Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kar ta sace mata kai... Yaya Dan Allah....!” Kanta a k’asa tana duk’e take maganaganun saidai d’agowar da zatai ta hangi wajen wayam babu Mahmood babu dalilinsa, b’at ya b’ace a wajen ba tareda yace da ita k’ala ba.... Juwariyya ta sauk’e ajiyan zuciya a hankali had’ida dafe k’irjinta... Idan bata mance Innani na basu labari a lokutan baya idan aka sameka da laifin cin amana a Masarautar hukuncin kisa ake yankewa mutum idan bawa ne, idan kuma d’ah ne hukuncin shekaru masu yawa ake yanke masa a kurkukun masarauta... Ta kuma Sauk’e ajiyan zuciya a hankali tana mai ayyanawa har abada Ta dena aikiwa Raheema da Gimbiya Zeenat.. Yo ita koma sanin wanann Muhibbar da suke cewa tai masu bincike kanta batai ba....Toh wacece Muhibbah...? Sannan mai ya kawota Masarautar..?”Take taji tana son sanin ko wacece Muhibbah... Lokaci guda kuma ta shiga neman layin Raheema Dan sanar da ita abinda ke wakana.... Raheema dake kwance saman gado tana jiran Yazeed ya fito daga bathroom sai ganin kiran Juwariyya tai na kuma shigo mata... Tsuka tai had’ida tura wayar gefe tana furta “Banza kanki akeji har ni zaki nunawa Mulki da sarauta... Dama ki dawo kan hanya ne yarinya...!” Tana nan a haka Yazeed ya fito d’aure da towel yana goge sumarsa da k’arama guda d’aya... Cikeda salo Raheema ta mik’e ta isa gareshi had’ida shigewa cikin jikinsa tana fad’in “You look handsome my Prince..!” Yazeed ya tallafota suka nufo gadon a haka bakunansu cikin na juna.... Har wannan lokacin wayar Raheema bai daina ruri ba, k’arshe Yazeed ne ya danna wayar a silent saidai tuni Raheema ta hango shigowar sak’o tai k’ok’arin ture Yazeed kad’an Ta janyo wayar... Dik yanda Yazeed Ke k’ok’arin k’wace wayar Raheema tak’i saki har saida ta ida karance sak’on... Jikinta ya d’auki rawa... Innalillahi kawai take ambata, shikenan Mahmood yasan komai... Lallai wannan Juwariyyar anyi babban jaka gidahuma... K’ara Ta saki had’ida tura Yazeed daga kanta ta mik’e babu shiri tana k’ok’arin zira tufafinta.. Yazeed na tambayarta meke faruwa inaa ko amsasa batai ba ta suri handbag d’inta saida ta kusan k’ofa ta juyo tana fad’in “Zeed I can’t lose Mahmood... I just can’t, I need to go right now....!!” Bata ko jira cewar Yazeed ba Ta fice cikin sauri tamkar zata kifa k’Asa...... Yazeed ya fuzar da huci cikeda b’acin rai yana mai jifa da pillow guda, ya kuma dunk’ule hannunsa ya daki cikin katifa lokaci guda yake furta “Mahmood..! Komai Mahmood.. Kowa Mahmood...!! Mahmood Mahmood Mahmood..!! Zancen kenan, na gaji da jin wannan sunan... I hate you Mahmood... I hate you more than anything in this world...!!” Ya k’arashe yana mai kuma dukan garu da hannunsa kana ya mik’e ya soma shiryawa Shima... Ransa gaba d’aya a jagule...!! *** Har suka iso gida bai daina juya kalaman Juwariyya cikin kwanyarsa ba, if there’s one thing he hates shine ai abu akansa bayan idanunsa koda abin amfanin kansa ne.... For what Raheema zatai masa haka...! Ita wacece da zatai katsalandan haka cikin rayuwarsa... Waya bata wannan damar...?!! Yana tinanin yana mai ci gaba da murza zoben azirfa dake yatsarsa guda... Idanunsa kaw tinda ya shige motar na kallon window... Fu’ad dake gefensa ya kula da yanda yanayin Yayan nasa ya canza tin bayan shigowarsa motar... Yaso tambayarsa ko akwai abindake damunsa ne amma sai yai shiru zuciyarsa na mai raya masa cewa k’ila sabida ganin jikin Baba Wambai ne ya sanyasa cikin yanayin... A haka suka iso Fada... Suna isowa Ubandoma dake zaune gaban Jeep d’in ya fito ya bud’ewa Mahmood yanai masa Fadanci... Dogarai ma sai zuba masu fadanci suke daga Mahmood d’in har Fu’ad... Fu’ad yaso bin bayan d’anuwansa ganin yanda ya shige sashensa cikin sauri yana fad’iwa Ubandoma yai masa kiran Jakadiya.... K’arar da wayar Fu’ad d’in yai ya sanyasa baibi bayan Mahmood ba... Sahibarsa Muhibbah ce mai kira, Dan tinda ta hangi shigowar mota Fada jikinta ya bata su Fu’ad da Mahmood ne suka dawo... Fu’ad ya d’aga wayar cikeda jin dad’i yana mai zolayarta da fad’in har tayi kewarsa kenan tinda basu jima da yin waya ba.... Daga d’aya b’angaren Muhibbah ta murmusa kad’an kana tace “Karka laifina Prince... Soyayya Ke d’awainiya dani...!” Fu’ad ya kuma murmusawa kana yace “Toh ai ked’in ce kin hanani ganin kyakkyawar fuskarki cikin Fada da yanzu na k’araso har yanda kike....!” Ta kuma murmusawa kad’an kana tace “Gida na sarauta Rankashi dad’e sai anayi ana taka tsantsan kasan abin magana baya kad’an a gida irin naku, ni kuma bazanso naga abinda zai b’ata maka suna da martabarka ba dukda cewa ba abu maras kyau mukeyi ba...but nasan da yawa bazasu fahimcemu ba only few can understand...!” Ta k’arashe cikeda k’issa... Fu’ad ya jinjina kai yana mai amintada kalamanta yake fad’in “K’warai kuwa kinyi gaskiya Gimbiyata... Abun magana baya kad’an a wannan gida namu... Ni d’in shaida ne, kuma bazanso na zamto silan da zaisa ki bar Masarautar nan ba...Zanyi hak’uri naci gaba da ganinki a makaranta har zuwa lokacinda zaki amince mu bayyana soyayarmu ga kowa a cikin Masarautar nan....!” Rausayar da idanu tai cikeda k’osawa Dan Allah na gani kan sole take waya da Fu’ad, jin muryarsa da kalamansa take tamkar garwashin wuta cikin kunnuwarta... Lokaci guda ta saki murmushin dole da k’yar kana tace “So Ya kuka sami mai jiki....?” Fu’ad yace “Toh gashi nan dai bazamuce babu sauk’iba.. An godewa Allah... But yanda mukaga jikin Baba Wambai da alama ya d’aga hankalin Yaya Dan koda muka dawo tuni ya nufi sashensa, dik yanda yake k’ok’arin b’oye tashin hankalinsa hakan taci tura saida fuskarsa ya nuna... Tinda naji yayi kiran Jakadiya nasan hankalinsa a matuk’ar tashe yake... Yayana ya fuskanci rashi da dama a rayuwarsa ga mahaifinmu ga kuma matarsa shisa yakega kaman zai kuma rasa Baba Wambai ne...!” Ya k’arashe cikeda kulawa... Muhibbah Ta mik’e daga zaunen da take cikin sauri Dan tinda taji Fu’ad yace Mahmood yayi kiran Jakadiya jikinta ya bata wani abin Ke faruwa, ya zama dole tasan yanda zatai ta shiga sashen Mahmood danjin abinda zai tattauna da Jakadiya.... Suna ida waya da Fu’ad ta mik’e tai shirinta tsaf kana ta nufi sashen Mahmood a sace... Tana mak’ale jikin gini ta hango Jakadiya ta nufi sashen Yarima Mahmood Gimbiya Raheema na biye bayanta... Muhibbah ta murmusa a hankali tana mai ayyanawa dama jikinta ya bata sauyawan Mahmood da Fu’ad yace nada babban dalili... Suna shigewa ta sad’ad’o a hankali, daidai lokacinda Jakadiya ke magana da Dogarai masu tsaron k’ofa hakan ya bata daman shigewa cikin sand’a ba tareda sunyi noticing d’inta ba... SameenaAleeyou*MUHIBBAH* *029* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Tsaye ta hangosa yana fuskantar window ya baiwa parlorn baya, k’irjin Raheema yaci gaba da dukan tara tara... Harga Allah batasan mai zatace ba, batasan da wata kalma zata soma kare kanta gaban Yarima Mahmood ba, ganin har Ta ida shigowa cikin parlorn tai tsaye bai juyo ba bai kuma tankata ba abin ya kuma tada mata hankali... Ta soma k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta da nufin gaidashi.. Har lokacin baice da ita komai ba bai kuma juyo ba... Itadai Muhibbah na rakub’e daga gefe tana kallon ikon Allah... Saida suka kwashe dak’ik’ai a haka kana Mahmood ya juyo har lokacin hannayensa hard’e ta baya... Ba Raheema dake tsaye cikin parlorn ba harta Muhibbah saida yanayin fuskar Mahmood ya bata tsoro... Zatace bata tab’a ganin tsananin b’acin rai kwance saman fuskarsa kaman yanda Ta gani yau ba.... Raheema kaw rawa jikinta ya d’auka gaba d’aya sai ta tsure gani take tamkar yasan alak’ar dake tsakaninta da d’an uwansa Yazeed ne... Ta had’iyi miyau d’in da ya tsaya mata a mak’ogoro da k’yar... Kujera yai mata nuni murya a dake ya furta “Zauna...!” Jiki a matuk’ar sanyaye ta isa ta zauna kaman yanda yace.. Lokaci guda shima ya tako ya zauna a kujera guda... Dak’ik’ai suka kuma shud’ewa a haka kaman babu mai cewa komai cikinsu har saida Raheema Ta d’an d’ago ta saci kallonsa, tai saurin maida kanta k’asa zuciyarta naci gaba da tsinkewa... Hardai Muhibbah ta sadakar Bawan Allahn nan bazaice komai ba sai kuma ta sinkayo muryarsa mai amo kama daga sama yana furta “Maiyasa kika aikat..Why..?!!” Yai tambayar yana mai tsare Raheema da idanu... Raheema taci gaba da k’ok’arin had’o kalamai saman harshenta “Your Highness... Wllhi Allah ni dama kawai I wanted to help ne...Allah wllhi ni taimakonka nake son y.....!” Katseta yai da fad’in “Na tab’a neman taimakonki..?!” Tai saurin girgiza kai alamun a’a... “Na tambayeki ki taimaka min...?!” Nanma girgiza kai tai alamun a’a... “Namiki kamada mabuk’acin taimako daga wajenki..?!” Izuwa lokacin Hawaye sun soma wanke fuskar Raheema tai saurin girgiza masa kai tana mai furta “Dan Allah Your Highness kai hak’uri... Na sani na shiga hurumin da ba nawa ba but in sha Allah bazan sake ba... Dan Allah kai hak’uri ka yafe min...!” Mahmood yai mata K’uri yana karantarta kana ya kumayin gyaran murya kad’an yace “Kinsan hukuncin abinda kika aikata a dokan Masarautar nan...?!” Tai saurin d’agowa a zabure tana dubanta zuciyarta naci gaba da tsinkewa....Lokaci guda taci gaba da girgiza kai had’ida had’a hannayenta biyu waje guda “Rankaidad’e dan Allah kai hak’uri... Dan Allah kada ka sallameni daga Masarautar nan... Dan Allah kada ka bari a maidani Masarautar mu... Wllhi ina matuk’ar k’aunarka Yarima... Bazan rayuwa babu kai ba....!” Ta k’arashe tana mai kuma sakin sabon kuka.... Yai mata k’uri yana dubanta cikin yanayin zamansa irinta masu mulki ba tareda ya furta mata komai ba... Har saida kukan ya tsagaita dan kansa kana yace “Banikeda alhakin sallamarki daga Masarautar nan ba dan har yanzu ni ba sarki bane... Ita kuma wacce kikasa ai bincike akanta fah...?” Gaban Muhibbah ya yanke ya fad’i, wacece Raheema tasa abincika mata...? Bata ida tinanin ba ta sinkayo muryar Raheemar tana fad’in “Your Highness wllhi sharrin Juwariyya ne ni ban umarceta tai wani binciken k’wak’waf kan Muhibbah ba... Yarima dan Allah ka yarda dani... Why would I have her investigated... What for..? Wllhi sharri ne kawai irin ta mutanen Fada...!” Ta k’arashe cikin tsananin rawar murya mai raunin gaske... Daidai nan Ubandoma ya shigo parlorn yana mai zubewa k’asa yake fad’in “Ina mai neman afuwan Babban Yariman Masarautar nan da shigowa da nai Kai tsaye...Tuba nake Allah shi baka yawan rai...!” Mahmood yace “Ina saurarenka Ubandoma meke tafeda kai....?!” Ubandoma yaci gaba da fad’in “Dama su Galadima Danmadami da Talba da kuma D’anisa harmada Madaki ne sukace ai masu iso wajenka... Gaba d’aya suna haraba suna jiranka Allah shi baka yawan rai...!” Jinjina kai Mahmood yai kana yace “Ubandoma..!” Ubandoma ya amsa cikeda ladabi kana Mahmood ya k’arada “A bud’e masu Galadima Babban gwani su shiga ciki Ina nan tafe..!” Ubandoma ya kuma rusinawa yana mai amsawa had’ida mik’a gaisuwarsa ga Raheema tareda mata kirari kana ya mik’e da azama dan isarda sak’on ubangidansa... Ubandoma na ficewa Raheema ta kuma kifa kanta tamkar wata mumina tana mai ci gaba da shesshek’an kuka dan kawai Mahmood yaji tausayinta... Tsaye ya mik’e yana mai fuskantar center hannayensa hard’e Ta baya irin tsayuwar da masu mulki suka faye yinta... Lokaci guda ya karkato da fiskarsa yana dubanta kaman zai magana sai kuma yasa kai yai shigewarsa cikin tafiya da tafi kama da sassarfa... Yana ficewa Raheema Ta d’ago kanta had’ida sakin makirin murmushi, a fili take furta “Sannu a hankali zaka shigo hannuna..!” Ta kuma sakin murmushi kana ta waiga gefe da gefe... Lokaci guda tai azamar mik’ewa tsaye yayinda Muhibbah ta kuma mak’alewa bayan staircase tana hangota sosai... Cikin azama Raheema ta shiga d’aga alkyabbarta, tai saurin zak’ulo wani garin magani dake d’aure cikin leda bak’a... Ta kwance d’aurin cikin sauri kana ta isa saman kujerar da Mahmood ya faye zama.. Nan ta saki murmushi sannan Ta soma barbad’a garin maganin, haka tabi sauran kujerunma duk ta barbad’a sannan ta yayyafa a bakin k’ofar fita... Tana ida barbad’e barbad’enta ta cusa ledar maganin cikin alkyabbarta kana ta bubbuge hannayenta ta gyara zaman alkyabbarta sosai sannan Ta fice daga sashen zuciyarta nai mata sanyi... Tasan yau dole Aunty Zeenat tai alfahari da ita... Yau dai kam ta cika aiki tasan babu yanda za’ai Mahmood tsallake tarkonsu yau tinda hardai zai shiga sashen dole ya bi ta saman shirinsu sannan hardai zai zauna a parlorn toh fa sai ya zauna akan shirinsu... Daga rana mai kaman ta yau Mahmood ya zamto sai yanda tai dashi a Masarautar.... Raheema na ficewa Muhibbah ta sad’ad’o ta fito tana mamakin abubuwan da taga Raheema ta barbad’a... Ta K’araso cikin parlorn sosai tana ware idanunta ko zataga alamun garin magani amma to her surprise babu ko alamun gari... Bazaka tab’a cewa an zuba wani abu mai kaman gari wajen ba... Tsaye tai tana tinanin abinyi kafin wani ya shigo ya ganta a sashen.. Amma kam tabbas sai tayi yanda tasan ta kawar da abinda idanunta sukaga Raheema ta barbad’a koda ace bata iya ganin abin a zahiri... Waige waige ta soma cikin parlorn nan ta hangi goran ruwa saman dining table, tai saurin k’arasawa Ta d’auko goran ruwan, cikin azama ta warware d’aurin d’ankwalinta ta zuba ruwan ta jik’a d’ankwalinta dashi kana tabi gaba d’aya kujerun Ta gogesu da d’ankwalinta mai damshin ruwa... Haka dik yanda taga Raheema tayi barbad’an a parlorn saida tabi Ta goge tsaf... Harta da bakin k’ofan parlorn saida shima ta goge shi tass... Tana idawa ta Sauk’e huci a hankali kana tai k’ok’arin sad’ad’awa Ta fice daga sashen.... Saida ta isa masauk’i kuma ta soma tuhumar kanta, maiyasa ma zata taimaki Mahmood... Maiyasa bazata K’yalesa ya fad’a tarkon Raheema ba..? Wata zuciya tace hakan da kikai shine daidai dan idan kika bari asirinsu Raheema yai tasiri akansa toh fah zaki rama abinda yai maki ne bashi a cikin hayyacinsa... Gwara yana cikin hankalinsa yanda zaifi jin zafin duk abubuwan da zaki masa... Abinda kikai kinyi daidai Muhibbah ba taimakon mak’iyinki kikai ba... Ta k’arshe tinanin tana mai zama cikin sofa lokaci guda tunanin abinda taji Raheema na fad’i ya dawo mata... Wato binciken k’wak’wafa Raheema zata saka ai akanta... Idan kuwa haka ne toh fah zama bai ganta ba... Ya zama dole ta toshe duk wani hanya da real identity d’inta zai bayyana... Bazata bari Raheema Ta kawo mata cikas a shirinta ba... Toh ya zatai mai zata farayi... Ta ina zata b’ullowa Al’amarin...? Tai zaune tana tinani... Idan har Raheema zatai bincike kanta Toh fah saidai Ta tafi makarantarsu ta soma binciken don ta nan ne kawai zata iya yin bincikenta cikin sauk’i tinda ita ba ‘yar gari bace...! “Ansar...!” Ta furta a hankali... Shine kawai mutumin da zai zamto mata cover... Tai saurin janyo wayar salulantar da zummar dialing layin Ansar sai kuma taji jikinta yai matuk’ar yin sanyi ganin rabuwarsu Ta k’arshe da Fad’a suka rabu... Ta kuma ce masa bazata sake tambayar komai daga garesa ba koda shawari ne...Ta lumshe idanunta a hankali tana mai ije wayar gefe guda... *** A can babban gwani kuwa masu sarautar sunyi zaune gaba d’aya... Su Waziri Galadima Hakimi da Talba da dai sauransu, Sun zagaye Karagar Mulki dake daga center... Mahmood na gefen Waziri Talba yaci gaba da fad’in “Bazai yuwu mu zauna haka nan babu sarki ba har yanzu... Kundai ga abinda ya sami Wambai, kai tsaye bazance wanine ke nufinsa da sharri ba amma mu munsan gida irin namu... Tinda cikinta aka haifemu muka kuma yi wayo cikinta har kawowa girmanmu... Idan muka zauna muka zuba idanu toh haka kaf sai anbi kanmu d’aya bayan d’aya an illatamu.... A ajiye maganan b’angaranci da son Mulki a gefe kowa yayi hak’uri a baiwa wanda ya cancanta mulkin nan... Kuma ni nan na janye neman mulkin nan da nake na mik’a wuyaga d’ah na Mahmooda dan shine ya cancanci wannan sarauta...!” Su Waziri gaba d’aya suka shiga jinjina kai suna furta “Wannan gaskiya ne Mai Girma Talba....!” Dogarai dake tsartsaye gefe suka soma wasa Mahmood suna fad’in Allah ya bashi dama gadon gidansu ne... Talba yaci gaba da fad’in “Alhamdulillahi tinda duk munyi na’am sai a tsayar da ranan da za’a nad’a Sarki Mahmooda na biyu... Idan kuma akwai wanda bai amince ba sai muji dalilinsa..!!” Kaman daga sama suka sinkayo murya cikeda iko da gadara yana fad’in “K’warai kuwa akwai wanda bai amince ba..!!!” Gaba d’aya suka kaikaito suna duban k’ofar had’ida da mamakin wanda yai maganar.... Waziri ya kifa kansa kurum yana girgizawa a hankali.... SameenaAleeyou 📚[7/8, 10:10 AM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH* *030* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* “Majidad’i...!!!” Hakimin gari ya furta cikeda mamaki sanda Majidad’i yaci gaba da kutso Kai cikin tampatstetsen parlorn... Shamak’i ya zube yana kwasan gaisuwa yake furta “Ku gafarceni Majidad’i yak’i sauraro na saima nuna min takwabi da yai a wuyana.!” Ya k’arashe yana muzurai alamun har lokacin tsoro ne dabaibaye dashi... Masu sarautun gargajiya suka soma mik’ewa tsaye babu shiri ganin zarkwad’ed’iyar takwabin dake rik’e hannun Majidad’i sai faman shek’i take tana k’yalli.... Waziri yai azama yana mai furta “Kai Majidad’i lafiyarka... Meye haka nake gani... Ka kuwa San mai kake aikatawa..? Ka kuwa San ko ina kake... Ko kuwa hankalinka ne ya gushe...?!!” Cikeda izza had’ida rashin tsoro Majidad’i yace “K’warai kuwa Waziri babu wanda ya isa ya d’ale Karagar nan muddin ba’a zak’ulo mutumin da ya illata min mahaifina ba... Sannan sanin kanku ne muddin Wambai na numfashi a doron k’asa sai da yardarsa da amincewarsa a nad’a Sabon sarki a Masarautar nan.... Oh Wato kunzo nan kun had’e kawunanku zaku nad’a sabon sarki mahaifina nacen kwance... Toh ina mai tabbatar maku babu wanda zai hau Karagar nan har sai an zak’ulo wad’anda Keda alhakin kasancewar mahaifina a haka... A shirye nake na fafata da dik wani wanda yace zai jayayya dani....!!” Ya k’arashe yana mai ci gaba da sakin huci... Cikin tsananin b’acin rai Waziri Ke furta “Kayi kuskure Majidad’i.. Ka wulak’anta gidan nan kaci mutuncin ahalinta dan haka dole ka amshi horo... Sarkin Gidaaa...!!! Yai maganar cikin d’aga murya yana mai ci gaba da fad’in “A d’auke Majidad’i a tafi dashi Gidan Yarin Wutin gadi....!!!” Take Majidad’i ya bada balance ya d’aga takwabinsa yana fad’in dik wanda ya nufo yanda yake sai ya fille kansa... Mahmood ne ya tako gabansa ba tareda shakku ko tsoron makamin dake hannun Majidad’i ba... Gaba d’aya sukai K’uri suna duban ikon Allah... Majidad’i yana duban Mahmood take ci gaba da sakin huci yana kuma d’aga takwabin nasa sama.... Cikin tsananin huci yake k’ok’arin kaiwa Mahmood d’in sara ganin bai daina takowa yanda yake ba... Saidai ga tsananin mamakinsu tuni Mahmood yakaiwa takwabin damk’a ya rik’e sosai cikin tafin hannunsa dukda tsananin kaifi da takwabin kedashi.... Majidad’i yaci gaba da huci yana k’ok’arin cire takwabin daga cikin hannun Mahmood amma abu yaci tura... Su kansu saida sukai mamaki ga kuma jini dake gangarowa daga cikin tafin hannun Mahmood d’in alamun yanka... Su Galadima su Waziri sukai K’uri suna duban ikon Allah dan gaba d’aya sai Yarima Mahmood ya juye masu mahaifinsa Sarki AbdulJabbar.... Galadima da Waziri suka dubi juna a tare idanunsu na firfitowa waje sosai.... Sarkin Yak’i kuwa tuni ya daka tsalle ya zaro takwabin dake mak’ale gefen d’amaransa wanda dama dik sanda za’ai taro cikin Fada da d’amararsa ta yak’i yake halarta.... D’aga masa hannu guda Mahmood yai alamun dakatarwa kana ya maidoda dubansaga Majidad’i dake ci gaba da sakin huci har lokacin bai iya k’wace takwabin daga cikin hannun Mahmood ba.... Ga tsananin mamakinsu k’asaitaccen murmushi Mahmood ya sakarwa Majidad’i saikace baijin zafin yankar wuk’an na ratsa sa, lokaci guda yake furta “Ka kwantar da hankalinka D’anuwana, kaman yanda kace babu wanda zai hau Karagar nan har sai an binciko musabbabin ciwon Baba Wambai... Idan don ni Mahmood ne na amince da haka d’in... Ka sani Babu wani Sarki da zaiso a zubar da jini a mulkinsa, kuma babu wani sarkin da zaiso yaga an zubar da jinin Al’ummansa kafin ya d’ale Karagar mulki.... Zamanin yanzu yasha bambam da wancan zamanin, kasan ance Sarki goma Zamani goma..!” Ya k’arashe yana mai jifa da takwabin dake damk’e cikin hannunsa guda wanda ko motsata Majidad’i ya kasayi... Waziri ya had’iyi miyau da k’yar wanda tai masa k’ebebe a mak’ogoro... Lallai yau yaga jarumtar Mahmooda, sam bai tab’a kawowa shid’in zai jarumta irinta mahaifinsa ba sai gashi yana nema ya zarce AbdulJabbar... Anya bokan Turai bai shera mata k’arya ba kuwa... Anya idan suka sake Mulkin nan ya fad’o hannun Mahmooda zasu cimma burinsu cikin sauk’i kuwa...? Gaba d’aya Waziri ya zama lost, gaba d’aya yama rasa abinyi... Tsoro da tashin hankali sun cika zuciyarsa sosai... Mahmood nayin jifa da takwabin Dakaru suka K’araso a tamanin suka capke Majidad’i Waziri na fad’in a tafi dashi fursuna.... Mahmood ne ya dakatar dasu da fad’in “Ku sakeshi, ku k’yaleshi yai tafiyarsa... Amma wannan zai zamto gargad’i na k’arshe da zai kutso cikin Fada da takwabi tsirarta alhalin masarauta na cikin lumana.... Ubandoma..!!!” Ubandoma ya k’araso had’ida zubewa gaban Mahmood yana mai furta “Rabkaidad’e..!!!” Mahmood yaci gaba da fad’in “Ka raka Majidad’i har zuwa bakin k’ofar Masarauta, a tabbata Majidad’i ya fice daga cikin Masarauta cikin lumana da aminci....!!” Ubandoma ya kuma risinawa yana mai amsawa kana ya tasa k’eyar Majidad’i yana fad’in “Godiya Majidad’i yake Allah shi baka yawan rai...!!” D’anmaliki da Talba suka dubi Mahmood cikeda jin dad’in abinda yayi yanzu, hakan ya kuma tabbatar masu da cancantar Mahmood na zama Sarkinsu na gaba... Haka aka san Sarki da jib’antan lamuran Al’ummansa had’ida jarumta da kuma rangwame da sassauci ga wad’anda Allah ya hukunta masa zamtowa shugaba a garesu... Abinda Majidad’i yayi yaci a tafi dashi gidan Yari amma Mahmood yai masa afuwa ya kuma ce ai masa rakiya har k’ofar Fada a tabbata ya fita lafiya cikin aminci sannan ya janye sarautar da aka basa har sai an warware wasu al’amara a Masarautar kaman ciwon Baba Wambai dan shi bai yarda Bak’on Buzu nada alak’a da ciwon Wambai ba tinda dai yasan shid’in shine bak’on Buzu... Baisan dalili ba amma jikinsa na basa akwai wata k’ulleleliya a al’amarin.... ** Bayan an watse a Fada ne Waziri ya k’araso yana kuma ingiza Mahmood cewa lallai ya d’ale Karagar nan a yanzu, dan hakan ne kawai zai basa daman aiwatar da al’amara yanda suka kamata... Ya k’arada “Rankaidad’e Kaga dai yanda maras kunyar yaron nan d’an wajen Wambai ya shigo yai abin kunya da Allah wadai cikin Fada, na tabbata Mahaifiyarka bazataji dad’i ba muddin taji cewa Kingmakers sunyi ma’am gaba d’aya cewa ka zamto Sarki harma ana k’ok’arin tsaida ranan rantsar dakai matsayin Sarkin wanann nahiya tamu mai babban daraja amma kak’i kace a sarara zuwa wani lokaci... Rankaidad’e da dai an duba lamarin... Wanann sarauta dama gadonka ne Allah shi taimakeka...!” Ya k’arashe yana mai kuma k’ank’an dakai... Shiru tamkar mai nazari Mahmood yai hannunsa mai d’igan jini na dunk’ule yake furta “Waziri..!!” Waziri yai saurin mik’o masa jinjina yana mai amsawa... Mahmood yaci gaba da fad’in “Ina labarin neman Jafar da na wakiltaka.... Shin a ina aka tsaya...?!” Waziri ya had’iyi miyau da k’yar kana ya soma fad’in “Allah shi baka yawan rai, ai shi Bawa idan ya samu wata ‘yar k’ofar da zai tsere sam bazai tsaya gari kusa ba... Allah shi taimaki Saraki Babban Sarki a wannan daula tamu Jafar babu shi babu labarinsa... Babu hanyar da bamubi ba harta hanyoyin bincike na zamani dana gargajiya duk munbi amma shiru babu wani labari gameda Bawa Jafaru...!!” K’uri Mahmood yaima k’ofa yayinda Waziri yaci gaba da muzurai yana k’ok’arin had’iyi tuk’in goro da ya tsaya masa a mak’oshi... Bai kuma furta komai ba sai sa kai da yai ya fice daga parlorn hannayensa hard’e ta baya... Waziri yabi bayansa da kallo yana mai tofar da tuk’in goron dake bakinsa kaman ya bisa ya shak’esa... Lokaci guda yake sakin huci yana furta “Zamaninka mai k’aramin wa’adi ne Mahmooda... Zakabi zahun mahaifinka nan bada jimawa ba... Bazan tab’a bari jarumtarka na k’arya ya bani tsoro ba... Nayi Imani Sarki Yazeed sai yafika Jarumta dan ko a yanzu ma bazaka nuna masa komai ba...!!” Ya k’arshe yana mai sab’a babban garensa kana ya fice daga Masarautar cikin sauri dan a daren yau yakeso ya tura ‘yanta’adda zuwa gidan Wambai dan su zak’ulo masa k’undi koda kuwa a k’asan gini Wambai ya b’oye... *** A b’angaren Yarima Mahmood kuwa yana fitowa sashen Giwa ya nufa, kuyangi sai risinawa suke suna gaidasa had’ida basa hanya... Dik yanda ya shige kuwa jinin yankan hannunsa na nan na d’iga dukda cewa ya dunk’ule hannun sosai saidai abinka da yankan takobi ba k’aramin yanka bane.... B’angaren matakalan da zai sadaka da babban Parlorn Giwa ya nufa sai kuma yaja ya tsaya sakamakon sinkayo muryar d’iyarsa Zahra cikeda annashuwa... Haka kurum

Chapter 18 of 65