da yankewa, tanajin yanda k’irjinsa yai mata rumfa.. Meke faruwa da ita.. Shin Rankaidad’e ne yake bibiyarta haka..? Toh mai hakan yake nufi..?! Take taji zuciyarta naci gaba da tsinkewa abinda ya faru da ita shekaru goma sha hud’u baya ya shiga dawo mata.. Tsoro da firgici suka cikata..! Ya fahimci yanayin da take ciki na tsananin tsoro da firgici, hakan yasa ya kuma rufeta sosai da k’irjinsa, saitin kunnenta yake rad’a mata “bani daga cikin shaid’anun mutane, bani daga cikin wad’anda suke keta haddi kan abinda damarsu bai mallaka ba..! I’m here now, kiyi bacci cikin aminci.. Bazan bari wani abu ya cutar dake ba... I’ll watch you sleep the whole night..!!” Ya k’arashe yana mai rufa masu bargo da d’aya hannun nasa har lokacin bai saketa ba yana rik’eda ita cikin jikinsa...!
Cikin yanayin tsoro take furta “Rankaidad’e.. Shin kaine..? saida maka ni sukai..?!” Cikin tsananin rawar murya take ci gaba da furta “Kaji tsoron mahaliccinka wanda yake iya ganinka komin duhun daren nan... Kada ka cutar dani..!”
Ta sinkayo muryarsa kaman mai rad’a yana furta “Do you have to keep on buzzing..? Stop asking questions..! Just close your eyes and go to sleep now...!”
Samun kanta tayi tana mai bin umarninsa, Ta rintse idanunta da k’arfin gaske zuciyarta bata daina tsinkewa ba, wannan murya Ta Rankaidad’e ne..! Toh mai yake nufi da kalamansa da yace baya daga cikin shed’anun mutane wanda suke keta haddi kan abinda damarsu bai mallaka ba..? Toh kodai siyar masa ita Baffah Yawale yayi shiyasa ya kawota cikin Masarautar ya aje... Kardai a matsayin Kuyanga ya sayota, kardai ba’a d’aura mata aure da Ansar ba..! Shin Wai meke faruwa ne..?!! Toh kodai ma ba Rankaidad’e bane..!? Idan bashi bane Wanene...?
Ta lumshe idanunta har lokacin tsoron bai saketa ba, tanajin yanda zukatansu Ke bugu cikin na juna, bata San ya akayi bacci ya saceta a yanayin da take ciki ba, farkawa tayi da asuba taga baya nan... Tai saurin kunna side lamp zuciyarta na kuma tsinkewa bataga kowa ba sai wannan musulmin k’amshin nasa dake tashi a hankali kama daga jikinta zuwa yanda ya kwanta..! Ta lumshe idanunta a hankali tana ambaton Allah.. Kalaman mutumin yana dawowa kanta wanda tafi bada k’arfin zaton Rankaidad’e ne..! Meke faruwa..? K’ila dai sayota yayi matsayin Kuyanga..! Wannan tunanin shine yafi tsaya mata a zuciya..! Ta lumshe idanunta hawaye na kuma gangaro mata... Sai tana ganin abin tamkar a mafarki ne ya kasance..! Sosai Ta shiga rud’u da damuwa... Ta shiga lalumen magungunan data sha daren jiyan tana tinanin anya batayi overdose ba..!
**
A b’angaren Mahmood kuwa tinda ya dawo nasa b’angaren ko wane juyi zai sai ya tuna daren jiya, da yanda sukayi bacci cikin jikkunan juna, inama hakan ya kasance ko yaushe, yasan ya barta cikin tarin rud’u da tunanin abinda Ke faruwa tinda har wannan lokaci bai fito fili ya sanar da ita dalla dalla abinda ya faru ba..! Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai tuno k’amshin da ya shak’a cikin jikinta, shikad’ai sai sakin murmushi yake... Yana jan cazbahan dake rik’e hannunsa yana kuma sakin murmushi sanda ya tuna kalamanta a garesa wanda sosai sukaso basa dariya amma ya gimtse... A fili ya furta “So innocent..!!” Tunowa da yayi Muhibbah zata iya kasancewa ‘yaruwar Zahra ya sanyashi mik’ewa zaune sosai yana tuno abubuwan da suka faru...
Ya jima yana zaune wajen yana tuna abubuwan da suka faru sai faman sak’awa da warwarewa yake, dole ya gwada k’wayar halittarsu cikin gaggawa domin tabbatarwa idan sud’in ‘yanuwan juna ne, saida gari ya d’an soma wayewa kana ya fito domin ya nufi k’abarin mahaifinsa.. A hanya ya had’uda Ja’afar da alama shima k’abarin MaiMartaba mahaifinsu ya nufa..!
Ja’afar yana ganinsa ya k’araso suka gaisa, a tare suka jera suka nufi k’abarin mahaifinsu.. Suka jima sosai suna masa addu’a kafin daga bisani suka nufi b’angaren mahaifiyarsu...
A parlor suka taddasu itada Baba Nomau yana karanto mata Alk’ur’ani tana biyawa..!
Cikin jin dad’I suka k’araso suma suna sauraro, saida suka ida karatun kana Mahmood da Ja’afar suka risina suka gaisheda mahaifiyarsu... Suka isa can saman Darduman da Baba Nomau Ke zaune bisa sukai masa musabaha had’ida gaisuwa..!
Baba Nomau ya kamo hannun Ja’afar yace suje Bargan Dawakai ya nuna masa Doki mai Fararen sawaye da yake basa labari kafin ya koma gida..!
Ja’afar na murmushi ya amshi jakan fata ta Alk’ur’an d’in Baba Nomau suka nufo waje yana fad’in “Baba ashe dai baka mance ba..!”
Baba Nomau yace “Yarima ina zan mance, bayan abinda nake son gani ne..!”
Ja’afar ya kuma murmusawa yana mai furta “Aiko wajensu na nufa dan nayi kewan Dawakan gaba d’aya..”
Suka jera suka nufi Bargan Dawaki, Hadiman Masarautar duk yanda suka gansu sai Sun risina Sun gaidasu, abinda Ja’afar yakema wasu a baya yau sai gashi ana Yi masa..! Allah kenan mai juya al’amaransa a lokacin da yaso..!
A can parlorn Gimbiya Turai kuwa gyaran murya tai ta ambato Mahmood da fad’in “Saraki..!”
Mahmood ya amsa mata cikeda girmamawa..
Gimbiya taci gaba da fad’in “Dama inaso nai maka magana kan Saudah...!”
Ya d’ago a hankali yana duban mahaifiyar tasa sai kuma ya maida kansa k’asa...
Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Tinda ga yanda auren naku ya kasance, kafin Ayi shelanka matsayin Sarki.. Kafin ai maka nad’i ina son sanin matsayin auren naku tunda kasan sharud’a da k’aidojin al’adu da dabi’u na cikin Masarautar nan..! Idan har Saudah bata k’aunarka a matsayin miji da zatai rayuwa dakai bazanso Ta kuma wani rayuwar k’unci nan gaba ba... Ta cancanci Farin ciki bayan tulin iftila’i na rayuwa data fuskanta..! Shiyasa nace kafin ayi maka nad’i a ambaceka a matsayin Sarki, Ina son sanin matsayin wannan auren naku..!!” Ta k’arashe cikeda kulawa..
Wai ance ba’a San Sarki da fad’uwan gaba ba sannan ba’a Sarki rago amma shikam tabbas wannan tambaya da mahaifiyarsa tai masa ya d’auresa gaba d’aya had’ida haifar masa da fad’uwan gaba wani na bin wani...!
D’an gyaran murya yai yace “Ummi dama akwai wani alfarma da nake so..!”
“Alfarma kuma Saraki..?!” Ta nanata a hankali tana mai dubansa...
SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*
*78*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Kafin Mahmood yakaiga furta wani kalma amintacciyar Hadimar Gimbiya Turai ta nemi izinin shigowa, saida ta duk’a cikeda risinawa ta gaida Yarima da mahaifiyarsa kana tace “Allah shi baka yawan rai Barde yana k’ofa yace a sanar dakai isowan Turaki..”
Mahmood ya jinjina kai a hankali alamun amsawa, Ta kuma risinawa ta nemi izinin fita...
Maidoda dubansa ga mahaifiyarsa yai kaman zai magana sai ta katsesa da fad’in.. “Yanayin dana ganka ciki Allah yasa lafiya...? Ina saurarenka wane alfarma kake magana..?”
Shiru ne ya d’an biyo baya kafin yai gyaran murya kad’an yace “Kan batun d’iyata Zahra ce... Inaso ki bani lokaci kad’an, nayi alk’awarin zanzo miki da bayanin komai a dunk’ule..”
Maganan Muhibbah suke ba Zahra ba, amma da alama so yake ya kawar da zancen shiyasa ya kawo batun Zahra, shiru ne ya ratsa tsakani kana ta jinjina kai tace “Ba damuwa, Allah ya kaimu lokacin... Kaci karin kumallo ne..?” Ta tambaya tana dubansa cikeda kulawa..
Wani irin sanyi mai gauraye da rahama yakeji cikin zuciyarsa, tinda yake da Giwa bata tab’a tambayarsa lafiyarsa ba, yunwarsa ko k’ishin ruwansa damuwarta kawai ya cika mata burinta ya d’ale Karagar mulki... Yau ga mahaifiyarsa Ta asali tana kula dashi irin yanda akema k’aramin yaro Dukda yawan shekarunsa..
Ya jinjina kai a hankali yace “Naci Dibino da ruwan shayi kafin na shigo..”
Kanta a k’asa irin kunyar nan da akewa yaran fari ta murmusa domin kuwa ba kowa ya tuno mata ba face Mahaifinsa, hakan yakeyi wasu lokuta.. “Ka zama Bak’on Buzu da gaske kenan..” Ta fad’i murmushin bai bar saman fuskarta ba...
Shima d’in d’an Murmusawa yai kad’an yana mai k’ok’arin mik’ewa
Ya risina kad’an yace “Na barki lafiya Rankidad’e..!” Harda ‘yar d’aga babban yatsa yai mata alamun jinjina... Sai yana tuno mata da lokutan baya lokacin tana can masarautarsu kafin tayi aure... Hak’ik’a lokaci yayi da zasu waiwayi gida...
**
A parlornsa ya tadda Turaki yana jiran k’arasowarsa... Bayan sun gaisa Turaki yai gyaran murya yace “Wai lafiya ka d’add’agoni da sassafen nan... Kodai Gimbiya turned Rankaidad’e down ne..” Ya k’arashe cikin sigan wasa..
Mahmood yai masa wani duba da gefen idanu had’ida girgiza kai, shidai Turaki ba’a rabasa da jin baki, ba tareda ya furta komai ba ya nufi upstairs.. Jim kad’an ya dawo rik’eda sealed ledoji guda biyu a hannunsa, ya mik’awa Turaki yace “Gwajin k’wayar halittar samples d’in nan nake so... If possible kar ya shige cikin satin nan kafin ayi nad’in sarautar nan...”
Turaki ya dubesa da mamaki yace “DNA test your Highness..? Samples d’in su Yazeed ne ko kuwa na su waye..?”
Fuzar da huci yai kad’an ba tareda yace komai ba saima juya ledojin yake a hannunsa wanda d’aya toothbrush d’in Zahra ne ciki d’aya kuma sumar Muhibbah ne da ya tsinko jiya akanta a ciki...
Murmusawa Turaki yai yace “Mahmoodu hadari sa gabanka yanda kake so.. Tambihi gagari fasahar yaro... Idan tayi tsami dai zata fito Fada Sank’ira ya mana shela..”
Murmusawa yai kad’an wannan karon suna duban juna su duka biyun sanda Turaki yasa hannu ya amsa...
A hankali ya furta “Thank you..”
Murmusawa kurum Turaki yai had’ida furta “An gama Rankaidad’e.. Zanyi k’ok’ari na tabbata an samu within the week..”
Mahmood ya jinjina masa kai, har zai fice ya dawo da baya yace “Aff kaga na mance Rankaidad’e.. Tare muke da Dr Ansar zai shigo yai maka sallama idan anyi masa izini, sannan a bashi dama yayi sallama da Gimbiya Muhibbah, yau yake son komawa garinsu...”
Take ya had’e rai sosai yana duban Turaki k’asa k’asa, kaman wanda baison magana ya soma fad’in “How Many times do I have to tell you.. I don’t trust that Dr, especially around my wife..!”
Turaki ya d’anyi jim kansa a k’asa yake furta “A dai duba lamarin Rankaidad’e.. A basa wannan damar duba da matsayin da ahalinsa kedashi wajen Muhibbah.”
Ya tsare Turaki da idanu na wasu dak’ik’ai kana yakai dubansa gefe, a hankali ya jinjina kansa yana mai furtawa da k’yar “Send him in..”
Turaki ya murmusa yana duban Mahmood d’in “Godiya yake Rankaidad’e..” Ya k’arashe yana mai d’ago masa babban yatsarsa guda alamun jinjina...
Bai kuma bi takan Turaki ba ya k’arasa saman kujerarsa yai zama irinta masu mulki yana jiran shigowar Ansar...
Kan Ansar a k’asa ya shigo Barde na biyedashi yana kod’a Sarki Mahmood mai jiran nad’i , Ansar ya k’arasa ya zauna saman Darduman dake gaban Mahmood had’ida masa gaisuwa irinta masu mulki... Da kai kurum Mahmood ke amsawa yana karantar Ansar d’in da idanu, sam shi bai yarda dashi ba...
Barde ne Ke amsa gaisuwar da fad’in “Sarki ya amsa maka Likita Bokan Turai.. Jaaa zamanin Sarkin Sarakuna...”
Ansar yaci gaba da furta “Godiya nake Rankaidad’e.. Akan hanya nake yau in sha Allah zan koma gida shine nace b’arin shigo nai maku sallama.. Allah shi taimakeka..!” Yai maganan yana dunk’ule hannunsa guda had’ida mik’a jinjina ga Mahmood d’in...
Shiru ya ratsa tsakani sai sautin kirari kawai da Barde keyiwa Mahmood “D’awisu Sarkin kwalliya.. Kaga d’an jimina gagara d’aukan shaho..! Girgije sa gabanka yanda kake so.. Dogon Sarki mai dogon zamani.. Allah shi jaa zamaninka...”
Ansar ya zaci Mahmood d’in bazai kuma fad’in wata kalma ba har saida ya d’an d’ago ya dubesa.. Ya soma k’ok’arin mik’ewa yana furta “Idan Sarki yamin izini ni zan wuce...Na barku lafiya your Highness..”
Yai maganan yana mai risinawa...
Ya kuma jinjina masa kai ba tareda ya furta koda kalma guda ba...
Barde ya soma k’ok’arin rakiyawa Ansar yana furta “Sarki ya maka izini Likita..”
Gyaran Muryar Mahmood da suka sinkayo ne yasasu dakatawa Barde na k’ok’arin k’arasowa cikin d’an gudu gudu ya zube gaban Sarkin...
Murya can k’asa yake furtawa Barde a zab’awa Ansar doki mai kyau cikin Bargan Fada sannan ai masa rakiya wajen Gimbiya Muhibbah..
Barde ya jinjina masa yana mai furta “An gama Rankaidad’e.. Godiya yake..”
Ansar Wanda a gabansa akai maganan amma tsaban mulki ba’ayi direct to shi ba sai ya dawo da baya ya risina yana fad’in “Godiya nake Rankaidad’e.. Amma da dai an bar dokin..”
Baikai aya ba Barde ya katsesa da fad’in “Hattara Bokan Turai, Sarki baya kyauta a dawo masa..”
Ansar ya had’iyi abinda ya tsaya masa a mak’oshi... “Godiya nake Rankaidad’e..!” Ya fad’i tareda jinjina..
Har sun soma tafiya suka sinkayo muryarsa mai amo ya amsa illahirin parlorn cikin yin gyaran murya, babu shiri Barde ya koma da baya ya zube..
Mahmood ya d’ago yatsarsa yayi alama guda d’aya biyu zuwa uku, kaman wanda baison magana ya furta “Minti uku kacal..”
Barde ya jinjina kai yana mai furta “An gama Rankaidad’e...”
Barde ne kawai ya fahimci Sarki na nufin minti uku kacal aka baiwa Ansar yayi sallama da Gimbiya... Shikam Ansar d’in bai fahimci komai ba dan ba wani gane yaren sarakunan yake ba...
**
Tsaf Ta shirya cikin wani lallausan leshi da akai masa d’inkin riga da skirt, sosai ya amsheta, Ta jima tana duban kanta jikin full-length mirror abubuwa da dama suna zuwa zuciyarta, kaman anyi ruwa an d’auke Wai yau babu su Giwa cikin Masarautar.. Allah kenan Buwayi gagara misali... Ta tako a hankali tana mai tuna daren jiya da abinda suka faru, zama tai bakin gado tana mai kuma nanata lamarin cikin zuciyarta..Tana nan a haka Hadimarta ta nemi izinin shigowa kana ta shigo kanta a k’Asa bayan Muhibbar ta mata izini..
“Ki gafarceni Rankidad’e, Barde yace in sanar dake kinada bak’o a waje...”
“Bak’o.!” Ta nanata a hankali tana tunanin waye ma Barden.. Ta dubi Hadimar kad’an tace “Wanene Barde..?”
Hadimar ta kuma risinawa tace “Amintaccen Hadimin Sarki Mahmood mai jiran nad’i kenan Allah shi taimakeki..”
Muhibbah tai shiru kaman mai tunani sai kuma ta jinjina kai a hankali tace “Kije ki tambayo ko wanene bak’on..”
Hadimar ta kuma jinjina kai had’ida bin umarnin uwargijiyarta..
Jim kad’an ta dawo ta risina tace “Allah shi taimakeki kaman yanda Barde ya sanar dani, Maimartaba Sarki Mahmood ne ya turosa..”
Tai still tana duban Hadimar, jinjin kai tai a hankali tace “Kije ki sanar dashi ina tafe..”
Hadimar ta amsa cikeda girmamawa kana ta fice...
lokaci guda Muhibbah Ta mik’e had’ida janyo alkyabbarta ta rufa bisa kanta, A parlor Ta tadda Hadimar tana jiran fitowarta lokaci guda tai mata jagoranci zuwa wani madaidaicin parlor a k’asa...
Ga tsananin mamakinta Ansar ta gani, ta saki murmushi a hankali shid’inma murmushin ne saman fuskarsa...
Yana hangota ya mik’e tsaye yana jin zuciyarsa na fuzga kaman zai fasa k’irjinsa ya fito waje...
Tana K’arasowa ya silale k’asa hm had’ida d’ago babbar yatsarsa alamun jinjina gareta “Rankidad’e..!”
Dariya yaso bata amma sai ta murmusa kawai ta k’araso ta zauna saman kujera tana mai furta “Ka tashi ka zauna idan ba so kake nima na duk’a gaba gareka ba..”
Ya mik’e da sauri yana murmushi ya koma saman kujera ya zauna had’ida furta “Wane ni Gimbiya Ta zauna k’asa gabana.. Ai sai kisa na koma garinmu da k’afa guda..”
Nan ma murmushi kawai tai wanda da gani na k’arfin hali ne..
Shiru ya ratsa tsakani zukatansu saiko bugun zukatansu, gaba d’aya sai tana jin wane irin nauyinsa..
Muryarsa Ta sinkayo yana furta “Cant I talk to my sister in private..?” Yai maganar yana duban Hadimar dake tsaye gefen kujerar da Muhibbah Ke zaune bisa kanta a k’asa...
D’agowa Muhibbah tai Ta dubi Hadimar tai mata alama da hannu kan cewa Ta fice daga parlorn.. Hadimar ta risina tayi yanda Muhibbah ta umarta...
Shiru ya d’an ratsa tsakani kana Ansar yai gyaran murya ya soma fad’in “I know by now kinada masaniyar cewa ba’a d’aura mana aure ba..”
Ta d’an d’ago a d’an firgice tana dubansa, Ansar ya jinjina mata kai alamun Tabbatarwa yace “Muhibbah ba’a d’aura mana aure ba kaman yanda mukaci buri.. Sun mana fin k’arfi... Sun rabamu da k’arfin mulki da dukiya.. Ko Kinsan wanene ya aureki..?” Yai tambayar cikin rawar murya yana duban Muhibbah da tuni k’walls sun ciko idanunta... Ansar yaci gaba da furta “Muhibbah Yarima Mahmood shine ya aureki... Kuma ba don yana k’aunarki ba sai don yayi amfani dake ki zamto bakin zaren da zai warware masa duk wani k’ulli dake cikin Masarautar nan... Hibbah Mahmood sayenki yayi da mak’udan kud’ad’e daga wajen Yawale... Nasan shid’in d’an uwanki ne... Nasan bai kamata naita fad’in kalamai irin haka ba, but is the truth Muhibbah... Shid’in ba Auren soyayya yayi dake ba.. Satoki yayi daga wajen masoyinki na asali..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Muhibbah dake jin batun tamkar wani sauk’an aradu duban Ansar take hawaye na gangaro mata “Kace ya auroni ne domin na zamto bakin zare a garesa..?”
Ansar ya jinjina kai yace “K’warai domin yayi amfani dake ki warware masa duk wani k’ullin dake cikin Masarautar nan, Don’t you find it strange yanda yazo ya ajeki ba tareda wani bayani ba, sannan saida aka drugging d’inki aka kawoki cikin Masarautar nan, nima kuma akai drugging d’ina aka hanani halartar aurenmu... Mahmood da Baffah Yawale planed everything Hibbah.. Harta Mommy batasan da wannan shirin nasu ba.. Tana can hankalinta tashe da tunanin wanene mijin da aka aura miki..Hibbah Mommy bata cancanci haka ba.. None of us deserve this..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya..
Izuwa lokacin kukan da Muhibbah keyi ya k’aru, Wato wannan shine dalilin Rankaidad’e na bibiyanta, she was right sayota yayi tamkar wata baiwa ya ajiyeta babu wani bayani, shin ta ya ma za’ai mata irin wannan auren kawai dan yana basarake.. Har abada bazata aminta da wannan auren ba.. D’ago idanunta masu zuban ruwa tai tana mai jinjina kai take furta “Ina mai tabbatar maka wannan auren won’t last, ban amince ba kuma bazan tab’a amincewa ba...!”
Har cikin ransa yaji dad’in kalamanta, shawo kanta bazai masa wahala ba... Bazai bar masarautar ba har sai ya tabbata ya d’auke abinda aka sace daga garesa.. Wannan dalili shiyasa ya sauk’ar da kansa ya saye zuciyar Turaki da d’abi’u masu kyau tinda ya fahimci duk duniya babu wanda Yarima Mahmood yake d’aukar maganansa irin Turaki shiyasa ya biyo ta jikin Turaki dan ya sami amincewa e Ammar Mahmood cewa shid’in mutumin k’warai ne kuma baizo dan ya lalata aurensa ba.. Ya saki murmushi a hankali yana mai duban Muhibbah yanda take cazgan kuka mai tab’a zuciya, Ya jinjina kai a hankali kana ya soma furta “Don’t ever agree to this marriage Muhibbah..! Baffah Yawale sold you, martabanki da kimarki ya wuce a aurar dake a wulak’ance just like that...You’ve been through a lot, you deserve happiness... Ke Sarauniya ce, Martabarki ya wuce a aurar dake a wulak’ance...!”
Muryarsa ya soma rawa sanda yake ci gaba da furta “Mahmood doesn’t love you Muhibbah.. Kawai k’arfin mulki ya gwada akanki...Da ace yana sonki bazai auroki a wulak’ance ba, he kidnapped you, satoki yayi Hibbah... Na sani d’anuwanki ne but I’m sorry to say he’s just like them.. Shima d’in d’an ta’adda ne tin da sayenki yayi wajen Yawale ya kawoki nan sabida baki cikin hayyacinki.. Hibbah please don’t agree to this marriage, do it for me.. For the love we have for each other.. Muhibbah kar ki bari su k’wace min ke... I still love you, so much..!” Ya k’arashe yana mai silalowa daga saman kujera ya duk’a gwiwoyinsa gabanta had’ida had’e hannayensa biyu waje guda alamun rok’o..
Hawayene kurum Ke ziraro mata d’aya na bin d’aya... Ansar ya mata hallaci a rayuwa, kuma sud’in masoyane basu cancanci haka daga Rankaidad’e ba.. Dama dangin sayenta yayi, tayi gaskiya da tace sayota yayi tamkar Baiwa.. Kenan yajesa ya saye Yawale da kud’i ya saida masa ita... Ta yaya zai aikata haka..?! Ta yaya zai sayota tamkar wata Baiwa, dole mana ya kulleta a d’aki ya hanata fita.
Raheemah dake lab’e jikin window wani irin murmushi ne saman fuskarta, Wato abinda ya faru kenan, idan kuwa haka ne dole tayi amfani da wannan damar su had’a k’arfi da k’arfe itada wannan mutumin su raba Mahmood da Muhibbah, itama ta sami chance da zata rama abinda Mahmood d’in da Muhibbah sukai mata...
Ansar ya mik’e jiki a sanyaye yana furta “Ni zan koma Hibbah, I hope zakiyi abinda ya dace ... Ki k’wace ‘yancinki daga hannun mutumin da ya sayoki tamkar Baiwa a kasuwa..!” Yana ida fad’in haka Barde ya lek’o yana furta “Lokacinda mai Martaba ya d’ibar maka ya cika Bokan Turai...”
Ansar ya jinjina kai yana mai k’ok’arin saita kansa had’ida mik’ewa “Na barki lafiya Rankidad’e..!” Ya fad’i yana duban k’asa kana yasa kai ya fice yanda ya bar Muhibbah naci gaba da matsan hawaye zuciyarta na tsananin mata zafi...
A hanya Raheemah Ta had’uda Ansar ya fito daga Bargan dawakai ya zab’i doki mai kyau kaman yanda Mahmood yai masa kyauta...
Yai tsaye da mamaki yana duban matar data tsaya gaba garesa cikin tufafi irinta masu mulki ga Hadimarta guda tsaye bayanta...
“Lafiya..?” Ya furta yana dubanta...
Alama da hannu Raheemah taiwa Hadimar don ta basu waje...
Raheemah ta murmusa tace “Lafiya sai alkhairi..”
Shima murmusawan yai kad’an yace “Ban fahimceki ba.. Wacece ke..?”
“Call me solution to your problems..!” Tai maganar murmushi bai bar saman fuskarta ba...
Gajeren murmushi yai yace “I don’t get you..”
“Da sannu zaka fahimta tinda na kula kaima k’arfin mulki da iko aka nuna maka aka rabaka da masoyiyarka kaman yanda nima aka rabani da nawa masoyin aka aura min wanda bana so..”
Ansar ya dubeta da tsananin mamaki yace “Kina nufin yanda aka aura min wacce bana so kema haka aka miki..?”
Ta jinjina kai tace “K’warai kuwa and if you want Muhibbah back ni kad’aice zan taimakeka duk fad’in Masarautar nan..”
Yai K’uri yana dubanta sai kuma yace “How is that possible..?”
Raheemah ta murmusa kana ta mik’a masa wayar salulanta tace “Zuba digits d’inka a nan...”
Babu musu ya amsa ya hau zuba mata lambar wayan salulansa...
Ya amshi wayar bayan ya gama kana tace “Sai kaji daga gareni..” Daga haka sa kai tai Ta shige Hadimarta ta take mata baya..
Ansar yabi bayanta da kallo har ta b’ace masa cikeda mamakin makirce makirce dake cikin wannan masarauta.. Koda shike shi ina ruwansa idan dai zai samu Muhibbah ta dawo garesa, akan son da yakewa Muhibbah babu abinda bazai ba don kawai ta dawo garesa.. Bazai tab’a bari a rabasu haka kurum ba... Ya k’arashe yana mai jin zafin Wai Mahmood da gaske ya aure masa Muhibbarsa... Sabida tsaban an rainasa ma bacci akasashi yayi kafin akai masa wannan rainin wayon.. Yai k’wafa yana mai ayyanawa bazai tab’a hutawa ba har sai ya tabbata auren Muhibbah da Mahmood ya lalace..
**
A can b’angaren Ja’afar kuwa tun bayan da suka baro Bargan dawakai shida Baba Nomau ya nufo b’angaren Yazeed, tsaye yayi yana k’arema sashen kallo yana tuna abubuwa da na wulak’anci da tozarci da ya fuskanta daga wajen wad’annan ahali... A hankali ya soma takowa cikin sashen hannayensa hard’e ta baya yana mai kuma k’arema sashen kallo... Daga k’ofar Parlorn ya tsaya yana duban Yazeed dake zaune dirshan a k’asa hotonsa wanda da ka shigo parlorn zai maka marhaban cikin shiga irinta mulki aje gabansa ya tasa hoton gaba yana cazgan kuka kaman wani k’aramin yaro ga wasu Kuyangi tsartsaye gefensa suna bin umarnin da yake basu ba don sunso ba, harta abinci a baki suka basa da alama...
Suna ganin shigowar Ja’afar suka rirrisina suna kwasan gaisuwa.. J’afar ya amsa masu yana mai jinjina kai... Alama yaima Kuyangin da hannu kan cewa Su fice, babu shiri suka fice kawunansu gaba d’aya a k’asa...
Yai tsaye gaban Yazeed har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya... Daga k’afafu Yazeed ke duban Ja’afar har izuwa Fuskarsa take yaji kaman an luma masa mashi a k’ahon zuciya, yai saurin rintse idanunsa dan bazai iya jure ganin wannan kayan bugawar zuciyar ba..
Ubandoma dake biyeda Ja’afar ganin yayi shiru yana k’arewa Yazeed d’in kallo ya sanyashi fad’in “Rankaidad’e mai kake so ayi dashi, a fattatakesa daga cikin Masarauta ne ko kuwa a fatattakesa ya koma can yanda aka fito.. Ma’ana b’angaren Bauta..!”
Hannu yasa ya d’an sosa kunnensa guda kana yace “Kasan idan mutum nada zuciyar musulunci duk yanda yaso rama mugunta bazai jura ba.. Kuma wad’annan ahali duk abinda zamu masu bazamu rama zalunci da sukaima Al’umma ba, ko a haka Sun amshi sakamakon duniya.. Right Yazeed..!” Ya k’arashe yana mai duban Yazeed dake zaune dirshan gabansa..
Yazeed bai iya amsawa ba saima dad’a kifa kansa da yayi...
Ubandoma ya kai masa shura da k’afa yana mai furta “Hattara D’an Bayi..! Tashi ka duk’a da kyau ka amsa Yarima... Yarima baya jiran amsa daga wajen k’ask’antacce Bawa irinka...”
Cikin tsananin huci Yazeed yake furta “I rather die akan na risina gaban wanda yake a matsayin Bawa na a baya...!” Ya k’arashe Wasu irin hawayen d’acin rai suna gangaro
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 65