, ya sani zai matuk’ar wahala ya koma Paa d’in da Zahra ta sani a baya musamman ranan da tasan sirrin da ya jima yana b’oye mata tsawon shekarun nan... Zama sukai saman kujera hannayensu cikin na juna, lokaci guda Mahmood yai gyaran murya kad’an “Zahra... Inaso ki saka a Ranki duk abinda zai faru ina k’aunarki kuma kar ki tab’a kokonton haka kinji koh...!” Ta d’an saka bayan hannunta Ta goge hawayen da ya gangaro mata kana tace “Paa, is there something you’re not telling me...?!” Hannu yasa ya d’an dafa kanta kad’an kana yace “I love you.... Is getting late, tashi kije Ki kwanta... You’ve school tomorrow..!” Ya k’arashe yana mai mik’arta tsaye... Tai masa K’uri tana mamakin har yanzu kallon k’ararramar yarinya yake mata, bata kuma cewa komai ba sai jinjina masa kai da tai... Murya can k’asan mak’oshi tace “Que pases una buena noche paa..!” (Na barka cikin dare mai aminci Paa) Ya jinjina mata kai a hankali alamun amsawa kana Zahra tasa kai ta shige jiki a matuk’ar sanyaye... Ya bita da kallo har Ta b’acewa ganinsa... A hankali ya lumshe gajyayyan idanunsa yana mai shak’an iskar Ubangiji... ** Yazeed ya kuma duban Ubandoma a karo na biyu kana ya gyara tsayuwarsa yana mai maida hannayensa duka biyu baya “Ka shirya kayi magana...?!” Ubandoma ya d’ago jigataccen fuskarsa yana duban Yazeed, ya had’iyi miyau da k’yar cikin rashin sanin abinyi.... Lokaci guda ya kuma kauda fuska gefe.... Yazeed ya tako gabansa cikeda k’asaita “Kar ka damu kanada daga nan zuwa wayewar gari, karka mance gobe kake cika kwanaki uku rufe a wannan fursunan da bakada ranan fita muddin baka yanke shawarin da zai ceceka ba... Idan kuma kaga ka fice daga Fursunan nan ka tabbata gawanka aka fitar, dani dakai munsan yanda al’amara ke gudana cikin Masarautar nan... So shawari ya rage naka Ubandoma..!” Ya k’arashe shu’umin murmushi saman fuskarsa.... Yazeed yana ficewa Ubandoma yaci gaba da matsan k’walla, shin da waye zai Yarda Mahmood ne kokuwa Yazeed ne..? Yasan babu mai ciresa a ukun da ya shiga face Allah... Toh waye zai sanadin fitarsa Mahmood kokuwa Yazeed... Sarai yasan shirin Giwa akan Mahmood ya kuma san idan yayi gigin sanar da Mahmood wani abu toh fah saidai wani bashi ba dan ko shakka babu Waziri da Giwa har lahira zasu aikasa... Toh amma Yazeed fah... Yace zai basa muk’ami a mulkinsa, ya masa alk’awra masu yawan gaske... Amma zai cikasu..? Amsar da baida tabbas akai... Wata zuciya tace tabbas idan har kai sanadin hawansa mulki zai baka duk wani muk’ami da kake so cikin Masarautar... Zai ‘yantaka k’ila ma har ka zamto Wazirinsa... Idan kuwa ka tsayaga Mahmood tabbas koda ka fice a gidan Yari zaka tabbata ne matsayin bawa k’ask’antacce ‘yanci da kake mafarkin samu har abada bazaka tab’a samu ba....! Ya k’arashe tinanin basa yana mai aza kafad’arsa saman katifa da aka sak’ata da buhu da ciyayi.... Can bayan ya kwanta da kad’an yaji ana kokawa jefa kansa cikin buhu.... Ubandoma ya mik’e firgit daga baccin da yake yana k’ok’arin k’watan kansa yana ihu neman d’auki.... Cikin azama yake kokawan k’watan kansa.... Kaman daga sama saiji yai b’at mutanen sun b’ace alamun sun danna layun zanansu... Bai ankara ba saiji yai an d’aukesa cak an fice dashi daga cikin furaunan gaba d’aya... ** Washe gari ta kama juma’a ranan da masu sarautun gargajiya na cikin Fada Ke shirin shirya zama ta musamman dan tabbatar da Yarima Mahmood matsayin sarki mai jiran Gado.... Waziri sai safa da marwa yake cikin zauren nasa, ya kasa ficewa Fada... Shi kad’ai yakai mari yakai gwauro... Can wasu maza guda biyu k’arfafa suka shigo kawunansu a k’asa.... A d’ari Waziri ya nufesu yana furta “Yaya yaya menene labari... Kada kuce min bakuyi nasaran kashe Ubandoma ba...!” Matansa sai duban juna da ido kurum suke wannan ya kalli wannan suna kifa kawuna a k’asa suna sosa k’eya.... Daga impressions d’insu kawai Waziri ya fahimci basu cika aikin da ya basu ba... Wasu jahilan mari ya dinga d’aukesu dashi, cikin tsananin k’unan rai yake furta “Ashe ku sakarkaru ne... Ta yaya za’a ce bawan nan shi kad’ai ya gagareku....?!” D’ayan yace “Tuba muke mai Girma Waziri, gaskiya bashi kad’ai bane cikin d’akin wani ne ya taimaka masa...!” Waziri ya danna masa harara yace “Ban gane bashi kad’ai ba... Duk kuyi nasaran sakawa masu tsaronsa maganin bacci amma ku kasa kashesa...? Wai mai kuke nufi ne ma...?” D’ayan yace “Duk munyi haka mai girma Waziri, Ina mai tabbatar maka masu tsaronsa mun barbad’a masu hodar gusar da hankali amma mun iske wani cikin d’akin wanda bamu iya tantance fuskarsa ba shi ya taimakawa Ubandoma...!” Gumi ya shiga ketowa Waziri, sai faman kama gefen babban garensa yake yana kece gumin... Cikeda b’acin rai ya furta “Ku b’ace min da gani Bana buk’atar sake ganinku... Sakarkaru marassa amfani...!!” Suna ficewa ya kuma iza babban garensa kana ya fice ya nufi Fada a fujajan.... ** Turaki yai tsaye gaban paint work d’inda Mahmood yai a daren jiya yana kalla yana sakin murmushi a hankali.... Daidai nan Mahmood d’in ya fito cikin shiri farar jampa k’al sai k’amshin Dolce & Gabbana ke tashi a jikinsa lokaci guda yana k’ok’arin saka cuff links yake fad’in “Muje mu samu ayi addu’ar nan damu, and banso na rasa hud’uban juma’a...!” Juyowa Turaki yai yana duban abokin nasa har lokacin murmushin ne saman fuskarsa.... Mahmood da gaba d’aya hankalinsa kega mak’ala links d’insa jin Turaki yai masa banza ya sanyashi d’agowa yana duban Turakin.... Ya k’arasa abinda yake kana ya furta “I hope dai lafiya kake tsaye wajen kanata faman sakin murmushi... Ko Hidaya na hanya ne yau d’in...?!” Ya k’arashe cikin sigan zolaya... Turaki yai taku kad’an ya k’arasoga Mahmood d’in, har lokacin murmushin bai bar saman fuskarsa ba... “Rankaidad’e akwai abinda ake b’oye mana ne ba’a so mu sani...?!” Yai maganar cikeda zolaya... Girgiza kai kad’an Mahmood yai kana yace “Kaga babu lokacin hayaniyar nan naka Turaki...!” Bai kuma cewa komai ba yasa kai ya nufi downstairs cikin sassarfa... Turaki ya fad’ad’a murmushinsa yana furta “Allah huci ran Sarki mai jiran Gado tuba nake... Inama sarki zaimin izini na fad’i wani abu da ya tsaya min a mak’oshi....!” Shidai Mahmood bai amsasa ba har suka nufo parlor, yanda Turaki Ke ci gaba da fad’in “Yarima I can see you’re in love..!” Cak Mahmood ya tsaya ya kasa ci gaba da tafiya... Lokaci guda ya kaikaito yana duban Turaki, girgiza kansa kad’an yai yana mai furta “Where is that coming from..?!” Turaki ya gyara tsayuwarsa yace “You paint in the middle of the night when you’re in love... And this is exactly what happened when you fell for Marigayiya, Allah yai mata rahama... Musamman kake neman waje maras hayaniya ka keb’e kaita zanen abubuwa masu ban sha’awa a tsakiyan dare, Sannan zanan can da kai yayi shige da wanda kayi lokacin Aliya...!” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da takowa a hankali “Mahmood tell me wacece Ta kuma sace zuciyarka haka dan dai na tabbata ba Raheema bace...?!” Gajeren tsaki yai kana yace “Stop talking nonsense, will you..! You talk too much...!” Yaci gaba da tafiya dukda heart d’insa dake beating very fast... Lokaci guda yake furta “Banida lokacin shiririta nan naka Tukraki...!” Yai maganar yana mai ficewa daga parlorn... Turaki ya rakasa da ido hannayensa sakale cikin aljihu kana ya d’an fuzar da fuci kad’an had’ida tab’e baki murmushi saman fuskarsa... Mahmood kenan, shid’in yasan abokinsa Farin sani kuma ya san abokin nasa needs him now more than ever...! Ya kuma murmusawa a hankali kana ya takewa Mahmood d’in baya... ** Giwa ta kuma kece gumin da ya sauk’o mata.. Cikin tsananin tashin hankali take furta “Waziri bamuyi haka dakai ba, kayi alk’awarin bazaka bani kunya ba toh mai kuma nakeji haka... Ubandoma na raye...? Kenan duk wanda Ubandoma Ke masa aiki yafimu saurin motsawa kuma ko shakka babu shine bak’on Buzu, ina tsoron kada wannan bak’on Buzun ya rigamu isaga Mahmood... Dani dakai duka mun sani idan har ya rigamu isaga Mahmood toh fah kashinmu ya bushe cikin Masarautar nan...!” Ta k’arashe cikin tsananin huci tana hura hanci... Lokaci guda ta tako zuwa gaban Waziri, bata daina huci ba take furta “Waziri tun wuri ka gyara wannan al’amari... Matsaloli sunmin yawa ko kasan Jamal ya auka soyayya da yarinyar nan Umaima...? Sannan har yau Izzatu tak’i sanar dani yanda Saudatu take... Kodashike ta yaya zan tsammaci samun amsoshi daga wajen matar da babu hankali tattareda ita cikin sauk’i... Na bijiro mata tako ina amma babu wani canji, na mata da k’arfi na mata da lallama na mata da hauka duka babu canji... Waziri kar ka k’ara wani abin kan matsalolin da suke kaina, ka ida abinda ka riga ka soma... A binciko Ubandoma da mai taimaka masa yanda suka shiga suka fita idan kuma ba haka ba kana iya mancewa nid’in TAKACE....!” Ta k’arashe cikin tsananin karaji.... D’ago idanu yai yana dubanta, lokaci guda yake furta “Zan gyara abinda na b’ata na miki alk’awari... Sabida Ke Turai babu abinda bazanyi ba..!!” Ya k’arashe cikin tsumewa yana sakin huci.... Giwa ta murmusa a hankali kana tace “Inaso naga Mahmood saman karaga Sati mai zuwa...!” Waziri ya jinjina kai “An gama Allah shi taimakeki...!!” Daga nan ficewa yai waya manne kunnensa... ** Fitowarsu daga gidan Wambai suka nufi fursunan da Ubandoma ke rufe ciki dan yau ne wa’adin da Mahmood d’in ya d’ibar masa ya gama duk wani tunanin da zai kafin masarauta ta yanke masa duk hukuncin da zata yanke masa... Toh amma labarin da suka tadda wajen masu tsaron fursunan shine ya d’aure masu kai... Mahmood ya tsaresu da idanu yana karantarsu sai sosa Kai suke suna neman afuwansa.... Ya d’an taka kad’an zuwa cikin d’akin yana k’arema d’akin kallo... Ya kaikaito yana duban guard guda “Kace baku San yaya akai ya fice ba..?” Guard d’in ya jinjina kai cikeda risinawa “Allah shi baka yawan rai bacci ya d’aukemu daga nan bamu kuma sanin komai ba sai farkawa mukai muka tadda babu Ubandoma..!” Mahmood ya fuzar da fuci a hankali yana mai binsu da idanu.... Tsaban takaicin da suka sakasa ciki bai iya cewa komai ba saima fitowa daga cikin fursunan da yai Turaki na take masa ba.... Waya ya ciro ya kirawo Sankira yace a sanar dasu Galadima akwai zama yau d’in na gaggawa a nan cikin Fada... Kan kace mai masu sarautun gargajiya sun hallara... Waziri sai muzurai yake kaikace baisan meke wakana ba.... Gaba d’aya suka had’u a babban Zauren zama na musamman dake a cikin Masarautar... Waziri ne ya soma yin gyaran murya yace “Allah shi taimaki Yarima kuma Sarkin mu mai jiran Gado... Mun amshi sak’on kira na gaggawa daga bakin Sankira...Allah yasa dai lafiya...!” Ya k’arashe cikeda risinawa... Mahmood yai gyaran murya kad’an daga yanda yake zaune “Haka ne Waziri, na umarce Sankira ya kirawoku gaba d’aya dan na sanar daku abindake wakana cikin Masarautar...!” Wannan ya dubi wannan wancan ya dubi wancan haka suka dingayi.... Suna iya hango tsagoron b’acin rai kwance saman fuskar Mahmood... Waziri ya kuma duk’awa yace “Allah shi huci zuciyan Sarki mai jiran gado...!” Mahmood yaci gaba da fad’in “Na sani ko baku fad’i ba wasu daga cikinku zasuyi kokonton cewa ba ni ne na tura Ubandoma gidan Wambai ba sabida Ubandoma Hadimina ne..!” Basu iya furta komai ba sai duba da ido da suke dan gizonsa bazai bari su katse zancen nasa ba... Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Magana Ta gaskiya bani na tura Ubandoma gidan Wambai ba... Hasalima ni Mahmood banida masaniyar yayi hakan har sai bayan da aka kamashi..!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya hannayensa hard’e ta baya yayi tsayuwa irinta masu mulki.. Gaba d’aya suka shiga jinjina kai Waziri na fad’in “Wannan gaskiya ne Yarima... Kuma muna masu tabbatar maka duk mun aminta bazaka aikata wani abu mai kamada wannan ba... Dole a hukunta Ubandoma na cin amanan da yaima Masarautar nan...!” Mahmood ya kuma yin gyaran murya cikin muryarsa mai amo wanda kana iya sauraron dirin sautin nasa na amsa babban Zauren yake ci gaba da fad’in “A daren jiya Ubandoma ya gudu daga fursunan da aka ajesa wutin gadi.... A sabida wannan zanso ku gama duk wani shawarin da zakuyi zuwa gobe a nad’a sarki a wannan masarauta namu dan bazai yuwu muyita zama haka babu shugaba ba kowa yayi abinda yakeso... Sannan dole a zak’ulo Ubandoma yanda ya shiga ya fita...!” Rufe bakinsa Keda wuya suka sinkayo murya na fad’in “Basai kunsha wahalan neman Ubandoma ba... Gashi nan zai bayyana gabanku ya kuma fad’i wanda yake ma aiki dan hallak’a rayuwar Wambai... Sannan da akai rashin sa’a aka kamashi sai wannan mutumi ya tura a kashe Ubandoma a daren jiya... Ni ne nan na ceci rayuwar Ubandoma, da yanzu ya zama tarihi kaman yanda saura suka zama...!” Ya k’arashe yana mai k’arasowa gaban Yarima Mahmood su duka biyu suna duban idanun juna... Yazeed ya sakar masa shu’umar murmushin nan nasa kana ya maidoda dubansaga masu sarautun gargajiya dake faman jifan juna da kallon mamaki, gyaran murya yai kad’an yana mai takowa gaba garesu cikeda k’asaita yake furta “Kuna mamaki ne...? Well, gaskiyar kenan mutumin da kuka d’auki yarda kuka d’aura masa shid’in ba mai gaskiyar bane kaman yanda duk kukai zato...” Waziri dake faman muzurai ne gumi na kuma keto masa yai azaman katse Yazeed da fad’in “Hattara Yarima Yazeed, kasan cewa Sarki ne gaba gareka...!” Yazeed ya watsawa Waziri jahilan kallo kana ya matso dab gaban Wazirin, ya tsaresa da idanu kaman zai magana sai kuma ya saki murmushin nan nasa... “Waziri kenan, ai a iyaka sanina ba’a nad’a Muk’amin Sarki a Masarautar nan ba tun bayan mutuwar mahaifina... Saidai kuma ban sani ba idan Kai ka nad’a... Kuma ma ka d’an dakata kad’an... Ai a iyaka sanina duk mutumin da aka kamasa da laifi mai girma irin na kisa da cin amanan masarauta bazai tab’a yin mulki ba haka nan jinjinsa bazasu tab’a gadan sarauta ba... Shin nayi gaskiya..?!” Ya k’arashe cikin sigan tambaya yana mai tsare Waziri da firgitattun idanunsa... Waziri bai iya furta komai ba sai muzurai da yake yana k’ok’arin had’iye ragowar tuk’in goro da ya tsaya masa a mak’oshi... Yazeed ya kaikaito cikeda iko kana yaci gaba da fad’in “Wai aka ce wak’a bakin mai ita tafi dad’in saurare... Hakimai masu daraja Zan bada izini a shigo da Ubandoma domin ya fayyace maku komai da bakinsa...!” Lokaci guda ya dokawa Hadiminsa Hauni kira yace a shigo da Ubandoma... Ga mamakinsu sai hango Ubandoma sukai na shigowa kai a k’asa hannayensa a d’aure waje guda.... Manyan masu muk’amin cikin Fada suka ci gaba da kallon kallo suna ‘yar k’usk’us tsakaninsu... Masu aza babban gare daga zaune nayi.... Ubandoma ya k’araso ya zube a k’asa ba tareda ya iya d’ago idanu ya dubi jama’an dake wajen ba.... Yazeed yai gyaran murya kad’an yace cikeda isa “Kai muke saurare Ubandoma..!” Zauren yai tsit gaba d’aya ana jira aji daga bakin Ubandoma wanda ko motsi k’wakk’wara bai iyayi sai had’iyan miyau da yake da k’yar.... Ganin yayi shiru ya kasa magana yasa Mahmood soma takowa gaba gareshi cikin salo irinta masu mulki... Saida ya d’ibi wasu dak’ik’ai yana duban Ubandoma dake duk’e wajen yana muzurai daga zaune kana yai gyaran murya kad’an... “Karkaji tsoron kowa kuma kada kaji shakkan kowa... Ka sanar damu abinda Yarima Yazeed Ke k’ok’arin fad’i...!” Zuciyar Ubandoma yaci gaba da bugawa musamman yanda ‘Yay’an Sarkin guda biyu suka sakashi gaba... A hankali ya d’ago ya saci kallon Yazeed dake ci gaba da aika masa mugun kallo lokaci guda na sakar masa wannan murmushin nasa da gefen bakinsa... SameenaAleeyou📚[8/7, 8:10 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *41* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallon ina binka bashin ceton rayuwarka da nayi Yazeed Ke aika masa... Gumi yaci gaba da tsartfsafowa Waziri, ya kasa koda duban b’angaren da Mahmood yake balle su had’a idanu, hasalima bazai iya duban cikin idanun nasa ba.... Gyaran muryar da Mahmood yai ne wanda saida ya amsa illahirin Zauren ya sanya Ubandoma k’ok’arin had’o kalamai saman harshensa.... “K’warai... K’warai Wannan gaskiya ne Yarima Yazeed shi ya ceci rayuwana a daren jiya da aka kawo min farmak’i har cikin fursuna... Badon Yarima Yazeed ba da yanzu na zama tarihi nabi sahun Wambai....!” Ya k’arashe cikin rawar jiki.... Mahmood da tinda ya soma magana ya tsaresa da idanu cikin dakewar murya yace “Baka amsa tambayar da masarauta tai maka ba Ubandoma.... Shin wanene yake baka umarni... Wanene jagoranka a wannan laifi da kuka aikata...?!” Ya k’arashe cikin kakkausar murya mai amo.... Ubandoma ya kasa magana sai k’ok’arin ware idanunsa da tin bugun da Majidad’i yai masa ya sauya masu kamanni... Ubandoma ya kasa cewa uffan sai muzurai da yake... Ya jima yana ha’intan Yarima Mahmood duk bai isheshi ba ace yanzu kuma ya k’ago babban k’arya ya lak’a masa.. Muryar Yazeed ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yai nisa ciki “Kai magana Ubandoma.. Ka fad’i waye yake baka umarni..?!” Ya k’arashe yana jifan Ubandoma da kallon Karka mance na ceci rayuwarka you owe me that one.. Ya kuma had’iyan miyau da k’yar kana ya d’ago hannayensa dake d’aure yana k’ok’arin pointing Mahmood cikin tsananin rawar jiki, hannayen nasa sai b’ari suke ya k’arashe nuna Mahmood yana mai furta “Gashi nan... Gashinan.... Shine wannan...Yarima Mahmood ne..!” Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kurum Mahmood ke nanatawa cikin zuciyarsa... Yayinda sauran masu muk’amin Fada suka shiga tsananin shock, sai duban juna suke cikeda tsananin mamaki.... Mahmood ya lumshe idanunsa a hankali had’ida fuzar da fuci... Ya tako gaban Ubandoma ya tsaresa sosai da idanu, kan Ubandoma a k’asa ya kasa d’agowa sai matsan k’walla yake.... Waziri ya mik’e a birkice yana sab’a babban gare ya isaga Ubandoma dake duk’e wajen yana furta “K’arya kake la’ananne bawa... Ba’a haifi Bawan da zai tozarta jinin mulki a Masarautar nan... Tsinuwar Allah ya tabbata kanka Ubandoma... Allah ya kwashe maka k’ask’antaccen bawa..!!” D’aga hannu Mahmood yaiwa Waziri alamun dakatarwa cikin wane irin yanayi da basu tab’a ganinsa ciki ba.... Ya tako ya k’araso gaban Ubandoma... K’afafunsa dake rufe cikin bak’ak’en Lacoste cover shoe kurum Ubandoma ya gani yaji k’irjnsa yai wani irin bugawa kaman an sauk’e masa guduma...Jikinsa yaci gaba da karkarwa, ya soma yunk’urin d’ago idanu da zummar duban Mahmood saidai yana d’ago kai yai saurin maida idanunsa k’asa... Yazeed na jifansa da wane irin kallo... Take Ubandoma ya zube a wajen sunamme tun kafin Mahmood yakaiga masa magana.... Yazeed yai saurin duk’awa yana jijjiga Ubandoma lokaci guda yake cewa a kawo ruwa a yayyafa masa... Take d’akin taron ya hautsine... Waziri sai tokarinsa da k’afa yake yana fad’in suman k’arya yai ya tashi ya k’aryata abinda yace cewa Mahmood ne ya turasa gidan Wambai.... Waziri baiji bai gani sai tokarin Ubandoma yake, ta ko ina kai naushi yakewa Ubandoma dake zube wajen tamkar maras numfashi... A fusace Yazeed ya mik’e yana sakin wane irin huci yake nunida Waziri lokaci guda yake furta “Waziri..! Idan kayi sanadin mutuwar Ubandoma a wajen nan karkaji da Wai zan zaro takobi na fille wuyanka kaima take a wajen nan..!!” Yanda yake maganar k’irjinsa na sama na k’asa idanunsa a waje zai tabbatar maka cewa tsaf zai aika abinda ya furta... Waziri ya zaro idanu waje jin Yazeed na cewa har lahira zai kashesa muddin yayi sanadin rayuwar Ubandoma.... Take Waziri ya kifa kansa yana fad’in “Tuba nake Yarima..!” Yazeed ya kuma watsa masa wata muguwar kallo take ya doka kirawa Hauni, babu shiri Hauni ya k’araso tareda wasu dogarai guda biyu... Yazeed yace ya d’auki Ubandoma a wuce dashi asibitin cikin Masarauta a basa kulawa na musamman... Bayan ya gama bada wannan umarnin an kwashe Ubandoma an fice dashi ya maidoda dubansaga masu sarauta.... Gaba d’aya risinawa sukai gaba ga Yazeed saikace wani Sarki... Abin ba k’aramin dad’i yayiwa Yazeed ba ganin yanda masu muk’amin cikin Fada har sun soma basa girma tamkar an nad’asa Sarkin... Musamman da ya waiga yaga babu ko k’yallin Mahmood wajen... Murmushin nan nasa ya kuma sakewa, cikin zuciyarsa yake furta “Good... Bravo Prince Yazeed..! You actually did it... In no time zaka zama Sarkin wannan Masarauta... Burinka yana gab da cika... Kai d’in baka saka abu gaba Kaga kasawa...!!” Ya k’arashe tinanin nasa yana mai sakin muguwar murmushi lokaci guda kuma ya tsime sosai tamkar wanda ya tina wani abin.... Gyara tsayuwarsa yai had’ida yin gyaran murya ya dubi Waziri da gaba d’aya tamkar ba’a hayyacinsa yake ba kana ya kuma takowa dab gaban Waziri ya d’ibi wasu ‘yan dak’ik’ai yana duban Wazirin... Saida yai gyaran murya kad’an yace “Waziri... Na tabbata bakaso kai wasa da muk’aminka... Toh ina mai shawartanka da kai hattara kafin soyayyar da kake nunawa criminal irin Yarima Mahmood ya kaika ya baroka....!” K’asa k’asa yai maganar yanda Waziri ne kad’ai ka iya sauraro... Waziri ya had’iyi miyau da k’yar musamman da yaga yanda Takororinsa masu Sarauta tuni kaman sun soma goyawa Yazeed baya.... ** Tinda ya fito daga Zauren taron tafiyar kurum yake ba tareda yasan yanda yake jefa k’afafunsa ba... Kallo guda zakai masa ka fahimci yana cikin matsananin tashin hankali had’ida b’acin rai... Tafiyar kurum yake yana dukan k’asa da k’afafunsa yake ratsa cikin Fada, dik wanda ya gansa a haka sai yasha jinin jikinsa ya k’ame ya risina saidai shi Mahmood d’in baima kula da kowa, gani yake tamkar shi kad’ai ne tareda matsalolinsa cikin Masarautar... K’arfin halinsa yasa yake k’ok’arin danne abindake tasowa daga can k’asar zuciyarsa amma kam shi kansa yasan ana gab da kaisa mak’ura a Masarautar... Raheema da fitowarta kenan daga sashen Gimbiya Zeenat Ta hangi Yarima Mahmood tafe ya nufi sashensa, yanayinsu ya bala’in tada mata hankali... Ta dubi Hadimarta Mashkura da a yau d’in ita ke take mata baya... Jinjina mata kai tai alamun tana iya tafiya bata buk’atarta... Mashkura na shigewa Raheema tasa kai tabi bayan Mahmood... A daidai k’ofar sashensa Ta cimmasa, tai gyaran murya kad’an had’ida risinawa kaman yanda tarbiyan babban gida yake “Barkada yammaci Your Highness..!” Duba d’aya yai mata ya watsar Dan har yanzu ba Wai sun koma normal bane tun bayan tattaunarwarta da Juwariyya da ya sinkaya.... Raheema ta kuma gyaran murya kad’an tace “Rankaidad’e akwai abinda ke damunka ne... Kai hak’uri na tunk’aroka ba tareda iso ba... Yarima I just couldn’t help it... Ganinka haka ya d’aga min hankali.. Definitely nasan something is wrong... Zan iya taimakawa da wani abu....?!” Ta k’arashe tana k’ifk’if da idanu had’ida rau rau da fuska alamun nuna damuwa.... Dubanta yai na wasu ‘yan dak’ik’ai, ba tareda ya furta koda kalma guda ba yasa kai ya shige sashensa.... Raheema ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai ayyanawa cikin zuciyarta, wannan damarta ne to win Mahmood back zatai duk yanda zatai ta tabbata shid’in ya kuma zama nata a yau d’in... Murmushi Ta saki kana tasa kai Ta shige cikin sashen nasa... Tsaye ta hangesa ya bada baya yana duban window, hannayensa hard’e Ta baya... Raheema ta k’arasa Kai a k’asa yawa mutumiyar arziki... Saida ta kuma yin gyaran murya kad’an kana tace “Yarima there’s something I need to tell you... Ka cancanci ka sani...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... A hankali ya kaikaito yana dubanta, kanta a k’asa taci gaba da fad’in “Nasan ba lallai ka kuma yarda dani ba Yarima... I did something behind your back... But believe me nayi komai ne don amfaninka kuma with pure intentions... Yarima I

Chapter 25 of 65