Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kana tayi d’auri wanda ake turosa gaban goshi... Ya salam ita da kanta tasan tayi kyau Masha Allah.. Alkyabba mai ruwan zinari ta rufa kan sequence material d’in wanda shi kad’ai ma d’aukan idanu yake ga kuma alk’yabbarta... Ta feshe jikinta da turaruka masu natsettsen k’amshi kana ta fito.. Daidai da hadimarta saida ta shaga da kallonta.. Ta risina tace “Ki gafarceni Rankidad’e.. Kin k’ara kyau fiyeda kullum...!” Muhibbah ta murmusa kad’an tace “Babu komai Hasiya, muje kimin rakiya zuwa k’ofa.” Hadimar ta kuma risinawa cikeda girmamawa tace “Toh Rankidad’e..!” Muhibbah tai gaba Hadimar na biyeda ita.. Har k’ofan sashensa tai mata rakiya kana ya bata umarnin komawa... Dikda zuciyarta dake tsananin bugawa hakan bai hanata daurewa ta nufo cikin parlorn kanta a k’asa sallama saman bakinta... Daga nan yanda yake zaune ko k’yafta idanunsa bai iyayi, saima tsarkake mahaliccin wannan kyakkyawar halitta dake nufosa da yake... Tin daga yatsun k’afafunta yake duba har izuwa fuskarta.. Ita kaw da k’yar take takowa dan tasan babu shakka idanunsa akanta yake, sai had’e hanya take sabida yanda zuciyarta ke tsananta bugu, hakan sai ya zamto mata tamkar wani salo ne na tafiya... Da k’yar ta iya k’arasowa cikin parlorn ta risina gaba garesa had’ida baza alkyabbarta a k’asa irin yanda masu mulki keyi... Dak’ik’ai suka shura kaman bazaice komai ba sai gani tayi ya mik’e tsaye, zuciyarta taci gaba da bugawa tana tinanin Toh mai kuma ya mik’arsa tsaye... Gabanta ya k’araso ya tsaya, zuciyarta naci gaba da tsinkewa, ga tsananin mamakinta hannayenta guda biyu taga ya mik’o mata... Ta d’ago idanunsa masu haske wanda kwalli ya k’ara masu haske tana dubansa dasu... Da gaske hannayensa yake mik’a mata... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa tana tinanin Ta mik’a masa nata hannayen ne kokuwa, k’in mik’awar ka iya janyowa ta fad’i jarabawarta tinda duk abubuwan nan da take cikin jarabawa ne.. Ta d’ago hannayenta a hankali ta mik’a saman nasa, ji tai ya rik’e hannayen nata cikin nasa, ya mik’ar da ita tsaye a hankali kana suka soma takowa a jere.. Zuciyarta bata daina tsinkewa ba har saida ya k’araso da ita gefen kujerar da yake zaune bisa ya zaunar da ita... “Yanzu zan amsa gaisuwarki..” ya fad’i yana mai dubanta... Ta murmusa kad’an tace “Na zaci ba’a gaisar da Sarki a saman kujera..!” Cikin sigan wasa tai maganan amma sam bata hango alamun raha saman fuskarsa ba.. Ta had’iyi sauran kalaman nata tana tinanin kardai tayi abinda zaisa ta fad’i jarabawarta.. Lokaci guda ta tsime ta sadda kanta k’asa tana gaishesa.. Ya amsa a tak’aice daidai sanda Jakadiya ta nemi izinin shigowa parlorn... Mahmood ya bata izini, ta shigo ta risina gaba garesu tace idan an bata izini zata gabatar da girkin Gimbiya... Mahmood ya kuma jinjina mata kai yace anyi mata izini... Ta mik’e ta fice tana godiya... Jim kad’an Ta shigo tareda wata Hadima rik’eda parantin.. Jakadiya tai mata nuni da yanda zata ajiye.. Hadimar Ta isa ta ajiye tana mai kwasan gaisuwa daga garesu... A tare Hadimar da Jakadiya suka nemi izinin fita... Mahmood ya zauna saman darduma irin zaman da ake na cin abinci, Muhibbah ta k’araso cikin tsanaki tana serving d’insa, duk wani motsi da zatayi idanunsa na kanta... A haka ta ida jera masa komai Ta koma gefe saman Darduman ta zauna... Saida wasu dak’ik’ai suka shura kafin ya d’auki spoon ya d’ebo abincin da Bismillah yakai bakinsa still idanunsa akanta, itama wannan karon idanu ta d’an d’ago tana dubansa dan taga kalan expression d’in da fuskarsa zai bada... Zuciyarta taci gaba da tsinkewa ganin ya bar abincin cikin bakinsa shi bai tauna ba shi bai had’iye ba... Idanunta suka firfito tana fad’i cikin zuciyarta.. Shikenan k’ila abincin ya bada taste maras dad’i ne dan idan bata mance ba ko tasting abincin batai ba... Taga ya had’iyi first spoon da k’yar, jikinta a mugun sanyaye take ayyanawa cikin zuciyarta shikenan na fad’i.... Jakadiya ce ta nemi izinin shigowa.. Tana shigowa ta risina ta gaidasu... Lokaci guda taci gaba da fad’in “Allah shi taimakeka abincin Gimbiya ya zaga cikin Fadah kaman yanda yake a al’ada... Kuma..!” Ta d’anyi shiru kaman bazatace komai ba, Muhibbah na kuma zaro idanu tana dubanta... “Ina sauraronki Jakadiya.. Kuma mai..?” Jakadiya ta murmusa tace “Mafi rinjaye Sun yana hasalima ba’a sami wad’anda suka kushe wannan girki ba... Masarauta tayi dace Rankaidad’e hannun Gimbiya mai Albarka ne...” Muhibbah bata San sanda Murmushi mai kyau ya kufce mata ba, harda ‘yar sauk’e ajiyan zuciyarta... Shikaw yai mata K’uri yana kallon yanda farin ciki ya mamayeta... Duban Jakadiya ya jinjina kai a hankali kana ya Bawa Jakadiya izinin tafiya... Har lokacin Muhibbah bata daina sakin murmushi ba, Ta d’an tsuke fuska kad’an ta waigo tana dubansa had’ida d’aga masa gira guda alamun an wuce wannan... Spoon d’aya zuwa biyu yai ta nemi izinin tafiya... Ya jinjina mata kai alamun yayi mata izini, saidai tana isa k’ofa ta sinkayo muryarsa yana furta “And where do you think you’re going Your highness..?!” Ta tsaya cak had’ida lumshe idanunta zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Izuwa lokacin ya mik’e ya nufo yanda take tsaye hannayensa hard’e Ta baya ya d’an kwanto da hab’arsa saitin kafad’arta, cikin sigan rad’a yake furta “Find some clues that will lead you to the next part of the exam..!” Yana ida fad’in haka ya juya ya nufi upstairs cikin takun k’asaita... Muhibbah ta bi bayansa da kallo har ya shige had’ida fuzar da huci kad’an....clues dazasu leading d’inta... Tai tsaye tana k’arema parlorn kallo tana tianin wasu clues kenan... A hankali Ta shiga zagaye parlorn tana neman clues d’in... Harta pillows saida ta d’add’aga... Can idanunta suka sauk’a gefen yanda ya zauna, akwai remote control a wajen... Tai saurin k’arasawa ta d’aga remote d’in dan taga kaman akwai takarda k’asan remote d’in Aiko takarda ce a ninke, ta warware tana karantawa an rubuta, _Escalera.._ (Staircase) Ta rik’e takardan tana juyawa tana nanata kalman ya mata kama da yaren Spanish.. Toh mai Escalera yake nufi.. Ta d’an dafe kanta tana tunanin words d’in data sani a yaren bata fahimci menene ba... Amma kuma ya mata yanayi da escalator... Ta juya hagun da dama bataga alamun escalator ba amma akwai matakalan bene... Cikin sauri ta nufi matakalan benen tana dubawa... Nan jikin staicase taga anyi drawing arrow ya kalli sama an rubata a k’asan arrow d’in _Sigue moviéndose recta_ (Ci gaba da tafiya a mik’e) Taita nanata kalaman dan akwai words d’in data fahimta hakan yasa ya mik’e taci gaba da hawa benen... Tana cikin cikin tafiya taji kaman Ta taka wani paper, tai saurin duk’awa ta d’auki paper d’in ta warware an rubuta _Sigue tu izquierda_ (Ki bi b’angaren hagunki) Nan ma Kalmar izquierda ta fahimta yana nufin hagu, take ta soma bin wannan b’angaren tana k’arema ko ina kallo ga d’akuna a jere... Nan ta kuma cin tuntub’e da wani takardan.. Ta duk’a ta warware tana karantawa an rubata _Segunda a la última habitación_ (D’aki na kusa da k’arshe) Wannan yafi ko wanne bata wahalan fahimta dan bayan sunan d’aki data sani batasan wani kalma ba kuma dake cikin takardan sannan d’akuna da dama a wajen batasan wanne yake nufi ba... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana kuma nanatawa, zuciyarta tace kawai ta bud’e duk wanda ya kwanta mata... Ta shiga bin k’ofofin d’akin da kallo tana tinanin wanne zata bud’e tinda idan ta bud’e ba wanda yake nufi ba k’ila ta fad’i jarabawarta.. Kalmar k’arshe ne ya fad’o mata dan haka ta nufi k’ofa na k’arshe har bata tura taga d’akin dake gefe gefe da wannan key d’in jiki yana d’an kad’awa a hankali alamun ba’a jima da bud’ewa ba.. Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai furta Allah yasa daidai tayi.. Da Bismillah ta tura k’ofar d’akin... Tai tsaye tana mai k’arewa d’akin kallo... A hankali Ta soma takowa cikin d’akin tamkar mai gudun kar aji motsinta, taita yaba kyaun d’akin da tsarinsa... Can saman gado ta hango wani kwali ajiye... Ta k’arasa a hankali tana duba kwalin... Jikin kwalin taga an rubuta open... Ta saka hannunta a hankali tana d’aga marfin k’aton kwalin... Cikin tsanaki take zaro abindake linke cikin kwalin wanda rigace ta bacci ‘yar yaloluwa mai siririyar hannu... Ta zaro idanunta waje tana kuma juya rigar mai kalar ja... Cikin girgiza kai tana mai kuma juya rigar take furta “No.. I’m not wearing this... I’m done playing your games Rankaidad’e..! bazanci gaba ba kuma.” Ta k’arashe tana mai jifa da rigar saman gado... But idan bata k’arasa jarabawarta ba shikenan Rankaidad’e zai ajeta gidan tsaffin matan sarakuna... She can’t afford to fail the exam..Bata da wani zab’i da ya wuce taci jarabawar nan komin wahalarta... Ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali kana ta janyo rigar ta nufi wani hanya dake daga can gefe cikin d’akin wanda tayi zaton closet ne... Canza kayan jikin nata tai tana mai duban yanda rigar ta zauna jikinta wanda ita kanta kunyar kanta taji...A gefen mirror taga an rubuta da hausa wannan karon “D’aki na k’arshe...” Ta furta cikin rarrabewar kalma...Duban kanta Ta kumayi jikin dressing mirror kana ta janyo Alkyabba ta rufa ta tukukuye jikinta cikin Alkyabbar, Allah ya gani bazata iya tunk’arar Rankaidad’e da ‘yar wannan rigar ba, ta fito ta nufi d’akin k’arshe.. Zuciyarta sai tsinkewa yake... Tafi minti uku masu kyau tana tsaye bakin k’ofa tana zullumin shiga cikin d’akin.. Sai tazo kaman zata shige sai ta fasa... Daga k’arshe dai tai ta maza ta murd’a handle d’in sallama saman bakint kanta a k’asa... Ta ida shigowa tana mai ayyana kyau da tsari na d’akin.. Tai tsaye tana faman waige waige dan bataga kowa ba... Saitin kunnenta ta sinkayo muryarsa yana furta “I don’t remember asking you to wear this Alkyabba your Highness..” Yai maganar cikin wane irin salo Ta rintse idanunta a hankali tanajin tururin numfashinsa cikin kunnenta,.. Murya na rawa take furta “But Rankaidad’e..!” “Shiiiii” ya d’aura yatsarsa guda saman labb’anta, har lokacin tsaye yake Ta bayanta “No buts.. Remember the rules.... Take it off..!” Ya fad’i cikin tsarewa.. Ta Ware idanunta a d’an zabure... Kaman mai shirin kuka take furta “Rankaidad’e ni dai dan Allah wllhi kunyar nake..!” Taso basa dariya yanda tayi maganar amma ya gimtse yace “Do you want to fail the exam..?” Idanunta a rufe take girgiza kai alamun bataso ta fad’I jarabawar... “Then take it off..!” Ya kuma fad’i babu wani walwala... Rintse idanunta kurum tai tanajin sanda alkyabbar Ke k’ok’arin isa k’asa... Zuciyarta taci gaba da harbawa hawayen na k’ok’arin ciko idonta... Tai k’ok’arin kai hannunta zata rik’e alkyabbar taji ya kamo hannun nata cikin nasa...har lokacin idanunta a rintse suke ta kasa bud’esu... Tana jin hucin numfashinsa saitin kunnenta yana rad’a mata “You’re more beautiful like this..!” Ta ware idanunta da sauri tana jin abin wani irin bambarak’wai Wai Rankaidad’e Ke furta wad’Annan kalman... Ganin yana k’ok’arin kaikaito da jikinta su dubi juna ya kuma sanyata saurin rintse idanunta...Sosai taso basa dariya yanda ta tamke idanun nata da k’arfin gaske... Ya murmusa da gefen baki yana mai duban fuskar nata wanda har lokacin light make up d’inta na nan, d’an bakin nata shi yafi komai tafiya dashi kafin ya soma sauk’o da idanunsa yana duban yanda ‘yar rigar ta zauna cas a jikinta... “Open your eyes..!” Kasa bud’ewa tai saima dad’a tamke idanun da tai... Ya d’auki lokaci sosai yana k’are mata kallo kafin ya bud’e murya yace “Kinsan idan baki bud’e idanun nan ba zamu koma daga farko komai ya rushe..?” Zumbur ta bud’e idanunta had’ida waresu tar saman fuskarsa... Kallon kallo suke ma juna zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Tamkar wacce aka zabura cikin rawar murya take furta “I think I’m hungry your Highness.. Can I please go get something downstairs..!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Saida dak’ik’ai suka gifta ya bud’e murya yace “So bakici that spicy food da kika bani ba...?!” Ta d’an dubesa a razane, shi d’inma ita yake duba fuska a tsare, lokaci guda yaci gaba da furta “Does the Queen know that har yanzu ina jin yajin a bakina.. I can’t get rid of the taste..” Ya k’arashe yana mai kuma tsareta da idanunsa masu matuk’ar firgitata.. Ta d’an kauda kanta gefe tana dariyar mugunta a hankali, ashedai abincin yaji yayi shiyasa Rankaidad’e ya kasa had’iyewa at first.. Yayi just one spoon ya ajiye.. Ahtoh mai yake expecting an tara mata girkin gayya... Ya gode Allah ma da ba gishiri bane.. Itakam saidai ma tace Allah k’ara alhakinta ne ya kamasa.. Ya tallafo fuskarta yana furta “Dariya kike...?” Ta girgiza kai kad’an had’ida sadda kan nata k’asa har lokacin bata daina murmushi ba sai kuma tace “Wai gani nayi Sarki bai kamata yaji zafin yaji ba..” Ya saka hannunsa guda a kunkuminta ya d’an janyota zuwa jikinsa da hannun nasa “Why..? Is he not human..?” Ya fad’i yana kasheta da wane irin duba wannan karon.. Dukda tsananin tak’ura da tai hakan bai hanata furta “Sabida shi Sarki ne.. Baijin zafin komai... Baka tab’a jin tarihin Sarkin da aka kulle yatsarsa a mota ba bai magana ba har saida suka isa yanda zasuje aka bud’e yatsar nasa.. Da kuma Sarkin da kunama ya cijesa ya take kunamar ba tareda yaji zafin cizon ba...” Tinda Ta soma magana yake duban yanda bakin nata Ke motsawa a hankali, baisan ta iya zuba surutu haka ba... Ta cika masa kunne da surutu bata ankara ba taji ya manne bakunansu waje guda... Tanzaro idanu waje tanajin bak’on Al’amarin da Rankaidad’e keyi... Saida suka jima cikin yanayin kafin ya cire bakinsa a hankali yana jin yanda ta kwantar da kanta cikin k’irjinsa sabida tsananin kunya da ya dabaibayeta... Cikin sigan rad’a yake furta “You talk too much...!” Lokaci guda tsakala yatsunsa cikin nata ya soma janyotaya suka nufi tapkeken gadon nasa ta alfarma... Binsa kurum Muhibbah take tamkar rak’umi da akala... Tana gani ya nufi wani d’an madaidaicin fridge ya d’auko farm fresh ya mik’a mata “Drink this..!” Ta mak’e kafad’a tace “I’m not hungry anymore... I just want to sleep, na gaji sosai, please ka k’yaleni na tafi..!” Ta k’arashe cikeda shagwab’a... Hab’arta ya tallafo yana mai k’ura mata idanu lokaci guda yake furta “Yau daren jarabawarki ne Rankidad’e, babu bacci...!” Idanunta da sukai rau rau take dubansa dasu, bata kuma fahimtar abinda Ke wakana tsakaninsu ba cikin wane irin salo da ya jefata shakkun anya da Rankaidad’e take tare kokuwa dai an canzasa ne... Illahirin jikinta ya d’auki rawa, yanayi ne da ya jefata cikin tunanin abinda ya faru da ita shekaru gomasha hud’u ba... Hawaye suka shiga gangaro mata, ta soma shid’an numfashi tana tuno sanda suka keta mata tufafi sukaci zarafinta... Wane irin k’ara ta saki tana mai janye jikinta had’ida tak’urewa waje guda hawaye na kuma ambaliya a fuskarta.. Cikin sauri Mahmood ya rungumota cikin jikinsa yana k’ok’arin calming d’inta “Is ok.. Kiyi shiru kinji... Ya isa bazan miki komai ba..!” Ya d’anyi fasali yana mai kuma shafa bayanta a hankali yanajin yanda take shan zuciya alamun tsoro da tashin hankali... Yaci gaba da lallashinta yana furta “Until you’re ready..!” Ya kwantar da ita a hankali had’ida rik’eta sosai cikin jikinsa bai daina lallashin nata ba.. Yanajin yanda tai lak’was a jikinsa zuciyarta naci gaba da bugawa, A haka ya janyo masu bargo ya rufa yanajin yanda zuciyarta Ke tsananin bugawa kusan tare tare na nasa bugun zuciyar...Idan yace zai tab’a yafe masu kan abinda suka aikata wa Muhibbah Tabbas yayi k’arya... Yana jin wane irin zogi da rad’ad’i cikin zuciyarsa wanda bazai iya misaltuwa ba... Gaba d’aya sun cancanci duk wani misfortunes da suke fuskanta... Ya lumshe idanunsa a hankali yana mai shak’an k’amshin sumarta... A haka bacci b’arawo yayi gaba da su... ** Safiyar Washe gari koda Ta farka bata gansa a gefenta ba, saidai taga takarda aje gefe yanda ya kwanta da red rose saman takardan, Tai saurin janyo takardan tana warwarewa... _Buenos dias su alteza_ (Barkada safiya Rankidad’e) Ina tayaki murnan cin jarabawarki zagayi na farko... Murmushi saman fuskrta ta ida karantawa Wanda ita kanta batasan daga yanda murmushin ke zuwa ba, a hankali ta shafe fuskarta tana tuno abubuwan da suka faru daren jiyan... Kaman dai ba Rankaidad’e ba... Ta sauk’e fuci a hankali tana tuna sauranta kwanaki biyu... Tana nan zaune tana sakin murmushi a hankali Ta hango saitin kaya aje daga gefe.. Ta mik’e ta nufi yanda kayan yake tana duba, shima takarda ne aje saman kayan an rubuta _De rey a su reina_ (Daga Sarki zuwaga Sarauniyarsa) Tabbas Ta fahimci kalmar Sarki da Sarauniya a wajen.. Ta kuma sakin murmushi tana duban tufafin wanda Sarkin nata ya ajiye mata domin tai masa kwalliya cikinsa... A hankali take furta “Yau naga wane irin jarabawa ni Muhibbah wanda ake maka da yarenda baka iya ba..!” SameenaAleeyou📚 [10/2, 12:37 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *82* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Saida ta ida shiryawa tsaf kafin ta fito tana k’arema sashen kallo, wani k’ofar glass ta gani daga can center yana bud’e gaba d’aya, lokaci guda taji tabi wanann k’ofar taga sararin waje... Cikin taku mai cikeda natsuwa ta nufi wannan k’ofar... Tai tsaye tana kallon frames d’in dake aje wajen jeri jeri wanda Mahmood ya zana... Dangin zanen k’oramu bishiyoyi da dai abubuwa masu ban sha’awa had’ida jefa natsuwa cikin zuciya idan kana dubansu... Taci gaba da takowa a hankali tana mai kallon zanen, babu wanda yafi tafiya da tinaninta kaman wani zane da yakeda yanayi da gidan sarauta.. Ta isa jikin zanen tana tuna Taswiran da ya zamto mabud’in sirrin su Giwa a garesu... Ta jima sosai tana duban zanen kafin Ta sinkayo muryar Zahra ta shigo a guje Ta rungumeta tana fad’in “Tia, good morning, I’m glad I found you here..! I told Aunty Umaima you and Paa loves each other so much..!”Tai maganar suna rungume da juna Muhibbah ta murmusa kad’an kana ta janyo hannun Zahra suka zauna saman wasu k’anan kujeru da aka k’awata wajen dasu.. Zahra bata daina murmushi ba take duban Muhibbar lokaci guda take ci gaba da furta “Zanfi kowa jin dad’I idan kika zama matar Paa d’ina.. Coz I know he loves you.. So much..!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta... Ita kuwa Muhibbar har lokacin bata iya tanka Zahra ba saima k’urama beautiful art works d’in Mahmood idanu da tai... Zahra ta dubeta taga abinda idanunta Ke duba.. A hankali ta murmusa kana taci gaba da furta “You know, Paa loves to paint.. Especially when he’s in a good mood.. Ta haka nida Maama muke gane idan wani abu na damunsa back then in Spain.. And ever since Maama passed away ya daina painting.. Har sanda muka dawo k’asar nan... Sai bayan kin shigo rayuwarmu Paa yaci gaba da painting.. Tia inada tabbacin kece sanadi, you’re the one who inspired him again... Please don’t leave my Paa shid’in masoyinki ne da gaske..!” Ta k’arashe idanunta na rau rau... Cikin sanyin jiki Muhibbah ta kamo hannunta guda tace “Zahra don’t you think this is something your Paa and I should decide..” Cikin rawar murya Zahra ta katseta da fad’in “I know I shouldn’t interfere, but my Paa has been through a lot... Baki tunanin ya cancanci Farin ciki... Please don’t break his heart..!” Muhibbah ta kuma kamo hannayenta tace “Zahra kalleni..!” Zahra ta d’ago idanunta masu d’igan hawaye tana duban Muhibbah wacce itama tuni k’walla sun ciko idanunta, lokaci guda taci gaba da furta “ Your Paa doesn’t love me, bai tab’a fad’in haka ba.. Aurenmu K’addara ne..!” Cikin sanyin jiki Zahra tace “But I know he does, ta yuwu bai furta ba.. But as they say actions speak louder than words...” Murmusawa kad’an Muhibbah tai tana mai duban yarinyar kana ta rik’e hannunta cikin nata, saida ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali taci gaba da fad’in “There are some points in life da zaka zamto baka da zab’i... Sadaukarwa shine zai zamto zab’inka... You might be too young to understand all that I’m telling you now, but banida zab’in da ya wuce na fad’a miki.. Inada tabbacin akwai lokacinda zaki fahimci abinda nake nufi...!” Zahra na hawaye take girgiza kai alamun k’in amincewa lokaci guda take furta “No Tia... Maybe har yanzu bansan mecece soyayya da kamanninta ba.. but We both know that you and Paa loves each other.. You can’t deny you love him... Maiyasa zakiyi sadaukarwar da zai cutar dake...?” Muhibbah na hawaye take furta “Bazaki tab’a fahimta ba Zahra duk yanda zan so na fahimtar dake...!” Zahra ta girgiza kai tace “But you’re married to my Paa now... You’re his wife, you’re not going anywhere right..?!” Cikin tsananin sanyin jiki tai maganar Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tace “Only for three days Zahra.. After three days shikenan your Paa and I will be separated... Nasan bai kamata na sanar dake wanann ba, but banida zab’i, bazaki k’yaleni da tambayoyi ba... Zahra nida mahaifinki munyi yarjejeniya.. Our marriage will only last for three days...!” Ta k’arashe cikin rawar murya.. Da tsananin mamaki Zahra ke dubanta.. Lokaci guda take girgiza kai cikin rashin yarda da abinda takeji... Muhibbah ta jinjina kai a hankali alamun tabbatarwa tace “Promise me bazaki sanar da kowa abinda na sanar dake ba.. Especially Ummi..!” Dubanta tayi da idanunta masu zuban ruwa ba tareda ta iya furta koda kalma ba.. Muhibbah Ta kuma kamo hannunta with a straight face tace “Promise me Zahra..!” Ta kuma fad’i tana d’an jijjiga Zahran A hankali Zahra ta shiga jinjina kai idanunta na kuma zuban ruwa take furta “As you wish your Highness..!” Muhibbah ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai k’ok’arin share hawayen da suka wanke fuskar Zahran... Saidai ga tsananin mamakinta ji tayi Zahra ta saka hannu ta janye hannun Muhibbar daga fuskarta.. Lokaci guda take furta “If you may excuse me Rankidad’e..!” Ta k’arashe da alamun risnawa, lokaci guda ta mik’e ta fice cikin sauri kaman zata kifa k’asa Muhibbah tabi bayanta da kallo har ta b’ace mata hawaye naci gaba da gangaro mata, kifa kanta tayi tana kuka da gaske lokaci guda tana tambayar kanta Maiyasa rayuwa yake zuwa haka, daga wannan k’alubalen sai wancan.. Shin ta yaya zata fahimtar da Zhara cewa dole ce ta sakata rabuwa da mahaifinta.. Ta yaya zata fahimtar da ita sadaukarwa take wa mutanen da suka sadaukar da abubuwa da dama sabida ita.. Shin meye laifinta a nan..? Ta kuma fashewa da sabon kuka... Haka yinin ranan tayisa jikinta babu K’warai, sannan bata sami kiran Rankaidad’e daga wajen Jakadiya ba dan da alama yau d’in shima ya zama busy ne da maganan nad’in sarautar sa.. Yini zubur yayi a cikin Fadarsa suna tattauna al’amaran da ya shafi cikin gidan da manyan masu sarauta na gargajiya.. Sallah ce kawai yake fitar dasu sai ko lokacin cin abinci... Tin Ja’afar yana ganin abin bak’on Al’amari a garesa har dai ya saki jiki... Neman duniya anyi ba’a san yanda Waziri yake ba, Ja’afar ya hani Ubandoma da fad’in yanda suka b’oye Waziri a cewar J’afar d’in Waziri bazaici banza ba... Ko kullesa a bak’in fursuna da sukayi suka tsoratar dashi duk dare ya ishesa horo.. Ta tabbata dai ba’a ga Waziri ba an nemesa sama da k’asa an rasa, can iyalansa ma nemansa suke.. Daga wanda suka damu da b’acewar nasa sai wanda damuwarsu kawai ya bayyana ya amsa masu laifukan da ake tuhumarsa da bakinsa ne musamman matansa da yaci amanarsu da Giwa harda d’ah tsakaninsu... A b’angaren Fu’ad ma duk wanann kwamacala da abubuwan ban mamaki da na al’ajabi harma da tausayi da suka faru cikin Masarauta baida labari da shike yana killace ne can a asibitin masu tab’in hankali... ** BAUCHI Tinda Ansar ya dawo gida baya kula kowa bai shiga hark’ar kowa, babu yanda Mommy batayi ba yayi hak’uri da al’amarin Ubangiji suci gaba da addu’a Allah ya bayyana masu Muhibbah shi kuma ya d’auki matarsa su tare can gidansu amma Ansar yak’i aiwatar da hakan... Sosai Mommy ta damu da yanayin da tilon d’an nata ke ciki, uwa Uba ga tausayin Hamida da takeji wacce sunan aure kawai tayi amma tinda tayi auren babu komai cikinsa sai tashin hankali.. Tabbas auren dole bashida wani alfanu, gashi ta gani akan d’anta... Kyakkyawar magana bai tab’a shiga tsakaninsa da Hamidar ba tinda ya dawo Sannan ko Asibiti ya daina zuwa saima tsananin fad’a fafa da ya soma, d’abi’arda sam ba nasa bane a baya yanzu kuwa ya ara ya yafa.. Daidai da iya Larai bai ragar mata ba, ‘yar wasan da suke a baya yanzu bai d’auka.. Gaba d’aya ya koma very violent kaman ba shi ba... Iya Larai

Chapter 58 of 65