Yazeed ya kumayi kana yace “Ta yuwu a idanunka kaga kaman ka fini k’arfin jiki... Amma saidai ni inada k’arfin tunani wanda zan iya yak’an tawaga guda da wannan tunanin nawa...!!”
“Ban gane mai kake nufi ba...!” Majidad’i yace yana duban Yazeed d’in...
Kafad’arsa kad’an Yazeed ya buga kana ya kuma matso da fuskarsa dab kunnen Majidad’i “Waye kake tunanin ya umarci Ubandoma da ya shiga Gidan Wambai...?!”
Majidad’i ya dubesa shaye da mamaki yana nazarin maganar.. Lokaci guda yake girgiza kai yana mai furta “Ta yuwu shi yakai kansa babu wanda ya turasa tunda wannan gida namu kowa ba abin yarda bane... kuma babu irin bugun da banyi masa ba dan ya fad’i Waye ya turo shi amma ya sanar dani babu wanda ya turo shi..!”
Yazeed ya kuma sakin wata murmushi yace “And you believe him...?” Yai tambayar yana mai tsare Majidad’i da idanu.... Lokaci guda ya kuma sakin murmushi ganin ya jefa Majidad’i cikin shakku da kokonto, Yazeed yaci gaba da fad’in “Ubandoma Hadimin waye... Waye Ubangidansa...?!”
Majidad’i na tsananin sakin huci ya d’ago yana duban Yazeed... Lokaci guda cikin karaji yake furta “Yarima....Mahmood..!!!”
SameenaAleeyou 📚
[7/16, 5:34 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*034*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Yazeed ya kuma sakin murmushi yana mai jinjina kai “Tabbas Mahmood is behind all this, shine silan ciwon mahaifinka... Zai iya yin komai dan yaga ya mallaki sarautar nan Ta ko wacce hanya ce, gashi ya soma da mahaifinka... Wannan dama ce ta samemu muyi amfani da ita wajen kaisa k’asa...!” Ya k’arashe yana sakin huci a hankali...
Majidad’i ya d’anyi shiru tamkar mai nazari sai kuma ya nusa yace “Toh amma kan wane dalili Mahmood zai cutar da mahaifina... Da ni da kai munsan cewa tun daga fari mahaifina is being very supportive to Mahmood, Toh kan mai zai nemi rayuwar mahaifina bayan shid’in ya zabi ya goyi bayansa yayi sarauta sama dani da nake d’ansa....?!”
Yazeed ya daidaita tsayuwarsa hannayensa hard’e ta gaba ya d’an turo k’irjinsa gaba kad’an irin tsayuwar da masu mulki keyi... “Da alama har yanzu baka fahimci yanda al’amara Ke gudana cikin gidan nan ba... So tari a gida irin namu mafi kusanci dakai shine mak’iyinka, wanda ka aminta dashi can easily betray you... Correct me if I’m wrong..!”
Jinjina kai Majidad’i yai yana mai kuma karantar Yazeed lokaci guda yace “Kana tunanin Mahmood could be behind my father’s illness..?!”
Yazeed ya saki murmushin cin nasara yana mai ware hannayensa “Isn’t it obvious..? Ai a bayyane yake Mahmood shine sila, da umarninsa Ubandoma ya shiga gidan Wambai... And believe me idan bakai komai akai ba sai Sun kashe Wambai har lahira...!”
Majidad’i yace “Toh yanzu miye abunyi Ta yaya zamu kama Mahmood da laifin idan har ba Ubandoma bane ya fad’i cewa da umarninsa ya kutsa gidan Wambai kuma shine bak’on Buzu...?!”
Yazeed ya murmusa a hankali kana yace “We make him talk... We gonna make sure he rats Mahmood out... Dole mu tabbata ya fad’i cewa Mahmood shine yai masa umarni da ya shiga gidan Wambai... After all, haka zancen yake tunda Ubandoma Hadiminsa ne...!” Ya k’arashe babu alamun jin k’ai ko imani cikin k’wayan idanunsa...
Jinjina kai kurum Majidad’i yake cikeda tsanani tsanar Mahmood “Zan d’auki fansar ciwon mahaifina zan tabbata Mahmood bai zama sarki ba sannan sai ya tafi gidan Yari har tsawon lokacinda mahaifina zai kwashe a kwance....!”
Yazeed ya saki murmushi yana mai furta “Impressive..!! Yanzu abinda ya kamata muje muga Ubandoma musan ta yanda zamu b’ullo masa..!”
Babu musu Majidad’i ya jinjina kai kana yabi bayan Yazeed suka shige cikin Fursuna...
**
Dogari guda ne ya k’araso cikeda risinawa ya bud’ewa Mahmood gark’amemen k’ofar fursunan da aka rufe Ubandoma ciki wanda sai ka shige manyan k’ofofin k’arfe har kusan guda uku kafin ka cimma d’akinda Ubandoma Ke ciki.....
Ubandoma na hango Yarima Mahmood ya shiga sanne kansa ya zube gwiwoyinsa ya had’e hannayensa waje guda yana fad’in “Rankaidad’e dan Allah ka ceceni kamin rai ka fitar dani daga wajen nan... Wllhi banida laifi sahun b’arawo na ta...!” Hango tsagwaron b’acin rai saman fuskar Mahmood wanda bai tab’a ganin irinsa ba tattaredashi tsawon zamansu tare ya sanyashi saurin had’iye zancensa gumi naci gaba da tsartsafo masa...
Yazeed da Majidad’i da k’arasowarsu wajen kenan tin daga k’ofa Yazeed ya umarci dakarun dake tsare da fursunan da su bud’e masu suga Ubandoma...
Dogarin ya risina yace “Allah shi taimakeka Mai Girma Yarima Mahmood yana ciki bazamu iya barinku ku shiga ba...!”
Wani jahilin duba Yazeed ya watsa masu “Kun kuwa San ko ni wanene...? Kun kuwa San da waye kuke magana..?!”
Dogaran suka kuma risinawa d’ayan na fad’in “Umarnin Yarima Mahmood ne kuma zab’ebb’en sarki na gaba Allah shi taimakeka... Wannan ba umarninmu bane...!”
Yazeed da Majidad’i suka dubi juna... Yazeed dake tsananin huci yana k’ok’arin damk’o wuyan Dogarin Majidad’i yai saurin taresa kana ya d’aga bakin rigarsa kad’an zarkwad’ed’iyar wuk’a mai tsananin shek’i sabida kaifi Ta bayyan...
Dodagarin ya had’iyi miyau da k’yar dan tsoro yana mai k’ifta idanu... Lokaci guda ya matsada baya yana mai basu hanya...
Yazeed ya dubi Majidad’i yace “Zaifi kyau idan ka jirani a nan... Shiganmu a haka mu biyu zaisa Mahmood ya zargi wani abu....!”
Majidad’i ya jinjina kai kana ya koma da baya ya bar Yazeed ya soma shigewa...
**
Mahmood ya girgiza kai yana duban Ubandoma lokaci guda ya d’an gyara tsayuwarsa yana mai fad’in “Kai nake saurare, ka sanar dani gaskiyar Al’amari idan har kanaso na taimakeka..!!”
Ubandoma ya kuma goge gumin dake ci gaba da karyo masa, Ta ya zai soma sanar da Mahmood ga abinda ya kaisa gidan Wambai, Ta yaya zai soma sanar dashi zancen Giwa da Waziri yaji har ya jefasa a ukun da ya tsinci kansa... Sanar da Mahmood gaskiya na nufin tono komai na Masarautar kenan... Idan har ya sanar dashi ga shirin Giwa da Waziri komai ya riga ya lalace kuma yayi imani hakan na iyayin sanadiyan rayuwarsa tinda yasan wacece Giwa ballantana Waziri...
“Kai nake saurare Ubandoma..!!! Wai ma tsaya tukuna, who are you..? Wanene Kai..? Ka sanar dani idan akwai wanda kake munafunta dashi cikin Masarautar nan..!!” Ya k’arashe cikin tsananin zafin rai...
Ubandoma ya shiga girgiza kai yana furta “Allah shi taimakeka BillahilAzim bani ha’intarka da kowa... Ka yarda dani Rankaidad’e, ka min rai ka cireni daga wajen nan..!” Ya k’arashe cikin tsananin rawar murya yana mai k’ank’an da kai...
Girgiza kai kurum Mahmood yai kana yace “Had’in kanka shi kad’ai zai bani damar taimakonka Ubandoma... Amma a halin yanzu ni kaina ban yarda dakai ba, inada kokonto da tarin shakku akanka... Zan baka nan da kwanaki Uku Ubandoma, ka gama dik tinanin da zakai... Idan ka zab’i ka fad’i gaskiya watak’ila ka tsira da mutuncinka amma idan ka zab’i akasin haka... Kafi kowa sanin zaka dawwama cikin k’ask’anci a gidan Yari har lokacinda Allah zai baiwa Wambai lafiya ya bud’e bakinsa ya fad’i komai...!”
Daga haka juyawa yai da niyya ficewa Yazeed dake mak’ale daga gefen gini ya gama sauraren duk abinda suka fad’i, shiru yai yana nazari... Kenan Ta tabbata ba Mahmood bane ya tura Ubandoma..? Kenan akwai wani wanda Ubandoma yafi aminta dashi a Masarautar sama da Mahmood... Idan ya fahimci wani abu tabbas akwai wanda yake son ganin bayan Mahmood cikin Masarautar fiyedashi... Toh wanene wannan wanda Ubandoma kema aiki... Waye mak’iyin Mahmood har haka..? Lallai ya zama dole yasan ko wanene wannan...?! Ya k’arashe tinanin yana mai juyawa da baya shiga wajen Ubandoma da baiyi ba kenan... Dole yai shiri ya kuma San takunsa da alama Kuraye sunyi yawa a Masarautar tasu... Mahaifiyarsu tana cen tana fatan Mahmood ya d’ale Karaga ashe akwai wani wanda Ke cin dunduniyarsu basu sani ba.. Yayi imani Giwa batasan Ubandoma na munafuntar d’anta da tafi so da sarauta ba...!
Shafa hab’arsa yake a hankali yana nazarin waye ke son ganin bayan Mahmood sama dashi irin haka a cikin Masarautar..!?
**
Mahmood yana fitowa yaceda Dakaru masu tsaron Fursunan kar su bari wani ya gana da Ubandoma har nan da tsawon kwanaki uku, dan yasan idan aka bari kowa yana shiga munafukin da Ubandoma ke masa aiki zai iya tsoratasa har ya canza niyyansa na fad’in gaskiya tinda ya kula kaman Ubandoman ya soma karaya da alama zai fad’I gaskiya bayan kwanakin da ya d’ibar masa cewa yai shawari da zuciyarsa....
**
Wayar mak’ale kunnenta na b’angaren hagu ta kuma sauk’e huci a karo na biyu, saida ta canza wajen zama kana taci gaba da fad’in “Ansar I’m quite certain matar nan sunana Ta kira... She knows me Ansar... Duk yanda akai ta sanni... Tambayar a nan shine wacece ita..?!”
Daga d’aya b’angaren Ansar ya fuzar da fuci a hankali kana yaci gaba da fad’in “Hiba kiyi tinani maybe kin tab’a saninta a shekarun baya, watak’ila tun tana cikin hankalinta kafin lalurar hauka ya sameta... Kiyi tinanin mutanen da kikai rayuwa dasu a shekarun baya...!”
Shiru tai tamkar mai nazari sai kuma tace “Ansar bazan iya tunawa ba, bazan iya tuna sanin wata mace mai yanayinta ba... The only thing da na sani shine inajin wani babban al’amari gameda matar sannan inaso na taimaketa bayan haka inason sanin asalin labarinta da kuma yanda akai Ta k’are rufe a cikin wannan masarauta..!” Ta k’arashe maganar cikin rawar murya..
Shiru na d’an dak’ik’ai suka gifta kana Ansar yace “I have faith in you Hibbah... Nasan duk wad’annan abubuwan da kika saka gabanki da izinin Allah zaki Kai k’arshensu... Addu’ata da soyayyata na taredake ko yaushe kinji koh, dan haka Koda wasa kada Ki karaya...
Jinjina masa kai tai a hankali tamkar yana ganinta kana sukai sallama cikeda kewar juna... Takardan zanen da mahaukaciyar ta damk’a mata Ta d’auko Ta ware tana kuma k’are masa kallo.. Ya kamata taje sashen Giwa ta had’e zanen waje guda don ta tabbatar ko iri guda ne...
Mik’ewa tai ta soma shirin nufa sashen Giwa...
**
Cikeda ladabi Jamal ya k’araso gaban Giwa yana sauraren kiran gaggawa da tai masa...
“Ina zanen yake..?!” Ta tambaya cikeda kulawa...
“Maami wane zane kenan...?!”
Fuzar da fuci tai a hankali kana tace “Jamal sanin kanka ne Masarautar nan babu lafiya akwai wanda Ke mana zagon k’asa.. Na tabbata yana nan yana neman zanen nan... A ina ka ijiye...?!”
D’an jim yai kana yace “Maami na kyautar...!”
“Ka me...?!” Giwa Ta tambaya tana dubansa
“Na kyautar Maami...!”
Take gumi ya shiga tsartsafowa Giwa... Wannan zane guda UKU ne rak a duniya, kuma ko wanne nada alak’a da juna... D’aya bazai tab’a warwaruwa ba saida d’aya, duk randa zanen nan guda uku suka shiga hannun mutumin da yake masu zagon k’asa a Masarautar tabbas mabud’an sirrikanta sun yaye...
Guda d’aya yana wajen d’anta Jamal, d’aya yana wajen Wambai guda d’aya ne batasan yanda yake ba saidai tafi k’arfafa zaton yana wajen Jafar ne....Tabbas idan aka had’e wad’annan zane guda uku waje guda zai baka jimillan wasu hanyoyi da k’ofofi masu rikitarwa da wahalan fasaltuwa.... Tayi imani Bak’on Buzu wannan zanen yake nema wajen Wambai....
Ta juyo cikin tsananin fusata tana duban Jamal... “Ashe kai bakada hankali ban sani ba... Jamal ta yaya zan sanar dakai mahimmancin abin nan ka kama ka kyautar...Anya cikin hayyacinka kake...?! Jamal cewa nayi ka k’ona k’urumus tun a wancan lokacin bawai ka kyautar ba..!!!” Ta k’arashe tana mai k’ok’arin cakumo wuyansa....
Tsoro da mamakin mahaifiyarsa ya somaji ganin yanda ta fice a hayyacinta lokaci guda... Fincikar rigarsa yai yana mai ci gaba da sakin fuci, lokaci guda yake furta “Maami laifina kike gani..? Maami idan ban mance ba kece da kanki kika dank’a min zanen nan kikace Abbah ne ya bani, lokacin ina yaro sosai mukayai wani tafiya kikace a wancan Masarautar aka bashi kyauta shi kuma ya bani... Da bakinki kikace nayi nesa da hoton daga cikin Masarautar nan... Kuma nayi kaman yanda kikace...!”
Ya k’arashe yana sakin huci....
K’ok’arin saita kanta Ta d’anyi had’ida dafasa “Gwarzona ka tabbata zanen baya cikin Masarautar nan...?!”
Saida ya had’iyi miyau don tunda yake bai tab’a k’aryawa mahaifiyarsa ba sai yau sannan bai tab’a questioning duk wani umarni da zata basa ba....Lokaci guda ya shiga jinjina kai yana fad’in “I promised Maami... Wanann zanen yayi nisa da Masarautar nan..!” Ya k’arashe yana dubanta...
Murmusawa tai kad’an tana mai shafa fuskarsa take fad’in “Kasan na aminta dakai sama da sauran yarana, nasan bazaka tab’a bani kunya ba..!”
A hankali ya jinjina kansa yana mai k’ok’arin d’aura murmushi saman fuskarsa “Har abada bazan tab’a baki kunya ba Maami... Alk’awari ne..!” Yana ida fad’in haka yasa kai ya fice...
Bai zarce ko ina ba sai parlornsu Umaima... Yai tsaye yana duban hoton... Tabbas mahaifiyarsa bata shigowa b’angarensu Umaima sabida mulki irin nata amma kam tabbas da tayi tozali da zanen nan... Yau ce rana ta farko da ya tab’a mata k’arya tsawon rayuwarsa, akan macen da yake so ya zab’i yayiwa Giwa K’arya for the first time... Bazai iya k’wace abinda ya baiwa Umaima da hannunsa ba... ya shirya daukan risk d’in ko menene nufin Giwa na cewa a fitar da zanen cikin Masarautar tun wancan lokacin....
Taku kad’an yai ya k’arasa jikin hoton ya k’ura idanunsa... Lokaci guda yasa hannu ya ciro hoton ya shiga juyashi yana k’are masa kallo....
Umaima ce ta fito daga d’aki cikin shirin sauk’a k’asa sai kuma tai karo da Jamal tsaye nan wajen rungume da Taswiran yana sakar mata murmushi...
Harga Allah batasan dalili ba amma sosai taji tsoron ganinsa a wajen...Tai k’ok’arin k’ak’aro murmushi ta sakar masa “Yaya... Barkada safiya ..!”
Murmushi bai bar saman fuskarsa ba ya amsa mata kana ya dubi writs watch d’insa yace “Looks like wata yanzu tashinta a bacci shiyasa take mun gaisuwan safiya bayan yanzun agogo ya nuna k’arfe shabiyu ne da rabi na rana..!” Ya k’arashe murmushi kwance saman fuskarsa
Murmushin da yafi kama da yak’e tai kana tace “Kuma fah haka ne ashe rana tayi already...!”
“Ina zaki sani your Highness tunda kina kwance cikin d’aki kina hutawa...!”
Ta d’an murmusa kad’an “Kai Yaya hutu ai na wajenku...”
Shid’inma murmushin yai “Ina wani hutu bayan ban jima da dawowa daga bargan dawaki ba na duba lafiyarsu....!”
Murmusawa ta kumayi tana dubansa simplicity d’insa na burgeta harga Allah... Sam bai d’auki sarauta wani aba ba... Kasancewarsa d’an sarki bai saka masa girman kai ko jin shid’in daban ne ba, ba kaman d’an uwansa Yazeed da yakeda tsananin jida mulki da isa ba... Kai gaba d’aya ma cikin yaran sarki Jamal ya fita daban, sam baida wani aibu baida tashin hankali uwa uba ga sauk’in Kai wanda kaf harta Mahmood baida sauk’in kai irin nasa dan idan jin mulki ne ma da alama Mahmood d’in duk ya d’ara sauran sabida shi sarauta mai aji yake ba kaman Yazeed wanda zaka fahimci tsantsan hauka a lamransa ba...Sannan tana iya tuna sanda Jafar ya gudu ya bar Masarautar bayan zuciyarta tayi dumu dumu cikin kogin begensa Yarima Jamal ne yaita consoling d’inta har ta d’an mance da ciwon da Jafar ya tafi ya bar zuciyarta ciki... Har abada bazata tab’a mance halaccin Yarima Jamal a gareta ba... Idanunta suka sauk’a kan Hoton zanen dake rik’e hannunsa...
D’ago zanen yai shima yana dubawa... Ta sakar masa murmushin da yafi kama da yak’e....
Dai dai lokacinda ya soma takowa gareta zuciyarta naci gaba da bugawa...
Muhibbah da isowarta kenan tai tsaye tana dubansu, lokaci guda Ta d’an matsa kad’an Ta mak’ale jikin cottons tana mai kuma b’oye zanen dake hannunta cikin rigarta....
SameenaAleeyou📚
[7/23, 9:36 PM] +234 703 453 9908: *MUHIBBAH*
*35*
*©️Sameena Aleeyou...✍🏽*
Daidai gaban Umaima yaja ya tsaya yana mai jifanta da wani irin kallo dake ci gaba da haifar mata da fad’uwan gaba... Baice komai ba sai kallon k’urilla da yake mata da matsakaitan idanuwansa da basu faye girma ba, uwa uba sam bata hango annuri saman fuskar nasa ba wanda hakan sosai ya kuma haifar mata da matsanancin tsoro wanda sam batasan dalilin jin hakan ba... Ba Umaima dake tsaye k’ik’am gaban Jamal ba harta Muhibbah dake mak’ale jikin cottons ta razana da irin kallon da Jamal keyiwa Umaima....
Zuciyar Umaima bata daina yankewa ba take k’ok’arin matsawa baya tana neman kalamai saman harshenta saidai murmushin da Jamal ya sakar mata ya sanyata fasa janye k’afafunta..
Lokaci guda yake furta “Ina kuma zakije your Highness... Did something happen..?!” Ya tambaya yana d’an bud’e idanunsa...
Murmushin da yafi kama da yak’e ta sakar masa “A’a no... Nothing has happened, babu komai...I think I left my phone in the room....I need to go get it...!” Ta k’arashe tana mai saurin juyawa da niyyan komawa d’aki saidai tuni Jamal yasha gabanta yana mai ci gaba da aika mata mayen kallo wannan karon fuskarsa a marairaice...
Ta d’ago tana dubansa k’irjinta naci gaba da bugawa, Jamal ya d’anyi k’o’arin saita kansa had’ida d’aura murmushi saman fuskarsa, lokaci guda yai stepping back yana mai furta “Did I scare you...?!” Ya tambaya yana dubanta, sihirtaccen murmushi kwance saman fuskarsa...
Bata iya cewa komai ba sai girgiza masa kai da tai alamun a’a, Jiki a matuk’ar sanyaye...
Murmusawa ya d’anyi sai kuma ya d’ago mata frame d’in yana mai furta “Zaki iya bani aron wannan..?!”
Ta saki murmushi wanda yafi kama da yak’e “Ai..Ai dama naka ne Yaya... So zaka iya d’auka ko babu iznina...”
Ya girgiza kai kad’an murmushin bai bar saman fuskarsa ba “No it’s yours Umaima... Na riga na baki ai, wannan kyauta da na miki tamkar zuciyata ne na mallaka miki idan Kinga na amsa toh ki tabbata zuciyata na amsa daga gareki...!” Ya k’arashe cikin wane irin siga yana k’ura mata idanu...
Gaba d’aya sai ta rasa gane ina kalaman nasa suka dosa, sai ta zama lost and confused....
Jamal da tuni ya fahimci hakan ya d’an sakar mata murmushi da gefen baki “Sorry, I mean kawai zan ara ne zuwa wani d’an lokaci.. I promise zan dawo miki dashi... Amma idan baki min izina ba babu yanda na iya bazan d’auka ba...!”
Sigan da yai magana dashi sai ya bata dariya, ta d’an murmusa kad’an tace “Aw haka ne..? Toh na baka aro har lokacinda kaji ka dawo min dashi dan rad’in kanka..!”
Yai murmushi mai d’an bayyana hak’wara wannan karon “Gaskiya naji dad’i K’anwata... Thank you...!” Ya k’arashe yana mai kasheta da wani irin duba wanda Ke kuma haifar mata da wane irin yanayi...
Shiru ya d’an ratsa tsakani kaman babu mai cewa komai... Jin shirun yai yawa ya sanya Umaima d’agowa da niyyan magana saidai shima Jamal d’in maganan tasoyi... Kowa yai shiru dan baiwa juna dama suyi magana...
Jamal yace da ita “You go first...!”
Ta girgiza kai alamun a’a sai kuma ta d’ora da “Dama Babu komai... Kawai zan shige ne...!”
Ya jinjina kansa kad’an yana mai kuma karantar Ta, lokaci guda yai gyaran murya yana mai gyara tsayuwarsa “Umaima there’s something you need to know... Something I’ve been keeping for a long time now... Umaima I don’t know if you’ve ever noticed... But...!” Ya d’an fuzar da huci a hankali had’ida murza tafukan hannunsa “Wait, how do I put it...!”
D’an dubansa tai k’irjinta naci gaba da bugawa lokaci ba tareda Ta iya furta komai ba...
Jamal ya d’an kauda kai gefe yana mai sauk’e fuci a hankali..
Lokaci guda ya kuma juyowa yana dubanta “Bansan yaya zaki d’auki lamarin ba k’anwata, but I think lokaci yayi da zan sanar dake...!!” Ya k’arashe cikeda tsananin kulawa...
K’ok’arin saita kanta tai kad’an “Yaya mai kake son sanar dani you making nervous already... Allah Sa ba wani abin nai maka ba..?!” Ta k’arashe tana rau rau da idanu...
Ya sakar mata murmushi mai taushi kana yai mata nuni da kujera “Sit down..!”
Babu musu Ta isa ta zauna...
Shima ya k’arasa ya zauna yana mai aje Frame d’in zanen dake hannunsa gefen kujeran wanda tuni idanun Muhibbah sun sauk’a kai...
Jamal ya d’anyi gyaran murya kad’an “Umaima I fell in love...!!!” Yai maganar kaman mai tsoron yinta..
Tamkar sauk’an aradu haka taji batun... Tai saurin d’agowa tana dubansa, fuskarta d’aukeda alamun tambaya...
Jinjina mata kai yai kad’an alamun jaddadawa “Yes I fell in love with you... I don’t know when or how... But all I’m certain of shine na aukawa soyayyarki... It might sound weird or maybe ridiculous... But, believe me I’m deeply in love with you... I love you so much that I couldn’t hold myself back anymore... I love you...!!” Ya k’ara fad’i yana mai duban cikin idanunta wannan karon sosai had’ida zamowa kad’an daga cikin kujera...
Har lokacin shock bai saketa ba... Ta kasa aminta da abinda takeji... If there’s one person da zatazo tai soyayya dashi cikin yaran Yayan mahaifiyarta, that person should be Mahmood... Shine mutumin da take so da duka zuciyarta tun tana k’aramar yarinya koda ta fahimci su d’in were never meant for each other sai ta hak’ura tai k’ok’arin yakice soyayyar Mahmood sannan bayyanar Jafar cikin rayuwarta ya kuma sa ta mance babin Mahmood ta kuma aminta yarinta ne yasa takejin bata da miji bayan Mahmood...But Jamal, yeah they get along and he has all the qualities da ko wace mace zataso ace ya zama mijinta amma batajin sonsa ko kad’an cikin zuciyarta, da zai tsaya matsayin Yayanta da yafi mata sauk’i... Muryarsa ne ya dawo da ita daga duniyar tinanin data tafi...
“You don’t need to answer me right away... Ki samu lokaci kiyi tunani, at least yau zanyi bacci mai dad’i na sanar da masoyiyata abindake cikin zuciyata....!” Ya k’arashe yana mai k’ok’arin mik’ewa tsaye ya nufi k’ofa... Har ya kusan k’ofa ya juyo kaman wanda yai mantuwa daidai nan Zahra dake haurowa daga k’asa ta nufo parlorn nan idanunta suka sauk’a kan Muhibbah dake da fitowarta kenan daga cikin labule tana duban abinda Jamal zai d’auka tana addu’an Allah yasa kar ya d’auki zanen nan har sai ta comparing...
Zahra ta dubeta da mamaki murmushi saman fuskarta ta kirawo sunanta...
Ai a d’ari Muhibbah ta daka tsalle ta isa kusan Zahra ba tareda ta bari Jamal dake k’ok’arin waigowa ya ida waigowa ba...
Da mamaki Zahra ke dubanta, saidai kafin Zahran tai magana Ta katseta da fad’in “I... I was looking for you dama... Thank Goodness I found you here..!”
Zahra ta d’an dubeta “Is something wrong...?!”
Tai saurin girgiza kai alamun a’a sai kuma tace “About our Spanish classes.. Yaushe zamu fara...!” Ta k’arashe tana mai fari da idanu...
Murmusawa kad’an Zahra ta d’anyi kana tace “Wai dama wanann ne ai kin riga kin fara Tia coz already kin iya gaisuwa kuma kin fara tsintar wasu words...!”
Muhibbah ta murmusa hannun Zahra cikin nata take furta “Yeah dukda haka dai nafi gane na shiga class, kinsan ance cikar d’alibi saida aji...!” Suka d’an dara kad’an a tare daidai sanda suke isowa cikin parlorn....
Kallo guda zakaiwa Umaima ka fahimci ba daidai take ba... Shiko Jamal murmushi saman fuskarsa yake dubansu, Zahra ce ta soma gaidashi... Ya amsa da sakin fuska yana mai dafa kanta da hannu guda yayinda Muhibbah ta sauk’e idanunta kan d’aya hannun nasa dake rik’e da zanen....Kauda kanta gefe kurum tai had’ida rintse idanunta a hankali... Shikenan Jamal ya b’ata mata shirinta, yanzu bazata ita comparing zanen ba... Mai zatai yanzu...?
Bata kaiga nemo amsa ba ta sinkayo muryar Zahra na tambayar Umaima ko lafiya take Dan tuni Jamal kam yayi ficewarsa.....
Zahra ta kuma dafa Umaima da Ta zauna gijif cikin kujera tana faman k’irga ‘yan yatsun hannunta... “Aunty Umaima.. Lafia, Wai meke faruwa....? Are you sure you’re okay...?!”
Murmushin k’arfin hali Ta sakarwa sanin cewa bazata daina tambayar nata ba kana tace “Babu komai Zahra... I’m fine, kawai yau Uncle d’inki ya karb’e kyautar da ya bani ne...” Ta k’arashe tana mai duban ma’ajiyan frame d’in...
Zahra ta d’anyi Jim sai kuma tace “Shiyasa kike fushi.. Amma maiyasa Uncle Jamal zai amshi frame d’in nan bayan ya jima da baki.. Kodai naje na amso miki ne..?”
Ta murmusa kad’an sai kuma tace “No it’s okay, ni na bashi da kaina... I think kaina Ke ciwo, zan koma d’aki na kwanta...!”
Muhibbah ta tako gabanta kad’an tana mai dubanta “Do you need a pain killer..?”
Ta girgiza kai alamun a’a “Idan nayi bacci shikenan... Na gode da kulawarku..!” Ta k’arashe tana mai mik’ewa tsaye da k’yar ta nufi d’aki...
Suka bita da kallo har ta shige kana Zahra ta sauk’e ajiyan zuciya tana mai furta “She’s like a mother to me... Ina sonta sosai, Aunty Umaima nada zuciya mai kyau just like you Tia...!” Ta k’arashe tana duban Muhibbah dake tsaye..
Muhibbah ta murmusa kad’an had’ida zama gefen Zahra, Zahra taci gaba da fad’in “She lost both her parents when she was very young, Maami itace mahaifiyarta kuma itace mahaifinta... Kaman yanda naji labari tun tana jaririya Maami tazo da ita cikin Masarautar nan...”
Muhibbah ta gyara zama sosai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 65