Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya kuma duban Ubandoma, murmushi ya sakar masa wannan karon kana yace “Idan ma baka goyi bayana kayi abinda na umarceka sanin kanka ne bazasu barka da rai ba... You know perfectly well how they do things here... Bazasu barka ka fita da rai dubu ya faru da haka... Kuma kar ka mance Wambai ya riga ya rasu fitarka a nan a halin yanzu zai matuk’ar wahala...!” Ubandoma ya kuma zaro idanu yana maimaita “Wambai ya rasu...?!” Yazeed ya murmusa yace “Karka damu idan ka bani had’in Kai zan fitar dakai muddin na zama Sarki... Sannan zan baka matsayi mai girma, zan fifitaka fiyeda yanda ba’a tab’a fifitaka cikin Masarautar nan ba... Kawai Kayi abinda na umarceka shikenan ka tsira...!” Ya k’arashe cruel smile d’in nan nasa saman fuskarsa... Ubandoma ya had’iyi miyau da k’yar yana duban Yazeed da tuni yakai k’ofa.... Ya kuma juyowa kaman zai magana wayarsa Ta d’auki ruri Raheema ce mai kiran nasa... Yana d’agawa daga d’aya b’angaren tace “You and I need to talk... Let’s meet up...!” Bata jira amsarsa ba Ta katse kiran.... ** Zama Muhibbah tai tana kuma warware zanen nan had’ida nazarinsa, nan Ta d’auko wayarta Ta kunna ta had’e zanen tana k’are masu kallo... Babban abinda ya bata mamaki shine duk yanda tai zaton zanen nan abu guda ne ashe ba abu guda bane, sunada salo da tsari iri guda amma Sun banbanta kad’an... Ita kanta bazatace ga difference d’in tai figuring out a halin yanzu ba hasalima sosai kanta ya kuma shiga duhu... Ga dai hikima iri guda anyi amfanida wajen tsara Taswiran amma sun banbanta da juna... Ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya a hankali, ya zatai yanzu... Lumshe idanunta tai a hankali ta tafi duniyar tunanin abinyi... Idan har tana so ta fahimci zanen nan Ta iya warwareta ya kamata ta zaga cikin gidan nan ta k’arewa ginin kallo tunda gida ne na sarauta sannan ta shiga museum na cikin Masarautar nan taga Taswirori na tarihi wala’alla Ta sami wani clue gameda wannan Taswira mai wahalan fasaltuwa da fahimta... Watak’ila Ta iya samun wani HASKE a can Zauren Ajiya na kayan tarihi dake cikin Masarautar... Sauri sauri ta mik’e ta shirya tsaf, tai shiga irinta masu mulki harda Alkyabba, sosai shigar ya amsheta, nan ta fito tana taku cikeda k’asaita irinta masu mulki... Tana tafe take tinanin toh wa zata soma tunk’ara tunda hankalin mutanen gidan gaba d’aya bai jikinsu sabida rashi da aka masu, Toh kodai ta kirawo Fu’ad ne.... Toh amma bataso ake ganinsu tare balle wani yai suspecting wani abu... Kawai ta yanke shawarin tambayan Sarkin Fada... A haraban Masarautar ta tadda wasu bayi ‘yanmata guda biyu yanda ta tanbayesu suyi mata jagoranci zuwaga Sarkin Fada, babu musu bayin sukace Ta biyosu... Muhibbah tasa kai tana tafe biyedasu Can Rumfar Sarkin Fada suka taddashi tareda wasu Fadawan, suna ganinta suka isa sukai mata gaisuwa... Muhibbah ta dubi Sarkin fada tace “Da Allah wani tambaya nake...!” Sarkin Fada yace “Rankidad’e kyakkyawa fad’i tambayarki..!” Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Shin yaushe ne ake bud’e d’akin ajiya na cikin Masarautar nan... So nake nasan wasu al’adu na cikin gidan nan kafin na tafi...!” Sarkin Fada da sauran Fadawan suka dubi juna jin tambayar da tai... Muhibbah ta bisu da kallo gaba d’ayansu yanda suke kallon kallo ma juna... Murmushin yak’e tai wannan karon kana tace “Ah shikenan, Ina tunanin ba ko yaushe ake bud’ewa ba kenan...!” Sarkin Fada yace “Ba haka bane Rankaidad’e Mai kyau, ai Wato idan ba ahalin gidan nan ba Sarkin Fada baida hurumin bud’e miki Ma’ajiyin Gidan nan... Yin hakan zaisa na shiga matsala...!” Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana tace “Toh shikenan babu matsala, na gode sosai...!” Har tasa kai ta juya saiga wani bawa guda ya k’araso yayiwa Sarkin Fada magana a kunne... Tana tafe ta sinkayo muryar Sarkin Fada na fad’in “Rankidad’e Mai kyau... Dawo da baya... An umarce Sarkin Fada ya bud’e miki duk wata zaure da kika buk’ata cikin Masarautar nan.... Sarkin Fada yana neman afuwanki...!” Ya k’arashe yana mai baza babbar riga had’ida mik’ewa... Ita dai sai ‘yan waige waige take tana mamakin waye yai umarni da a bud’e mata Zauren Ajiya.... Tafiya mai d’an tazara kad’an sukai kana suka iso Zauren ajiyan kayan tarihi na Masarautar.... Sarkin Fada yasa mabud’i ya bud’e... Ta ware idanunta tana duban dogon ginin mai tsawon gaske da dadd’en tarihi... A hankali tasa k’afarta tana takawa cikin ginin tana duban manyan zanen hotunan bayi da masu sarauta da irin yak’i da akai a shekarun baya shekaru masu yawan gaske na wasu k’arnin.... Ji tai k’ofar mai nauyin gaske ya rufe da ita a ciki, dan bata ankara ba sai jin sautin rufuwarsa tai gashi abinka da tsohon gini mai girman gaske ko ina saida ya amsa... Ta waigo cikin sauri tana duban bayanta, gabanta ya yanke ya fad’i ganinsa da tai tsaye bayanta hannayensa a hard’e Ta baya shid’inma ita yake duba... Yana sanye cikin bak’ar rigar Kufta wanda ya fito da asalin Farin fatarsa, shigar kufta yai gaba d’aya dan harta takalman k’afafunsa bak’ak’en Kuftane da akai masu kwalliya da farin zare mai d’aukan idanu k’warjininsa sai ya cika wajen gaba d’aya....Tai saurin janye idanunta daga barin dubansa k’irjinta naci gaba da bugawa... ** Gimbiya Zeenatu na kishingid’e a parlornta na alfarma bayan sun dawo daga ta’aziyan gidan Wambai Hadimarta ta shigo ta sanar da ita shigowar Yarima Yazeed... Sosai tai mamakin jin Yazeed yazo gaisheta har sahsenta, kodashike ba abin mamaki bane tunda rashi akai gaisuwan ta’aziya ya shigo mata... Tuni Ta basa izinin ya shigo... Ya kuwa shigo cikeda k’asaita, sukai gaisuwa irinta masu mulki kana yai mata ta’aziya... Gimbiya Zeenat taji dad’in shigowarsa tuni aka cika gaban Yazeed da kayan mak’ulashe da tand’e tand’e, ya kuwa zauna sosai kaman wani mutmin arziki, Gimbiya Zeenat ta mik’e ta basa waje dan ya saki jikinsa yaci kayan motsa baki da aka kawo masa.... Haurawarta sama da kad’an Raheema ta fito cikin gayu da kwalliya... Yazeed dake kishingid’e irin zaman masu mulki murza zobban hannunsa kurum yake yana k’arema Raheema dake sauk’owa kallo from head to toe.... *Sak’on gaisuwa mai tarin yawa tareda fatan Alheri gareku msoyana... Sameena na kaunarku a dik yanda kuke..!* SameenaAleeyou📚 [8/1, 8:41 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *39* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tai k’ok’arin tarttaro natsuwarta gaba d’aya, murmushin da yafi kama da yak’e saman fuskrta “Your Highness... Barka da yammaci.!” Tai maganar tana mai daidaita tsayuwarta... Kaman bazaice komai ba har wannan lokacin, sai dubanta da yake daga nan yanda yake tsaye hannayensa hard’e Ta baya... Gaba d’aya sai tajita ba daidai ba, zuciyarta yaci gaba da bugawa da sauri sauri... Maiyasa yake dubanta haka..? Kodai ya karanceta ne ya soma zarginta... Kai inaa hakan bamai yuwa bane, musamman yanzu data soma samun hanyar da matsalanta zai warware.. She can’t allow someone to get suspicious of her...Tai saurin d’ago idanunta aiki nan idanunsu ya sark’e waje guda.. Fuskar nan nasa tamau... Ta had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’oshi ya kasa shigewa.... Gyaran murya Tai kad’an tana k’ok’arin had’o kalamai saman bakinta “Tuba nake your Highness... Na zaci kowa zai iya ziyartan Zauren ajiya na.....” Burki tai ma kalaman nata ganin ya soma d’ago k’afafunsa yana takowa cikeda k’asaita... Zuciyarta taci gaba da bugawa ganin ita yake nufowa... Tai saurin lumshe idanunta tana k’ok’arin karanto duk addu’an da yazo bakinta... Dai dai gabanta Mahmood yaja ya tsaya har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya yai k’uri ma labb’anta yanda take motsasu a hankali alamun tana karanto addu’a, a hankali yake k’arewa fuskar nata kallo tin daga labb’anta zuwa karan hancinta har zuwa idanunta da suke a lumshe masu cikeda tsoro... Wani irin yarr yaji gaba d’aya illahirin jikinsa... Yanayin da ya jima baiji hakan ba a tsakanin lokacin... A hankali ya janye idanunsa daga barin duban nata, cikin takunsa mai cikeda k’asaita ya soma takawa har ya isa gaban wani k’aton hoto mai k’unshe da zanen mutane cikin shiga irinta mulki da sarauta... Ya kafe hoton da idanu hannayensa hard’e ta baya... “Halittanmu baisha bambam da mutanen da sukazo kafin mu ba, saidai halayya da d’abi’unmu sun banbanta...Wani zamani muke ciki wanda cin amana da yaudara, zalunci da k’eta su sukafi jagoranci sama da kyawawan d’abi’u masu nagarta...!” Ya k’arashe yana mai juyowa... Tinda ya soma magana take k’ok’arin bud’e idanunta a hankali har Ta ida waresu... Daga nan yanda yake tsaye yai gyaran murya kad’an yace “Having curiosity aroused..?!” K’ak’aro murmushin da yafi kama da yak’e tai ta d’ora saman labb’anta “K’warai your Highness... Masarauta mai cikeda d’inbin tarihi da kyawawan d’abi’u had’ida al’adu irin haka... Babu wanda zaiso ya shigo cikinta ya tafi ba tareda ya yi dubi da wad’ann kyawawan hikayoyi da suka aje Martaban Masarautar har Ta kawo tsawon wannan lokaci...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta.. Baisan dalili ba amma tunda ta soma magana yakejin kumatunsa na motsawa kad’an sihirtaccen murmushi da ba lallai ka fahimci hakan ba shine sama fuskarsa tasa... Ya d’an gyara tsayuwarsa yana dubanta sosai, saida yai taku kaman guda uku, sai kuma yaja ya tsaya “You seemed so sure...?!” Ya fad’i yana dubanta.... Ta kuma murmusawa kad’an tana mai k’arasawa jikin wani k’atoton zane mai d’aukeda hoton wani basarake sanye da rawani da alkyabba wanda ko ba’a ce ba kasan dadd’en zane ne... Tasa hannu tana shafa wasu rubutun da akai k’asan zanen da haruffan ajami na Arabic... Lokaci guda taci gaba da furta “An samu Masarautar ne ta hanyar nagartattun mutane wanda jajircewarsu da k’wazonsu had’ida gaskiyarsu da son gaskiyarsu sune suka had’u suka kafa Daular... Kuma da sannu al’umman Masarautar zasuyi fatan magadansu suyi koyi da kyawawan d’abi’u masu nagarta irin nasu... Fata mai kyau a koda yaushe yana tafiya tareda Al’umma nagartacciya ce Rankaidad’e...!” Ta k’arashe tana mai juyowa gareshi... Kai tsaye bazaice ya fahimci duka abubuwan data fad’i ba, amma har k’asan zuciyarsa yake jin kalaman nata.... Ya isa jikin k’atoton hoton ya tsaya gefe da ita, su duka biyun suna duban hoton... Cikin kalmomi da basu shige uku zuwa biyar ba ya fad’i k’arnin da aka kafa Daular a tak’aice... Ta karkato kad’an tana dubansa murmushi saman fuskarta... Lokaci guda tace “Ka iya bada labari your Highness... Kodai History ka karanta...?” Duban da yai mata ya sanyata had’iye sauran zancen nata tana mai furta “Tuba nake Rankaidad’e...!” Baice komai ba sai soma takawa da yai zauren na amsa sautin duk wani aje k’afarsa da zai a k’asa mai cikeda charisma... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai furtawa cikin zuciyarta _Muhibbah nemi abinda ya kawoki kafin lokaci ya k’ure miki.._ Take ta hangi wani dogon shelf d’aukeda manyan takardu da littafai, ta waiga gefe da gefe bata hangi Mahmood ba hakan ya bata daman k’arasawa jikin shelf d’in cikin sauri tana dubawa a hankali... A yayinda shima Mahmood d’in tsaye yake ta bayan shelf d’in yana bincika takardu wanda zai iya kamanceceniya da zanen gidan sarauta da Wambai ya damk’a masa... A tare suka hango wani littafi mai tarihin gaske, ba tareda sun sani ba sai kai hannunsu sukai lokaci guda kowanne cikinsu na son ya d’auki littafin.... K’irajensu ne suka buga sakamakon jin hannayensu da sukai cikin na juna sun sark’afe waje guda... Muhibbah tai saurin zaro idanu waje zuciyarta naci gaba da bugawa.... Hannunsa guda yasa ya matsar da littafan da cikin shelf d’in dan tabbatarwa idanunsa cewa hannunta ya rik’e... Sukai tsaye suna duban juna ta cikin shelf d’in... Muhibbah ce ta soma yunk’urin janye hannunta cikin tsananin rawar jiki, saidai fuzge hannunta da zatai k’atoton ma’ajiyan takardun ya dawo kanta.... Suka d’aga idanu suna duban katakon yanda ya nufota... Tsayuwa kurum tai had’ida dafe kanta tana jiran mai aukuwa ya auku.. Lokaci guda ta saki wane irin k’ara... Bata ankara ba sai ji tai ya bangajeta gefe guda katakon ya fad’o kansa... Muhibbah dake zube gefe dafe bakinta tai da duka hannayenta biyu tana mai kuma firfito da idanunta waje ganin bata ko hango Yarima Mahmood sai k’uran shelf d’in nan da ya fad’o kansa.... Gaba d’aya k’ura ya turnuk’e wajen.. Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un kawai zuciyarta Ke nanatawa... A d’ari ta mik’e ta nufo wajen tana ambato sunansa amma shiru bai amsa ba, zuciyarta ya kuma tsinkewa... Take taji hawaye na neman ciko idanunta... Ta shiga k’ok’arin janye shelf d’in daga kansa tana kiran sunansa amma inaa shiru babu amsa... Hawaye na gangaro mata take kuma k’ok’arin janye k’atoton katakon da ko motsa sa bata iya yi... A hankali k’uran Ke lafawa yanda Ta soma hango fuskarsa da k’ura ya lullub’e idanunsa a lumshe.... Cikin azama taci gaba da k’ok’arin janye katakon tana furta “Yarima..! Yarima please wake up... Dan Allah ka tashi..!!” ** Yazeed ya kuma relaxing cikin gadon yana mai rakata da idanu shu’umar murmushin nan nasa saman fuskarsa... Raheema ta margino cikin k’irjinsa tana shafa fuskarsa a hankali take furta “You seems to be in a good mood Your Highness... Fad’a min sirrin...” Ta k’arashe cikin salo tana mai fatan ya zayyano mata komai gameda shirinsu shida Majidad’i kan Mahmood cikin zuciyarta... Sumarta yake shafawa a hankali murmushin bai bar saman fuskarsa ba “Well, I’ve every reason to be in a good mood... Soon enough burina zai cika..!” Raheema Ta kuma gyara kwanciyarta sosai tana mai dubansa take furta “Wow... Da gaske.. Ba dai burinka na zama sarki ba..!” Yai murmushi da gefen bakinsa yana mai dubanta da wutsiyar ido wannan karon “Very soon komai a Masarautar nan zai zamto yana k’ark’ashin iko na... Kowa zai zama yana k’asa dani... Sai abinda nace kuma sai abinda naga dama za’ayi... Ciki harda Yaya na Mahmood..!” Ya k’arashe muguwar murmushin saman labb’ansa... Raheema Ta kuma zama sosai tana dubansa lokaci guda tana k’ok’arin karantarsa... “Tell me... Mai kake shiryawa...?!” Da wutsiyar idanu ya kuma dubanta wannan karon ma... “Sabida kije ki fad’awa Mahmood..?” Ta d’an sha jinin jikinta kana tace “Ban gane naje na fad’awa Mahmood ba... Mai kake nufi Zeed..?!” Murmusawa ya kumayi lokaci guda ya mik’e yana mai zura tufafinsa yake furta “Drop the act Princess... You can’t fool me... Na gane nufinki...And believe me bazakiji komai daga bakina ba... Kinyi kuskure da kikai underestimating d’ina... You might be a woman but Prince Yazeed AbdulJabbar ya shige duk makircin wata mace Sweetheart..!” Ya k’arashe yana mai kuma sakin murmushi had’ida zira zobbansa yasa kai ya fice... Gimbiya Zeenat dake lab’e jikin staircase tana ganin shigewan Yazeed ta fuzar da fuci a hankali.. Ta rasa Raheema wace irin kariya ce mai take samu wajen wannan watsettsen Yazeed d’in da ta tabbata ko sarautar ce bazai tab’a yi ba... A fusace Ta nufi d’akin da Yazeed ya fito yanda Ta tadda Raheema na shirin fitowa... Fincikota tai Ta dawo da ita baya tana fad’in “Shige ki Fada’ min uwar mai kuka gamayi Keda watsettsen can...!!” ** Duk iyaka k’ok’arinta Ta kasa janye katakon, gaba d’aya itama ta jigata, tuni ta kwab’e alkyabban jikinta tana k’ok’arin had’o duka k’arfin da Allah ya huwace mata ganin Ta ceci rayuwar Mahmood... Ganin dai bazata iya janye katakon ba ya sanyata saurin nufa k’ofa neman agaji... Saidai wani tashin hankalin shine ta kasa koda motsa k’ofar ne abinka da ginin zamanin da mai aminci.... Ta shiga dukan k’ofan tana kiran taimako nan ma shiru dan yanda ginin Keda matuk’ar zurfi da tsawo zai wuya na waje ya iya saurarenka... Sabbin hawaye suka kuma ciko idanunta, yanzu idan ya mutu nan no one would believe cewa ba ita ta kashesa ba.... She can’t let him die here...! Lokaci guda ta koma da baya tana mai ci gaba da k’ok’arin janye k’kk’arfan katakon mai minci... Da k’yar da nishi ta samu ta d’an matsar da katakon.. Lokaci guda tana mai kuma ambato Yarima, daidai nan Mahmood ya soma tari da atishawa alamun yana fitar da k’uran da ya shak’a.... Muhibbah tai hamdala cikin zuciyarta tana mai ci gaba da k’ok’arin janye katakon take furta “Rankaidad’e ka tashi... Alhamdulillahi... Sannu Rankaidad’e...!” Hannu yasa da k’yar ya matsar da katakon daga kansa yana mai k’ok’arin mik’ewa da k’yar had’ida kakkab’e k’uran dake bisa jikinsa... Sai faman sannu take masa fuska fal damuwa, harda ‘yar murmushin da bata San ya subce mata ba... Ta kuma matsowa kusansa kad’an tanai masa sannu... Ido ya d’ago yana dubanta wanda ya sanyata stepping back kad’an... Lokaci guda yake furta “Are you hurt..? Did something happen to you..?” Saurin girgiza masa kai tai alamun a’a.. “I’m fine your Highness, babu abinda ya sameni... We need to get out of here...” Jinjina mata kai yai a hankali yana mai d’an dafe kansa dake masa zogi had’ida lumshe idanunsa a hankali... Lokaci guda yasa kai ya nufo k’ofa dukda d’an jan k’afafunsa da yakeyi... Tai tsaye tana binsa da kallo daga nan yanda take tsaye... Kaman wacce aka sinkaya tai saurin nufosa tana mai furta “Rankaidad’e..!” A hankali ya kaikaito kad’an yana dubanta, cikin tsananin sanyin murya take furta “Thank you for saving me..!” Baice da ita komai ba sai kallonta da yai na wasu ‘yan dak’ik’ai, lokaci guda ya isa jikin k’ofan ya danna wani b’angare ya tura baya nan k’ofan ya bud’e... Muhibbah taita mamakin yanda ita ta kasa bud’ewa... Sauri sauri ta biyo bayansa kafin k’ofan ya kuma rufewa da ita ta rasa na yi... Sai faman waige waige take, ita kanta batasan biye take dashi ba ta dai San tafiya kurum take... Saida suka nufo kusan sashen Mahmood d’in a haka tana biye dashi a baya Zahra ta habgosu... Ta k’araso da sauri saidai tuni tai turus ganin jikin Mahaifin nata duk k’ura... Ta dubesa ta dube Muhibbah... Zahra tace “Paa mai ya sameka... Daga ina kuke...?!” Sai lokacin Mahmood ya juya ya dubi Muhibbah dake biye bayansa... Jin babu amsa ya kuma sanya Zahra matsowa ta kamo hannun mahaifin nata “Paa are you alright...?!” Baice da ita komai ba sai k’ok’arin sa kai da yai ya nufi cikin sashen nasa... Zahra ta dubi Muhibbah da tai sororo wajen “Aunty Muhibbah meke faruwa... Mai ya sami Paa d’ina...?” “A minor accident, please Ki bashi pain relief... And take care of him...!” Tana ida fad’in haka ta juya cikin sauri ta nufi nata b’angaren har k’afafunta na hard’ewa waje guda... Ga zuciyarta da ya kasa daina bugawa... Zahra ta d’an bita da kallo kana Ta maido da dubanta ga Mahaifinta da tuni ya shige sashensa... Cikin sauri ta take masa baya... ** Raheema dafe da k’uncinta take duban ‘yar uwar tata da ta shafeta da mari mai kyau... Lokaci guda Gimbiya Zeenat Ke fad’in “Sabida Ke bakida hankali shashasha ce gidahuma ko..? Toh bari kiji ban d’auko na kawoki Masarautar nan dan ki shantak’e da ‘ya’yan Sarki ki jaza min abun kunya ba... Kawoki nayi domin ki maido min da Martabata da na rasa cikin Masarautar nan ki auri Mahmood wanda zai kasance Sarkin gobe kin fahimta..!” Ta k’arashe cikin tsananin huci... Raheema ma hucin take sosai “This is who I’m Aunty Zeenat... Ya rage naki ki accepting d’ina yanda nake ko kar kiyi... Baki fini son kasancewa Matar Mahmood ba amma Yazeed nada wani gurbi mai girma cikin zuciyata kuma barikiji na fad’a miki wannan ya zama na k’arshe da zaki kuma d’aura hannunki a fuskata da sunan mari... Wllhi kinji na rantse miki dik sanda kika sake gigin tab’a lafiyata sannan ne zan nuna miki hauka gaskiya ce... Kuma Wllhi sai na sanar da Giwa duk shirinki akan d’anta da kuma Masarautar nan... Dan haka idan kunne yaji jiki ya tsira...!!” Tana ida fad’in haka tasa kai ta fice fuu kaman zata tashi sama... Gimbiya Zeenat tabita da kallo shaye da tsananin mamaki... ** Tunda ta iso d’aki ta rasa sukuni, tinanin abubuwan da suka faru sun kasa barin kanta... Bathroom ta fad’a tai wanka da ruwa mai d’umi sosai kana ta d’auro alwala dan magrib ya hararo already... Doguwar riga mai laushi Ta zira kana Ta nufo wayarta yanda yaketa faman ruri... Fu’ad ne mai kiran nata... Bata d’aga ba saima fuzar da fuci da tai a hankali ta zauna gefe tana duban wayar har ta k’arashi ringing d’inta, daidai nan Umaima tai sallama... Zama sukai suna fira har aka soma kiraye kirayen sallan Magrib, nan Umaimar Ke sanar da ita gobe Juma’ar k’arshen wata akwai Royal Gathering kaman yanda aka saba gudanawar duk juma’ar k’arshen wata amma saidai batasan ko rasuwar nan da akai yasa a d’aga ba... Ita kaw Muhibbah da za’a d’aga da hakan yafi mata dad’i dan harga Allah ji tai batason fuskantar yaran Sarkin a halin yanzu musamman bayan ceton rayuwarta da Mahmood yai a yau d’in gaba d’aya sai tana jin shakku can k’asar zuciyarta... Maiyasa take ji Mahmood d’in tamkar mutumin kirki ne... She needs to get her head straight... Ta lumshe idanunta a hankali had’ida tada ik’aman sallah.... ** Bayan an ida sallah a masallaci Galadima, Hakimi, Waziri da kuma Danmaliki suka had’e kansu waje guda suna kuma jajantawa juna rashin Wambai da sukai lokaci guda suna karanto masa addu’an samun rahamar Ubangijinsa... Waziri ya gyara zama had’ida yin gyaran murya “Toh kunga dai abinda ya faru da Wambai, kai tsaye bazamuce kashesa akai ba amma alamu sun nuna hakan...” Galadima ya jinjina kai yace “Wannan gaskiya ne.” Waziri yaci gaba da fad’in “Toh bazai yuwu mu zauna mu zuba idanu har a gama mana kisan d’auki d’ai d’ai a Masarautar nan bamu nad’a Sarki ba... Idan nan mance ba duk munyi ittifakin cewa Mahmooda shine zai gaji sarautar mahaifinsa....!” Danmaliki yai karaf yace “Bayan abunda ya faru na fara shakkun mik’awa Yarima Mahmood mulki... Duba da cewa Ubandoma da ake zargi da saka hannu cikin salwantan rana Wambai Hadiminsa ne... Inaga bai kamata muyi saurin yanke hukuncin mik’a masa mulki ba har sai an gama bincike kan Ubandoma...” Hakimi ya jinjina kai yace “K’warai na yarda da shawarin Mai Girma Danmaliki....” Waziri ya gyara zamansa sosai yana mai ci gaba da fad’in “Dani daku duka munsan Mahmooda bazai aikata haka ga Wambai ba... Cikin ‘yan uwansa yafi kowa cancanta ya gaji Karagar nan... Kuma shi Ubandoma har yau bai amsa cewa Mahmooda ne ya turasa gidan Wambai ba... Idan zamu adalciwa Yarima Mahmood bai kamata mu soma tunanin zarginsa da mummunan laifi irin wannan ba... Kundaiga halin dattakon da yai lokacin da Majidad’i ya kawo masa hari har cikin fada a gabanku... Mutumin da yai haka bazai yuwu ace zai cutar da wani ba... Musamman ma ace Wambai...!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Gaba d’aya masu sarautun suka shiga jinjina kansu da kalaman Waziri... Galadima yace “K’warai kuwa Waziri, Wannan gaskiya ne... Nidai a b’angare na har yanzu banida canditate bayan Yarima Mahmooda... Idan duk mun amince akan haka inaga gobe juma’a idan Allah ya kaimu mu sanar cewa rana iteyau Wato Juma’a mai zagyowa kenan za’a nad’a Mahmooda matsayin Sarki a wannan masarauta....!” Waziri ya shiga jinjina kai cikeda jin dad’in burinsu shida Giwa ya kusa cika... Nan suka soma masabaha had’ida sallama da juna kan cewa sai Sun had’u goben.... A daren Waziri ya shiga ya tadda Giwa da batun, Farin ciki kaman Ta zuba ruwa a k’asa tasha... Giwa tace “Amma wani hanzari ba gudu ba Waziri, ya kamata mu aika Ubandoma lahira dan ya riga yasan abubuwa da dama game damu...!” Waziri ya jinjina kai yace “Kar kiji komai ni zan kula da wannan ina mai tabbatar miki kafin safiya Ubandoma ya zama tarihi...!” Ya k’arashe muguwar murmushi saman yanutsattsen fuskarsa.... SameenaAleeyou📚 [8/5, 6:03 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *40* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zahra ce ta shigo sashen nasa rik’eda pain relief Ta isa jikin dispense ta tara masa ruwa a cup kana ta nufi upstairs tana kirawo sunansa a hankali... Ta d’an dakata bakin k’ofar d’akinsa tai knocking shiru babu amsa, tai kaman sau uku tana mai k’wank’wasawa take ambato Paa amma shiru babu motsinsa hakan ya bata daman d’an tura k’ofan kad’an, ta shigo da sallama amma shiru babu alamun mahaifinta a d’akin Sannan babu alamun yana bathroom..Fitowa tai ta kuma nufan d’aya d’akin nan ma shiru.... Tai tsaye rik’eda maganin had’ida fuzar da fuci a hankali “Where could he be..?!” Ta fad’i tana mai d’an k’ifta idanunta... Juyawan da zatai ta hango bayansa zaune daga can farfajiyan filin saman nasa hasken k’wan wutan lantarki ya haskaka ko ina tarau Tamkar rana, k’aramar allo gabansa saman ‘yar stand irin yanda ma’abota zane Keyi... Ta saki murmushi a hankali kana ta nufi k’ofar... A hankali take takowa tana kallon painting d’in da mahaifin nata keyi mai matuk’ar kyau cikeda k’warewa da fasaha... Kansa ya d’aga yana duban sararin samaniya yanda wata Ta baje sosai cikin gajimare lokaci guda yake kuma zana abubuwan da idanunsa ke iya gani.... Zahra

Chapter 24 of 65