Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
malamar jinya take....” Shiru yai tamkar mai nazari yana sauraren Umaima kana yace “Wacece MUHIBBAH...?” *** “Jakadiya na kasa aminta Mahmood zai b’oye min babban al’amari irin wannan... Da ace wani na umarta ya gudanar min da aikin tabbas da zan amince aikin bai yuwu bane... Tabbas da zan amince Aliya bataci saiwar nan ba... Amma da hannuna na bata ta kuma ci dan bana fatan had’a iri da dangin bayi wanda basu gaji komai ba face bauta... Na kuma tabbata nayi aikin yanda Tal’udu ya umarta.... Toh ya akai bayan tafiyar Mahmood da Aliya k’asar Spaniya zasu dawo da d’iya... Kuma tabbas Tal’udu ya tabbatar min cewa yarinyar jinin AbdulJabbar ce...Shin ya akai aka haifeta bayan na tabbata da kaina Aliya bazata tab’a haihuwa da d’ahna Mahmood ba... Jakadiya wannan dalili yasa sam banajin k’aunan yarinyar cikin raina... Akwai wani rufeffen sirri gameda al’amarin yarinyar....Idan har ba Aliya bace ta haifeta toh hakan na nufin Mahmood ya haifeta da wata mace kenan...? Shin wannan dalili yasa yake gudun mulki...?” Ta k’arashe tana duban Jakadiya daga nan yanda take tsaye hannayenta hard’e ta baya... Jakadiya dake risine gabanta k’asa, girgiza kai tai a hankali kana tace “Allah shi taimakeki kina ganin Yarima mai jiran gado zai aikata babban laifi irin wannan...? Bana tunanin zai aikata babban abun kunyaga Masarautar nan irin haka... Idan har akace yarinyar nan ‘yar gaba da Fatiha ce toh fah kinsan wannan bak’in fenti sai ya shafi ahalin Marigayi Mai Martaba gaba d’aya... Wannan dalili ka iya janyowa Sarauta ta fice cikin gidan nan Allah shi baki yawan rai....!” A matuk’ar harzuk’e Giwa ta waigo tana watsawa Jakadiya firgitaccen kallo “K’arya ne... Wannan k’Arya ne Jakadiya... Shiyasa sam bazan tab’a bari magana mai kama da haka ya bayyana a Masarautar nan ba... Na gommaci ace wannan yarinyar jinin ‘yantacciyar baiwa ce akan ace sakamakon abin kunya ce... Bazan tab’a bari sunan zuri’ata ya b’aci ba Jakadiya....!!” Jakadiya ta shiga jinjina kai cikin sauri tana mai furta “Wannan haka yake Allah shi taimakeki... Allah huci zuciyar Giwar Amale... Allah shi baki yawan rai shugabata.. Ki jima kinayi zuri’arki su jima sunayi... Mulkin k’asar nan taki ce ya Shugabata...!!!” Ta k’arashe tana d’aga babbar yatsawa Giwa daga nan yanda take duk’e alamun jinjina... Giwa ta kuma sakin huci tana mai ci gaba da zagaya d’akin take ci gaba da fad’in “Na zab’i maganan ta zauna a haka, hardai bayyanarsa na nufin tarwatsa kan ahalina ne da mulki na...!” Jakadiya ta kuma jinjina kai tana mai furta “Allah shi baki yawan rai har abada wannan magana bazai fito ba...!” Giwa tai K’uri ma waje guda tana tinanin tabbas Yazeed ka iya sanin wani abu gameda al’amarin amma for now ta zab’i ya zauna a haka, akwai lokacinda ya dace maganar ta bayyana idan ma haka d’in ne... Ta k’arashe tinanin nata tana mai ci gaba da zagaye tapkeken d’akin nata... ** “Yaya Muhibbah K’awatce, karatu take a nan asibitin koyarwa, batada wajen sauk’a shine nai mata masauk’i a Masarautar nan...” Jinjina kai yai a hankali yana mai kuma takowa kad’an kana yai gyaran murya yace “Yayi kyau... Ina take yanzu...?”Ya k’arashe yana mai zama gefen Zahra Umaima ta d’anyi gyaran murya kana tace “Tana cen b’angaren bak’i dake bayan sashen Maami..” Jinjina kai ya kuma yi kana yace a tak’aice “Ina son ganinta...” Umaima murmushi fal fuskarta tace “Alright Yaya zanje na sanar da ita...” Jinjina mata kai kurum yai ba tareda ya amsata ba kana ta fice tana mai fatan samun lafiyawa Zahra... Murmushi kad’an Zahra tai kana tace “Tanada kirki sosai Paa...” Ya murmusa kad’an yana mai shafa sumarta lokaci guda yake furta “Akwai yanda Ke maki ciwo...?” Ta girgiza kai alamun a’a... Sai kuma taci gaba da fad’in “Please stay here with me Paa...” Dafa kanta ya kumayi kana yace “I’m here baby, I’m not going anywhere.. Okay...” Jinjina masa kai Ta kuma yi murmushi bai bar saman kyakkyawan fuskarta ba... Ya sumbaci goshinta a hankali yana mai furta “I love you...” Cikeda k’aunar mahaifin nata take furta “I love you too Papa...” Taita tina lokaci da dama da suke k’asar Spain... Saidai dikda jarumtarsa da k’warewa wajen b’oye dik wani abindake damunsa, zata iya karanto damuwa cikin idanunsa... Tin bayan rasuwar mahaifiyarta ya canza sosai amma wannan karon zata iya cewa akwai wani babban abin kuma dake damunsa, zatai iyaka k’ok’arinta wajen gano ko mai ke damun mahaifinta sannan dikda k’arancin shekarunta zatai k’ok’arin kawar masa da damuwar tinda baida wacce ta fita bayan mahaifiyarsa a halin yanzu.. Babu Maama d’inta dan haka bazataso taga mahaifinta cikin damuwa da tashin hankali ba... Suna nan a haka Rahima ta shigo cikeda d’imauta tana tambayar mai ya sami Zahra... Zahra kaw tamkar wacce akai mata albishir da ajalinta, Rahima na shigowa ta kauda kanta gefe had’ida rausayar da idanunta tana fad’in kalamai cikin harshen spanish a hankali... *** Ida wayarta da Ansar bada jimawa ba Umaima ta turo k’ofa ta shigo... Lokaci guda ta rungume Muhibbah tana fad’in “Kin cancanci yabo da godiya Hibbah, harta likitan da ya duba Zahra ya fad’i hakan... Zahra taji dad’I sosai da agajin gaggawa da kika bata... Ba don Ke ba ciwonta could’ve been worse... Thank you Hibbah...” Gajeren murmushi Muhibbah tai kana tace “You don’t need to thank me Umaima, I only did what’s right... After all, haka aikin mu ya gada... And haka ya kamata dik d’an Adama ya kasance, ka taimaka a lokacinda kakeda halin yin hakan... Besides this is nothing compared to taimakon da kuka min, kuka bani wajen zama kukai welcoming d’ina cikin masarautarku...I’ll be forever be grateful..” Murmusawa Umaima ta kumayi kana tace “Aff Kinga kafin na manta Ya Mahmood yace yana son ganinki...” Ambato sunansa da tai ya kuma haifar mata da fad’uwan gaba, lokaci guda tai k’ok’arin dakewa had’ida zaro idanu waje kad’an kana tace “Allah yasa ba wani laifi naiwa Yarima ba....!” Umaima ta d’an dungureta kad’an kana tace “Kinjiki da wani batu kuma... Kinga idan babu abinda kike tashi muje, nasan by now Giwa ma ta sauk’o k’Asa....” Muhibbah ta mik’e tana mai gyara zaman alkyabban dake jikinta kana tace “Amma kafin nan sai mun k’arasa kin ida zagawa dani dik yanda ya kamata...” Umaima ta zaro idanu waje kana tace “Aw sai mu k’yale Yaya na jira... Babban Yarima guda...?!” Rausayar da idanu Muhibbah tai a hankali kana tace “Yarima shike son ganina bani Ke son ganinsa ba, a duk lokacinda yamin zan amsa kiransa... Dan haka nace sai mun k’arasa zagaye Fada, saidai kuma idan Yarima zai min mulkin kama karya ne... Dan na tabbata ko wani d’an adam yanada right d’insa koda kuwa k’ask’antaccen bawa ne...” Girgiza kai kurum Umaima tai tana murmusawa kana tace “Kuma kinada gaskiya ta wani b’angaren... Amma nan goyi bayanki ba wannan karon sai don hakan kika zab’a....” Suka murmusa a tare Muhibbah na fad’in “Naji na amince... Tinda jikin Zahra da sauk’I abinda ake so kenan... Komai zai biyo bayan wannan...!” “Zancenki haka ne ..” Umaima tace sanda suke fita.... SameenaAleeyou📚 [5/31, 11:08 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *010* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Da mamaki Umaima Ke duban Muhibbah “Ke kaw mai zaki gani a sashen bayi...?” Murmusawa kad’an Muhibbah tai kana tace “Ranki shi dad’e bayi na taka muhimmiyar rawa a kowace masarauta, sannan dik Masarautar da babu b’angaren bayi bai kai a ambacesa da sunan masarauta ba... Bayi suke gina masarauta, sune k’ashin bayan ko wani masarauta sannan ko wacce masarauta na alfahari da tulin bayin da take dashi, idan babu bayi babu masarauta... Bayi sune cikar Fada....” K’uri Umaima tai mata har takai aya kana ta jinjina kai a hankali “Kedai ko da yaushe baki rabo da hujja mai k’wari.. Tinda kince haka muje na kaiki....” Muhibbah ta jinjina mata kai murmushi saman fuskarta... Suna tafe sukazo shige Bargan dawakan Sarki.... Su duka biyun yanayinsu ya sauya sanda suka doso wannan waje... Umaima taja Ta tsaya tana duban wani spot a nan cikin Bargan dawakan Maimartaba yayinda Muhibbah tai saurin d’auke idanunta tana mai k’ok’arin saita kanta sabida wasu irin hawaye masu d’umi da suka ciko idanunta lokaci guda.... Saida ta tabbata ta saita kanta kana ta d’an dubi Umaima da har lokacin duban wannan b’angaren take “Wannan fah... Ina ne nan...? Ga dawakai masu kyau da d’aukan idanu gwanin ban sha’awa...!” Hannu Umaima ta saka tana goge hawayen da suka gangaro mata cikin sauri dan bataso Muhibbah ta fahimci wani abu, lokaci guda take furta “Nan Bargan Maimartaba kenan, yanda ake aje dawakansa...” Tai maganar a tak’aice... Dafata kad’an Muhibbah tai kana tace “Are you alright..? Akwai wani abu ne... Ki sanar dani dan Allah...” Ta k’arashe cikeda kulawa... Umaima ta k’ak’aro murmushi kana tace “Babu komai Hibbah mu k’arasa...” Hannunta Muhibbah ta rik’o had’ida girgiza kai har lokacin damuwa ne k’arara saman fuskarta kana tace “No Umaima, ban yarda babu komai ba, tinda mukazo wajen nan yanayinki ya canza, dan Allah ki sanar dani idan akwai wani abu ne... Hardai kin amince ‘yaruwa kika d’aukeni...!” Ta k’arashe cikin tsananin kulawa dan san jin taji ko menene... K’ak’aro murmushi Umaima tai kana tace “Wannan waje yana tina min shi... Yana tuna min irin zallan soyayyar da na nuna masa dikda cewa yasha jadadda min bai tab’a sona ba... Zuciyarsa mallakin wata yarinya ce k’arama wacce suka rabu ba tareda su duka biyu sunsan ma’anan soyayya ba a wancan lokacin... Ta tafi da zuciyarsa ta bar gangan jikinsa cikin Masarautar nan... Yasha jaddada min kar nayi gangancin fad’awa soyayyarsa dan bazan samu ba... Dikda sanin cewa shi d’in bawa ne hakan bai hana zuciyata afka ma soyayarsa ba domin kaw ita soyayya batasan bawa ba bata San Y’antacce ba, faruwa take a wani lokaci da sam baka shiryawa aukuwarta ba...!” Ta k’arashe hawaye na gangaro mata... Muhibbah da k’irjinta Ke ci gaba da tsananin bugu, dafa Umaima tai kad’an kana tace “Kiyi hak’uri ba nufi na bane na sakaki kuka....!” Umaima ta girgiza kai kad’an tana mai sakin murmushi “Babu komai Hibbah, Ja’afar ya riga ya zama tarihi a gareni domin kaw yau shekara guda kenan da barinsa Masarautar nan... An wayi gari aka nemesa aka rasa dan yasha jadadda min dama lokuta da dama dik daren dad’ewa zai fice ya nemo SAUDATU koda kuwa hakan na nufin bijire ma iyayen gidansa ne... “ Numfashinta ne ya sark’e lokaci guda... Take taji jiri na neman Kaita k’asa, duniyar taci gaba da juya mata... D’an uwa ta d’auki Ja’afar bata tab’a zaton shak’uwarsu yakai munzanin soyayya mai k’arfi haka ba... Maiyasa Ja’afar zai tafi ya bar Masarautar nan a lokacinda ta dawo kuma lokacin da tafi buk’atar kasancewarsa cikin Masarautar... Shin kodai yanada masaniyar abinda azzaluman cikin Masarautar nan sukai masu ne itada iyayenta...? Idan har kuwa yanada masaniya tabbas zai iya sanin mai akai da mahaifinta da har yau bata san wane hali yake ciki ba... Shin kashesa akai..? Ko kuwa dai Yana nan cikin wannan masarauta... Tabbas Ja’afar zata iya samun wasu amsoshi daga wajen Ja’afar idan har yanada masaniyar abinda akai masu... Toh amma Ina Jafar...? Ta ina zata soma nemansa bayan babu shi cikin Masarautar... D’an dungurinta da Umaima tai ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi... Ta saki murmushi a hankali kana tace “Kinga kallon dawakan nan ya d’auke hankali na...” Umaima ta murmusa kana tace “Ai naga alama... Mu k’arasa ko...” Muhibbah ta jinjina mata kai kana suka nufi b’angaren bayi... Suna tafe Umaima naci gaba da mata bayani... Sun kusan nufa gate d’in bayin kenan Umaima ta hango Rahima sai buga sauri take ta nufi wani b’angare nan cikin sashen bayin yanda tai parking motarta daren jiya... Mamaki ya d’an kamata ita kaw mai ya kawo motarta k’ofan bayi....? Muhibbah ta sauk’e idanunta a yanda Umaima ke duba... Lokaci guda take furta “Wacece wancan... Batai kama da bayi ba, mai ya kawota b’angarensu...?” Umaima ta d’an girgiza kai kana tace “Rahima ce k’anwar Aunty Zeenat..” Muhibbah tace “Matar da Yarima Mahmood zai aura...?” Umaima ta jinjina mata kai alamun eh kana taci gaba da fad’in “Toh amma mai ya kawo motarta nan...? Kinga mu k’arasa wajenta sai nai introducing naku...” Babu musu Muhibbah tabi Umaima suka nufi Rahima dake k’ok’arin shigewa mota, sai waige waige take tamkar maras gaskiya.... “Rahima..!” Muryar Umaima ya daki dodon kunnuwanta, abinka da maras gaskiya sai ta firgita, ta juyo cikin sauri tana dubansu... Lokaci guda kuma ta d’an saki murmushi kana tace “Haba Umcy wllhi kin razanani....” Tai maganar tana d’an dungurin Umaima da car keys d’inta... Umaima ta murmusa kad’an saidai kafin Takaiga bata amsa suka sinkayo muryar Muhibbah tana fad’in “Yo miye abin tsoro Keda kike kusa da Dakurun sarki idan ma hari aka kawo Masarautar...?” Tai maganar cikin sigar wasa tamkar itada Rahimar sunsan juna.... I zuwa wannan lokaci Umaima kam Ta soma Sabo da halin Muhibbah, ita kaw Rahima da tsananin mamaki take duban budurwar da tai maganan wacce sam kallo guda tai mata taji ko kad’an bata kwanta mata ba.... Murmushin yak’e ta saki kana tace “Toh wa ya sani ko harin ta cikin k’asa aka kawo wanda Dakaru bazasu ankara ba...!” Tai maganar tana juya idanu... Daga Muhibbah har Umaima murmusawa sukai kana Umaima tace “Rahima ga k’awata Muhibbah ku gaisa.. Muhibbah wannan itace Rahima ko nace our big Aunty, matar Yaya Yarima Babba...” Wannan kirari da Umaima tai mata ya sanyata sakin murmushi tana kuma jijjiga had’ida gyara tsayuwarta tana jin tabbas ta isa.... Muhibbah ta murmusa kad’an tana yaba kyaun halitta da Allah yayiwa Rahima, tabbas tayi kama da matan masu mulki.... Wayar Rahima ne yai ringing, ta d’an d’aga yatsarta guda alamun excuse kana ta matsa gefe ta d’auki wayar ganin ba kowa Ke kiranta ba face aminiyarta Zuhra.. Aiko tana d’agawa ta sinkayo muryar Zuhra cikin kuka... Gaban Rahima ya yanke ya fad’i, lokaci guda take furta “Zuzu meke faruwa... Please talk to me... Yazeed ya miki wani abu ne....?!” Cikin muryar kuka Zuhra Ke fad’in “Rahima na gaji, na gaji da wulak’ancin Yazeed, dan Allah kizo I really need you...!” Ta k’rashe cikin shesshek’an kuka... Fuzar da fuci Rahima tai a hankali kana tace “Alright ya isa haka Ki daina kukan nan, gani nan zuwa...!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin saita kanta yayinda kacaukam hankalin Muhibbah ke gareta tinda ta soma wayar, gaba d’aya hankalinta baiga Umaima daketa faman karanto mata bayani yawa malamar makaranta gaban d’alibai... Rahima ce ta K’araso yanda suke tsaye kana tace bara taje sashen Zuhra, gaba d’aya yanayinta ya sauya ko takan motar ma batabiba ta shige cikin sauri... Muhibbah tabi bayanta da kallo har ta b’ace mata kana ta maido da hankalintaga Umaima, ta riga da ta samu information d’in da take buk’atan sani gameda Ja’afar dan dama hakan ne yasa tace suzo sashen bayi...ta d’an langab’e kai tana fad’in “Gaskiya mu juya haka nan your highness, na gaji sai wani lokaci kuma....” Umaima ta murmusa kana tace “Da wuri haka...Dik San sanin Masarautar naki....?” Murmusawa itama Muhibbar tai kana tace “Fada da fad’i take your highness bazan iya zagayawa ba...!” Umaima ta kuma murmusawa kana tace “Toh mu k’ara gaba kad’an na nuna miki Rumbur sarki....” Muhibbah ta jinjina kai tana mai murmusawa kana tace “Idan kince haka...” ** Sauri sauri Rahima ta nufi b’angaren Zuhra tamkar zata tashi sama, dik kuyangin da zata gifta sai sun risina Sun gaidata, alla alla take ta isa taji wata uwar yau kuma d’an maras mutuncin nan yaiwa k’awarta... Aiko tana isowa ta hangesa tsaye k’ofar sashen cikin shiga irinta alfarma, yai tsayuwa irinta wanda keji da tsananin mulki da izza hasken rana ya haske kyakkyawar fuskarsa, kaman kullum babu alamun rahama ko fari’a a fuskar tasa... Ta sauk’e fuci a hankali tana girgiza kai kana taci gaba da dosowa sashen.... Tana hango dogaransa suna jinjina kai suna darewa a wajen alamun sallamansu yai, ta K’araso had’ida risinawa alamun gaisuwa... Har lokacin hannayensa hard’e suke ta baya ya k’urama waje guda idanu... A zahiri zakai zaton gaisar dashi Rahima keyi... Bai amsa gaisuwar nata ba sai cewa da yai “What brought you here...?” Yai maganar idanunsa na duban wani b’angaren... Ta d’an saci dubansa kada’an kana tace “Prince what happened to Zuzu, is she well...?” Tai tambayar cikeda damuwa Shu’umin murmushin nasa ya saki a hankali kana ya d’an kaikaito yana k’are mata kallo daga sama zuwa k’asa.... “Maiyasa bazaki shiga ba and find out yourself... After all, abinda ya kawoki kenan... !” Tana gani yai alamawa Hauni cewa ya k’araso, lokaci guda tasa kai ta shige tasan koda taci gaba da tsayuwa wajen ba samun amsa zatai ba.... Tana fad’awa cikin gidan ta haye d’akin Zuhra... Kwance ta taddata saman gado sai kuka take hannunta dunk’ule da wani abu... Rahima na shiga Zuhra ta taso a guje ta rungumeta tana kuka sosai mai ban tausayi... Jikin Rahima a matuk’ar sanyaye ta rik’e Zuhra suka zauna saman sofa, lokaci guda take furta “Zuzu Kukan nan ya isa haka... Mai kuma ya faru....?” D’aga mata wuyarta tai taga alamun shati yayi jajazir, bata iya magana ba sai wani kukan da ta kuma fashewa dashi... Rahima ta zaro idanu waje... “Zuzu kina nufin kice min Yazeed ne yai maki wannan tabon..? Zuzu mai ya faru....?” Zuhra tai k’arfin halin share hawayen dake idanunta kana ta soma fad’in “Yazeed baida imani Rahima...Yazeed mugu ne, azzalumi ne.... Yazeed ya maidani tamkar shara cikin gidan nan, wllhi ko kuyanga ta fini ‘yanci cikin gidan nan... A duk lokacin da yaga dama zai d’ebo dik wani wulak’ancinsa ya zuba akaina... Rahima mai nai masa da tsanani...? Laifi ne don Allah ya jarabceni da soyayyarsa... Rahima na baro masarautarmu da Gata na da komai na, na zabi na zauna dashi... Amma kiga irin wulak’anci da cin kashin da yake min wanda ko kuyanga bazata d’auka ba... Daren jiya bai dawo gidan nan ba sai tsakiyar dare kuma na tabbata bai samu yanda yake so bane wajen ‘yanmatan nasa shiyasa ya dawo gareni ya sauk’e gajiyarsa da dik wani takaicinsa akaina... na tabbata da ya sami yanda yake so bazan ganshi ba sai Washe gari...wannan wace irin rayuwa ce...?” Ta k’arashe tana mai kuma share hawayenta... Cikeda kulawa Rahima ta dafa hannayenta kana tace “Shine yai maki wannan tabon don Kinyi magana...?” Zuhra na hawaye take jinjina mata kai, lokaci guda taci gaba da fad’in “Dama zai k’ara auren da yafi min sauk’i... Ni ba fita aiki nake ba balle hakan ya d’ibe min kewa, bana zuwa ko ina, kullum ina kulle cikin gidan nan ina cazagan bak’in cikin mijina... Shin haka auren masu sarauta yake...? Ba haka na tashi naga mahaifina nayiwa iyayena ba... Maiyasa ni zan tadda haka cikin gidan aurena...?” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya... Sauk’e ajiyan zuciya Rahima tai kana tace “But kin tabbata biye biyen wasu matan yakeyi, kodai Kawai zarginsa kike...?” Dubanta Ta d’anyi had’ida yin murmushi mai ciwo “Rahima kenan... Yazeed ne fah ba wani ba, wanda idan na hanasa kaina yakance yanada dubun wanda suka fini... Wllhi badon yana matuk’ar son mulkin Masarautar nan ba, nayi imani da a cikin gidana zai dinga aikata fasik’anci da matan banza, kawai yasan yin hakan ka iya shafa martabansa ne shisa...!” Ta k’arashe wasu hawayen na kuma gangaro mata.... Rahima ta sauk’e ajiyan zuciya kana tace “K’awata zan baki shawari, kici gaba da hak’uri wataran komai zai wuce ya zamto tarihi... Wataran macen da ya raina, Ke d’in da ya raina sai Allah ya jarabcesa akanki... Ki kwantar da hankalinki k’awata kima daina saka ma ranki damuwarsa kiji da yaranki kawai kinji koh... Kuma koda wasa kada Ki bari wannan batu ya isa Masarautar ku don kimanki ne zai zube...” Zuhra ta jinjina kai a hankali kana tace “Na gode K’awata... Allah ya bar min Ke, zanyi dik yanda kikace in sha Allah...!” Rahima ta murmusa kana tace “Yauwa yanzu naji batu K’awata, share hawayen ki ki kuma cancad’a kwalliya, ki nuna masa kaman ma ba’ai komai ba kinji koh...” Zuhra ta jinjina mata kai kana ta mik’e ta fad’a bathroom dan wanke fuskarta.... Tana shigewa Rahima ta sauk’e nannauyan ajiyan zuciya had’ida kishingid’a cikin kujeran... *** Kishingid’e suke k’asar wata ‘yar bukka dake wani b’angar a haraban Masarautar, anyi ado da kwalliya ma wajen da dardumai da kuma manyan pillows na alfarma, ko wannensu sanye cikin shiga irinta alfarma, kallo guda zakai masu su birgeka... Yazeed, Jamal saiko Fu’ad, an K’awata gabansu da kayan marmari... Jamal ya dubi Fu’ad da ya b’ata shiru tamkar bashi a wajen kana yaci gaba da fad’in “You can’t go on like this Fu’ad, you need to put an end to this... idan hakan yaci gaba da faruwa Ina mai tabbatar maka zamu maidaka yanda ka fito ne....!” Yai maganar Cikin zafin rai... Sai lokacin Fu’ad ya d’ago yana dubansa kana ya soma girgiza kai yana fad’in “No, no Jamal... You know I can’t go back to that place..” Baikai aya ba Yazeed dake kishingid’e daga tsakiya irin yanda masu sarauta keyi, cikeda izza yake jefa gyad’ar kwalba a bakinsa, ya katsesa da fad’in “Of course zaka koma, dear brother... So kake ka dinga jifanmu da abin kunya kana dawowa cikin Fada high, kana amai kana hauka gaban kowa bayi da sauransu...If you can’t control yourself, wllhi kaji na rantse ni da kaina zan mayar dakai....!” Fu’ad ya waigo yana d’an dubansa kana yasa tafukan hannayensa biyu ya shafe fuskarsa, lokaci guda ya d’an murmusa kana yace “Wait..? What are you two afraid of... You don’t want Yaya to find out.. Right..?” “Shut the hell up Fu’ad...!!” Jamal ya katse sa da fad’in haka kana yaci gaba da fad’in “Idan maganan nan ya fito fili, we are not going to lose only our Family and our power...Harta gidan nan sai mun rasa, So you better shut your mouth, and stop living in the past..!” Yazeed dake ci gaba da jefa gyad’arsa a baki kaman bashi a wajen K’uri yaima waje guda yanda suke k’arasowa... Tin daga k’afafunta yake dubanta har zuwa fuskarta.... Dik maganan da Jamal keyi baima saurarensa har saida Jamal d’in ya kaikaito yana duban abinda ya d’auke hankalin Yazeed, Fu’ad dake dubansu su duka biyun waigowa shima yai yana duban abinda suke kallo..... SameenaAleeyou📚 [6/1, 7:13 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *011* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Zuciyarta taci gaba da bugawa da sauri da sauri tamkar zata b’alle daga cikin k’irjinta ta fito waje... Koda bata d’ago ta dubesu ba tayi imani ita suke kallo, ji tai k’afafunta na k’ok’arin sark’ewa, Ta soma ganin hanya duru duru, ita dai kawai jefa k’afafunta take... Shin ta yaya ma bazata tsinci kanta cikin wannan yanayi ba bayan yau d’in tayi arangama da mutanen da suka zama jigo wajen tarwasta rayuwarta, ahalinta da dik wani Farin cikin data baro a baya.... Tana jin yanda Umaima Ke karanto mata cewa wancan wajen hutu da yaran sarki Ke ciki nasu ne su kad’ai babu wani wanda Ke shiga cikin ‘yar bukkan nan kaf Fada face ahalin Sarki AbdulJabbar... Umaima taci gaba da fad’in “K’warjininsu ya cika wajen...Tabbas Ubangiji ya lullub’e Sarki AbdulJabbar da rahama da ya azirtasa da zaratan yara maza masu kyau irin wad’annan wanda zasu zama magadan wannan Masarautar... Mahmood shine babba cikinsu mai kimanin shekaru 46, lokacin da Giwa ta haifesa a yanda naji tarihi ansha bikukuna da shagali a wannan Masarautar kasancewarsa babban d’ah ga Sarki AbdulJabbar... Bayan ta haifesa ta jima bata kuma haihuwa ba dan saida tai shekaru a k’alla goma kana ta haifo Yazeed, d’ah na biyu a Masarautar nan mai kimanin shekaru 36, daga shi sai Jamaluddeen d’ah na uku mai kimanin shekaru 32 sannan d’an autan Yarimomin Fu’ad mai kimanin shekaru 28... Wad’annan sune ‘Ya’yan Sarki AbdulJabbar mai rasuwa...” Ta k’arashe murmushi kwance saman fuskarta... Batasan ya akai ba saiji tai bakinta ya bud’e yana furta “Tabbas Giwa ta haifo yara, cikinsu akwai Maciji, akwai Rak’umin dawa, akwai Kunama, Sannan akwai bushiya mai lullub’e da k’aya...Saidai kashhh, bata haifo Sarkin Dawa ba...!!” Tai maganar cikin wane irin yanayi da dik wandake dubanta zai iya firgita... Da mamaki Umaima Ke dubanta kana tace “Mai kikace..?!” Muhibbah tai k’ok’arin saita kanta kana ta d’an rausayar da idanu “Aw nace wani abu ne...?! Sorry that was nothing... Wani tunanin na daban nake...!” Ta k’arashe kyakkyawan murmushi saman fuskarta... Umaima ta d’an murmusa kana tace “I’m used to it by now, Allah yai maki baiwa da tsara kalamai saman harshe... zakiyi kyau da zama matar Saraki....” Ta murmusa kad’an kana tace “Mai mulki sai mulki, Talaka sai talaka, Mai arziki sai mai arziki...Haka rayuwar Ta koma k’awarya tabi k’warya... Ko ba haka bane...?” Ta

Chapter 6 of 65