Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gaba da ambaliya a fuskarta sahu sahu, wani na bin wani... Ta kasa gasgata abubuwan da taji daga bakin wannan azzalumar mata wacce take tantama anya ‘yaradam ce..? Idan kuwa ‘yar adam ce Anya akwai zuciya cikin k’irjinta...? Hawaye had’eda zufan da ya wanke mata fuska take duban yanda Giwa Ke kuma sakin wane irin shewa akanta, ji tayi kaman maganan Ta ya d’auke cak sabida tsananin shiga tashin hankali da tayi domin kuwa ko kalma guda ta kasa furtawa, ga wani irin juyawa da kanta yake sai tanajin kaman a wani nisan duniya take sinkayo dariyar Giwa da shewarta... Bata kuma sanin meke wakana ba saidai kawai ganin Jamal tai tsaye kanta muguwar murmushinsa saman fuskarsa yake furta “Saudatu.!!! So you’re back..! Kin dawo dan Ki d’auki fansarki akanmu, kin dawo kin tarwatsa ahalinmu... Kin lalata komai, Na rasa k’afata guda d’aya, kin rabani da matata Umaimah..! Ban damu ba idan itad’in ‘yar uwarki ce, Umaima itace rayuwata, kuma har abada bazata tab’a sanin cewa ked’in ’yar uwarta bace, baza San cewa ga abinda na aikata ma ‘yar uwarta ba wanda suka had’a uba d’aya..! Ita d’in tawa ce bata da sauran ahali a halin yanzu da ya wuce ni Jamaluddeen..! Kece kika dad’a haukata Fu’ad sannan kika toni asirin Yazeed kika hana Mahmood Auren Raheemah..! Yazeed lost both his hands sabida Ke, he even lost his children duk a dalilin ki.. Ke harta aurensa ya rasa duk sabida Ke..! Ta yaya kike zaton zan goyi bayan a yafe miki..! Ai yanda Giwa ta fad’i Zata cika mana mulkin ahalinmu da gudan jininki babu ja babu komawa baya.. Sannan abu na k’arshe kafin Ki tafi daga wannan rayuwar zanso na sake d’and’ana zumarki dana d’and’ana a baya domin kuwa dukda shud’ewar shekarun nan, na lalata rayuwar ‘yan mata da dama banci karo da wacce naji dad’in kasancewa da ita sama dake ba..! Kafin na mik’a ki ma bokan Gimbiya ya gama abinda zai dake ya tura ma Sarauniya mai gadon Mulkin tsafi tarihin abinda muka aikata maki shekaru goma sha hud’u baya zai maimaita kansa...!” Ya kuma d’aga allurar dake hannunsa yace “Kinga wannan allurar ban mance da ita ba, musamman sabidake na zubata a syringe, sai na miki ita kafin na mik’aki ga bokan sarauniya, zan nuna miki k’arshen taurin kai yau, sai kinyi da kinsanin dawowa cikin wannan masarauta..! Zan miki wulak’ancin da ban miki irinsa a baya ba domin kuwa nid’in na k’ware wajen wulak’anta ‘ya’yan mutane ta hanyar lalata masu rayuwa wanda duk kece sila..! Duk yaran da na lalata ma rayuwa kece sanadi domin akanki na fara..! Da ace kin tsaya tun wancan lokacin an cika mulki da gudan jininki watak’ila da ban zamto abinda na zamto a halin yanzu ba... Dan ni da kike gani ban tab’a kusantar wata d’iya mace ba ba Ta hanyar fyad’e ba...!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin b’alle botiran rigarsa muguwar murmushin bata bar saman fuskarsa ba... Allah ya gani babu abinda take fahimta saima idanunta da suka kakkafe suna kallon sama, haka nan Ta koma tamkar wacce bata numfashi... Ga tsananin nauyi da k’irjinta harma da harshenta suka mata, addu’an ma bata iya furtawa da baki... Iyakacin abinda Ta sani shine shine zuciyarta bata daina ambaton mahaliccinta ba, zuciyarta bata daina tsarkake mahaliccinta tana mai k’ak’antar dakai garesa had’ida neman taimakonsa da agajinsa daga hannun wad’annan mugayan mushirikan mutanen data fad’a hannunsu..! Tayi imani Ubangijinta maiji ne kuma mai gani wanda ganinsa da jinsa suka sha bambam dana ko wani makhaluk’i..! ** Jikin Mahmood na tsananin rawa yake warware k’undin...! Ga tsananin mamakinsu wannan alamun shatin kwabo da suka gani daga tsakiyar ginin coin mai irin alamun ne cikin k’undin wanda yakeda matuk’ar nauyi a hannu sai faman shek’i yake kaman an tsoma cikin ruwan silver..! Baba Nomau dubi Mahmood da har lokacin jikinsa bata daina rawa ba bai kuma saki wannan shatin kwabon ba yace da Mahmood d’in “Ka natsu Mahmooda ka ambaci sunan Allah ka saka wanann shatin kwabo a jikin gini yanda yake d’aukeda alamun..!” Jinjina masa kai Mahmood yai, yayi kaman yanda Baba Nomau yace, da sunan Allah saman harshensa ya manna wannan shatin kwabo jikin garun..! Yana mannawa gaba d’aya Masarautar tayi wane irin girgiza wanda duk wani mahaluk’i da yake cikin Masarautar saida yaji wannan diri da d’aukacin Masarautar tayi.. Tsofaffin gini wasu saida suka b’anb’are wasu na zubewa k’asa..! Baba Nomau yace dasu kowa ya nastu suci gaba da ambaton sunayen Allah suna tsarkakesa..! Wannan dirin da d’aukacin Masarautar tayi sai gani sukayi wajen da Mahmood ya manna shatin kwabon gini yana bud’ewa kaman ana turasa...! Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un zukata Ke ambato..! Cikin iko na Ubangiji ginin nan yake bud’ewa suna hango wani alk’arya guda a bayan wannan ginin, domin kuwa cikin wannan gini wani masarauta ne mai zaman kansa..! Mahmood ya yunk’ura zai danna kai ciki Baba Nomau yayi saurin rik’osa ya dawo dashi baya yace dashi, gini irin wannan da yayi shekaru da dama a rufe haka dole akwai wasu halittu dake rayuwa ciki wanda mu namu idanun bazasu iya gani ba..! Inaso cikinmu gaba d’aya wanda duk baiyi azkar na safiya na neman tsari ba Toh yayi yanzu..!” Sannan karanto masu addu’o’in neman tsari da zasu karanto kafin su shiga..! Ya kuma karanto matayassara daga littafin Allah mai tsarki..! Su Duka suna masu yak’in da kariyar Ubangijinsu wanda babu abinda yafi k’arfin jkinsa..! Kowa yayi kaman yana Baba Nomau yace, suka nufi cikin wannan gini da basa iya ganin komai sai jemagu da wasu irin k’wari marassa kyaun gani.. Ja’afar da Mahmood saiko Baba Nomau da Ubandoma sune suka shigo cikin wannnan kangon Masarauta mai tarin kayan al’ajabi .. Bakunansu basu daina ambaton Allah ba..! ** Tun sanda ginin yayi wani irin diri fatar jikin Tal’udu ke fitar da wani irin bak’in hayak’i mai mummunan d’oyi, Kan Giwa da hannunta da ya tab’a cin wuta suna fitar da irin wannan hayak’in da kuma d’oyin... Jakadiya Ta razana matuk’a sai faman muzurai take tana tambayar Giwa mai ke faruwa...Giwa Ta rufa bak’ar Alkyabbarta hannunta rik’eda rik’eda fitilar tsafi.. Ta zauna saman Darduman tana fad’ida Jakadiya “Wannan shine cikan Mulkina Jakadiya..! Wannan alamu ce da take nuna Sarauniya zata cika mulki na a yau d’in..!!” Ta k’arashe tana mai kuma tura fitilar cikin Bak’in tukunyar Tana ganin yanda bak’in hayak’i ya rufe Tal’udu gaba d’aya... Jakadiya tace “Amma Rankidad’e bamu ganin alamun Tal’udu bak’in hayak’i ya rufesa.!!” Giwa taci gaba da fad’in “Sharad’in kenan ranan da Mulkina ya cika ranan Tal’udu zai bar cikin gidan nan tareda duk wani abu da yake daga tsatsonsa inada tabbacin wannan bak’in hayak’i alamu ce ta nasara..!!!” Jakadiya tai K’uri tana kallon wannan tashin hankali tana mamakin ta ya za’a ce bak’in hayak’i had’ida mummunan d’oyi ya zamto nasara..!! A daidai wannan lokaci su Mahmood suka iso...! Su Giwa suka soma hangowa tana zaune saman Jan Dardumanta na tsafi ga tukunyar tsafi gabanta gacan wani bak’in hayak’i turnuk’e gabanta wanda Tal’udu ne cikin hayak’in, bak’in hayak’in ya rufesa baka iya hango komai nasa..! A take suka soma toshe hancinsu suna kuma k’arasowa wajen..! Jakadiya ce ta soma hangosu, ta saki wani irin k’ara tana mai sililalewa k’asa Giwa kam hankalinta naga bak’in Tulu tana kuma tura fitalar tsafi ciki tana furta “Ya Ke Sarauniya uwar tsafi yau na cika miki k’udirinki na kawo miki Amaryarki da Ta gudu daga gareki shekara goma sha hud’u baya..! A yau na mallaka miki gudan jininta ki cika min Mulkina dashi..!!” Mahmood dake tsnanin huci ne yai wani irin tsalle ya tokari bayan Giwa kwatsam fuskarta ya fad’a cikin bak’in tulu had’e da jan fitilar dake hannunta..! Aiko fuskar Giwa na fad’awa cikin tulun nan wuta bal bal ya kama a cikin tukunyar ya shiga cin naman fuskarta..! Ta saki wani irin k’aran azaba mai muni gashi fuskarta ya rik’e cikin tulun mai ci da wuta..! Juyin duniya ta ciro fuskarta ta kasa cirewa sai ihu take zallan fuskarta na cikin Tulu yana cida wutan azaba..! Jakadiya jiki na rawa tab’e furta “Kumin rai..! Kuji k’an baiwarku mai biyayya a gareku..!!” Ubandoma yace “Allah yaji k’an masu jin k’an bayinsa na K’warai amma banda Ke Talle..!!!” Batakai aya ba Mahmood dake ci gaba da sakin huci ya damk’o wuyarta da duka hannayensa biyu cikin wane irin yanayi da babu wanda ya tab’a ganinsa ciki yake furta “Ina Muhibbah..! Ina Muhibbah..! Ina matata nace..?!!” Jakadiya da taji damk’a hannu na tsananin rawa take nuni da d’akin da Muhibbah da Jamal ke ciki wanda yake daga center k’ofar a bud’e..! Jifa yayi da Jakadiya tana ida nuna masa ya nufi d’akin a guje..! Jakadiya bata fad’a ko ina ba sai hannun Giwa dake ci gaba da kururwa tana kalaumen iska tana neman agaji take fad’in a cire mata tulun azaban da ya kame fuskarta..!! Aiko Giwa tanajin ta capko mutum ta damk’e Jakadiya gam tana fad’in sai ta cire mata tulun azaban dake mak’ale a fuskarta..! Jakadiya na kokawar k’wace kanta daga hannun Giwa, inaa Giwa bata daina janta ba tana fad’in ta cire mata tulun har saida suka dangana da hayak’in Tal’udu..! Jakadiya na kururuwa tana fad’in su ceceta zata mutu, inaa tuni Giwa ta jefata cikin hayak’in Tal’udu..! Babu wanda ya iya kusantar wutan tsafin da yake tasowa daga jikin Tal’udu yana haurawa jikin Jakadiya ...Tun ana hango hannun Jakadiya da take d’agowa sama har dai aka daina hangowa..! Baba Nomau da Ja’afar da Ubandoma suka fantsama sauran d’akunan dake jere wajen Ja’afar yana tokarin ko wace k’ofa tana bud’ewa..! Wani kayan tashin hankali da al’ajabi shine ko wane d’aki sai Sun tsinci gawan mace budurwa..! (Idan baku mance ba wad’annan ‘yanmata sune wad’anda Jamal ya lalata masu rayuwa Tal’udu da Giwa suka ajesu a wad’annan d’akuna da sunan sud’in matayen Sarauniya ce wanda d’aya d’akin da a kullum yake bud’e shine Saudatu... Sun rigada sunyi tsafi da wad’annan ‘yan mata sun halak’asu...) Mahmood yana fad’awa d’akin ya hango Jamal haihuwar uwarsa yana k’ok’arin duk’awa ga Muhibbah..! Cikin wane irin daka tsalle ya isa ya kai masa wata jahilar naushi wanda saida ya watsar dashi da sandarsa gefe guda..! Ya kuma janyosa ya shiga kai masa naushi ta ko ina kaman wanda aka aikosa, yana tokarinsa hawaye na tsartowa daga idanunsa... Bai daina tokarinsa yana kai masa bugu ta ko ta ina ba a haka ya dinga naushinsa yana cillosa waje da tsananin bugu gashi babu k’afa balle ya tashi ya gudu..! Ja’afar ne ya k’araso ya dafa Mahmood yace “Yaya Kaji da matarka..! I’ll take it from here..!!” Duban Ja’afar kurum yake da rinannun idanunsa yanajin idan bai kauce masa ya kashe Jamal ba zai iya had’awa dashi... Ja’afar na k’ok’arin kuma tausan Mahmood da Ko kalma guda ya kasa furtawa har lokacin sai wani irin tsima da jikinsa keyi yana fidda gumi kaman wani rikitaccen zaki wanda ya birkice cikin garken Giwaye..! A d’an wannan tsakanin Jamal ya samu yake rarrafawa ya nufi wajen mahaifiyarsa.. Da lalume Giwa ke fad’in “Jamal..! Gwarzona ka cire min wannan tukunyar azabar..!” Inaa tsaban bugun da Jamal yaji hannun Mahmood bai iya furta koda kalma sai nishi.... Ana haka Giwa taji ana janye Jamal daga cikin hannunta..! Taci gaba da kuruwa tana fad’in kar Jamal ya tafi ya barta ya cire mata wannan tulun azaban da ya manne mata fuska..! Fad’I take “Gwarzona ka taimakeni..!” Saidai Gwarzo ma takansa yake..! Ashe Tal’udu ne Ke janye Jamal yana fad’in shid’in daga tsatsonsa yake bazai tafi ya barsa ba..!! Manna hannun da Tal’udu zai jikin Jamal wuta ta kama tin daga Kwankwason Jamal har zuwa cinyarsa... Haka wuta tai masa sutura ta zamto wandonsa domin kuwa wuta ce ta rufe al’auran Jamal gaba d’aya ta zamto sitira garesa..! Ihun azaba da ya saki ya maidoda hankulan su Ja’afar..! Giwa na ihun Fuska cikin Tulu Jamal yana ihun wuta na cin iyakacin al’aurarsa ta masa sutura bata bari al’aurarsa ta bayyana ba, mummunan jan wuta taita ci yana ihu yana neman agaji.. A d’ari Mahmood ya koma cikin d’akin yanda Muhibbah Ke kwance har lokacin idanunta kaman a kakkafe suke..!A hankali cikin wane irin murya mai rarrabewa ya furta sunanata, jikinsa har wani irin rawa yake ya janyota cikin jikinsa, ya shiga jijjigata yana ambato sunnanta... A hankali yaga idanunta suna dubansa kaman zatayi magana..! Yaci gaba da jijjigata yana ambato sunanta.. Saidai lokaci guda idanun nata suka kuma rufewa ruf jikinta ya kuma sakewa cikin jikinsa...! Yai saurin d’agota yai mata irin rik’on da akema jarirai ya fice da ita daga wajen hankalinsa a matuk’ar tashe..! Giwa na ihu Jamal na ihu, a haka Giwa take takawa tana lalumen wajen tsira har ta nufi d’akin da Muhibbah ta kub’uta daga ciki, tana shiga da shike ba gani take ba fuskarta na rufe cikin tulu nan taji k’afarta ya cakki wani abu kaman allura..Aiko nan ta fad’i k’asa ta tuma da k’arfin gaske domin kaw gaba d’aya ji tayi jikinta ya sake kaman babu wani jijiya da ya kuma rik’e gab’ob’inta.. Aiko tana fad’uwa tulun ya fashe fuskarta da ya gama melewa ya koma kaman jan gauta ya bayyana, tulun tsafin na fashewa wani d’oyi ya kuma gauraye wajen, ashe allurar paralyze da Jamal ya aje zaiywa Muhibbah bayan ya ida cin zarafinta a karo na biyu shine Giwa Ta taka tayi takalmi dashi ya cakketa a k’afarta..! Haka Giwa Ta zube a wajen tana fitar da wani irin turiri had’ada gurnani na azaba ga fuskarta baka hango komai sai alamun melewar fata..! Shi kaw Jamal saida wuta ta ci al’aurarsa sosai kafin Ja’afar ya samu ya k’araso ya rufa masa rigar kuftarsa da yake sanye da ita Dan sanda wutar ke gauk’in ci tsaban turirin da take da huci Babu mai iya kusantarsa balle ya basa agaji.... Shid’inma sakin hucin azaba kurum yake... Can bayan wutan ya lafa suka hango Jakadiya itama wuta sosai yaci b’angaren jikinta gefe da ita Mushirinki mutumin ne wanda da alama shikam ma kaman babu rai jikinsa, ya k’one sosai baka hango komai tattar dashi sai wannan jan banten da a kullum yake d’aurawa..! Wutan duniya kenan taci wad’annan bayin Allah cikin ‘yan mintoci da basu shige a k’irga ba amma suka k’one irin haka, inaga wutan lahira wanda baida misali... Tun daga duniya Fuskar Mushirika Giwa wanda bata sujada wa mahaliccinta dashi sai Bokanta da sarauniyar tsafinsu yaci wuta ya mele ya koma abin tsoro da k’yama, shi kuwa Jamal al’aurar da yake sab’on Allah dashi yake cin zarafin ‘ya’yan mutane dashi ana tsafi dasu yaci wuta ya mele ya k’one k’urumus..! Allah kasa mufi k’arfin zukatanmu kayi mana mai kyau duniya da lahira Ameen..! A can b’angaren Mahmood kuwa yanda ya fito da Muhibbah saman hannunsa yana gudu cikin Masarautar duk yanda ya gifta sai Sun zabura Sun kuma dubansa... Can ya hango Turaki da Ansar suna tsayuwar jiran fitowarsu ne daga cikin ginin da alama..! Cikin wane irin murya yake sanar da Turaki ya kawo mota..! Gaba d’aya Turakin ma ya rikice, sai ya rasa wace hanyar zaibi saida Ansar yai directing nasa..! Mahmood bai daina jijjigata cikin hannunsa yana ambato sunanta ba.. Turaki na isowa da motar Yarima Mahmood ya bud’e baya ya shimfid’ata, take shima d’in ya shige ya aza kanta bisa cinyarsa har lokacin bai daina jijjiga fuskarta yana ambato sunanta ba..! Shi kuwa Ansar da yake likita ne sai ya k’araso yana k’ok’arin dubata..! Mahmood da bai daina sakin huci ba cikin wane irin darara tsawa yaceda Ansar “Don’t touch her..! Don’t you dare touch her..!!” Yanda yake maganan zai tabbatar maka bai k’aunan yaga hannun wani namiji kusanta..! Ansar da tsawar ta shigesa sosai, girgiza kai yake yana duban Mahmood d’in yake furta “Ni likita ne, zan duba na gani ne if she’s still breathing..!” Baikai aya ba saiji yayi Yarima Mahmood ya shak’o wuyarsa ya janyosa kusan fuskarsa yana furta “She’s breathing..! She’s alive..! Kada ka sake tunanin Ta mutu..! Idan na kuma jin irin wannan kalma daga bakinka zansa Dakarun Masarautar nan su fille wuyarka..!!” Yana ida fad’in haka yayi jifa da Ansar gefe guda..! Turaki yai masa K’uri sanda yake fad’i da Turakin ya tada mota su fice..! Turaki bai kunna motar ba sai duban Mahmood d’in kurum da yake da idanu..! Mahmood ya d’ago a zuciye yana tambayan Turaki mai yake jira..! Har lokacin Turaki bai amsasa ba bai kuma tada motar ba sai k’arasawa da yayi ya d’aga Ansar daga k’asa..! Cikin tsananin tafarfasan zuciya ya fito daga motar ya isa ya Turaki yana fad’in ya basa keys..! Turaki bai basa sai ma duban Ansar da yayi yace “Dr please check on her..!” Cikin huci Mahmood ya janyo Turaki da wuya ya maidasa gefe ya kuma tare gaban Ansar yana furta “Wannan mutumin bazai tab’a min mata ba..!!” Turaki ya dafe kansa yace “Your Highness please..! Ba maganar matarka ake a nan ba..! Maganan ceton rayuwar Muhibbah ake a nan..! What if tana buk’atan wani taimako na gaggawa before we make it to the hospital, what if akwai abinda ya kamata a mata kafin mu tafi asibitin wanda zai taimaka..! Mahmood idan Muhibbah ta mutu yanzu a nan zai zamana kai k’arasata, kishinka ne ya k’arasa kasheta..! Please let him check on her , ka bari ya dubata don ko asibtin kaje wani likitan ne zai dubata..!” A hankali Yarima Mahmood ya janye jikinsa ya baiwa Ansar hanya ba don yaso ba, yana mai aikawa Turaki muguwar kallo, idanunsa k’yam akan Ansar d’in yana duban yanda yake k’ok’arin kai hannunsa saman fuskar Muhibbah da zummar d’aga marfin idonta..! Cikin sauri Mahmood ya mik’a hannunsa ya d’aga masa marfin idon nata yana furta “Duk abinda zakayi ka fad’a min ni zan maka..!” Turaki dai girgiza kai kurum yayi yana kallon wannan drama na Rankaidad’e..! Ansar ya d’anyi gyaran murya yace “Rankaidad’e da ka kaita d’aki ka kwantarta saman gado, inaga ba wani abin tashin hankali bane, Shock d’in data tsinci kanta ciki had’ida girman abubuwan da suka faru da ita that’s the reason she passed out, you can take her to her room your Highness..! Idan yaso sai ka kirawo likitan daka yarda dashi ya dubata..!” Idanunsa na kan Ansar bai daina fitar da huci ba yake furta “You don’t tell me what to do..! Musamman Abinda ya shafi matata..!! Now get lost..!” Ya k’arashe yana mai kuma d’aukota saman hannunsa.. Har ya soma tafiya ya kaikaito ya dubi Turaki yace “I need a female Dr..!” Bai kuma furta komai ba ya nufi sashensa da ita.. Turaki ya sauk’e fuci a hankali, kafin yayi magana Ansar ya girgiza masa kai yace “Kar ka damu I understand where he’s coming from, yanzu da ya fahimci abinda ya faru da Muhibbah bazai aminta da ko wane namiji kusanta ba koda kuwa likita ne..!” Turaki ya jinjina kai a hankali yana fuzar da wani hucin, lokaci guda ya ciro wayarsa ya shiga kiran asibiti..! ** D’akin dake gefe da nasa ya kaita ya kwantarta saman gado, ya d’an rank’wafo da wuyarsa kad’an sanda yake k’ok’arin ajiye kanta saman pillow, daidai saitin wuyarsa yaji kaman hucin numfashinta, ya karkato da fuskarsa yana duban nata fuskar yanda idanunta ke lumshe... Ya jima sosai yana duban fuskar nata da yanda jini ya d’an bushe ciwon da Jamal yaji mata, sosai ya runtse idanunsa sanda ya tuna ganin Jamal da yayi yana k’ok’arin auka mata wanda ba don Allah ya kawosa akan lokaci ba da ya aikata mata abinda suka aikata gareta shekarun baya, wancan ma da suka aikata duk tunowa da zai sai yaji kaman mashi ake caka masa a k’ahon zuciyarsa balle yanzu da yaga Jamal akan idanunsa na k’ok’arin aikatawa..! Sai faman dunk’ule hannunsa yake idanunsa na duban wani b’angaren zuciyarsa na kuma masa zogi yana murza zoben dake hannunsa, har saida yaji k’aran fad’uwar zoben saman tile kafin ya maidoda dubansaga zoben nasa..! A hankali ya mik’e ya nufi bathroom ya d’ebo ruwan d’umi kad’an a roba had’eda k’aramar towel ya zauna gefenta ya shiga danna mata goshinta dashi..! Yana danna mata towl d’in yana tuno duk abubuwan da suka faru tin daga lokacin da ya d’aurata saman dokinsa tana k’arama ranan Washe garin sallah da suka tsinceta, ranan da Giwa da ‘ya’yanta suka b’ata mata rayuwa..! A hankali ya soma furta “I shouldn’t have left you alone with them..! I should have stayed..!” Muryarsa ya sark’e sabida tsananin rawa da muryar keyi, lokaci guda yake furta “Please Ki yafe min, Ki yafe min da ban tsaya na kaiki gida ba..!” Ya k’arashe yana mai k’ura ma fuskarta idanu fsukarsa dab kusan nata, hawayen dake mak’ale cikin idanunsa guda ya d’igo, ya d’iga a daidai saitin idonta, hawayen nasa ya ratsa ya shige cikin idonta wanda yasa idanun nata motsawa..! Idanunsa a lumshe hannunta guda rik’e cikin nasa ta soma k’ok’arin bud’e idonta..! A hankali take jin idanunta suna k’ok’arin bud’ewa, tana iya hango fuskarsa dururu, har sai da ida bud’e idon nata.. Cikin yanayin tsoro Ta soma k’ok’arin mik’ewa, Mahmood ya bud’e idanunsa Tar cikin nata idanun... Zuciyarta yaci gaba da bugawa abubuwan da suka faru suna kuma dawo mata, yanzu ga Rankaidad’e zaune kusanta hannunta cikin nasa..! Zuciyarta yaci gaba da tsinkewa, tsoron abubuwan da suka faru da wanda taji suka kuma dawo mata..! Numfashinta ya soma fita da sauri sauri tana mai kuma k’ok’arin fuzge hannunta daga rik’onda Mahmood d’in yai mata..! Bai saki hannun nata ba saima dad’a matse hannun nata da yayi cikin nasa...! Tana gani yake k’ok’arin kwanto da fuskarsa kusan nata, idanunta suka kuma firfitowa waje tana k’ok’arin k’walla ihu yai amfani da d’aya hannun nasa ya toshe bakinta, saitin kunnenta yakai bakinsa had’ida rad’a mata “You’re safe now, you’ll always be safe... around me..! Stay here in bed and get some rest..! Likitarki zata K’araso nan bada jimawa ba..!!” A hankali yake jin bugun zuciyar nata na raguwa alamun tsananin tsoron na d’an sakinta, idanunsu cikin na juna har lokacin hannun Mahmood na saman bakinta, har saida yaji natsuwa na sauk’o mata a hankali kana ya zame hannunsa daga saman bakinta..! Ta ja wani irin ajiyan zuciya tana mai dubansa har ya mik’e tsaye, tana gani ya ciro wayarsa a aljihu yana amsa kiran Turaki da alama maganar likitar suke..! Mahmood na ficewa ta mik’e zaune da k’yar tana mai kuma jan wani dogon numfashin had’ida dafe kanta idanunta a rintse..! Kusancinta da Rankaidad’e ya soma d’aure mata kai, a yau d’in tasan Shi baidaga cikin ahalin Giwa kuma shid’in d’ah ne ga yayar Mahaifinta amma kasancewarsa d’an uwanta bai halatta masa kusantuwa da ita har haka ba..! Tab’a k’ofar da akai ya sanyata saurin bud’e idonta da yai mata tsananin nauyi, wata mata ce ta gani wacce kaman tasan fuskarta a wani wajen, gefe da ita wata matar ce wacce ke sanye cikin shiga irinta likitoci... SameenaAleeyou 📚 *MUHIBBAH* *77* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Muhibbah tai K’uri tana duban matar wacce itama d’in ita take duba, tana mai takowa cikin d’akin a hankali..! Sai yanzu ta fahimci ko wacece wannan matar, mahaukaciyar nan ce data bata Taswira, wacce ta taimaka masu suka fice daga cikin Masarauta taredasu Ubandoma da Ja’afar, sannan itace Giwa ta sanar da ita cewa mahaifiyar Yarima Mahmood ne da kuma Ja’afar, ‘yar uwa ga Marigayi mahaifinta..! Take taji wasu irin hawaye suna zuwa idanunta, duk labarun zalunci da Giwa tayi ma wannan mata da ahalinta suka shiga dawo mata daki daki..! Tana gani matar dake zuban hawaye takai hannunta dake tsananin rawa tana shafa fuskarta, su duka biyun suna duban juna hawaye na gangaro masu... A hankali matar ta janyota cikin jikinta ta rungumeta sosai kuka mai k’arfi na kufce masu gaba d’aya, saida sukayi mai isansu kana ta kamo hannayen Muhibbah tana juyawa tana kuma kallon illahirin jikinta har zuwa fuskarta... Muhibbah dake sakin murmushi takai hannunta a hankali tana share hawayen matar, su duka biyu murmushi ne mai gauraye da hawaye saman fuskokinsu... Hannayenta rik’e cikin na matar take tambayarta “Sun kuma cutar dake..?!” Ta girgiza mata kai a hankali alamun a’a “Allah bai basu nasara ba..!” Ta fad’i cikin tsananin rawar murya.. Lokaci guda taci gaba da fad’in “Ke ‘yaruwar.. Mahifina ne... Giwa ta fad’a min haka da bakinta, ta sanar dani abubuwa da dama, ciki harda yanda ta rabaki da ‘ya’yanki guda biyu... Rankaidad’e da Ja’afar ‘ya’yanki ne..! Haka tace..! Muje muje mu samesu mi

Chapter 53 of 65