Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Giwa taci gaba da fad’in “Nasan ban canci yafiyarki ba.. Amma Rankidad’e dukda haka zan nemi yafiyarki ya Shugabata..!” Muryar Muhibbah ne ya katseta yanda take takowa gaba Gareta tana furta “Sabida kinsan tanada zuciya mai kyau zata yafe miki Ko ince ta riga ta yafeki tuntuni shiyasa kika sami k’warin gwiwar rok’onta gafara.. Shin idan ita ta yafeki ina Allahan mutanen da kika zalunta Giwa..? Shin mahaifinta Sarki Jamaluddeen da kika rabasa da raywuwarsa shi ya yafeki..? Kokuma ‘ya’yanta da kika rabasu da mahaifiyarsu sun yafeki..? Kika kashe matar Mahmood bayan kin datse mahaifarta Dan kar ya samu magaji sannan kika maida Ja’afar Bawa a gidan Mahaifinsa.... Kin mance da d’an uwanta Yarima Alfah wanda kika halak’asa kika kuma tarwatsa ahalinsa... Matar da kika maidata baiwa mahaukaciya a cikin gidan mijinta kika azurta kanki da Martabarta kika toshe duk wani hanya na kwanciyar hankali cikin rayuwarta, daga k’arshe kika kashe mijin nata kika hana ta masa takaba yanda ya kamata wannan matar kike neman yafiya da afuwa daga gareta..? Ki fad’a min Izzatu wannan matar ce kike rok’onta Ta tafe miki..!!” Muhibbah ta k’arashe cikin d’aga murya hawaye na gangaro mata, illahirin mutanen dake wajen hawaye na gangaro masu.. Lokaci guda Muhibbah taci gaba da girgiza kai tana furta “Saidai ita din tanada zuciya mai kyau na tabbata bazataso ganinki a yanayi Da kike ciki ba... Zataso Ki samu sassauci dukda tulin abubuwan nan da kika mata..!” Giwa na hawaye take furta Saudatu..!!” Muhibbah Ta jinjina kai tace “K’warai ni ce nan SAUDATU wacce kika k’udiri niyyan cika Mulkinki da ita kuma nice nan MUHIBBAH wacce Ta miki alk’awari zata kawo k’arshen Mulkin ki da zaluncinki da taimakon Allah.. Yau gashi na cika miki alk’awarinki GIWA...Na fad’a miki dama zaki koma sharan cikin Masarautar nan Sai ya fiki daraja, zaki kasance cikin k’ask’anci da tozarci yau gashi nan duk sun tabbata akanki... Ki sani Allah baya barin zalunci ya tabbata...!!!” Ta k’arashe hawaye na gangarowa daga idanunta... Daidai nan Gimbiya Turai Ta k’araso ta rungumeta su duka biyun suna hawaye kana Gimbiya ta bud’e murya tace “Duk abinda zan fad’i d’iyata ta riga ta fad’i maki Izzatu.. Bayan tulin abubuwan da kika mana zan barki ki k’arasa jinyarki cikin Masarautar nan dan iyakacin abinda zan iya miki kenan dan nasan bakida wani wajen zuwan da yafi nan..!” Ta kuma duban tsohuwar Jakadiya da kanta Ke kife k’asa tana matsan hawaye itama kana tace “Ke kuma Jakadiya bayan cin amanan Masarauta da kikayi hukuncin ki daga Masarauta shine kiyita kula da ita har k’arshen rayuwarta tinda tare kuka jima kuma sak’awa kuna k’ullawa... Ubangiji ya sassauta miki Izzatu...!!” Giwa ta shiga godiya tana hawaye Jakadiya ma na hawaye tana godiyan dole dan Allah ya gani kukan hukuncin kulada Giwa da aka yanke mata kawai take, kashi futsari cin abincin Giwa da komai ya dawo hannunta... Kafin su baro wajen Gimbiya Turai ta tsawatar ma Bayin da yaransu akan wulak’anta mutum, a cewarta duk cikin masarauatr babu wanda yake abun wulak’antawa daga masu Mulki har b’angaren Bayi.. Masarauta bazata lamunci mummunan d’abi’a ba.. Kowa yanada ‘yancin rayuwa mai kyau a matsayinsa na d’an adam cikin Masarautar... Wannan jawabi nata sosai ya kuma yin dad’i ma ahalin Masarautar gaba d’aya... Rayuwar masarautar ta kuma sauyawa kowa daraja kowa yake da mutuntawa babu wulak’anci babu tozarta kowa... Giwa da Jakadiya suna can b’angaren su suna jinya dukda cewa wasu lokutan Jakadiya bata iya jurewa.. Sosai Jakadiya tayi nadaman rayuwar data tsinci kanta ciki, da ace batabi son zuciya ba da yanzu tana nan cikin Masarauta a matsayinta na Jakadiya gashi yanzu ta dawo b’angaren k’anan bayi wanda ko matsayin shiga sashen masu mulki basu dashi... Bayan faruwan haka da kaman sati biyu Jakadiya ta farka daga bacci cikin dare taga wani irin k’atoton bak’in kumurcin maciji ya kanannad’e Giwa ga wasu irin kukiyoyi munanan sai yagan naman jikinta suke... Giwan tana sakin wane irin k’ara na azaba... Ai da rarrafe Giwa ta fice daga d’akin tana neman d’auki.. Saidai tana ficewa k’ofar ya rufe da Giwa... Akayi akayi a bud’e tun cikin daren k’ofa Ta kasa bud’uwa.. Tun ana sauraro gurnananin ihun Giwa har dai aka daina saurarowa, wajen yai tsit alamun ran Giwa yayi halinsa...! Allahu Akbar kabiran... Yau babu Giwa, Duk Mulkin data baza a doron k’asa yau Ta tafi a wulak’ance..... Rayuwa kenan, yau kaine gobe ba kai ba... Haka da k’yar aka b’alla k’ofar aka fitar gawan Giwa wanda banda d’oyi baya komai... Da k’yar daga cikin tsirarru suka fitar da ita daga cikin Masarautar ko ina suka nufa da ita sai Allah ko Sun mata sallah ko basu mata ba Allah kad’ai ya Sani dan labarin mutuwar Giwa bai isa cikin Fadah ba saida gari ya waye sosai... Dukda abubuwan da Giwa tayi wanda hankula suka gaza d’auka hakan bai hana ahalin Masarautar tausaya ma irin mutuwar da tayi ba.. Da k’yar aka sanar da Fu’ad dake can k’asar Spain.. Ya nuna damuwarsa da tausayin yanda mahaifiyarsa ta k’are dama yasan akwai rana irin wannan da zaizo tunda Giwa dai babu wani abu na alkhairi data shuka a rayuwarta sai akasin alkhairi.. Ta kashe rayuka da dama ta cutar da dama sannan uwa uba laifin Shirka da take wanda Allah na yafe ko wani irin laifi da rahamar sa idan yaso matuk’a baka mutu kana shirka ba... Mutuwar Giwa ya zamto wa’azi Babba ga d’aukacin Al’umman cikin wannan Masarauta harmada wad’anda labarinta ya cimmasu... Kaman anyi ruwa an d’auke yau babu Giwa da ahalinta da duk wani Mulkin zalunci datayi a Masarautar... Bayan wasu kwanaki da faruwan wannan al’amari Ja’afar da Ubandoma suka fito da Waziri, ya koma kaman bashi ba duk ya jeme ya zama abin tausayi, suka gurfanar dashi gaban Mai Martaba.. Mahmood yace yaci Albarkacin Yazeed, Masarauta tai masa rangwame yajesa an tub’esa daga sarautar Waziri sannan bazai sake tako k’afarsa cikin Masarauta ba har abada..Waziri yana kuka yana godiya haka ya fice daga Fadah babu rawani... ** Kwanaki sun tafi, satuttuka sun shud’e har an soma k’irga watanni... Tsaye take gaban k’atoton madubin d’akin nata tana d’aura d’ankwali.. Kallo guda zakai mata ka fahimci hutu da kwanciyan hankali sun Zauna a wajen.. Ta k’ara cika da kyau ga wani annuri na musamman daya cika fuskarta... Zahra ce ta shigo da sallama tana fad’in “Your Highness Mommy unborn Ke kad’ai ake jira a rufawa Amarya Alkyabbarta.. Ummi tace babbar Ya Uwa baza’a rufawa Aunty Umaima Alkyabba ba sai kina nan...!” Muhibbah Ta murmusa a hankali tace “Aiko Ummi tayi gaskiya dan ko an rufa alkybbbar nan sai an yaye na sake rufa ma ‘yaruwata...!” A tare suka murmusa kana Muhibbah takai dubanta ga cikinta mai kimanin watanni biyar wanda har ya fito waje kaman wani cikin wata bakwai... Zahra Ta d’anyi gyaran murya tace “You know I can’t wait Baby na ya fito duniya zanfi sonsa fiye da kowa.. Coz I’d be his or her Godmother..! Muhibbah ta d’an ja hancinta kad’an tace “Toh Sarkin ‘yan surutu zaki shige muje ne ko kuwa..!” Zahra na murmushi tace “Tia..!” Muhibbah Ta dubeta tace “Yes princess..” D’an kwantowa jikinta tai kad’an tace “I love you..” Murmushi saman fuskarsa Muhibbah ta rungume ‘yar uwar tata had’ida furta “I love you too Baby..!” Suka kuma sakar ma juna murmushi kafin suka nufo downstairs yanda Hadimansu Ke jiransu... Ansha Bikin Yarima Ja’afar da Gimbiya Umaima lafiya.. Amarya da ango sun tare a b’angaren su wanda Sarki ya k’awata masu shi da kayan alatu.. Saidai Fu’ad bai samu yazo ba dan jarabawa suke.. Zahra ce taita nuna masa Bikin Ta hanyar tura masa pictures wasu lokutan kuma Sai ya kirata suyi video call tana had’asa da mutane ‘yan biki su gaisa... A haka akaci biki lafia aka tashi.. Rayuwa tayi dad’i Ta ko wanne b’angare sai son Barka... Amarya Umaima da angonta Ja’afar sun bud’e Sabon shafin soyayya na rayuwarsu... Zahra ma ta maida hankalinta sosai ga karatunta... A haka Muhibbah Ta isa watan haihuwarta yanda Ta haifo d’anta namiji kyakkyawa mai kama sak da mahaifinsa.. Kaman Kakin Mahmood.. Allahu Akbar Zo kaga murna wajen Mahmood Dama d’aukacin mutanen cikin wannan masarauta.. Babu ya Gimbiya Turai wacce bayan tsawon shekarun nan yau Allah ya nuna mata gudan jinin Mahmood d’inta.. Allahu Akbar lallai mai rai kar ya zamto mai cire tsammani ga Rahamar Ubangijinsa...Bayan Giwa tayi duk yanda zatai ganin cewa Mahmood bai samu Magaji ba yau Sai gashi Allah ya azurtasa da Magaji.. Yai tsaye yana dubanta yanda take bacci hankali kwance ga Baby a gefenta. A hankali ya k’arasa ya duk’a gaban gadon.. Yai mata K’uri yana duban fuskarta da yai fayau dashi.. A hankali ya sumbaci goshinta yana mai duban fuskarta kyakkyawan murmushi saman fuskarsa.. A hankali take bud’e idanunta har ta sauk’esu saman kyakkyawan fuskarsa.. Suka sakar ma juna murmushi, lokaci guda yakai hannunsa guda yana shafa fuskarta, a hankali yake furta “How are you feeling my Queen..?!” Hannunsa Ta sakale cikin nata had’ida sumbatar hannun nasa tace “Good.. I’m feeling Good my King.!” Murmushi bai bar saman guskokinsu ba suke ci gaba da duban juna cikeda so da k’auna.. Mahmood ya zauna gefenta kad’an kana yasa hannu ya d’auki jaririn dake kwance gefenta Sai wutsil wutsil yake alamun ya tashi bacci.. Ya sumbaci yaron a goshi yana mai lumshe idanunsa.. Muhibbah tai masu K’uri tana godiya wa mahaliccinta da ya lullub’eta da wannan rahama bayan iftila’in rayuwa data fuskanta kala kala wanda bata tab’a tsammanin rayuwa zata sauya mata irin haka ba.. Ya shiga jijjiga yaron daketa k’ok’arin tsala kuka yana lallashinsa yake furta “C’mon Champ, Paapa is here.. Are you hungry..? Or do you wanna go horse riding my prince .. Shiii is okay, Maama is still weak ka barta Ta huta kaji koh..!” Ya k’arashe yana mai jijjiga yaron a kafad’arsa.. Sosai ya birge Muhibbah tai masu K’uri tana dubansu murmushi saman fuskarta.. A haka Mahmood yaita jijjiga yaron har ya koma bacci... Ya d’ago yana duban Muhibbah da tai masu K’uri ya d’an kashe mata idanu guda yace “You can go back to sleep now shima yayi bacci..!” Murmusawa tai kad’an tace “I never knew Sarki ya iya raino haka..” Kusan kunnenta ya matso kaman mai rad’a yace da ita “Ni kuma yanzu waye zai raine ni tunda sun rufeki a nan..Inaga dai k’arshe zan karb’i tayin da aketa min daga garuruwa daban daban ne..!” Ai bai kai aya ba tai kicin kicin da fuska kaman mai shirin kurma ihu tace “Your Highness Ummi fah zata iya shigowa yanzu kawai ka tashi kaje.. ai dama nasan ku sarakuna baku iya zama da mace guda.. So nasan wataran zakayi ai ko an maka tayi ko ba’a maka ba..” Ta k’arashe fuska a tamke kaman ba ita ba.. Ya d’an murmusa kad’an yace “Allah huci ran Gimbiya Giwar Amale...Duk suyi zamansu I don’t need to do what other Kings are doing, To me you’re more than enough my Queen..!” Ya k’arashe idanunsa cikin nata.. Ta murmusa kad’an cikeda kunya.. Shima murmushin yai yace “Wai dama haka kikeda kishi ne..?” Murmushin ta kuma yi tana mai sanne kanta... Ya ajiye Jaririn gefenta kad’an yana mai dubansu su duka biyu.. Lokaci guda Muhibbah tace “Wanne suna zaka saka masa have you thought of the name..?” K’uri yai mata ya kuma duban yaron kana yace “You choose the name.. Duk wanda kike so..!” Tai murmushi a hankali kana tace “Mahmood..! Mahmood (Hamdaan)..!” Yai mata k’uri yana dubanta kana yace “Yarima Mahmood Hamdaan ibn Mahmood..! Wow what a beautiful name.. Na gode da aka min Takwara..!” Ta matso kusansa a hankali ta saka hannunta cikin nasa lokaci guda take furta “Ka cancanci fiyeda haka my King.. Ka haskaka min rayuwata a lokacinda nayi zaton babu wani haske da zai kuma bayyana cikin rayuwata.. Ka dawo min da Farin cikin dana rasa a rayuwata ko ince Wanda banyi zaton zan samu ba bayan iftila’in da ya auka min.. You’re not just my king Your Highness..! You’re my world..!” Murmushi saman fuskarsa ya sumbaci goshinta zuwa labb’anta.. Lokaci guda yake furta “Manzon Allah S.A.W yana cewa _Aldunya mata’un.. Duniya jin dad’i ne.. Wa khairu mata’uddunya.. Mafi alkhairin jin dad’in duniya Almar’atussaliha.. Itace mace Ta k’warai.._ Ni nayi dace da samun mafi alkhairin jin dad’I na duniya wacce nake fatan har a aljannah ta zamto wannan jin dad’in nawa.. I love you so much My Queen..!” Ya k’arashe yana mai rungumeta had’ida lumshe idanu.. Su duka biyu suka jima cikin jikin juna kaman kar su rabu da juna har saida suka soma sinkayo kukan Yarima Hamdaan kafin Mahmood ya sassauta rik’on da yai mata.. Ya d’auki yaron ya mik’a mata, Ta shiga bama yaron abincinsa Mahmood na tayata cikeda nuna kulawa da k’auna.. Ranan juma’a akayi shagulgulan rad’in sunan Yarima Mahmood Hamdaan.. Akayi wasan Dawakai a Fadah aka buga Tambura aka busa algaita.. Kowa na son barka da Yarima da mahaifiyarsa yanda suka amshi kyauttuka kama daga kan Mai Martaba har izuwa sauran ahalin gidan.. Suna yayi albarka an cika sosai su Mommy dasu Gudidi duk sunzo harmada matar Ansar wacce itama nata cikin ya d’an soma fitowa dashike tafiyar ba wani mai tsawo bane kuma da lafiyarta shiyasa Mommy Ta amince suka taho gaba d’aya... Harta Raheemah ma tazo suna daga can masarautarsu... Kaman yanda yake a tsarin gidan daren Jumma’an aka had’a hamshak’in Royal Gathering, kowa yai shiga Ta alfarma harta da jariri Yarima Hamdaan shima ba’a barsa a baya ba.. Yana rungume hannun Kakarsa Gimbiya Turai.. Muhibbah tai tsaye daga can saman benen Mahmood tana hango yanda aka hallara gaba d’aya Masarautar.. Hasken wuta ya gauraye ko ina tamkar rana.. Ta lumshe idanunta tana godiya wa mahaliccinta da wannan baiwa da ya lullub’esu dashi.. A hankali taji alamun Rankaidad’e Ta bayanta yanda ya rungumota had’ida d’aura hab’arsa kad’an saman kafad’arta.. Su duka biyun sukai k’uri suna kallon yanda Ahalinsu ya cika da albarka.. Zahra tana video call da Fu’ad tana nuna masa Prince Hamdaan, Fu’ad sai wasa ma yaron yake ta cikin waya kaman yana ganinsa, Umaima da Ja’afar wasu love birds d’in suna daga gefe suna zuba nasu love d’in... Allah ya raya Yarima Hamdaan..! Mahmood ya kuma matseta cikin jikinsa yana shak’an k’amshinta mai sanyaya zuciya.. Murmushi kwance saman kyakkyawan fuskarta take ci gaba da duban illahirin fad’in Masarautar, a hankali Ta furta “Hamdaan katheeran Ya Rabb..!” Nima a nan na tayata da furta ALHAMDULILLAH..! ************* Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** *A nan na kawo k’arshen wannan littafi nawa mai taken MUHIBBAH.. Ina rok’on Allah ya yafe min kurakuren dake ciki, fad’akarwan dake ciki Ubangiji ya amfanemu dashi baki d’aya..Ameen..!* *Bazan iya ajiye alk’alamina ba tareda na mik’a godiyata da jinjinata a gareku ba d’imbin masoyana.. Hak’ik’a kun nuna min k’auna dani da wannan labari nawa mai taken Muhibbah.. Idan babu ku babu Muhibbah...A duk yanda kuke a fad’in Duniyar nan ina k’aunarku nima.. Ubangiji ya bar k’auna...* *Sameena Ke maku Fatan Alkhairi...* SameenaAleeyou📚 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 65 of 65