gaban Ubangidanta...?!”
Jamal ya kuma murmusawa yace “So nake yau ki zamto Sarauniya cikin d’akin nan... Sabida ke kikeda mulkin wannan d’akin a yau.. Na tabbata zakiso kiji yanda Iyayen gidanki sukeji koda na rana guda ne..!”
Jakadiya ta had’iyi miyau da k’yar tana washe baki wanda yafi kama da yak’e “Toh Rankidad’e idan kace haka.. Ni umarninka nake bi...!”
Jakadiya ta isa saman kujerar ta zauna tana mai daidaita saman kujerar a hankali lokaci guda tana mai ci gaba da wage baki yawa an mata alk’awarin kujerar Makkah... Sai bud’e kafad’a take saman kujerar tana jinta tamkar Sarauniya...
Yai tsaye jikin sandar crutches d’insa daga nan yanda yake tsaye yana dubanta, murmushi bai bar saman fuskarsa ba...
“Ya kikaji Jakadiya..? Ya kikaji zak’in ‘yanci da Mulki..?!”
Jakadiya tace “Ba’a magana Rankaidad’e... Duk yanda zanso fasaltawa bazan iya ba..!”
Ya jinjina kai a hankali kana ya isa gefe ya d’auko wata igiya... Itadai Jakadiya duk bata ankare ba sai juyi take saman kujera tana jinta yawa Sarauniya.... Bata ankara ba sai ganin Jamal tai duk’e gabanta...
Cikin kid’ima take furta “Allah shi taimakeka kai min rai ka tashi a gabana kar wani ya shigo ya ganmu haka tsire kaina za’ai... Kai min rai ka tashi Rankaidad’e...!!”
Duk surutun da take Jamal Bai tankata ba har saida ya ida abinda yake tsaf kana ya dafa sandarsa ya mik’e yana sakin murmushi...
Jakadiya ta yunk’ura zata tashi amma mai..? Saiji tai k’afunfunta gaba d’aya an d’aure jikin kujerar...
Ta d’ago a firgice tana duban Jamal da ya koma tamkar bai tab’a dariya ba...
Murya na rawa take furta “Rankaidad’e... D’aureni Kai.. Rankaidad’e idan wani laifi nayi ka yafeni, tuba nake..!!”
“Karki damu yau Sarauniya kike... Mulki zaki baza amma a saman kujerar nan...” Ya ida maganar yana mai d’aure hannayenta biyu jikin kujerar...
Izuwa lokacin hanjin cikin Jakadiya sun soma kad’awa... Taga irin azaban da wannan mahaukacin yayiwa Jafar har suka zaci Jafar mutuwa yayi tsawon shekara guda wannan mugun ya kullesa yana azabtar dashi...bata fata ya kwatanta hakan da ita...
Jiki na matuk’ar rawa take furta “Rankaidad’e... Wayyo ni Talle... Wayyo Allah na... Rankaidad’e kamin rai na tuba...!!” Yanda Ta rikice gaba d’aya sai ta zamto Tamkar mai laifi abinka da wacce bata k’ulla gaskiya da alkhairi tsawon rayuwarta...
Gabanta ya k’araso bai daina sakin murmushin ba yace “Relax Jakadiya, ke ai yau Sarauniya ce... Har yanzu sai wasan kwaikwayon muke...!!”
Jin haka yasa Jakadiya Ta d’an sauk’e ajiyan zuciya kad’an kana ta saki murmushi tace “Rankaidad’e ai ka bani tsoro ne...!!”
Jamal ya tsareta da idanu yana mai ci gaba da karantarta, lokaci guda ya gyara tsayuwarsa jikin crutches d’insa kana yace “Jakadiya a matsayinki na Sarauniya saman karagarki wani hukunci zaki yanke wa bawan da yaci amanarki...?!”
Jakadiya Ta jinjina kai tace “Hukunci mai tsauri, hukuncin da nan gaba bazai sake tunanin cin amanan bawa d’an uwansa ba balle Ubangidansa...!!”
Jamal ya murmusa yace “Da kyau Jakadiya... Naji dad’in wannan shawari naki...!”
Ya isa jikin ‘yar k’aramar jakan ya bud’e... Equipments d’in da ake operation ma dabba sune a jejjere cikin jakan....
Jakadiya ta ware idanu tana kallan k’araffan dake shirye cikin wannan ‘yar jaka.... Wata k’usa ya d’auko mai kamada noti ya k’araso kusan Jakadiya yana mai sakin murmushi yake furta “Nasan zaki tuna a zamanin da can baya kakanninku an masu huji a labb’an bakunansu yanda ake gark’ame bakunan nasu da kwad’o koh...?!”
Jikin Jakadiya ya d’auki rawa, Ta shiga rawar d’ari tana mai furta “Rankaidad’e Yarima amin rai... Tuba nake...! Wllhi bani k’aunar zama Sarauniya... K’arya nake Rankaidad’e... Kaji k’aina kada ka azabtar dani... Wayyo ni Talle k’arshena yazo....!!” Ta k’arashe cikin murya irinta mai kuka...
Tsawa ya daka mata yace tai masa shiru...! Jakadiya ta had’iyi kukanta tana mai rintse idanunta had’ida jinjina kai alamun tayi shiru....
**
A wane irin hautsine ya shigo ya tadda Ubangidan nasa... Mahmood ya mik’e daga kishingid’en da yake yana mamakin yanda Barde ya fad’o kansa haka...
Har k’asa ya risina yana fidda haki yake fad’in “Tuba nake Allah shi baka yawan rai... A gafarceni...!!”
Mahmood yace “Lafiya ka shigo haka nan...?!”
“A gafarceni Rankaidad’e kira na samu daga matuk’i....!!”
Sosai wannan karon ya kuma gyara zamansa yanda Barde yaci gaba da fad’in “Matuk’i ya nemi Gimbiya Zahrau ya rasata...!!”
Baikai aya ba sak’o ya shigo cikin wayar Salulan Mahmood d’in wanda ba kowa Keda layin ba sai amintattun mutane...
Bai kuma tsayawa sauraren Barde ba sai duba Sak’on da yake
_We’ve your daughter your Highness, and if you want to see her alive you need to do exactly as we say.._
Cikin sauri ya shiga k’ok’arin dialing layin amma bata shiga... Wani sak’on ya kuma shigo masa
_Don’t try anything foolish your Highness... Don’t involve cops, Kai even watchmen na cikin Fada do not involve them.... Kai d’aya mukeso kazo.._
Take aka rubuto masa address d’in location d’in da ake so yajesa....
Barde na gani Ubangidan nasa ya mik’e ya fice ba tareda yacedashi komai ba...
Mota ya shige yana k’ok’arin dialing layin Zahra amma bai shiga... Cikin tsananin k’unan zuciya yake tuk’a motar yana falfala gudu saman kwalta...
Bai zarce ko ina ba sai k’ofan gidan Turaki...
Turaki na ganin wayar aminin nasa ya saki murmushi a hankali dan yasan dole Mahmood d’in ya nemesa, d’aya bazai Iya babu d’aya ba haka abotansu yake... Kaman bazai d’aga ba sai kuma ya d’aga shima babu wani walwala taredashi ya gaida Rankaidad’e...
Daga d’aya b’angaren Mahmood yace “Ka fito Ina jiranka waje..!”
Daga haka bai kuma cewa komai ba saima katse kiran da yai...
Turaki ya tsaya juya wayar cikeda mamaki, yana nanata abinda Mahmood d’in ya fad’i masa... Bai ida tinanin ba ya soma jiyo sautin horn alamun dai da gaske yana k’ofar gidansa...
Girgiza kai kurum Turaki yai ya mik’e ya nufo waje...
Yana K’arasowa Mahmood da tuni ya hangosa Ta mirror ya zuge glass d’in “Get in the car..!”
Turaki yai masa k’uri cikeda mamaki lokaci guda ya girgiza kai, lokaci guda kuma ya d’an saki murmushi yace “Rankaidad’e nasan gaba d’aya fad’in garin nan talakawan ka ne amma bazakazo har k’ofan gidana ka nuna min iko ba..!”
Mahmood ya kaikaito yanai masa wane irin duba lokaci guda ya bud’e security lock yana mai furta “We don’t have much time... Please get in..!”
Yanayin da yai maganan yasa jikin Turaki d’anyin sanyi, sai kuma ya gyara tsayuwarsa yace “I’m sorry your Highness but I’m not going anywhere har sai kamin bayanin ina zamuje...!”
Izuwa lokacin Mahmood ya soma k’osawa da taurin kan Turaki.... Bai amsasa ba sai mik’a masa wayar da yayi daidai kan sak’on da aka turo masa...
Turaki ya karance, lokaci guda ya d’ago yana duban Mahmood d’in a d’an firgice... Babu shiri ya finciki marfin motar ya shige, cikin ‘yar daburcewa yake furta “Your Highness bazamu biye tasu ba... We need to inform the authority right away..!”
Katsesa Mahmood yai da fad’in “No Turaki hukuma bazata sani ba... can’t you see my daughter’s life is at stake here...! What if they did something to her... No bazamu kira kowa ba... We do exactly as they say..!!”
Turaki ya jinjina kai a hankali yace “Toh mai suke buk’ata... Did they ask for Ransom..?!”
Girgiza masa kai yai alamun a’a sai kuma yace “Ina zaton ba kud’i suke buk’ata ba nid’in suke buk’ata... Kuma duk bazai wuce akan wannan banzan sarautar ba... Mai yuwa rayuwata suke nema domin su cimma burinsu na d’akewa Karagar nan... Turaki son duniya da Mulki ba abinda ba zaisa mutane suyi ba...!”
Turaki ya jinjina kai yace “Tabbas it might be a trap... Rayuwarka suke buk’ata ba kud’in Fansa ba... Rankaidad’e shisa nace muyi abin in the right way... Let’s call the cops right away...!”
Saurin dakatar dashi Mahmood yai da fad’in “Have you ever lost your loved one...? Turaki rayuwar d’iyata muke magana a nan... No one must know about this... I’ll submit myself to them idan hakan zaisa su sakar min d’iyata..!!” Ya k’arashe yana mai sakin huci...
Turaki ya jinjina kai cikeda tausayin abokin nasa yace “I’m sorry your Highness, I understand where you’re coming from... Amma abinda nakeso yanzu muyi before mu confronting kidnappers d’in let’s check the hospital first... Maybe sunga wani abu... Ko ma su nuna mana CCTV footage d’insu watak’ila mu samu wani clue gameda kidnappers d’in kuma shima driver d’in da ya kaita dole Mu bincikesa tinda kace tareda Jakadiya ka had’asu suka fita..!”
Mahmood ya jinjina kai ba tareda yace komai ba... Ganin irin driving d’in da yake yasa Turaki karb’an motar yaci gaba da tuk’asu...
Koda sukaje asibiti suka tadda driver d’in duk a rikice nan yake sanar dasu Zahra ita kad’ai ta fito ba tareda rakiyar Jakadiya ba, sannan masu kula da majinyata na cikin asibitin sun tabbatar masu Zahra ta shiga wajen Fu’ad tareda wata mace... Saidai babu wanda yasan macen da Zahra Ta shigo da ita amma kam tabbas ba Jakadiya bace... Koda suka shiga wajen Fu’ad suka tambayesa ko zai iya tuna matar da Zahra Ta shigo tareda ita Fu’ad d’in bai iya cewa komai ba sabida halinda yake ciki dukda cewa gashi kaman so yake ya masu magana... Mahmood ya matso jikin gadon Fu’ad ya d’an rank’wafo kad’an yana kuma tambayarsa cikin tsanaki “Fu’ad try to remember something... Who’s that woman..? Please Fu’ad your niece’s life is in danger... Please try to remember something..!!”
Kallonsa kurum Fu’ad yake hawaye na gangaro masa yana son yin magana babu hali.. Lokaci guda ya shiga buge buge yana tak’urewa waje guda... Babu shiri nurses d’in suka k’araso suna rok’on Mahmood ya fice sabida jikin Fu’ad d’in da ya kuma rikicewa...
Turaki yai k’ok’arin janyo Mahmood d’in suka fice waje, shi kansa Turaki tsananin tausayin ahalin Mahmood ke d’awainiya dashi....
Suna fitowa daga wajen Fu’ad Mahmood ya buk’aci a nuna masu CCTV footage na asibtin saidai akai rashin sa’a Cameras d’insu gaba d’aya basa aiki...
Huci kurum yake sakarwa yana fad’ida Turaki “You see... K’asarmun kenan, komai babu maintenance babu management mai kyau... Ba dole ta’addanci yayi yawa ba..!!”
Turaki ya jinjina kai yace “Hakane Rankaidad’e saidai muyi addu’an Allah ya kawo mana sauk’i... Shisa muke so mu samu shuwagabanni ire irenku wanda zasu kawo mana sauyi... Ka bar batun komawa Spain d’in nan ka karb’i ragamar mulkin Masarautarmu..!”
Bai tsaya sauraren Turaki ba ya nufi mota.. Tuni Turakin ya take masa baya, daidai sanda sak’o ya kuma shigowa Mahmood cewa idan yana son sake ganin d’iyarsa da rai yazo address d’in da aka turo masa nan da mintoci da basu gaza arb’ain ba idan kuma ba haka ba ya shirya d’aukan gawar d’iyarsa... Time ya soma reading tik tok..!!
Jifa da wayar yai ya finciki d’an makullin hannun Turaki ya shige Mota ba tareda ya kuma bi takan Turakin ba... Turaki na k’ok’arin tsaidashi inaa tuni ya kwali motar ya fice daga cikin asibitin... Haka Turaki yai tsaye yana duban motar har ya fice... Yana ficewa Turaki yai saurin ficewa daga asibitin ya tari motar haya dukda baida tabbacin location d’in da Mahmood ya nufa....
SameenaAleeyou 📚*MUHIBBAH*
*57*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Mamaki ne ya cikasa ganin motar Yazeed pake farfajiyan gidan da aka tura masa adireshin... Toh meke faruwa..? Badai tsanar da Yazeed yai masa har ya kawo wannan munzanin ya nemi cutar da d’iyarsa ba... Kai Yazeed bazai haka ba, dikda cewa yasan baida hali akasarin lokuta amma zai wuya ace zai aikata abu makamancin wannan... Jiki babu laka Mahmood yaci gaba da takowa yana k’arema gidan kallo har ya iso jikin k’ofar da zai sadaka da asalin cikin gidan... Shewan mutane mace da namiji da ya soma saurare ne ya sanyasa d’an dakatawa kad’an daga jikin k’atoton window na parlorn...
“Gaskiya zanyi kewarki... Wai haka kika k’ara sugar, tab lallai da bakizo ba dana tapka babban asara dan wannan garan tsaf Mahmood ne zai kwashe... Amma ko yanzu saidai ya sami saurana..!” Ya k’arashe shu’umin murmushin nan nasa saman fuskarsa...
Raheema ta rausayar da idanu tace “Ai kama kasan nid’in bata wasa bace na d’ara matarka sau babu iyaka, kuma duk cikin matan da kake Mu’amala dasu babu wacce takaini... Aini bari kaji Yazeed duk d’ah namijin da ya riga ya shiga hannuna toh fah zai wuya ya iya manceni... Haka nan nake da tsayuwa a zuciya, ko shi Mahmood d’in da yake wani jin kansa yana ganin ba auren soyayya zai dani ba auren jeka nayika ne kawai to save his daughter da zaran ya shigo hannuna Ina mai tabbatar maka zai sauk’e wannan jin kan nasa ya susuce akaina... Daga nan sai yanda nayi dashi nayi da d’iyarsa, kai k’arewa wannan shegiyar d’iyar tasa da ya samota Ta gurb’ataccen hanya sai na rabasa da ita dan bana buk’atan bastard child d’insa a gidana... ‘Ya’yan sunnah zan haifa masa...!!”
Yazeed bai daina shafa hab’arsa ba idanu a kannare yake dubanta, lokaci guda yaci gaba da furta “Allah Sa Ki jure rashina kusanki dan Yaya na bazai iya dake kaman yanda ni na iya dake ba...!”
Raheema Ta kuma murmusawa tace “Haka kake tunani.. Ai ba’a sanin maci tuwo sai miya ya k’are... Kai ko a ido kasan Yarimana Gwarzo ne ba rago ba... Wani abin ma sai mun d’aga zuwa k’asar Spain na kashesa da kissa da makirci tinda na kula asiri bai tasiri akansa... Da kissa zalla zan rabasa da wannan shegiyar d’iyar tasa muci soyayyarmu a k’asar Spain...!”
Yazeed ya kuma murmusawa yace “Toh Nidai kar a cikani da zancen Mahmood, tinda yau d’in gaba d’aya nawa ne..!” Ya k’arashe yana mai kuma janyota kusansa...
Raheema na murmushi take furta “Karka damu ai yau d’in gaba d’aya takace dan ko masarauta babu wanda zai San nazo... Till down za...!!” Bai juri k’arasa sauraren maganganun nasu ba yai saurin juyowa idanunsa na kuma kad’awa... Saidai d’aga idanun da zai yaga Zuhra tsaye tana hawaye...
Mahmood ya dubeta da mamaki sai kuma ya juyo yana duban k’ofan parlorn, bazaiso ta shiga taga wannan mummunan cin amana da k’awarta da mijinta sukai mata ba...
Ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali dan baisan da mai zai soma ma Zuhra ba...
Zuhra na hawaye take girgiza bata tsaya sauraren Mahmood dake k’ok’arin dakatar da ita ba ta finciki k’ofar parlorn....
A wane irin firgice Raheema ta mik’e zuciyarta na kuma tsinkewa...
Hawaye na gangaro mata take dubansu... Take Raheema tai saurin kame bakinta had’ida d’aura hannu aka... Lokaci guda ta silale saman gwiwoyinta tana duban Zuhra dake zuban hawaye... “Zuzu wllhi ba yin kaina bane... Zuzu dan Allah Ki yafe min...!!”
Yazeed ne ya katseta da fad’in “Ke dallah shut up... Kar Ki ishe mutane... Uban mai akai mata...?!”
Ya dubi Zuhra dake tsaye wajen idanunta sun kad’a sunyi jazir yace “Ke Uban mai ya kawoki wajen nan..? How did you get here..? Da izinin wama kika fito...?! Zaki bud’e baki kiyi magana ne Ko sai na K’araso wajen na faffalla miki mari..!!”
Cikin tsananin huci Zuhra Ke furta “Try it please...! Ka kwatanta marina Yazeed, yau ni kuma zan nuna maka jinin mulki da sarauta na nan na Yawo jikina... Azzalumi macuci maci amana... Ka cuceni ka zalunci yaranmu tirr ace kaine mahaifin ‘ya’yana... Nayi nadaman had’a zuri’a dakai, amma ka saka a ranka daga yau ni Zuhra na gama zaman aure dakai... Kuma ka jira hukuncin da zan yanke..!!!”
Tana ida fad’in haka tasa kai zata juya... Raheema tai saurin rarrafawa ta kamo bakin zaninta... “Aminiyata dan Allah Ki yafe min, wllhi sharrin shaid’an ne kuma tilasta min Yazeed yayi... Wllhi ba halina bane... Dan Allah karki bari Yarima Mahmood yaji wannan batu nayi imani fasa aurena zai... Dan Allah Zuhra kimin rai kimin wannan alfarmar kinji k’awata...!”
“K’awa...?!” Zuhra Ta nanata tana dubanta, lokaci guda tai murmushi wanda da gani kasan na takaici ne “Amma lallai na yarda Raheema bakida kunya, kuma baki gaji kunya ba... Anya Ke jinin babban Gida ce... Babu Gimbiya ko Sarauniya da zata watsar da kanta taci mutuncin kanta kaman yanda kikayi... Wllhi ko a haka kin shafawa Masarautarku b’ak’in fenti wanda zai wuya ya shafe.. Bani kika cuta ba Raheema..! Kanki kika cuta.. Kin cuci rayuwarki, kin kwab’ar da duk wani daraja da k’ima da Allah yayi miki a matsayinki na d’iya mace... Kin yaye Hijabin mutunci da Allah ya halicceki da ita... Kin..!”
Yazeed ya katseta da fad’in “Idan kin gama wa’azin naki ki fice kuma kije ki jirani a gida... Ina nan zuwa dan wllhi kinji na rantse sai na hukuntaki..!!”
Zuhra ta d’ago tana watsa masa duban k’yama... Lokaci guda Ta murmusa tace “Zakasha mamaki irin wanda baka tab’a sha ba Yazeed..!!”
Daga haka fincikan mayafinta tai daga hannun Raheema had’ida shureta da k’afarta tasa kai Ta fice abinta... Zuciyarta na tsananin mata zogi...
Tana fitowa ta tadda babu Mahmood alamun ya tafi... Mota ta shige ta kifa kanta tana kuka sosai... Driver d’in da Hadimarta dake jiranta daga nan waje cikin mota abin sai ya masu wane iri ganin shugabar tasu tana kuka..
Hadimar tata ta umarci driver d’in ya fice daga cikin motan ya d’an basu waje taji damuwar Uwargijiyar tata...
Driver yayi yanda tace
Hadimar ta d’an risina tace “Rankidad’e kuka bai kamaci kyakkyawar Gimbiya irinki ba... Ko akwai abinda zan iyayi na tsaida hawayen shugabata masu tsada su daina zuba..?!”
Zuhra ta d’ago Tai k’ok’arin saita kanta “Babu komai Hindu kiyi magana ma driver ya shigo mu koma masarauta...!”
Baiwar data kira da Hindu ta dan jinjina kai sai kuma tace “Ki gafarceni ya Shugabata, Kodai wani abin tashin hankalin kika gani cikin gidan nan..?!”
D’an daka mata tsawa tai da fad’in “Nace miki babu komai Hindu, Ki kirawo Driver mu tafi... Bana son gardama..!!”
Hindu Ta risina tace “Tuba nake Rankidad’e... Kimin aikin gafara..!!” Ta k’arashe tana mai bin umarnin shugabar tata...
Har suka isa masarauta Zuhra bata daina matsan k’walla ba tana tina kalan cin amanar da K’awarta aminiyarta da mijinta sukai mata...
**
A b’angaren Mahmood kaw tinda ya bar wajen yake falfala gudu saman kwalta, clash Turaki yayi da motar tasa yai saurin takewa Mahmood d’in baya... Ganin irin tuk’in da yake kaman wani mai shirin barin gari yasa Turaki umartan mai tasi d’in yasha gaban motar Mahmood...
Haka mai tasi d’in ya k’ure malejin motar saida suka cimma Mahmood d’in... Turaki ya sallami mai tasi kana ya nufo yanda Mahmood d’in ya paka motarsa....
“Rankaidad’e Wai mai ya faru...? Ina Zahran...? Ya na ganka kai kad’ai, badai wani abin sukai mata ba koh...?!” Ya k’arashe cikeda kulawa...
Mahmood ya d’ago rinannun idanunsa yana duban Turaki dasu... Sosai Turaki ya razana da yanayin abokin nasa... Murya na rawa yake furta “Rankaidad’e... Kamin magana dan Allah...!!”
Bud’e masa lock yai ba tareda yace komai ba, Turaki ya shige cikin motar Jiki a matuk’ar sanyaye dan shi dik a zatonsa wani abin ne ya sami Zahra...
Suna tafe a motar babu mai cewa uffan, sai falfala gudu da Mahmood keyi dasu bisa kwalta... Idan ya danna birki saidai Turaki ya dubesa, Turaki ya sauk’e ajiyan zuciya a hankali har suka iso wani waje mai yawan ciyayi da duwatsu... Shidai Turaki duban Mahmood d’in kurum yake a matuk’ar tsorace da yanayin nasa...
Murya can k’asa yace “Kenan a wannan dajin suka b’oyeta...?!”
Sai lokacin Mahmood yace “Ita wa..?!”
Turaki da mamaki yace “Rankaidad’e Zahra’u nake nufi...!”
Nusawa Mahmood yai kad’an kana ya juyo yana duban Turaki idanunsa na kuma kad’awa, ya fuzar da fuci mai d’umi yana shafe fuskarsa da tafukan hannayensa... Lokaci guda ya zauna saman Dutse guda d’aya had’ida kalmashe k’afarsa guda...
Turaki ma ya k’arasa ya zauna jikina sanyaye “Rankaidad’e...”
Bai bari ya ida fad’in abinda zai fad’i ba yace “Zahra bazatai wannan tunanin ita kad’ai ba... Ta yaya ma zata San cewa akwai wata alak’a mai muni tsakanin Yazeed da Raheemah... Dole akwai wanda ya shirya mata hakan..!” Ya k’arashe yana mai duban Turaki...
Turaki da gaba d’aya ya zama confused yace “Your Highness... Ban fahimceka ba.. Wai meke faruwa ne..?!”
Cikin kalmomi k’alilan Mahmood ya sanar dashi abinda ya faru a gidan da sukai zaton an aje Zahra...
Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un Turaki Ke nanatawa yana jinjina lamarin “Turk’ashi..!” Ya d’an nusa kad’an sai kuma yace “Abokina Allah ne ya soka da alkhairi ya nuna maka hakan tun kafin akaiga aure... Amma kuma maganarka akwai k’amshin gaskiya cikinta Rankaidad’e, Zahra bazata iya tsara wannan abin ba, dole akwai wanda ya tsara mata hakan... Toh amma wa kenan..?!”
Mahmood ya d’an dubesa yace “Na tadda Zuhra matar Yazeed a wajen wanda bansan ya akai taje wajen ba... It might be possible Zuhra tasan komai tuntuni ko tana zarginsu sai ta had’a wannan plan d’in domin ta kamasu red handed..”
Turaki ya jinjina kai yace “Kaji tunani na manya.. Tabbas haka ne Rankaidad’e, kuma ko acan asibiti ma an tabbatar mana Zhara tajeta tareda wata mace... Ko shakka babu hakan ne..!”
Mahmood yai shiru tamkar mai nazari har lokacin ransa a matuk’ar b’ace yake.. Turaki ya d’an sadda kai yace “Hak’uri zakai Rankaidad’e, ita rayuwa...”
Duban da Mahmood d’in ya aika masa ya hana Turaki k’arasa magana.. Lokaci guda Mahmood d’in Ke fad’in “Maiyasa kake bani hak’uri bayan nan tab’a sonta ba... Abinda ya dameni shine involving Zahra da akai... Bai kamata tasan ire iren wad’annan abubuwan ba... Why must she involve my daughter, da ni ta samu da batun yafi Ta samu d’iyata da irin wannan batu...!” Ya k’arashe cikin tsananin nuna b’acin rai...
Turaki ya d’an shafi kansa yace “Haka ne Rankaidad’e amma kasan ba kowa zai iya samunka da wannan batu ba... Watik’ila shiyasa Ta biyo Ta wajen Zahra...!”
Mahmood ya katsesa da fad’in “That doesn’t justify what she did....she shouldn’t have involved my daughter... !!”
Turaki ya risina yace “Allah ya huce zuciyar Sarki... Tuba take Allah shi taimakeka, itama na tabbata tana cikin tashin hankali tinda Yazeed mijinta ne... A gafarceta Rankaidad’e..!!” Ya k’arashe yana risinawa gaban Mahmood d’in...
D’an girgiza kai kurum Mahmood yai yace “Tashi mu tafi...!”
Babu musu Turaki ya mik’e yana fad’in ya kamata suje masarauta suga halinda Zahra ke ciki... Yai maganar yana mai amsar car keys d’in Mahmood d’in....
**
Koda suka iso masarauta Mahmood ya tadda Zahra bacci ma take hankali kwancewa a d’akinta... Yai mata k’uri kaman mai tinanin wani abu, lokaci guda ya janyo mata k’ofan d’akin ya rufe... Yana ficewa Zahra ta bud’e idanunta a hankali tana sauk’e ajiyan zuciya lokaci guda tana addu’an Allah yasa Plan d’in Aunty Muhibbah yayi aiki akan Paa d’inta zai fasa Auren wannan mai suffar mayun.... Ta k’arashe tinanin nata tana mai darawa harda ‘yar tsallanta saman gado....
Mahmood na ficewa sashensa ya komo yanda ya tadda Zuhra zaune saman darduma alamun isowarsa take jira, har lokacin bata daina matsan hawaye ba....
Tana jin sallamansa tai k’ok’arin saita kanta had’ida risinawa Ta gaidashi...
Mahmood ya amsa cikeda tausayinta yasan tayi hak’urin zama da d’anuwansa... Can kujerarsa ya isa ya zauna kana ya soma fad’in “Zuhra, Yazeed mijinki ne kuma nasan kinyi hak’urin zama dashi tsawon shekarun da kukayi tare... Bazan hanaki yanke duk hukuncin da kikaso gameda ci gaba da zama dashi ba... Idan kin yanke hukuncin tura sak’o Masarautarku bazan hanaki ba sabida Ke aka zalunta, sannan idan kin yanke hukuncin komawa Masarautarku shima duk bazan hanaki ba... Kinada duk wani zab’i gameda ci gaba da zamanki cikin Masarautar nan... Idan har ni ne Sarki zan baki goyon baya d’ari bisa d’ari akan duk hukuncin da zaki yanke... Amma saidai inaso na miki wata tambaya Zuhra.! Shin ya akai kikasan abinda Ke wakana har kika tafi wancan gidan..?!”
Ta risina kad’an tana goge hawayen da suka kuma gangaro mata “Rankaidad’e sak’o na samu an turo min cikin wayata cewa Yazeed yana cikin wane yanayi naje na cecesa... Shine najeni nai wannan mugun ganin...!”
Mahmood yai shiru yana mamakin jin cewa itama batada masaniya gameda alak’ar Yazeed d’in da Raheemah..!
Jinjina kansa yai a hankali sai kuma ya d’an nusa yace “Kikace sak’o aka turo miki da bak’uwar lamba..?!”
Zuhra ta jinjina kanta a hankali “K’warai Rankaidad’e, sak’o aka turo min gashi ma ka gani..!” Ta k’arashe tana mik’a masa wayar....
Ya duba sak’on sosai kana ya ciro wayarsa yai comparing sak’wannin... Lambobi daban daban ne suka tura masu sak’on... Koda yayi dialing wannan lambar ma bata shiga... Watak’ila ma mai turo sak’on ya karya SIM cards d’in... Fuzar da fuci yai a hankali ya mik’a mata wayar... Ta tabbata Zuhra kanta batada masaniyan cin amanan da mijinta da k’awarta suke mata sai yau... Mutum gudace zata amsa masa tambayoyinsa itace d’iyarsa Zahra....
Ya d’anyi gyaran murya Murya kad’an yace “Sanda kika tadda Yazeed da Raheema sunada masaniyar naje wajen..?!”
Ta girgiza masa kai a hankali alamun a’a ta k’arada”Basu sani ba Rankaidad’e dan Raheemah har rok’ona take kada na sanar dakai don kar ka fasa aurenta..!”
Ya jinjina kai a hankali yace “Yayi kyau..!”
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 65