janta Ta nufi wannan hanyar....
Dik irin saurinda Muhibbah keyi bata cimma wannan mutumin ba, ba kuma taga lungun da ya shige ba... Komawa da baya tai tana sauk’e huci a hankali kana Ta furta a hankali... “Muje zuwa watarana zan fahimci ko kai d’in wanene da kuma yanda kake zuwa....!!”
Ta kuma fuzar da iska a hankali kana Ta juyo da zummar soma tafiya saidai ganin wad’annan Kenwa guda biyu data kuma gani yau ma yaso firgitata... Ta shiga karanto addu’o’in da suka Zo bakinta tana mai barin wajen cikin sauri....
Jefa k’afafunta kawai take dik yanda suka sauk’a tana mai jero addu’o’in da dik suka Zo bakinta.... A daidai k’ofan shiga sashen masauk’in nata ta kusa yin karo mutum... Tai saurin matsawa da baya tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali....
D’ago fuskan da zatai sukai ido hud’u da juna, hannayensa hard’e ta baya yake dubanta... Bugun zuciyarta ya k’aru ganin shid’in ne gabanta... Tai k’ok’arin tattaro natsuwarta had’ida d’aura murmushi mai kyau saman fuskarta dan harga Allah ganin shine ba wani ba sosai hakan ya jefa zuciyarta cikin natsuwa...
“You again..” ya fad’i yana mai dubanta fuska babu walwala.....
Ta k’ak’aro murmushi had’ida risinawa kana tace “Barkada dare Rankashi dad’e..!”
Ya jinjina mata kai a hankali kana yace “Mai ya fito dake cikin daren nan...?”
Ta d’an daburce gaba d’aya tama rasa mai zatace...
Gajeren murmushi tai mai cikeda k’asaita yai kana ya gyara tsayuwarsa wann karon....
“Da alama yauma kin b’ace a hanya...!”
Dubansa ta d’anyi kana ta kuma sadda idanunta k’asa...
Gyaran murya ya d’anyi kad’an kana yace “Roaming around the palace at this hour..?”
Batakaiga samo amsa ba Ubandoma ya k’araso ya risina yana mai gaida Shugaban nasa yake fad’in “Allah shi baka yawan rai mun duba ko ina bamuga mutumin da kace ka gani ba.... Masu tsaron k’ofofi da dogarai duk suma sun tabbatar basuga kowa ba..!”
Yarima Mahmood ya jinjina kai kana yace “A baza dakaru da dogarai Ta ko Ina a zak’ulo mutmin nan kafin wayewan gari...!!”
Ubandoma ya risina yana mai jinjina kai had’ida amsawa kana ya baza babban rigarsa ya nufi aiwatar da umarnin Ubangidansa...
Muhibbah da zuciyarta Ke raya mata Anya ba mutumin da take gani bane Rankashi dad’e yake nema... Toh Wai waye wannan mutumin....? Batakai ga samo amsa ba ta sinkayo muryar Mahmood yana fad’in “Zaifi kyau idan koma d’aki a daidai wannan lokacin..!”
Daga haka bai kuma cewa komai ba yasa kai ya shige...
Muhibbah tabi bayansa da kallo har ya b’acewa ganinta... Tana kallo Dogari suka soma firfitowa Ta ko wane sak’o cikin Masarautar...
Cikin sauri itama ta koma masauk’inta ta natsu waje guda tana tinanin toh Wai waye mutumin nan da yake Yawo cikin dare a Masarautar....
***
Giwa sai kaiwa da kawowa take, takai mari takai bango.... Mahmood yana neman zamema rayuwarta barazana... Shin maike shirin faruwa da ita ne... Anya batayi gangancin barin Mahmood raye ba... Maiyasa bata kashesa ba tintini, Maiyasa ya rainesa da hannunta... Anya ba ajalin mulkinta Ta raina da hannuwanta ba... Lokaci Ta kuma fuzar da fuci daidai sanda Jakadiya ta shigo a firgice tana fad’in “Rankishi dad’e Ta bayyana...! Izzatu Ta bayyana..!!!”
A d’ari Giwa Ta mik’e tsaye idanunta suka firfito waje cikeda tashin hankali....!
Sameena📚
[6/24, 11:48 AM] +234 703 881 5154: *MUHIBBAH*
*023*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Hankali tashe Giwa Ke fad’in “Ke Jakadiya Ki natsu Ki sanar dani abindake tafe dake cikin daren nan... Bana san shashanci da hauka...!”
Jakadiya na sauk’e haki take fad’in “Allah shi baki yawan rai Ina tinanin Izzatu ce ta bayyana dan ga Yarima Mahmood ya cika Fada da dakarai, ga dukkan alamu Masarautar babu lafia...!”
Giwa ta isa jikin window ta yaye labule nan ta hangi dogarai sai kaiwa da komowa suke... Juyowa tai tana duban Jakadiya kana tace “Kin tabbata Izzatu ce ta bayyana... Ko kuwa wani abinne daban...?!”
“Allah shi taimakeki idan ba Izzatu ce ta bayyana ba maizaisa Dakarai su bazama cikin masarauta...?!”
Giwa ta girgiza kai tana mai furta “Sam hakan bamai yuwa bane Jakadiya... Sanin kanki ne bayyanar matar nan na nufin tashin hankalinmu ne...Ina Ubandoma...?”
Jakadiya batakaiga bata amsa ba Jamal ya shigo yana tambayan Jakadiya abinda Ke faruwa cikin Masarautar nasu dan yaga Dakarai ta ko wani angle....
Jakadiya ta basa amsa da fad’in “Allah shi taimaki Gwarzon Giwa, ai Ina tsammanin cikin Fada ne Babu lafia...!”
Yarima Jamal ya jinjina kansa kad’an kana ya dubi mahaifiyarsa yace “Maami are you alright..?!”
Ta jinjina masa kai alamun lafia take... Lokaci guda Jamal ya nufi k’ofa yana fad’in bari ya duba meke faruwa cikin Masarautar....
Jinjina masa kai kurum Giwa tai ba tareda ta iya basa amsa ba... Yana ficewa Ta kuma duban Jakadiya kana tace “Maza kije ki nemi Ubandoma yanda ya shiga ya fita kiji abindake wakana cikin Masarautar sannan ki tabbata Mahmood baiga Izzatu ba....!!”
Jakadiya ta jinjina kai tana mai amsa mata kana Ta fice cikin sauri... Ta bar Giwa nan d’aki sai kaiwa da komowa take, ga hannunta dake rufe cikin safa sai mintsilinta yake a hankali, wannan alamace na cewa shirinta na iya backfiring d’inta kaman yanda Tal’udu yasha sanar da ita.... Sosai Ta matse hannun tana huci take furta “Turai nake, murucin kan Dutse ban fito ba saida na shirya, kayi kad’an Mahmood iyayenka ma sunyi kad’an... Na kassarasu balle kai... Na d’aid’aita ahalinka, kaid’in kayi kad’an kace zakajada Giwa.....!!”
Tana ida fad’in haka ta d’an zame safar hannun nata... Gabanta ya yanke ya fad’i ganin Yana nan a halittansa na launin bak’i... Tai saurin maida safar ta rufe kana takai dubanta ga d’aya hannun nata dake sarari shi d’in fari ne tas gwanin ban sha’awa.... A hankali ta fuzar da fuci tana jiran taji da mai Jakadiya zatazo mata....
A kusan k’ofan bayi Jakadiya ta had’uda Ubandoma... Ta d’an murmusa kad’an kana tace “Wai fushi kake dani har yanzu, kaima kasan bayin kaina bane.. Ya na ita da umarnin Giwa...”
Ubandoma ya kuma watsa mata harara kana yace “Wannan hannu naki da ya jeme ya sud’e dan bauta ba dole naji marin nan ba, har yanzu Jakadiya jinyar k’uncina nake...!”
Dariya yaso kubcewa Jakadiya, Ta d’anyi kad’an kana tace “Yanzu dai ba wannan ba, Giwa ce ta aikoni dan sanin meke wakana cikin Masarauta... Ko Izzatu ce ta bayyana...?!”
Ubandoma ya watsa mata muguwar kallo kana yace “Banda k’ask’anci da tozarci a rasa waye zai mareni sai Baiwa gajiyayya...!”
Jakadiya ta kastesa da fad’in “Kai Ubandoma... Zaka amsa tambayar Uwargijiyarka ce kokuwa wani marin kake so ka sake amsa...?!”
Ubandoma ya sab’a babban riga yana mai kad’a Kai cikeda takaici kana yace “Wannan karon kam saidai kece zaki amsa marin dan kin sanar da Giwa abinda ba haka ba... Take ya sanar da Jakadiya abindake wakana cikin Masarautar da kuma yanda Yarima Mahmood ya bada umarnin binciko wannan mutumin cikin gaggawa... Babu b’ata lokaci Jakadiya ta shige Kai sak’owa shugabanta...
**
A babban haraban Masarautar Jamal ya tadda Mahmood, ya k’arasa gareshi suka gaisa yana tambayansa ko wani abu ne Ke wakana cikin Masarautar...
Mahmood ya sanar dashi abindake faruwa... A tare Mahmood da Jamal suka ci gaba da gudanar da binciken mutumin da aka gani cikin Masarautar wanda ba’a ita identifying kamanninsa ba sabida shiga Ta bak’ak’en tufafi da yakeyi... Haka nan suka umarta Dakarai da aci gaba da searching cikin Fada har zuwa wayewan gari don Mahmood ya tabbatar mutumin cikin Masarautar yake, babu yanda za’ai ace shigowa yai bayan irin tsaron dake a cikin Masarautar... Haka sukaita bincike har kusan asubahi babu wannan mutumi babu dalilinsa...
Yarima Mahmood ya d’an dafa kafad’ar Jamal kana yace “Kaje ka huta k’anina...!”
Jamal ya girgiza kai cikeda kulawa kana yace “A’a Yaya, bazan tafi na Barka kai kad’ai a nan ba... Kar ka damu dani, lafia lou nake..!” Ya k’arashe cikeda kulawa...
K’uri Mahmood yai masa kana ya jinjina kai a hankali alamun gamsuwa... Suna nan tsaye a wajen Sport car d’in Yazeed k’irar Lamborghini ta kutso Kai cikin masarautar... Suka bi motar da kallo har ya k’araso ya shige sashensa ... Girgiza kai kad’an Mahmood yai yana duba lokaci a wayar salulansa....
Jamal ya d’an kai dubansaga Mahmood d’in kana yai gyaran murya kad’an “Yaya ko zaka koma cikin gida ka huta, ka barni in charge zan kula da komai...!”
Baice komai ba sai sa kai da yai ya nufi sashen Yazeed... Ya tadda Yazeed d’in ya fito daga mota...
Kallo d’aya Yazeed yai masa ya watsar.... Ko a jikinsa ya nufi cikin gidan... Mahmood ya bud’e murya kad’an ya kirawo sunansa....
Cak ya tsaya ba tareda ya juyo ba...
Yarima Mahmood yaci gaba da takowa har ya k’araso kusan Yazeed d’in....
“Yazeed kakuwa San yanzu k’arfe nawa ne..?!” Ya tambaya yana duban Yazeed d’in...
Sai sannan Yazeed ya kaikaito yanaima d’an uwan masa wani irin duba... “Na sani... Why...Do you’ve problem with that...?!” Ya fad’i cikeda gadara ga tangad’i da yake alamun giyar bata sakeshiba dikda k’ok’ari da yake kar a gane a buge yake....
Mahmood ya girgiza kai a hankali kana yace “Yazeed mai ka d’auki rayuwar nan ne... Yazeed mata da giya duka biyu ka had’a...? Yazeed I thought ka canza, I thought ka aje duka wad’annan d’abi’un tuntuni.... Yazeed mai kake son maida rayuwarka data iyalanka...? A haka ne kake so ka zamto Shugaba a Masarautar nan...? Kana dawowa cikin Fada tsakar dare kuma a d’auke..? Wannan shine misalin dake so ka bayar a mulkin ka... Wannan shine misalin da kakeso ka baiwa yaranka...”
Katsesa Yazeed yai da fad’in “Cut the lecture please Yaya... Will you..?”
Lokaci guda yaci gaba da fad’in “Why do you even care.. Rayuwatace nayi yanda nake so da ita... Kuma wannan bashi zai hanani zamtowa Sarki na gaba ba... Wllhi kaji na rantse maka da Sarkin dake busan numfashi akan sarautar nan zan iya aiwatar da komai... Ko mene shi, and just so you know, I won’t hesitate to run over who ever gets in my way...!!” Yana k’arasa fad’in haka yasa kai ya shige yana mai ci gaba da tangad’i...
Fu’ad dake tsaye daga bayansu cikin sanyin jiki ya k’araso ga Mahmood...
“Yaya good evening...!” Ya fad’i yana d’an shafa sumarsa....
Mahmood ya dubesa da mamaki kana yace “Bakai bacci ba Fu’ad.... Mai kakeyi a nan...?!”
D’an shafa kansa Fu’ad ya kuma kana yace “Na farka ne Yaya sai nakeji kaman cikin Masarautar babu lafia... Can I be at any help..?”
Mahmood ya jinjina kansa a hankali kana yace “Is ok karka damu, ba wani abun damuwa bane... Guards are already taking care of the situation..!”
Fu’ad ya jinjina kai cikeda k’aunan d’an uwan nasa, Mahmood d’in ma murmushi ya saki masa kad’an yana mai d’an buga kafad’an Fu’ad yake tambayarsa ya yake Kwana biyun.... A haka suka jera gwanin ban sha’awa suka ratsa cikin Masarautar...
A haka suka k’araso suka tadda Jamal yanda yake ci gaba da umartan dakarun tsaron cikin gidan....
Jamal na hangosu ya k’araso yana tambayarsu ko akwai abinda ya canza... Yarima Mahmood ya girgiza masa kai a hankali alamun babu...
Gyaran murya kad’an Jamal yai kana yace “Yaya maybe idonka ne ya gane maka wannan mutumin, maybe wani ka gani cikin dakarun gidan nan kai tinanin ko wani daban ne ko wani mugu ne... Yaya I’m sure babu wanda zai iya haye manyan ginin Masarautar nan ya shigo kokuma ya tsallake dika Jami’an tsaron dake cikin gidan nan... I think babu kowa kaman yanda muke tinani....!” Ya k’arashe cikeda kulawa...
Fu’ad ya jinjina kai yana mai furta “I agree with Jamal Yaya... Maybe wani ka gani cikin dakaru...!”
D’an jim Yarima Mahmood yai kana ya jinjina kai yana mai fuzar da fuci a hankali “You’ve a point... But I’m sure naga mutum cikin bak’ak’en tufafi, sannan zuciyata bai kwanta da ganin wannan mutumin ba.. Na soma binshi sai naga tafiyar tasa kaman gudu gudu ne...! But is okay, let’s not think of the worse...”
Fu’ad ya jinjina kai alamun gamsuwa kana Jamal yace “I’ll check on Maami...”
Jinjina masa kai sukai a tare kana ya shige Mahmood da Fu’ad ma sukai ma juna sallama kowa ya nufi b’angarensa...
***
Sosai hankalin Giwa ya kwanta jin ba Izzatu bace Ta bayyana kaman yanda Jakadiya tazo mata da batun daga fari...
Washe gari sassafe sukai shirin zuwa ganin Izzatu itada Jakadiya...
Kasancewar Giwa takan fita rangadi a Masarautar yasa sam bazakai zaton wani mugun nufi ne da ita ba.... Dik yanda ta shige bayi sai Sun risina suna kwasan gaisuwa... Jakadiya Ke amsa masu...
Muhibbah da tin fitowarsu take biyedasu ba tareda sunyi noticing d’inta ba tana ganin sun nufi wata k’ofa daga cen b’angaren hagu dake gabashin Masarautar taji gaba d’aya jikinta bai aminta da yanda suke zuwa ba....
Mak’alewa tai jikin dogon gini tana mai sauk’e ajiyan zuciya a hankali, lokaci guda take k’arfafawa kanta gwiwa, zuciyarta na ayyana mata cewa zaki iya Saudatu... Zaki iya...
Lokaci guda taji wane irin k’warin gwiwa na zuwa mata... Abinka da gida na sarauta Kuyangi dik sabgogin gabansu suke babu mai noticing d’inta musamman dashike itama d’in shiga irinta mulki tai dan haka babu wanda zai kawo wani zargi ko shakku da kokonto a gameda ita....
Tafiya mai d’an tsawo sukai cikin Masarautar kafin Ta hangi Giwa da Jakadiya sunja sun tsaya jikin wani gajeren garu wanda saika kula sosai ka fahimci akwai d’aki wajen... Muhibbah ta kuma mak’alewa jikin gini tana mamakin mai sukeyi tsaye wajen nan.... Cen bada jimawa ba ta hango wani mutumi ya k’araso ya nufi k’ofan gajeren ginin yana k’ok’arin bud’ewa... Sam bazakai zaton akwai gini wajen ba... Tsananin mamaki ya kamata... Wai dama d’aki ne a wannan wajen.... Take ta kuma jin tana san ganin menene cikin d’akin nan... Ta d’an sad’d’o had’ida fitowa daga mab’oyar nata sanda taga sun sunkuya Sun shige cikin ‘yar d’akin nan....
Cikin sand’a Muhibbah ta k’araso jikin d’akin k’irjinta na tsananta fad’uwa.... Hankalinta bai ida tashi ba saida ta lek’a cikin d’akin yanda ta hango Giwa tsaye gaban wata mata dake duk’e gabanta an d’add’aureta da manyan sark’a.... Tsoro da firgici sosai ya kama Muhibbah ganin wannan matar dake d’aure da manyan sark’ok’i ba kowa bace illa wannan Mahaikaciyar da suka fara arba da ita farkon shigowarsu Masarautar....
Jikin Muhibbah ya d’auki rawa, take taji k’afafuwanta na yunk’urin gaza d’aukarta, hawaye taji na k’ok’arin ciko idanunta... Tai saurin saka hannayenta biyu ta toshe bakinta dan ko shakka babu kuka ne sosai Ke k’ok’arin b’alle mata... Innalillahi wa inna’ilaihi raji’un... Kalaman da zuciyarta Ke iya nanatawa kenan... Tai saurin komawa da baya ta jingina jikin garu har lokacin hawaye basu daina zarya a fuskarta ba... Hannayenta kuwa sosai ta k’unshe bakinta dasu dan karma sautin kukan ya bayyana.... Cikin sauri Tai k’ok’arin barin waje dan take taji duniyar na juya mata, take taji tana kewan gida, tana son kasancewa da Ansar da kuma Mummy....
Da k’yar ma ta fahimci hanyar databi har Ta samu Ta k’araso masauk’i... Tana k’arasowa d’aki ta fad’a saman gado tana kuka mai tsuma zuciya....
Tana a haka taji k’aran shigowan sak’o... Tai k’ok’arin mik’ewa Ta janyo wayar nata tana mai goge hawayen fuskarta... Ansar ne ya turo mata sak’on barkada safiya kaman yanda yakeyi ko wace safiya, yakan turo mata sak’o dan jin ya Ta kwana Ta kuma tashi....
Ta kuma saka bayan hannunta tana share hawayen bayan Ta ida karantawa... Ta saki murmushi a hankali tana mai jin dad’in sak’on da Ansar ya turo mata wanda ko yaushe sai ya fad’i mata how much he loves and misses her... Sosai taji tana son tafiya gida bayan ganin mahaukaciyar nan da tai cikin tsananin ukuba... Lallai Giwa tayi nisa a mugunta, azzaluma ce wacce batasan ta yanda zata misalta kalan zaluncinta ba... She wasn’t mistaken, she was right all along... Wannan masarauta babu komai cikinsa face bak’in zalunci.... Take Ta turama Ansar sak’o cewa tana zuwa gida gobe....
Koda Ansar yai receiving sak’onta yayita kiranta amma bata d’agawa, k’arshe haka ya hak’ura ya zubawa sarautar Allah ido dan yasan halin kayansa idan batayi niyyan bazata d’aga ba.... Haka nan take da kafiya akan dik abinda Ta saka gaba...
***
Washe gari kaw Ta kama monday tsaf tai shirinta da zummar tafiya makaranta, sassafe Ta shirya tin k’arfe bakwai ta nufo tasha ta d’auki hanyar Bauchi.... A hanya take ganin kiran Umaima, bata d’aga ba sai sak’o data tura mata cewa ta tafi makaranta tanada aji tin daga safiya har zuwa yamma, Umaima ta tura mata da sak’on nasara da fatan alkhairi... Murmushi Muhibbah tai tana ayyanawa cikin zuciyarta cewa tabbas Umaima ta banbanta da mutanen wannan masarauta...
Haka Fu’ad da Zahra suka tasa Umaima gaba da tambayar ko Ina Muhibbah, nan Umaiman Ta sanar dasu kaman yanda Muhibbah ta sanar da ita....
Fu’ad ya d’an dubi Umaima kana yace “Perfect place kenan for us be meeting nida ita....”
Umaima ta d’an murmusa kana tace “Prince F naga alama zuciyarka fah tai nisa bata jin kira...!”
Ya murmusa kad’an cikeda k’asaita wanda Ke k’ara masa kyau ba tareda yace komai ba....
**
BAUCHI
(Tambari Housing Estate)
Misalin k’arfe 8:30am ya shigo cikin parlorn sanye da tracksuit d’insa da alama daga motsa jiki yake.... Mummy da fitowarta daga kitchen kenan tai tsaye sororo tana dubansa...
“Kai kuma fah...? Wai ba ce min kai kamada appointment a asibiti 8:30am ba, ya na ganka a nan...?!”
Rage kayan jikinsa yake yana fad’in “Nayi shifting d’insa zuwa yamma ne...!” Ya fad’i yana nufa dining table...
Mahaifiyar tasa ta d’an kuma dubansa kana Ta tab’e baki kad’an tace “Wani wajen zaka jene...?”
Ya d’an girgiza kai kad’an yana mai bud’e foodflask d’in dake bisa dining table d’in lokaci guda yake furta “Ina nan a gida Mommy....!”
Ta d’anyi Jim tana dubansa kana Ta jinjina kai tana mai furta “Toh Allah shi taimaka....” Lokaci guda Ta nufi corridor ta barsa nan tsaye jikin dining table sai kuma shafa wayar salulansa yake...
Wayarta yaketa k’ok’arin nema amma bai samunta, gajeren tsaki ya saki a hankali kana ya fice daga parlorn ya nufi d’akinsa danyin wanka....
Wajajen k’arfe 9:30am Mommy na tsaye parking lot tana k’ok’arin bud’e mota da zummar tafiya aiki sai hango Muhibbah tai tana shigowa... Baki sake Mommy Ke dubanta, motar da bata shige ba Ta karkata sosai tana kuma dubanta...
Muhibbah na hango Mummy ta tafi da gudu ta rungumeta harda ‘yar tsallenta...
Mommy ta d’ago sosai tana dubanta kana tace “Wai wa nake gani haka kaman Hibba... Daga tafiya sch ko sati bakiyi ba shine har kinzo...?”
Muhibbah Ta d’an cuno baki gaba kana tace “Kai Mommy nifa kewarki nake sosai bazan iya sati ban ganki ba...”
Mommy ta d’an harareta kana tace “Toh mai amfanin wayarki basai muyi vid call ba....”
Kafad’a ta d’an mak’ake kana tace “Vid call daban zuwa daban Mommy...!”
Dungurinta Ta d’anyi tana fad’in “Kyaji da gulmarki dai... Kinga ni Office na nufa ma...”
Rik’eta Muhibbah tai tana fad’in “Chabb! Ai wllhi mommy tinda dai nazo ba wani tafiya Office nida yau yau zan juya Jos... Haba Mommy...!” Ta k’arashe tana kwantar da kai cikin jikinta had’ida janyota suka nufi cikin gida...
Ansar dake tsaye daga cen k’ofar parlornsa hannaye sakale cikin aljihun wandonsa ya nufo yanda suke...
Sukaima juna K’uri daga shi har Muhibbar....
Mommy Ta dubesu kana Ta jinjina kai tace “No wonder kak’i tafiya office ashe ta sanar dakai tana tafe... Kun k’ulla abunku dama tare..!”
Itadai Muhibbah murmushi kawai take shi kuwa Ansar babu wani walwala saman fuskarsa, saima kallon tuhuma da yake bin Muhibbar dashi....
Dikda ganin irin duban da Ansar ke mata hakan baisa tabi takansa ba saima dad’a shigewa jikin Mommy da tai tana fad’in yanda tayi kewarta...
Office d’in da Mommy bataje ba kenan suka b’ige da hira da d’iyarta har saida akai mata waya daga office d’in ana nemanta cikin gaggawa kafin ta kuma shirin fita...
Har bakin haraban gidan Muhibbah ta rako Mommy tana fad’in da la’asar zata wuce Jos ba lallai ta dawo ta sameta ba...
Mommy Ta d’an dafata kad’an kana tace “Banso kina tafiyan yamma yanzu lokaci ne na damuna Ki bari da safe Ansar ya maidake...”
Muhibbah ta d’an sadda kai kana tace “Mommy zanso hakan but first thing tomorrow morning inada class mai mahimmanci ne shisa...”
Mommy Ta d’anyi Jim kana tace “Oh is that so...? Toh ko na bar tafiya Office d’in na maidaki ne...”
Gaban Muhibbah ya ya Ke ya fad’I tai k’ok’arin saita kanta kana tace “No Mommy you don’t need to worry ai zan iya komawa da kaina...”
Girgiza mata kai Mommy tai kana tace “Ni drivers d’in nan ne ban wani aminta da tuk’insu ba musamman duba da yanda suke gudun fitan hankali saman kwalta ga kuma lokaci na damina....”
Kafin Muhibbah takaiga bata amsa suka sinkayo muryar Ansar yana fad’in “Zan mayar da ita Mommy..!”
Dubansa Mommy tai kana ta jinjina kai tace “Toh shikenan hakan yayi, amma kaima idan ka kaita sai kaika kwana cen Jos d’in gobe da safe idan Allah ya kaimu ido na ganin ido saika komo...”
Ansar ya jinjina mata kai yana mai amsawa... Mommy suka kuma yin sallama da Muhibbah kana ta shige mota tana fad’iwa Muhibbar “Nacewa Larai yau Ta girka favorite d’inki for lunch...”
Murmusawa Muhibbah ta kumayi cikedajin dad’i da k’aunar mommy kana suka kumayin sallama sannan Mommy ta fice tana mai mata fatan alkhairi...
Motar mommy na ficewa ta juyo kad’an tana duban Ansar dake jingine jikin k’arfen parking lot har lokacin fuskarsa babu walwala...
K’arasowa tai itama nata Fuskar babu walwala kana tace “Maiyasa ka cewa Mommy zaka maidani bayan ko gaisuwata baka amsa ba...?”
Da wutsiyar ido yake dubanta kana yace “Kaman bakisan laifin da kikai ba....!”
Ta kuma dubansa kad’an kana tace “Laifi kuma... wane irin laifi...?”
Faran kujera dake gefe ya janyo ya ajiye mata kana yace “Zauna..!” Babu musu ta gyara kujeran ta zauna shima ya janyo wata kujerar ya zauna...
Ansar yace “duba wayarki kiga sau nawa na kiraki...”
Murmusawa Ta d’anyi kana tace “Wannan ne yasa ake fushi dani Likita...?”
Ya d’an dubeta kana yace “Not only that... Maiyasa bazaki bari nazo na kawoki gida ba na maidake dakaina kaman yanda muka faro...Maiyasa zaki taso Ke d’ayanki Ki fito... What if wani abin yaje ya sameki Hibbah...?” Ya k’arashe cikeda damuwa...
“Relax Doc, babu abinda ya sameni... Haba saikace wata k’aramar yarinya... I can take care of myself fah Yaya Dr, kuma kaima bai kamata na katse maka aikinka ba ai... Nifa zan iya komawa ma, kawai kayi saurin fad’iwa Mommy zaka maidani ne...!”
Girgiza kansa yai kad’an kana yace “So tell me... Meke faruwa a cen Masarautar...?”
Gyara zamanta ta d’anyi had’ida fuzar da huci kad’an kana tace “Let’s not talk about that...besides nazo nan ne na mance da abubuwan dake faruwa, na d’an sami fresh air naga gida da mutanen da nayi kewarsu..”
Ansar ya d’an fito daga cikin kujeran fuska fal damuwa yake fad’in “Tell me did they do something to you..? Did they hot you...? Talk to me Hibbah... Mai suka miki...?!” Ya k’arashe cikeda tashin hankali...
Ganin yanda hankalinsa gaba d’aya ya kad’u sai ya bata tausayi, sosai Ansar ya damu da ita fiyeda yanda ta damu da kanta...
Girgiza masa kai kad’an tai kana tace “Basu mun komai ba.. But naga abinda ya d’aga min hankali ne... Ansar mutanen nan basuda imani...!”
Ansar ya kuma gyara zamansa yana fad’in “Tell me, mai kika gani...?”
Batakaiga basa amsa ba wayarta ya d’auki ruri... Bak’uwar lamba ce Babu suna... Ta d’anyi excusing kanta kana ta d’aga wayar da sallama...
Kaman baza’a mata magana ba dan har saida ta kumayin sallama tana tambayar ko wanene sannan taji anyi gyaran murya cikeda k’asaita....
Jin muryar Yarima Fu’ad cikin wayar ya sanyata d’ago fuska tana duban Ansar da shi d’inma ita yake duba....
SameenaAleeyou📚
[6/27, 10:26 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*024*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
“Barkada safiya Rankashidad’e..!” Ta fad’i murmushin da yafi kamada yak’e saman fuskarta...
Daga cen b’angaren Fu’ad ya murmusa kana yace “Ashe zaki d’auki muryata...”
Ta kuma murmusawa kana tace “Murya mai kaman busan sarewa ba’a mancesa cikin gaggawa Rankashi dad’e...!” Tai maganar cikeda k’issa...
Ansar dake zaune gabanta fuzar da fuci yai had’ida mik’ewa tsaye yana mai juya baya lokaci guda yana fuzar da fuci d’aya na bin d’aya...
Yana jin sanda Muhibbah ta kuma murmusawa tana fad’in yau d’in batada hutun tsakankanin class gaba d’aya busy day ne da ita bazasu iya had’uwa ba saidai next time... Ji yake kaman barbad’a masa garwashin wuta take a kunne da wannan wayar da take wanda ya tabbata ko shakka babu da d’aya ne daga cikin ‘Ya’yan Sarki AbdulJabbar take...
Kasa jurewa Ansar yai sai faman dunk’ule hannunsa yake yana sakin fuci, lokaci guda ya juyo had’ida fincike wayar daga hannunta ya kashe yana mai furta “Ok that’s enough.! Ya isa haka..!!”
Da mamaki Muhibbah ke dubansa, lokaci guda ta mik’e tsaye cikin tsananin b’acin rai “Ansar miye haka...? Ka
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 65