gama ya Shugabata...! Allah ya huce zuciyar Giwar Amale...!!”
Daga nan mik’ewa tai cikin sauri tabi ta hanyar da suka shigo....
Giwa da Jamal suka jera suma suka fito su duka biyun, kowa da abunda yake sak’awa cikin zuciyarsa....
Suna isowa sashen Giwa Jamal ya dubeta yace “Maami idan an kamo Ubandoma I’ll be the one to punish him... Zai d’and’ani kud’arsa...!”
Giwa ta fuzar da fuci tana dunk’ule hannu take zaga cikin d’aki lokaci guda tace “Ni kaina bansan irin horon da zan masa..!”
Jamal ya murmusa yace “Ki barni dashi, ni ne Gwarzonki Maami kuma na tanadi muggan horo da zanyima wannan k’ask’antaccen Bawan....!!”
Giwa ta jinjina kai tace “Nasan bazaka bani kunya ba Gwarzona... Zan baka Ubandoma kayi duk abinda kaso dashi, idan kaga dama kada ka ragar masa ruhi...!!”
Jamal yai wata murmushi da gefen bakinsa yana mai ayyanawa cikin zuciyarsa cewa muddin ya damk’o Ubandoma zaiji jiki, zai masa horo fiyeda wanda yayima Ja’afar, tabbas ba’a shiga gonarsa a wanye lafiya... Dik manyan syringe na zira ma dabbobi da yaita huda jikin Jafar dashi mai sauk’i ne akan irin horon da ya tanadarwa Ubandoma muddin yayi ganganci shiga hannunsa....
**
Firgita ta farka daga baccin nata salati saman harshenta, Wai ashe daga kishingid’a har bacci b’arawo yayi gaba da ita... Baccin da zata iya cewa sam bataji dad’insa ba domin kuwa haka taita mafarkai sarara marassa dad’i ciki harda na auren Yarima Mahmood da Gimbiya Raheemah... Wai anyi aurensu sun taho masarauta tare... Gabanta ya kuma tsinkewa tana add’uan Allah ya hana wannan mafarki nata yuwa... Wayarta ta lalub’a taga time yaja sosai dan da alama magrib ma yana shirin karatowa... Sauri sauri ta mik’e ta kuma d’auro alwawa tazo ta tada Sallan la’asar wanda daga yin alwala tana jira a kira sallan baccin ya saceta...
Bayan ta gabatarda Sallan La’asar d’in ne ta koma gefe tai lamo tana tinanin mafarkin da tai... Abu biyu ne a mafarkin nata... Na farko bayan auren Raheema da Mahmood yayi Raheema ta dab’awa Zahra makami ta kasheta, sai kuma auren Jamal da Umaima wanda Jamal da Giwa suka taru suka jefa Umaimar cikin wata irin kasko mai girman gaske suka busneta ciki.... Duk iyaka k’ok’arinta ganin ta taimaki Zahra da Umaima bata iya taimakon su ba cikin baccin.... Ta lumshe idanunta a hankali tana karanto Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Wad’annan aurattaya dake shirin wakana cikin Masarautar da alama sam babu alkhairi a tattaredasu... Shin ta yaya zata iya hana yuwar wad’annan auratayya...? Amasar data kasa samowa... Saida Ta jira akayi sallan Magrib kafin Ta mik’e ta nufi b’angaren Giwa ko Allah zaisa ta sami wani chance da zata iya karkato ra’ayin Umaima gameda Jamal....
A parlor ta tadda Umaimar harma da Jamal d’in alamun zance suke... Takaici ya turnuk’e mata mak’oshi, tai k’ok’arin sa kai da zummar juyawa dan ji tai bazata iya shigewa ba kuma... Saidai tuni Umaimar ta ganta, taceda ita ta shigo mana ai Zahra na ciki...
Badon taso ba Ta ida shigowa... Ta gaida Jamal babu yabo babu fallasa... Saidai ganin k’afarsa a guntule ba k’aramin mamaki ya bata ba... Ashe dai an guntule k’afar nasa..? Tai zancen cikin zuciyarta... Allah ya gani ko tausayi bai bata ba.. It is what he deserved after all..
Ta shige ta nufi wajen Zahra tana sinkayo muryarsa yana kuma kashe Umaima da salon k’aryarsa... A zuciyarta take Addu’an Allah ya fitar da Umaima daga sharrin wannan bawa nasa...
**
Giwa ta kuma karkatowa tana duban Jakadiya data kawo mata labari maras dad’i... Babu Ubandoma babu ahalinsa... Gasu Waziri har yanzu basu samu dawowa daga tambayo auren Yarima Mahmood ba...
Giwa ta tsare Jakadiya da idanu kana tace “Jakadiya dole a samo Ubandoma bazai yuwu Jafar ya kuma dawowa cikin Masarautar nan ba daga shi har Izzatu... A halin yanzu Bana buk’atar Izzatu koda kuwa itace zata sanar dani Duniyar da Saudatu take... Akan asirina ya tonu gwara na rasa Saudatu har abada... Zan iya sadaukar da komai akan na rasa mulki na...!”
Jakadiya Ta jinjina kai tace “Allah ya kareki ya kare Karagarki, a yanda nasan Ubandoma bazai tsaya nan kusa ba.. Zai wuya a samesa... Rankidad’e Anya kuwa abubuwan nan lafiya suke faruwa yanda suke faruwa a yanzu... Karfah ki mance ga auren Yarima Jamal da yarinyar nan Umaima da ya kafe akai babu jada baya..!”
Giwa ta murmusa cikeda izza da k’asaita tace “Har abada bazan tab’a barin hakan ya kasance ba... Sanin kanki ne mai auren Yarima Jamal yake nufi, inaji Ina gani bazan rasa d’ah na ba...!!”
Jakadiya ta d’an gyara zama tace “Allah shi taimakeki ga wani shawari... Tinda dai yarinyar nan da k’udurin sadaukarwa na k’arshe kike aje da ita... Mai zai hana Ki amince Yarima Jamal ya aureta, tinda a k’a’idan Sarauniya Tamuna sau d’aya zai tara da mace ta zama tata... Duk matayen Sarauniya sai yayi mu’amala dasu sau d’aya kafin su zama nata... Toh mai zai hana ki amince da auren... Daren da suka tare muka tabbatar mu’amala na auratayya ya shiga tsakaninsu sai mu d’auke ita Umaimar mu damk’ata ma Tal’udu kinga hakan ka iya sanyaya ran Tal’udu da fushin da yake dake... Anyowa Sarauniya sabuwar Amarya...! Rankidad’e inaga wannan shawari ce kawai ta kamata tinda mun sani Yarima na matuk’ar k’aunar yarinyar nan bazai tab’a janye k’udirinsa na aurenta ba..!!”
Giwa taiwa Jakadiya K’uri tana mai jin dad’in shawarin Jakadiya... Lokaci guda Ta saki murmushi tace “Madallah da wannan shawari naki Jakadiya... Dama Sadaukarwa ta Farko Jinin Sarki Jamaluddeen ne mahaifin Turai... Sannan na aje wannan yarinya Umaima ce jininta ya zamto Sadaukarwa na k’arshe.... Wannana shawari naki yayi Jakadiya, hakan za’ayi.... Zan amince ayi auren nan, sauran aiki naki ne Jakadiya... Dole kiyita zarya a sashen Yarima Jamal daren da aka kai masa Umaima... Idan har kika tabbata mu’amala ya shiga tsakaninsu mu kuma sai mu saceta akaitaga Tal’udu ya cika aiki ya baiwa Sarauniya Tamuna amaryarta Kinga jinin d’ah na ya kub’uta..!” Ta k’arashe murmushi saman fuskarta...
Jakadiya ta jinjina kai tace “Wannan haka ne Ya Shugabata... Allah ya k’ara miki lafiya.. Jaaa zamaninki... Ki jima kiyi kargo zuri’arki suyi Kargo..!!” Ta k’arashe tana d’aga mata babban yatsa alamun jinjina....
Suna a haka sukaji k’aran shigowar motoci cikin Masarautar alamun su Yarima Mahmood Sun dawo....
Muhibbah da Zahra dake zaune d’akin Zahran a tare suka mik’e suka nufi jikin window... Zahra tai saurin yaye masu labulen suna hangen sararin waje ga wutace sun haske ko ina cikin Masarautar....
Zuciyarta ne yai wani irin bugawa sakamakon hangosa da tai yana fitowa daga cikin mota hasken wutan lantarki ya haske kyakkyawar fuskarsa mai cikeda k’warjini sai kirari ake masa
“Takwarka lafiya Hadari malfar duniya..! D’an na gada Kafi d’an na koya... Lafiya baya goya marayu..! Lafiya limamin sarakuna..! Lafiya Azurfa babu gauraye..! Lafiya linzamin sarakuna..!Laaafiya mai ado da tagulla..! Lafiya mai sulken yak’i.. Lafiya mai tambura goma sha biyu..! Lafiya Uban gabasawa..!! Lafiya zauna gari k’i tashi..! Lafiya Bango majinginan Al’umma..! Lafiya tada kufayi..! Lafiya cika sarari..!! Laaaafiya D’an mai kiran gabas Arewa ta amsa..!! Allah ya Jaaa zamaninka Uban Fadimatu Zahra’u...!!”
Muhibbah tai masa K’uri tana kallon yanda ake masa kirari yana takawa gwanin ban sha’awa... Sosai sarautar ta amshesa, batansan sanda take sakin murmushi zuciyarta na mata wane irin sanyi...
Yazeed dake hangowa daga can saman benensa anaima Mahmood d’in kirari yanaji kaman garwashin wuta ake watsa masa illahirin jikinsa...
Giwa da Jakadiya dake hangosa daga nasu b’angaren, yanda ake masa k’irarin yana takowa ba k’aramin tada masu hankali hakan yayi ba... Ga Waziri a gefensa yana rarraba idanu wanda shima ko ba’ace a firgice yake....Ko shakka babu sunga jinin mulki a tattareda Mahmood d’in wanda k’warjininsa yai bala’in firgita duk wani mai k’ullin a zuciyarsa....
SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*
*54*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kaman ance ya d’aga kansa sama b’angaren d’akin Zahra, nan ya hangosu su duka biyun suna dubansa, idanunsa ya sauk’a kan Muhibbah wacce baisan ta dawo Masarautar ba...Cak ya tsaya ba tareda ya ci gaba da tafiya ba... Harga Allah ganinta tareda Zahra ba k’aramin sanyaya zuciyarsa yayi ba dukda cewa yau d’in gaba d’aya zuciyarsa a cubkunshe take bayan decision da ya yanke na auren Raheemah... Turaki dake gefensa ya d’aga Kai yana duban abinda yake kallo... Take Turaki ya saki wata irin sassanyar murmushi dan yaga abinda Mahmood ya gani... D’an matso da bakinsa kusan Mahmood d’in yai yace “Rankaidad’e jama’an Fada na kallonka, ya kamata ka sauk’e idanunka bamu fatan Mai Martaba Amale yai tuntub’e gaban Talakawansa..!!”
Sai sannan ya janye idanunsa ya aikawa Turaki wata irin duba cikeda k’asaita ba tareda yace komai ba.. Shi kaw Turaki sai k’ok’arin tsime dariyarsa yake a matsayinsa na hannun daman Mai Martaba... A haka akaiwa Yarima Mahmood rakiya zuwa b’angaren mahaifiyarsa Giwa...
Kafin su shigo Giwa da Jakadiya sunyi k’ok’arin kintsawa... Yarima Mahmood na shigowa Giwa ta isa garesa da fari’arta wanda da gani kasan da k’yar take nuna hakan... Waziri na bayansa kai a k’asa sai faman muzurai yake yana kuma kod’a Sarki Mahmooda...!
Giwa kanta yau d’in kirari tai masa irinta Saraki...Ta rik’o hannayensa bayan tawagarsa sun fice, sannan Ta sallami duk Hadiman dake cikin parlorn ya rage saura su kad’ai...Fuska a marairaice Giwa Ke fad’in “Alhamdulillah..! Allah zai cika min burina na ganinka saman Karaga Sadauki...! Yau ina ma mahaifinka nada rai ya ganka saman Karagar nan.. Babban burinsa kenan ka gajesa ka gaji gidanku...! Nafi kowa Farin ciki da wannan Al’amari... Na godewa Allah da ya karkato da hankalinka daga can k’asashen Yamma ya dawo dakai gida, mahaifarka ka kuma amince zaka gaji Gidanku... Sadauki ka gama min komai...!!” Ta k’arashe tana matsan k’walla...
Harga Allah yaji babu dad’i ganin yanda Giwa Ke farin ciki zai zamto Sarki... Anya hukuncin da ya yanke bai tsauri ba... Maiyasa zai zab’i ya watsawa mahaifiyarsa k’asa a idanu... Amma idan hakan shine zaman lafiyar d’iyarsa fah..! Mahaifiyarsa tanada sauran yara a nan, idan ta rasashi akwai sauran ‘yanuwansa, hasalima this is not the first time da ya tafi Turai ya zauna da family d’insa, dan ya kuma yi bazai zama bak’on Al’amari ba.. Sannan Zhara ita kad’ai yakeda... Bazaiso ya rasata ba, he’s doing all this for her.... But still mahaifiya mahaifiya ce ko yayane... Kuma ko ‘ya’ya nawa takeda tana son ‘ya’yanta equally, bazataso taga babu guda d’aya ba...Take yaji duk babu dad’i, ya d’ago hannu ya shafi fuskar Giwa yace “Maami Ki daina yawan shiga damuwa, everything will be alright in sha Allah...!”
Jamal dake tsaye daga bayan Giwa ya k’araso cikin dogarawa da sandar crutches d’insa yana sakarwa Mahmood d’in Murmushi yake furta “Congrats Yaya..! I’m so happy for you, zaka angwance kuma za’a nad’aka matsayin Sarki...!”
Mahmood ya sakar masa murmushi kana ya bud’e masa hannayensa yace “Come here, give your big brother a hug..!”
Jamal na murmushi had’ida sinne kai yake furta “Yaya kaifa yanzu Sarki ne..!” Ya k’arashe yana shafa kai alamun jin nauyi...
Murmushi mai kyau Mahmood yai yace “Koda ace ni sarki I’ll always be your big brother kaji koh..!” Ya k’arashe yana d’an buga kafad’an Jamal d’in kana ya k’arada “Ya jikin naka..?”
“Da sauk’i Yaya Alhamdulillah..!”
Mahmood yace “Masha Allah.. Allah ya k’ara maka lafiya...! Ka shirya gobe da safe in sha Allah zamuje asibiti mu duba Fu’ad...!”
Jamal ya jinjina kai yace “In sha Allah Yaya, dama nima goben inada zuwa ganin Dr na...” Ya d’anyi fasali kana yaci gaba da fad’in “ Yaya akwai maganar da nakeso muyi... Idan bazaka damu ba...Allah shi taimakeka...! Allah shi ja zamaninka..!!” Ya k’arashe yana kirariwa Yayan nasa...
Giwa ta had’iyi miyau da k’yar kana tace “Jamal ka k’yale Yayanka yaje ya huta yayi tafiya ya gaji...!”
Mahmood ya girgiza kai yace “A’a no... Family first, Ka tafi sashe na ka jirani a can, I’ll check on Zahra idan na fito sai muyi maganan koh...!” Ya k’arashe cikeda tausayin Jamal d’in duba da lalurar da yake fama dashi a yanzu...
Jamal ya jinjina kai cikeda jin dad’i yana mai masa godiya had’ida kwad’a masa kirari har ya haye sama... Ya maidoda dubansaga Giwa wacce Ke muzurai ya danna mata wata muguwar harara kana yasa kai yai shigewarsa, tana kiran sunansa ko tsayawa baiba balle ya amsata... Muguwar haushi take basa sabida bata goyon bayan aurensa da Umaima..!
Giwa tai saurin bin bayansa ta kamo sandar crutches d’insa hakan yasa ya dakata ba tareda yaci gaba da tafiya ba...
Fuska babu walwala yace “Let go... Ki k’yaleni na tafi Maami, I’m not in the mood for your lectures..!”
Giwa ta kuma had’iyan miyau da k’yar tace “Jamal ka saurareni please... Ba abinda kake tinani bane, ba maganan hanaka auren Umaima zanyi ba..!”
A hasale yace idan ba haka ba mai zakiyi... Mai zaki cemin...?!”
Giwa ta kuma marairaice fuska tana mai k’ak’aro murmushi yawa mutumiyar arziki tace “Ce maka zanyi na amince ka auri ‘yaruwarka Umaima.. Na amince ka fad’awa Yayanka a saka maku rana tare..!”
Da mamaki yake dubanta murmushi saman fuskarsa “Da gaske Maami...! Kin amince na auri Umaima..?!”
Giwa ta jinjina masa kai murmushi saman fuskarta... Baisan sanda ya rungumeta yana furta “Thank you..! Thank you Maami.. Kin gama min komai...Na miki alk’awari zan rik’e Umaima da amana, zan d’aura daga yanda kika tsaya.. Tin tana k’arama rik’onta a hannunki yake dan haka ni zanci gaba da rik’eta bisa gaskiya da amana..!”
Giwa Ta kuma murmusawa ta shafi gefen fuskarsa kad’an “Nasan zaka iya Gwarzo... Na gama iyaka tunanina idan ba kaiba babu wanda zai rik’e min Umaima bisa gaskiya da rik’on amana... I trust you Gwarzona..!”
Shima murmushin ya sakarwa mahaifiyar tasa su duka biyun suna duban juna...
**
Mik’ewa Muhibbah tai ta dubi Zahra tace “Princess zan wuce, zan koma masauk’i, Ina fata zakiyi duk abubuwan dana fad’a miki...”
Zahra ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida jinjina mata kai baki a ture kad’an...Muhibbah Ta sakar mata murmushi kana ta d’an dafata kaman zatace wani abu sai kuma tasa kai ta shige cikin tsananin kariyar zuciya, ta sani Raheema bata dace da Rankaidad’e ba amma yaya zatayi idan zab’insa kenan, bayan abubuwan da suka faru dashi bata fata ta kuma ganinsa broken, kuma tayi imani duk randa yasan abinda mahaifiyarsa da ‘yanuwansa sukai zai zama broken, bazataso Ta k’ara masa akai da matsalar Raheema ba...Zatai masa addu’an Allah yasa alkhairi a cikin aurensa da Raheema ya kuma shiryeta ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ahalin da yake k’ok’arin ginawa tareda ita...Tana fatan aurensa da Raheema zatai ya zamto silan shiriyarta domin shid’in mutumin kirki ne ya cancanci mace Ta k’warai....A hankali Ta saka hannunta ta murd’a handle d’in k’ofar.... Idanunta dake duban k’asa suka soma hango had’add’iyar takalmin kufta da k’afafunsa Ke rufe ciki, gabanta ya yanke ya fad’i.. Ga wani musulmin k’amshi da yai sallama ma k’ofofin hancinta, k’amshin nan dai da ya cika motar abokinsa sanda suka maidata gida...Cikin d’ak’ik’a zuciyarta Ke harbawa da sauri da sauri... A hankali take k’ok’arin d’ago k’wayar idanun nata zuciyarta bai daina harbawa ba har ta d’ago sosai suka dubi juna... Gani tai idanunsa k’yam akanta hannayensa hard’e waje guda fuskarsa d’aukeda alaman tambayar ya akai kika dawo..?!
Ta had’iyi miyau da k’yar ganin babu wani walwala saman fuskrsa, tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi wanda kai tsaye zaka kirasada yak’e. “Your Highness..! Barkada sauk’a..!!” Tai maganar cikin rabewar kalmomi...
Zaida ya kuma d’iban wasu dak’ik’ai kaman bazaice komai ba sai kuma yai mata alama da kai alamun amsawa ba tareda ya furta komai ba sai duban tuhuma da yake mata wanda sosai hakan ya haifar mata da tsarguwa... Ta d’an sadda kanta tana k’ok’arin matsawa alamun basa hanya...
Bai janye idanunsa ba har saida yaga tana k’ok’arin d’ago fuskarta.... Yai saurin kauda fuskarsa sabida zuciyarsa data gaza natsuwa... Muhibbah tasa kai Ta shige zuciyarta naci gaba da bugawa... Kaman daga sama ta sinkayo muryarsa na fad’in “Maiyasa kika dawo..?!”
Taji tambayar tamkar sauk’ar aradu..! Ta d’ago da sauri tana dubansa, sosai ya had’e gira... Rasa mai zatace tai sai murza ‘yan yatsunta da take... Da wutsiyar idanu yake dubanta alamun yana jiran amsa...!
Saida Ta had’iyi miyau da k’yar, kana Ta soma k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta dikda cewa lokaci guda taji bata k’aunar tai masa k’arya amma babu yanda Ta iya ne... “Amm... Dama lecture free week nake shisa na koma gida... And and Mommy was sick, so sai naje duba jikinta... But she’s ok now shisa na dawo sabida exams..!” Ta k’arashe da k’yar kaman mai laifin da aka titsiye gaban Kuliya...
Ya tsareta da idanu sosai kana yace “Dole sai cikin Masarautar nan zaki zauna..?!”
Maganarsa ya haifar mata da sanyin jiki, dan sam bata fahimci cewa ya fad’i haka ne gudun kada Yazeed ya kuma attempting cutar da ita har dai zasu zauna gida guda... Itakam ji tai maganar nasa kaman hannunka mai sanda yake mata... Batakaiga basa amsa ba ta kuma sinkayo muryarsa yana fad’in “At least you’ve someone to protect you here... It’s not safe out there...!!”
Tai saurin d’agowa tana dubansa dan sai yanzu ta fahimci mai yake nufi, saidai tuni yasa kai ya nufi cikin d’akin ba tareda ya tsaya jiran amsa daga gareta ba...Tabi bayansa da kallo had’ida sakin murmushi kad’an..
Daga nan yanda take tsaye tana iya hango alamu daga yanayin Zahra ko shakka babu Ta d’auki hud’ubar da tai mata cewa Ta nemi yafiyar mahaifinta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali zuciyarta na mata wane irin sanyi Mahmood da d’iyarsa zasu sasanta... A haka ta nufi masauk’i tai kwance tana tinanin abubuwa da dama... Saidai duk juyi da zatai sai Rankaidad’e ya fad’o mata... Maiyasa tinaninsa ya addabeta..? Toh Kodai dan a baya tanajin guiltiness ne, toh amma yanzu fah..? Ai ya kamata ta yakishesa a zuciyarta tinda ta tabbata Zahra zata d’auki hud’ubarta ta baiwa mahaifinta hak’uri su sasanta tsakaninsu... Ta kuma sakin murmushi a hankali tana tuna had’uwarsu da sukai d’azu... Kalamansa na k’arshe zuciyarta keta nanatawa _You’ve someone to protect you here.._ Ta kuma sakin murmushi a hankali had’ida lumshe idanunta...
**
Washe gari Zahra Ke sanar da ita yanda sukai da mahaifinta, sosai taji dad’in hakan, saidai a cewar Zahran duk sabida Muhibbar tai haka... Aje dai a hakan taji dad’i sosai da suka sasanta tsakaninsu... Zataso komawa gida tinda tayi Major abinda ya dawo da ita saidai alk’awarin da ta d’aukarwa Ubandoma da mahaukaciyar matar nan harmada Jafar shine kawai zai iya zaunarta a Masarautar bacin haka bataga kuma mai zata zauna tai ba tinda tayi abinda ya dawo ita...A bakin Zahran take jin cewa mahaifinta ya sanar da ita an saka bikinsu da Raheema nan da sati biyu kuma ta basa goyon bayanta dikda cewa bata k’aunar alak’arsu da Raheemar amma tinda yana so zatai hak’uri ta accepting d’inta muddin hakan zai faranta masa rai....
Take jikin Muhibbah yai sanyi tamkar an tsoma a k’ank’ara... Ta d’ago idanunta masu rauni tana duban Zahra dasu “Kikace an saka auren Paa d’inki..?!”
Zahra ta jinjina mata kai tace “Haka Paa yace min an tsaida aurensu nan da sati biyu dan masu mulki basa jira... Amma na gaya masa dan dai kawai yana sone idan ta ni ne bana son ya aureta... But I guess I don’t have a choice then..!” Ta k’arashe cikin sanyin murya tana mai zama saman koren ciyawan da yaima lambun shak’atawan k’awanya...
Muhibbah ta zauna a sanyaye tana mai jinjina lamarin, in the next two weeks Rankaidad’e zai auri matar nan... Ta had’iyi miyau da k’yar tana mai ayyanawa cikin zuciyarta, tabbas bazata jira sati biyu yai mata a wannan masarauta ba gwara kawai ta tafi dan Allah ya gani bazata juri ganin auren Rankaidad’e da matar nan ba... Zataji kaman taci amanarsa ne tinda ita tasan mai zai aura shi kuma bai san mai zai aura ba... Duk surutun da Zahra ke mata bata d’aukan komai tuni tai nisa cikin duniyar tunani...
Yarima Mahmood da Turaki kaw daga can saman bene suke hangan Zahra da Muhibbah, hannayensa hard’e ta baya yake dubansu zuciyarsa naci gaba da raya masa wasu abubuwa...
Turaki dake tsaye gefensa sauk’e ajiyan zuciya yai kad’an kana yace “Your Highness har yanzu kana nan akan bakan ka na barin k’asar... Dan Allah think your decision through, wacce kake shirin yin wannan abu domin ita gashi ta kwantar da hankalinta, a tunanina Rankaidad’e you don’t need to leave anymore...!”
Ba tareda ya dubesa ba har lokacin idanunsa naga Muhibbah yake furta “I’m sure this is all her doing... Inada tabbacin cewa ita ta shawo kan Zahra, she’s a good influence to my daughter... Saidai ita d’in ba mai zama cikin Masarautar nan bane, akwai randa zata gama abinda ya kawota Ta tafi... I’m afraid idan ta tafi Zahra zata iya komawa ruwa, musamman akwai ire irensu Yazeed cikin Masarautar nan masu poisoning zuciyarta da gurb’atattun tinani... Zaifi kyau idan na d’auketa daga cikin Masarautar nan...!”
Turaki yayi shiru yana dubansa, lokaci guda ya girgiza kai yace “I’m sorry Rankaidad’e but ya zama dole na fad’a maka gaskiya hardai kana nan a matsayinka na Abokina.... Mahmood bari na maka magana da siga ta abokantaka mu aje mulki da matsayinka a gefe.. Ina maka magana ne a matsayina na abokinka ba a matsayinka na Sarki ba...Wannan hukunci da kake k’ok’arin yankewa akwai ranan da zakai nadamar yinsa... Your life is right here, cikin Masarautar nan... Bakada sauran rayuwa a Spain...!”
Cikin karaji yaceda Turaki “I don’t remember asking for your opinion...!”
Turaki ya nusa kad’an kana ya furta “Fine naji baka nemi shawarina ba... But ya zama dole na fad’a maka ko bazaka saurareni ba Your Royal Highness...!! Haka zaka tafi kana mai sab’a alk’awari..Haka zaka tafi ka bar mutuwar mahaifinka da matarka unpunished..? Haka zaka tafi ka k’yale mahaifiyarka da jin kunya bayan Ta aminta da kai..? Haka zaka tafi ka bar Al’ummanka masu k’aunarka broken..?!” Ya d’an sassauta muryarsa yana mai ci gaba da fad’in “Haka zaka tafi ka k’yaleta da k’aninka mai kwad’ayin jikinta cikin Masarautar bayan ka mata alk’awarin kareta..?! Haka zaka tafi ka hana zuciyarka kasancewa da zab’inta... You can’t leave all these behind your Highness...!!Ya k’arashe yana mai duban abokin nasa cikin wane irin yanayi....
A hankali ya karkato yana duban Turaki zuciyarsa na kuma bugawa, lokaci guda yake furta “What exactly do you mean..? Wacece kake nufi..?!”
Turaki bai basa amsa ba saima maida dubansaga b’angaren dasu Muhibbah Ke zaune da yayi... Lokaci guda yake ci gaba da furta “You can’t deny it your Highness, You love her... So much...!!” Ya k’arashe yana duban Mahmood d’in cikin idanu...
Bai iya furta komai ba sai duban Turaki da yake babu k’yafta idanu, fuskar nan tasa kaman bai tab’a dariya ba...
Turaki na ci gaba da sakin huci yake furta “Your Highness abinda kake k’ok’arin yi cin amanan Masarauta ne..! Cin amanan Al’ummanka ne...! Cin amana Ahalinka ne..!! Ba’asan Sarki da sab’a Alk’awari ba Rankaidad’e... Sunnan Sarakuna ne cika alk’awari da yin magana k’wara d’aya tak..! Kada ka zamto Sarki na farko da zai bar abin fad’i a tarihi..!!”
Da tsananin mamaki Mahmood ke dubansa, shine Turaki Ke fad’a masa magana haka....Lokaci guda yai gyaran murya Parlorn ya amsa... Take Hadiminsa ya k’araso yana mai zubewa had’ida kwasan gaisuwa...
Har lokacin idanunsa naga Turaki hannayensa hard’e ta baya, fuskar nan tasa tamau, saida ya kwashe dak’ik’ai kaman bazai magana ba Hadimin nasa na nan risine wajen sai kuma ya bud’e murya yace “Kai masa rakiya zuwa k’ofan Fada...! Kuma kar a sake barinsa ya shigo har sai na bada umarnin hakan..!!”
Turaki ya sadda idanunsa k’asa dan yasan hakan ka iya faruwa... Lokaci guda yake furta “I’m sorry Your Highness... But I know my way out..!!”
Yana ida fad’in haka ya risina yace “Na Barka Lafiya Rankaidad’e..!!” Lokaci guda yasa kai ya nufi k’ofa...
Barde ya mik’e yana an gama Rankaidad’e..! Allah shi ja zamaninka..!!” Lokaci guda yabi bayan Turaki yana furta “Fada bata Marhaban da kai...!!”
Mahmood dake nan tsaye wajen fuzar da huci mai tsananin d’umi yayi zuciyarsa na masa k’una... Yana mai tuhumar kansa da abubuwan da Turaki ya zayyano masa, ciki babu wanda ya tsaya masa a rai kaman cewa da yai son yarinyar nan yake...
Hannayensa biyu yasa ya shafi fuskarsa yana mai kuma fuzar da fuci yake taka cikin tampatsetsen parlorn nasa cikin taku d’ai d’ai irinta masu mulki...
SameenaAleeyou📚*MUHIBBAH*
*55*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yau kusan sati kenan babu su Ubandoma babu labarinsu, fad’in tashin hankalin da Giwa Ta tsinci kanta ciki b’ata baki ne... Ga duk wanda yai mata Farin sani kallo guda zai mata ya fahimci bata a hayyacinta, tabbas duniya tai mata atishawan tsaki, abubuwa sunci
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 65