Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rufe wajen har kawo ranan da kuka kub’utar dani cikin ikon Allah..!” Ya k’arashe yana mai sauk’e ajiyan zuciya...! Jafar yaci gaba da fad’in “Sun kashe Mai Martaba..! Kuma basu bari ya sanar dani abinda yake son sanar dani ba..! Sunyi zalunci mafi muni cikin Masarautar..!!” Baba Nomau yana mai girgiza kai yake jinjina zalunci irin na Giwa... Ubandoma yai shiru kaman mai nazari... Ya sani shi da hannunsa ya canza Jariri Ja’afar da d’an Bawa Sarkin Dawakan cikin Fada... Kardai Jafar d’an Sarki AbdulJabbar ne Giwa Ta damk’a masa ta umarcesa ya canza da gawan jaririn Sarkin Dawakai... Tabbas Giwa ta basa jariri a tsumma wanda baisan daga inda ta samo ba kuma ta umarcesa ya canza wannan jaririn da Jaririn Sarkin Dawakai wanda daga jaririn har uwar jaririn Ta kashesu... Ta kuma sanyashi ya kawo mata gawan jaririn amma banda na uwar yaron...! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un..! Yasan yayi mugayen ayyuka ma Giwa amma wannan yana d’aya daga cikin aikin da bazai tab’a mancewa ba sabida ya shafi jariri wanda baida hakkin kowa, hakan yasa tun tasowar Jafaru cikin Masarautar yake k’aunarsa dan yasan shi ya canzasa da d’an sarkin Dawaki bayan Giwa ta kawosa cikin Masarautar... Toh ina Giwa takai wancan gawan Jaririn da ya kai mata wanda ta saka shi ya canza da Jafar... Kenan Ta aje Jafar ya rayu da Sarkin Dawakai kan cewa uwar Jafar matar Sarkin Dawakai Ta mutu Ta bar jinjiri a raye kenan.. Bayan kuma ya sani Matsafan Giwa su suka kashe Matar Sarkin Dawakai da jaririnta, Giwa ta karb’i gawan jaririn ta canzasa ma uwar Jafaru... Toh Wai ma wacece Uwar Jafaru da Giwa tayi wannan badak’ala da d’anta... Maiyasa ta canza mata d’anta da macacce..?!” *MUHIBBAH* *63* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* A hankali take jin idanunta da suka matuk’ar mata nauyi suna bud’ewa... Ta saka hannayenta tana murtsuka idanun nata... Tin daga kan gadon da take kwance bisa ta soma bi da kallo har izuwa d’akin da take ciki... Ta d’aga kanta sama sosai tana duban d’akin wanda yafi mata yanayi royal bedroom, komai na cikin d’akin gwanin ban sha’awa ne da burgewa... Ta kuma mik’ewa zaune sosai tana mai kuma k’are ma tangamemen d’akin kallo, ga kayan ado na alfarma da aka k’awata d’akin dasu... Toh inane nan...? Yama aka tazo nan, ita abinda zata iya tunawa shine tana zaune rik’eda Taswiran da mahaukaciyar nan ta damk’a mata tana kallo tana hawaye tana ayyanawa cikin zuciyarta shikenan Allah ya nufa bazata San dalilin da yasa matar nan ta bata taswiran ba kwatsam Aunty Gudidi ta shigo da wani had’i cikin cup tace da ita maza ta kafa kai ta shanye yanada kyau wa amare..! Koda taji shigowar Aunty Gudidi sai tayi saurin dunk’ule takardan cikin hannunta.. Ta amshi cup d’in da d’aya hannun Ta kafa kai ta shanye abinda Aunty Gudidi Ta umarceta da Ta shanye, tin daga nan bata kuma sanin ina take ba tasan dai kaman bacci ne yayi awon gaba da ita...! Toh mai ya faru tinda tayi baccin..?! Kenan ta jefar da zanen garin bacci ba tareda ta sani ba..! Toh Wai ma ina sauran mutanen suke, ina k’awayenta ina Ansar.. Ina Mommy..? An d’aura auren ko ba’a d’aura ba..? Waima a wace duniyar take ne..??! Tambayoyin da Ta dinga jerowa kanta kenan... Ta mik’e k’afafunta a hankali ta sauk’o saga saman gadon tana mai taka cikin d’akin kaman mai tsoron tafiya... Allah ya gani kanta ya d’aure Ta rasa meke wakana a rayuwarta... Ta isa jikin window a hankali tasa hannunta kaman mai tsoron kada a ganta ta d’an janye labulen... Nan ne gabanta yayi wane irin yankewa ya fad’i, ta sake shafe idanunta domin tabbatarwa.. Cikin masarauta Ta dawo..? Waye ya dawo da ita..? Shin kodai Giwa tabi sawunta ne ta dawo da ita bayan ta fahimci itace Saudatu..? Kodai Fu’ad ne ya sanar dasu itace Saudatu kuma tana raye shine suka bita har gida suka saceta ranan aurenta suka dawo da ita cikin Masarautar..! Tinani barkatai taketa faman yi tana sak’awa tana warwarewa... Da alama daga ita sai suturan dake jikinta tazo... Gashi babu wayarta a tareda ita balle tayi k’ok’arin kiran Ansar taji meke faruwa.. Ita kam gaba d’aya kanta ya k’ulle.... Tana nan tsaye wasu bayi ‘yanmata guda uku suka turo k’ofa suka shigo... Gaba d’aya suka zube har k’asa suna kwasan gaisuwa wajenta... Muhibbah tabisu da kallo cikeda mamaki tana ganin abin banbarak’wai... Bayin cikin Masarautar sun saba duk’awa suna gaisheta amma yanda wad’annan suka zube gaba d’aya gabanta lokaci guda sai taga abin yayi mata wane iri... Ta kasa furta komai sai binsu da kallo da take... ‘Yar babbar matar daga cikin Kuyangin ta bud’e Murya tace “Sunana Kande sunan wancan Julde, ita kuma wannnan sunanta Hasiya.. Mune masu kula da al’amaranki da duk abinda kike so Ya Shugabata..! Ga ruwan zafi mai k’amshin furanni an shirya miki a ban d’aki Ki shiga kiyi wanka..! Idan kika fito sai ki sanar damu kalan abincin da kike so a kawo miki..!” Izuwa lokaci Muhibbah ta soma k’osawa da wannan karatun da Baiwar ke karanto mata wanda bama fahimta take ba, hakan yasa ta katseta da fad’in “Wa ya baku umarnin kuyimin wannan hidima..? Kuma Maiyasa aka kawoni nan aka ajeni..?” “Ki gafarceni ya Shugabata.! Umarni muke bi muma, idan kinyi mana izini zamu baki waje domin Ki kimtsa..!” Ta k’arashe kanta a k’asa... Muhibbah tai shiru yana dubansu ba tareda Ta kuma cewa komai ba... Can kaman bazatayi magana ba sai kuma tace “Ina son sanin umarnin wanda kuke bi...!” Kuyangar Ta murmusa kad’an tace “Zan sake neman gafara a gareki.. Ki gafarceni Rankaidad’e amma sanar dake umarnin wanda muke bi ba huruminmu bane... Aikinmu kad’ai shine kula dake... Allah shi taimakeki..!!” Takaicin Kuyangar ya kama Muhibbah sanin cewa ita Amarya ce ta tabbata mijinta da Mommy suna can suna neman duniyar take wannan matar ta zauna tana mata wani fadanci maras dalili... Ta dubi sauran bayin ‘yanmata guda biyun tace “Ku kuna iya tafiya amma Ke ki tsaya..!” Ta k’arashe tana nuni da Babbar wacce ta gama mata magana... Suka dubi shugabar kuyangar tasu ta jinjina masu kai alamun suje.. Take suka kuma duk’awa alamun girmamawa ga Muhibbah kana suka fice... Suna ficewa Muhibbah ta k’araso gaban Matar tana dubanta, lokaci guda kuma Ta zauna dirshan a gabanta itama, cikin yanayi kaman Ta mai son yin kuka Ta soma fad’in “Dan Allah Ki taimakeni..! Kada Ki bari azzaluman Masarautar nan su cimma burinsu akaina.. Wllhi nasan kasheni sukeda niyya... Kinga ni Amarya ce yau ake d’aura aurena suka sato ni.. Kin gani kinga k’unshi na kin gani dan Allah Ki taimakeni kema mace ce ki tai..!” Gaba d’aya tamkar wacce bata a hayyacinta haka yake maganganun tana nunawa Kuyangar lallen hannuwanta tana kwaye zaninta tana nuna mata na k’afafunta alamun tana tabbatar mata da cewa ita d’in Amarya ce.. Saurin rik’o hannunta Kuyangar tai ta dakatar da ita da fad’in “Kiyi hak’uri Rankidad’e, ni kaina banida bayanin da zan miki a halin yanzu.. Abu guda da na sani shine zaki rayu a nan na d’an wani tsawon lokaci... Watak’ila Ki samu amsoshin da kike nema..!!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye, Ta risina alamun girmamawa tace “Zan jiraki daga waje har ki gama kimtsawa..!” Ta k’arashe kanta a k’asa... Muhibbah tana gani Kuyangar nan ta fice ta barta nan zaune dirshan a k’asa wani irin kuka had’ida tausayin kanta na zuwa mata... Meke faruwa da ita..? Shin kodai nan ba Masarautar data sani bane.. Ko wasu mutane ne daban..! Innalillahi wa Innalillahi raji’un..! Shi take nanatawa cikin zuciyarta... Ta mik’e da sauri ta isa jikin window ko zata hango wasu mutane tayi ihun taimako... Toh amma idan tayi ihun taimako tasan babu mai taimakon nata tinda mutanen da suka ajeta a nan dole sun bata tsoron da bazata iya guduwa ba... Allah ne kad’ai zai ceceta daga wannan uku d’in data tsinci kanta ciki... Ta koma kan gadon ta zauna ta tak’ure waje guda tana kuka sosai... Daga nan cikin d’akinsa yana zaune saman sofa k’afarsa d’aya bisa d’aya yake kallon duk wani movement nata a makeken na’uran nasara dake gabansa wanda k’ank’anuwar camera dake cikin d’akin nata yana nad’o masa komai ya nuna masa... Yai mata K’uri yana duban yanda take cazgan kuka... Ta kuma mik’ewa ta nufi window harda ‘yar k’ok’arin tsallanta alamun tana son ta bud’e tagar tai escape... Yanda take tsallen yaso basa dariya amma bai dariyar ba sai ma saita remote da yayi ya kashe na’uran... Zobban dake hannunsa yake murzawa a hankali yana mai furtawa a fili “Whatever you’re hiding nasan dole zai fito... Sannu a hankali zan fahimci wacece Ke da kuma abinda kike b’oyewa...!!” Yai shiru yana nanata kalamanta ga Baiwar _Ni Amarya ce ki taimaka ki fitar dani, mijina na can yana nemana... kasheni zasuyi.._ Kalmar zasu kasheni data fad’i yaketa nanatawa, kenan tabbas akwai wani k’ulli da take dashi cikin Masarautar.. Ko menene wannan k’ullin... Sannu a hankali zai fahimci haka.. Ya k’arashe tunanin nasa yana mai warware zanen ginin gidan sarauta da ya samu a hannunta... Lokaci guda yake kuma karantar zanen... A hankali ya mik’e ya fito sararin waje daga nan saman benen nasa yana k’arewa fad’in Masarautar kallo... Can ya hangi motoci ‘yan kawo Amarya Raheema suna tururuwar shigowa... Ya saki murmushi da gefen bakinsa a hankali kana ya nad’e hannayensa ta baya yana mai kallon yanda motocin Ke shigowa sahu sahu... Yana ganin aka fito da Raheema rufe cikin Alkyabba aka nufi b’angaren Giwa da ita.. Bai kuma bi takansu ba sai ma sauk’owa parlornsa na k’asa da yayi ya kunna labaru... ** A can Fadar Giwa kaw ana tsaka da bukin al’ada Amarya Umaima na tsakiya an rufa mata alkyabba ana raye raye da kid’i kid’i kaman yanda yake a al’adarsu ranan d’aurin aure akanyi irin wannan bukiga amarya kwatsam sukaji isowar su Raheema da masu kawota...dama tuni labari ya iso masu cewa auren Yazeed da Raheema aka d’aura... Hankalin Giwa da Waziri idan yayi dubu ya tashi dukda k’ok’arin danne hakan da Giwa take dan a halin yanzu abubuwan dake kanta sun sha k’arfinta k’iris ya rage su tarwatsa mata kwanya, ga takaicin shikenan shirinsu na d’aura alhakin mutuwar Mahmood kan Raheema da Zeenatu ya tashi a aiki tinda ba’ayi auren da Mahmood d’in ba, Gashi tinda abin ya faru ko idanun Mahmood basu gani ba dan su duk a nasu zaton shima can wajen Auren Raheemar ya tafi hakan yasa Giwa bata ko yi tunanin nemansa ba... Har sai yanzu da aka shigo mata da Raheema matsayin matar Yazeed..! Yanzu ne suke kuma tabbatarwa Yazeed aka aurawa Raheemah ba Mahmood ba.. Tirk’ashi..! Kuka sosai Raheemah take cikin dandatson taron ‘yan biki tana fad’in itafah sai an canza wannan aure an maida kan Sarki Mahmood... Ita ba Yarima Yazeed bane mijinta...Gimbiya Zeenat na gefenta tana lallashinta... Abinka da gidan biki cike gidan yake da ‘yanuwa da abokan arziki dikda cewa sabida tsaban mugun hali irin na Giwa bata cika tara mutane ba amma an cika kam abinda da gida na sarauta... Matayen masu madafan ikon cikin Masarautar duk suna nan, kama daga matan Waziri Galadima Matawalle Liman Sardauna da dai sauransu duk Sun hallara a Fadar Giwan dashike yau d’in ranan shagalin buki ne Giwa ta dubi tawagan ‘yan tawagan kawo Amarya tace “Ku kwantar da hankalinku za’ai komai a tsanake irinta babban Gida...!” Muryar Zuhra ne kaman daga sama suka sinkayo tana fad’in “Ina girma a gidan da babu wani Girma..!” Gaba d’aya kallo ya dawo kan Zuhra harta Giwa saida ta kaikaito tana duban Zuhra dake K’arasowa cikin Fadar...! Zuhra ta K’araso tsakiyan taron ta isa har gaban Raheemah... Gimbiya Zeenat na k’iftawa Zuhra idanu kan tayi shiru amma inaa ko kallo bata ishi Zuhra ba... Zuhra ta tsaya sosai gaban Raheemah.. Ta saka hannu ta d’aga alkyabbar da aka rufa mata, fuskarta ya bayyana.... Murmushi Zuhra ta saki kana tace “K’awata ko ince kishiyata...Haba Amarya miye na d’aga jijiyar wuya kan cewa sai an canza aure ya koma kan Mai Martaba Sarki Mahmood..? Karfa ki mance kowa da daidanshi Allah yake had’asa kuma shi Sarki taimakonku kawai yayi ya rufa maku asiri gashi Ke kina neman tonawa kanku asiri..!” Gimbiya Zeenat ta katseta da fad’in “Ke Zuhra ya kike abu kaman ba d’iyar manyan mutane ba... Kaman ba jinin sarauta ba...!” Zuhra ta murmusa tace “Tuba nake Rankidad’e..! A gafarceni amma gaskiya nake fad’i... kuma Ita wacce aka d’aurama auren ta fini sanin gaskiya nake fad’i..!” Ta juyo tana duban Raheema da Hawaye Ke kuma gangaro mata tace “Da bakiyi bore kin tonawa kanku asiri ba kika bar abin a rufe kaman yanda Sarki mai adalci da halin Dattako yayi maku abin a sutirce da ya fi miki... Amma kika zab’i Ki tona kanku.. Toh nidai babu abinda zance saidai nace Allah ya bada zaman hak’uri dan idan a baya anyi zaman sharholiya da shagala yanzu kam saidai Ayi hak’uri... Ayita hak’uri da juna ana kai zuciya nesa dan shi maci mana baya fasa hali.. Sai ki gani ki kauda kai kiji kiyi kaman bakiji ba shawarita kenan...” Katseta Gimbiya Zeenat tayi da fad’in “Amma dai ke bakida kunya, dik yanda akai ke ba ‘yar babban gida bace... Kishi ne kawai yasa kike fad’in haka dan Raheema ta aure mijinki..!” Zuhra ta katseta da fad’in “Wazai b’ata lokacinsa ya tsaya kishi kan wanda baisan k’imar d’iya mace ba balle har yasan sadakar Aure.?! Rashin kunya yasan yanda ya samo asali... Auren Sarki Mahmood da kike k’ok’arin k’ullawa tsakaninsa da k’anwarki ba sabida komai bane sai don kinaso ku shanye Sarki Mahmood ya koma sai yanda kukayi dashi, dan bakida burin da ya wuce ki mallaki matsayin Giwa cikin Masarautar nan.. Shin gaskiya na fad’i..!” Ta k’arashe tana dubanta... Gimbiya Zeenat Ta soma muzurai tana tattare tabarmar kunya da bori... Ita kaw Giwa batai mamakin jin haka ba tinda har Waziri ma ya tasamma cin amanarta,kowa ba abin yarda bane a wannan Masarauta... Ita Giwa tana k’ok’arin k’ulla tugguwa Raheema da Zeenatu bayan Raheemar Ta aure Mahmood ashe suma su Raheemar da nasu k’ullin akan Giwan... Tirk’ashi Mahmood dai da baida hakkinsu gaba d’aya Allah ya tsallakar dashi, shiyasa duk abunda mugu ke k’ulla maka idan baka da hakkinsa sai Allah ya maida masa sharrinsa kansa... Gashi dai Allah ya tsallakar da Mahmood tsakanin k’ullin wad’annan mugayen mutanen... Taro ya hargitse mata aka soma ‘yar k’usk’us ana kame baki... Kayan kunya dai bazasu daina faruwa cikin wannan masarauta ba... Matar Wambai kaw da nata tawagar suka sami abinyi... Iyakacin kunya dai Giwa ta gama shansa a bainar jama’a... Haka aka dinga silalewa ana ficewa daga Fadar Giwa... Umaima kaw kuka Ta dinga yi ganin wannan kayan tashin hankali dake faruwa ranar aurenta... Haka Zahra da Hadimanta suka janyota d’aki suna lallashi... Giwa ma dai da taimakon Hadimanta ta bar cikin Fadar dan har yanzu Jakadiya jinya take bata warware ba da itace zatai jagorawa Giwa... Aka bar Raheema da tawagarsu nan wajen, sai kuma jinjina lamarin suke, masu k’usk’us daga gefe nayi.. Lallai sun sami labarin komawa masarautarsu dashi... ** Hankali kwance yake kallon tashan labaru na Aljazeera, hayaniyar Yazeed ya somaji da alama dogarai masu tsaron k’ofarsa sun hana Yazeed d’in shigowa... Can kuma saiga Yazeed d’in ya kutso yana fad’iwa Hadimin Mahmood koda wasa kada ya k’araso kusa dashi... Hannu Mahmood ya d’agawa Hadimin alamun ya fice ya k’yalesu... Barde ya risina alamun girmamawa kana ya fice... Yazeed na huci yake duban Mahmood lokaci guda yake furta “Yaushe Bayi k’ask’antattu suka samu ‘yanci cikin gidan nan da har zasu hanani shiga yanda duk nakeso a fad’in Masarautar nan... Waye ya baiwa Bawa k’ask’antacce ikon dakatarda ‘yantacce...!?” Daga yanda yake kishingide ya lank’wasa k’afarsa guda had’ida d’aura hannunsa guda saman k’afar yana murza zobensa a hankali, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa ya baiwa Yazeed amsa da fad’in “Ba ma kowa na saka shamak’i cikin ahalin gidan nan ba... Wa mutum d’aya na saka kuma kaine... So umarnina suke bi da sukayi yunk’urin hanaka..!” Yazeed na sakin huci yake furta “Ka daina yin wani abu kaman kaid’in ka zama Sarki... Karka mance har yau ba’ai bikin nad’aka matsayin Sarki ba, ba’ai maka wankan sarauta ba, ba’a mallaka maka sandar Mulki ba, ba’a d’aura maka rawanin Sarki ba, ba’a d’aura maka d’amaran Sarki ba, ba’a rufa maka alkyabbar sarauta ba, ba’a kuma buga maka Tambarin Saraki ba... Har yau baka d’ale Karagar ba suna suke baka a baki...So komai ka iya faruwa...! You never know mai zai faru anjima ko gobe... Everything is possible... Ta yuyu wannan karaga da kake ganin k’iris ya rage ka d’ale ba Naka bane..!!” Ya k’arashe yana sakin muguwar murmushi.... Murmushin Mahmood ya mayar masa kana yace “Allah shike bada Mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso a kuma lokacin da yaga Dama...! Zuciya da ta aminta da tayi imani da hakan bazata tab’a damuwa don ta samu ko ta rasa ba... Komai a rubuce yake tuntuni..!!” Yazeed yaci gaba da sakin huci yana duban Mahmood d’in yana ayyanawa cikin zuciyarsa ranan da Mahmood d’in zai San cewa ba Giwa ce ta haifesa ba k’ask’antacciyar Baiwa ce ta haifesa... Har ya sa kai zai fice sai kuma ya dawo da baya yace “Kayi gaggawan warware auren wasan yaran daka d’aura min dan ban amince da wannan auren ba kuma bazan amince ba...!” K’asaitaccen Murmushi kwance saman fuskar Mahmood yake fad’in “ Wuk’a da nama a hannunka suke dear brother..! Kayi yanda Kaso da Matarka taka ce..! She is all yours... Igiyar aurenta a hannunka yake ba’a hannuna ba sai yanda kaso kayi..!” Daga haka maida hankalinsa kacaukam ga talabijin yayi ba tareda ya kuma bi takan Yazeed dake tsaye nan waje takaici na neman kashesa ba... Ji yake kaman ya k’arasa ya lumawa Mahmood d’in wuk’a a ciki kowa ma ya huta... Ya tsani Mahmood ya tsanesa, baida babban mak’iyi a duniya sama dashi..! Fuuu yasa kai ya fice kaman zai kifa k’asa, duk ya fice hayyacinsa ko buttons d’in wuyar rigarsa bai iya had’awa duk ya koma kaman wani zaucecce lokaci guda.... ** Safa da Marwa kurum Giwa take nan k’uryar d’aki, takai mari Takai gauro... Ya zama dole taga Tal’udu dan yanda take tunanin al’amaran sun kai har sun zarce nan... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *64* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Koda Zuhra ta koma sashenta rungume yaranta tayi tana kuka sosai, sai kuma taji sam bata kyauta ba... Komin yaya ne halin Yazeed he’s still her children’s Father, Ji take kaman Ta muzanta yaranta ne a idon duniya... Gaba d’aya sai tausayin yaran nata ya rufe ta... Tana kuka ta rungumesu sosai tana furta su yafe mata dukda cewa yaran bama su fahimci nufinta ba sudai kawai sunga mahaifiyarsu na kuka sosai... Ta macen tasa hannu tana sharewa mamarta hawaye suna masu ci gaba da bata hak’uri.... Hadimarta Ta K’araso ta risina tace “Rankidad’e an gama shirya kayyakin gaba d’aya...!” Zuhra ta jinjina kai tana mai k’ok’arin saita kanta tace “Ki sauk’o da kayan k’asa gobe idan Allah ya kaimu fitan sassafe zamuyi...!” Hadimar ta jinjina kai had’ida risinawa tana mai amsawa... Sultan ya dubi nahaifiyarsa yace “Momy tafiya zamuyi..? Ina zamuje..? Ba’ayi hutun sch ba..!” Ta k’ak’aro murmushin k’arfin hali ta shafi kan yaron tace “Masarautar su Deedah zamuje baka so..?!” Jin an ambaci Deedah kakarsa sai ya soma murna yana cewa eh yana son zuwa...! Suna a haka Yazeed ya shigo tagajan magajan tamkar wanda aka jefosa... Sultan ya tafi ga mahaifinsa da gudu yana fad’in “Daddy zamu tafi Masarautar su Deedah kaima zaka bimu...?” Baki sake Yazeed Ke duban yaron cikin rashin yarda da abinda yakeji daga bakin yaron, ya dubi Zuhra wacce tai kaman bata San yana wajen... Bai ida mamaki ba saida ya hango Kuyangar taba sauk’owa da suitcases nik’i nik’i... Ya kuma maida dubansaga Zuhra wacce Ke k’ok’arin mik’ewa... Tamkar zautacce ya isa gareta yana fad’in “Can you tell me what’s the meaning of this..?!” Zuhra ta bud’e murya ta kirawo Hadimar tace ta haura da yaran upstairs.. Babu musu Hadimar ta k’araso ta risina ta gaida Yazeed Wanda ko kallo bata ishesa ba kana Ta janye yaran suka haura sama... Zuhra tasa kai kaman zata shige Yazeed yai saurin rik’ota da k’arfin gaske yana sakin huci yake fad’in “I think I asked you a question..?!” Murmushi tai wanda kai tsaye za’a iya cewa na takaici ne kana tace “Abinda idanunka ya gane maka Toh haka ne..!” “I’m still your husband Zuhra..! You’re not going anywhere.. Dan haka ki cire ranki... Kina nan a Masarautar nan tareda ni da yaranmu... Bazan tab’a barinki ki tarwatsa ahalinmu ba... Sultan zai gaji sarautar wannan masarauta dan haka bazan barki ki b’ata min shirina ba kin fahimta..!” Ya k’arashe yana sakin huci... Wulak’antaccen kallo take aika masa kana tace “Wane ahali kake magana..?! Ahalin da ka riga ka gama tarwatsawa.. Tausayin yarana nake ace sunada Uba irinka.. Shiyasa sam bazan barsu su girma cikin wannan Masarautar ba wanda koba jima ko ba dad’e sai an goranta masu halin mahaifinsu da abun kunyar da ya jawo masu..! Yazeed ka mance da batun aurenmu dan ka sami wacce zata maye gurbina a yanzu, yarana kuma bazan barsu hannun azzalumar matarka ba dan bansan wane irin tarbiya Zata basu ba, idan sun girma sun mallaki hankalin kansu zasu iya dawowa Masarautar mahaifinsu amma ba yanzu ba... A halin yanzu yarana ni sukeda buk’ata bakai ba...!” Tana ida fad’in haka tasa kai zata shige... Yazeed yai saurin shan gabanta yana mai ci gaba da huci... Sallaman mutane ne da suka sinkaya daga k’ofar Parlorn ya karkata hankalinsu.... Tawagan ‘yan rakiyar Amarya Raheema ne suka rakota sashen angonta.... Zuhra tana ganinsu Ta saki murmushi mai kyau kana Ta maidoda dubantaga Yazeed tace “Looks like your bride is here already, Allah bada zaman Lafiya ya kad’e fitina..!” Ta kuma sakar masa murmushi tayi hayewarta sama ya barsu... Shi kuwa Yazeed dafe da kunkuminsa yake dubansu... Baiko bi takansu ba yayi ficewarsa... Can spot d’insu ya tafi dan gaba d’aya ji yake duniyar na juya masa, da ace zai sami sararin yin kuka da yayi ko zai d’an ji sanyi cikin zuciyarsa... Haka ya dinga d’irkawa cikin barasa babuji babu gani a tinaninsa hakan ne kawai zaisa ya sami sauk’in abinda yakeji cikin zuciyarsa.... Tin ma’aikatan club d’in na d’aukan abin kaman wasa hardai sukaga abin ya zarce tunaninsu gashi yau d’in babu abokan Yazeed ko guda da suka je, haka dole guda d’aya daga cikin ma’aikatan ya d’aga waya ya kirawo Zayyad ya sanar dashi halinda Yazeed ke ciki... Babu shiri Zayyad ya k’araso ya tadda Yazeed sai layi yake yana sunbatu ma’aikatan club d’in sun hanasa fita bai biyasu kud’i ba... Yazeed ya cakumo guy d’in yana fad’i cikin murya irinta ‘yan maye “Kasan ko ni wanene...! Kasan ko ni wanene da har zaka hana ni fita...? I’m Prince Yazeed AbdulJabbar..! I can buy the whole club including you yourself..!” Ya k’arashe yana mai kuma shak’e masa wuya... Da k’yar Zayyad ya b’anb’are mutumin hannun Yazeed ya ciro kud’i ya biya bashin da ake bin Yazeed d’in kana ya shiga janyosa yana fad’in su tafi, Yazeed d’in sai tarjewa yake yana sunbatu yana amo da bak’in cikinsa... Har cikin Masarauta Zayyad ya kawosa a haka, yana shiga sashensa yaci karo da Raheemah cikin d’akinsa saman gadonsa ta baje tana shek’a bacci... Da tangad’i ya isa gareta ya k’ura mata idanu, baice komai ba ya nufi closet ya zaro belt ya nannad’e cikin hannunsa, Raheema da san bataji shigowar mutum ba sai sauk’ar bulala taji cikin jikinta, ta kwand’ara ihu ta mik’e tana fad’in kwarankwatsa ya fad’o mata... Yazeed yace “Bai fad’o maki ba tukuna somin tab’i ne wannan.... Uban wa ya baki izinin d’ale min kan gado..?!” Raheemah na hawaye take furta “Yazeed Ina zanje fisabilillahi, Aunty Zeenat ta koroni daga sashenta tace tinda Bazan zama matar Sarki Mahmood ba zamana wajenta baida amfani tace dole na tafi d’akin mijina na bar mata sashenta..!” Yazeed ya tintsire da dariya yana nunata da belt belt d’in yake fad’in “Itama tasan bakida amfani kenan tinda baki auri Mahmood ba... Toh haka nima babu amfanin da zaki min tinda kika kasa cika min burina na auren Mahmood... Da yanzu kin auri Mahmood da na zama Sarki amma sabida dolanci irin Naki kika bari Zuhra tabi bayanki har Ta gano ina kike zuwa...!” Cikin kuka Raheema ke girgiza kai alamun a’a tana fad’in “Wllhi Allah ban San Zuhra zataje wajen nan ba, kaima kasan nafi kowa yin taka tsan tsan... The

Chapter 42 of 65