mai za’ayi da irin wannan sarautar..?!”
Ba Giwa dake rarraba idanu gabansa ba harta Jamal dake daga can bayan Giwan saida yasha jinin jikinsa ya tsaya cak ya kasa ci gaba da dogara sandarsa..!
Zuciyar Giwa na bugu take furta “Sadauki ban fahimceka ba... Mai kake nufi...?!”
Sosai ya kaikaito wannan karon yana dubanta, jijiyoyin jikinsa na kuma mik’ewa yake furta “Ina nufin babu abinda zanyi da sarautar da kika nemawa ahalinki ta hanyar Malamai ‘yan tsubbu mushurikai masu kaikuga halak’a...! Maami how could you..! How could you do something like this..? How could you turn your children into criminals..!!”
Cikin rawar murya Giwa Ke furta “Mahmood ban fahimce ka ba... Mai kake nufi..?!”
Girgiza kansa kurum yake cikeda tsananin takaici, lokaci guda yake ci gaba da furta “Fu’ad told me everything... Abubwan da suka faru fourteen years back, Fu’ad ya sanar dani how you ruined our family and destroyed the life of an innocent child....! Shin Maami ina zaki kai girman zunubin da kika d’auka, kin saka yaranki sun lalata rayuwar k’aramar yarinya akan son zuciya... Kin maida yaranki ‘yan ta’adda..! Fyad’e fyad’e Maami..! Shin wace uwa ce zatai jagoranci ma yaranta su aikata mummunan laifi irin wannan... Wace irin uwace zata aikata haka Maami, Fu’ad was only a kid then amma da k’arfi saida kukasa ya aikata laifin... Ki fad’a min ina zaki kai girman zunubin nan..?!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya irin na wanda ransa yakai k’ololuwa wajen b’aci...
Giwa na girgiza kai take furta “Mahmood Fu’ad mahaukaci ne mai yasa zaka yarda dashi...! Ko a kotu ne mahaukaci baya bada shaida..! K’wayarsa ce ta sanar dashi hakan shiyasa ya sanar dakai duk wannan k’arerayi marassa asali balle tushe..! Yanzu kai a naka tunanin zan aikata laifi makamancin wannan..? Haba Mahmood ya kake abu kaman ba Babba ba..!”
Katseta yayi da fad’in “I tried not to believe him amma zuciyata ta k’i aminta da hakan...! Na yarda Fu’ad ya fad’i gaskiya sabida bayan duka wannan shekarun bai mance komai ba..!”
Sai sannan Jamal ya k’araso yana fad’in “Yaya Fu’ad was lying to you... How can you believe a psychopath like him..!”
Cikin tsananin huci Mahmood ya katsesa da fad’in “Shut up..! Rufe min baki...!! That’s because kun tilasta masa yin hauka.. You and our mother tormented Fu’ad.. Ya sanar dani yanda kayita drugging d’insa kana injecting d’insa dan kawai ku mantar dashi komai ku hanasa magana.. You’re the real psychopath here Jamal... Na zaci gaba d’aya cikinku ka fisu hankali, kullum ina maka zato mai kyau dan kafi Yazeed hankali a fuska Ta d’abi’a ashe ba haka bane, you’re the worse..! Ta yaya zaka halak’a kwanyar d’an uwanka da strong drugs, Kai kayi introducing k’wayoyi masu gusar da tunani ma Fu’ad tun yana k’arami baisan illan abunba... kawai dan ku hanasa fad’in laifin da kukayi tarayya wajen aikatawa... How could you do this to your own brother...! I can’t believe this, I can’t believe my on family can be this heartless..!!”
Kan Jamal na k’asa yawa mutumin arziki yake furta “Yaya wllhi Fu’ad cikin haukarsa ya sanar dakai haka, duk abubuwan da ya sanar dakai none of them is true..!”
“Nace kamin shiru kafin na k’araso wajen na k’arasa karya d’aya k’afar taka mutumin banza kawai...!”
Giwa na k’wak’ulo kukan k’arya take kuma k’aryata zancen...
Girgiza kai kurum Mahmood yake kana yai saurin sa kai ya fice daga asibitin dan idan yaci gaba da tsayuwa wajen zai iya mance ita d’in mahaifiyarsa ce wanda baya fata a isa peak d’in....
**
K’AUYEN GALAMBI
Jafar da Ubandoma zaune daga can wani b’angare na tsakar gidan sun kunna k’irare suna shan d’umi dashike tsakar gidan akwai yalwan fili... Ko wannen su rik’eda gasasshiyar masara suna ci suna shan d’umin wutan dan anyi ruwa garin ya d’auki sanyi sosai, Ubandoma na kuma labartawa Ja’afar abubuwan da sukaita faruwa cikin Masarautar a lokacinda yake rufe...!
Jafar sai faman murza masaran dake hannunsa yake yana hango k’uran da zai tashi idan ya saka k’afarsa cikin Masarautar... Dan yayi imani koda ace shi bawa ne duk wanda suka cuzgunawa rayuwarsa cikin Masarautar sai sun biya abinda suka masa... Ko zafin k’una hannunsa da masarar keyi bayaji sai kuma mutsuk’ata yake cikin tafin hannunsa.. Hasken Farin wata ya haske kyakkyawar fuskarsa wanda a ‘yan kwanakin da sukayi wannan K’AUYEN har ya sauya kamaninnsa na asali ya kuma bayyana... Gaban Ubandoma ya yanke ya fad’i domin kuwa harta zaman da Ja’afar yayi irinta masu mulki ne... Kardai jinin Saraki ne Giwa ta basa ya canza da d’an Bawa...! Idan kuwa hakan ne baijin Jafar zai yafe masa musamman da yaga irin tanadin da Jafarun yayiwa wad’anda suka zaluncesa randa duk ya saka k’afarsa cikin Masarautar...
Bai ida tunanin ba suka sinkayo muryar Tabawa matar Baba Nomau ta fito tana furta “Malam..! Malam kazo kaga abin mamaki...!”
Jafar da Ubandoma suka dubi juna, cikin sauri suka mik’e suka nufi yanda Mama Tabawa ke kira...
A tare suka saka kai k’asan rumfar yanda Mama Tabawa Ke haske Mahaukaciya Izzatu sai aman bak’ak’en zaren masu kama da saiwar itaciya take... Ga wasu dogayen bak’ak’en allurai masu kamanni da k’ayar beguwa tana amo dasu...
Baba Nomau da k’arasowarsa kenan hamdala ya soma yana furta “Allah ya amshi addu’armu gashi nan ta fitar da mugun k’ullin tun kafin kwanaki uku su cika... Alhamdulillahi Allah abin godiya..!”
Yana ida fad’in haka ya zauna daga can gefe saman tabarmarsa ta azara.. Ya dubi Ubandoma da Jafaru yace suma su zauna...!
Babu musu sukayi yanda Baba Nomau yace....
SameenaAleeyou 📚
*MUHIBBAH*
*70*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Tambayoyi Baba Nomau yake jero mata daki daki tana amsawa “Zaki iya tuna wacece ke, daga wace nahiyar kike..? Kuma yaya akayi kika k’are a halinda kika tsinci kanki ciki...?!”
Ta d’ago ta dubesu d’aya bayan d’aya kana ta jinjina kai a hankali, cikin tsananin sanyin murya Ta furta “Sunana Turai, ni d’iya ce ga Sarkin Benin Jamaluddeen...!” Ta d’anyi fasali sai kuma taci gaba da fad’in “Allah shi ya k’addari kasancewata a yanayin da na tsinci kaina ciki domin kuwa Bawa bai shige k’addararsa...!”
Baba Nomau ya murmusa a hankali yana mai jinjina kai yake furta “Wannan haka ne..!”
Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Amma Amintattar Hadimata wacce na aminta da ita ta zamto tamkar ‘yar uwa a gareni itace tayi sanadiyan halinda na tsinci kaina ciki..! Sabida tsananin amintaka dake tsakaninmu a wancan lokacin wasu har cewa suke muna da kamanni, kasancewar ban zab’i Hadimata ba saida na darje na zab’o mai kyau cikin Hadimaina wacce muke kusan tsara a shekare, dan tun ina yarinya ‘yar kimanin shekaru takwas na zab’o Izzatu matsayina wacce zata zamto amintattar Hadimata, harta abinci da wasanni tare mukeyi da ita koda kuwa sauran ‘yan uwanta Bayi basa k’aunar suga hakan... Saidai ni sam bai dameni ba dan tuni Allah ya jefa k’aunar junanmu cikin zukatanmu, wasu lokutan haka zan tashi daga bacci naga Izzatu rik’eda mahuci tana min fififta, sai nace mata Ta hawo gadon itama ta kwanta, tun tana tsoro har Ta daina tsoro, dai dai da ‘yar tsanata tare muke wasa da... Tayita d’aukan ‘yar tsanar tana mata kitso, wasu lokutan har tambayata take ta saka tufafi na, ni kuwa nakan ce mata duk wani abuna nata ne, kada ta damu...! Da murnanta takan saka tufafin tayita kallon kanta jikin madubi... Wata rana ne data saka tufafun ta fito dasu jikinta bayi ‘yan uwanta sukayi mata chaa har horo saida akayi mata... Tayita kuka har ta d’an ja jiki dani... Abinka da yarinta sai nace da ita ta kwantar da hankalinta itama wata ran zata zamto mai mulki idan ma tana so ni zan bata nawa mulkin mu raba...Wannan kalman da na Fad’i ashe Izzatu tana rik’edashi har zuwa girma cewa itama zata zamto mai Mulki zamu raba nawa sarautar mu biyu....Tai shiru hawaye na gangaro mata...
Baba Nomau ya nusa yace “Zaki iya tuna ko mai tayi miki...?!”
Ta d’ago ta d’an kuma dubansu kana Ta jinjina kai tace “K’warai zan iya tunawa..!” Take ta shiga jero masu bayanin yanda Giwa ta amshe mata mijinta da kuma sarautar Ta ta maida ita Baiwa a gidan aurenta...!
Ja’afar ya kasa motsawa sai duban matar yake da tsananin mamaki, ya kasa aminta abubuwan da yaji gaskiya ne Wai Giwa Baiwa ce ba Basarakiya ba, ya kasa aminta da abubuwan da yake ji na fitowa daga bakin matar nan...!
Gimbiya Turai taci gaba da basu labari
“Tin daga lokacin da Izzatu ta jefeni da muguwar asirinta na zamto banida ta cewa sai abinda tace... Bokanta ya sanar asirinta zai tasiri akaina na d’an wane lokaci, bayan wanann lokacin asirin zai karye sabida tun lokacin da aka haifeni an dafani da magunguna na bada kariya, kunsan gidajen Sarauta sun yarda da neman tsari kuma ko wanne gidan Sarauta da nasu al’adar, musamman zamanin da da ilimi bai yawaita ba, hakan yasa sam hankalin Izzatu bai kwanta ba dukda cewa banida Ta cewa a wajen kowa sai abinda ta min umarni, daidai da sunanan na asali banida iko akansa dan tuni Ta mana musayen sunaye, na kuma yi na’am da abinda tace, na soma amsa sunan Izzatu tin daga wannan lokacin, ita kuwa ta koma amsa sunan Gimbiya Turai ta k’asar Benin....”
“Kaman yanda Izzatu ta buk’ata kan cewa mijinmu bayan ya ‘yantani daga bauta ya aureni ya maidani matarsa bayan ta kyautar dani garesa matsayin tukuici, Toh sai aka barni a wancan garin yanda muka soma zama nidashi, sam Izzatu bata bari an kaini cikin Masarauta ba koda da rana guda ne...! Ina zaune a wannan gari matsayin Matar sarki kuyangarsa wacce ya ‘yanta ya kuma aura... Tunda Sarki yasa k’afa ya koma masarauta ban kuma saka shi a idanu na ba, Ina zaune a wannan garin ina zaman jiran tsammani daga ni sai Hadimata mai suna Fattu saiko mijinta mai suna Giro, suna zaune ne a wani b’angare na cikin gidan dan kula dani kaman yanda Mai Martaba yai masu umarni ya kuma ajesu a kusana..Toh muna zaune a wannan k’aramar k’auye ga laulayi da ya addabeni, dan tinda Sarki ya tafi ban kuma yin lafiya ba...! Kwatsam wata rana ina tsaka da amai saiga Izzatu tazo ta wannan gidan ba tareda rakiyar kowa ba, dan ko Hadimanta bata taho dasu ba, ta razana sosai da ganin halinda nake ciki... Tin daga nesa ta tsaya ta zuba min idanu tana duban yanda nake durk’ushe tsakar gidan shek’a amai.. Ta k’araso Ta dafa kafad’ata tace “Ke Izzatu mai zan gani, amai..! Ciki..!” Ta shiga zaro idanunta waje tana dubana.. Duk’awa tayi gefena tace “toh kina jina koda wasa kada ki tura sak’o wa mai Martaba cewa kina d’aukeda juna biyu, kinji abinda na fad’a miki...!!”
Cikin sauri na shiga jinjina kai dan idan baku mance ba na sanar daku cewa Asirin da Izzatu tamin shine duk abinda ta bani umarni na amsa mata nai mata biyayya irin yanda bawa yakema Ubangidansa, ko kusa bana mata musu...
Ta murmusa tace dani na mik’e tsaye..! Babu musu nayi yanda tace..! Ta d’aga tufafina tana duban shafeffen cikina wanda babu wani alamu, sai gani nayi tana murmushi... Wani bak’in Dutse ta manna min a saman cikin... Naji wane irin zogi ya ratsa cikin jikina tinda ta manna min wannan bak’in dutsin..!
Koda ta manna min tsugunawa nayi wajen Ina rik’e marana dake tsananin min zogi... Take naga ta juya ta bani baya wani mummunan halitta ya bayyana gefenta sanye da bak’ak’en tufafi, dariya ya kece dashi yace “Wannan juna biyu bazai fice ba sai an haifosa duniya... Kuma shine zai zamto d’ah na farko ga Sarki AbdulJabbar...!”
Giwa ta shiga girgiza kai tana fad’in “Bazai yuwu ba..! Wanann k’ask’antacciyar baiwar bazata rigani baiwa mijina Magaji ba domin kuwa ni ce nan zan kafa Mulki na a wannan Masarautar, kowa sai ya zamto yana k’ark’ashin iko na...Menene abinyi..?!”
Daga nan ban kuma jin tattaunawarsu da matsafin mutumin data shigo tareda shi ba nidai na kwanta nan wajen ina rik’e marata dake tsananin murd’a min Ina neman agaji... Can da jimawa Fattu tazo ta taddani, cikin rawar jiki take fad’in “Rankidad’e..! Lafiya kike..?! Rankidad’e ko na kira Giro ne ya nemo amalanke mu fitar dake gari mu kaiki asibiti...?!”
Girgiza mata kai nayi nace “Fattu ba sai kun fitar dani ba ki bani ruwa nasha k’ishin ruwa nakeji..!”
Cikin sauri Fattu ta kawo min ruwa nasha..! Na lumshe idanuna ta taimaka min na kwanta bisa tabarmar sak’a dake gefe..
Fattu tayi jigum tana dubana cikeda tausayawa, lokaci guda ta kuma fad’in “Rankidad’e kodai Giro yayi tattaki ya tafi Masarauta ne ya sanar da Amale halinda kike ciki..?!”
Cikin sauri na d’ago sabida tsananin tsoron abinda ka iya zuwa yazo tinda Izzatu ta haneni nace da Fattu koda wasa, ko ita ko mijinta kar sukai wannan batu wa Amale..! Fattu dai ba dan taso ba sai dan babu yanda ta iya ta amince da batu na..!
Muna nan a haka wasu lokutan haka zanyita ganin abubuwa na ban tsoro suna kawo min ziyara, a haka cikina yaketa girma har zuwa ranan da zan haihu... Wani ikon Allah ranan haihuwata Fattu bata gidan, ko ita ko Giro Babu kowa amma saiga Izzatu tafe da zungureren ciki tareda wannan mutumi matsafin, Izzatu ita ta amshi hauhuwata dukda zungureren cikin dake jikinta... Inajin kukan jariri sanda ya fito daga jikina.. Amma daga haka ban kuma sanin mai ya faru ba ban kuma farkawa ba sai a gadon asibiti a nan cikin k’auyen dan dajin da gidan yake yana da d’an nisa da gari... Na tashi ina tambayar Ina jariri na Malam asibiti sukace haka aka kawo masu ni rai hannun Allah, Allah ne ma yayi taimako an iso dani asibiti da wuri da tuni jinin jikina ya k’are.. Fattu ta tusani gaba cikeda tausayawa tana tambayar Rankidad’e ina jaririn ya akayi hakan ta kasance mai ya faru..?!”
Kuka kurum nake ban Iya ceda Fattu komai ba dan na tuna duk abinda ya faru, na tuna cewa Izzatu Itace ta amshi haihuwata...! Fattu tace Giro zai tafi Masarauta yaje ya sanar da mai Martaba..! Kuka sosai na dingayi Ina rok’on Fattu idan tana ma Allah ko Giro kada ta sanar dashi wannan al’amari..! Na tambayi Fattu ya akayi Ta kawoni asibiti..? Fattu ta sanar dani tana can gona itada Giro ta dawo gida kai masa abinci nan Ta taddani a halinda nake ciki, tayi gaggawan fitowa gari ta sami masu amalanke suka taimaka suka kawoni asibiti...!”
Gimbiya Turai ta lumshe idanunta wasu hawayen suka kuma zubo mata...
Daidai da Jafar da Ubandoma suma hawayen ne suka zubo masu, harta Mama Tabawa itama hawayen take da jin irin wannan al’amari....
Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Muka rufe wannan batu nida Fattu babu wanda yaji tinda dama Sarki baisan da labarin juna biyun ba, bayan wani lokaci mai tsawo Mai Martaba ya waiwayeni, baida labarin ya barni da ciki har na haihu kuma har na rasa abinda na haifa...Ashe a wannan lokacin juna biyun da Izzatu kedashi shine ya janye hankalinsa har ya mance da ni ya bada hankalinsa kacaukam akan Izzatu da cikinta...Bansan ya akayi ya kuma waiwayoni ba, nadaiga yana zuwa wajena akai akai, dukda babu wani Sabo a tsakaninmu yakan bani labarin d’ansa mai suna Mahmood wanda matarsa Basarakiya ta haifa masa... Saidai nayi murmushi amma bana iya cewa komai...
Bayan wasu shekarun yaci gaba da ziyartata, amma ban sake koda b’atan wata bane sannan da alama Izzatu ma bata kuma haihuwa ba tin d’anta mai suna Mahmood da yace ta haifa masa, ya kasance Mahmood shine kad’ai dan Sarki AbdulJabbar wanda ya d’auki son duniya ya d’aura masa, a nan a haka kwatsam ya sanar dani matarsa ta haihuwa ta kuma haifa masa wani d’ah ya saka masa suna Yazeed, Yazeed ya taso ya fara wayo shima, saidai har lokacin magana Mai Martaba bai wuce Mahmood, da matuk’ar wahala kaji ya ambato k’aramin d’ansa mai suna Yazeed, nikam har na mance da haihuwa domin kuwa shekarun da d’an yawa tun bayan dana rasa abinda na haifa daga farko, a tsakanin wannan lokacin nima kwatsam sai na soma laulayi... A lokacin da yazo min da labarin Gimbiya ta haifa masa d’ah namiji ya kuma saka masa sunan mahaifinta Sarki Jamal a lokacin ashe nima inada ciki k’arami ba tareda na sani ba... Naci kuka sosai jin Izzatu ta kuma haihuwa an sakawa yaron sunan mahaifina Sarki Jamaluddeen saidai banida ikon fad’iwa Sarki AbdulJabbar komai... A ‘yan kwanakin da Mai Martaba yayi wajena nan ya fahimci nima ina d’aukeda juna... Toh sai yayi dogon zango wajena bai koma masarauta ba, ashe hankalin Izzatu ya tashi matuk’a ganin Sarki bai waiwayeta ba dukda sabon jariri da take dashi, koda Mai Martaba ya koma sai ya sanar da ita juna biyu gareni da alama Allah ya amshi addu’arsa gashi bayan duk tsawon shekarun nan Izzatu ma zata haifo masa Magaji Wato Izzatu ni kenan kaman yanda ya sanni... Giwa Ta shiga damuwa ashe ciki ne dani kuma har ya fito sam bata kawo zan kuma haihuwa da Sarki ba dan rata ne sosai tsakani tinda da ace jaririn dana rasa yana raye da ya kusa isa munzanin k’aramin matashi, lokacin jaririnta yayi k’wari sosai dan yakai watanni kusan takwas, ta barsa wajen masu kula dashi tazo ta ga halinda nake ciki, saidai wanann zuwan da zatayi batazo da rakiya matsafinta ba, ga dai ciki jikina har ya fito babu halin ta salwantar da cikin tinda Mai Martaba ya sani... Sosai na hango tashin hankali tattareda ita, ta tanbayeni komai gameda cikin, babu abinda na b’oye mata harta asibiti da Mai Martaba ya kaini da kansa saida na sanar da ita, ta dinga sakin huci jin irin kulawa na musamman da Sarki Ke bani sabida cikin... Ta tambayeni yaushe akace zan haihu a asibiti..? Babu musu nan ma na sanar da ita...! Duk wannnan abinda ake Hadimata na tsaye bayan k’ofa rik’eda yarinyarta mai suna Aliya ‘yar shekaru uku a duniya, dan lokacin Hadimata Fattu Allah ya azurtasu d samun yarinya d’iya mace kuma har Ta shekaru hud’u a duniya...!”
Ubandoma da gumi Ke ci gaba da tsartsafo masa yace “Fattu da d’iyarta, Dama Fattu Hadimarki ce..?!”
Gimbiya Turai ta jinjina kai tace “Fattu Hadimata ce wacce Mai Martaba ya ijeta da mjinta matsayin masu kula dani...!”
Gimbiya Turai ta nusa taci gaba da fad’in “Fattu taga duk abinda ya faru kan idanunta yanda Izzatu ta tasani gaba da tambayoyi kuma ban b’oye mata komai ba na sanar da ita... Hankalin Fattu sosai ya tashi daga nan yanda take lab’e... Kukan yarinyarta shine ya janyo hankalin Izzatu ta dubeni tace wacece wannan..? Nace da ita Hadimata ce mai Martaba ya bani...! Giwa ko ince Izzatu ta tsare Fattu da d’iyarta Aliya da idanu... Bata masu dai komai a wannan lokacin ba saidai Ta gargad’eni cewa kada Mai Martaba yasan ta kawo min ziyara..! Na jinjina mata kai nace bazai sani ba... Toh ko bayan data tafi Fattu taso mu sanar da Mai Martaba cewa matarsa ta kawo min ziyara amma na gargad’i Fattu nace da ita kada ta sanar da mai Martaba ko mijinta ma kada ta sanar dashi.. Abin sosai ya dami Fattu dan haka nan kawai bata aminta da ziyaran da Giwar Amale ta kawo min ba na bazata... Toh a haka Mai Martaba yakan kawo min ziyara har dai lokacin haihuwata yazo, a lokacin haihuwata banga Mai Martaba ba, baizo ba saidai kwatsam naga Izzatu tace min Mai Martaba ya turota ta amshi haihuwata... Ta bani wani ruwan magani tace nasha shine zai d’aga min nak’uda..! Babu musu na amsa ruwan maganin na shanye kaman yanda Ta umarceni, ai kuwa Ina shan ruwan nan nak’uda ya tashi gadan gadan, na haihu ban haihu ba ban sani ba, tin daga wannan lokacin ban kuma sanin wacce duniya nake ba sabida tsananin azaba, bani a cikin hayyaci na, farkawa kawai nayi na ganni gefen Fattu dake kuka rungume da jariri... Cikin d’imauta naceda Fattu ina jaririna..! Fattu na hawaye ta mik’o min shi tace dani jaririna baizo da rai ba...! Naci kuka sosai, na rungume gawan jaririna ina hawaye.... Giro da wasu mutanen gari su sukaima jaririna sutura aka rufesa... Bayan faruwan wannan al’amari da kad’an Mai Martaba yazo ya tadda na haihu yaro baizo da rai ba... Sosai shima ya shiga damuwan rasa jaririn da mukai... Ashe abinda ya hanasa zuwa ya kwanta jinya ne na d’an wani lokaci wanda har bai fita koda Fadarsa ne, yana warkewa kuwa ya taho gareni dan duba halinda nida Jaririna muke ciki...! Tin daga bayan wannan lokaci ban kuma samun haihuwa ba, tun bayan rasa jaririna da nayi...!”
Muryar Ubandoma suka sinkaya yana fad’in “Ki yafeni Rankidad’e..! Kimin aikin gafara Ranki dad’e..!!” Cikin kuka yana mai zubewa saman gwiwoyinsa yake furta wad’annan kalamai...
Gaba d’aya kallonsu ya koma kan Ubandoma dake duk’e gaban Gimbiya Turai yana kuka yana neman gafara....!
Baba Nomau ne ya dafa Ubandoma yace “Kar ka katseta ka dakata ta ida sanar damu dukkan abinda ya faru gudun kada mu fad’a wani labarin..!”
Ubandoma ya jinjina kai har lokacin yana duk’e yana hawaye...
Gimbiya Turai taci gaba da fad’in “Bayan kaman shekaru biyar da faruwan wannan al’amari wasu fatake suka tsaya a garinmu suka nemi a taimaka masu da ruwan sha a nan gidan da aka ajeni...! Sun razana sosai sanda sukayi tozali dani a cikin gidan...
D’aya daga cikin rundunar fataken ta saki Kwanun shan da aka kawo mata ruwa ciki ya zube sabida tsananin tsorata da tai da ganina... Cikin rawar murya ta ambato sunana “Gimbiya Turai..!” A razana nake sanar dasu bani bace...! Nayi saurin guduwa d’aki ina kuka... Fattu Ta bisu da kallon mamaki tana kuma mamakin jin sun ambaceni da Gimbiya Turai...
Fattu ta k’arasa garesu tace “Bayin Allah ko akwai wani abu ne..?!”
Matar data ambaceni da Gimbiya Turai tace “Mu Fatake ne daga can Nahiyar Benin, wannan matar data gudu d’aki d’iyar Sarkin k’asarmu ne wanda bayan aurenta da kad’an mahaifinta Sarki ya mutu, dangin dangau sukai qaqa gida suka haye gadon mulkin mahaifinta sabida d’an uwa d’aya tak gareta, kuma a lokacin da Sarki mahaifinta ya rasu d’anuwanta yana k’arami bazai iya yak’in neman mulki ma kansa ba, dangin mahaifiyarsa suka d’aukesa sukai nesa dashi, kwanakin baya ya dawo k’asar Benin yana tambayar Sarkin wane nahiya ne ya auri ‘yar uwarsa dan a halin yanzu ya girma har ya zamto Magidanci.. Ashe ‘yaruwasa tana nan a wannan Nahiya, tabbas zamu koma masa da labari..!”
Fattu dai saurarensu kawai tayi har suka gama shan ruwan da zasu sha suka d’auki hanya....
Bayan sun tafi Fattu ta shiga k’wank’wasa min k’ofa tana sanar dani Sun tafi... Na fito illahirin jikina rawa yake... Na mance inada d’an uwa sunansa Alfah...! A lokacin da wad’Annan Fataken suka ambaci Alfah sai na tuna shi, take naji ina son sanar da Mai Martaba duk abinda ya sameni, take naji kaman an sauk’e min wani dutse mai nauyi a k’irjina, tsoron sanar da Mai Martaba halinda Izzatu ta jefani ciki duk sai naji kaman an yaye min lokaci guda... Na sanar da Fattu komai duk abinda ya faru..! Fattu ta dinga aljabi tana mamakin yanda Izzatu ta canza kanta dani.. Nan naga kukan Fattu ya kasa tsagaitawa..! Na dafa Fattu nace “Fattu akwai wani abu ne..?!”
Fattu na kuka take cedani “Rankidad’e tabbas na yarda matar nan zatayi duk abinda kikace domin kuwa Jaririn da kika tashi kika gani matsayin d’anki ba naki bane... Ina lab’e akan idanuna Ta canza jaririnki da gawa.. Naji tsoron yin magana ne a matsayi na na baiwa tinda banida shaidu babban magana ne da ya shafi matar Sarki wanda ban isa nayi jayayya da ita ba... Shiyasa kika tashi kika ganni rungume da hajaririn ina kuka... Rankidad’e duk yanda akayi jaririnki yana nan a raye.. Watak’ila Giwa ta b’oyesa a wani wajen... Kuma zai iya yuwuwa cikinki na fari kin haifa.. Zai iya yuwa itace ta salwantar da jaririnki na farko..!”
Ubandoma dake hawaye jinjina kai yake yana furta “Tabbas inada masaniyan kan jaririnki na biyu kuma yana nan a raye..!” Yayi maganar cikin rawar murya...
Gimbiya Turai ta share hawayen da suka zubo mata kana taci gaba da fad’in
“Nida Fattu muka yanke shawarin idan d’iyar Fattu ta dawo daga makarantar Allo Giro ma ya dawo daga Kasuwa zamu tattara mu d’unguma mu tafi Masarauta dan mu sanar da Mai Martaba halinda ake ciki tunda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 47 Chapter of 65