Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ajeta ai..?!” Barde ya jinjina kai yace “K’warai Rankaidad’e...!” Mahmood ya kuma daidaita tsayuwarsa yace “Akai Kuyangin wajen, aikinsu kenan su dinga kula da ita, kama daga abinda zataci zuwa komai na buk’atarta... Koda wasa kada a bari ta lek’o koda k’ofa ne har sai idan ni ne na umarta..!” Barde ya kuma risinawa yace “An gama Allah shi taimakeka...! Jaaa zamaninka dogon Sarki mai dogon zamani..!” Ya gama kirariwa Ubangidan nasa kana ya mik’e ya fice... Barde na ficewa Turaki da har lokacin bai daina sakin murmushi a hankali ba yace “Rankaidad’e ango yanzu haka za’ai hidimar nan bazaai shelan auren mai Martaba cikin Fada ba..! Ko Haka zaka tare ne bazaka bari ahalin Fada su shaida ba..!” Ya k’arashe cikin sigan zolaya yana sosa kai... Wani irin duba kurum Mahmood d’in ya aika masa, Turaki yai murmushi da tafi kama da yak’e yace “Tuba nake Allah shi taimakeka...!!” Girgiza kai kurum Mahmood d’in yayi yace “Kanada gaggawa Turaki... Sau nawa zan ce maka Ina buk’atarta cikin Masarautar nan shiyasa na aurota kafin su aurarta ga wani... Idan amfaninta ya k’are a cikin Masarautar nan zan sawwak’e mata taje ta auri wanda take so.. Babu wani abu da zai shiga taakanina da ita.. Hakan yasa na killaceta b’angare guda..! Ka fahimta..?!” Turaki ya jinjina kai yana mai k’ok’arin matse dariyarsa dan ko babu komai gaban Sarki yake... Shidai yanzu hankalinsa ya kwanta tinda bai aurarta ga wani cikin Masarautar ba ya aurawa kansa, yasan daga baya zai yarda da batunsa cewa sonta yake... Sallama Turaki yai masa dan shi kam ba baisan auren Raheema da Yazeed Mahmood ya umarta a d’aura ba... Hakan yasa baibi takan ahalin masaeautar ba yai tafiyarsa gida dan huta gajjiya daga baya yazo yayiwa Jamal murnan aure... ** Yazeed dake zaune spot d’insu shida abokansa su Zayyad suna kuma kid’asa dan ya sanar dasu daga yau ya zama Sarki, sabida ana d’aura auren Mahmood zai d’auki matarsa su koma Spain... Abokan sai kuma haukatasa suke suna duk’awa gabansa suna fad’in Allah shi taimakeka Rankaidad’e Mai Martaba Sarki Mai talakawa...! Zayyad ne ya koma gefe yana amsa waya da alama labarin ta iso masa da d’umi d’uminta... Dama a ido ne suke nuawa Yazeed suna sonsa cikin zuciyarsu kuwa har kullum downfall d’insa suke son gani shiyasa duk abotan da ba’a gina cikin tsoron Allah ba ka guji irin wannan abota da wad’annan miyagun abokai wanda zasu kaika su baroka... Babu shiri Zayyad ya k’araso yana labarta masu labarin da yaji... Tamkar sauk’an aradu haka Yazeed yaji abun, ya mik’e ya cakumo Zayyad yana fad’in “K’arya kake... K’arya kake Zayyad Mahmood ne ya auri Raheema kuma d’aukanta zai su tafi Spain ni ne nan zan zama Sarki..!!” Zayyad ya finciki wuyarsa daga hannun Yazeed yana furta “Ka zaci zan maka k’arya ne haka kawai, ai taimakonku yayi daga kai har Raheemar ya aura maku juna yanzu sai kuyi wanda babu zunubi sai Lada Your Highness ko ya kukace guys..?!” Ya k’arashe yana duban sauran abokan... Gaba d’aya suka tuntsure da dariya suna jinjina k’arfin hali irin na Mahmood, kuma abinda Mahmood d’in yayi sosai ya burgesu... Sai dariya sukewa Yazeed suna fad’in karfa ya zama loser da gaske... Mahmood ya d’arasa a ko ina... Da alama sarautar nan bazai tab’a gadanta ba... Huci kurum Yazeed yake yana ayyanawa cikin zuciyarsa Wai Yayansa Mahmood ya aura masa Raheema... Kenan shi bai aureta ba ya aura masa, kenan shirinsu ya b’aci, Mahmood bazai koma can k’asar Spain ba... Waima sabida tsaban wulak’anci da bai aureta ba shine bari ya aura masa... Who does he think he is da zai dinga yin abu gaba gad’i ba tareda neman izinin kowa ba... Lallai ma Mahmood ya wuce iyakarsa.. Waye ya basa daman deciding ma rayuwarsa... Wllhi ya taro fad’an da bazai iya, yau sai ya shayar dashi mamaki ya nuna masa bai isa dashi ba...! Fuuu ya mik’e yai ficewarsa... Zayyad yasha gabansa yace “Your Highness the bill waye zai settling bills...?!” Rai b’ace Yazeed ya ciro card d’insa ya mik’awa Zayyad zai fice Zayyad yace “No Your Highness, na sani ko empty account ka bani, ai jira zakai a duba a gani...!” Shi dai Yazeed bai iya cewa komai ba sai tururi da yake... Aiko ana zuwa wajen biyan Kud’i kati yak’iyi saima nuna declined da yakeyi... Yazeed da mamaki yake dubansa kenan an rufe katinsa bazai samu access to family account d’insu na cikin Fada ba... Gashi d’aya account d’insa babu kud’i ciki kwanakin baya abokan sunyi duping d’insa ba tareda saninsa ba suka kwashe miliyoyin dake ciki... Zuciyar Yazeed kaman zata tsage ta fito waje... Lallai Mahmood ya gama raina masa wayo... Toh wllhi yau sai anyita ta k’are koda zasu raba zumunta ne na har abada...! Yana ficewa abokan suka bisa da kallo suka fashe da dariya Zayyad na fad’in “Idan talauci Ta cinyesa ya kawo min SUV d’in nan na saya a wulak’ance dan nasan za’a kai wannan stage d’in dama ni ita nake hari..!” Sauran abokan suka kuma kwashewa da dariya d’ayan na fad’in shi kuma Ford d’in Yazeed d’in zai saya idan an karya mata farashi..! Haka suka dinga aibata Yazeed suna fad’in yanda suke tsananin son ganin k’arahensa a tsiyance... ** Da tsananin mamaki Giwa take duban Waziri da alama da matarsa ya gama waya yana sanar da ita amfani kawai yakeda Giwa tinda ta gama aminta dashi idan suka kawar da Mahmood shi kuma bazai bari Yazeed ya d’ale karaga ba kaman yanda Giwa taci buri... Zaisan yanda zai ya kawar da Yazeed sarauta ya zamto nasu...! Yau saiga hawaye na fitowa daga idanun Giwa jin irin bak’in cin amana da Waziri ya tasamma yi mata.... Giwa na hawaye take furta “Ni zaka cuta Shayibu... Ka rasa wa zaka cuta saini... Kana ikirarin kashe d’ah na dan ka d’ale karaga.. Bayan duk fad’i tashin da mukayi tare ashe cin dunduniyata kake ban sani ba... Shayibu ka bani mamaki.. Ni Turai zaka cuta..!” Waziri na muzurai yake furta “Baki fahimceni bane Rankidad’e, kinsan halinku mata saida dabara... Ta tab’a kamani ina waya dakene shine nai mata wayo nace da ita munafuntarki nake don na sami yardarki... Idan ba ya haka ba bazan tab’a shawo kanta ba da yanzu tuntuni ta jima da fallasamu.. Amma kema Kinsan bazan tab’a cin amanarki ba Giwata..!” Giwa ta katsesa da fad’in “Rufe mun baki munafukin banza munafukin wofi, bayan d’an da kake k’ok’arin ganin k’arahen nasa ma D’anka ne..! Yazeed d’anka ne ba d’an AbdulJabbar ba.. Idan ka kasheshi ka kashe d’anka da hannunka ne..!!” Muryar Yazeed suka sinkayo yana fad’in “Maami...!! Mai nakeji.... Mai nake jin kina cewa..?! Wannan mutumin... Shine mahaifina..!!!?” Ya k’arashe hannunsa na tsananin rawa yana nuna Waziri... Giwa da batasan da shigowar Yazeed ba dafeda k’irji take dubansa yanda yake wani irin tururi da huci jikinsa sai karkarwa yake yana nuna Waziri... Shi kansa Waziri da yaji batun a bazata idanu waje yake duban Giwa yana duban Yazeed.... Yazeed da jijiyoyinsa suka firfito waje tsalle yayi ya shak’o wuyan Giwa yana fad’in “Answer me..!! Tell me the truth... Waye mahaifina... Kuma karkice min wannan k’ask’antaccen mutumin shine mahaifina... Dan nayi imani sai na hak’a rami na banka maku wuta dukanku biyu kun mutu..!! Ki amsa min Maami... Kice min Abbah na mai Martaba shine mahaifina ba wanann wulak’antaccen mutumin ba..! Ki amsa min Turai..!!!” *MUHIBBAH* *62* *©️Sameena Aleeyou...✍🏽* Giwa taji damk’a irin wanda bata tab’aji ba sai muzurai take idanunta na kuma firfitowa waje, Ji take kaman ranta zai fice daga cikin jikinta sabida tsaban azaba don wane irin damk’a Yazeed yai mata irinta wanda ransa Ke tsananin k’una... Ganin Yazeed dai kashe Giwa yake k’ok’arin yi yasa Waziri Saurin k’arasawa yana k’ok’arin ceton Giwa daga hannun Yazeed... Wawan naushin da ya kaiwa Waziri saida ya zaunar dashi har k’asa Waziri ya rik’e cikinsa yana murk’usoson azaba a wajen abinka da wanda shekaru ya ja tsufa ya sauk’o masa, zai wahala idan naushin da Yazeed yai masa bai targard’a masa wani k’ashi ba.... Yazeed bai saki Giwa ba yana hawaye yake dubanta yanda take k’ifk’if da ido tana neman tsira daga azaban da take ciki... Hawaye na zubo masa yayi wurgi da Giwa Ta koma gefe, bai daina huci ba yake nunata da yatsa yana fad’in “Kin cuceni kin zalunceni, Allah da kikayi sanadin zuwana duniya, da na zamto d’an wannan mutumin gwara ba’a haifeni ba..!! Ki tashi ki sanar dani komai da bakinki..! Ki tashi nace..!!” Ya k’arashe yana kuma finciko Giwa da har lokacin bata daina haki tana sosa wuyanta yanda Yazeed ya shak’eta ba... Shar shar da hawaye Yazeed Ke kuka yana kuma jijjiga Giwa yake fad’in “Talk to me..! Tell me everything..! Ki fad’a min ya akai wannan k’ask’antaccen mutumin ya zamto mahaifina..!!!” Ya k’arashe hawayen k’unan rai na tsartowa daga idanunsa da ya koma jazir... Giwa na hawaye take furta “Yazeed ka yafe min, wllhi bada son raina bane... Duk abinda nayi dominku nayi kaida ‘yanuwanka... Yazeed ka yarda dani, wllhi sabida ku nayi komai...!” Cikin daka tsawa hawaye basu daina zuba masa ba ya kuma fad’in “Ki gaya min ta ina kika taimakeni bayan kin sameni Ta haramtacciyar hanya... Hanyar da ko sarautar da nake da buri tsawon rayuwata banida gadonta... How could you do this to me Giwa..! How could you..?!!” Ya k’arashe yana mai kuma jijjigata hawaye naci gaba da zuba masa.... Cikin kuka Yazeed yaci gaba da fad’in “Now I get it... Shiyasa kika fifita Mahmood sama dani sabida Mahmood shine d’an AbdulJabbar ni kuma d’an wannan k’ask’antaccen mutumin... That’s why kika dage sai Mahmood ne zai sarauta... Yanzu na fahimci komai..!” Katsesa Giwa tai da fad’in “No Yazeed ka saurareni ba haka bane..!” Cikin huci ya katseta “Then how..! Yaya ne...? Bakida wani dalili da ya wuce wannan..!” Giwa ta katsesa da fad’in “Mahmood shine babban mak’iyina a duniyar nan... Mahmood shine ya hanani rawar gaban hantsi... Mahmood shine ya zame min ciwon ido... Banida buri da ya wuce na kawar dashi a doron k’asa..!!!” Ta k’arashe tana sakin huci tamkar wata zakanya... Izuwa lokacin da tsananin mamaki Yazeed ke dubanta cikin tsananin sanyin jiki.. Ya shiga girgiza kai alamun ya kasa aminta da abinda yakeji Wai mahaifiya zata tsani d’anta haka..! “Maami shin Mahmood ba shine d’ah mafi soyuwa a gareki ba..?!” Muryar Waziri ya sinkayo yana fad’in “Yazeed Mahmood ba d’an mahaifiyarka bane..!” Cikin tsananin shock Yazeed ke k’ok’arin juyowa yana duban Waziri da yayi maganar.... Waziri ya jinjina masa kai alamun tabbatarwa kana yaci gaba da fad’in “Mahmood d’an Baiwa ce, Baiwar da sukaci amanar mahaifiyarka itada AbdulJabbar bayan mahaifiyarka Ta basa kyautanta a matsayin tukwici...!!” Girgiza kai Yazeed keyi kana ya kuma karkatowa yana duban Giwa cikin rashin fahimtar abindake wakana... “Mai...Mai yake cewa Maami...? Ki min bayani.. Shin abinda mutumin nan yake fad’i gaskiya ne..? Ba kece kika haifi Mahmood ba...?!” Giwa ta jinjina masa kai hawaye na zubo mata “K’warai Yazeed kaman yanda kaji Waziri yace Mahmood shine product na cin amanata da Baiwata Izzatu da kuma mijina AbdulJabbar sukayi... Shiyasa naci alk’awarin maidashi nawa dan na d’au fansata akansa... Duk yanda Kaga na k’agu ya d’ale karaga ba sabida komai bane sai don malami na ya sanar dani wanda duk ya fara sarauta cikinku bazai k’argo ba zai mutu.. Kaga idan Mahmood ya d’ale yayi guntun zamaninsa sai kai ka d’ale ka jima kana mulkin ka wannan shine tanadin da nayi maka... Wannan shine dalilin da yasa kaga na dage Mahmood ya soma d’ale karaga dan ya tafi ya bamu waje mu kafa mulkinmu da zuri’armu..!!” Yazeed ya zauna dirshan a k’asa yana nanata kalaman mahaifiyar tasa cikin kwanyarsa... Ganin yayi shiru yana nazari yasa Giwa kamo hannayensa tana fad’in “Yazeed ina matuk’ar k’aunarka duk wannan fad’i tashi da nuna ina son Mahmood a fili dukda kasheni da hakan yake can k’asar zuciyata wa kai nake da ‘yanuwanka mu samu mu kawar da Bare d’an Baiwa cikinmu..!” Jajayen idanunsa ya d’ago yana dubanta kana yace “Koda ace shi d’an Baiwa ce but at least he carries my father’s blood, yana d’aukeda jinin AbdulJabbar na Yawo a b’argonsa... But what about me... Bana d’aukeda jininsa sai na wannan k’ask’antaccen mutumin kwarto mai bin matan mutane... Now I get it... Ashe ga yanda nayi gado..!!” Ya k’arashe yana sakin muguwar murmushinsa yana aikawa Waziri jahilar kallo... Lokaci guda ya maidoda dubansaga Giwa ya tsime sosai yana mai ci gaba da fad’in “Su kuma ‘yan uwana waye mahaifinsu tinda naga alama k’aryace zalla cikin rayuwar ahalinki... Baki haifi Mahmood ba kikac kin haifa.. AbdulJabbar bai haifeni ba kikace ya haifa.. Toh su kuma Jamal da Yazeed fah...? Naki ne ko suma satansu kikayi... Ko kuwa dai suma wannan mutumin shine mahaifin nasu.. Kodai ma akwai wani wanda bamu sani ba..?! Talk kimin magana Giwa..! Ki bud’e baki ki amsa min tambayoyi na..!!” Ya k’arashe yana mai firfito da idanunsa waje tamkar zai kuma shak’ota.... Kaman daga sama suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “Fad’a mana Turai... Jamal da Fu’ad suma ‘ya’yana ne...?!” Giwa Ta d’ago tana dubansu, ta kalli wannan ta kalli wancan, ta had’iyi miyau da k’yar sai kuma ta soma fad’in “Banida tabbas akan Jamal, Don a lokacin na shiga rud’ani... Amma Fu’ad d’an AbdulJabbar ne... Shi kad’ai ne jininsa cikin yarana guda uku...!!” Yazeed na sakin huci yake aika mata wulak’antaccen kallo, lokaci guda yake jinjina kai yana fad’in “No wonder mahaifinmu yafi son Mahmood da Fu’ad ashe yanaji a jikinsa sune jininsa na asali, no wonder sukafi kamanceceniya Ta fuskar halitta ashe sud’in sune ‘yan uwan juna...!” Ya mik’e sosai yana ci gaba da fitar da huci yake fad’in “Now that I learned banida wata alak’a ta jini da d’an Baiwa Mahmood I won’t have mercy on him... I’ll not spare him...! Now more than ever I’ve every right to the throne sabida D’an Baiwa bai gaji sarauta ba...!” Giwa tai saurin katsesa da fad’in “Karka d’auki mataki yanzu Don idan Mahmood ya san cewa banice na haifesa ba shirinmu zai lalace akansa...!!” Cikin k’unan rai Yazeed yace “To hell with your plans Giwa..!! Do you think I care...?! My life is ruined...! Kin lalata rayuwana da kika bari wanann mutumin ya zamto mahaifina..! Kin cuceni da baki bari na fito a tsatson Abbah ba... I don’t give a damn idan Mahmood yasan cewa shi d’an Baiwa ce..!!” Giwa na girgiza kai take fad’in “Idan ka sanar dashi yanzu shikenan bazai d’ale karaga ya mutu ba.. Kaga idan ka d’ale kaine zaka mutu ni kuma bazan juri rasaka ba d’ah na..!!” Ta k’arashe tana rau rau da idanu.. Shiru yayi yana dubanta tamkar mai nazari har lokacin bai daina sakin huci ba... Suka sinkayo muryar Waziri na fad’in “K’warai d’ah na sarauta takace amma ka bari har mu kawar maka da Mahmood..!” A fusace Yazeed ya katsesa da fad’in “Don’t you dare call me your son ever again..! I’m not your Son.. I’m my Father’s Son..! I’m Yazeed AbdulJabbar Mahmood...! You’re not my father and you’ll never be..Get that through your this empty skull of yours..!” Ya k’arashe yana mai bubbuga rawanin Waziri Giwa Ta had’iyi miyau da k’yar sai kuma tace “Yazeed ka basa girma ko d’an kad’an ne tunda yanzu kasan komai...!” Shu’umar murmushinsa yayi yana watsa masu wulak’antaccen kallo dukansu biyu sai kuma yace “Ai kun zubar da girmanku tun lokacin da kuka zab’i ku haifoni Ta wannan hanya... Thai man is not my father, zan fad’a kuma zan nanata... I might carry his blood but har abada bazai tab’a zama mahaifina ba... My Father is dead.. Mai Martaba AbdulJabbar shine mahaifina, and Ni ya fi dacewa na gajesa ba Mahmood d’an Baiwa ba k’ask’antacciya ba...! I’d never allow d’an Baiwa jinin Bauta ya mulki Masarautar nan ba..!!” Ya k’arashe yana mai watsa masu muguwar kallo lokaci guda yasa kai ya fice daga d’akin kaman zai tashi sama zuciyarsa naci gaba da suya... ** K’AUYEN GALAMBI Ubandoma yai jigum yana duban Baba Nomau yanda yake had’a wani ruwan magani cikin sabon goran da suka ciro daga daji suka fafeta.... Ubandoma ya d’an gyara zama yace “Yanzu Baba Wai kana nufin dama ba yanke harshenta matar nan akayi ba..?!” Baba Nomau ya murmusa yace “Ubandoma kenan, matsafa babu abinda bazasu iya yi ba kai dai muyi addu’an Allah ya shiga tsakaninmu da mugu.... Ba yanke harshenta sukayi ba saidai sun d’aure harshen nata ne da muggan bak’ak’en zare da allurai na tsafi... Kaga wannan ruwan magani ne da Allah ya sammana wani d’an b’angare na ilimin saninsa, mukan tsinko ganyen cikin daji shine zatake kuskure bakinta dashi har na tsawon kwanaki uku... sai kuma ruwan addu’o’i da ayoyin Alk’ur’ani mai girma wanda babu shirka ciki da zata Ke sha na tsawon wannan kwanaki ukun..... Cikin ikon Allah da buwayarsa muna fata wannan sihiri ya karye harshen nata ya warware ya dawo dai dai cikin bakinta..!” Ubandoma ya jinjina kai yace “Masha Allah..! Allah Ubangiji yasa a dace ya kuma bamu nasara..!” Dattijo Baba Nomau ya amsada Ameen..! Suna a haka suka sinkayo muryar mai d’akinsa tana fad’in su taho Jafaru ya farka..! A tare Baba Nomau da Ubandoma suka mik’e Ubandoma na taimakawa Baba Nomau sabida girma sosai da ya sauk’o masa.... A haka suka isa wajen Jafar wanda idanunsa Ke bud’e tarau yana duban sama... Ubandoma ya zuru yana duban ikon Ubangiji Wai yau Jafar ne ya bud’e idanunsa wanda tun zuwansu wannan gari kusan sati biyu kenan yana kwance a haka ko motsawa baiyi yau sai gashi ya bud’e idanunsa.... Allahu Akbar ashe dai Allah zai tashi Jafaru...! Baba Nomau yaceda maid’akinsa Ta kawo masa ruwan maganin Jafar da ake yayyafa masa... Babu musu ta mik’e ta kawo, Baba Nomau yai bismillah ya soma yayyafawa Jafar ruwan maganin daga kansa zuwa k’afafunsa.... Wane irin mik’a Jafar yayi numfashinsa na fita a hankali a hankali.... Baba Nomau ya bud’e murya yace “Sannu yaro sannu kaji... Allah ya k’ara maka lafiya..!” Ubandoma da mai matar Baba Nomau mai suna Tabawa suka amsada Ameen a tare... Bana Nomau yace “Tabawa kawo masa ruwan addu’an da nace Ki aje shi zai soma sha idan ya farfad’o..!” Tabawa ta amsa da toh Malam kana ta mik’e ta nufi can wata Rumfar zana ta d’auko ruwan addu’an rufe cikin kwano... Ta kawowa Baba Nomau Baba Nomau ya dubi Ubandoma yace ya d’ago masa Jafar kad’an... Ubandoma yayi kaman yanda Baba Nomau yace... Baba Nomau yace “Yi bismillah kasha ruwan nan yaro..!” Lumshe idanunsa Jafar yai da alama yayi bismillah kaman yanda Dattijon ya fad’i masa amma saidai maganan nasa bai fitowa sosai... Ya kafa kansa ya shanye ruwan tas... Sauran Baba Nomau ya shafe masa fuskarsa dasu... “Sannu yaro... Ya sunanka..?!” Ya tambaya yana dubansa da alama so yake ya gane ko Jafar d’in ya dawo hayyacinsa... “Sunana Ja’afar...!” Sukaji Jafar d’in ya baiwa Baba Nomau amsa da fad’in haka... Ubandoma dake gefe bakinsa ya gaza rufuwa sabida tsananin farin ciki baisan sanda ya rungumi Jafar yana fad’in “Alhamdulillah..! Alhamdulillah Jafaru..! Jafaru Allah yayi ikonsa akanka...!!” Jafar ya d’ago idanu yana duban Ubandoma lokaci guda ya furta “Ubandoma..!!” Ubandoma ya kuma Washe baki cikeda Farin ciki yace “Jafaru ka ganeni...! Jafaru ya gane ni..!” Ya kuma fad’i yana duban Baba Nomau da tuni ya umarci matarsa ta kawowa Jafar damin fura mai kauri yasha... Jafar ya d’aga kai yana duban duniyar da yake da kuma mutanen dake wajen, lokaci guda ya maidoda dubansanga Ubandoma yace “Ina ne nan... A ina nake...? Su waye wad’annan mutanen..?!” Ubandoma yace “Ka kwantarda hankalinka Jafaru kana hannu mai kyau... Labari ne mai tsawo.. Amma kana Iya tuna mai ya sameka..?!” Take Jafar ya shiga jinjina kai idanunsa na kuma kad’awa... Lokaci guda yake furta “Na tuna..! Na tuna komai..!! Take ya soma basu labari da fad’in _Falsh back_ “Wata rana ina gyaran harawan da zan baiwa dawakin mai Martaba, ya aika a kirawoni... Kasan akwai shak’uwa da kusanci sosai tsakanina da Mai Martaba wanda sam babu shamak’i a tsakaninmu, na jima da sanin cewa matarsa Giwa bata son wannan alak’a dake tsananina da Mai Martaba Sarki...!Koda aka kirawoni ban samesa a Fadarsa ba, hakan yasa na zauna a mazaunin da na saba zama Ina jiran fitowarsa... Jim kad’an Mai Martaba ya fito da kaya irinta masu mulki a hannunsa... Bansan dalili ba amma naga daga fitowarsa ya k’araso ya rungumeni... Ya sumbaci goshina kuma naga hawaye kwance cikin idanunsa... Jikina yayi sanyi matuk’a da ganin wannan yanayi daga MaiMartaba Sarki... Yanayi ne da ban saba ganin Sarki ciki ba... Lokaci guda naga ya kamo hannayena yana duban yanda suka koma sabida ciro ciyawan abincin dawakai da aikin wahala... Take ya tambayane cikin rawar murya “Ja’afar Ina ka samu wad’annan raunin..?!” Cikin sanyin jiki nace dashi “Allah shi baka yawan rai wannan ai ba komai bane...!” Take naga Mai Martaba yasa bayan hannunsa ya share hawayen da suka zubo masa... Ban kawo komai ba dan duk a zatona cikin irin shak’uwa da Sabo ne da mukayi da juna... Jiki na ya soma matuk’ar yin sanyi, na d’an risina nace “Rankaidad’e zaka fita kilisa ne kana so a shirya maka Doki..?!” Sai gani nayi ya saki murmushi mai bayyana hak’wara, lokaci guda ya shiga bubbuga kafad’ata guda kana ya damk’a min tufafin dake hannunsa yace “Ka shiga wancan d’akin ka saka wad’annan suturan..!” Na dubi tufafin da ya bani masu daraja na kuma dubesa... Lokaci guda na kuma risinawa nace “Allah shi baka yawan rai Bawa kaman ni ban kamaci saka wad’annan kayan ba...!” Gani nayi ya saka hannu ya rufe mun baki yace “Kada ka sake ambata kanka da Bawa... Akwai maganan da nakeso muyi amma sai ka saka wad’annan suturan....!” Na jinjina masa kai a hankali dan bazan iya musu da Mai Martaba... Nayi kaman yanda yace na nufi d’akin da ya nuna min... Koda na shige d’akin tsayuwa nayi Ina kallon kayan alatu da aka k’awata wannan d’aki dashi... Nan dai na makare wajen kallon kayyayakin da idaniyata basu tab’a gani ba abinka da wanda ya taso cikin Bauta....! Bayan kaman shud’ewar wasu muryoyi sai na soma jiyo sautin Mai Martaba da Mai D’akinsa yana mata magana cikin tsananin fad’a da fushi amma bana iya fahimtar abubuwan da yake fad’i nayi saurin matsowa jikin k’ofa Ina lek’en abindake faruwa... Gani nayi Giwa ta duk’a saman gwiwoyinta ta d’aga hannayenta guda biyu sama tana rok’on Mai Martaba tana kamo k’afafunsa yana bugeta... Bai tsaya saurarenta ba ya shige wata k’ofa... Nan naga Waziri ya fito daga wata k’ofar yana dariya... Itama Giwar Dariya tayi Ta mik’e tana fad’in “Yana isa d’akin Zeenatu kafin yayi wani katab’us ya mutu dan ya riga ya shak’i iskar guban dana busa masa hannuna bazan tab’a bari ya tona min asiri ba...!” Waziri yace “Toh wani hanzari ba gudu ba, inada tabbacin ya sanar da Jafaru komai... Duk yanda Jafaru ya shiga ya fita cikin Masarautar nan mu kamasa mu gama dashi mu b’atar dashi kaman yanda muka b’atar da saura...!” Giwa tace “Aiko ya zama dole mu kashe Jafaru...!” Ni kuma jin haka yasa nayi tunanin ya zama dole nasan yanda zanyi na tsira da rayuwata daga cikin wannan masarauta da ake farautar rayuwata...! Sosai na hango tashin hankali kwance saman fuskar Giwa tana fad’in “Waziri na tabbata idan har Mai Martaba ya gana da Jafar Toh ya sanar dashi komai... Ya zama dole mu kashe Jafar... Idan har kana son alak’armu ta d’ore toh a kawar da Jafar a kashesa har lahira abinda ya kamata muyi tuntuni bamuyi ba...!” Daga nan ban kuma tsayawa saurarensu ba na nemi hanyar tsira... Na k’ulle ‘yan kayyakina da niyan barin gari koda kuwa zan sami k’alubale... Cikin daren na nemi Umaima dan nayi mata sallama a yanda muka saba had’uwa saidai wannan had’uwar cikin dare mukayi dan bazan bari gari ya waye min cikin Masarautar ba... Dan nayi imani kafin wayewar gari mugayen mutanen nan zasu iya zartar mugun nufinsu akaina...! Ban samu damar mata bayani ba saidai nace tai k’ok’ari Ta cireni cikin zuciyarta Ta mance dani... Taci kuka sosai kaman bazata k’yaleni na tafi ba... Haka dai na bata hak’uri nace Ta mance dani zanyi nesa da Masarautar nan...! A haka mukayi sallama da Umaima na tafi na barta tana kuka... Saidai Ina k’ok’arin guduwa daga cikin Masarautar naji an rad’eni da sanda an buga min sanda akai na fad’i sumamme... Ban kuma farkawa ba sai a cikin wani d’aki mai duhuwan gaske yanda naga D’an Sarki Yarima Jamal ashe shine ya dakeni da sanda ya kawo ya d’aure da sark’ok’i yana azabtar dani saidai kullum dare sai ya kawo min abinci a tsawon shekara guda da nayi

Chapter 41 of 65