Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kana tace “Mai kike tinanin yana b’oye miki...?” Zahra ta d’an dubeta kaman zatai magana sai kuma ta mik’e tsaye tana mai fuzar da huci a hankali, lokaci guda take furta “I don’t know, but jikina na bani its something that has to do with my Maama’s mysterious death... What if Paa yasan wani abu gameda mutuwar mahaifiyata... Mutuwan da gawanta kawai aka tsinta cikin d’aki..” Mik’ewa tsaye Muhibbah ma tai had’ida dafa Zahra kad’an kana tace “But do you think your Paa can do something as evil as that...?” Saurin d’agowa Zahra tai tana dubanta kana Ta shiga girgiza kai, lokaci guda take furta “No, no I don’t want to believe that... Paa bazai tab’a kashe mutum ba and much less my Maama, ya sota da dika zuciyarshi... But what I don’t understand here shine Maiyasa bazai sanar dani ba idan yasan wani abu ne gameda mutuwar nata, who is he protecting...?!” Ta k’arashe damuwa kwance saman fuskarta... Muhibbah dake ci gaba da karantar yarinyar matsowa kusanta Ta kumayi kana tace “Then talk to your Father... Ask him... Ki tambayeshi meye yake b’oye miki...!” Zahra ta d’an dubeta kana tace “But how... Paa kallon yarinya yake min har yanzu, I’m quite certain bazai Fad’a min komai ba...” Janyo hannunta Muhibbah tai suka zauna saman kujera kana tace “In that case, maybe baiso Ki damu ne... Tinda kince har yanzu kallon yarinya yake miki wacce bakisan komai ba... But if I were you, zan bud’e idon mahaifina ya gane cewa ni fa yanzu ba yarinya bace... I can differentiate what’s right from wrong... You’re already a young lady now... So bai kamata Ki bari yaita treating d’inki kaman wata k’aramar yarinya ba musamman in some cases like this... We’re talking about your Mother here Zahra... Idan har da gaske kasheta akai cikin Masarautar nan and your Paa knows something about it, but baidata cewa coz he’s protecting someone kaman yanda kika ce... Ni a ganina Ke bai kamata kiyi shiru ba.... Mahaifiyarki Ta cancanci adalci koda kuwa nan d’in gidan sarauta ne da basu d’auki doka kan masu mulki a bakin komai ba..!” Yanda take maganan zaka fahimci tamkar tana fitar da wani abu ne da ya jima yana cin zuciyarta... Zahra tai shiru tamkar mai tinani yayinda Muhibbah taci gaba da karantarta.... Lokaci guda Zahra ta shiga jinjina kai tana mai furta “You’re right... I need to find out about everything..!” Jinjina kai Muhibbah tai cikeda jin dad’in yanda cikin sauk’i tai convincing yarinyar... Lokaci guda take ayyana yanda zata tarwatsa rayuwar Mahmood Ta hanyar amfani da gudan jinin da yafiso a rayuwarsa... Tabbas D’iyarsa itace weakness d’insa.... A haka Umaima ta shigo ta taddasu... ** A b’angaren Mahmood yana ficewa ya tadda Ubandoma yanda yake samar dashi zuwan Waziri... Jinjina kai Mahmood yai cikeda sarauta kana yaceda Ubandoma a shigar da Waziri d’akin ganawa na bak’i.... Ubandoma ya kuma aza babban riga yana d’agowa Yarima Mahmood hannu alamun jinjina, lokaci guda yake furta “An gama Rankashi dad’e... Allah shi baka gidanku... Waziri godiya yake...!” Lokaci guda Ubandoma ya kuma aza babban riga kana ya shige cikin sauri... Daidai nan Yazeed ya k’araso wajen shu’umin murmushin nan saman fuskarsa, hannunsa na dama rik’eda hannun d’ansa Sultan...”Taking a break your Highness...?” Ya fad’i murmushin bai bar saman fuskarsa ba... Murmusawa kad’an Mahmood yai kana ya shafi kan Sultan yace “Hello your Royal Highness..!” Yaron ya d’ago fuskarsa yana murmushi yake duban iyayen nasa kana ya dubi Mahmood yace “Do you also think one day I’ll become a King Uncle...?” Duban Yazeed dake ci gaba da sakin shu’umin murmushinsa Mahmood yai kana ya maido da dubansaga Sultan ya shafa gashinsa kad’an kana yace “Of course Champ, one day zaka zama Sarki mai mulkin Masarautar nan... But when that time comes inaso kasa a ranka cewa shi shugaba Bawan Al’ummansa ne mai masu hidima da tausayinsu kaji koh...!” Saurin katse tattaunawar Yazeed yai da fad’in “Sultan jeka Hauni ya d’auraka saman doki, I’ll catch up with you in a bit....!” Yaron ya jinjina kai cikeda jin dad’i kana ya wuce... Duban Mahmood Yazeed yai kana yace “Yaya I’m sorry, but you’ve no right to discipline my son... Idan akwai wanda yafi dacewa ya baiwa d’ah na horo that person should be me,just me and no one else...! Sabida Kai bakada Magaji shine bari ka cire masa son mulki da izza... Sultan jinin sarauta ne dan haka dole ya zamto namijin gaske maiji da mulki da izza...!” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “You’re right... He’s your Son, after all...” Yazeed ya kuma jinjina kai cikeda jin dad’i kana yace “K’warai kuwa d’ah na ne kuma Magajin Masarautar nan..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya shige shu’umin murmushinsa saman fuskarsa... Yarima Mahmood ya bisa da kallo har ya b’acewa ganinsa kana yasa kai yai shigewarsa... Yana shigowa parlorn ganawa da bak’in Waziri da Ubandoma suka risina suna kwasan gaisuwa... Mahmood ya k’arasa ya zauna a mazauninsa kana Ubandoma yai ficewarsa ya basu waje... Mahmood ya dubi Waziri kana yace “Naji dad’i daka amsa kirata ta gaggawa Waziri...” Waziri ya kuma risinawa kana yace “Allah shi baka yawan rai Farin cikin nawa ne, da sarki mai jiran gado zai nemeni... Ka fad’i dik abinda kake so Waziri yai maka shi a Masarautar nan Rankashi dad’e..!” Shiru ne ya d’an ratsa tsakani kana Mahmood ya d’anyi gyaran murya yace “Waziri..!” “Allah shi baka yawan rai...!” Waziri ya amsada haka... Mahmood yaci gaba da fad’in “Mai zakace gameda b’acewan Ja’afar a Masarautar nan...?!” Tambayar da ya sanya Waziri saurin d’agowa yana duban Mahmood saidai gizo da k’warjini had’ida cika idanun da Yarima Mahmood kedashi ya sanyashi saurin sadda kansa... Lokaci guda yake furta “Allah shi taimakeka Jafaru dai rana d’aya aka nemeshi aka rasa cikin Masarautar nan...!” Shiru ya kuma ratsa tsakani kana Mahmood yace “Yaushe ne aka fahimci cewa Jafar baya Masarautar nan...?” Waziri da gaba d’aya tamkar a birkice yake ‘yan kame kame ya soma da fad’in “Eh toh... Allah shi taimakeka Yau kusan shekara guda kenan idan ban b’ata lissafi ba...!” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Kenan hakan yana nufin, da mutuwar mahaifina, da mutuwar matata da b’acewan Jafar sun faru ne a jere, d’aya na bin d’aya right Waziri...?!” Shiru Waziri yai kaman mai tunani kana yace “Eh Toh hakan ne yake a bayyana Allah shi jada ranka...!” Shiru ya biyo baya kana Mahmood yace “Yanzu kai a naka shawarin Waziri ta ina za’a fara nemo Jafar sabida ina buk’atarsa a Masarautar nan...!” Waziri ya d’an d’ago yana duban Mahmood kana yace “Eh Toh Allah shi taimakeka ban isa ince ga nan ta yanda za’a soma neman yaron nan ba don kar a sami mishkila ko akasi....” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Haka ne Waziri... Toh amma ni inada aiki da zan baka....!” Waziri ya kuma gyara zamansa kana yace “Mecece wannan aiki Rankashi dad’e....?” Mik’ewa tsaye wannan karon Mahmood yai hanayensa hard’e ta baya, yana d’an takawa kad’an irin yanda masu mulki keyi kana yace “Inaso ka wakilta masu bincike... A bincika duk k’asashen da muke gab’a dasu dan na tabbata bawa kaman Jafar bazai nisan da zai tsallake wad’annan k’asashenba...” Sauk’e ajiyan zuciya a hankali Waziri yai kana yace “An gama Allah shi baka yawan rai... Za’a baza dakaru domin a zak’ulo Jafar yanda ya shiga ya fita...!” Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “Da kyau Waziri... Kana iya tafiya...!” Waziri ya kuma mik’a godiyarsa kana ya kwashi babban rigarsa a hannu ya fice.... Yana ficewa sukaima juna wane irin duba shida Ubandoma tamkar wasu mak’iya... Waziri yaci gaba da sab’a babban rigarsa takalma a hannu ya fito daga b’angaren Maimartaba yanda nan cikin b’angaren sashen Mahmood yake.... Waziri yana fitowa wata Kuyanga dake daga b’angaren Gimbiya Zeenat Ta k’araso tai masa gaisuwa kana ta mik’a masa takardan dake hannunta... Yasa hannu ya amsa yana karantawa.... Babu b’ata lokaci yaceda Kuyangar Ki sanar da ahugabanki Waziri Yana nan tafe.... Kuyangar ta jinjina kai kana tai shigewarta... A cen wane b’angare mai duhuwa suka had’u shida Giwa Jakadiya na take mata baya....Duba guda yai mata ya d’auke kansa sai faman sakin huci yake... Giwa taci gaba da takowa cikeda k’asaita.... “Yaya kukayi da d’ah na Mahmood Waziri...?!” Ta tambaya cikeda izza... Saida ya kuma fuzar da fuci kana yace “D’anki ji yake shi d’in kaman wani sarki ne...Doka da Umarni yake bani tin yanzu Ina a matsayin Wazirin mahaifinsa....!” Giwa ta murmusa cikeda k’asaita kana tace “Na d’an lokaci ne Waziri.....!” Dubanta Waziri yai a kaikaice kana yace “Kin tabbata na d’an lokaci ne.... Shin kinada masaniyan cewa Yarima Mahmood ya soma tono diddigin abubuwa... Mai zai faru sanda ya isa k’arshen k’urya...?!” Murmushi Giwa tai kana tace “Mai ya tambayeka...?” Waziri ya gyara tsayuwarsa yana mai furta “Matarsa, mahaifinsa da kuma Jafaru...!!” Nan ma murmushi Giwa Ta kumayi kana tace “Toh mai zai dameka Waziri bacin bamuda alhakin mutuwar matarsa dana mahaifinsa a wuyanmu.... Kaima kasan wakeda alhakin Mutuwar Maimartaba da Aliya...!” Ta k’arashe wani murmushin saman fuskarta... Waziri yai mata K’uri kana yace “Kin tabbata Jafar baya raye....?” Cikeda isa Giwa Ke kuma murmusawa kana tace “Jafar ya zama tarihi tinda jimawa...!” Waziri ya jinjina kai kana yace “Allah yasa gaskiya kike fad’i, domin kuwa Jafar shi kad’aine yasan hanya da kuma launin mabud’in kurkun dake k’ark’ashin Masarautar nan, wanda tonoshi na nufin k’arahenmu ne... Dan nayi imani Yarima Mahmood sawa zai a fille kawunanmu koda kuwa Ke d’in mahaifiyarsa ce...!!” Giwa Ta kuma murmusawa kana tace “Anyima kurkukun rufinda har abada bazai kuma bud’ewa ba....!” Waziri ya murmusa kad’an kana yace “Kar kiyi gaggawa Turai domin kaw mabud’an wannan kurkuku mijinki ya mallakama wani wanda har yau bamu San ma waye ya mallaka ba...” A harzuk’e Giwa ta d’ago tana dubansa kana tace “Inada tabbacin ma Jafar ya mallaka shiyasa na b’atar da Jafar.... Na kuma rufe bakin Jafar rufuwa ta har abada....!!!” Waziri ya kuma jinjina kai kana yace “Allah yasa bakiyi kuskure ba wannan karon... Zan wuce na duba Gimbiya Zeenatu...!!” Giwa Ta murmusa kana tace “Zeenatu Karen farautarmu... Kaje kaji da mai tazo wannan karon...!” Waziri ya d’an murmusa kad’an kana yace “Tana nan tana haukarta akan mulkin Mahmood.... Da ace tasan tarkon da kika d’ana mata na tabbata da tayi yanda tayi ta fitar da kanta da kuma ‘yar uwarta daga wannan masarauta...!!!” Ya k’arashe mummunan murmushi saman fuskarsa... Giwa Ta murmusa cikeda k’asaita kana tace “Gimbiya Turai bata yima kowa alkhairi face tanada nufinta akansa....Zeenatu da ‘yaruwarta tabbas sun fad’a Tarko na... Tabbas Alhakin mutuwar Mahmood zai rataya ne a wuyansu... Zasu fice daga cikin Masarautar nan suna k’ask’antattu... Kaga na kashe tsuntsu biyu ko nace uku da Dutse d’aya tak..!!” Ta k’arashe mummunan murmushi saman fuskarta... Waziri ya murmusa kad’an kana yace “Mahmood mai Uwa... Tabbas kin cika Uwa Ta gari...!!” Giwa Ta kuma murmusawa kana tace “Na masa d’aurinda sam babu mai warwaresa...!!” Ta k’arashe dikda cewa cen k’asan zuciyarta kalaman Tal’udu ne Ke mata Yawo cewa wannan gudan jinin bai shiga cikin tandun tsafi ba kuma dik a ta dalilin wannan tsinanniyar yarinyar Saudatu.... Take tinanin Mahaukaciya Izzatu ya fad’o mata, lokaci guda Ta dubi Jakadiya dake cen gefe kana tace “Jakadiya...!” Jakadiya ta k’araso cikin sauri had’ida zubewa k’asa tana mik’awa Giwa jinjina... Giwa taci gaba da fad’in “Yau da dare zamu kaiwa Izzatu ziyara...!” Jakadiya ta jinjina kai cikeda girmamawa tana mai amsawa shigaban nata... Waziri da Giwa sukaima juna wane irin duba kana Waziri yace “Na k’agu naga Yazeedu kan Karagar nan...!” Murmusawa Giwa ta kumayi kana tace “Na d’an lokaci ne kad’an... Masarautar zata zama mallakinmu gaba d’aya...!” Suka kuma murmusawa a tare kana Waziri yai masu sallama yayi shigewarsa.... *** Misalin k’arfe tara da rabi na dare ta shigo b’angaren nata, ta soma gudanar da shirye shiryenta na bacci, bayan tayi wanka da alwala ta tada sallah tai shafa’i da wutiri kaman yanda yake a al’adarta... Tana zaune saman abin sallah tana tinanin yanda al’amara Ta kaya yau tsakaninta da Fu’ad ga kuma fargaban abinda ka iya zuwa yazo tsakaninta da Yazeed, sannan ga rashin yarda da juna da take so Ta k’ulla tsakanin Mahmood da d’iyarsa, kaman daga sama taji ana knocking a k’ofar parlor... Bata kawo komai ba dan a zatonta Umaima ce ko wata Kuyanga ce ‘yar aike... Dan haka ba tareda wani damuwa ba ta isa ta bud’e k’ofar.... Saidai mutumin data gani ne tsaye k’ik’am a bakin k’ofar yai mugun bata shock..... Sameena📚 [6/22, 1:05 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *022* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Kallon kallo suke ma juna su duka biyun, idanun Yazeed ko k’yaftasu baiyi dikda cewa Allah yasa bata cire Hijab d’in data ida sallah dashi jikinta ba.... Take ta tuna kalaman da ya fad’i mata d’azu da safe, kardai yazo ya tona asirinta ne... Ga wani irin mayen kallon da yake binta dashi... Ganin idan tai wasa zata iya b’ata komai dan gaba d’aya ji take kaman wuta ne Ke cin illahin jikinta da wannan irin duban da Yazeed Ke mata, d’aya daga cikin mutane biyar d’in da tafi tsana a duniyar ta... Lokaci guda tai K’ok’arin tattaro nutsuwarta kana ta d’an saki murmushi “Your Highness... What brings you here...?!” Ta fad’i murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskarta... Har lokacin bai furta komai ba sai k’are mata kallo da yake ci gaba da yi.... Lokaci guda kuma yasa kai ya shigo cikin parlorn k’irjinta sai bugawa yakeyi da sauri da sauri ganin Yazeed ya kutso Kai cikin parlorn kai tsaye... Tai saurin jada baya don tabbas idan bata matsa ba zai bangaji jikinta ne... Ta had’iyi abinda ya tsaya mata da k’yar a mak’oshi kana ta d’ago tana dubansa.... Ko gizau babu a tattredashi.... Baibi takanta ba saima k’arasawa da yai ya zauna saman kujera irin zaman da masu mulki suka fayeyi... Muhibbah tai saurin kauda fuskarta gefe tsan tsan tsanar wannan halitta naci gaba da wanzuwa cikin zuciyarta.... Har wannan lokaci Yazeed bai furta koda kalma ba saima ci gaba da murza zobban hannunsa da yake yi... Gaba d’aya sai ta d’an daburce don yanzu kam abin Yazeed tsoro ya soma bata amma dole tai jarumtar kauda tsoron kodan tsira da mutuncinta domin kaw sam bazata bari Yazeed ya kamata ba, bari Ta b’ullo masa a k’wararriya.... Ta sauk’e fuci a hankali kana ta saki murmushi mai kyau wannan karon... Jikin k’aramar fridge ta isa ta d’auko masa bottle water harda glass cup Ta kawo Ta ijiye gabansa, kujerar dake cen gefe ta k’arasa ta zauna, k’afafu d’aya bisa d’aya... Lokaci guda take furta “To what do I owe the honor your Highness...!” Tai maganar tana mai rausayar da idanu had’ida girgiza k’afafunta dake d’aya bisa d’aya.... Murmushi ya sakar mata wannan karon yana mai dubanta, kaman bazaice komai ba sai kuma ta sinkayo muryarsa yana fad’in “I can see you’re well trained... Tabbas kin K’ware a fanninki...!” Ta kuma dubansa ba tareda ta fahimci Ina ya dosa ba.....Saida ya lank’wasa k’afarsa guda wannan karon kana yace “Tell me, a ina kika tsaya..? Mai da mai kikai discovering zuwa yanzu..?!” Gabanta yai wane irin fad’uwa... Ta d’ago dara daran idanunta da suka k’ara girma lokaci guda tana dubansa... Shikenan Yazeed ya gane ko ita wacece... Su duka biyun suna duban juna, k’irjinta sai fat fat yake... Kai no bazata bari ya kamata ba, she will play his game.... Lokaci guda kuma ta saki murmushi kana tace “Excuse me your Highness, but I don’t get you... What exactly do you mean...?!” Shu’umin murmushinsa ya saki kana yace “Kin fini sanin mai nake nufi...Aren’t you a spy....!?” Wane irin ajiyan zuciya ta sauk’e jin bai fahimci cewa itace Saudatu ba... Lokaci guda ta kuma sakin murmushi kana tace “A spy...? Where’s that coming from your Highness...?!” Mik’ewa tsaye yai had’ida maida hannayensa baya, lokaci guda itama Ta mik’e tsaye.... Saida Yazeed ya kuma daidaita tsayuwarsa kana ya soma fad’in “Daga Masarautar su matata kike... Sun turoki domin ki bincika irin zaman da Zuhra keyi a Masarautar nan....Am I right...!” Harga Allah dariya yaso bata jin yanda gaba d’aya tinaninsa ya karkata.... Murmushi mai bayyana hak’wara wannan karon tai tana mai d’an rufe bakinta da yastun hannunta, dariyar take d’anyi har wannan lokacin.... Yazeed yai tsaye yana dubanta, lokaci guda take d’an k’ok’arin saita kanta kana tace “Oh I’m sorry your Highness, but you’ve that got that wrong....Do I look like a detective to you Rankashi dad’e...? I’m here to study... Karatu nake a nan, you can have me investigated if you wish.... But wait..!” Ta k’arashe tana mai dubansa sosai wannan karon... Shid’inma ita yake duba musamman labb’anta da k’wayan idanunta... Lokaci guda Muhibbah taci gaba da fad’in “Mai yasa zakai tinanin ni ‘yar bincikece... Akwai wani abu ne da bakaso Masarautar su matarka su sani gameda kai..?!” Ta k’arashe tana mai rage girman idanunta.... K’uri yai mata kaman mai tinani, kana ya saki murmushi da gefen bakinsa had’ida daidaita tsayuwarsa “You expect me to believe that...? Well I don’t buy that... I’m not the kind of prince that can be easily fooled... But be grateful you’re beautiful... Idan kinaso ki fanshi kanki, kinada abinda zaki iya fansar kanki dashi ba tareda kin fuskanci horo da k’ask’anci daga Masarautar nan ba...!” Ya k’arashe yana mai k’arasowa dab kusanta had’ida mata kallon k’urilla.... Dikda bugu da k’irjinta keyi hakan bai hanata k’ok’arin tattaro natsuwarta ba... Tai k’ok’arin janye jikinta ta matsa daga kusansa lokaci guda take furta “I’ve got nothing to be afraid of your Highness... Like I told you, idan kana so zaka iya yin bincike akaina and clear all your doubts...!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta.... Miyau ya had’iya da k’yar kana ya d’anyi gyaran murya yace “If you’re really telling the truth, idan har gaskiya kike fad’i, baki tinanin ya kamata Ki samawa kanki Yarima a Masarautar nan wanda zai zamto garkuwa a gareki kafin ki gama karatunki ki tafi...?!” Ya k’arashe shu’umin murmushin saman fuskarsa... Kauda fuskarta tai had’ida fuzar da fuci a hankali dan sarai Ta fahimci ina zancen nasa ya dosa kana ta kuma maidoda dubanta garesa ta saki murmushi a fili dikda cikin zuciyarta kuwa tsananin k’una ne, lokaci guda take furta “I’m sorry your Highness, but I really don’t need a Prince, coz I already have a King..!!” Ta k’arashe murmushin saman fuskarta... Tamkar an buga masa babban Dutse akai haka yaji, lallai wannan yarinyar babban ‘yar rainin hankali ce, yau shi mace Ke turning d’insa down... Shi Yazeed.... Kai no, babu macen data isa tai turning Prince Yazeed down, babu ita dik fad’in duniyar nan... Murmushin k’arfin hali Yazeed ya saki kana yace “Then name your price...!” Yai maganan yana mai kuma matsowa kusanta... Dikda k’una da zuciyarta ke tsananin yi hakan bai hanata sakin murmushin takaici ba kana ta k’arasa da sauri ta bud’e masa k’ofa... Lokaci guda take furta “You’ve got a reputation to protect Rankashi dad’e...? And na tabbata baka fatan abinda zai shafawa sarautarka bak’in fenti....Zaifi kyau idan ka fice daga nan... And never think of coming back...!!” Da tsananin mamaki Yazeed ke dubanta, da gaske ne abinda yakeji... Shine mace Ke fad’a masa haka yau d’in... Shi Yarima Yazeed...!!! Kasa motsa koda d’an yatsar k’afansa dake sanye cikin takalaminsa yai, sai duban mamaki da yake binta dashi... Muhibbah da tuni taji hawaye na neman ciko idanunta lokaci guda Ta d’an kauda kanta gefe har lokacin tana nan rik’eda k’ofa tana jira Yazeed ya fice... Tai k’ok’arin maida hawayenta dikda sakin huci da take ci gaba da yi a hankali... Cikeda k’asaita ya soma takowa bai daina bintada kallon mamaki ba, saida ya k’araso daidai k’ofan kana ya kuma karkatowa yana dubanta kaman zai magana sai kuma yasa kai ya nufi k’ofa yana sakin huci... Muhibbah ta bud’e murya tace “One more thing your Highness.... Remember this, not all women have a price... Some can’t just be bought... Have a good evening, Rankashi dad’e..!!” Daga haka Ta maida k’ofa ta rufe ta bar Yazeed nan tsaye tamkar an dasa sa.... Idanunsa jajir yake duban k’ofar parlorn, jijiyoyin jikinsa sukai rud’u rud’u... Idanunsa sukai jazir... Yau shine mace Ta yarfa... A Masarautar Sa....in his very own kingdom.... Shi Yazeed AbdulJabbar..!!! Yaci gaba da sakin wani irin huci maganganun suna masa Yawo a kunnuwansa... Cikin sassarfa yasa kai ya fice a wajen kaman zai kife k’asa... Muhibbah kaw tana maida k’ofar ta lumshe idanunta hawayen da taita k’ok’arin hanasu fitowa suka shiga gangaro mata d’aya na bin d’aya... Lokaci guda ta durk’usa a wajen tana mai sakin kuka mai tsuma zuciya.... *** Yazeed gaba d’aya ficewa yai a Masarautar.... Cen club d’in da suka saba had’ewa da abokansa ya tafi..... Kaman ko yaushe, kansa a sama ya nufi spot d’in da yake nasu ne su kad’ai babu mai zuwa wajen saidai idan su suka buk’ata.... Ta wani k’ofa da babu mai noticing d’insu suke shiga, yanda aka ware masu domin zamansu, a wajen kuwa K’atoton TV ne suna ganin dik abindake wakana cikin club d’in, idan sunga budurwar da tai masu saidai suce a shigo masu da ita su d’auketa su fita... Sam bazaka San suna zuwa club d’in ba.... Zayyad amininsa ya tadda a wajen, yana ganinsa ya mik’e yana zolayarsa had’ida masa gaisuwa irinta masu sarauta.... Ko takansa Yazeed baibi ba ya zauna cikin kujerar yana mai ci gaba da sauk’e fuci a hankali.... Zamansa Keda wuya ma’aikacin club d’in ya k’araso dan taking order d’insa.... As usual Zayyad ne yace da waiter d’in a had’owa Rankashi dad’e double whisky... Shidai Yazeed bai furta koda kalma ba har wannan lokacin k’afarsa d’aya bisa d’aya yana sauk’e huci lokaci guda kalaman Muhibbah naci gaba da buga kwanyarsa... Zayyad ya matso kusansa kad’an kana yace “Your Highness Wai meke faruwa ne...? I thought bazamu sake ganinka a club d’in nan ba tun bayan mutuwar mahaifinka.... I thought kace ka daina b’ata lokaci a nan tinda Kai d’in Sarki ne mai jiran gado..!!” Shak’o wuyarsa Yazeed yai yana mai ci gaba da sakin huci yake furta “Haven’t I informed you yet, that my despicable brother is back in the country..? yana k’ok’arin k’wace abinda na jima ina hari....!!!” Zayyad da yasha damk’a da k’yar yake k’ok’arin k’watan wuyarsa yana furta “Easy your Highness... Let me go please, bani na kar zomonba....!!” Yazeed yai jifa dashi yana mai ci gaba da sauk’e huci, lokaci guda haushin abinda Muhibbah tai masa had’ida tsanar d’an uwansa Mahmood naci gaba da fuzgarsa a zuciya.... He really needs to teach that girl a great lesson... Shine Prince Yazeed wanda yafi k’arfin wulak’ancin ko wacce irin mace....!! Ganin yanayin da yake ciki yasa Zayyad kiran sauran abokan nasu guda biyu a waya.... Sosai ya razana da yanayin da yaga Yazeed ciki... Gefensa ya komo ya zauna yana mai ci gaba da sosa wuyansa yanda Yazeed ya shak’esa “Zeed.... Wai meke faruwa ne, ni ban yarda kan brother d’inka kawai kayi haka ba.... Tell me akwai wani abu ne bayan wannan....?!” Yazeed dake ci gaba da sakin huci yana murza zobban hannunsa a hankali lokaci guda yakai dubansaga Zayyad kana yace “You wanna know the whole thing..? Then fine.... Tonight, I’ve just received the insult of my life.... My evening is completely ruined, all thanks to her...!!!” Da tsananin mamaki Zayyad ke dubansa kana ya furta “Unbelievable! Yau kaine kake maganan mace taci mutuncinka your Highness...? Wow.. Just wow.... this is unbelievable..!!!” Daidai sanda ma’aikacin club d’in ya kawowa Yazeed barasan sa... Ba tareda b’ata lokaci ba ya shiga kwankwad’a kaman mai shan ruwa... Wa’iyyazubillah... D’an dafasa Zayyad yai yana duban TV d’in yanda ashararrun mata Ke rawa suna bayyana jikinsu kana ya murmusa yace “I think you needs someone to take out a little bit of stress you’ve been going through your Highness..!” Ya k’arashe yana duban ‘yanmatan murmushi saman fuskarsa... Lokaci guda yana kuma fasa kan Yazeed da cewa ba’ayi macen data ci mutuncinsa ba ta nuna masa kasawansa *** A b’angaren Muhibbah kaw tun bayan ficewar Yazeed bacci ya k’aurace a idanunta, sai faman juyi take a gado ba tareda bacci ya d’auketa ba... Ta mik’e ta zauna had’ida kunna side lamp, Ta janyo wayar salulanta tana duba time... K’arfe shad’aya da kusan rabi na dare... Jan labule ta d’anyi tana lek’a waje sararin samaniya... Taji natsuwa na zuwa zuciyarta a hankali... Lokaci guda taji tana son fita waje tasha fresh air... Mik’ewa tai ta zira doguwar riga kana ta d’aura mayafi akanta ta nufo waje.... Tana tafe taga kaman giftawan mutum sanye cikin bak’in tufafi... Exactly irin wancan mutumin data gani kwanaki biyu da suka shige... Mutum sanye da bak’ak’en tufafi ba’a ganin komai nasa.... Ta jima tana duban hanyar da taga giftawar nasa... Take taji k’afafunta sun soma

Chapter 13 of 65