daga mazauninsa ya komo gabanta, durk’usawa yayi nan gabanta yanda take shesshek’ar kuka bayan Ta gama karanto masa abinda ya faru da ita shekarun baya, shekaru goma sha biyar da ya shud’e....
Cikin tsananin k’unan rai yake furta “Dama abinda suka miki kenan.... Hibbah now more than ever bazan iya barinki Ki koma cikin Animals d’un nan ba.... Hibbah no..... No, bazan barki ba...!”
Cikin kuka itama Ta mik’e tana furta “Ansar ban sanar dakai ba saida ka amince mun da buk’ata ta... Ka fad’a ta yaya zan cika alwashin da na d’auka na fanasar rayukan iyayena har biyu.... Ta yaya zan sami justice d’in da nake nemawa kaina da iyayena...? Ansar those people are powerful, sunada dukiya da mulki, bazan iya shari’a dasu ba amma zan iya rama abinda suka min, Ansar ko a addini banyi kuskure ba dan na rama abinda suka min... The only way to get the justice that I deserve shine na shiga rayuwarsu and ruin them all... Kuma Wllhi alwashi na d’auka sai na tarwatsasu... Ansar you can’t stop me now....!!” Ta k’arashe cikin tsananin kuka mai tab’a zuciya....
A hankali ya fuzar da huci yana dubanta kana ya jinjina kai a hankali.... Shafa fuskarsa yai da duka hannayensa biyu kana ya zauna saman sofa gijif..... “You’re so stubborn..!” Ya furta a hankali
Muhibbah ta tako gabansa a hankali ta duk’a k’asa nan gabansa....
“please do this for me... And my parents...!” Tai maganar cikin tsananin rawar murya...
Da gefen idanu yake dubanta, saida ya d’an d’ibi lokaci a haka kana yace “Hibbah I’m sorry, how can I allow you to endanger your life just like that, Hibbah mai na zama...? I wouldn’t be there to protect you....And... what should I tell Mum.... Naci gaba da mata k’arya cewa makaranta kike a jos... What if tace zata Kai maki ziyara...? What if something went wrong...? What if your plan fails...? Hibbah what if... Na rasaki...? Do you think I can bear that...!!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya ga idanunsa da suka kad’a sukai jazir....
Mik’ewa tsaye tai tana goge ragowar hawayen idanunta kana tace “Shekara d’aya tak kawai zanyi cikin Fadar, da zaran an gama rikicin mulki, da zaran na gama tarwatsasu zan San yanda zanyi na fice daga wannan waje... And we would finally be together.... Please Dr... Kamin wannan alfarmar idan har da gaske kana k’aunata...”
K’uri yai mata kana ya kuma mik’ewa tsaye yana mai zagaya parlorn yake fitar da fuci a hankali, a hankali yake furta “This is a tough decision Hibbah...!!!”
“Ansar...!” Ta kirawo sunansa a hankali...
Sauk’e ajiyan zuciya yai kana yace “Shikenan, I don’t want you to think that I don’t love you... Zanyi komai as far as zaki kasance cikin Farin ciki.... Akwai Umaima d’iyar k’anwar Hajiya Turai Giwar Sarki AbdulJabbar mai rasuwa, a gaban Hajiya Turai take zama, zan kirata na sanar da ita akwai ‘yar uwata zatazo karatu na tsawon shekara guda a nan asibitin koyarwa na jos, kuma ta rasa accommodation gashi batasan kowa ba, zan rok’i alfarmar Ta baki masauk’i a nan Fadarsu, karki damu Umaima mutuniyar arziki ce, Sabon social media mukai, tana following page d’ina da nake bada shawarwari kan irin abincin da mutum zaikeci ya rage tumbi k’iba da sauransu, da yanayin motsa jiki da ya kamata ya dingayi... Daga nan muka saba dan idan naje Jos har gayyata Ta Fada tanayi tamin tarba mai kyau.... So na tabbata bazamu sami matsala daga wajenta ba in sha Allah....”
Tsananin Farin ciki yasa taji tamkar tai tsalle ta rungumesa.... Godiya taita jero masa cikeda Farin ciki... Ansar kaw dubanta kurum yake cikeda tausayawa musamman idan ya tuna labarin data gama bashi....
A ‘yan kwanakin Muhibbah ta soma shirin tafiya Fadar Jos, dan tuni Ansar sun gama magana da Umaima wacce tace dashi ya wuce neman alfarma wajenta, Fada gidansu ne shima, Masauk’i ko mutum nawa ne ya kawo zai samu balle k’anwarsa...
A b’angaren Mum d’in Ansar kuwa sanar da ita yayi Muhibbah makaranta zata tafi Jos kaman yanda suka tsara shida Muhibbar, Sam Mum batada labarin wannan al’amari nasu....
Koda tace zatai rakiyawa Muhibbah sai cewa Ansar Yai tai zamanta kawai tinda ba lafiya bane ya isheta shi zai kaita, hakan kuwa akai...
Muhibbah ta gama shirinta sukai sallama da Mum kana suka nufo Jos Babban gida.....
SameenaAleeyou📚
[5/20, 10:31 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*003*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kishingid’e yake saman darduma shatin kwabo ta zallar fata, yana sanye da riga ‘yar shara irinta shan iskar masu sarauta... Gaba d’aya sai shekarunsa suka bayyana ba kaman lokacin da yake turai yake saka k’anan kaya dake b’oye yawan shekarunsa ba, sam bazaka bashi shekaru 46 ba a lokacinda yake k’asar Spain, yau kam sai Zahra taga girman Baban nata ya d’an bayyan dikda cewa Allah yayisa mai kyaun k’ira, da sallama saman bakinta Ta shigo farfajiyar harabar benen yanda Yarima Mahmood Ke kishingid’e.... Ya aje jaridar hannunsa yana mai amsa mata had’ida mik’ewa sosai ya zauna, kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.... Lokaci guda yai alama da hannu ma dogarai guda biyu dake tsaye wajen tamkar an dasasu... Babu musu suka sa kai suka fice cikeda risinawa...
Kaman kullum yauma fuskarta a murtuk’e yake alamun har yanzu batai Na’am da hukuncin da mahaifinta ya yanke na dawowa k’asarsu ta gado da sukai ba....
Gyara zamansa yad’an kumayi murmushi saman fuskarsa yake dubanta, lokaci guda yake furta “Esa ropa te queda bien mi princesa..” (Kayan nan sun maki kyau my Princess)
K’ok’arin k’ak’aro murmushi tai kana tace “Buenos dias Paa..” (Barka da da hutawa Paa) Ta fad’i a tak’aice...
Hannunta guda ya kamo kana yace “Zahra d’ago ki kalleni....”
Ta d’anyi rau rau da idanu tana dubansa, shid’inma ita yake duba....
“Zahra Spain ba k’asarmu bane dole dik daren dad’ewa mu dawo nan wata rana... Ina fata ki fahimci haka...”
Share hawayen da suka gangaro mata tai kana ta soma fad’in “Paa ba Wai dawowa Nigeria bane bana so... Dejè mi vida allá en españa Paa... Mis amigas, mi escuela, and everything..” (Na baro rayuwata a Spain Paa, abokaina, makaranta na and everything)
Ta d’an ware idanunta kana taci gaba da fad’in “And you know what is worst...? Maami yanzu zata saka kayi aure, and Paa I hate Aunty Raheema... Bana so ka aureta Paa....!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya...
Bata Kai aya ba kuwa babban bawan Yarima Mahmood mai kula da al’amransa mai suna Uban Doma ya shigo had’ida zubewa k’asa cikeda ladabi irinta babban gida yake fad’in “Allah ya taimakeka Jakadiya ta sanar dani isowar bak’uwarka....” Yai maganar kansa a k’asa...
Duban Zahra Yarima Mahmood yanda annurin fuskarta ya kuma d’aukewa chak dan ta tabbata Aunty Rahima ce ta iso kaman yanda taji Kakarta d’azu na maganan tareda Jakadiya....
Ba don yayi niyyan maraba da bak’uwar tasa ba sai don baiso mahaifiyarsa ta kawo wani zargi ko kokonto gameda shirinsa, hakan ya sanyashi yin d’an gyaran murya kad’an kana ya jinjina kai a hankali, Uban Doma yasan mai hakan Ke nufi dan haka tuni ya kuma risinar da kansa yana mai furta “Godiya take Yariman Yarimomi Magajin Masarautar Jos.. Allah ya baka gidanku...Jaaa zamanin ka...!!!” Ya k’arashe yana mai baza jan babban gyaren dake jikinsa had’ida mik’ewa ya fice yana mai k’an k’an da kai alamun girmamawa.....
Zahra kaw tana jin haka mik’ewa tai tana mai furta “Paa zanje k’ofan Aunty Zuhrah.... Na Barka lafia Paa...”
Yarima Mahmood ya dakatar da ita da fad’in “Ki tsaya ku gaisa da Rahima....”
Kanta a k’asa kaman zatai kuka take fad’in “Pero Paa....” (Amma Paa) Kasa k’arashewa tai ganin yanda mahaifin nata ya kafeta da dara daran idanunsa masu firgita duk wani mai laifi....
A hankali ta shiga jinjina masa kai kana tace “Estaré abajo Paa...” (I’ll be downstairs Paa)
Ya jinjina mata kai a hankali kana ta mik’e cikeda risinawa ta sauk’o k’asa....
****
Tafe yake bisa k’osasshen dokinsa da shi kansa dokin tafiyar k’asaita da mulki yake, ko ba’ace ba zaka fahimci kilisa ya fito, bayan tattaunawa da su Galadima su Hakimi su Waziri da sauransu suka gudanar a yammacin jiya kan batun bada sarautar Masarautar dole ne ma ya fita kilisa ko zai rage wasu damuwar da sukai masa karan tsaye a k’ahon zuciyarsa...Dogarai guda biyu Ke take gabansa biyu Ke take bayansa, suna tafe suna kod’a Yazeed abinda yafi so a rayuwarsa... Kaman daga sama ya hangota tafe sun nufi sashen Mai Martaba itada Jakadiya, ‘yan mata bayi guda biyu suna take masu baya d’aukeda parantai na alfarma.....
Shu’umin Murmushi Yazeed yai kana yai gyaran murya daga nan yanda yake saman dokin, cikeda ladabi dogaran suka tsaida dokin dan sunsan mai gyaran muryar Uban gidan nasu Ke nufi....
Lokaci guda bawa guda ya k’araso had’ida duk’awa Yazeed ya taka bayansa ya sauk’o daga saman dokin, kan kace mai guda d’aya ya bud’e lema ya rufawa Yazeed wanda tuni ya doshi su Rahima da Jakadiya cikin tafiyarsa irinta masu ji da mulki da kuma isa....
Suna k’arasowa gaban Rahima ya yanke ya fad’i dan k’amshin turarensa kurum taji Ta fahimci shine ya k’araso wajen, janye hular alkyabban dake d’an rufeda fuskarta tai tana mai kuma tabbatarwa idanunta....
Tuni Jakadiya da bayin nan sun soma zubewa suna gaida Yazeed....
Duban Jakadiya yai had’ida yin gyaran murya kana ya furta “Jakadiya ina san yin magana da Rahima...!”
Jakadiya ta d’an d’ago a hankali kana tace “Allah ya taimaki Yarima Yazeed, Gimbiya Rahima tana kan hanyarta ne na ganawa da Yarima mai jiran gad.....”
Bai bari takai aya ba ya dakatar da fad’in “Jakadiya kin kaw San da wa kike jayayya...!!!!” Cikin tsananin fushi yai maganar, yayinda dogaransa Ke ci gaba da fad’in “Hattara Jakadiya, Hattara dai Jakadiya.. Allah huci ran Wakilin Sarki Marigayi....!!”
Cikeda tashin hankali Jakadiya Ta zube gwiwoyinta a k’asa tana mai furta “Tuba nake Yarima... Tuba nake Wakilin Mai Martaba...! Allah ya huci zuciyar Yarima..Tuba nake..!!!”
Baice komai ba sai gyaran murya da yai dan tuni Jakadiya ta umarci bayin nan su baiwa Yarima Yazeed da Rahima fili suyi magana...
Shima Yazeed d’in alama yayi da hannu wa dogaran nasa cewa su basu waje harda shi mai rik’e masa lemar....
Cikeda ladabi suka basu waje ya rage daga Rahima saiko Yazeed....
Shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa yake dubanta, banda lugude babu abinda k’irjin Rahima keyi.... Ta soma ‘yan waige waige tana mai furta “Yazeed not here please.... Mai kake tunanin kanayi ne... What if your brother sees us here, mai kake tunanin zai zaton muna tattaunawa... Na fad’a maka daga yanzu babu komai tsakaninmu ya riga da ya k’are tin lokacin da Mahmood ya amince zai dawo Masarautar nan... So please stay away from me, as far far away as you can....” Ta k’arashe cikin huci...
Murmushin bai bar saman fuskarsa ba idanunsa a kannare yake dubanta, lokaci guda ya tsime had’ida furta “You Shut up..!! Babu wanda yake d’aga min murya bari kiji na fad’a miki...!!” Ya kuma kannare idanu yana k’are mata kallo daga sama har k’asa wannan shu’umin murmushin nasa saman fuskarsa yake furta “Does my brother knows... Yaya na yasan saurana zai kwasa....?” Ya k’arashe yana mai shafa hab’arsa...
Waige waige Rahima taci gaba da yi kana ta rage murya sosai tace “Yazeed na rok’i arzikinka karka rusa min Farin cikin da na jima ina mafarkin samu tareda Mahmood, dan Allah ka barni na cika wannan buri nawa na mallakarsa.....”
Murmushi mai d’an sauti wannan karon yayi kana yace “Bazan hanaki auren Mahmood ba, amma da sharad’i guda...”
D’agowa tai tana dubansa cikeda k’osawa kana tace “Mecece sharad’in...?”
Hannayensa ya hard’e ya maidasu baya kana yayi gyaran murya kad’an “Sharad’in shine ko bayan kin auri Yayana zamu ci gaba da mu’amala da juna... Idan yayi miki banida matsala idan kuma bai maki ba, ina mai tabbatar maki ni da kaina zan tunk’ari Mahmood na sanar dashi komai sannan zan sanar da matata Zuhra kalan cin amanar da kike mata claiming to be her best friend.... Kinsan ni Yazeed zan iya dik abinda na jero...!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa...
Lokaci guda ya kuma gyara tsayuwarsa bai daina murmushin ba yake ci gaba da fad’in “Kije ku ganada Yariman naki, idan kun gama nima akwai ganarwamu da dare a yanda muka saba had’uwa...” Ya k’arashe yana mai fad’ad’a murmushinsa...
Lokaci guda yayi alamawa dogaransa suka k’araso kana ya dubi Jakadiya da itama k’arasowarsu kenan yai gyaran murya yace “Jakadiya na bar Gimbiya Rahima lafiya a hannunki, da fatan Gimbiya zata kular min da Yayana fiyeda yanda Marigayiya Ta kula dashi...!” Ya k’arashe murmushin nan nasa mai tsorata wanda ake jifansa dashi saman fuskarsa, anayin murmushi ne aji sanyi amma na Yarima Yazeed sam ba haka bane, tsoratarwa yake, yanda ya bambambanta da sauran mutane kenan....
Zahra daketa lek’ensu Ta window haka kurum taji tattaunawar da Uncle Yazeed suka gamayi da Aunty Rahima sam bai kwanta mata ba, ita dai Allah ya gani bata k’aunar matar nan sam, bata sonta da Paa d’inta, sam tarayyarsu bai kwanta mata ba... A hankali ta sauk’e ajiyan zuciya had’ida komawa cikin parlorn ta zauna saman kujera tana jiran k’arasowarsu....
Shigowarsu yayi daidai da sauk’owar Yarima Mahmood cikin shiga ta mulki da kamala ....Yayi kyau har ya gaji... Ba Rahima data daskare tana dubansa yanda yake sauk’owa daga bene tamkar wani d’awisu harta Zahra saida ta yaba kyaun da mahaifin nata yayi... Ta saki murmushi a hankali kana ta maidoda da dubantaga Rahima wacce Ta kafe mata Paa d’inta da idanu tamkar zata lashesa, take annurin fuskar Zahra ya d’auke....
Jakadiya da sauran bayin tuni suka zube suna gaidasa....
Rahima kam gaba d’aya Ta shagala da kallon Yariman nata, har saida Jakadiya ta d’an tab’ata kad’an alamun ta sadda idanunta kana Rahima tai k’ok’arin saita kanta had’ida sadda idanunta k’asa, ta d’an janyo hular Alkyabban nata zuwa goshi kad’an....
Cikin tafiya irinta wanda jinin Mulki da sarauta Ke Yawo a jinin jikinsa Yarima Mahmood ya k’araso parlorn, gaba d’ayansu risinawa suka kuma yi suna masu gaidashi cikeda girmamawa kana bayin nan guda biyu suka k’arasa saman tampatseten carpet d’in suka aje trays d’in dake hannayensu wanda Ke rufe da k’yallaye masu ruwan zinari saman darduma mai taushin gaske dake a saman carpet d’in, tuni suka kuma risinawa suna masu komawa cen k’arshen parlorn kansu a k’asa...
Jakadiya ce ta bud’e murya kana ta soma fad’in “Allah ya taimaki Dan Sarki jikan Sarki, Allah ya taimaki babban Yariman Yarimomi a fad’in Masarautar nan, Madallah da samuwarka a wannan masarauta, hasken annurinka ya haskakaka illahirin wannan masarauta, D’awisu kake Sarkin Ado, Farin wata kake sha kallo... Jakadiya tana maraba da sauk’arka Yariman Yarimomi...!!”
K’asaitaccen murmushi saman kyakkyawar fuskarsa ya d’anyi gyaran murya kad’an kana ya furta “Madallah da wannan yabo naki Jakadiya....”
Jakadiya Kai a k’asa take furta “Godiya nake Yariman Yarimomi.... Idan kamin izini zan gabatar maka da isowar Gimbiya Raheema,Zinariya k’wara d’aya tak a masarautar k’asar Akwanga...!” Ta k’arashe tana nunida Raheema wacce kanta ke kife k’asa sai faman murmusawa take....
Jinjina mata kai yai ba tareda ya kuma furta koda kalma ba kana Jakadiya ta soma matsawa da baya.... Kanta a k’asa take furta “Na barku lafiya Allah shi taimakeka...!” Ta k’arashe tana mai ficewa daga parlorn
Lokaci guda Mahmood Ke takowa zuwa gaban Raheema da Farin cikinta Ke ninkuwa.... Tana jin sanda ya iso dab gabanta ta kuma sadda kanta k’asa tana furta “Barka da sauk’a your royal highness...!”
Murmushi yai da gefen bakinsa had’ida jinjina kansa alamun amsa gaisuwar nata, lokaci guda yake nuna mata kujera kana yace “Bismillah..!”
Babu musu ta isa zuwa kujerar da yai mata nuni dashi ta zauna...
Zahra Ta d’an dubesa tana son ta soma zuba masa shagwab’a saidai sam bataga wannan fuskar ba dan gaba d’aya mahaifin nata ya juye mata babban mutum ne yau d’in tamkar wani babban basarake, saikace ba Paa d’inta data saba tsalle jikinsa ba, ita wannan na d’aya daga cikin abinda yasa bataso suka dawo Nigeria ba dan tasan dole wannan sarautar ya zama shamak’i tsakaninta da Paa d’inta, bazasu tab’a zama kaman yanda suke a baya ba...
Nuni yai mata itama da kujerar dake gefen Raheema yace ta zauna... Babu musu ta isa ta zauna dikda cin magani da take....
Raheema ta d’ago tana dubanta fuska d’aukeda murmushi, Zahra dai batako tankata ba saima dad’a d’aure fuska da tai, duban da mahaifinta yai mata ya sanyata sakin fuskarta kad’an kana ta gaida Raheema...
Raheema ta amsada sakin fuska tana k’ok’arin creating guntun conversation tsakaninsu....
A taka’ice kawai Zahra Ke amsata, shid’inma sabida mahaifinta ne dikda rabin hankalinsa naga wayar salulansa ne.... Suna nan a haka Uban Doma ya shigo cikeda risinawa had’ida zubewa yana mai furta “Allah shi taimaki Babban Yarima... Gimbiya Umaima tana neman izinin shigowa...”
Jinjina kai kad’an Mahmood yai alamun bada izini...
Godiya Uban Doma yai kana ya fice ya sanar da Umaima cewa anyi mata izini....
Cikeda risinawa Umaima Ta shigo ta gaidasu kana tace “Yaya inaso na kamin izini na d’auki Zahra dan ta tayani tantance kalolin abincin da zan sauk’i bak’uwata dashi... K’awata zata iso Masarautar nan a yammacin yau da yardar Allah...” Ta k’arashe fuska d’aukeda murmushi...
Zahra da kaman akan k’aya take zumbur Ta mik’e had’ida shagwab’e fuska tana fad’in “Paa please...!”
Murmushi ya d’anyi kad’an kana ya jinjina masu kai alamun suna iya tafiya... Umaima Ta risina had’ida masa godiya, itama Zahran godiyar tai masa cikeda risinawa kana Umaima ta janyo hannunta suka fice...
A b’angaren Raheema kaw ma iya cewa hakan yafi mata dan dama bawai San zaman yarinyar take a wajen ba kawai dai dan babu yanda ta iya ne...
Tuni ta soma zak’ewa tana sanar dashi kalolin abincin data girka masa, tai alamu da hannuwa bayin cewa suzo su bud’e farantan da suka shigo dashi... Shi dai gogan daki daki kurum yake dubanta yana karantar wasu halayya da d’abi’u nata dikda hirar tasu ma iya cewa Raheema ce keyin akasari
***
Isowarsu Fadar kenan suka tadda wata mata sai gudu take wasu mutane na biye da ita, gashin matar yayi duguzun alamun hauka, yanayin yanda take gudu kad’ai zai tabbatar maka babu hankali jikin matar.....
Dikda bata iya ganin fuskar matar gaba d’aya ba, tsikar jikinta sosai ya tashi da ganin wannan mahaukaciyar matar, suna a haka wani Bafaje ya k’araso dan yi masu iso zuwa cikin Fada....
SameenaAleeyou📚
[5/21, 10:47 PM] +234 703 453 9908: *👑✨MUHIBBA✨👑*
*004*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Muhibba bata ida firgita da lamarin matar nan ba saida matar ta k’araso ta tsaya cak gabanta tana binta da wani irin duba da idanunta masu matuk’ar firgitarwa, suffar matar kad’ai abin firgitarwa ne.... Tamkar irin bayin da aka ciwosu a zamanin farko...Gashi bata furta koda kalma ba sai duba irinta k’urilla da take binta dashi...
K’irjin Muhibba yaci gaba da bugu a daidai lokacinda wasu dogarai k’arfafa har guda uku suka k’araso a guje suka capke matar nan daketa zillewa tana waigowa tana kuma duban Muhibbah.... Itama Muhibbar duban matar take har suka b’acewa ganinta
Ansar ne ya d’an sunkuyo kad’an kana yace “Are you okay...?”
Ta jinjina masa kai a hankali a daidai sanda aka bud’e masu wani tapkeken gate mai d’aukeda kuyangi sahu sahu, dik yanda suka Zo wucewa sai kuyangi Sun risina Sun gaidasu.... Tafiya mai d’an tsawo sukai kafin suka soma hango asalin cikin Masarautar....
Dogarin da yai masu rakiya ya sadda kansa cikeda risinawa kana yace a nan zai barsu akwai wad’anda zasu Zo su k’arasa dasu ciki....
Ansar ya jinjina masa kai murmushi saman fuskarsa had’ida masa godiya...
Maidoda dubansaga Muhibba yai wacce har yanzu tamkar bata a cikin hayyacinta kana ya d’anyi gyaran murya yace “Hibbah, are you sure about this...? Hibbah kodai mu koma gida... I don’t know... But I’ve a bad feeling about this....!” Ya k’arashe cikeda kulawa...
K’ak’aro murmushi tai kana tace “There’s no going back, I’ve already started... Dole na k’arasashi...” Ta d’anyi still kana taci gaba da fad’in “Ganin matar nan ya firgitani... Sam batai kamanni da bil’adama ba...”
D’an dubanta kad’an Ansar yai kana yace “Da gani bamai hankali bace, mahaukaciya ce... Kiga yanda tazo ta tasamu a gaba da kallo tamkar mai san yi mana magana, musamman ke.... “
Muhibbah ta jinjina kai a hankali “Allah kad’ai yasan silan haukar matar nan...” Tai maganar a hankali...
Sauk’e ajiyan zuciya Ansar ya d’anyi kana yace “Muhibbah Fada gida ne mai k’unshe da halittu iri daban daban, wanda ido ka iya gani dama wanda idanuwanmu bazasu iya gani ba, Muhibbah Fada babban gida ne wanda komai ka iya faruwa cikinta, dik yanda aka ce miki akwai mulki da sarauta Toh zai matuk’ar wahala ace babu zalunci sai wad’anda Allah ya kiyayesu.... Akan neman mulki da sarauta ta duniya wasu mutanen babu abinda bazasu iya ba... Shisa sam banso Ki dage da k’udirin nan naki ba... Dan dai kawai babu yanda na iya ne....!”
Fuzar da fuci tai a hankali kana tace “Ansar mecece makomar rayuwata... Shin da wata fuska kake duban rayuwata a halin yanzu...?”
Matsowa kusanta kad’an yai kana yai mata K’uri na wasu dak’ik’ai....
“Gwarzuwar mace, Jaruma a filin daga, Mace k’wara d’aya tak data tari gungun mayak’a Majiya k’arfi masu d’aukeda manyan makamai.... TAKWABI d’aya tak da zatai zarra Ta kwantar da dubban takwabban da suka zagayeta sukai mata kawayanta...SARAUNIYA k’wara d’aya tak a illahirin Masarautar nan....!” Ido cikin ido yake dubanta sanda yake furta mata kalaman....
Tabbas sai taji tsoron da ya lullub’eta ya yaye, ji tai ya bata wani irin k’arfin gwiwa wanda ko a baya bata sami hakan ba, tabbas sanda Ta saka k’afarta cikin Masarautar nan abubuwan da suka faru shekarun baya sun shiga dawo mata daki daki, sannan tsoro da firgici sun mamaye zuciyarta, koda yanzu Ansar yai mata wad’annan kalamai saiji tai zuciyarta Ta kuma samun k’warin gwiwa....
A hankali ta jinjina masa kai kana tace “Na gode daka d’aukeni matsayin Jaruma, kuma in sha Allah bazan baka kunya ba... Zakai alfahari dani a lokacinda na kawar da mulkin Zalunci da wad’ann azzaluman bayi na Allah suka gina a doron k’asa.... Labarin Masarautar da kalan zalunci da sukai bazai shafe a tarihi ba... Zan zamto sanadin bank’ado wasu bak’ak’en sirrikansu da suka jima da bisnewa... Labarinsu zai zamto izna ga wata Al’umma da zatazo a gaba....!!” Ta k’arashe tana goge hawayen zafin Rai da ya gangaro mata....
Ansar ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali, dan ko babu komai yanzu hankalinsa ya d’an kwanta, ya cirewa Muhibbah dik wani sauran burbud’in tsoro dake kwance cikin zuciyarta, yak’i ta tara wanda shi kansa bai isa yace ga yanda zata kaya ba, dan haka dole ya k’arfafa mata gwiwa domin kaw Muhibbah tana tsananin buk’atar hakan daga garesa....
“Yanzu ne naga asalin Muhibbar da na sani, wacce bata failing dik abinda Ta saka gabanta da izinin Allah... Always remember we are in this together, dik sanda kikaji wani abu ya canza, don’t forget I’ll always be here... Muhibbah ina sonki... With all my heart, bayan labarin gaba d’aya da naji yau, kin kuma zama tauraruwa d’aya tak a birnin zuciyata... I’ll wait for you till the end of this...!” Ya k’arashe cikin tsananin sanyin murya wanda ya sanya wani b’angare na zuciyar Muhibbah tsananin tausayin Ansar d’in... Ansar da mahaifiyarsa sune komai na rayuwarta... Mutanen da suka bud’e mata k’ofofin Alkhairai a lokacinda Duniya tai mata d’aurin goro... Mutanen da suka zamto shimfid’a mai taushi a gareta a lokacinda dik yanda ta saka hak’ark’arinta kaya ne mai tsananin suka... Shin ta yaya zata mance halarcin wad’ann bayin Allah a gareta... Da izinin Allah bazata tab’a watsa masu k’asa a idanu ba... Zasu sameta mai rik’oda Alk’awari.... Suna nan a haka muryar wasu kuyangi ‘yanmata guda biyu ya katse masu nisar da sukai a duniyar tunani su duka biyun....
Cikin ladabi irinta babban gida Kuyangin suka gaidasu kana guda d’aya Ta d’auki luggage d’in Muhibbah dake gefen k’afar Ansar yayinda guda d’aya tai masu jagoranci zuwa sashen Gimbiya Turai Giwar Sarki kuma uwar Taurari Hud’u dake a wannan masarauta....
***
Daga yanda yake tsaye saman bene hannayensa hard’e yana kuma nazarin mahaukaciyar matar da ya hango dogarai na kokawan kamata, shin wacece ita...? Tambayar da yai masa karan tsaye a zuciyarsa.... Yana nan a haka Ubandoma ya shigo cikeda risinawa had’ida fad’uwa k’asa yana kwasan gaisuwa....
Yarima Mahmood ya jinjina masa kai ba tareda ya amsa gaisuwar tasa ba, lokaci guda ya soma takowa gaban Ubandoma had’ida yin gyaran murya kad’an
“Ubandoma...!” Yarima Mahmood ya ambato sunansa cikin muryarsa mai cikeda k’warjini....
Ubandoma ya amsa a lada ce yana mai furta “Allah shi taimakeka...”
Yarima Mahmood yaci gaba da fad’in “Wacece mahaukaciyar cen da d’azu naga dogarai suna kokawan kamata....?”
Tambayar da ya haifarwa Ubandoma fad’uwar gaba....
Gumi ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 65